Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yana ɗaya daga cikin abun da ya ja hankalinta a kansa, gashi ya iya kula da mace, ta tabbatar za a bashi lamba ɗaya a wannan fannin, ta san sai a tara maza ɗari kafin a samu wanda iya tarairayar mace da nuna mata tsantsar k'auna kamar Ameen ɗinta. Ya miƙe ya fice daga falon, ta bi shi da kallo. Komai nasa kyau yake mata, tafiyarsa ma kaɗai abun burgewa ce. Tana son Ameen over shi yasa bata son ɓacin ransa ko kaɗan, duk abun da ta san zai ɓata masa rai ko yaya ne gudun shi take. Shi yasa take danne duk abun da take ji a ranta a duk lokacin data gan su tare da Neehal, dan ta san bata isa ta nuna masa ɓacin ranta ba akan haka. Ta tsani Neehal over, tsanar da ita kanta bata san adadinta ba, tun lokacin data samu labarin ba su Mama ne suka haife ta ba ta ji yarinyar gaba-d'aya ta fice mata a rai.. Maganar Mama data dawo falon ne ya katse mata tunanin da take. Mama ta ce "Au Ameen ɗin fita ya yi?" Hafsah ta ce "Eh ya je masallaci." Mama ta ce "To mu je sama kema ki yi Sallar, na ji an fara kira." Hafsah ta miƙe ta bi bayan Mama. Bayan ta idar da Sallah Mama ta kawo mata abinci, tana cikin ci Ameen ya dawo gidan. Neehal kuwa tana ɗakinta ta ƙi fitowa, har sai da ta tabbatar sun bar gidan sannan ta fito falo. Anan ta tarar da Mama, ta zauna a kusa da ita ta shiga bata labarin zuwan ta gidan Uncle Umar. Cikin farin ciki Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin wannan labarin, dama kullum fata na da addu'a ta Allah ya waiwayo da hankalin danginki gare ki, ku dinga zumunci kamar kowan ne ahali." Neehal ta ce "Nima Mama na ji daɗi sosai, ba ki ga yanda Uncle Umar yake mun magana ba, cikin kulawa kamar ma kunya ta yake ji akan abubuwan da yay mun a baya." Mama ta ce "Haka muke so dama, Allah ya ƙara shirya mu ya nuna mana gaskiya da sani akan abubuwan da muke aikatawa ba dai_dai ba." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci, bari na je part ɗin Daddy." Neehal ta ce "Toh." Tare da miƙewa, ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta ta kira Uncle Usman ta sanar masa sauyawar da Uncle Umar yay mata. Daren yau ba su yi waya da Ahmad ba, tana ganin yana kiran ta ƙi pick. Washegari da safe ma tana ganin kiran sa lokacin tana gurin aiki shima ta ƙi ɗauka. Bayan Magriba Sadik ya zo gidan kamar yadda ya saba zuwa, sun jima suna hira a gurin da suka saba zama. Har yake mata zancen shi kam zai turo iyayensa a yi maganar aurensu ya matsu ya ganta a cikin gidansa a matsayin matarsa ta sunna. Cikin jin kunya ta ce masa babu matsala zata yiwa Mama maganar idan ta koma ciki.








