Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ce ban da ita. Cikin mamaki na ce musu da gaske ban da ƴa mace ta cikina, ɗana ɗaya ne tal a duniya kuma namiji ne, kuma Kabir ya fi kowa sanin haka. Kabir ya bayar da labarin ganin da yaywa Neehal jiya a gidana. Sarauniya ta yi bincike a ƙwaryar tsafinta sai ga fuskar Neehal ta bayyana. Ta dube ni ta ce. Tunda ni nake ciyar da Neehal nake shayar da ita nake tufatar da ita kamar ƴar cikina take a yanzu, dan haka ƙungiya tana buƙatar budurcinta. Na ce gaskiya ba zan iya cutar da ƴar amana ba marainiyar Allah. A fusace Sarauniya ta ce mun. Dole in yi, in ba haka ba su kashe iyalina su kashe ni kuma sannan wani a cikin ƙungiya ya karb'i budurcin Neehal ɗin. Hankalina idan ya yi dubu ya tashi a ranar, dan na san duk abun da sarauniya ta faɗa zata iya aikata fiye da hakan ma. Ba zan so in rasa matata da ɗana ba, kuma ba zan so a ɓata rayuwar Neehal ba. Dan haka na yanke wata shawara, na nuna musu na amince zan yi abun da suke so, amma a lokacin Neehal ta yi yarinta su ɗan bari ta ƙara girma. Da ƙyar suka amince da abun da na faɗa, dan a cewar su wanda ba su kaita ba ma ana musu fyaɗen. Na dawo gida hankali a tashe cikin rashin sanin mafita, ni ba'a abun in ce Fateemah ta mayar da Neehal gurin ƴan'uwanta ba dan tserayar da rayuwarta ba, ta ce mun akan me? Na dai ƙudurce a raina komai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa haikewa Neehal ba har abada, gwara na rasa raina dana aikata wannan abun kunyar. Ni babban tashin hankalina da suka ce ko ban aikata mata da kaina ba wani zai aikata mata. Ban taɓa sanin ina son Neehal sosai ba sai a wannan lokacin, Na saka ido sosai akanta saboda na san tsaf zasu iya ɓullo mata ta wata hanyar, musamman Kabir da kodayaushe cikin zancen ta yake. Haka shekaru suka shud'e ina ƙara bawa ƙungiya excuse akan Neehal, na rasa me yasa su kuma suka damu da ita over, kodayaushe cikin yi mun nacin in yi in far mata suke, wai hakan ba ƙaramin cigaba zai ƙarawa ƙungiya ba, yarinyar ta musamman ce gashi nima ban taɓa yiwa ƙungiya irin wannan aikin ba shi yasa suka damu da abun. Lokacin da na yi released soyayyar Neehal da Jameel sai na ce ya turo a yi auransu idan dagaske yake, Fateemah ta ce, na bari ta ɗan yi karatu mana tunda time ɗin candy kawai ta yi. Amma na ce a'a, dan so nake kawai na aurar da ita na huta da fargaba a kanta, a ganina idan ta yi aure ai dole su haqura da batun. Ban san a inda Kabir ya samu labarin Engage ɗinsu ba dan ban faɗa masa ba saboda bana son ya sani. Amma sai tsintar maganar na yi a ƙungiya, aka dinga zazzaga mun masifa wai ina son cin amanar ƙungiya ne, na ce musu danginta ne suke son aurar da ita ba ni ba ne. Sai suka ce to duk yadda za'a yi a yi a fasa batun bikin nan, ko kuma in karɓo musu abun da suke so kafin lokacin bikin. Na amsa musu kawai amma ban aiwatar ba. Wallahi ban san ya aka yi ba, ban kuma san ta yanda aka kashe Jameel ba, kuma bani da masaniya a lokacin da suka shirya kisan. Sai da aka yi sannan nake ji a ƙungiya Kabir ne ya shirya komai. Sarauniya ta tabbatar mun da cewar haka zasu yi ta yiwa duk wanda zai auri Neehal, tunda ni taurin kai gare ni na ƙi yi musu abun da suke so. Manyan ƙungiya sun so hukuntani amma Sarauniya ta hana, ni kaina ina mamakin yanda Sarauniya bata iya hukunta ni duk laifin da zan yi, ita da bata da tausayi da imani ko kaɗan. Duk uwar bautar da kake mata kana mata laifi na rana ɗaya zata rufe idonta ta azabtar da kai.










