Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan siyo mata magani. Ba jimawa ya dawo da katan ɗin ruwan jakar da yoghurt da kayan fruits. Ganin bata farka ba ya dubi Nurse ɗin da take duba ruwan da aka saka mata ya ce zai je ya dawo. Sai da ya yi Sallar isha'i sannan ya dawo bayan ya siyo mata Balango mai yawa a leda. Zama ya yi akan kajerar dake fuskantar gadon da take a kwance ya zaro wayarsa daga aljihu wadda ake ta kira tun zuwansa asibitin ba jima wa. Missed call ɗin Ummi (Yayar Abba) ya gani sai na Uncle Umar rurutu da kuma na wani abokin kasuwancinsa. Bai bi bayan kiran ɗaya daga cikinsu ba saboda wani dalili nasa, sai ma Numbern budurwarsa daya kira. Ringing biyu ta d'aga, bayan sun gaisa ya ce "Halima dan Allah idan babu damuwa zan zo gida na karb'i aron blanket da darduma, muna asibiti ne Neehal babu lafiya." Halima ta ce "Subahanallah, me ya same ta?" Uncle Usman ya ce "Zazzaɓi take shine aka bamu gado." Halima ta ce "Allah ya sauqaqe, ka zo ka karb'a babu matsala." Godiya ya mata sannan suka yi sallama ya katse wayar. Wata Nurse ya ƙara ba wa amanar Neehal sannan ya bar asibitin. Gidan su Haleemah da ɗan nisa daga asibitin, hakan yasa sai da tara ta wuce ya dawo da kaya a hannu, dan har da su plates da cups da spoons sai da Halima ta haɗo shi da su, shi kuma ya biya ya siyo wa Neehal sabon brush da sosan wanka da su sabula da ƙaramin macLean gami da takalmi slifas. Sai wajen goma Neehal ta farka a zabure cikin dashashshiyar muryarta take faɗin "Uncle ka yi haquri dan Allah ba zan kuma ba." Uncle Usman ya tashi da sauri yana cize lips ɗinta saboda takaici ya ƙasara gaban gadon. Kama hannunta ya yi ya ce "Neehal!" Neehal ta buɗe kumburarrun idonta da sauri ta ce "Uncle ɗina." Uncle Usman ya ce "Na'am Neehal, sannu kin ji, ya jikin naki?" Gyaɗa masa kai ta yi tana bin shi da kallo alamun tana cikin mamakin ganin sa. Shafa fuskarta ya yi ya ce "I'm coming Baby." Fita ya yi da sauri ba jimawa sai ga shi sun dawo da likita, dudduba ta ya yi bayan ya mata sannu sannan ya cire mata drip ɗin hannunta da ya ƙare a lokacin. Magungunan da Uncle Usman ya siyo Doctor ya nunnuna masa wanda zai bata yanzu. Uncle Usman ya masa godiya sannan ya fita. A hankali Neehal ta ce "Uncle zan sha ruwa." Uncle Usman ya tayar da ita zaune ya sa mata filo a bayanta ta jingina da shi yana mata sannu. Ruwa ya dauko ya buɗe mata sannan ya kafa mata a baki, kaɗan ta sha ta cire robar daga bakinta. Lumshe ido ta yi ta ce "Uncle ina Uncle Umar da Aunty Fauziyya?" A dak'ile Uncle Usman ya ce "Suna gida." Neehal ta buɗe idonta da ya cika da hawaye ta ce "Please Uncle ka ba su haquri su daina duka na." Uncle Usman ya ce "Shikenan kar ki yi kuka kin ga baki da lafiya." Neehal ta gyaɗa masa kai ta ce "Uncle ka kira mun Aunty, idan na cewa Uncle Umar ya kira mun ita baya kiran ta." Uncle Usman ya ce "Yanzu dare ya yi ki bari sai da safe in Allah ya kai mu." Zata kuma magana ya katse ta da faɗin "Ki yi shiru haka kin ga baki da lafiya." Neehal ta ce "Toh." Ya ce "Yawwa good girl mu je in kai ki ki yi brush sai ki