Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni, dan Allah Mama ki tashi karki tafi ki bar ni., Mama! Mama!..." Aunty A'isha ta zo ta janye ta tare da rungume ta, ta shiga rarrashinta cikin dauriya. Dan itama hankalinta ba a ƙaramin tashe yake ba na ganin halin da Maman take ciki, ta umarci Zulai dake tsaye ta ɗauko ruwa mai sanyi a shafawa Maman ko Allah zai sa ta farfaɗo. Hajiya kuwa bata motsa ba, dan bata jin idan ta tashi ƙafafunta zasu iya ɗaukar gangar jikinta balle har su yi tafiya, sai salati take yi tare da duk addu'ar da ta zo bakinta cikin matuƙar gigita na wannan mummunan al'amarin. Aunty Sadiya ta bar jikin Mama ta ɗauko wayarta ta shiga kiran Numbern Ameen, tana shiga amma ba ya ɗauka. Aunty Sadiya ta karɓi ruwan da Zulai ta kawo ta fara shafawa Mama a fuska, amma ko alamar zata motsa ba su gani ba. Hankali a tashe suka ɗauke ta sukay Mota dan kai ta asibiti. Ganin yanda aka ɗauki Mama kamar gawa ya ƙara tayar da hankalin Neehal, stress ɗin sun mata yawa, ga tashin hankalin tafiyar da aka yi da Daddy ga halin da Mama take ciki ga kuma dunbin damuwar dake cunkushe a cikin zuciyarta, hakan yasa ta sume itama. Sai daukar ta aka yi aka haɗa da Mama aka kai su asibitin.








*AFTER TWO HOURS*














*HOSPITAL*


A hankali Neehal ta buɗe idonta tana kallon saman ɗakin da take na wasu sakanni, sannan ta juyo da kanta gefen damanta domin fahimtar gurin take. Aunty A'isha dake zaune a kujerar gaban gadon marasa lafiya ta rafka tagumi ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi tsaye cikin sauri ta ƙarasa kusa da Neehal ta kama hannunta ta ce. "Sannu Neehal, kin tashi? Bari a kira Doctor." Neehal ta d'aga mata kanta dak'yar, tana so ta tambaye ta ina Mama amma kuma ta kasa motsa bakinta da niyyar magana, ga wani irin ciwon kai da kanta ke yi mata. Aunty A'isha ta fice daga ɗakin, Hajiya dake zaune akan sallaya ta taso ta shiga yiwa Neehal sannu, Neehal ta gyaɗa mata kai kawai tare da mayar da idanunta ta lumshe. Har lokacin tana jin nauyin da ƙirjinta da yay mata gami da zafin zuciya. Bayan mintuna kaɗan Aunty A'isha suka dawo tare da wani likita, ya dudduba Neehal ɗin tare da yi mata ƴan tambayoyi, ta amsa masa da kai kawai ta nuna masa kanta da ƙirjinta a matsayin inda yake yi mata ciwo. Ya cire mata drip ɗin hannunta sannan ya cewa Aunty A'isha ta bata magungunan da suka siyo mata, amma su bata ko da tea ne ta fara sha. Zai je ya haɗo allura ya dawo yay mata. Sukay masa godiya shi kuma yay mata addu'ar samun sauƙi. Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi zaune ta kuskure mata baki, sannan ta haɗa mata tea ɗin ta bata ta sha. Da ƙyar Neehal take had'iye tea ɗin saboda ɗacin da take jin yay mata a bakinta, kaɗan ta sha ta ɗauke kanta. Aunty A'isha ta bata magungunanta ta sha sannan ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Ta dubi Aunty A'isha cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Ina Mama?" Aunty A'isha ta ce. "Tana Emergency na asibitin nan sun bata gado, amma jikin nata da sauƙi yanzu." K'walla ta taru a idon Neehal, kamar zata yi kuka ta ce. "Ina son na gan ta." Aunty A'isha ta ce. "Gurin da take ba'a bari a shiga, kin ga Hajiya ma tun d'azu take naci sun hana ta shiga, sun ce sai ta farfaɗo za'a samu ganin ta, amma Sadiya tana gurin, da zarar ta farfaɗo zata kira mu ta sanar mana." Neehal ta fara hawaye amma bata ce komai ba. Aunty A'isha ta ce. "Mene abun kuka kuma ke da baki da lafiya? Ki kwantar da hankalinki zata samu lafiya Insha Allah, karki saka damuwa a ranki ki ƙarawa kanki ciwo." Neehal ta gyaɗa mata kai sannan a hankali ta ce. "Ƙarfe nawa? Ina son na yi Sallah Aunty." Aunty ta ce. "Ƙarfe tara na dare, mu je in kaiki toilet ki yi alwala ko in kawo miki ruwan nan ki yi idan baza ki iya tafiya ba?" Ta taune lip ɗinta sannan ta ce. "Zan iya zuwa toilet ɗin." Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi da ƙyar ta kai ta toilet ɗin ta yi tsarki sannan ta ɗauro alwala suka dawo ɗakin ta yi Sallar Magriba da isha'in dake kanta a zaune.














