Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce "Nagode sosai Ya Anwar, amma Ni dai ka ba ni in saka da kaina" Anwar ya ce "A'a my Queen ni dai ki barni na sa miki" Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin ba za ta iya musu da Anwar ɗin ba, hannun damanta ta kalla, a hankali ta sa hannun hagunta ta cire zoben dake babban ɗanyatsanta ta ajiye, sannan ta miƙa masa ɗanyatsan, murmushi Anwar ya yi ya matso ya zira mata zoben, hakan ya yi dai_dai da fitowar Ameen daga part ɗinsa domin tafiya Masallaci dan anfara kiran sallar isha'i, karaf a idanunsa Anwar ya zirawa Neehal zobe...........✍️








*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










0️⃣6️⃣










............Doctor an..an...an ka..kashe An...Anwarrrr!' ta fad'i maganar a rarrabe saboda tsananin tashin hankali. Mama suman zaune ta yi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu, Ammi ba ta jira amsar Mama ba ta katse wayar. Ita kuwa Mama wayar ma sakin ta ta yi ta fad'i ƙasa. Ganin yanda Mama ta k'ame kamar gunki ga kuma wayarta da ta saka ta faɗi ya sa Hajiya a ruɗe ta ce "Ke lafiyar ki kuwa, ki ka zuba mana na mujiya ga waya kin saki ta fad'i ƙasa?" Uncle Mahmud da ya fuskanci da akwai wata matsalar ya taso ya dawo kusa da Mama, ganin yanda ta sandare sai ya ɗan girgiza ta, wani nannauyen numfashi Mama ta ja ta sauke, saitin zuciyarta ta dafe da hannunta jin yanda ta ke bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga k'irjinta, sai a sannan wani uban gumi ya fara tsatstsafo mata ta ko wanne k'ofofin gashi na jikinta, duk da sanyin Ac'n dake falon. Kallo ɗaya za ka yiwa Mama a wannan lokacin ka hango zallar tashin hankali da ɗimuwar da take ciki, gabad'aya ta rasa a duniyar da take jinin jikinta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta ta cak da aiki. Ganin yanayin Mama Uncle Mahmud ya ƙara tabbatar da ba k'alau ba, a ɗan ruɗe ya ce "Doctor lafiya kuwa, me ke faruwa ne?" Mama ba ta bashi amsa ba, numfarfashi kawai take sauke wa. A ruɗe Hajiya ta ce "Na shiga uku Ni Zainaba, Fatima ki faɗa mana me ya faru mana, yanayin da ki ka koma Lokaci ɗaya ya tada mana hankali" Mama ta runtse idanunta ta ce "Anwar ya rasu" A gigice Hajiya ta mik'e tsaye ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta ce "Innalillahi_wa'inna'ilaihirraji'un, wanne Anwar d'in?, kar dai ki ce mun na Neehal" Uncle Mahmud innalillahi kawai ya shiga maimaitawa a fili domin mutuwar ta bige shi ba kaɗan ba, Hajiya ta saka kuka ta na salati ta ce "Allah ya ji ƙanka Anwar yaron kirki, mai biyayya, Allah ya sa aljannah ta zamo makoma a gareka, Ni Zainabu yaya Neehal za ta ji mutuwarnan?" Dai_dai nan Dad ya shigo falon a firgice, ganin yanayin su Mama ya tabbatar masa da suma sun ji mutuwar.




