Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda aka tsikara na nufi ƙofar ɗakin na fara ƙoƙarin buɗewa amma na jita a kulle gam, ni kuma jikina babu k'wari balle na yi yunƙurin buɗe ta. So nake in yi ihu ko wani zai jiyo ni ya kawo mun ɗauki amma k'warin muryar ihun ma bani da shi. Idan na tuna ranar ne fa d'aurin Aure na sai hankalina ya ƙara dugunzuma ya kai k'olokuwar tashi. Na zube a bakin ƙofar jin jiri na neman yarda ni, babu irin tunanin da ban yi ba akan kawo ni gurin da akai. Na ce ko wani abokin aikina ne yake jin haushina yasa a sato ni? Ko kuma kidnappers ne? Ko kuma wani case ɗin na yi daya ɓata wa wani rai ya k'ullace ni? shine zai saka a zato ni ranar Aure na a matsayin ɗaukar fansa. Ni kaɗai a ɗakin babu alamar wani yana inda nake, ko kukan tsuntsu ban ji ba balle na wasu dabbobin ko na mutum. Ina nan zaune aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo, na d'ago da sauri sai na ga mutumin d'azu ne, hannunsa ɗauke da take away da ruwa da lemo, ya ajiye a gabana ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fita. Ni kuma kamar an ɗaure mun baki na kasa yi masa magana, duk da tarin tambayoyin dake raina. Na yi ball da abincin da ƙafa cikin tsananin takaici, na san zuwa lokacin ahalina da abokan arzik'i da amaryata suna can cikin tashin hankalin ɓata na.








Haka na wuni ni kaɗai a ɗakin cikin tunanin mafita, Sallah ce kawai take tayar da ni idan na ga lokacin ta ya yi. Har bayan Magriba ko ruwa ban kurb'a na saka wa cikina ba, yunwar ma da ƙishirwar ko jin su bana yi, ko ma ina ji bata su nake ba. Kafin isha'i mutumin ya ƙara dawowa ya kawo mun wani abincin da ruwan. Na tashi da sauri cikin ƙarfin hali dana zuciya na cakumi mutumin ina tambayar sa dalilin yasa suka kawo ni nan? Me nay musu? Kamar wani kara haka mutumin ya yakice ni daga jikinsa ya dank'wafar da ni a ƙasa ya juya ya fice. Na rarrafa a ƙoƙarina na ganin na riƙe ƙofar kafin ya rufe, amma tuni ya ja ta sai motsin saka mukulli a jikinta na ji. Na kwanta akan carpet ɗin dake malale a ɗakin cikin tsananin damuwa. Sai da takwas ta wuce sannan na miƙe ina layi na shiga toilet na ɗauro alwala na yi Sallar isha'i, na ƙara da nafila a cikin kowacce sujjada ta ina roƙon Allah ya fitar da ni daga cikin wannan riskin da nake ciki. Ina kan sallaya mutumin ya sake shigowa, na zuba masa ido in ga mai kuma ya shigo yi, da yake ɗakin akwai hasken wani farin k'wan wuta guda ɗaya dake sak'ale a bango. Ga mamakina sai na ga ya kama ni ya kai ni kan gado ya kwantar, na bishi da kallon mamaki, ban gama mamakin ba na ji ya juya ni gefe ya d'aga jallabiyar jikina ya tsikara mun allura. Daga nan na fara ganin bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan bacci ya yi gaba da ni. Ban farka ba sai ƙarfe shida saura na safe, na bi ɗakin da kallo, sai na ga fankar sama tana wulwulawa, na juya b'arin damana sai na ga Television ta bango manne a bangon dakin, sai wani abu mai kama da GO TV a ƙasan ta da remotes biyu a kansa. A gefen ta kuma wani ɗan table ne an ɗora Alkur'ani izifi sittin akai. Mamaki fa ya kusa kashe ni, na shiga tambayar kaina abun da mutanen nan suke nufi da ni? Ko duk a cikin salon cutarwar da za su mun ne? Ko kuma wani abu suke nema a guri na? Na yunƙura na tashi sai a lokacin na lura da bargon dake lullub'e a jikina, kaina kuma ashe akan pillow yake. Sai na rasa da yaran da zan fassara wannan al'amarin da na tsinci kaina a ciki. Haka na yunƙura na sakko daga kan gadon, jikina a matuƙar sanyaye kamar jiya na nufi toilet. In tak'aice muku zance haka na kasance a cikin ɗakin nan, kullum za'a kawo