Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sani ba Haneefah." Haneefah ta mik'e ta koma kusa da Neehal ta dafa kafad'arta, cikin son kwantar mata da hankali ta ce "Kin ga Neehal kar ki saka wannan abun a ranki har ya yi tasiri a cikin zuciyarki, Jameel da Anwar lokacin mutuwar su ne ya yi, da lokacin su bai yi ba babu wanda ya isa ya kashe su. Kawai Allah ya yi ajalinsu ya na hannun waɗanda suka kashe sun ne, amma wlh Neehal ni har yanzu zuciyata ba ta yarda saboda ke a ka kashe su Anwar ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "Amma kuma Haneefah yanayin yanda ake kashe sun ɗaya ne, duk harbe su ake fa." Haneefah ta ce "Kar ki yi la'akari da wannan, duba da yanda zamani ya sauya, yanzu ai ko barayi ne za su yi sata zai yi wahala ki gansu da wuk'a ko wani makamin, sai dai yara, amma waɗanda suka shahara da bindigu suke zuwa, Dan haka idan an harbe Anwar da Jameel ba hakan ya na nufin mai kisan ɗaya ba ne." Neehal ta yi shiru kawai ta na kallon Haneefah tare da auna maganganunta a mizanin nazari. Bayan kamar minti uku ta ce "To Haneefah ko dai aljanu ne?" "Haba Neehal, wanne aljanu kuma? Kar ki ɗauki alhakin bayin Allah, idan aljanu ne kuma sai su dinga harbe mutum, su da suke da hanyoyin cutar da mutane kala_kala." Haneefah ta katse Neehal da faɗin haka cikin tarar numfashi. Neehal ta runtse idonta kawai tare da dafe kanta cikin kullewar kwanyarta. Haneefah ta saki kafadunta ta koma kujerar da ta taso sannan ta ce "Da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, idan da rabon shan numfashin mutum a duniya ko a na yanka naman jikinsa sai ya rayu, idan kuma kwanan mutum ya ƙare ko da lafiyar sa k'alau dole sai ya amsa kiran mahaliccin sa, ki sa wannan a ranki Allah shine mai yin komai a kuma sanda ya so." Neehal ta ja wani gwauron numfashi ta ce "Tabbas maganganunki gaskiya ne Haneefah, kuma Insha Allahu zan cire wannan tunanin daga raina, amma zan dage da addu'a a kan Allah ya bayyana gaskiyar al'amari." Haneefah ta ce "Ko ke fah, su kuma sai ki ta musu addu'ar neman gafara da dacewa a gurin Ubangiji" Neehal ta ce "Insha Allah, Ni kuma tawa ƙaddarar kenan duk wanda na so ba ma kasancewa tare sai mun rabu." Yanda Neehal ta yi maganar sai da Haneefah ta murmusa ba tare da ta sani ba, Neehal ma murmushin ta yi domin kalaman Haneefah sun fara sanyaya mata zuciya. Ta na murmushin ta ce "Dariya ma na baki ko?" Haneefah ta ce "Ai yanda ki ka yi maganar ne kamar wata sabuwar marainiya." Neehal ta ce "Me ne marabata da sabuwar marainiyar?" "Marabar ku ki na da iyaye samari kawai ki ka rasa, kuma suma za ki samu wasu nan gaba wanda har za ki manta da na baya." Neehal ta mata wani kallo ta ce "Hmmmm, ki na tunanin zan iya ƙara son wani ɗa namiji a duniyar nan ne? ai ni da soyayya kuma sai dai na ga a na yi" Haneefah ta yi wani ɗan murmushi ta ce "Zance ma kenan, za ki yi ta zama ne ba ki yi aure ba? Ko kuma za ki yi Aure ba tare da soyayya ba? Ni na faɗa miki ki rubuta ki ajiye sai kin so wani fiye da son da ki ka yi wa Jameel da Anwar." Neehal ta tab'e baki ba ta ce komai ba, dan ita ba ta ɗauki maganganun Neehal da mahimmanci ba, ban da haka ta yaya za ta so wani fiye da son da ta yi wa Anwar d'inta? Ai tun ranar da Anwar ya rasu ta yi wa kanta alƙawarin ta bar soyayya har abada.