Mama ta shafe wasu mintuna a zaune a gurin, abu biyu ne yake ƙara dugunzuma mata hankali a kan mutuwar Anwar, na farko cewa da Ammi ta yi an kashe shi, na biyu kuma halin da Neehal za ta shiga idan wannan mummunan labarin ya riske ta. Hajiya kuwa ban da kuka babu abin da take, Dad ma kallo ɗaya mutum zai masa ya gane ya na cikin tsananin tashin hankalin mutuwar Anwar ɗin, musamman idan ya tuna halin da daughter d'insa za ta shiga idan ta ji mutuwar, Uncle Mahmud ne ma mai dauriyar cikin su, amma babu ƙarya wannan ahali mutuwar Anwar ya dake su ba kaɗan ba. Da k'yar Mama ta yi ƙarfin halin kiran Aunty Sadiya da Aunty A'isha ta sanar musu, suma sun shiga tashin hankali da jin mutuwar Anwar d'in ba kaɗan ba, Ameen kuwa ta yi ta neman Number'nsa amma ba ta shiga, kuma duka layikansa ta yi ta gwadawa amma sun ƙi tafiya, dole sai haƙura ta yi ta ajiye wayar ta fara tunanin hanyar da za ta sanar da Neehal.




Neehal yau tunda ta tashi take jin wata irin faduwar gaba na riskar ta, shi ya sa ma ta shirya ta tafi gurin aiki, ko idan tana cikin mutane za ta ji sauƙin abin da yake damunta, amma tunda ta je gurin aikin ta kasa tab'uka komai, wayar da su ka yi da Anwar ne ma da safen nan ta ɗan sanyaya mata rai, kowa ya ganta sai ya mata sannu, dan su duk ɗaukarsu rashin lafiyar da take ne. Haneefah na tsaka da aiki, Mama ta kira ta, ba ta d'aga ba ta bari idan ta gama sai ta kira ta, ganin kiran da Maman take mata ba k'ak'k'autawa ya sa ta ɗaukar excuse ta fita ta d'aga kiran,Mama cikin dauriya dan kar Haneefah ta fuskanci da wata matsalar tace "Haneefah ku taho gida yanzu ke da Neehal" ba ta jira amsar Hannefan ba ta katse wayar, duk da Mama ta yi ƙoƙarin b'oye damuwarta amma sai da Haneefah ta fuskanci akwai wani abu a Muryar Maman, office d'in da Neehal ta ke ta nufa da sauri, Neehal ta na zaune ta kwantar da kanta a kan table ɗin office Haneefah ta shigo, taɓa ta yi ta na faɗin "Neehal taso mu koma gida tunda ba ki da lafiya" Neehal ba ta yi musu ba dan ita ma ta na bukatar zuwan gidan, dan har wani jiri_jiri ta ke ji daga zaunen da take, d'ago da kanta ta yi a hankali, wayarta ta ɗauka jikinta a matukar sanyaye ta zira a cikin jakarta, ganin yanda take Haneefah ta kama ta suka fito daga office din, Manager d'in gidan TV Haneefah ta sama ta masa bayani, sannu ya yi wa Neehal sannan ya haɗa su da ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan TV'n ya kai su gida.