mun abinci da ruwa da lemo safe, rana, dare. Da farko bana ci, sai daga baya dana ji yunwa na neman yi mun illa sannan na fara ci ba don daɗi ba. Kuma duk dare sai mutumin nan ya mun allurar nan, wanda na fuskanci ta bacci ce, amma asuba tana yi zan farka. Hakan yasa jikina kodayaushe babu k'wari, ya yi mun wani irin lagwab. Ban taɓa wanka ba sai sau ɗaya da na ji kamar zan mutu saboda k'aik'ayin da jikina yake mun, a toilet ɗin akwai kat'on soap na wanka da toothpaste da brush sabo. Tun ina tambayar mai kawo mun abinci wanda ban taɓa ganin fuskarsa ba dalilin da yasa suka ɗauko ni suka ajiye ni a gurin, har na haqura na daina na zubawa sarautar Allah ido da ganin iya gudun ruwan su, amma har na baro gurin ba su taɓa ƙoƙarin cutar da ni ba, Alkur'ani nan shi ya zamo abokin hira ta, shine nake karantawa wuni guda cur, hakan yasa nake samun nutsuwa a cikin zuciyata. Kwana na huɗu aka kawo mun jallabiya guda biyu da ƙaramin wando, da har na ƙi sakawa sai kuma na ɗauka na saka, da na yi tunanin ina Sallah kar kayan jikina su yi dattin da baza su yi Sallah ba, Tunda ban san ranar fita ta daga gurin ba. Jiya da ya kasance kwana na shida a wannan ɗakin na lek'a waje ta window, sai na fuskanci kamar gida ne inda nake ciki, saboda dana lek'a like bayan gida na gani. Yau na tashi kamar kullum na yi Sallah na ɗan taɓa abincin da aka kawo mun kaɗan, sannan na ɗauki Alkur'ani na fara karatu. Wajen sha biyu lokacin na ajiye Kur'anin inata ta tunane_tunane na, mutumin nan ya shigo ɗakin. Ya ɗauke Alkur'anin gaba na ya ajiye akan table ɗin nan, sannan ya fito da wani baƙin k'yalle ya ɗaure mun idanuna tamau, ina tirje_tirje da yi masa ihun ya rabu da ni amma bai kula ni ba. Na ji an ƙara buɗe ƙofar ɗakin an shigo, daga nan kuma sai ji na yi sun kama ni mun fice daga ɗakin. Inata tambayar su ina zasu kai ni, amma babu wanda ya ce mun kanzil. Har suka saka ni a cikin mota suka ɗaure mun hannuna ta baya muka fara tafiyar da ban san inda za'a kai ni ba. Addu'ar neman tsari kawai nake karantawa a raina. Mun yi tafiya sosai sannan na ji mun tsaya, suka fito dani muka shiga wari guri, sai da muka shiga suka kunce mun daurin fuskata dana hannuna, suka buɗe wata ƙofa suka kaini bakinta, ina shiga na ga toilet ne. Mamakin waɗan nan mutanen nake da basa wasa da Sallah, dan na gane tsayawa suka yi da tafiyar dan na yi Sallah. Na ɗauro alwala na fito na tayar da Sallah akan carpet ɗin dake tsakiyar gurin mai kama da ɗaki, amma babu komai a cikin sa, ko labule babu. Na tayar da Sallar kenan ɗaya daga cikinsu ya taso ya juyar da ni, da alama ban fuskanci alk'ibla dai-dai ba, tunda dama shata kawai na yi. Ina idarwa suka mayar mun da k'yallen fuskata suka kuma ɗauren hannuna, suka kama ni muka fice daga gurin. Muka koma motor aka cigaba da tafiya, wadda har sai ana la'asar muka shigo cikin gari, nan ma sai da suka tsaya suka shigar da ni wani gida da babu kowa a cikinsa na yi Sallah, sannan muka fito, tafiya kaɗan muka yi suka sauke ni tare da kunce mun d'aurin fuskata dana hannuna cikin sauri sannan suka juya suka shiga cikin Mota suka manne ta da mugun gudu. Na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi lokacin dana fuskanci a bayan gidan nan nake. Jikina har rawa yake dan murna da zumud'i na miƙe na nufo gida, ina son na yi gudu dan ƙarasowa da wuri amma rashin k'warin jikina ya hana ni, dole sai a hankali na tako na zo, ina tafe ina tunanin mutanen nan da tambayar kaina menene fa'idar ɗauke ni da sukay? Kuma gashi sun dawo da ni gida ba tare da cutarwar ko ƙwarza ne a jikina ba? Wannan shine abun da ya faru da ni."