Yau ma gidan Mama Haneefah suka wuce bayan sun tashi daga aiki, suna shiga ta ga Hameedah ita ba ma tasan ta zo ba, dan Neehal ta ma manta da zuwanta ba ta faɗa mata, ita kuma rabonta da gidan tun ranar Alhamis. Suka yi sallama, Hameedah ta d'ago ta musu wani kallo kamar ta ga kashi ta ƙi amsa musu sallamar. Haneefah da ta fi Neehal saurin ɗaukar zafi ta ce "Sai ka ce mutum ba musulmi ba a yi sallama ya na ji ya ƙi amsa wa." Aiko Hameedah dama kaɗan take jira, dan ta je part d'in Ameen za ta masa shirme ya korota, gashi dama ta tsani Haneefah kamar yadda ta tsani Neehal. Mik'ewa tsaye ta yi kamar wata sabowar kamu ta fara ɗura_ɗuran ashar ta na zagin Haneefah har ma da Neehal da ta bata kula ta ba. Haneefah za ta biye mata Neehal ta ja ta su ka hau sama. Bayan sun shiga daki Neehal ta dube ta ta ce "Mai ya sa ki ka kula ta dan Allah? Kin san halin ta fa." Haneefah ta na ware rolling d'in kanta ta ce "Amma dai ai gaskiya na faɗa mata, ita say ta yi ta yi wa mutane kallon banza ta na musu masifa, ni kuma zan mata shiru ne, ai ba tsoron ta nake ba." Neehal ta ce "Na san bakya tsoron ta dama, amma dan Allah ki dai na kula ta, kome za ta yi." Haneefah ta ce "Shikenan Insha Allahu haka ba za ta kuma faruwa ba." Washegari tun safe su Hameedah suka shirya suka wuce Abuja. Mama ta haɗa musu tsaraba kamar yadda take wa kowa idan ya zo gidanta. Hameedah kuwa kamar karta tafi saboda ganin Ameen da take, shi kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba. Hameedah ta na bala'in mutuwar son Ameen, shekarun ta kusan 30 amma ta ƙi aure wai jiran shi take, Family kowa ya ɗauka soyayya suke nan kuwa ita kaɗai take haukan ta. Mahaifiyarta kullum ta zo sai ta ce wa Dad ya kamata a saka ranar bikin su, a duk lokacin da ta fadi haka sai Dad ya yi murmushi ya ce "Suwaiba Na fi so Ameen ya yi maganar Hameedah da kansa, ko kuma so ki ke ya raina mini 'yar tawa ya ga kamar neman kai muke da ita." Ita kuwa Suwaiba (Momy) sai ta kada baki ta ce "Yoo tunda shi ya ƙi magana ai mu sai mu yi, abu duk na gida ai duk ɗaya ne."


Da daddare Mama ta na part d'in Dad suna tattaunawa akan maganar Ameen ɗin da Hameedah, ya na faɗa mata yanda Mommy'n Hameedah ta takura masa da zancen ayi_ayi aurensu. Mama ta ce "Ni kaina Gen. na matsu Ameen ya yi aure, na gaji da yawo da hankalin da yake mana." Dad ya ce "Hakane, nima ina son na ga ya yi auren, amma bari na kirashi na ji ra'ayinsa a kan Hameedan, tunda ni bai taɓa mini batun ta ba da kansa." Mama ta ce "Toh." Dad ya kira Ameen a waya ya sanar masa ya na son ganinsa yanzu. Bayan 10 minutes sai gashi ya zo, ya zauna a ƙasa ya na duban Dad ya ce "Ga Ni Dad" Dad ya ce "Dama akan maganar Hameedah ne, tunda auren Neehal ɗin Allah bai nufa ba, dama shi muke jira a yi sai mu yi zancen naka, to yanzu ka na son Hameedan ne?" Ameen ya d'ago ya dubi Dad, cikin nutsuwarsa ya ce "Ni fa Dad ba na son Hameedah, Ina da wadda nake so!" Da sauri Mama da ta k'ura masa ido ta ce "Kamar ya ba ka son ta?" Dad ya d'aga mata hannu ya na ɗan murmushi, sannan ya dubi Ameen ya ce "Wa ce wacce ka ke so ɗin?"..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