**************






Ameen tun bayan da ya kawo Neehal gida ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗaki ya cigaba da binkicen da yake hankalinsa a matuƙar tashe. Gabansa na faɗuwa ƙirjinsa na dokawa a million saboda fargaba. Baya son abun da yake zargi ya tabbata. Yana jin Hafsah tana ta yi masa knocking amma bai bi ta kanta ba, Sallar la'asar ce kawai ta fitar da shi daga gidan zuwa masallaci, yana dawowa ya koma ɗakin ya ƙara rufe kansa. Wannan karon sai da ya yi wanka saboda uwar zufar da yake haɗawa. Bayan ya fito ya ɗauki wayarsa ya kira wani suna magana yana lallatsa laptop ɗinsa, da alama tare suke aikin da wanda yake wayar da shi.








Bayan wasu mintuna yana cikin aikin lokaci ɗaya ya yarda wayar hannunsa da system ɗin gabansa a matuƙar gigice. Ya shiga bubbuga hannunsa akan goshinsa yana maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a fili. Ya miƙe tsaye idanunsa a lumshe, wani irin jiri ya ji ya kwashe shi hakan yasa ya yi saurin dafe hannayensa a jikin bango, ƙirjinsa na d'agawa saboda yanda zuciyarsa take bugawa. Ya daɗe a haka kafin ya zame ya zauna a ƙasa hannunsa dafe da ƙirjinsa, idanunsa sun yi ja jajur. Cikin wata irin murya dake nuni da tsantsar tashin hankali yake faɗin. "Ya Allah...! Dad why? Why?" Yana jin wayarsa tana ringing amma ko kallon inda take bai yi ba. Sai da ya ga Magriba tana ƙoƙarin yi sannan ya lallaɓa ya tashi da ƙyar ya ɗauki wayarsa ya kira wani abokinsa jami'in SS, ba tare da tunanin komai ba ya sanar masa da buƙatarsa tare da ƙudirinsa akan Daddy. Sannan ya koma ya kwanta akan gado ruf da ciki, yana son ya ɗauki system ɗinsa ya cigaba da duba abu amma ya san ko ya ɗauka babu abun da zai gane a cikinta, balle har ya fahimci wani abu. Duk wani bincike da zai yi akan al'amarin Neehal ya yi kuma ya gano komai duk abun da yake son gani, sai dai ya yi da na sanin yin binciken, da ya san abun da zai binciko kenan da tun farko bai fara binciken ba. Duk yanda mutum yake tunanin tashin hankalin da Ameen yake ciki ya wuce nan, mahaifi fa! Mahaifinsa wanda yake matsayin uban Neehal a yanzu amma shine da aikata mata wannan abubuwan? A matsayinsa na babban jami'in tsaron ƙasa mai ƙoƙarin ganin ƙasar sa ta gyaru tare da kama duk wani ɓata gari amma shine da kansa a cikin ɓata