Gaba-ɗaya mutanen Parlour'n suka yi shiru kowa yana jimanta al'amarin a cikin ransa cikin tsananin mamaki. Abban Sadik ne ya fara magana a cikinsu cikin matuƙar mamaki ya ce. "To fa, ka ji kuma wani ikon Allah, amma wannan abun da ɗaure kai yake, to su waye waɗan nan mutanen, mene kuma fa'idar su na yin hakan?" Kawu ya ce. "Shine abun tambayar." Hajiya ta ce. "Yo wanne abun tambaya kuma ga abu nan a zahiri? An sace Sadik ba dan komai ba ne sai dan kawai akan wannan yarinyar, saboda kar auransu ya yiyu, Allah ya rufa mana asiri shi ba'a kashe shi ba kamar na bayan da aka kashe." Cikin sauri Sadik ya kalle ta amma bai ce komai ba. Hajja (Mahaifiyar Maamah) ta ce. "Gaskiya ne zargin mu ya zama gaskiya, saboda yarinyar ne." Kawu ya ce. "Lallai Sadik ka auna arzik'i, Allah ya yi da sauran kwanan ka a gaba kana da rabon shan ruwa, Eh, Alhamdulillah mun godewa Allah, fatan mu Allah ya baka wata matar ta gari, wannan yarinya kam ba matar Aure ba ce." Abba ya ce. "Nima na tsorata gaskiya, gwara da ba mu yarda an ɗaura Auren ba, wataƙila da waɗan da suka sace shin sun ji labarin an ɗaura Auren da tuni sun kashe shi." Hajiya ta ce. "Zancen yaushe kuma? Ai Allah ne yay mana gyaɗar doguwa, gobe in Allah ya kai mu sai a karb'o kaya da kuɗin da aka kai gidansu yarinyar, maganar aure kuma ta ruguje, tunda yarinya ta zama annoba." Abba ya dubi Sadik dake cikin tashin hankali ya ce. "Ka yi haquri Abubukar, tun kafin ka dawo mun gama yanke hukunci baza ka auri yarinyar nan ba, dan alamu sun nuna kota yi auren ma za'a iya bi har gida a kashe mijin." A ruɗe Sadik kamar zai yi kuka ya ce. "Abba ni na san ba domin Neehal aka sace ni ba, abun da kuke tunani ba haka ba ne Abba, ka manta aikina, ka manta wani zai iya yin komai dan yana jin haushi na, may be mun samu wata matsalar akan wani case daban, ko kuma....." A zafafe Hajiya ta katse shi da faɗin. "Lallai Sadik na yarda baka da hankali, ka ci akai ka dawanau a duba ƙwaƙwalwarka, yarinyar da kafin kai samarinta biyu an kashe su, kai kuma aka sace ka ana i gobe d'aurin Auren ku shine kake ƙoƙarin kare ta? Saboda Kai ne Majnoon sarkin soyayya, ko kuma in ce sarkin hauka? To yarinyar nan in ma mayya ce ta lashe maka kurwa sai ta sake ka wallahi, kai da ita kuma haihata_haihata kun rabu, rabuwa ta har abada, in ma zaka cire ta daga ranka ka cire ta, na san wannan farar fatar ta_ta da dogon hanci da manyan idanu su suke rud'ar ka a kanta, to indai wannan ne zaka samu wadda ta fita sau dubu a duniyar nan." Sadik ya dafe kansa dake sara masa kamar zai tsage lokaci ɗaya. Abba ya ce. "Abubakar ka yi tunani da hankalinka mana, idan dan jin haushin ka ko dan ɗaukar fansa aka sace ka baza a barka lami lafiya ba sai an cutar da kai, amma wannan fa dubi yadda aka kula da kai, harda saka maka kayan kallo dan su ɗebe maka kewa. Amma na jinjinawa koma waye ya sace ka, yanda bai bari ka yi wasa da Sallah ba, kuma yake baka abinci akai_akai, tabbas ya san darajar ɗan Adam. Sai dai ba mu san mene a cikin zuciyarsa ba daya aikata hakan." Ɗaya daga cikin k'annen Abba ya ce. "Abun da mamaki ba kaɗan ba, ita kuwa wannan yarinya wa yake yiwa rayuwarta haka, ni tausayi take ba ni dan na san su ma ba su da masaniya akan mai aikata mata wannan al'amari." Hajja ta ce. "Abun da tausayi gaskiya." Umma ta ce. "Wataƙila aljanu gare ta." Kawu ya ce. "Koma