Mama ce kaɗai a falo tana zaune ta na hawaye, su Dad sun wuce gidansu Anwar harda Hajiya da ta dage sai ta bisu. Jin shigowar su Neehal ya sa tai saurin share hawayen fuskarta ta mik'e tsaye, ganin yanayin Neehal gabanta ya faɗi, dan ta yi tunanin ko ta ji mutuwar ne, Haneefah ta ce "Mama ga ta mun dawo, nima dama tun d'azu nake son na ce mata ta dawo gidan saboda jikinta, sai kuma gashi kin kira ni" Mama ta kama Neehal a jikinta ta rungume, ta na sakin ajiyar zuciya jin ba su ji mutuwar ba, Haneefah kallon Mama kawai take yi ganin yanayinta, hakan ya tabbatar mata da tabbas da akwai wata matsalar ba iya ciwon Neehal ɗinne ya maida Mama haka ba, Neehal kuwa luf ta yi a k'irjin Mama ta na sauke ajiyar zuciya, wayar Mama ce ta yi ƙara, hakan ya sa ta sakin Neehal da sauri ta zaunar da ita, Dad ne ke kiran ta, ɗagawa ta yi ta kara wayar a kunne, daga ɗaya ɓangaren Dad ya ce "Doctor, Neehal d'in sun dawo?" Mama ta ce "Eh." Dad ya ce "To ku taho yanzu an kawo gawar." Mama ta ce "Ohk ga mu nan." Daga haka ta katse wayar, dama ta ce wa Dad idan ankawo gawar su kirata dan gawar ta na asibiti fiye da awa biyu Police na binkice a kanta, sai yanzu aka ba da ita. Mama da ma da hijabinta a jikinta, mukullin Motor kawai ta ɗauka ta dubesu ta ce "Ku taso mu je" Kallon ta Neehal ta yi cikin mamaki amma ba ta ce komai ba, sai Haneefah ce ta ce "Ina zamu Mama?" Mama ta ɓata rai ta ce "Siyar da ku zan yi" Haneefah ba ta ƙara cewa komai ba, ta kama hannun Neehal suka bi bayan Mama, a tunanin Haneefah asibiti za su itama Neehal haka. A bayan Motor suka tarar da Mama, sai driver a gaba, suma bayan suka shiga. Tunda suka shiga Motar idanun Neehal a lumshe suke, Haneefah ce ma take ɗan kallo hanya, a tunaninta Nasarawa Hospital za su sai ta ga sun yi hanyar Hotoro ba ta kawo komai a ranta ba, sai da ta ga sun shiga layinsu Anwar sannan ta fara tambayar kanta a kan mai kuma za su yi a gidan su Anwar d'in, gabanta ne ya yanke ya faɗi Lokacin da driver ya yi parking a ƙofar gate ɗin gidansu Anwar, ga mutane an taro a na ta d'aura rumfuna, duk wata alama da za nuna mutuwa a ka yi a gidan Haneefah ta gan ta, sai dai ko kaɗan ba ta yi tunanin Anwar ne ya mutu ba, ta yi tunanin dai wani dabanne a gidan, tunda mahaifinsu already ya rasu balle ta ce ko shine. Mama ta buɗe Motar ta fita, Neehal ta biyo ta itama ta fito, sai da ta fito ta gane inda suka zo, Mama ta kama hannunta kawai ganin yanda take jujjuya idanunta ta na bin layin da kallo kamar wata doluwa suka nufi cikin gidan, Haneefah jiki a sanyaye ta fito ta bi bayansu. Bin Mama kawai suke zuciyoyinsu na bugawa har suka shiga part ɗin Mahaifiyar Anwar inda suka tarar da Mutane damk'am a falon an yi jugum_jugum, masu kuka na yi masu salati na yi, Kakarsu Anwar ta na hango su Neehal ta rushe da kuka, cikin kukan ta ce, "Allah sarki, ga yarinyar da Anwar zai aura nan, Allah ya ji ƙanka Anwar, Anwar ya saka mana, ya tona asirin azzaluman da suka kashe ka" ta ci gaba da rizgar kukanta, wani irin wul Neehal ta ji a kanta kamar an ɗora mata dutse, k'wace hannunta ta yi daga na Mama ta yi baya za ta faɗi, cikin dauriya Mama ta ruk'ota da sauri, Haneefah kuwa tuni ta durk'ushe a ƙasa dan ƙafafuwanta ba za ta su iya ɗaukar ta ba, jin wai Anwar ne ya mutu.