garin. Shine dalilin da ya saka kenan ya hana shi Auran Neehal ashe yana da wata manufar ne a kanta? Tambayar da yake ta yiwa kansa wanda ba shi da mai ba shi amsa me yasa Daddy ya shiga wannan ƙungiyar? Wanne irin rud'in shaid'an ɗin ne da huɗubar mummunar zuciya suka ɗebe shi ya faɗa cikin halaka ta duniya da lahira? Babban tashin hankalinsa ɗaya halin da Mama zata shiga idan ta ji Daddy ne ke aikata duk waɗannan abubuwan. Ya zata ji? Ya duniya zata ɗauki maganar? Wata zuciyar tasa kuma ta kasa yarda cewa Mahaifinsa ne da wannan ɗanyen aikin, tana ta faɗa masa ya sake bincike may be gaskiya ta bayyana, wataƙila wani ne ya shiryawa Dad ɗin haka, ko kuma wasu abokan nasa suke wannan harkar yake bin su amma shi ba ya yi? Ko ko ko.......Babu abun da bai kissima a ransa ba dangane da wannan harkar da Daddy yake yi. Ya fara bibiyar al'amarin Neehal ne tun lokacin da aka biyo ta har cikin gidansa, ada baya ɗaukar abubuwan da suke faruwa da wata manufar, ya yi zaton daga Allah ne kawai, sai lokacin zuciyarsa ta fara yi masa kokwanton tabbas da wata a ƙasa. A yau ya ji duniyar tay masa zafin da bata taɓa yi masa irinsa ba a rayuwarsa, ya ji ya tsani kansa da Daddy, bai san da idon da zai kalli Mama da Neehal ba, a ce Mahaifinsa wanda Neehal takewa kallon Uba a gare ta shi yake aikata mata haka? Tsananin tashin hankali da damuwar da Ameen ya shiga a yau baza ta faɗu ba. Har bayan Sallar isha'i yana kwance a inda yake cikin mawuyacin halin damuwa, zuciyarsa na k'issima masa abubuwa mara sa kyau a kansa, harda wacce ta bashi shawarar ya kashe kansa saboda damuwa da tsananin takaici da kunyar duniya. A hankali ya fara dawowa cikin nutsuwarsa da taimakon Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da yay ta maimaita a cikin ransa. Hakan yasa ya iya tashi dariyar cikin k'unar zuci, bai bi takan wayarsa da ake ta kira ba da bugun ƙofar da Hafsat take masa ya shiga toilet ya ƙara watsawa jikinsa da ya ɗauki zafi ruwa tare da dauro alwala. Ya fito ya xora jallabiya ya tayar da Sallar Magriba da isha'i dake kanshi. A kowacce sujjada yana roƙon Allah yasa mafarki yake ba gaske ba ne abin da binciken sa ya nuna masa, tare da roƙon ya farkar da shi cikin gaggawa, ko kuma idan ma gaske ne Allah yasa ba Daddy ba ne, wani ne daban gaskiya zata bayyana a gaba.......