ci abinci." Kamata ya yi a hankali ganin yanda take yamutsa fuska alamun tana jin ciwon jikinta ya kai ta toilet ɗin ya taimaka mata ta yi brush, sannan ta yi fitsari ya kama ta suka fito. Zaunar da ita ya yi ya ɗauko balangon da ya siyo ya juye a plate ya janyo kujera gabanta ya fara bata a baki, kaɗan ta ci ta ce ta k'oshi saboda bakinta da babu daɗi. Banana ya bata ta ci ɗaya da ƙyar, sannan ya bata magungunanta ta sha ta kora da ruwa. Bayan 5 minutes ya kwantar da ita sannan ya dauk'o blanket ya lullub'e mata jikinta. Neehal tana duban sa ta ce "Yaushe ka zo Uncle?" A tak'aice Ya ce "D'azu, inane yake miki ciwo yanzu?" Neehal ta ce "Kaina da duka jikina." Uncle Usman ya ce "Ki rufe ido ki yi bacci, Insha Allahu in kin tashi da safe zaki ji kin warke." Neehal ta gyaɗa masa kai tare da murmushi cikin jin daɗin ganin sa. Shi ma murmushin ya yi ya ce "Ki yi addu'a kin ji daughter." Neehal ta gyaɗa masa kai tare da lumshe idonta.










Washegari bayan Uncle Usman ya dawo daga masallaci ya tarar Neehal ta tashi zaune. Da mamaki ya ce "Har kin tashi?" Neehal ta ce "Ehh, ina kwana Uncle." Uncle Usman ya ce "Ai sai an yi Sallah ake gaisuwa." Neehal ta fara ƙoƙarin saukowa daga kan gadon tana faɗin "To bari na je na yi alwala sai na yi sallah." Cikin jin daɗi Uncle Usman ya ce "Jiki ya yi sauqi kenan Masha Allah." Neehal ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet, duk da bata gama jin jikin nata dai-dai ba amma zazzaɓin da ciwon kai sun mata sauqi sosai, jikinta ne dai take jin shi da ɗan tsami saboda dukan da ta sha. Bayan ta fito ta tayar da Sallah akan darduma, duk da bata da Hijab sai ɗan kwalinta ta yafa. Uncle Usman ya zuba mata yughurt ɗin da ya siyo jiya a cup ya bata. Ta sha sosai kuwa saboda da yunwa ta tashi. Wajen 7 da wani abu sai ga Haleemah da ƙanwarta sun zo duba Neehal, dan jiya da Uncle Usman ya je ya faɗa mata asibitin da suke, amma ya yi mamaki lokacin data kira shi ta faɗa mishi ta shigo asibitin ya zo ya ɗauke ta, domin bai taɓa tunanin zuwanta da safiya haka ba. Da k'aton tea flaks ɗinta kuwa wanda ta ciko da ruwan zafi kamar ta san za su buƙata. Basu wani jima ba suka tafi. Tea mai kauri Uncle Usman ya haɗa wa Neehal ta sha sannan ya bata magungunanta suma ta sha. Cikin dabara Uncle Usman yake tambayar Neehal tana faɗa masa irin zaman da take a gidan Uncle Umar. Sosai ransa ya ɓaci fiye da jiya da ya ji irin azabtar da Neehal da Aunty Fauziyya take. Wayarsa ya ɗauko ya bi kiran da Uncle Umar ya masa jiya, ringing ɗaya Uncle Umar ya d'aga tare da faɗin, "Usman wannan wanne irin iskanci ne, zaka ɗauke yarinya tun jiya kuma dan wulaqanci inta kiran ka ka ƙi d'agawa, ina ka kai ta to?" Uncle Usman ya ce "Asibiti na kai ta dan ceto rayuwarta." Ya faɗa masa sunan asibitin sannan ya kashe wayar. Da ruwan zafin da Halima ta kawo Uncle Usman ya haɗa wa Neehal ruwan wanka ta yi, kayan jikinta da ta cire ya ce ta mayar anjima zai ɗauko mata wasu a gidan Uncle Umar. Wajen 8:40 Likita ya zo ya ƙara duba ta sannan ya mata allura, tana kukan allurar bacci ya ɗauke ta.