Mama ta na riƙe da Neehal har suka ƙarasa gurin da Mahaifiyar Anwar take, Neehal ta kwace jikinta daga na Mama ta je ta tsugunna a gaban Maman Anwar ta ce "Ammi ke kaɗai ce za ki faɗa mun Anwar ya rasu in yarda, Ammi dan Allah ki faɗa mun dagaske Anwar ya mutu, dagaske wannan taron na rasuwar Anwar ne?" Ammi ta share hawayen fuskarta ta kama hannun Neehal cikin lallami da dangana ta ce, "Neehal, Allah shi ya bamu Anwar kuma ya fimu sonshi ya karbi abinsa, Addu'a kawai Anwar yake buƙata daga gurinmu" Tunda daga Allah ya karb'i ran Anwar da Ammi ta ce, Neehal ba ta ƙara fahimtar komai da yake wakana ba, sai farkawa ta yi ta ganta a jikin Mama ta na shafa mata ruwa a fuska, ga Haneefah a gefenta ta na kuka, dafe kanta da yay mata mugun nauyi ta yi, ga kirjinta ma kamar an ɗora mata dutse saboda nauyin da yay mata. Mahaifiyar Anwar ta na hawaye sosai ta zo ta d'aga Neehal ta na faɗin "Mu je ki ganshi kafin a fita dashi" Neehal ta bita kamar wani mutum_mutumi jiri na kwasarta su ka shiga wani ɗaki, gawar Anwar ta hango kwance samb'el an gama shiryashi har an sanya shi cikin makara, jini gaba-daya ya ɓata likafanin ta saitin k'irjinsa, wata ƙara Neehal ta k'walla ta ƙarasa inda gawar take a gigice ta fara faɗin, "Anwar dagaske ka mutu, kai ma za ka tafi ka barni, mutuwa me ya sa zaki mun haka, me ya sa za ki ɗauke mun Anwar ɗina, dan Allah Anwar ka tashi kar ka tafi ka barni, ka tashi ka ce musu ba ka mutu ba, ka....." Mama da ta shigo ɗakin saboda ƙarar da Neehal ta k'walla, ta rufe mata baki, ta na hawaye ta ce "Addu'a za ki yi masa Neehal ba surutai da kuka ba, addu'arki ya fi buƙata a halin yanzu" Neehal ta ture hannun Mama daga bakinta ta ce "To..to, zan masa addu'ar" Ka na ganin yanayin Neehal ka san ba ta cikin hayyacinta a wannan lokacin. Mama ta dubi Ammi dake tsiyayar da hawaye kamar an buɗe famfo ta ce "Wuk'a aka soka masa ne?" Ammi ba ta iya ba ta amsa ba saboda halin da take ciki, sai wani k'anin mahaifin Anwar ne dake tsaye a ɗakin ya ce "Harbin sa aka yi da bindiga" Neehal ta kalli Mama a matuƙar firgice ta ce, "Mama shi ma harb'e mun shi a kai, kamar yadda a ka harb'e mun JAMIL ɗina da....." Mama da ita ma kalmar Harbin ta firgita ta, ta rungume Neehal a jikinta ba ta ce komai ba, zuciyarta na wani irin bugu. Neehal kuka take a jikin Mama ta na sumbatu na fitar hayyaci. a haka a ka shigo a ka ɗauki gawar Anwar a ka fita da ita dan kai sa gidansa na gaskiya😭 (Ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani🙏.)...........✍️








