Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce. "Ko ɗaya Sadiya babu d'igon ɓacin ran Ameen a raina, dan ya wanke mun shi tass kafin ya tafi. Amma Sadiya ni na haifi Ameen, na san halinsa ciki da waje, tabbas ko tantama bana yi akwai abun da ke damar mun yaro." Aunty Sadiya ta ce. "Tunda ya ce miki babu, a matsayin ki na mahaifiyarsa wadda babu hijabi a tsakanin addu'arki a gare sa, ki yi masa addu'a, Insha Allahu in ma da akwai abun da ke damun sa to Allah zai yaye masa." Mama ta ce, "Haka ne, Allah yasa mu dace. Mu je kiga kayan fitar bikin da ya kawo wa Neehal kafin ki wuce, ya ce mun ya kawo mata." Aunty Sadiya ta ce. "Masha Allah, Allah ya saka masa da Alkhairi. Mama ta ce, "Amin." Tare da miƙewa.








Washegari Neehal suka fita da Freind's ɗinta guda biyu na B.u.k rabon I.v, ba'a son ranta ta fita ba Mama ce ta tilasta mata. Da cewa ta yi zata turawa kowa ta waya, gate pass ɗin dinner kuma zata wakilta wasu su bayar a ranar. Mama ta ce, bata isa ba yara su yi mata anko sannan ta ƙi kai musu kati har gida. Sai yamma liss suka dawo, tana cin abinci kuma aka ɗora mata daga inda aka tsaya a gyaran jiki. Washegari ma ta fita, ta je gurin aikin su ta kai musu katin, sai kuma sauran Freind's ɗinta da ba su ƙarasa jiya ba. Ranar talata mai ƙunshi ta zo har gida tay musu ita da Mama da su Aunty Sadiya da Haneefah. Saboda Washegari ran Laraba za'a fara bikin, a yi Kamu Laraba, Alhamis a yi Dinner, Juma'a a daura aure akai ta gidan mijinta. Tun yau da taga an yi mata lalle ta ga tabbas da gaske dai auren zatai zata bar gaban Mama ta fara kuka sosai. Mama ta tsaya kawai tana kallon ikon Allah, ta rasa hali irin na Neehal, ta ga dai yara ma ƴanv17_18 years ana musu aure amma basa damuwa haka, sai ita mai 24_25 years. Aunty A'isha ce mai aikin rarrashinta. Tun yau gidan ya fara wadatuwa da baƙi, ciki har da Uncle Usman da matarsa da yaransa guda biyu. Neehal ta rungume shi cikin tsananin farincikin ganin sa. Ta ce "Uncle ɗina na yi kewar ka sosai." Ya yi murmushi ya ce, "Nima haka Daughter, rabo na dake tun kina ƙarama, gashi har kin girma kin zama ƙatuwa." Ta yi dariya cikin jin kunya. Aunty Hauwa ma amaryar Uncle Umar tun yau ta zo, su Hajiya ma da wasu ƴan Gombe haka. Ƴaƴan Ummi (Yayar Abba) Maza guda biyu su ma sun zo tare da matansu daga Lagos. Can yamma kuma sai ga Zahra da twins. Farincikin ganin yan'uwa da mutane anata zuwa ya ɗaukewa Neehal hankalin damuwar da take ciki. Ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud da Haneefah da Zahra, duk inda ta yi suna biye da ita, dama amarya akwai farinjini.










Ranar Kamu da safe sai ga Hameedah da Mommy'nta sun zo, abun ya bawa Mama mamaki amma bata nuna ba, ta karɓe su hannu bibbiyu. Saboda yanda suke nuna tsana ga Neehal bata yi zaton za su zo tun yau ba, ta ɗauka sai ranar D'aurin Aure za su zo. Kafin ka ce me gida ya ƙara cika da baƙi, ƴan'uwan su Mama da ƴan'uwan Daddy. Ba ya ma na Mama, dan Familyn su Mama suna da yawa Masha Allah. Ga shi dama Mama ita ta kowa ce, ko bata je inda kake akai_akai ba, akwai kira a waya ta sadar da zumunci. Hafsah ma ranar tun safe ta zo. Mama zuciyarta fari k'al da farinciki, yau Allah ya nuna mata zata fara taron bikin Neehal, duk da ba'a daura aure ba, amma yanzu zuciyarta babu fargabar komai kamar a baya da suke cike da tsoron kar a kuma kwata kashe wanda Neehal zata aura. Duk da sun fi alaƙanta hakan da shawarar da Uncle Mahmud ya bayar ta ɓoye batun auren sai da ya zo daf sannan aka bayyana. Gidansu Sadik ma ya fara harama da baƙi ƴan biki, suna ta nasu shirye-shiryen su ma. Amma fa har yanzu Hajiyarsu da Kawu ba san bikin suke ba, babu yanda za su yi ne kawai dan suna matuƙar jin kunyar Mahaifin Maamah, baza su iya yin jayayya da shi ba. Umma kuwa ta yi makircinta da kisisina akan ganin an fasa Auren amma bata yi nasara ba. Tun a jiya da safe bayan an gama yiwa su Aunty ƙunshi suka tafi gidan Neehal dake unguwar Tarauni yi mata jere, yau da sassafe kuma suka koma dan ƙarasawa. Masha Allah Gidan ya yi kyau, falo biyu ne da three bedrooms. Sai kitchen da store. Sai kuma ɗakin mai gadi kana shigowa gate daga gefe. Su Mama da Daddy kuma sun cika mata gidan da kaya na gani na faɗa.
