Aunty Sadiya tana tsaye a bakin window'n ɗakin da Mama take tana lek'enta cikin tsananin tausayawa, Maman na kwance akan gadon ƙaramin ɗakin da take ita kaɗai an saka mata robar numfashi (Oxygen) a hancinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta ta buɗe sannan ta yi baya ta zauna akan kujera tana sauke numfashi cikin yanayin tsantsar damuwa. Wayarta dake hannunta ta latsa, hakan ya yi dai-dai da shigowar kiran mijinta cikin wayar Barrister Ahmad. Ta d'aga tare da karawa a kunne gami da sallama, bayan ya amsa mata cikin taushin murya ya ce. "Haleemah ya jikin Yaya Fateemah da Neehal?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Da sauqi Habibi, naga Ya A'isha ta mun text ta ce Neehal ta farfaɗo, Yaya Fateemah kuma gata nan a kwance har yanzu dai shiru." Uncle Ahmad ya ce. "Masha Allah, itama Yayan Insha Allahu zata farko cikin k'oshin lafiya, damuwar data riske ta lokaci ɗaya ne yasa ta cikin wannan halin." Aunty Sadiya ta ce. "Allah yasa." Uncle Ahmad ya nisa ya ce. "Komai zai wuce Insha Allah, gobe da sassafe nima zan taho Kanon sai mu je can inda Yaya Tafida yake mu san ya za'a yi da case ɗin." Aunty Sadiya ta ce. "Ɗazun nan Yaya Hamza (Abba) ya bar asibitin nan, kuma daga can inda aka tafi da Daddy yake, ya ce sun ƙi bari ma ya gan shi, sun ma ƙi saurarar shi balle a yi magana." Uncle Ahmad ya ce. "Kin san case ɗin nan ba ƙaramin case ba ne, musamman ma da bamu san evidence ɗin da Ameen ya ba su ba, amma Insha Allahu zamu yi iya yin mu wajen ganin Yaya Tafida ya fito, su kuma sauran ƴan ƙungiyar an kama su." Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Barrister kana ganin Yaya Tafida zai iya fita daga cikin case ɗin nan kuwa? Su kuma sauran ƴan ƙungiyar a iya kama su?" Uncle Ahmad ya ce. "Insha Allah Habibty, babu abun da ya fi ƙarfin Ubangiji, bincike kuma shi zai bayyana gaskiya." Aunty Sadiya ta ce. "Haka ne." Uncle Ahmad ya ce. "Ameen ɗin ya zo asibitin kuwa?" Ta ce. "Ina ta kiran wayarsa ba ya pick." Ya ce. "Allah yasa dai lafiya yake, ki cigaba da kiran sa, Insha Allahu za'a yi sa'a ya ɗauka." Aunty Sadiya ta ce. "Toh." Daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Layin Ameen ta kira. Har lokacin yana zaune akan sallaya hannunsa dafe da kansa. Yana jin kira ya shigo cikin wayarsa, kamar ya share sai kuma ya yi wani tunani, ya san definitely cikin kiran da ake ta yi masa baza a rasa na Mama ba, rashin ɗaukar mata waya kuma zai ƙara saka ta a cikin damuwa, hakan yasa ya miƙe da sauri ya ɗauko wayar a inda ya yasar da ita cikin tsananin dauriya saboda wani irin juyawa da kansa yake masa. Ganin Aunty Sadiya ce yasa ya ɗaga wayar ya saka ta a handsfree amma bai ce komai ba. Cikin sauri Aunty Sadiya ta ce. "Ameen ina ka shiga ne yau?" Shiru ya yi bai bata amsa ba. Ta kuma cewa. "Kana lafiya Ameen? Ka yi magana mana." Ya runtse idonsa numfashinsa na fita da sauri da sauri cikin matuƙar sanyin murya ya ce. "I'm fine." Aunty Sadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Masha Allah." Cikin matuƙar damuwa ya ce. "Ina Mum?" Ta ce. "Muna tare da ita, tun d'azu take kiran ka tana son magana da kai amma baka pick call ɗin." Ajiyar zuciyar