_*Manage please 🙏*_








*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










*0️⃣7️⃣*












..........Neehal ta k'wace jikinta daga jikin Mama ta yi falo da gudu a matuƙar gigice ganin dagaske dai Anwar ɗin ya mutu har za'a tafi da shi, riƙe ta a ka yi ganin ta na ƙoƙarin bin masu ɗauke da gawar, bin gawar kawai ta yi da ido hawayen idanunta ya ƙafe ƙaf kukanma ta kasa yi, kawai gani a ka yi ta yi ƙasa ta fad'i sumammiya. Farkawa kawai ta yi ta ganta a cikin wani d'aki kwance a kan gado, ƙoƙarin tashi zaune ta yi amma ta kasa saboda nauyin da kanta ya yi mata. Muryar Mama ta ji ta na faɗin, "Sannu Neehal kin tashi?" Neehal ta gyad'a mata kai ta na bin d'akin da take da kallo, ƙoƙarin ƙara tashi ta yi Mama ta taimaka mata ta sa mata filo a baya ta jingina da shi, ta na sauke Numfashi, Aunty Sadiya ce ta shigo ɗakin ita da Maman Haneefah, Aunty Sadiya ta ce "Sannu Neehal" Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mommy ma sannu mata. Neehal ta dubi Mama ta ce "Zan yi Sallah Mama" Mama ta taimaka mata ta kaita toilet ta yi alwala, kafin su fito Mahaifiyar Anwar da ta ci kuka ta k'oshi ta shigo ɗakin, sannu ta yi wa Neehal sannan ta shimfid'a mata darduma ta yi Sallah. Bayan ta idar Haneefah ta kawo mata wayarta da'ake ta zuba mata uban kira, ajiye wayar kawai ta yi ba tare da ko dubawa ta yi ba, domin ba ta ita take ba a wannan lokacin, rashin Anwar ba ƙaramin rashi ba ne a gare ta, wayar da su ka yi da safiyar yau ta shiga tunawa bayan sun gaisa ya mata ya jiki sai ya ce mata. _Neehal kwana biyun nan na lura kamar akwai wani abun da yake damun ki, ba zan matsa miki a kan dole sai na ji ba, Amma ki sani, ita rayuwa ba ta taɓa tafiya dole sai ka na fuskantar wani K'abule ko kuma jarrabawa daga Ubangiji, kuma komai ya same ka muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu mai yaye maka sai shi a kuma lokacin da ya so, dan haka a kodayaushe ki zama mai kaiwa Allah kukanki, kuma ki zama mai haƙuri a kan dukkan wata jarabawa da ta same ki, domin dukkan mai haƙuri ya na tare da Nasara a rayuwarsa._ Hawaye mai dumi ne ya zubo daga idon Neehal cikin ranta ta fara faɗin "Ashe dama Anwar mutuwa zai yi, shiyasa ya mata yar gajeriyar nasiha a zantawarsu ta ƙarshe da shi a duniya, Ya Allah ka ji k'an Anwar, ka gafarta masa zunubansa kasa Aljannah ta zama makoma a garesa."