Zuciyar Sadik Cike da farinciki ya koma gida, a main Parlour ya tarar da iyayensa da k'annensa kamar kodayaushe. Ya yiwa iyayen nasa sannu da gida ƙannansa kuma suka yi masa sannu da zuwa ya shige ɗakinsa. Bayan shigar sa ɗakin ba jimawa Batul ta zo ta ce ya je Abbansu yana kiran sa a part ɗinsa. Ya amsa tare da tashi ya biyo bayanta suka fito. Abba yana zaune shi da Umma da Maamah, kamar yadda tsarinsa yake idan zai yi magana da ƴaƴansa a gaban su Maamah yake yi. Sadik ya samu guri ya zauna a ƙasa bayan ya ƙarasa falon Abban. Abba ya dube shi cikin kulawa ya ce "Abubakar na kira ka ne akan maganar yarinyar da kake zuwa gurinta, kamar yadda na ce zan yi bincike akanta da iyayenta na yi, kuma Alhamdulillahi na samu kyakkyawan sakamako kamar yadda ake fata dama. An tabbatar mun yarinyar tana da tarbiyya, mahaifinta kuma mutumin kirki ne. Dan haka na yarje maka ka cigaba da zuwa gurin ta." Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Maamah na farinciki. Sadik kuwa ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bayanan Abba, daman ya san babu wata matsala da za'a samu a gurin Neehal. Maamah ta ce "Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Abba ya ce "Ameen." Tare da mayar da duban sa ga Sadik wanda kansa ke ƙasa ya ce "Ashe ma yarinyar nan ce mai aiki a gidan TV na ASTV?" Sadik ya shafa kansa ya ce "Eh ita ce Abba." Abba ya ce "Masha Allah, Allah ya yi mana jagoranci." Umma da baƙin cikinta ya kasa b'oyuwa akan fuskarta ta tari numfashin Abba ta ce "Alhaji wacce yarinya na ji kana magana a kanta? Ba dai Neehal ɗin nan ba ta gidan Alh. Tafida?" Abba ya ce "Ita mana, ai yarinyar da mahaifinta sanannun mutane ne a ƙasar nan." Umma ta jinjina kai irin ta ga mugun abun nan ta ce "To gaskiya Alhaji baka yi bincike yanda ya kamata ba, indai akan yarinyar nan ne?" Abba ya ɗan canza fuska ya ce "Kamar yaya kenan?" Umma ta tab'e baki ta ce "Ita yarinyar fa su Alhaji Tafidan ba su ne asalin iyayenta ba." Sadik ya d'ago da sauri ya kalle ta, Maamah zata yi magana Abba ya riga ta da faɗin "Kamar ya ba su ne iyayenta ba Ruqayyah? Ban gane me kike son faɗa ba." Umma ta ce "Ina nufin riqon ta suke Alhaji ba ƴarsu ce ta cikinsu ba, riqonta kawai suke amma ko dangi ba su haɗa ba." Abba ya ce "Wannan ai ba wata matsala ba ce, indai tana da asalinta ai shikenan." Umma ta ce "Hmm, hakane. Amma kuma akwai wata matsalar bayan wannan." A harzuk'e Maamah ta ce "Wai ni Rukayya dan Allah me Yaron nan ya tsare miki a gidan nan ne, duk abun da zai yi sai kin san yanda kikai kika kawo masa cikas, akan wane dalili zaki takurawa ɗana? Me ya tsare miki?" Abba ya d'aga mata ya ce "Ya isa haka Kaltum, barta ta ƙarasa maganarta." Umma ta harari Maamah sannan ta cigaba da magana. "Abu na biyu Alhaji, wanda na same sa daga majiya mai ƙarfi akan yarinyar, na so in ɓoye maka kar in faɗa a mun wata fassarar daban, amma na kasa saboda yanda ba zan bari a cutar da ɗan cikina ba, haka ba zan bari a cutar da naka ba. Ita yarinyar ce duk wanda zata aura sai an kashe shi..." A zabure Sadik ya miƙe tsaye yana duban Umman, zuciyarsa na wani irin bugu ba tare da ya ji ƙarshen zancen nata ba." Abba ya haɗe rai sosai ya ce "Kin ga Rukayya, bana son shirme wannan wacce irin magana ce mara ma'ana?" Umma ta ce "Wlh Alhaji ba ƙarya ba ne, nima na girgiza da na ji zancen dan da farko ma ban yadda ba sai da aka tabbatar mun, samari har biyu sai an saka ranar Aurensu sai a wayi gari a tarar an kashe su idan....." A fusace Abba ya katse ta da faɗin, "Wannan duk ba hujja ba ce Rukayya, Babu mai kashewa da rayawa face Ubangiji, suma waɗanda suka rasun kwanansu ne ya ƙare. Dan samarin yarinya guda biyu sun rasu baza a ce daga ita ba ne, Ubangiji ne ya karb'i abinsa. Dan haka kar na ƙara jin wannan maganar mara kai da tushe, kuma wannan dalilin ba zai sa na hana Sadik cigaba da neman Auren yarinyar ba." Yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakin baccinsa. Maamah ta sauke ajiyar zuciya cikin jin daɗin yanda mai gidan nasu bai goyi bayan abokiyar zamantata ba a wannan karon. Miƙewa ta yi ta kama hannun Sadik dake tsaye kamar an dasa shi suka bar falon, ba tare da ta kuma kallon inda Umman take ba. Umma ta yi ƙwafa tare da raka su da harara, a fili ta furta "In kun san wata baku san wata ba ai, wallahi indai ina raye Sadik ba zai auri wannan yarinyar da Ubanta yake da arzik'i ba, mu zuba mu gani, shege ka fasa."