Abun da ya taimake ni akan Neehal ƙa'ida ne kowa shi zai yi amfani da ƴarsa, wani ba zai taɓa replace ɗinsa ba a ƙungiya, wannan dalilin ne yasa ba'a bawa wani damar keta wa Neehal haddi ba sai ni. Ban taɓa tunanin zasu kuma kashe Anwar ba a lokacin dana bashi auran Neehal, na yarda Ubangiji ne ke rayawa da kashewa rayuwar kowa a hannunsa take, dan haka sai kwanan mutum ya ƙare zai mutu. Ga dukkan alamu ba su samu labarin auren Neehal da Anwar da wuri ba sai gab da za'a kawo lefen ta, wallahi shi ma kamar kisan Jameel ban san sanda aka shirya kisan aka kashe shi ba. A lokacin hankalina yay matuƙar tashi domin na san idan aka cigaba da tafiya a haka akwai matsala, tunda dole hankalin mutane zai dawo kan abun, za'a fara zargin lallai da wata a ƙasa. Na rasa ya zan yi, na rasa hanyar neman mafita. Challenges da barazanar dana samu a ƙungiya baza su faɗu ba akan wannan al'amarin, wai ina ta raina musu hankali shekara da shekaru na ƙi yin abu. Ni kuma na ƙudurce a raina gara na mutu dana aikatawa Neehal wannan mummunan abun. Lokacin da Fateemah ta zo mun da batun tattaunawar da suka yi da su Sadiya akan suna zargin da akwai wanda yake aikata kisan su Anwar hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin na san tabbas idan tafiya ta yi tafiya asirina zai iya tonuwa. Ban tabbatar da hakan ba sai lokacin auransu da Sadik. Domin ƙungiya ba su san da bikin ba sakamakon ɓoye zancen bikin da kay sai da ya zo daf sannan aka bayyana, ana i gobe d'aurin Aure cikin dare sun tura a kashe Sadik aka tarar baya nan an sace shi. Hankalin ƙungiya ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin sun gane da alamun akwai wanda yake bibiyar al'amuransu kenan, nima hankalina ya tashi ba kaɗan ba dan bana son asirina ya tonu duniya ta san halin da nake ciki. Duk zuwa masallacin da na ce ina yi mu yi karatu ba can nake zuwa ba, gidan ƙungiya nake zuwa mu kwana muna bincike dan gano waye yake bibiyar al'amuranmu amma har yau mun kasa ganowa. Gidan da aka kai Neehal nan nake zuwa kullum muna aikin ƙungiya tun bayan dawowar mu Kano da zama. Wancan ɗayan gidan sai idan za'ai gagarumin aiki nake zuwan sa. Da Sadiya take cewa akwai wanda take zargi bayan an sace Sadik ko kaɗan ban yi tunanin ni take zargi ba, dan duk wata kafa ko alama da zata saka ayi zargi na akan al'amarin Neehal na toshe ta, duk binciken mutum bai isa ya gane ina cikin wannan mummunar harkar ba, dan takatsantsan nake bana wasa ba. Lokacin dana bawa Neehal Mota na saka yarana suna bin bayanta duk inda zata je, saboda kaɗan daga sharrin yan ƙungiya su saka a sace ta su tsare ta, su kira ni su ce dole sai na aikata abun da suke so a gaban su. Ni kuma idan su kay hakan bani da wata sauran mafita dole na aikata. Allah ya taimaka ya dubi maraicinta ba su yi hakan ba sai a wannan karon. Wallahi ban san time ɗin da suka shirya sace Neehal ba, sai bayan sun ɗauke tan nake sani. Kuma wannan duk shirin Kabir ne, shi yake shirya komai akan Neehal. Sarauniya kuma ta yi farinciki da hakan har da ƙarin matsayi tay masa na yanda duk wata hanyar mugunta ya san ta. Suka kuma shirya gagarumin shagali dan murnar mallakar BUDURCIN NEEHAL. Abun da suka daɗe suna fata da burin samu, domin bincikensu ya tabbatar musu ba ƙaramin cigaba ƙungiya zata samu ba idan member ɗin cikinta ya mallaki Neehal. Sun riga sun saka ni a tasku da tsaka mai wuya, dole na je na