Kafin Yamma labarin Mutuwar Anwar ya karad'e ko'ina a garin Kano, dama jahohin Nigeria da wasu ƙasashen, kasancewar harbeshi a ka yi, kuma gashi ya na shirin angoncewa nan da wata ɗaya, gashi kuma shahararriyar 'ƴar jaridar da duniya ta santa zai aura, hakan ya ƙarawa labarin armashin yayatawa. Sosai mutuwar Anwar ta girgiza Mama, musamman idan ta tuna mutane masu Mahimmanci a rayuwar Neehal duk kashe su akai ta hanyar harbin su, zuwa yanzu Mama ta tabbatarwa da kanta akwai wata a ƙasa a rayuwar Neehal ɗin, tausayin ɗiyarta ta ne ya ƙara cika mata zuciya, tun ta na 'yar ƙaramar ta za'a ɗora mata abin da ya fi ƙarfinta. A ɓangaren su Aunty Sadiya da Aunty Aisha, suma tunanin da suka wuni da shi kenan a ransu, musamman Aunty Sadiya da ta kasance Barrister, tunanin abun take cike da nazari, Maman Haneefah ma haka. Har wannan time ɗin Mama ta na ta trying number'n Ameen, amma ba ta sameshi, abun ya bata mamaki ba kaɗan ba, domin Ameen ko cikin dare ka kira shi sai ka same shi ba ya taɓa kashe wayoyinsa. Neehal kuwa ta na zaune kawai ta na bin mutane da ido, amma ita ko tunanin ma ta kasa, Mutanenta maza da mata ana ta zuwa yi mata gaisuwa, amma abun da ya bata mamaki rashin ganin Yayanta har zuwa wannan lokaci da yamma ta yi Magriba ta gabato. Bayan isha'i su Mama suka tattara suka koma gida, duk da Neehal ta so a barta ta kwana amma Mama ta ce ta bari gobe da sassafe sai su dawo, tunda yanzu gidan damk'am yake da mutane 'yan'uwan Mahaifin Anwar da na Mahaifiyarsa. Neehal har dare ko ruwa bata kai bakinta ba, ga ciwon mara da yake murd'a mata kaɗan_kaɗan, ta na daga zaune ma jiri take ji. Gabad'aya gidan Mama suka wuce, su Haneefah dai gidansu suka wuce. Neehal ta na kwance akan gadonta Mama ta shigo ɗakin da cup a hannunta, ajiye shi ta yi akan bedside locker sannan ta zauna a gefen gado, a hankali ta ce "Daughter!" Neehal ta buɗe idanunta a hankali ta sauke akan Mamanta, Mama ta ce "Tashi ki sha tea" Neehal ta girgiza mata kai alamar a'a, Mama ta ce "Haba Neehal ki tashi kisha ko kaɗan ne, ko haka za ki kwanta da yunwa" cikin raunin murya Neehal ta ce "Ba zan iya sha ba ne" Mama ta ce "Ki daure ki gwada dai" ƙoƙarin tashi Neehal ta yi Mama ta taimaka mata ta shi, kanta ta dafe da sauri alamun ya na mata ciwo, Mama ta ce "Sannu" sannan ta tashi ta ɗauko tea d'in ta fara bata a baki, Neehal shan tea ɗin kawai take yi amma babu test ko ɗaya a bakinta, tamkar ruwan mad'aci haka take jin sa, tasha kusan rabi kafin ta ture cup d'in daga bakinta har ruwan tea d'in ya d'an zuba a jikinta, Mama ta na shirin yi mata magana, amma ganin ta tashi da gudu ta nufi toilet ya sa Maman ajiye cup d'in ta bi ta, amai take k'wararawa sosai, hankalin Mama a tashe ta shiga yi mata sannu, bayan ta gama ta wanke mata bakinta sannan ta kamata ta mayar da ita ɗaki, ta kwantar. Sosai hankalin Mama ya tashi ganin yanayin jikin Neehal ɗin, ga zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta, lullub'a mata duvet Mama ta yi, sannan ta fita ta haɗo allura ta mata, duk rashin son Allura irin ta Neehal wannan kam ba ta ma sam an yi ta ba, ba jimawa kuwa bacci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ƙara gyara mata kwanciya gami da tofa mata addu'a, cike da tsananin tausayinta, ta san a daren yau Neehal ba za ta taɓa rintsawa ba shiyasa ta mata allurar bacci dan ta samu ta rintsa. Falo ta koma inda su Aunty Sadiya suke, Hajiya kuwa ta na ɗakinta itama baccin ya ɗauke ta, ba tare da ta shirya masa ba. Aunty Sadiya ta na duban Mama ta ce "Yaya Fateemah me ki ka fahimta a kan kisan Anwar?" Mama ta sauke Numfashi ta ce "Sadiya na Fahimci kamar yadda a ka kashe Jamil haka a ka kashe Anwar, kuma idan har hakane to saboda Neehal ake kisan" Aunty Sadiya ta jinjina kai ta ce "Hakane, amma shi Jamil ɗin an gano waɗanda suka kashe shin?" Mama ta ce "A'a, dan ko last week mun haɗu da Mahaifiyarsa a asibiti mun daɗe ma, har nake faɗa mata bikin Neehal ya kusa, kuma na tambayeta ya maganar kisan Jamil ta ce mun, an yi binkicen, an yi binkicen amma shiru har yanzu babu wani labari, shiyasa su sun ma haƙura sai addu'a kawai suke, koma waye ya yi kisan Allah ya bi musu hakkinsu" Aunty Sadiya ta ce "Tabɗijan, ni tsoro na ɗaya idan har aka cigaba da bincike a kan mutuwar Anwar, za'a gano a baya Neehal an taɓa kashe mata wanda za ta aura, dan haka gabad'aya binkicen kanta zai koma fa." Mama ta yi shiru dan ta ma rasa me za ta ce, Aunty Aisha dake saurarensu ta ce "To wai abun tambayar ma a nan Sadiya, idan har saboda Neehal ake wannan kisan waye ya ke yi?" Aunty Sadiya ta ce "Ba mu da amsa Ya A'isha" Mama ta ce "Wannan abun shine babbar damuwata, yau tunanin da na wuni kenan ina yi, akan waye ya kashe wa Neehal duk mijin da za ta aura, kuma me ta yi masa yake mata hakan, me ne ribarshi na yi mata Hakan?" Aunty Sadiya ta ce "Hmmm sai Allah, amma na yi wa kaina alƙawari daga yau zan fara zurfaffen binkice akan wannan abun, insha Allahu ko ma waye yake bibiyar rayuwar Neehal sai mun binciko shi" Mama ta ce "Ba na jin ki a kan aikin ki Sadiya, na san ki na da k'warewa da kuma Sa'a gami da jajircewa, amma kuma sai na ji zuciyata ta na tsoron ki yi aikin nan, kar su gano ki na binkice akan su su yi miki wani abun." Aunty Sadiya ta yi wani guntun Murmushi ta ce "Kar ki damu Ya Fateemah, insha Allahu babu abin da zai faru da ni, kuma da ma harkar Shari'a a ƙasar nan indai kai me gaskiya ne, sai addu'a kawai, ku dai kawai ku taya mu da addu'a." Mama ta yi shiru kawai, dan ita kaɗai ta san me yake damun zuciyarta akan wannan baƙon al'amari da ya shigo cikin rayuwarsu yake ƙoƙarin tarwatsa masu farin cikinsu, ita fatan ta ma a ce kisan ba saboda Neehal ake ba, duk da tasan hakan da wuya, domin Neehal ba iya samarinta kawai aka kashe mata ba har da...... Shigowar uncle Ahmad mijin Aunty Sadiya ya katse wa Mama tunaninta, amsa masa sallamar da ya yi suka yi. Ya zauna suka gaisa, sannan suka ƙara tattaunawa a kan al'amarin kasancewar shima Barrister ne, kamar matar tasa, Dad ma ya shigo falon aka cigaba da tattaunawar da shi.