Har ɗakin Sadike Maamah ta kai shi ta zaunar da shi a bakin gadonsa. Cikin tausasawa ta ce "Kar abun da Rukayya ta faɗa ya d'aga maka hankali Sadik, ka dai san halinta ba sai na faɗa maka, zata iya yin ko wanne irin sharrin dan ganin auran ka da yarinyar nan bai yiyu ba. Ka dogara da Allah, ka kuma dage da addu'ar neman zab'insa ka ji." Sadik ya d'aga mata kai yana sakin ajiyar zuciya. Sai da kwantar masa da hankali sannan ta bar ɗakin. Kwanciya ya yi bayan fitar Maamah zuciyarsa na tariyo masa abun da Umma ta faɗa akan Neehal, tabbas ya san Sauratinta ya rasu kafin su haɗu, har Haneefah ma ta tabbatar masa da an kusa bikinsu lokacin da ya rasun. Amma bai san da wani ba bayan shi ba. Wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake da mamakin cewa wai ba su Mama ne suka haifi Neehal ba, shi ko kaɗan ma bai yarda da wannan batun ba. A yanda yake jin Neehal a cikin ransa koma me za'a faɗa a kanta ba zai iya rabuwa da ita ba, ko yaya take yana son abarsa kuma a haka zai aure ta. Balle ma ya san bata da wani aibu. Tashi zaune ya yi a ransa yana faɗin 'Dole ma ya yiwa Maamah magana ta faɗawa Abba ayi_ayi a saka ranar bikinsu kowa ma ya huta.' Ko da suka yi waya da Neehal yau sai da ta gane kamar yana cikin damuwa har ta kasa shiru ta tambaye shi. Amma ya ce mata babu komai, dan Maamah ta gargad'e shi akan kar ya sake ya yiwa Neehal zancen. Umma kuwa bayan ta koma ɗaki Yayan Abban su Sadik wanda suke kira da Kawu ta kira ta sanar masa ƙarya da gaskiya akan yarinyar da Sadik yake nema. Kawu ya dinga masifa a waya kamar zai ari baki yana faɗin "Shi Surajon (Abba) ba shi da hankali ne yana ji yana gani zai salwantar da rayuwar ɗansa har zai da ce wannan abun ba wata matsala ba ce? To ina nan zuwa a cikin satin nan in same shi, domin kuwa wannan yarinyar dole Sadik ya rabu da ita." Cikin jin daɗi Umma ta masa sallama, zuciyarta fari k'al kamar takarda.
















Bayan kwana biyu Ranar Laraba Neehal ta dawo daga gurin aiki da Yamma, tana zaune a ɗakinta tana operating system Mama ta shigo ɗakin, bayan ta yi Sallama Neehal ɗin ta amsa mata ta ce "Neehal Ahmad ya zo, yana ƙasa." Ta d'ago kanta da sauri ta ce "Uncle Ahmad kuma?" Mama ta ce "Ki yi sauri ki je kar ki bar shi yay ta jiran ki, na san ki da shiririta." Neehal ta ce "Toh." Sannan ta miƙe ta ɗauki Hijabi ta zira ta fito. Haka kawai ta ji zuciyarta na d'okin ganin sa, ko dan ta kwana biyu rabon ta da shi ko a waya ne. Yana zaune hannunsa tallafe da fuskarsa idanunsa akan steps, wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke jin takun tafiyarta. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon. Ya miƙe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya ƙarasa gabanta ya tsaya daf da ita kamar zai rungume ta, cikin wata irin murya ya ce "Princess!" A hankali ta ce "Na'am Uncle." Ya kamo hannunta tay saurin k'wacewa tare da yin baya ta zauna akan kujera. Ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta ya ce "Princesss mai ya faru idan na kira wayarki bakya ɗauka, ko wani laifin na miki?" Ganin yanda yake magana cikin damuwa sai ta ji tausayinsa mai tsanani ya cika mata zuciya, har ta fara da na sanin abun da ta yi masa. Cikin raunin murya ta ce "I'm sorry Uncle, ka koma ka zauna akan kujera." Ya girgiza mata kai tare da faɗin "No Princess, please tell me me ya faru." Ta ce "Seriously babu komai Uncle ɗina." Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa jin yanayin da ta yi magana ya tabbatar masa babu komai ɗin. Ya koma ya zauna sosai tare da zuba mata idanunsa. Cikin marairaicewa ya ce "But Princess why? Na shiga damuwa sosai da ƙin d'aga kira na da kike, har na fara tunanin ko ba lafiya ba. Na karb'i Numbern Mama a gurin Ummi na kira ta, dan nasan in ma ba lafiya zata sanar mun, amma jin bata ce mun akwai matsalar komai ba sai hankalina ya ɗan kwanta, amma kewarki gaba-d'aya ta hana ni sukuni. Kwana ukun nan da ban ji muryarki ba gaba-ɗaya bana cikin nutsuwata, yau dai na kasa jurewa na ce sai na zo na gan ki." Ta lumshe idonta cikin sanyin murya ta ce "Nima na yi kewar ka Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce "To me yasa kika daina ɗaukar kira na." Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa ta ce "Babu komai fa Uncle ka yarda da ni." Ya ce "Uhm, salon ki tayar mun da hankali ne kawai ko?" Ta ce "A'a, i'm sorry ba zan kuma ba." Ya ce "Shikenan Princess." Ta ce "Ina yarana, me yasa baka zo mun da su ba?" Ya ce "Bari na yi sai next week idan sun yi hutun school sai na kawo miki su." Ta ce "Allah ya kai mu, Ya su Ummi?" Ya ce "Duk suna nan lafiya lau." Hira suka sha sosai yau, dan ita kanta sai yanzu ta tabbatar ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Anan ya yi Sallar Magriba, yau kam ya ci abinci kaɗan a gidan saboda gudun ɓacin ran Princess ɗin tasa. Sai kusan isha'i ya tafi zuciyarsa cike da nishad'i, saɓanin kwana biyun da suka wuce wanda ya yi su cikin damuwa. Itama Neehal anata ɓangaren cike take da farincikin kasancewa da Uncle ɗin nata a yau. Bayan ya koma gidan Mamy tai ta tsokanarsa tana faɗin "Ai fa yanzu dole yay ta musu zarya a Kano tunda zuciyarsa tana nan." Murmushi kawai yake mata baya cewa komai.








Bayan Sallar isha'i Mama tana falon sama tana kallo wayarta dake hannun kujerar da take kai a zaune ta fara ringing. Ta ɗauko ta duba tare da d'agawa ganin Aunty A'isha ce ke kiran. Ba tare da gaisuwa ba Aunty A'isha ta ce "Adda Fateemah! Yanzu Mai_gidan su Abban Neehal ya kira ni ya sanar mun cewar an samu nasarar kama mutanen da suka kashe Abban Neehal ɗin da Ummanta........✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*








```Ku yi haquri da rashin ganin update akan lokaci, kun san an ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi.```














..........Cikin hanzari mai nuni da tsantsar mamaki Mama ta tari numfashin Aunty A'isha da faɗin. "Da gaske A'isha?" Aunty A'isha ta ce "Dagaske mana Adda, shi Alhaji Alin ne tun bayan rasuwar su Abban Neehal ba jimawa ya kamu da rashin lafiya, aka fitar da shi Saudiyya ake masa magani. Ashe duk wannan shekarun da suka wuce abun yana ransa, sai a ƴan watannin da suka wuce ya samu lafiya ya dawo Nigeria. Shine yana dawowa yasa aka duk'ufa da binkicen waɗanda suka yi kisan a lokacin da ya samu labarin har yanzu ba'a gano su ba. Yanzun nan shi ya kira ni da kansa muna gama waya da shi na kira