1️⃣0️⃣










............ Ameen ya yi shiru tare da sunkuyar da kansa ƙasa. Mama ta na duban Dad ta ce "Kai ka biye masa ai, ban da haka mene aibun Hameedan da zai ce ba ya sonta?" Dad ya ce "Haba Doctor, kin san dai ba zan yi masa auren dole ba tunda ba ya sonta Shikenan." Dad ya maida dubansa ga Ameen ya ce "Kai muke sauraro." Ameen cikin dakiyarsa ya ce "Hafsah!" "Hafsat kuma?" Mama ta tambaya cikin mamaki. Ameen ya gyad'a mata kai. Mama ta ce "Dama har yanzu ku na tare da ita ?" Nan ma kan ya kuma gyad'a mata. Dad ya na murmushi ya ce "Masha Allah, A Ina ita Hafsan take? 'Yar waye?" Mama ta ce "Hafsat fa 'yar gidan Alhaji Nuhu Ɗan gaske" Dad ya ce "Allah sarki, to Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Insha Allahu a satinnan zan samu shi Mahaifinnata mu yi magana, a san abun yi." Mama ta ce "To Allah ya tabbatar da Alkhairi" Dad ya ce "Amin" Ameen ya mik'e kansa a ƙasa ya fice daga falon, Mama ta bishi da kallo cikin mamakin shi, maida kallonta ta yi ga Dad bayan ya fice ta ce "Al'ameen halinsa sai shi, yarinyar nan Hafsat ba irin son da ba ta nuwa masa ba a baya, amma ya nuna ba ya son ta, yanzu kuma da bakin shi ya dawo ya ce ya na sonta" Dad ya ce "Haka Al'amarin Allah yake, kin san matar mutum kabarinsa, wata ƙila duk wannan abun da ake itace matar tasa" Mama ta ce "Hakane, Allah ya sa Albarka ya sa da mu za'a yi." Dad da fara'a ta ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce "Amin." Mama ta ce "Um, sai wata fara'a kake kamar an maka wani albishir ɗin." Dad ya yi 'yar ƙaramar dariya ya ce "Wlh ba ki ji yanda farin ciki ya lullub'e ni ba da Ameen yau ya furta mun ya fidda mata, dama ni tsoro na kar mu bashi mata a zo a samu matsala zumuncinmu ya ɓaci." Mama ta ce "Gaskiya kam, amma Ni na so Ameen ya auri Hameedah, ko dan yanda take k'aunarsa, ga ta kuma jininsa ce, yanzu idan Family suka ji zancen nan ya kake ganin za su ɗauki maganar, tunda kowa ya na tunanin Ameen Hameedah zai aura, ita kanta Hameedan ban san wanne hali za ta shiga ba idan ta ji wannan zancen." Dad ya gyad'a kai ya ce "Nima na so hakan Doctor, Amma kin san yaran yanzu ba'a musu dole, ni ba na so a samu matsala ne, shi ya sa ban tursasawa Ameen a kan lallai sai ya Auri Hameedah ba, itama Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta." Mama ta ce "Amin ya Allah." Wayar Dad ce ta fara ringing, dubawa ya yi sai kuma ya saci kallon Mama, ƙin d'aga wayar ya yi har ta katse, aka kuma kira ya kuma ƙin d'agawa. Mama ta ɗauke kai kamar ba ta gani ba, kiran da aka kuma yi ya sa Mama mik'ewa tsam ta zagaya ta ɗauki wayar ta duba, Dad ya yi murmushi ya na kallonta ya ce "Ba wata ce take kirana ba sarkin kishi." Mama ta haɗe rai ta ce "Hubby! Har yanzu dama ka na tarayya da Alhaji *Kabir Ginyau* ?" Dad ya riko hannun Mama tare da zaunar da ita a gefensa ya ce "Ehh, amma ba tarayya irin wadda muka yi da ba, kawai dai mu na gaisawa ne sama_sama." Mama ta ce "Amma..." Dad ya d'aga mata hannu cikin lallami ya ce "Kin ga Doctor, Dan Allah kar ki tada hankalinki a kan dan Kabir ya kira ni, yanda kike tunanin abun kwata_kwata ba haka yake ba." Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa.