shi ma ya sauke ya ce. "Zan zo yanzu in gan ta." Aunty Sadiya ta ce. "Ba ma gida, muna Hospital." A ruɗe ya ce. "What? Kuna me? Waye ba shi da lafiya?" Aunty Sadiya ta ce. "Neehal ce bata jin daɗi." Ya taune lip ɗinsa da ƙarfi sannan ya ce. "Wanne asibitin kuke?" Ta ce. "Nasarawa." Ya ce. "Okay gani nan zuwa." Bai jira amsarta ba ya katse kiran. Mukullin Mota kawai ya laluba ya buɗe ɗakin ya fita. A falo ya tarar da Hafsat zaune idanunta sun yi jajur alamun ta ci kuka ta k'oshi, ta bi shi da kallo zuciyarta fal kishi. Ya ɗan tsaya yana kallon ta. Miƙewa ta yi ta tako gabansa tana kallon sa cikin firgicin ganin yanda ya fice daga hayyacinsa a yini ɗaya. Ta fashe da kuka a hankali cikin kukan ta ce. "Meke damun ka Al'ameen da ka yi wannan ramar lokaci ɗaya? Tun d'azu ka rufe kanka a ɗaki ka bar ni cikin zullumi da damuwa, ka san kuma dole hankalina zai tashi." Lumshe idonsa ya yi cikin k'unar zuci, ya san bai kyauta mata ba tunda bata da masaniyar abun da yake faruwa balle tay masa uzuri akan halin da yake ciki. Bai ce komai ba ya kama hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawayen fuskarta. Ta kwace hannunta tare da faɗawa jikinsa ta rungume shi. A hankali ya kai hannunsa ya ɗan bubbuga bayanta alamun rarrashi, kafin ya zare ta daga jikinsa ya zaunar da ita akan kujera ya fice daga falon ba tare ya yi magana ba. Ta bi shi da kallo cikin tsananin takaici, a tunaninta duk wannan halin da yake ciki saboda Neehal ne, wutar kishi da tsanar Neehal ne ke ƙara ruruwa a cikin ranta. Ita kam wannan shegiyar yarinyar ta zame mata ƙarfen ƙafa a tsakaninta da mijinta, amma zata yi maganin abun, dole ne ta yiwa tufkar hanci tun kafin dare yay mata ta zo tana kuka da idanunta.










Ikon Allah ne kawai ya kai Ameen asibitin dan baya cikin nutsuwarsa ko kaɗan. Aunty Sadiya ya kira ta faɗa masa section ɗin da suke. Ya buɗe Mota da ƙyar ya fito yana jin jikinsa kamar ba nasa ba saboda damuwa. Cikin kulawa da tausayawa Aunty Sadiya ta tarb'e shi, kama hannunsa ta yi ta zaunar da shi sannan ita ma ta zauna. A hankali ta ce. "Ameen! Ka ga yanda ka koma kuwa? Kamar wanda ya yi jinyar shekara guda, ga jikinka na ji shi ya yi wani irin zafi." Lumshe idonsa ya yi bai ce komai ba. Cikin tausayawa Aunty Sadiya ta ce. "Ka yi haquri Ameen, haka rayuwa take cike da kalubale da jarrabawa, damuwa baza ta taɓa maka maganin abun da ke damun ka ba sai dai addu'a." Gyaɗa mata kai ya yi a hankali sannan ya motsa labbansa da ƙyar ya ce. "Ina Mum da Miemerh?" Aunty Sadiya ta ce. "Neehal tana cikin asibitin nan amma ba'a nan wajen ba, Ya A'isha da Hajiya suna tare da ita, Yaya Fateemah kuma tana cikin ɗakin nan." Ta ƙarashe zancen da nuna masa ɗakin da Mama take. Cikin mamaki ya buɗe idonsa yana kallon ɗakin bugun zuciyarsa ƙaruwa. Aunty Sadiya ta ce. "Damuwar data same ta lokacin ɗaya ce yasa har ta suma, amma zuwa yanzu Doctors sun shawo kan matsalar har ta samu bacci, bana son ka ƙara tayar da hankalinka akan tashin hankalin da kake ciki already, shi yasa da muka yi waya ban sanar maka ba." Bai jira jin ƙarashen zancen Aunty Sadiyan ba ya miƙe ya nufi ɗakin cikin sauri. Ya ƙarasa gaban gadon da take ya