aikata abun da suke so, domin sun ce idan ma ban yi ba zasu saka wani ya yi, kuma bayan sun mata fyaɗen zasu kashe ta, su yanka ta su sha jininta. Shi yasa na amince za ni amma har ga Allah ba dan na aikata ɗin ba ne, sai dan na fito da ita daga wannan gidan, in yaso ni su kashe ni a matsayin hukuncin fitar da itan da na yi. Taimakon ta da Sagir ya yi ma nina saka shi, na san dole zata tambaye shi dalilin da yasa ya taimake ta, sai na ce masa ya ce mata saboda Ameen ya taimake ta idan ta tambaye shi." Daddy ya yi shiru yana mayar da numfashi, ɗakin ya yi tsit kamar babu halitta a ciki. Ya fara hawaye sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. "Wallahi bani da niyyar cutar da Neehal a rayuwata, ku yarda da ni. Tamkar ƴar cikina haka na ɗauke ta. Da ace ina son cutar da ita da tuni na yi abun da suke so an wuce gurin, tunda ina da opportunities ɗin hakan da dama. A gidana take kwana take tashi, zan iya yin komai da ita a duk sanda naso ba tare da an gane ni na yi ba, ko kuma na saka a sace mun ita in yi duk abun da nake so da ita a wani gurin sannan in dawo da ita ba tare da an gane nina aikata hakan ba. Amma kuma sai ban yi ba saboda ba zan iya ba, ba zan iya cutar da ita ba. Lokacin da ta je gidan Ameen ni na je gidan na fesa mata abu a fuska, a lokacin na gaji da ƙwarzabar da ƙungiya take mun gami da barazanar kashe iyalina akan ƙin yi musu abun da suka umarce ni, a lokacin na saduda kawai zan aikata ɗin. Amma ina zuwa sai na kasa aikatawa saboda wasu dalilai, na farko idan har na yi rape ɗinta a gidan Ameen za'a ce shi ne ya aikata, domin babu wanda zai yarda ba shi ba ne, tunda babu alamar da zata nuna wani ya shigo gidan daga waje, Nima na yi amfani da spare keys ɗin kowacce ƙofa dake gidan na gurina kasancewar gidan nawa ne na mallakawa Ameen. Kuma ta ƙofar baya na shiga balle mai gadi ko wani ya ga lokacin dana shiga, shi yasa na fasa dan ba zan iya bari a k'ullawa ɗana sharri ta sanadiyya ta ba. Na biyu kuma wani tsoron Allah ne ya dirar mun a zuciyata a lokacin, na ji ba zan iya farantawa ƙungiyar mutane ƴan'uwana na sabawa Ubangijin da ya halicce ni da laifika biyu ba, laifin zina da kuma laifin cutar da ita, na ji kawai koma me zai faru sai dai ya faru amma ba zan iya ba, sai kawai na fasa na fice na bar gidan. A lokacin ni addu'a nay ta yi dama ƙin aikatawar tawa yasa su kashe ni, amma ba su yi hakan ba sai faɗa da fatar baki kawai da sukay mun. A ranar har na je na dawo Fateemah bata san na fita ba, sakamakon maganin bacci dana zuba mata a lemo ta sha. Kuma ranar da wuri na kwanta na nuna mata a gajiye nake bacci zan yi, ina ganin bacci ya ɗauke ta na tashi na fice. A yau na ɗauka Sarauniya zata fille kaina ne saboda tsananin takaici da baƙin ciki, domin ba ƙaramin buri ta ci ba na mallakar BUDURCIN NEEHAL. Amma sai naga ba tay hakan ba, ta ce zamana a cikin ƙungiya ba ƙaramin cigaba yake ƙarawa ƙungiya ba, dan haka baza ta so su rasa ni a cikinta ba, sannan kuma tana sona ba zata iya cutar da ni ba, amma duk da haka sai ta hukunta ni, hukunci mai tsanani, kuma dole sai na aikata abun da suke so akan Neehal baza su haqura ba. Ban san dame zata hukunta ni ba dan bata faɗa ba. Amma ina fatan dama ta kashe ni in huta da wannan asararriyar bak'ar rayuwar da nake mara amfani. Wannan shine gaskiyar abun da yake faruwa." Sai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro.
