ki, ya sanar mun cewa tunda ya dawo ƙasar nan yake neman mu, amma bai samu labarin inda muke ba, sai daga baya tunanin ya je gadon ƙaya inda muka zauna ya zo masa, to a wurin wata mak'ociyarmu aka samo masa Number ta." Mama ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Alhamdulillah, Allah mun gode maka, yanzu ya ake ciki game da waɗanda suka yi kisan? Ya sanar miki ko su waye suka yi?" Aunty A'isha ta ce "A'a bai sanar mun ba, ya dai ce mun suna hannun Police a halin yanzu, ranar Monday za'a shiga kotu a yanke musu hukunci tunda sun amsa laifunsu, sauran bayani kuma ya ce sai mun haɗu." Mama ta ce "Ki ji wani ikon Allah A'isha, shekara fiye da goma sai yanzu Allah ya toni asirinsu, Allah ya ƙara tona asirin duk wasu masu laifi a cikin duniyar nan." Aunty A'isha ta ce "Ameen ya Allah, wallahi adda ba ki ji yanda na ji daɗi ba, Alhaji Ali ya cika ubangida na gari da ya tsaya tsayin daka ganin jininsu Abban Neehal bai tafi a banza ba." Mama ta ce "Allah ya saka masa da Alkhairi ya biya shi da gidan Aljannah." Aunty A'isha ta ce"Amin ya Allah, ya ce akai masa Neehal yana son ya gan ta." Mama ta ce "Aiko bai faɗa ba dole mu je har gida mu yi masa godiyar wannan jajircewar da ya yi, gobe gobe ma Insha Allahu za mu je, a wacce unguwa yake da zama?" Aunty A'isha ta ce "A rijiyar zaki, ya turo mun da address ɗin gidansa ta message." Mama ta ce "To Insha Allahu da safe za mu je, bari in je in sanar da Daddy wannan abun al'ajabi da farincikin." Aunty A'isha ta ce "Tom shikenan da safen zan biyo ta nan sai mu wuce, nima bari in je in sanar da Abban Maryam, in kira Sadiya itama in sanar mata." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben, sai mun yi waya." Daga haka suka yi sallama.






Mama ta dafe kanta tana sauke numfashi, zuciyarta cike da d'oki da zumud'in jin asalin zancen, domin ta san wa ya kashe su Abba ko kuma wa ya turo a kashe su, da kuma son sanin ko mutum ɗaya ne ya yi kisan su Abba da su Anwar? A ɓangaren Aunty A'isha itama tunanin da take yi kenan. miƙewa Mama ta yi ta nufi part ɗin Daddy cikin sauri dan ta sanar masa halin da ake ciki.










Cike da mamaki da kaɗuwa Daddy yake duban Mama bayan ta gama sanar masa da abun da yake faruwa. Zuwa can ya nisa ya ce "Allah buwayi gagara misali, dama an ce duk wanda yay kisan kai da wuya ya mutu Ubangiji bai toni asirinsa ba, saboda haqqin rai ba ya taɓa barin mutum ya zauna lafiya a duniya." Mama ta ce "Wannan haka yake, Allah ka raba mu da mummunar ƙaddarar da zata kai mu ga dana sani, su kuma azzaluman mutane irin waɗannan Allah ka cigaba da tona musu asiri!" Daddy ya ce "Amin Amin Doctor." Mama ta cigaba da magana. "Mutum bai ji ba bai gani ba kawai saboda rashin imani a zo har cikin gidansa a kashe shi saboda neman duniyar da kowa sai ya bar ta, mutane ba sa tuna Allah a ransu, ba sa tunanin inda suka kashe mutum ya je suma komai daren dad'ewa za su je." Cikin jimantawa Daddy ya ce "Ai ke dai ki bar mutum kawai Doctor, amma in dai duniya ce gata nan ta ishi kowa, kuma Duk *abin da mutum ya shuka* dai *shi zai girba* , walau na sharri ko na Alkhairi." Sun zanta akan al'amarin sosai sannan Mama ta miƙe dan zuwa ta sanar da Neehal itama.