mene ne Allah ya yaye mata, mu dai an yi walk'iya mun gani, ɗanmu ba zai aure ta ba, fak'at." Sadik zai yi magana Kawu ya katse shi cikin faɗa ya ce. "Karka ce komai, indai mun isa da kai daga yau ba kai ba wannan yarinyar." Sadik ya kalli Maamah da bata ce k'ala ba tunda ta zauna yana marairaice fuska, a ƙoƙarin na son ta roƙar masa su Kawu akan kar su raba shi da Neehal, amma sai ya ga ta sunkuyar da kanta ƙasa alamun tana bayan su Kawu, ta goyi bayan a raba shi da Neehal kenan ita ma? Ya ɗauke kansa daga kanta cikin ƙarfin halin radad'in da yake ji a zuciyarsa ya ce. "Shikenan Kawu, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi." Yana gama faɗar haka ya miƙe cikin sanyin jiki kamar zai faɗi ya fice daga falon. Suka bi shi da kallo dukan su. Maamah ta ji tausayin ɗan nata ya cika mata zuciya, sai ta ga kamar su Kawu ba su kyauta masa ba, daga dawowar shi su tarye shi da zancen rabuwa da abar son sa, wanda kowa ya san zai ji ciwon hakan ba kaɗan ba. A ganin ta aida sun bari an kwana biyu ya ƙara hutawa ya dawo cikin nutsuwarsa. Baza ta iya barin ɗanta a cikin halin damuwa ba tare da rarrashe shi ta faɗa masa abun da zai ji sanyi a ransa ba, hakan yasa ta miƙe ba tare data kalli kowa ba ta bi bayan shi. Umma ta tab'e baki. Hajiya ta shiga mita da masifar Neehal ba haka ta bar mata jikan ta ba, asirce shi ta yi, ban da haka mutum yana ganin mutuwa muraran amma yana ƙara kai kansa gare ta.














Yana kwance akan gadon ɗakinsa ruf da ciki Maamah ta shiga ta same shi, idanunsa a lumshe sai faman sassauke numfashi yake. Maamah ta zauna a bakin gadon tare da ɗora hannunta a kansa cikin sanyin murya ta ce. "Ka yi haquri Sadik, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, ka miƙawa Allah komai zaka ga ya warware maka damuwar ka cikin sauƙi, ta hanyar da baka taɓa tsammani ba. Ka saka a ranka idan Neehal matar ka ce duk runtsi duk wuya sai ka aure ta, just pray hard my son everything will be Okay by the grace of God." Sadik ya gyaɗawa mata kai tare da sauke ajiyar zuciya. Maamah ta ce. "Dan Allah karka damu kanka da tunani, ka kwantar da hankalinka, ka ga yau ka dawo kana murna muma muna murna, karka ɓata Mood ɗinka ka ɓata namu." Ya gyaɗa mata kai. Maamah ta shafi sumar kansa ta ce. "Allah yay maka Albarka, ya baka ƴaƴa masu biyayya kamar yadda kake mana, ya zaɓa maka abun da yafi Alkhairi a rayuwarka." Ya buɗe ido cikin daɗin addu'arta ya ce. "Amin Maamah ta, thank you so much." Maamah ta yi murmushi ta miƙe ta fice. Ya bita da kallo cikin matsananciyar k'aunar ta, uwa uwa ce, mai sanya farinciki a zuciyar ƴaƴanta akodayaushe, dole duk wanda ya rasa uwa ya yi kuka. Ya lumshe ido a ransa yana faɗin, dole ya yiwa iyayensa biyayya ya rabu da Neehal, duk da ya san zai cutu, cutuwa ba kaɗan ba, bai ma san ya zai kwatanta rayuwarsa babu Neehal ba, bai sani ba ko zuciyarsa zata ɗauki rayuwa babu ita ko ba zata ɗauka ba? A fili ya furta. "I'm sorry Neehal, dole zan bar ki ba dan san raina ba." Ya sauke ajiyar zuciya tare sakawa a ransa ya rabu da Neehal rabuwa ta har abada kamar yadda iyayensa suke zo, zai dage da addu'ar Allah ya rage masa soyayyarta a cikin zuciyarsa ko da rabi ce, dan ya san ba zai taɓa daina son ta ba har abada. Amma Neehal fa? Yaya zata ji idan ta ji ya bar ta akan ƙaddarar da ba ita ta ɗorawa kanta ba? me yasa mutane baza su yi