A fili Abba ya shiga maimaita "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Cikin tsananin tashin hankalin jin halin da ɗan'uwansa yake ciki. Neehal ta ƙara volume ɗin kukanta kamar yadda Hajiya ta fashe da matsanancin kuka. Mama ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ganin wasu taurari na gilmawa ta cikin idonta, daga baya kuma ta daina ganin komai sai duhu dulum na wasu sakanni. Ta yi tunanin bayanin da Daddy zai yi zai ƙaryata abun da Neehal ta faɗa da kuma zargin da Aunty Sadiya take masa ne, ya ce ba shi Neehal ta gani ba wani mai kama da shi ne, ko kuma sharri akai masa kamar yadda Hajiya ta faɗa. Amma sai ta ji saɓanin hakan, sai ma amsa laifinsa da ya yi, ya tabbatar musu yana cikin ƙungiyar matsafa shi ɗan shan jini ne. Ta shiga tambayar kanta anya kuwa ba mafarki take ba? Anya mijinta adalin miji mutumin kirki zai aikata haka? Ko a mafarki bata taɓa tunanin zata faɗa irin wannan jarrabawar ba, bata taɓa tunanin ƙaddara irin wannan zata riske su ba. Muhammad ɗinta mijinta Mahaifin Ameen shine a cikin wannan mummunar harkar? Zuciyarta ta kasa yarda da wannan al'amarin, yay mata girma baza ta iya ɗauka ba. Ta d'ago kanta ta zubawa Daddy jajayen idanunta da suka rine saboda tashin hankali, ta yi gyaran murya cikin ƙarfin hali saboda muryarta da take a shak'e, cikin dauriyar ciwon da take ji a cikin zuciyarta ta ce masa. "Wannan labarin ƙaryar daka zauna ka tsara shi da kukan munafurcin da kake ba zai saka in yarda da kai ko ina yafe maka ba Muhammad, cuta ce ka riga daka cuce ni babu yanda zan yi. Wallahi da ba dan kai ka faɗa mun wannan maganar da bakinka ba da ba zan taɓa yarda ba inda wani ne ya faɗa mun, ko da kuwa Hajiya ce data tsugunna ta haife ni ta faɗa ba zan yarda ba, dan na maka kyakkyawar shaidar kai mutumin kirki ne. Ka bani mamaki Muhammad, ace shekara da shekaru da matsafi mashayin jini nake rayuwa." Daddy ya matso ya kama ƙafafunta ya ce. "Allah ne shaidata akan duk abubuwan dana faɗa muku shine gaskiyar al'amarin, dan Allah Fateemah ki yarda da ni, ki karɓi hakan a matsayin ƙaddara kamar yadda na ɗauka wannan ita ce *ƙaddarata* a rayuwata." Mama ta watsa masa wani kallo ta ce. "Ƙaddara ko son zuciyarka? Komai ɗan Adam ya aikata sai ya ce ƙaddara ce, saboda ita ƙaddarar ba'a ganin ta bare ta kare kanta ko? Wannan labarin naka shirya shi kawai ka yi ka faɗa mana. Ban da haka ta yaya kana cikin ƙungiya za'a shirya yanda za'a kashe ƴaƴan mutane amma ka ce baka sani ba? Ta yaya hakan zata kasance?" Daddy ya ce. "Wallahi bana sanin lokacin da suke shiryawar, na fi tunanin cikin dare ne da bana zuwa gidan suke shiryawa." Mama ta ce. "Me yasa ka san dalilin da yasa aka kashe su Jameel amma ka bar Sadik ya nemi Auran Neehal? Ko dan ba ɗanka ba ne ko an kashe shi baka da asara?" Daddy ya ce. "Babu yanda zan yi ne Fateemah, bani da mafita, ko so kike in ce miki Neehal baza tay Aure ba? Ki ce mun akan wanne dalilin in rasa amsar baki? Wacce fassara zaku mun idan na faɗi haka? Wallahi ko Anwar da Jameel dana san za'a kashe su a ranar dana fara ganin su da Neehal zan aura musu ita ba tare da duniya ta sani ba, balle har ƙungiya ta ji su ɗauki matarsu su tafi ba tare da an yi taron bikin komai ba, kinga da tuni na huta da wannan fargabar, da duk abubuwan da suka faru da Neehal ba su faru ba." Mama ta runtse idanta cikin matsananciyar damuwa ta ce. "Muhammad ka taɓa shan jinin mutum ɗan'uwanka? ka taɓa yin tsafi ta shirka da kanka?" Daddy ya shiga girgiza kai ya ce. "Fateemah tsafi