Ganin ta yi bacci Uncle Usman ya lalubo Numbern Aunty A'isha ya kira ta, sai da ta kusa katsewa sannan ta d'aga bakinta ɗauke da Sallama. Uncle Usman ya amsa ya ƙara da faɗin "Ina kwana Aunty dafatan kin tashi lafiya, ya su Hajiya?" Aunty A'isha ta ce "Lafiya k'alau Uncle Usman, su Hajiya suna nan k'alau, ya kwana biyu da bayan saduwa? inata kiran wayarka data Uncle Umar duk bana samun ku dafatan dai lafiya?" Uncle Usman ya ce "Lafiya k'alau, ai yanzu na koma Niger da kasuwancina ne, to idan ina can sai na sauke wannan layin, ina ta son na kira ki amma sabgogi sun sha mun kai, jiya_jiya ma na shigo garin." Aunty A'isha ta ce "Allah sarki, Allah ya taimaka ya ba da sa'a, wancan satin ai na fita daga takaba." Uncle Usman ya ce "Ikon Allah, lokaci ba wahala har kin fita, Allah ya ji k'an su Yaya." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, a satin nan ma nake son shigowa Kano zamu zo siyayya bikin Sadiya ya kusa, ya labarin Neehal kuwa? kana zuwa kana ganin ta? Kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, kwanaki ma na so zuwa na ganta Hajiya ce ta hana ni ta ce in bari na fita daga takaba tukunna." Uncle Usman ya ce "Hmm, bari kawai Aunty wallahi Neehal wahala kawai take sha a gidan Ya Umar gurin Matarsa, yanzu ma muna asibiti bata da lafiya saboda dukan da suka mata jiya." A ruɗe Aunty A'isha ta ce "Subahanallahi, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, asibiti kuma? Wannan wanne irin duka ne haka? ashe shi yasa jiya na wuni da tunaninta a cikin zuciyata, har na kasa daurewa sai da na yi zancenta a gida, Hajiya ta ce na kwantar da hankalina ai na kusa zuwa na ganta, ya jikin nata yanzu?" Uncle Usman ya ce "Da sauƙi Alhamdulillah, yanzu ma bacci take yi, Nima shekaran jiya na kira Ummi mun yi waya ne ta ce dan Allah in daure in je in dubo mata Neehal, ta tura ƴaƴanta sun ce ba su san gidan ya Umar ɗin ba, ita kuma tana fama da ciwon ƙafa baza ta iya zuwa ba, shine na zo na tarar da wannan abun takaicin. Wallahi Aunty A'isha baki ga ni ba, abun tausayi gaba-d'aya Neehal ta lalace ta yi baƙi ta rame duk ta fita hayyacinta." Aunty Aisha tana hawaye ta ce "Shi yasa naso tafiya da ita amma Uncle Umar ya hana ashe rabon wahala ne yake kiranta." Uncle Usman ya ce "Kar ki damu Aunty daga nan Gombe zamu zo na kawo miki Neehal da zarar ta ji sauƙi, ai kuma ta gama zama a gidan Ya Umar." Aunty A'isha ta ce "Kana ganin Uncle Umar ɗin zai yadda Neehal ta dawo gurina da zama?" Uncle Usman ya ce "Kar ki damu da wannan na san me zance masa kuma dole ya bari. Amma dan Allah Aunty kar ki tada hankalinki fa komai ya zo ƙarshe ai dan zuwa gobe ma za'a iya ba mu sallama tunda ta ji sauƙi sosai." Aunty A'isha ta ce "Shikenan Usman na gode sosai, idan ta tashi daga baccin ka kira ni dan Allah." Uncle Usman ya ce "insha Allah zan kira ki, a gaishe da su Hajiya da Amarya, ace ina