Washegari da safe Neehal ta na kitchen ta na yin breakfast Ameen ya shigo part d'in, ganinta a kitchen d'in ya sashi shiga kitchen d'in. Neehal ta juyo ta na kallonsa jin k'amshin turarensa, a hankali ta ce "Ina kwana Yaya?" Ameen ya ce "Lafiya k'alau, ina Mama fa?" "Ta na d'akinta" Neehal ta bashi amsa ta na satar kallonsa, shima kallon nata yake yi hakan ya sa suka haɗa ido. Neehal ta ɗauke idonta da sauri ta na turo bakinta gaba. "Idan kin gama ki kawo mun nawa breakfast d'in part d'ina." Ya fadi haka tare da juyawa ya fice, Neehal ta bishi da kallo kawai.
Mama ta na zaune a kan darduma ta na karatun Alkur'ani mai girma ya shigo d'akin, sai da ta kai ƙarshen aya sannan ta rufe ta d'ago tare da amsa masa sallamar da ya yi. Ameen ya zauna a gefenta ya ce "Ina kwana Mom, dafatan kin tashi lafiya?" Mama ta ce "Lafiya k'alau, and you?" Ya ce "I'm fine." Mama ta ce "Masha Allah, am Ameen dama ina son na tambayeka." Ameen ya dubi Mama amma bai ce komai ba. Mama ta ajiye Kur'anin hannunta a kan bedside locker, sannan ta fuskance shi da kyau ta ce "Me ya sa ka ce ba ka son Hameedah?" Ameen cikin nutsuwarsa da sanyin muryarsa ya ce "Mama! Kin san wace Hameedah kuma kin san halinta, kwata_kwata ba ta da qualities d'in matar da zan iya aura." Mama ta ce "Na san da haka Ameen, amma ba ka tunanin yanda Family'n Dad d'inka za su ɗauki abun? Kowa zai yi tunanin Ni na hanaka auren Hameedah saboda ba ma shiri da Mahaifiyarta." Ameen ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa sannan ya ce "Kar ki damu kanki Mama da su, su faɗi duk abun da za su faɗa." Mama ta tsura masa ido kawai ba ta ce komai ba. Kawar da zancen ya yi ta hanyar faɗin "Yaushe wacce old Woman d'in za ta tafi?" Mama ta ce "Bansani ba, tunda uwar tawa ce Old Woman." Ameen ya mik'e ya na faɗin "Tunda ba za ki faɗa mun ba zan tambaye ta da kaina." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa daga d'akin. D'akin Hajiya ya leƙa ya tarar da ita a kan darduma ta na lazimi ta na gyangyad'i, ya yi murmushi kawai ya juya ya fice. Neehal ta na gab da kammala aikin da take Mama ta shigo kitchen, Neehal ta kwab'e fuska tare da turo baki gaba. Mama ta dube ta, ta ce "Sannu Daughter." Neehal ta ce "Yawwa Mama, kin fito." Mama ta ce "Eh, amma ba yanzu zan fita ba, kawo na ƙarasa aikin ki je ki yi azkar ɗin safe dan nasan ba ki yi ba." Neehal ta ce "Toh Mama." Harta fita daga kitchen d'in sai kuma ta dawo, Mama ta kalleta da alamun mamaki amma ba ta ce komai ba, Neehal kanta na ƙasa ta ce "Yaya ya ce in kai masa break ɗinsa part ɗinsa." Mama ta ce "Yanzu dawowa ki kai masa?" Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce"Ki wuce ki yi abin da na ce miki, zan bayar a kai masa." Neehal ta turo baki sannan ta juya ta fice. Bayan ta gama azkar ɗin ta sakko ƙasa ta na break Mama ta ce mata, "Za ki aiki ne yau?" "A'a." Neehal ta bata amsa. Mama ta ce "Idan kin gama ki shirya ki je gidan Sadiya, daga nan sai ki biya gidan A'isha, su na ta complain kin dena zuwar musu 2 days." Neehal ta yi murmushi ta ce "To Mama, bari na kira besty mu je tare."