mata uzuri ba? Me yasa za'a ƙyamace ta a hana a aure ta? Mene laifin ta a cikin ƙaddarar ta? Hawaye masu d'umi ne ya ji suna zarya akan kuncinsa, na tausayin kansa da tausayin abar k'aunarsa, masoyiyarsa, muradin ransa, wadda ya saka ran zata zamto matarsa uwar ƴaƴansa amma *ƙaddara* ta raba su, a lokacin da ba su taɓa tsammani ba, lokacin da suke gab da mallakar junan su, su zamto abu ɗaya. Ya share hawayen fuskarsa wanda ya manta rabon da ya gan su akan fuskarsa sai yau, shi musulmi ne ya yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, haɗuwar su da Neehal wani shafi ne a cikin shafin littafin ƙaddarar rayuwarsa da Ubangiji ya rubuta masa, haka ma rabuwa da ita, dan haka He accepted it, Rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa daga Ubangijin sa. Fata kawai Allah yasa mu iya cinye dukkan jarrabawoyin rayuwar mu, wanda muke fatan hakan ya kai mu ga samun dacewa a duniya da lahira baki ɗaya........✍️










_*Not edit, sorry for the typed errors.*_












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣7️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














..........Tun ƙarfe biyar da ƴan mintuna Mama suka yi waya da Neehal ta sanar mata ta taho gida, amma har shida ta wuce bata dawo ba, abun ya bawa Mama mamaki dan daga ASTV zuwa gidansu bai fi tafiyar 10 minutes ba, indai ba mugun go slow mutum ya tarar a hanya ba, shi ma ba zai tsayar da kai har kusan 1 hour ba. kiran wayar Neehal Mama ta yi dan jin abun da ya tsayar da ita amma sai ta ji switch up. Ta kira another sim ɗinta shi ma ta ji shi a kashe, Numbobin Neehal huɗu gare ta amma duk ta kira abu ɗaya ake maimaita mata is switch up. Sai ta ji kawai hankalinta bai kwanta ba, ta miƙe daga zaunen da take gabanta na fad'uwa ta lulubo Numbern ɗaya cikin abokan aikin Neehal mai suna Rahama ta kira. Cikin sa'a wayar ta shiga ringing biyu ta ɗaya tare yin sallama. Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. "An wuni lafiya Rahmah ya aiki?" Rahmah ta ce. "Alhamdulillah." Mama ta ce. "Na ji kamar baki gane mai magana ba, Maman Neehal ce." Da fara'a a muryar Rahmah ta ce. "Laa Mama ke ce, ina yini, wallahi ban gane ki ba, Numbern babu save da yake na canza waya ne." Mama ta ce. "Babu komai, kin baro gurin aiki ne?" Rahmah ta ce. "Eh, tare ma muka fito da Neehal." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Mun yi waya da ita tun d'azu ta ce mun ta taho saboda bana son ta yi dare a waje tunda ba ishashshiyar lafiya ce da ita ba, to kuma har yanzu na ji ta shiru bata dawo ba, ga magriba ta kawo kai, na kira wayoyinta duka a kashe." Rahmah ta ce. "Too, kuma bata ce miki zata biya ta wani gurin ba, saboda sai da ta shiga Mota sannan direbanmu ya zo ya ɗauke ni." Mama ta ce. "Kina nufin ta ma riga ki fita?" Rahmah ta ce. "Eh, buɗe mata gate ɗin ma da akai ta fita kafin a rufe direbana ya shigo, da ya ɗauke ni muka fita daga cikin gidan TV'n babu ma motar ta a layin har ta ƙarasa titi." Mama ta ce. "Toh shikenan Rahmah na gode, dama na yi tunanin ko ta yi mantawa ne ta koma." Rahmah ta ce. "Gaskiya ban ga komawar ta ba, amma bari na kira wani a cikin masu night duty in ji ko bayan mun fito ta koma." Mama ta ce. "Yawwa Rahmah na gode sosai, yanda kuka yi sai ki kira ni ki faɗa mun." Rahmah ta ce. "Insha Allahu." Mama ta ajiye wayar a hannun kujera bayan