mata fatan Alkhairi kafin na zo." Aunty A'isha ta ce "Duk za su ji, sai anjima." Daga haka ya katse wayar. Ummi ya kira ya sanar mata halin da ake ciki, amma ya ɓoye mata wasu abubuwan dan kar hankalinta ya tashi sosai tunda ba ishashshiyar lafiya gare ta ba. Itama ta jajanta abun sosai ta kuma yi Allah wadai da halin Umar da Fauziyya, har ma da Ƴan'uwansu na cikin Kano wanda ko waiwayar Neehal ɗin ba sa yi alhalin suna gari ɗaya. Ta kuma yi na'am da mayar da riqon Neehal hannun Aunty A'isha da Usman ya ce mata zai yi, amma kafin su tafi Gomben ta ce ya kai mata Neehal ɗin ta gan ta..........✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:48] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_










*3️⃣3️⃣*










Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














...........Wajen ƙarfe goma na safe sai ga Uncle Umar a asibitin, Uncle Usman ya je ya shigo da shi. Tun kafin su shigo ɗakin ya fara masifa, Uncle Usman dai bai tanka masa ba. Har lokacin Neehal bacci take abunta. Uncle Usman ya zauna yana yi wa Uncle Umar wani kallo ya ce "Wallahi Ya Umar ka matuƙar ba ni mamaki ka kuma ba ni kunya da har kake kallo ana azabtar da Neehal amma baza ka hana ba sai ma tayawa da ka yi. To idan ka manta bari in tuna maka, mahaifin yarinyar nan shi ya fito da mu daga cikin duhun rayuwa zuwa mai haske, cinmu, shanmu, suturarmu, iliminmu, bai taɓa nuna gazawar sa ba ko a fuska balle a aikace, alhalin kuma mu ba dolensa ba ne kyautatawa ce kawai irinsa. Mutumin da yay maka duk waɗannan abubuwan sannan ya ɗora da samar maka aiki ya baka muhallin zama, hidimar bikinka rabi da kwata shi ya yi ta, dan ba ya raye ɗiyarsa guda ɗaya tak a duniya ta cancanci azabtarwa daga gare ka? A tunani na ko wani ka ga yana mata haka sai inda ƙarfin ka ya ƙare a ɗaukar mata mataki." Uncle Umar ya yi shiru kawai yana kallon Uncle Usman amma ya rasa bakin magana. Uncle Usman ya Tab'e baki ya ce "Abu na ƙarshe daga rana irin ta yau Neehal ta bar hannunka da zama, zata koma inda ake sonta da k'aunarta saboda Allah, tun da dama kai dan dukiyarta ka karb'i riqon ta, to ka riƙe dukiyar amma ita dai baza ta ƙara kwana a gidanka ba." Cikin fusata Uncle Umar ya ce "Ni kake faɗa wa waɗan nan maganganun Usman? Uban wa ya faɗa maka dan dukiyarta na karb'i riqon ta, wato an zugo ka zaka mun rashin kunya ko?" Uncle Usman ya yi murmushi ya ce "Calm down bro, abun duk bai kai haka ba, karɓe Neehal daga hannunka ba ya nufin za a karɓe dukiyarta daga hannunka ba ne, za'a bar maka kacigaba da juya ta domin wadda zata ɗauki Neehal bata buƙatar dukiyarta dan a gurinta ba komai ba ce." Uncle Umar ya mike tsaye ya ce "Wai me kake nufi da nine Usman eye? Wato kana so ka ce son cinye dukiyar Neehal nake son yi ko? To wallahi babu inda zata a hannuna zata cigaba da zama har auranta." Uncle Usman ya ce "Hmmm sai ku ji daɗin kashe