Tana kwance ruf da ciki akan gadonta, system ɗinta na gabanta tana latsa ta cikin kwarewa, idanunta sanye da siririn glass mai ɗan duhu, wanda bata fiya amfani da shi ba, sai irin wannan lokacin idan zata yi using system. Mama ta shigo ɗakin tare da zama a bakin gadon bayan ta yi sallama. Neehal ta amsa mata tare da tashi zaune ta cire glass ɗin fuskarta ta ajiye a gefen ta. Mama ta ce "Aikin ne har yanzu baki gama ba." Ta ce "Na kusa ƙarasawa saura kaɗan, zuwan Uncle Ahmad ne ma ya tsayar da ni." Jinjina kai Mama ta yi tare da juyowa ta fuskance ta sosai ta ce "D'azu Auntinki ta kira ni take sanar mun an kama waɗanda suka kashe su Ummanki." Neehal ta waro Ido waje cikin kaɗuwa ta ce "Su waye Mama?" Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Aunty A'isha ta sanar mata. Kuka ta saka cikin kukan take faɗin "Mama me su Umma suka musu da suka kashe su? Su waye waɗannan mutanen da suka raba ni da mahaifana rabuwa ta har abada a rana ɗaya? Me nay musu suka zaɓi mayar da ni marainiya?" Kuka take sosai mai ban tausayi, mutuwar su Umma ta dawo mata sabuwa fil a cikin ranta, duk da a lokacin da suka rasu tana ƙarama amma har yanzu gawar iyayenta kwance cikin jini bata daina hango ta acikin idanunta ba, kuma har ta koma ga mahaliccinta ba zata taɓa mantawa ba. Mama ta rungume ta a jikinta cikin tsananin tausayinta, tare da rarrashinta da kalamai masu taushi har ta samu ta bar kukan. Mama ta d'ago ta tana share mata hawaye ta ce "Komai rubutacce ne daga Allah, Ubangiji ya riga ya tsara rana ɗaya Umma da Abba za su rasu kuma a lokaci ɗaya, ko da waɗan can Mutanen ba su kashe su ba idan kwanan su ya ƙare dole su bar duniya. Dan haka addu'ar mu kawai suke buƙata a halin yanzu, ita ce kawai soyayyar da za mu nuna musu. Mutuwa dole ce Neehal, mu ma nan zaman jiranta muke, fatanmu Allah yasa ta zo mana cikin sauqi." Cikin matuƙar sanyin jiki Neehal ta ce "Haka ne Mama, Allah ya ji k'an Umma da Abba da ma dukkan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya, mu kuma Allah yasa mu cika da imani." Mama ta ce "Ameen dan darajar Annabi." Lumshe idonta ta yi bata kuma cewa komai ba, cikin zuciyarta kuwa ji take dama a bata dama ta kashe azzaluman mutanen da suka kashe mata iyaye da hannunta, saboda wata muguwar tsanar su data cika mata zuciya. A hankali ta yi baya ta kwanta akan gadon saboda sarawar da ta ji kanta ya yi mata lokaci ɗaya. Mama ta janyo system ɗin da take amfani da ita ta yi saved na aikin da take sannan ta kashe ta, ta ɗora ta akan bedside locker. Shafa fuskar Neehal ta yi cikin raunin zuciya da tausayinta, cikin kulawa ta ce "Ki yi addu'a idan kina jin zuciyarki babu daɗi ba wai ki yi kuka ba, idan kin kasa barci kar ki kwanta ki yi ta tunane_tunane, ki tashi ki kaiwa Allah Kukanki." Ta gyaɗa mata kai ba tare data buɗe idonta ba. Mama ta kashe mata light ɗin ɗakin sannan ta fice zuciyarta babu daɗi. Iyayenka ko da ace baka san su ba kana jariri suka rasu idan ka girma aka baka labarinsu dole ka ji feeling a kansu da son kasance tare da su, balle ita da tana da ɗan wayonta suka rasu, dole abun ya dinga taɓa mata zuciya. Kuma da a ce mutuwa suka yi kamar kowa ba kashe su a kay ba, abun ba zai dinga damun ta over ba. Amma yanzu gani zata dinga yi kamar da ba'a kashe su ba da suna raye har yanzu....










Washegari kafin ƙarfe goma sha ɗaya na safe sun gama shiryawa dan zuwa gidan Alhaji Ali, Neehal dai kamar mai cuta komai a sanyaye take yin sa. Daren jiya kam ko wayar love ɗin data saba bata iya yi ba, da ta tashi da safen nan ma ko bi takan wayar bata yi ba. Sai da Mama ta ce mata ta kira gurin aikinsu ta sanar musu ba zata samu damar zuwa yau ba sannan ta ɗauki wayar. A time ɗin ne ta ga missed call ɗin Sadik, Ahmad har ma da Ameen wanda kiran nasa ya bata mamaki. Ahmad kam har da text yay mata ya sanar mata ya wuce Abuja, dama tun jiya ya faɗa mata da sammako zai yi ya koma. Bata bi kiran ko ɗaya daga cikinsu ba saboda tana cikin mood ɗin da ko doguwar magana bata son yi.










A

Please Login or Register in order to submit comment