Kafin azhar su Neehal sun je gidan Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta tare su da fara'a sosai, bayan sun gaisa ta kawo musu drinks su na zaune a falo Aunty Sadiya ta dubi Neehal ta ce "Ni kuwa Daughter Ina son in miki wata tambaya." Neehal ta maida hankalin ta duka a kan Aunty Sadiya ta ce "Ina jin ki Aunty." Aunty Sadiya ta ce "Ki na da saurayi bayan Anwar ne?" Neehal ta ce "A'a, dan gaskiya ba na kula duk masu nuna suna so na, tun daga lokacin da a ka yi Engagement ɗinmu da Anwar." Aunty Sadiya ta ce "Babu wani wanda yake son ki tun da dad'ewa kafin haɗuwar ki da Jameel, kuma har yanzu ya na nuna ya na sonki?" Neehal ta ce "Ban gane ba Aunty?" Aunty Sadiya ta ce "Ina nufin kamar shekaru Biyar da suka wuce, ba ki yi wani saurayi da ya nuna ya na sonki ba, kuma har yanzu bai daina son ki ba.?" Neehal ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Gaskiya ba na jin akwai, idanma da akwai na manta." Aunty Sadiya ta gyad'a kai sannan ta maida dubanta ga Haneefah da take saurararsu ta ce "Ke fa Haneefah ko kin sani?" Haneefah ta ce "Gaskiya samarin Neehal na baya duk sun hak'ura da ita, wasu ma sun yi Aurensu." Aunty Sadiya ta ce "Alright." Neehal ta ce "Amma me yasa ki ka mun wannan tambayar Aunty?" Aunty Sadiya ta ce "Kawai." Daga haka suka shiga wata hirar. Sai bayan la'asar suka bar gidan Aunty Sadiya, wadda cikin hikima take yi wa su Neehal tambayoyi domin samun wani information d'in da zai taimake ta gurin binkicen da take. Kamar yadda Mama ta ce gidan Aunty A'isha suka wuce, nanma sun sha hira da Aunty A'isha sai bayan sallar Magriba suka yi haramar tafiya, shima sai da Mama ta kira su ta ce "Ko kwana za su yi a nan ɗin ne?" . Neehal ta na ɗaukar hand bag d'inta ta ce "Toh Aunty mun tafi sai gani na biyu." Aunty A'isha ta ce "Yanzu ba za ku jira driver'n ya dawo ya kai ku ba tafiya za ku yi?" Neehal ta ce "Gwara mu tafi Aunty, tunda ba mu sani ba ko ba zai dawo da wuri ba, gashi kin kira wayarshi ta ƙi shiga balle mu ji in ya na kusa mu jira shi." Aunty A'isha ta ce "Toh Shikenan, ku gaida gida, ku gaida su Hajiya da Yaya Fatimah." Neehal ta ce "Za su ji Insha Allah." Haneefah ta yi wa Aunty A'isha sallama, Aunty A'isha ta ce ta gaida Mamanta sannan suka tafi. Suna fitowa daga gidan Haneefah ta dubi Neehal ta ce "Wai me ya sa ba za ki kira driver'nki ya ɗauke mu ba?" Neehal ta ce "Kawai yau Napep nake so mu hau." Haneefah ta ce "Kin shiga uku da tsurfa, ko mai ciki haka ta ganki ta k'yale." Neehal ta ce "Na ji ɗin." Suna tafiya suna hirarsu, sun zo dai_dai ƙarshen layinsu Aunty A'isha za su fita titi wata had'ad'd'iyar Mota ta shigo layin, kamar ance Neehal ta kalli Motar suka haɗa ido da ma mallakin motar wanda ya kasance saurayi, kuma a ka yi sa'a ya zuge glass d'in Motar, wata irin fad'uwar gaba Neehal ta ji dalilin haɗa ido da suka yi da shi, da sauri ta ɗauke kallonta daga gurin Motar bugun zuciyarta na sauyawa...........✍️