ta kenan kai da matarka da duka ko? Yaya Umar, Yaya Fateemah bata cancanci haka daga gare ka ba, ka ji tsoron Allah ka tuna kai ma zaka mutu kuma kai ma ka haifi ƴaƴan nan. Yarinyar nan mai ta sani a rayuwa me ta tsare muku da kuka mayar da ita baiwa a gidanku, kuma wallahi bana ganin lefin Fauziyya sosai na fi ganin naka dan da ka tsawatar mata ba ta isa ta yi wa Neehal haka ba, amma babu komai rayuwa ce Duk *abin da mutum ya shuka shi zai girba* ." Uncle Umar cikin borin kunya ya ja tsaki ya fice daga ɗakin. Sai wajen 12 Neehal ta tashi daga baccin, bayan ta wanke baki Uncle Usman ya bata abincin da ya siyo mata ta ci sannan ta sha maganinta. Wayar Aunty A'isha ya kira ya haɗa su, Neehal ta dinga murna jin Muryar Aunty'nta, ta dinga tambayarta ina Maman Abuja. Bayan sun gama wayar ya kira Ummi ya haɗa su itama. Da kansa ya je har gidan Uncle Umar ya tattaro duk wani abu na Neehal ya haɗa a trolley ɗinta ya baro su daga gidan. Aunty Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Umma ta gai da Ashsha, ala raka taki gona." A yammacin ranar aka sallame su daga asibitin tun da Neehal ɗin ta warware sosai, sai dai zata cigaba da shan magungunanta. Gidansu Haleemah suka je ya kai mata kayayyakin da ta ba shi tare da yi mata godiya sannan suka wuce Gabasawa. Ummi ta yi kuka sosai ganin yanda Neehal ta lalace ga shatin duka b'aro_b'aro ajikinta. Kwanan su ɗaya suka wuce Gombe, nan ma Su Aunty A'isha sun sha kuka da ganin yanda Neehal ta koma. Hajiya ta dinga ja wa su Aunty Fauziyya alkaba'i. Lokacin da Neehal ta koma Gombe Mama ba sa garin ta je Saudiyya Umara daga nan ta wuce London, sai daf da bikin Aunty Sadiya ta dawo. Lokacin Neehal ta fara dawo wa hayyacinta saboda kulawar da take samu a gurin Aunty A'isha da Hajiya, har an saka ta a makaranta boko da islamiyya. Mama ta yi murna sosai da ta ga Neehal ta dawo gurin Aunty A'isha da zama. Bayan bikin Aunty Sadiya Neehal ta mak'ale wa Mama ta bita Abuja, wannan zuwan shine sanadiyyar komawarta hannun Mama gaba-d'aya da zama. Dama zuwa Kano siyayya da su Aunty A'isha suka yi ta haɗu da wani Alhaji da Allah ya yi wa matarsa rasuwa shekarar da ta wuce, shima bai taɓa haihuwa ba ya ce yana son ta kuma baya son a ja bikinsu da nisa tun da su ba yara ba ne. Cikin wata biyu bayan fahimtar juna da sukai da kuma duk wani binkicen da ya kamata aka ɗaura Auran Aunty A'isha da mutumin ta tare a nan Kano. Neehal tana jin daɗin zama a gurin Mama sosai dan babu abun da suka rage ta da shi na jin daɗin rayuwa ita da Daddy. Makaranta mai tsada Daddy ya saka ta. Cikin lokaci kaɗan Neehal ta koma Neehal ɗinta ta ainihi mai rawar kai da surutun tsiya, hakan ya sa ba sa shiri ko kaɗan da Ameen, a duk lokacin da ya zo gida to ba ta da sukuni ta dinga kumbure_kumbure a ɗaki tare da Allah Allah ya yi ya tafi. Tun Neehal tana tunawa da Ahmad a ranta har ta fara mantawa shi.