Ƙarfe biyu na rana Aunty Sadiya ta saka Neehal ta yi wanka. Ta fito ta zira doguwar riga ta saka hijabi suka ɗauki kayan da zata saka suka tafi gurin kwalliyar da already an yi bucking. Aunty Sadiya ta ce, ta kira Sadik ana yin Sallar la'asar saboda ba su san African time, ƙarfe huɗu aka saka a jikin kati amma kamar biyar haka su taho. Neehal ta amsa mata sannan ta je ta yiwa Mama Sallama suka tafi ita da Haneefah. Gurin kwalliyar ya haɗu sosai, shago ne a cikin wata ƙatuwar plaza dake nan cikin Nasarawa. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka fara yi musu kwalliyar, dan ba mutum ɗaya ce ke yi make up ɗin ba. An riga gamawa Haneefah saboda ita casual make up akay mata. Neehal kuma bridal ake mata. Masha Allah Haneefah ta yi kyau sosai, sai ma data saka kayanta akai mata dauri. Sai biyar aka gama shirya Neehal, faɗar irin kyawun da ta yi ɓata baki ne. Ta yi kyau ƙarshen kyau. Ita kanta ta kasa ɗauke idonta daga kan mirror, sai tambayar kanta take anya kuwa ita ce, ba wata aka canza ba. Aka yiyyi mata pictures da video's, sai 5:30 Sadik ya zo ɗaukar su shi da wani abokin sa. Ya yi kyau abunsa cikin dakakkiyar shadda sai maik'o take, kalar adon jikin kayan Neehal da head ɗinta. Zuwa lokacin Aunty Sadiya har ta fara kiran su akan su yi sauri su taho, saboda gurin biki fa ya ɗauki harama an fara shagali, amarya da ango kawai ake jira. Mai kwalliyar tasa dole sai da Sadik ya shiga cikin gurin, tana son tay musu pictures tare da Neehal and kuma tana son ta caze shi kuɗi. Yanda Sadik ya ruɗe da ya ga Neehal ba zai misaltu ba. "Wifey ke ce kuwa? Kai Masha Allah na yi dace da kyakkyawar mace." Su Haneefah da masu kwalliyar su kay tay masa dariya. Ya zaro kuɗi masu yawa a aljihun sa ya bawa mai kwalliyar, duk da already su Neehal sun biya ta, amma ya ƙara mata. Wai ta iya kwalliya babu ƙarya, bayan auran su zaina kawo Neehal ta dinga yi mata. Ita dai Neehal murmushi kawai take, a ranta tana jin abun kamar a mafarki. Wai yau ita ce a matsayin amarya, yanda take zuwa bikin wasu itama an zo nata. Sai 6 suka bar a wajen. Haneefah da abokin Sadik sune a gaban Motar, ita kuma da shi suna baya, ya addaba mata da kallo kamar zai cinye ta. Haneefah kuma na yi musu video da pictures daga inda take a wayarta. Suna isa gurin bikin ta ji gabanta ya faɗi, ta lumshe ido tana ambaton sunan Allah, tare da ƙoƙarin ganin ba ta yi kuka ba. Tana jin Sadik yana mata magana, da kai kawai take iya amsa masa. Sun yi 15 minutes a Motar kafin a gama arranged k'awayen Amarya da abokan ango da za su shiga tare da Amarya da Ango. Daga cikin ball ɗin kuma MC nata b'ab'atun sanarwar isowar ango da amarya. Aka buɗe mata Motor ta fito, tun daga lokacin Camera ta ce mata salama alaikum, aka fara ɗaukar ta a hoto. Kowa na yaba kyawun da ta yi. Ta ƙarasa ta tsaya a inda aka ce mata, Sadik na gefen ta yana ta zuba