ƙura mata ido, cikin zuciyarsa yana jera mata addu'ar samun lafiya. Yayin da tashin hankali da damuwar da yake ciki ya ninku ganin halin da Mama take ciki. Ya san ya rasa Daddy a rayuwarsa dan hukuma baza ta taɓa barin shi ba, koda ba'a kashe shi ba zai ƙare rayuwarsa a prison ne, amma ba zai so ya rasa Mama ba Mace mafi soyuwa a gare sa, Mahaifiyarsa mai tarin alkhairi ga duk wanda ya rabe ta. Ya ɗora hannunsa akan nata a hankali tare da lumshe idonsa da suka yi jajur yana kukan zuci. Daddy bai musu adalci ba, me yasa ya faɗa wannan mummunar harkar da har su koma ga mahaliccinsu tabon abun da ya aikata ba zai bar rayuwarsu ba? Haka ya zauna a gaban Mama yana ta tunane_tunane wanda yake ƙara masa radad'i da k'uncin zuciya. Da wanne ido zai kalli Neehal da ƴan'uwanta? Da wanne ido zai kalli Mama da nata ƴan'uwan? Da wanne ido zai kalli mutanen duniya da dangin Daddy akan abun da Dad ɗin ya aikata? Kunyar kowa yake ji har shi karan kansa, ji yake tamkar shi ya aikata wannan abun kunyar. Wani Doctor ne ya shigo ɗakin yasa shi dole ya fita, dan farko ma faɗa ya kama akan shiga ɗakin da ya yi, Aunty Sadiya ta bashi haquri ta ce ɗanta ne ya zo ganin ta. Ganin yanayin Ameen Aunty Sadiya ta shiga kwantar masa da hankali cikin kalamai masu taushi, da ƙyar ta lallaɓa shi ya koma gida wajen ɗaya saura na dare, dan da cewa ya yi a nan zai kwana, Aunty Sadiya ta ce ya baro Hafsat ita kaɗai ya koma gobe da safe sai ya dawo. Bai je yaga jikin Neehal ba saboda dare da ya yi, idan ya dawo da safen ya je ya duba ta.








Bayan Neehal ta idar da sallolin ta, ta koma kan gado ta kwanta, ba jimawa likitan ya dawo yay mata allurar bacci. Sai dai tashin hankali da damuwar da take ciki ya hana baccin zuwar mata, ko alamun shi bata ji. Ta lumshe idonta dai kawai ta fara tunane_tunane. Rayuwarta ta fara tunowa tun tana ƙarama lokacin iyayenta suna raye, bata iya tuno komai a lokacin sai fuskokinsu da wasu moment ɗinta tare da su kaɗan. Ta tuna yanda Aunty A'isha take bata labarin irin tarin k'aunar da mahaifinta yake mata, ta tuna farkon dawowarta hannunsu Mama da irin riqon gaskiya da amana da sukay mata, gami da tarin k'aunar da suke nuna mata. Mama ta nuna mata son da ko ɗan data haifa albarka, lokuta da dama tana danne farincikinta dana ɗanta domin nata farincikin. Ta tuna wasu lokutan baya lokacin tana ƙarama hankali bai gama isar ta ba, yanda take ɓatawa Ameen abubuwan amfaninsa tana sane, shi kuma babu haquri zuciya a kusa, yana ɗan maketa ta kwanta tay ta birgima tana ihu a ƙasa, Mama ta zo ta ɗauke ta, ta rarrashe ta, shi kuma tay masa faɗa ta ce ya daina dukar mata yarinya ƙarama, yay mata faɗa ko nasiha mana idan ta yi masa abu ba wai duka ba. Sai sun koma ɗaki sannan ita kuma Maman tay mata faɗan ta daina taɓa masa abubuwa. Ta tuna wata rana lokacin tana Jss Mama ta aike ta ta kira shi, ta tarar yana toilet yana wanka, ga laptop ɗinsa a ajiye akan bedside drower a kunne. Ta zauna ta dinga lallatsa masa tay masa barna ba kaɗan ba ta tay masa delete ɗin some important documents ɗinsa. Ranar ta gane Allah ɗaya ne a gurinsa dan tsallen ƙwado ya saka ta, wuni ta yi ranar kuka ƙafa ta ƙi takuwa. Yayin da Mama