Neehal ta tashi yarinya mai hankali da nutsuwa da biyayya, ga addini da tsafta, dan Mama duk ba baya ba ce a cikin waɗannan abubuwan. Dawowar Neehal hannun Mama sai dangin Mama suka ninka soyayyarsu a gareta, kowa ka ji yana Neehal ɗin Maman Abuja. Nan da nan Neehal ta ƙara saba wa da su, shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, saɓanin dangin Daddy da ba kowa ke son ta ba, musamman Maman Hameedah ƙanwar Daddy k'iri_k'iri take nuna tsanarta ga Neehal. Watarana Mama suka shirya ita da Neehal suka zo Kano, duk wani makusancin Neehal da Mama ta sani sai da ta kai ta gidansa dan ta gaishe shi, amma babu inda suka samu tarb'ar arzik'i sai gurin Ummi yayar Abba sai gidan wani cousin ɗin Abba wanda suke shiri da Abba sosai mai suna kawu Musa, shi ma dan yana gidan suka je ne, da dan ta matarsa ne ita ma baza su samu tarb'ar arzik'i ba. Uncle Umar kuwa da suka je gidansa cewa ya yi kar Neehal ɗin ta ƙara zuwa inda yake tun da ta zaɓi bare akan sa. Haka dai suka dawo Abuja rai babu daɗi, sosai Mama ta ji takaicin yanda ƴan'uwan mahaifan Neehal suka banzatar da ita, ta yi Allah wadai da zumuncin wannan zamani na ganin ido, dan ta san da iyayenta suna raye baza su mata haka ba. Neehal cikin danginta na Uwa da Uba da Uncle Usman da Ummi kawai suke waya, sai kawu Musa wani lokacin, lokaci zuwa lokaci kuma tana ziyartar Ummi. Riqon da Mama take wa Neehal ko ɗan data haifa da cikinta iya shi zata masa, Mama tana k'aunar Neehal sosai har cikin ranta, haka ma Daddy. Babu yanda za ai ka gane ba su suka haife ta ba, wanda bai sani ba ma ba ya gane wa. Dan ko a school da *Fateemah Muhammad Tafida* take amfani. Sunan Daddy kenan (Muhammad Tafida) amma Neehal da sunan Abbanta take amfani, Tafidan kawai ta ƙara, da yake sunan ɗaya ne duk Muhammad shi yasa ba'a gane wa. Daddy yana da kuɗi sosai kasancewar ya riƙe matakai na soja kala_kala har zuwa matakin ƙarshe wato General, kuma dama can zuri'arsu masu arzik'i ne. Asalin su Daddy su ma fulanin Gombe ne kuma ƴan'uwa ne na jini da su Mama, da Mahaifin su Daddy da Hajiyar su Mama cousin ne. Su Daddy su uku ne a wajen mahaifinsu, Yayansa Namiji mai suna Hamza sai shi, Haj.Saratu Maman Hameedah ita ce Autarsu. Iyayensu duka sun mutu ba jima wa, su ma su Mama mahaifinsu ya rasu daf da bikin Aunty A'isha da Abba. Daddy ya fara harkar siyasa, amma ganin siyasar ƙasar nan babu Allah a cikinta Mama ta ce gaskiya ya daina tun da dama bai yi wani suna acikinta ba, ba dan ya so ba haka ya haqura sai dan farincikin Maman kawai. Ameen shi kaɗai Mama da Daddy suka haifa a duniya, daga kan shi Allah bai ƙara ba su haihuwa. Kamar Ameen da Mama ɗaya sak tamkar an tsaga kara, bambamcinsu kawai shi Namiji ne Mama kuma mace ce, haka ma a halaye da d'abi'u duk nata ya yo, kama daga kan tsafta, addini, kyauta, iya mu'amala da mutane, tsare gaskiya ko mai ɗacinta, da kuma rashin tsoro. Ko dan shi Namiji ne,har ya fi Mama rashin tsoro da dakiyar zuciya, sai kuma Allah