murmushi. K'awayen amarya ne a gaba, suka fara tafiya cikin tsari suna ɗan yin rawa ta cool music ɗin da aka saka, wadda ta dace da shigowar amarya da ango. Su Neehal suka mara musu baya cikin taku ɗai_ɗai, abokan Ango na take musu baya. Abun dai gwanin burgewa mutane duk an tattashi ana musu video. Ango da amarya suka ƙarasa gurin zaman su, mutane da masu hoto suka baibaye su, kowa na san ya ɗauke su. Sai a lokacin Neehal ta ga twins ɗinta Zahra ta kawo mata su, wanda suke ta kuka tun yamma su sai an kai su inda take. Sun yi kyau sosai cikin shigar da akai musu, hannayensu da ƙafafuwansu sun sha lalle. Afrah ta zauna a gefen Neehal, Amrah kuma a gefen Sadik. Haka aka cigaba da gudanar da shagali a gurin, amarya da ango suka shigo tsakiyar fili aka dinga zuba musu lik'i kamar kuɗin ba su da wahalar samu. Su Haneefah da sauran k'awayen Neehal sun jajige sun ci rawa abin su, amarya dai ƙin takawa ta yi. Shigowa ta musamman aka yiwa Mama wadda ta yi kyau abun ta sosai, kana ganin ta ka ga uwar amarya. Duk yadda Neehal ta so daurewa sai da ta yi hawaye a lokacin, ana saka wak'ar wayyo Allah Mamana ta Ali jita ta ji zuciyarta ta karye, ta tuno Ummanta da Abbanta da basa raye, Allah ya yi baza su ga Auren ta ba. Hawaye take yi sosai, da ƙyar Aunty Sadiya ta lallaɓa ta, ta bar kukan. Mama ta yi musu lik'i sosai ita da Sadik su ma su kai mata, k'awayen Mama sun mata kara sun musu lik'i ita da Neehal. Sai a lokacin Neehal ta ga Ameen ya zo ya yiwa Mama lik'i, haka kawai ta ji daɗi a ranta dan bata yi tunanin zai zo ba, saboda sanin halin sa. Suka haɗa ido yay mata murmushi ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, ya matso kusa da ita ya shiga yi mata lik'in rafar ƴan dubu_dubu. Itama ta zari wasu a hannunsa ta dinga lik'a masa suna kallon juna cikin wani irin yanayi. Ahmad ma ya zo, ta yi mamakin zuwansa dan bai faɗa mata zai zo ba. Haka dai akay ta gudanar da shagali a gurin, a gefe guda kuma masu rabon abinci da drinks suna ta yi. Can na hango ƴan NEEHAL FAN'S GROUP an ci anko an kame akan kujera, su Meerah, Rachel, Ummu Hanif, Hany, Zainab AA, Zainab Aliyu kkm, Miemie Afreen, Aunty ruky, Maman Zahrah, Hauwa'u Sani, Fulani, Hafsat Garba da sauran team ɗin Ameen suna ta kai laumar shinkafa baki suna korawa da drinks. (🤣😅😂)Sai hararar Sadik suke tare da gulmar sa wai ko kyau bai yi ba, bai ma dace da Neehal ba. Gefe guda kuma su Ummul Amina ne ana ta yagar naman kaza. (🤣🤣🤣🤣😂😂😂) Ita da sauran team ɗin Ahmad irin su, Aysha Rawayau, mrs Suraj, mrs Jay, Ruk'ayya, Momyn ruky, A'ishat Abubakar, Aysha Khalil da sauran su dai. Su kuma Ameen suke zabgawa harara dan shi ya tsole musu ido. (🤣😂) Ummul Amina har da gulmar sa wai dan baƙin hali a gurin bikin ma ba zai yi fara'a ba sai haɗe rai yake. Sai da tara ta wuce aka tashi daga taron, bikin yau ya yi daɗi Alhamdulillah an yi lafiya an tashi lafiya saura kuma na gobe.












Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare, bayan Neehal ta yi wanka ta saka kayan bacci, tana ƙoƙarin kwanciya duk da ƴan'matan dake ɗakin suna ta hira ba su da niyyar kwanciyar su, ita kuwa ta gaji bacci kawai take buƙatar yi a yanzu. Mama ta aiko Aunty Sadiya ta kira ta. Ta zira hijabi ta fito ta nufi part ɗin Daddy inda Maman take. Ta same ta zaune a falo da kayan fruits a gaban ta. Ta zauna a kusa da ita tare da kwantar da kanta akan ƙafaɗarta. Mama ta ce. "Bacci kika fara ne?" Ta girgiza kai. Mama ta ce. "To sauka ki sha fruits ɗin nan, na san yau ba ki ci wani abincin kirki ba." A hankali ta ce. "Bana jin yunwa." Mama ta ce. "Ai ba cewa na yi kina jin yunwa ba, cewa na yi ki sauka ki ci." Ta zare jikinta daga na Mama a hankali ta sauka ta janyo plate ɗin da suke ciki a yayyanke ta ɗauki yankan Apple ta fara ci, ta yamutsa fuska lokacin da take taunawa. Mama ta ce, "Ya dai?" Bata ce komai ba sai hawaye. Mama ta girgiza kai ta ce. "Oh Allah, Neehal meke damun ki ne? Dan zaki yi aure sai ki koma kamar wadda aka cewa zaki mutu, haba Neehal karki ki kaini bango fa da wannan banzan kukan naki, sai kace a kanki aka fara Aure, duk wanda ake yiwa Auran haka kika ga suna yi?" Neehal ta fashe da kuka ta ce. "To ni Mama id'ont want to leave you." Mama ta yi murmushi kamar ba ita ta gama faɗa yanzu ba, ta sakko ta zauna a kusa da ita, tare da janyo ta jikinta. Tana ɗan bubbuga bayanta kaɗan ta ce. "Haba ƴar Mamanta, ai kina tare da Mama babu wanda zai raba ki da Ita, dan kin yi aure Neehal ai hakan ba yana nufin kin daina gani na ba ne. Nima dauriya kawai nake, dan ban ma san irin kewar ki da zan yi ba in kin tafi. Amma kuma ina cikin tsananin farincikin nuna mun lokacin Aurenki da Allah ya yi. Neehal burin kowace uwa idan tana da ƴa wadd ta girma ta isa aure to ta aurar da ita, ki yi haquri kin ji, kowa da haka yake sabawa, ai Aure ya zama dole." Neehal ta gyaɗa mata kai tana ƙara matso hawaye. Mama ta d'ago kanta ta yago tissue ta share mata hawayen. Cikin tsokana ta ce. "Ki rage wannan kukan naki, ko haka zaki haifa mun jikoki suna kuka ke kina yi?" Ta mayar da kanta jikin Mama tana murmushin jin kunya tare da turo baki. Mama ta ƙara d'ago ta, ta ce. "Taso in baki a baki, kin ji ƴar autar Mama." Ta tashi zaune, Mama ta fara bata fruit ɗin a baki. Sai da ta sha sosai sannan Mama ta ƙyale ta, ta koma part ɗinsu ta kwanta. Mama ta shiga ɗakin Daddy ta tarar da shi yana kaiwa da komowa cikin damuwa. Mama ta dafe kai ta ce. "Yanzu na gama da ƴarka kai ma gaka, sau nawa zan faɗa maka Gen. Ka kwantar da hankalinka, babu abun da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi, za'a yi bikin nan lafiya a gama lafiya." Daddy ya zauna a bakin gado cikin damuwa ya ce. "Wallahi Doctor bana son a kuma samun wata matsalar at this time, na rasa me yasa hankalina ya ƙi kwanciya, bana son a ƙara cutar da marainiyar Allah." Mama ta ƙarasa kusa da shi ta ce. "Ka saka abun a ranka ne shi yasa, ni duk damuwata tunda na ga bikin ya matso na kwantar da hankalina, addu'a kawai nake kuma na san Ubangiji yana sane da mu, duk wani mai ƙoƙarin cutar da mu Allah ya mayar masa da cutar kansa." Daddy zai kuma magana Mama ta hana shi, ta hanyar kama hannunsa tana faɗin. "Mu je ka yi wanka, ji bi yanda duk ka haɗa zufa." Ya miƙe ya bi bayan ta zuwa toilet ɗin, amma shi kaɗai ya san abun da yake ji a ransa na damuwa. Washegari aka yi Dinner bayan Magriba, a wani had'ad'd'en hall. Yau Neehal har tafi jiya kyau, gurin bikin ma ya fi na jiya tsaruwa sai dai bai kai shi girma ba, da yake ba kowa aka gayyata ba, bai fi rabin mutanen jiya ne suka je ba. Shima an warwarsa an ci an sha, Haneefah dai yau bata more da rawa ba kamar jiya, saboda zuwan Faruq gurin. Ya zaunar da ita ya ce baza ta ce ta jawo masa asarar ɗa/ƴa a banza ba. Ta zauna ta dinga ɓata fuska shi kuma yana mata dariya.