ta kusa cinye shi ɗanye da masifa. Hakan da Mama take yi ba wai tana yi dan ta saka ta raina Ameen ɗin ba ne, hasali ma bata yi masa faɗa koda wasa a gabanta sai dai wanda Allah ya yi ta ji ko ta gani, kuma kodayaushe cikin nuna mata ta girmama shi take, ita Maman tana yi masa haka ne dan tsoron kar su cutar da marainiyar Allah. Mama ta yi mata tarbiyya irin wacce ake fatan kowacce uwa ta yiwa ƴaƴanta, ta nuna mata respect ɗin na gaba da ita ko waye ne. Hakan yasa ko yaya mutum ya girme mata take girmama shi. Ta tuna Daddy da tarin k'aunar da ya nuna mata a duniyar nan, Daddy ko faɗa baya mata sai dai nasiha, a duk lokacin da zai mata magana cikin fara'a da zolaya yake mata, ko me take so a duniyar nan yana yi mata shi idan bai fi ƙarfin shi ba kuma abun ba mara kyau ba ne. Ko laifi ta yiwa Mama ta san inta kamata zata yabawa aya zaƙinta gurin Daddy take gudawa ta buya, shi kuma ya bawa Mama haquri ita kuma yay mata faɗan har ta kuma. Tun tana ƙaramarta Mama ta koyar da ita yawaita karatun Alkur'ani da azkar da yin nafilfili wanda zuwa yanzu sun zamar mata jiki, uwa uba ibadah da nusar da ita son lahira fiye da duniya. Ita kuma me zata ce da waɗannan bayin Allah a rayuwarta? Sun zame mata garkuwa, bango, jigo da duk wani abun tunk'aho a rayuwa. Komai za su yi baza ta taɓa ganin baƙin su ba a idonta. Wannan abun da ya faru ta san ƙaddara ce Allah ya ɗora musu su duka. Ta tuna yanda dangin mahaifinta dana mahaifiyarta suka banzartar da ita, k'anin mahaifiyarta uwa ɗaya ya kasa yi mata riqon tsakani da Allah, saboda a ganinsa wahala zata zamar masa. Yanzu gashi da bata hannun nasa ya zama abun tausayi, dan ganin da tay masa lokacin bikinsu da Sadik ya zama kamar wani almajiri, duk ya fita hayyacinsa duniya ta fara koya masa hankali. Ta tuna ƙaddarar rayuwarta da yanda al'amura suka dinga tafiyar mata, ashe ƙaddarar ba ta_ta ba ce ita kaɗai, ta shafi mutane masu girma da daraja mafi soyuwa a gare ta, wadda duk matsayin da ta kai a rayuwar nan su ne sanadi. 'Ya Allah ka fitar da Daddy daga cikin wannan al'amarin, Allah ka yafe masa dukkan abun da ya aikata maka ka shirya shi ya bar wannan mummunar hanyar, Allah ka saka masa akan sanya shi cikin wannan harka ba tare da yardarsa ba da bara_gurbin abokinsa ya yi sanadin shigar sa. Allah ka tashi kafaɗun Mama ka bata lafiya da ikon cinye wannan jarabawar daka ɗora mana.' Ta faɗi haka a zuci tana zubar da hawaye. "Yaya..." Ta faɗa can ƙasan mak'oshi, ko yana ina ko a wanne halin yake ciki yanzu sai Allah. Da tunanin Ameen da halin da yake ciki allurar da akay mata ta yi aiki a jikinta bacci ya ɗauke ta wajen ƙarfe uku na dare.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣3️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












...........Washegarin da aka sallamo Mama ya kama Ranar Lahadi. Da safe su Maman suka hallara a part ɗin Mama a Falon sama dan tattaunawa akan al'amarin Daddy. Uncle Mahmud, uncle Ahmad, Kawu Musa, Abba da Mama. Kawu Musa da bai san abun da ya faru da Daddy ba sai a yanzu Abba ya sanar masa da komai. Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai

Please Login or Register in order to submit comment