ya ɗora masa miskilanci tun yana ƙaramin sa. A ɓangaren aiki ne ya gaji Daddy shi ma ya zama soja. Sosai Neehal take tsoronsa, idan ya zo gida weekend sai ta zama salihar ƙarfi da yaji, dan abu kaɗan za tay ya balbale ta da faɗa dan yana da zafin zuciya, amma fa duk zuwan da zai yi da ƙatuwar ledarsa ta tsarabar Neehal yake zuwa, idan ƴan fara'ar suna kansa wataran yana sakar mata fuska. Neehal kam tana son Yayanta sosai, tana jinsa tamkar yayanta uwa ɗaya Uba ɗaya. Komai nata Yayanta Yayanta, sai dai wani lokacin in ta je gurinsa ya koro ta, ta dawo tana aikin turo baki, Mama ta ce mata "Dama wa ya aike ki gurinsa kin san hali." A hakan dai shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su. Shekarar Neehal shida a gurin su Mama Daddy ya yi retire, hakan yasa suka dawo Kano da zama gaba-d'aya, lokacin Neehal ta gama Secondary school tana 17_18 years. Ta yi saukar haddar Alqur'ani mai girma shekara biyu da suka wuce. A gurin registration ɗin Jamb suka haɗu da Haneefah, har suka yi musayar contact ɗin juna, sai da za su tafi gida suka gane ashe ma unguwarsu ɗaya. Tun daga time ɗin suka zama k'awaye sosai har Mama suke zumunci da Mommy'n Haneefah, ita ma Haneefah marainiya ce, mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama. A wannan lokaci Allah ya yiwa Ummi Yayar Abba rasuwa, Neehal ta ji mutuwar sosai kuma ta sha kuka. Duk da tarb'ar da Mama ta samu a gurin dangin Neehal bata daina kai ta tana gaishe da su ba, tun da jininta ne su, babu yanda zata yi da su, daga baya da Neehal ɗin ta girma da kanta ta cewa Mama dan Allah ta daina kai ta, ganin yanda suke wulaqanta ta da nuna halin ko'in kula a gareta kamar wadda ta je neman wani abu gurinsu, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa tako wa gidan Mama da sunan ya zo ganin Neehal. Ita kuwa Neehal tuni ta cire su daga ranta, yanda suka manta da ita a rayuwarsu itama ta manta da su. Da Uncle Usman ɗinta kawai take zumunci wanda shi ma ya yi aure suna zaune da matarsa a can Niger. Neehal kyakkyawa ce doguwa mai dirin jiki dai_dai misali da dogon gashi, ga ta ƴar gayu ce dan tana son gayu sosai, ko da yake ba ta ɗauka a ƙasa ba dan Mama ma akwai gayu da kwalliya, zai yi wahala ka ga hannu da ƙafarta babu jan lalle idan ka ganta baza ka ce ta haifi Ameen ba, ga iya girki, shi yasa duk ta kanainaye zuciyar Daddy, ba ya ganin kowacce mace sai ita. Aunty A'isha ta haifi yarinyarta mace mai suna Maryam, Aunty Sadiya ma ta haihu ɗanta Namiji.










Tun da Neehal ta fara zama budurwa Ameen ya daina sakar mata fuska kwata_kwata, wani lokacin kuma sai ta fito zata unguwa sai ya ce sai ta koma ta canzar shigar da ta yi ba zata fita a haka ba, babu yanda ta iya haka zata koma ta sake. Sannan ko ya ya ji k'amshin turare a jikinta kuwa sai ta koma ta sake wanka wai babu kyau ba zata fita tana k'amshi ba, janbaki wannan idan tasa sai ya ce sai ta goge shi. Mama da ta ga abun na

Please Login or Register in order to submit comment