Yauma kamar jiya Sadik ne ya kawo ta gida da aka tashi daga gurin bikin, time ɗin 11 na dare ta wuce. Suna zaune a bayan Mota abokinsa da ya yi driving ɗinsu yana gaba. Sadik ya ƙura mata ido tare da kama hannunta. Ta yi ƙoƙarin k'wace wa amma ya ƙi sakar mata. Ta turo masa baki gaba. Ya yi murmushi murya ƙasa ƙasa ya ce. "Wifey gobe by this time muna tare a gidana an kawo mun ke." Ta d'ago ta kalle shi tana murmushi, sun jima suna kallon juna ido cikin ido, kallo mai cike da k'aunar junan su. A hankali ta fara janye nata idanun tare da lumshe su. Sadik ya lumshe nasa shi ma tare da sakar mata hannu. Cikin matuƙar sanyin murya ya ce. "Mu je in raka ki, kar Mama ta ga kin daɗe, duk da dai na san baza ta damu ba, tunda ta san kina tare da mijin ki." Tay masa wani kallo ta ce, "Ka bari a ɗaura dai." Ya yi ƴar dariya sannan ya ce. "Yau da gobe duk ɗaya ne a gurin Allah." Bata ce komai ba, ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata ta fito itama. Sai da ya raka ta har bakin part ɗin Mama sannan ya juya, yana jin kamar kar su rabu. Dare ya tsala amma Neehal ta kasa bacci, duk hirar ƴan ɗakin sun gaji sun yi bacci. Ita kuwa sai juyi take akan gado, sosai gabanta ke faɗuwa duk bayan sakanni, ta rasa na mamaki ne ko na tsaron Ɗaura mata auren da za'a yi gobe. Sai tambayar kanta take wai da gaske ita za'a d'aurawa aure gobe, abun kamar almara haka take jin sa. Jin wayarta na vibrate ta tashi zaune da sauri ta ɗauka dan ganin wake kiran ta cikin tsakiyar daren nan. Ganin Sadik ne ta cika da mamaki, ta yi pick sannan ta ƙara a kunnenta amma bata yi magana ba. Cikin raunin murya ta ji ya ce. "Neehal baki bacci ba?" A hankali ta ce. "Uhm." Ya ce, "Why? Ko d'okin za'a kawo ki gidana gobe ne?" Cikin shagwab'a ta ce. "Ni ba haka ba ne, kawai na fara missing Mama ne." Ya ce. "Ki daina damuwa Wifey, idan Mama ce koyaushe kike so ki gan ta zan kaiki ki gan ta, I promised." Ta yi shiru tana sauke numfashi. Ya ce, "Nima zumud'i da farinciki sun hana ni bacci, idona murtsitsi babu alamar d'igon bacci, amma yanzu zan je in yi alawala in yi sallah in roƙa mana Allah ya wanzar mana da zaman lafiya a zaman auren mu, ke ma idan kin ji baccin ya ƙi zuwa ki je ki yi, mu raya daren kin ji Wifey." Ta ce. "Toh Husby." Suka yi sallama ta katse wayar, duba time ta yi ta ga uku na dare saura. Ta kunna light ɗin wayarta sannan ta sakko daga kan gadon, dan ta san ko ta cigaba da kwanciya baccin ba zuwa zai yi ba, gwara ta bi shawarar Sadik ɗin.....✍️










_*6k plus words, ten read more. Gaskiya na yi typed yau, sai dai ban yi edit ba, ku yi haquri da typing errors.*_












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣9️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















...........Haka rayuwa tay ta tafiya, bikin Neehal na ƙara kusantowa. Ɓangarorin biyu na amarya dana ango suna ta shirye-shiryen bikin, duk da dangin Angon ba kowa ke son auren ba. Sai dai kamar yadda Uncle Mahmud ya roƙi alfarma tun ranar da aka kawo kuɗin Auren, akan a ɓoye batun auren sai abun ya matso daf sannan a bayyana saboda tsaro, a cewar sa idan ma wani ne yake kashe samarin da Neehal zata aura kamar yadda ake hasashe, to lokacin da zancen bikin zai fito kafin ya gama duk wani shirinsa an yi bikin an gama Insha Allah. Hakan ce ta kasance kuwa domin ba kowa ya san da maganar