gaskiyar mai shi, wallahi ba yin kaina ba ne tsaface ni suka yi, idan na je gidan duk abubuwan da nake yi ba'a cikin hayyacina nake ba." Hawaye suka fara shatata daga idon Mama, cikin muryar kuka ta ce. "Fatana da addu'a ta ɗaya ne, Allah yasa kana yin Sallah da azumi Muhammad? Allah yasa baka sadaukar da su saboda san duniya ba?" Daddy ya ce. "Ban daina Sallah ba balle azumi kema zaki bayar da shaidan hakan." Mama ta buɗe idonta tare da dafe ƙirjinta ta ce. "Na san babu yadda za'a yi ace ana Sallah a gidan matsafa, a ina kake yin Sallar?" Daddy ya ce. "Idan na dawo da yamma nake haɗawa na yi, asuba da isha'i kuma ina yin su akan lokaci, Magriba ma wani lokacin inna dawo da wuri ina yin ta akan lokaci." Mama ta girgiza kai cikin takaici ta ce. "Da azumi a bakinka kana zuwa gurin shirka mene makomar azumin naka?" Daddy ya ce. "Bana zuwa gidan da azumi, hutu nake ɗauka." Mama ta yi murmushi mai ciwo ta ce. "Da kuɗin tsafi da shan jini kake ciyar da mu ka tufatar da mu?" Daddy ya ce. "Wallahi ban taɓa ciyar da ku da haram ba, ni akaran kaina ban taɓa cin kuɗin ƙungiyar nan ba, dan na san haram ba ƙaramin bala'i ba ce a jikin ɗan Adam. Fateemah kin san ina da kuɗi tun asalina, Baffa ya rasu ya bar mana kadarori da tarin dukiya, and then my salary is more than 1.5 kin san wannan kuma already, ina business ina da Mall a Abuja da Kano, waɗannan sun isa na ciyar daku nay muku komai na buƙatar rayuwa ba tare da k'azaman kuɗin ƙungiya ba. Ke tsarkakakkiya ce Fateemah, ba zan taɓa yi miki algus da kazanta a rayuwarki ba. Wallahi Fateemah baki san tarin yawan nadamar dake cikin zuciyata ba ne, ina jin dama ban taɓa sanin Kabir ba a rayuwata, dama ban faɗa harkar siyasa ba, da ana dawo da abun da ya wuce baya dana dawo da rayuwata na cire wannan dattin da ya ɓata mun tsaftatacciyar rayuwata." Mama ta sauke ajiyar zuciya bata kuma cewa komai ba. Ta mayar da idanunta ta lumshe tana jin yanda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri gami da wani irin zafi da take mata kamar ana gasa mata nama a cikin ta.








Daddy ya bar jikinta ya koma gaban Neehal, ya d'ago kanta yana hawaye ya ce. Ki yafe mun Daughter ni ne sanadin saka miki baƙin ciki a rayuwarki, dan Allah ki yafe mun ko zan samu sauƙin azabar Ubangiji idan na mutu." Neehal ta girgiza kai ta ce. "Babu abun da kai mun Daddy sai tarin Alkhairi, ka riƙe ni ba tare da ƙyara ko zangwama ko hantara ba a gidanka, ka bani tarbiyya ka bani ci da sha da sutura, ka bani ilimin addini dana boko ka samar mun aikin yi. Abun da ƴan'uwana na jini wanda Ubangiji ya ɗora musu hak'k'in hakan ba su mun ba, amma duk kai ka yi mun. You Are still my father Daddy, kai na sani a matsayin ubana a duniyar nan, wannan abun da ya faru ƙaddararmu ce gaba-d'ayan mu, amma kai ma ba laifinka ba ne." Sai ta faɗa jikinsa tana ƙara fashewa da kuka mai ban tausayi tare da faɗin. "You are still my father Daddy." Daddy ya rungume ta yana kuka sosai ya ce. "I'm Bad father for you Neehal, mahaifinki shine wanda ya yarda aka kashe shi saboda ganin ya kare mutuncinki da martabar ki, ni kuma ni ne nake ƙoƙarin raba ki da su, I'm not good fasher for you, please forgive me Daughter!." Aunty A'isha ta lumshe idonta hawayen tausayinsu na zuba daga cikin idanun nata, sun bata tausayi ba kaɗan ba, wannan wacce irin ƙaddara ce, gaskiya Kabir ya cuci Daddy, Amma Allah zai masa sakayya. Aunty Sadiya ma duk taurin zuciyarta sai da ta yi kuka. Abba ya jinjina kai ya ce. "Na rasa da sunan da zan kira wannan baƙin al'amarin, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un. Yanzu Muhammad kai da na sani mai riƙo da addini kai ne a cikin ƙungiyar matsafa fiye da shekara goma? Ya assamadu kasa mu yi kyakkyawan ƙarshe." Turo ƙofar ɗakin da aka yi yasa suka juya gaba-d'aya suna kallon ƙofar, Neehal ta bar jikin Daddy da sauri. Zulai ce ta fara shigowa sai kuma wasu mutum uku masu sanye da suit a jikinsu. Ɗaya daga cikin su ya yi sallama, babu wanda ya iya amsa masa. Bai damu ba ya ɗauko i.d card a aljihun rigarsa ya nuna musu tare da faɗin. "Ku yi haquri mun shigo muku har bedroom ba da izinin ku ba, mu ma ba'a son ranmu ba ne, mun yi ta knocking baku ji mu ba shiyasa muka shigo. Jami'ai ne mu daga hukumar S.S ta ƙasa." Ya kalli Daddy sannan ya cigaba da magana da faɗin. "Mun zo ne for arrest you bisa umarnin ɗanka Major col. Al'ameen Muhammad Tafida, akan laifin da in mun je office zaka ji." Abba ya waro ido cikin tashin hankali amma bai yi magana ba. Daddy ya yi murmushi sannan ya goge hawayen fuskarsa ya tashi ta haɗa tafukan hannayensa ya yi tafi sau uku sannan ya ce. "Wannan ya tabbatar mun da zargin da nake na Ameen ne ke bibiyar wannan al'amarin, sannan kuma shi ya saka a ɗauke Sadik saboda ya tseratar da rayuwar shi. Ko yanzu na faɗi na mutu zan yi farinciki ban yi asarar haihuwar ɗa ɗaya tamkar da dubu ba, na bar ɗan da ƙasa da duniya zata yi alfahari da shi. Duk ɗan da ya kama ubansa da laifi sannan bai yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar da hukuma domin a kama shi a hukunta shi hakan ya tabbatar ba zai ƙyale duk wanda ya kama da laifi ba kowa ye. Lallai Ameen ya cika jami'in tsaro na gari wanda ƙasar mu take buƙatar irin su. I'm proud of that, zan mutu da farincikin haka." Daddy ya dubi su Mama ya ce. "Zan iya ce muku sai watarana, domin ka'idar wannan ƙungiyar da nake ciki ne duk wanda ya fallasa sirrin su ga wasu sai an kashe shi, ni kuma na baku labarinta yanzu, dan haka a daren yau zasu tsotse jinina sai dai a wayi gari aga gawata, dan haka ina neman yafiyar ku gaba-d'aya akan baƙin ciki da damuwar dana saka ku a ciki." Ya ƙarasa gaban Mama ya yi kneel dawn ya ce. "Ki nema mun yafiya a gurin gwarzon ɗana Ameen." sannan ya matsar da bakinsa daf da kunnenta cikin raɗa ya ce. "Ina neman alfarmar ki aurawa Ameen Neehal, domin tun kafin ta yi candy ya sanar mun yana son ta, nina nuna masa ba zan ba shi ita ba saboda wani dalilina. Dan Allah ki mun wannan Alfarmar, koda zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwarki." Daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin cikin sauri ba tare da kuma kallon kowa ba, mutanen nan suka mara masa baya da sauri. Su Aunty sun shiga cikin tashin hankali ba kaɗan ba da jin furucin Daddy na wai ƴan ƙungiyar su zasu kashe shi, kuka Neehal ta fashe da shi mai ƙarfi tana kiran sunan Daddy. Hajiya kuwa gaba-d'aya bata cikin hayyacinta ta ma daina fahimtar abun da yake faruwa, Aunty A'isha ma kuka take sosai. Abba ya tashi da sauri ya bi bayan su Daddy. Mama ta miƙe tsaye tare da dafa bango ta ce. "Ina wayata in kira Ameen, na san yana can cikin damuwa da baƙin cikin abun da ubansa ya aikata na son zuciya da son duniya, ku kira mun ɗana in ji a halin da yake ciki, kar zuciyarsa ta buga saboda baƙin ciki. Dan Allah ku kirawo mun shi in ji lafiyarsa." Sai ta tsugunna ta fara laluben wayarta a ƙasan ɗakin cikin fitar hayyaci, ta samu ta ɗauko wayar amma sai wayar ta zubce daga hannunta ta faɗi saboda rawar da jikinta yake

Please Login or Register in order to submit comment