Misalin ƙarfe goma da rabi na dare Mama ta na ɗakinta a zaune a kan darduma ta na lazimi, domin babu d'igon bacci ko kaɗan a idonta, bayan tafiyar su Aunty Sadiya gidajensu Dad ya koma part ɗinsa, ita kam Mama yau ko part d'in nasa ba za ta iya zuwa ba, saboda damuwar da take ciki, sosai Mama ta damu da wannan al'amari, domin ba ta k'aunar abin da zai taɓa Neehal ko kaɗan a rayuwar nan, balle abin da zai taɓa farin cikinta, amma tasan ba ta isa ta goge rubutacciyar ƙaddarar da Ubangiji ya zana wa Neehal ɗin ba, a rayuwarta. A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakinta an shigo, a tunaninta Dad ne, amma jin k'amshin turaren Ameen ya sa ta d'ago kanta da sauri ta kalle shi, kansa a ƙasa ya yi sallama tare da nufo inda take, Mama ta ɗauke kanta daga Kallonsa tare da amsa masa sallamar da ya yi a zuciyarta. Kusa da ita ya zauna kansa na ƙasa still ya ce "Mum!" Mama ta ɗan kallesa ta watsar amma ba ta ce komai ba, ya ƙara faɗin "Ya haƙurinmu?" Mama ba ta amsa masa ba sai cewa ta yi "Me ya samu phones ɗinka?" Ba tare da ya yarda sun haɗa ido ba ya ce "Switch up d'insu na yi" Mama ta ce "Akan wanne dalili" ya ɗan yi shiru na wasu sakanni ita kuma Mama ta tsura masa ido. Cikin dakiyarsa ya ce "Aikin da ya kaini Lagos ne ba ƙarami ba ne, kuma ina so in gama shi a yau gobe kawai sai dai a rabawa masu yi, that is why na katse wayar kar a kira ni a tsayar da ni." Mama ta yi shiru dan ita ta

Please Login or Register in order to submit comment