bikin ba, sai na jiki_jiki wanda ya zama dole. Ita Mama kam ta ce babu wani shagali da za'ai da bikin, ɗaurin Aure kawai za'ayi akai amarya gidan ta. Sai dai fa shi Ango Sadik da bai san da shirin Mama ba yana ta shirye-shiryen haɗa gagarumar dinner shi da abokanansa. Haneefah ma ta ce baza su yi biki lami ba, sai sun cashe ko da na rana ɗaya ne, tana nan tana ta yiwa Mama naci da magiya akan ta amince. Ita kam Neehal tsarin Maman ya mata dai-dai, dan ita ba gwanar son harkar taro ba ce dama. A wannan azumin na bana Neehal suka ziyarci ƙasa mai tsarki ita da Mama, Mama ta cika alƙawarin data ɗaukar mata tun last year. Sun je sun yi Umrah, satin su biyu a can suka dawo. Bayan Sallah da sati ɗaya suka fara final exam ɗinsu. Neehal ta maida hankalinta sosai akan karatu, ta watsar da duk wani feeling da take ji a cikin ranta ta duk'ufa ga karatu, domin tana son yanda ta fara karatun ta successfully ta gama successfully. A gefe guda kuma zuciyarta cike take da murnar kammala karatunta da zata yi this year.






Yau Friday wadda ta kama sati uku da fara exam ɗinsu, kuma yau ne za su yi final exam. Exam ɗin safe gare su, hakan yasa tun asuba ta fara shirinta. Ta shirya cikin Black Tomy skirt ɗin da suka yi anko na ƴan class ɗinsu da farar t_shirt wadda aka yi rubutu a gaban rigar, aka rubuta sunan department ɗinsu da year da suka gama school. Ta zauna ta tsara ɗaurin ɗan_kwali a kanta da wani plan yadi Black. Ta saka ɗan kunne mai rawl white colour. Ta ɗaura tsadadden agogon hannu mai kyau Black a left hand ɗinta, sannan right kuma ta saka white abun hannu da k'aton zobe mai stone a ɗanyatsanta na tsakiya. Ta kalli kanta a mirror tare da yin murmushi, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin farinciki a yau. Ta tashi ta ɗauko sabon Black shoe ta zira kyakyawan ƙafuwanta dake sanye cikin socks a ciki. Bayan ta feshe jikinta da sanyayan turarukanta masu daɗin k'amshi ta ɗauko madaidaicin mayafi white colour ta yafa a jikinta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag mai ɗauke da exam card ɗinta da pen da kuɗi da phone's ɗinta a ciki.Ta riƙe jakar a hannun damanta, hannun hagunta kuma leda ta riƙe mai ɗauke da rigar graduation ɗinta a ciki. Ta fito ta nufi part ɗin Daddy domin Mama tana can. A falo ta tarar da su a zaune akan carpet Daddy yana breakfast. Ta ajiye kayan hannunta ta tafi da gudu ta rungume Mama tana murmushi. Mama tana murmushin itama ta shafi gefen fuskarta ta ce. "Congratulation my Daughter, Allah ya albarkaci karatunki da rayuwarki baki ɗaya." Tana murmushi ta ce "Amin, Thank you so Much Mum." Sannan ta tashi ta koma kusa da Daddy ta zauna ta ce. "Good Morning Dad." Yana murmushi cike da kulawa ya ce. "Morning Daughter, how was your preparation of been a graduate?" Ta ce "Alhamdulillah." Daddy ya ce, "To Masha Allah Daughter, Allah ya bayar da sakamako mai kyau, ya nuna mun ranar da zaki zama professor." Ta ce "Amin My Dad, than you so much." Ya ce "You are welcome Dear." Mama ta dube ta, ta ce, "Dafatan kin yi breakfast, ba saurin tafiya school ba." Ta girgiza kai ta ce. I'm full." Daddy ya ce, "A'a Daughter, ba'a yi celebration ciki babu abinci ba, zauna mu ci a nan taree." Ta ce "Toh Daddy na." Ta haɗa tea ta sha tare da bread. Ƙarfe bakwai da mintuna tay wa su Mama sallama ta

Please Login or Register in order to submit comment