ta katse kiran ta shiga kaiwa da komowa a falon idanunta akan makeken agogon bangon dake manne a kusurwar Parlour'n, duk second ɗaya da yake tafiya akan idonta, haka kuma duk second ɗin yana tafiya ne da ƙaruwar bugun zuciyarta na tsoron kar wani mugun abun ne ya samu Neehal. Girki take a ƙasa amma ta kasa sauka ta ƙarasa, girki na musamman take shiryawa Neehal ɗinta dan ta ci abinci sosai in ta dawo, dan ta san mawuyacin abu ne ta ci a gurin aikin, amma kuma rashin dawowar Neehal ɗin akan lokaci ya sanya mata wani irin abu a zuciyarta, duk da ba yau Neehal ta saba ƙara lokaci ba idan ta fita amma yau ɗin sai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya da hakan, ko dan yanayin damuwa da Neehal ɗin take ciki ne yasa take tsoron kar wani abu ya faru da ita? Like accident or something like that. Abun da yake ƙara d'aga mata hankali kuma jin wayoyinta gaba-d'aya a kashe, ta san ba zai yiyu a ce duka wayoyi ukun da Neehal take amfani da su babu charge ba, ta san kuma Neehal bata kashe wayoyinta haka kawai, dole sai da wani dalilin.......










Ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunanin da take, ta ƙarasa ta ɗauka cikin sauri tare da karawa a kunne ganin Rahmah ce take kiran. Rahmah ta ce. "Mama wai bata koma ba tunda ta fita." Ƙirjin Mama na tsananta bugu ta ce. "Shikenan Rahmah, na gode." Rahama ta ce. "Kuma bata ce zata biya ta wani gurin ba?" Mama ta ce. "Bata faɗa ba, amma bari na kira Auntie's ɗinta na ji ko ta je gurin su." Rahama ta ce. "Toh Mama, Insha Allah ma tana can ɗin." Mama ta ce. "Allah yasa." Sannan ta katse wayar ta kira Aunty A'isha. Cikin dabara yanda Aunty A'ishan baza ta gane da wata matsalar ba, Mama ta tambaye ta ko Neehal ɗin ta zo gidanta, Aunty A'isha ta ce bata zo ba, har take tambayar ta Neehal ɗin ta fara fita ne? Mama ta ce mata yau ta fara fita. Bayan sun gama wayar ta kira Aunty Sadiya ita ma ta tambaye ta, Aunty Sadiya ta ce bata zo ba, ita yanzu ma ta dawo daga gurin aiki. Mama ta zauna dab'as cikin tsananin tashin hankali, zuwa yanzu kam ta tabbatar da akwai matsala, gashi Haneefah bata nan suna Kogi state bare ta ce ko gidanta ta tafi. Ta yi tunanin ko gidan Ameen ta tafi, ko kuma gidan su wasu k'awayen nata. Duk wanda Mama take tunanin Neehal zata iya zuwa gidansa a cikin garin Kano sai da ta kira ta tambaya ko ta je, su Aunty matar Uncle Umar, da matar Kawu Musa, da k'awayen Maman da suke zuwa gidajensu da Neehal ɗin, da Maman Haneefah, har mak'ota sai da Mama ta kira amma ko ina babu labari. Ta kira few Freind's ɗin Neehal da take da Numbern su, su ma babu labari. Data kira Ameen bai ɗauka ba sai ta kira Hafsat ta tambaye ta, and amasar duk ɗaya ce nan ma Neehal bata je ba. A gigice Mama ta sauko ƙasa ta shiga duba all Apartments ɗin gidan ko Neehal ta dawo ta wuce can, duk da wasu a kulle suke amma duk sai da Mama ta duba, su Zulai na taya ta suma hankali a tashe da Mama ta labarta musu abun da yake faruwa, duk bayan mintoci Mama tana ƙara kiran wayar Neehal ko za'a dace, amma still a kashe. Har parking space Mama ta duba ko zata ga Motar ta amma bata gani ba, Mama ta tambaye yi masu gadi ko Neehal ta shigo ta kuma fita suka ce tunda ta fita bata dawo ba. Har an fara kiran Sallar isha'i amma Mama bata yi Magriba ba saboda tashin hankali, ita da

Please Login or Register in order to submit comment