*Ku yi hak'uri da wannan Please, wlh na shiga wani uzurinne, sai yanzu na samu time, da k'yar ma na iya typing ɗinnan saboda ciwon kai da nake fama dashi.😥🙏*








*By*
*Zeey Kumurya*


[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_










1️⃣1️⃣












*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽


*500MB* 200


*1GB* 300


*2GB* 600


*3GB* 900


*6GB* 1800


(CHECKING BALANCE * 461*4# )


VALIDITY : 1 MONTH




For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*












...........Ƙoƙarin b'oye baƙon yanayin da ya risketa lokaci ɗaya ta yi dan kar Haneefah ta fuskanta. Yanda take ta sauke numfashi a kai_a kai ya sa Haneefah dubanta da mamaki ta ce "Ya dai?" Neehal ta girgiza mata kai. Haneefah ta ce "Mu tsaya a nan mu samu Napep ɗin, tunda kin samu tafiyar ƙasa, gashinan ba'aje ko ina ba kin gaji." Neehal ta ce "Ni na ce miki na gaji?" Haneefah ta ce "Ba ki faɗa ba, amma na ga alama, sai sassauke numfashi ki ke kamar wadda ta yi tseren gudu raguwa kawai." Neehal ta harareta ba ta ce komai ba, suka tsaya domin duba abun hawa. A hankali yake yo baya da Motar tasa cikin tsananin zak'uwa da son ƙara ganin fuskar Neehal, tabbas idan har idanunsa ba gizo suke masa ba, matashiyar 'yar jaridar nan ya gani wadda take matuƙar burge sa tare da abokiyar aikinta. Duk yadda ya so ya wuce ba tare da ya musu magaba amma ya kasa, duk da tarin gajiyar dake addabar gaɓɓan jikinsa, hakan ya sashi bin shawarar zuciyarsa na bin su domin ya musu magana. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya hango su tsaye a bakin titin, da alamun abun hawa suke jira. Neehal da har lokacin zuciyarta ba ta daina bugawa ba ta ga Mota kamar daga sama ta yi parking a gabansu. Kallon juna suka yi ita da Haneefah da sauri da alamun mamaki. Ba su gama mamakinsu ba suka ji wata daddadar murya mai sanyi daga cikin Motar ta na faɗin "Assalamu alaikum." Haneefah ce ta yi ƙarfin halin amsa wa, Neehal kuwa ƙasa ta yi da kanta gabanta na ci gaba da fad'uwa. "Ina yininku?" Ya gaishe su idanunshi a kan Neehal. Haneefah ta yi ɗan murmushi haka kawai ta ji Matashin ya burgeta, "Lafiya k'alau, amma na ji kunyar amsawa, saboda mu yakamata mu gaishe ka, tunda ka na gaba da mu." Cikin jin daɗin kalaman Haneefah ya ce "Haba k'anwata kar ki ji komai, ai durk'usawa wada ba gajiyayawa ba ne." Haneefah ta ce "Hakane." "Ita k'awar taki ba ta magana ne?" Ya yi maganar idanunsa a kan Neehal. Haneefah ta ce "Hmmm, gajiya ta yi ne daga ɗan......." "Ke! ki zo mu tafi, ki na sane Mama ta ce kar mu yi dare, a hakan ma kin san sai ta yi faɗa." Neehal ta katse Haneefah a ɗan zafafe. Murmushi ya yi har yanzu ya kasa ɗauke idonsa daga kanta, cikin wani irin salo mai narkar da zuciya ya ce "Gaskiya ba na so Mama ta muku faɗa, idan babu damuwa ku shigo in kai ku gidan mana." Neehal ta yi sauri ta ce "A'a mun gode." Ta ƙarashe maganar ta na turo baki gaba ganin yanda ya tsareta da ido, duk ya bi ya wani dabaibaye ta." "Please and please, ba danni ba, 'yar k'anwata." Ya fadi maganar cikin marairaicewa. Haneefah ta ce "Ka yi hak'uri, idan ka kai mu gida za'a yi mana faɗa." Ya ce "Waye zai muku faɗan?" Haneefah ta ce "Mama, za ta ce me yasa ba mu kira an ɗauko mu ba." Ya ce "Sai in shiga in mata bayani, In ce sabon ɗa ta yi shine ya kawo k'annensa gida." Haneefah za ta kuma magana ya katse ta da faɗin "Kar mu tsaya ja_in_ja daku, ku shigo kawai mu tafi, kunga kun ce za'ai muku faɗa idan ku kai dare, ni kuma bazan barku ba sai na kai ku gida." Haneefah ta yi murmushi ta ce "To Mun gode." Neehal ta ɓalla mata wata uwar harara, Haneefah ta mata gwalo ta wuce ta zagaya ta buɗe murfin Motar ta shiga, ita ma Neehal ba ta da zaɓi wanda ya wuce ta shiga Motar tunda Haneefah ta riga da ta shiga. Karon farko a rayuwarta da ta shiga Motar wani wanda ba ta sanshi ba, amma fa ta ɓata rai sosai alamun ba ta so. *Sadik* ya yi murmushin jin dad'i, wani irin nishad'i yake ji a ransa, gajiyar da take damunsa tuni ya neme ta ya rasa. Neehal ta lumshe idanunta ta na sauke numfashi saboda k'amshin da ta shak'a da ta shiga Motar, wanda ya haɗe da sanyi Ac. K'amshin ya mata daɗi sosai domin har shige ta ji ya mata da na Yayanta. Sadik ya tambayi Haneefah unguwar su ta faɗa masa, kunna Motar ya yi suka hau titi suka fara tafiya. Su na tafiya su na hira da Haneefah wadda ta saki jiki sosai da shi kamar sun dad'e da sanin juna, Neehal kuwa sai harara take bankawa bayan Haneefah, ita ko ba ta ma san ta na yi ba. Har layinsu Neehal ya kai su, daidai k'ofar wawakeken gate d'in gidan Haneefah ta ce ya tsaya, bayan ya yi parking Haneefah ta ce "To new Bro, mun gode sosai fa." Sadik ya na murmushin da ya ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce "Haba sai kace wani abun, ai nine da godiya da har kuka yarda kuka shigo 'yar akwalar Mota ta, kuna Manyan 'yan jarida." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kai Yaya na akwai ka da zoyala." Neehal ta tab'e baki, kamar ba ta son magana ta ce "Mun gode, Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment