Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidanta, nan kuwa wanka ma ba kullum ake barinta ta yi ba. Ga rashin ishashshen abinci, abincin da yaro ɗan shekara biyar zai ci shi ake bata, shima kuma mara daɗi. Kullum da safe tana jin k'amshi ana soya k'wai da dankali amma ita ko ganin shi bata yi, haka ma naman miya ba'a bata ko gutsire. Misalin ƙarfe Uku na yamma Neehal ce tafe tana ta zuba sauri saboda gargadi'n da Aunty Fauziyya na mata akan kar ta daɗe, kayan miya zata siyo mata a can bakin titi, kuma daga gida zuwa bakin titi da ƴar tafiya, gaba-d'aya a gajiye take saboda aikin da tasha yau har da wankin kayanta ta yi, ga rana da ake k'walla wa a garin, gashi ba ta ci abincin rana ba kuma tana jin yunwa sosai gami da ƙishirwa, Aunty Fauziyya ta ce sai ta siyo mata kayan miyar sannan zata ci abincin. Ta shiga wani layi wanda daga shi sai titi, ta ga wani k'aton gida mai kyau, wani kyakkyawan matashi da ba zai wuce shekara 25 ba ne ya fito daga ƙaramar ƙofar gidan hannunsa ɗauke da robar ruwan faro mai sanyi. Tsayawa Neehal ta yi ta ƙura wa ruwan hannunsa ido tana maida Numfashi saboda gajiya, sau ɗaya matashin ya kalleta ya ɗauke kai ya nufi Motar dake fake a gaban gidan, Neehal ganin haka yasa ta ƙarasa kusa da shi da sauri ta ce...........✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_














*2️⃣9️⃣*
















Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*


















..........."Uncle please zan sha ruwa." Kallonta ya yi fuska a sake ya ce "Oh sorry Dear take it." Neehal ta karb'i ruwan da yake miƙa mata tare da faɗin "Thank you." Murmushinsa Mai kyau ya mata, Neehal ta buɗe robar ruwan da sauri har tana yar da kuɗin kayan miyan bata sani ba, kai robar ta yi bakinta zata sha ruwan ya katse ta da sauri ta hanyar faɗin. "No, go there ki zauna sai ki sha." Ya ƙarashe maganar tare da nuna mata wani dakali dake kofar gidansu. Da sauri Neehal ta ƙarasa ta zauna ta fara quqqutar ruwan, sai da ta shanye tass sannan ta yarda robar. Matashin yana tsaye yana kallonta, haka kawai ya ji ya kasa tafiya, Neehal ta dafe cikinta saboda k'ullewar da ya fara mata saboda yunwar da take ji. Cike da tausayawa Matashin ya sunkuya ya ɗauki kuɗin da ta yar a ƙasa ya ƙarasa inda take, cikin tausayinta da ya d'arsar masa a zuciya lokaci ɗaya ya ce "Are you Ok?" Neehal ta girgiza masa kai ta ce "I'm felling hungry." Ya ce "Okay, sorry, wait for me here, I will come now." Neehal ta gyaɗa masa kai tana ƙara dafe cikinta. Cikin 5 minutes ya shiga gidansu ya fito hannunsa ɗauke da Cake wanda aka yi rapping ɗinsa, sai kuma lemon jarka guda ɗaya. Miƙa mata ya yi ta karb'a da sauri tare da kallonsa, a hankali ta ce "Thank you so much." Sannan ta fara cin Cake ɗin, ƙura mata ido ya yi ganin yanda take cin cake ɗin cikin nutsuwa tana lumshe ido, ita kuwa Neehal daɗi Cake ɗin ya mata ba kaɗan ba. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta ɗauki leman ta sha fiye da rabin jakar, ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce "Alhamdulillah." Sai kuma ta miƙe zumbur kamar wadda aka tsikara ta fara ƙoƙarin tafiya, katse ta ya yi ta hanyar faɗin "Zo ki ɗauki sauran mana." Neehal ta ce "Na k'oshi ne." Ya ce "Are you sure?" Ta gyaɗa masa kai, ya ce "To ki tafi da shi gida anjima sai ki ci." Neehal ta waro ido waje ta ce "Aunty zata dake ni idan na je da shi gida." Miƙa mata kuɗin data yar ya yi ya ce "You forget." Neehal ta karb'a da sauri ta wuce. Cake ɗin data bari da lemo ya ɗauka ya shige Motarsa, yana fita titi ya hango ta a gurin mai kayan miya, an yi sa'a ita ma ta juyo suka haɗa ido, d'aga mata hannu ya yi yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tare da d'aga masa hannun, a gurin ya samu almajiri ya bashi ragowar Cake ɗin da lemon. Cikin sauri Neehal ta siyi kayan miyan ta koma gida, zuciyarta cike da tsoron Aunty Fauziyya, wani ɓangaren na zuciyarta ta kuwa farinciki take yau ta ci Cake ta sha lemo. Da masifa Aunty Fauziyya ta tare ta, ita dai tay shiru kawai tana kallonta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Aunty Fauziyya cikin bala'inta ta ce "Shegiyar yarinya mai kama da aljanu, ana miki magana ki tsare mutum da wasu idanunki kamar na mage." Ta kamo kunnen Neehal ta murd'e da ƙarfi tana faɗin, "Gobe ma in ƙara aiken ki ki kuma zuwa ki zauna." Neehal ta saka kuka saboda zafin da ta ji a kunnenta, Aunty Fauziyya ta dungurar da ita a wurin tare da daka mata tsawar ta rufe mata baki. Kayan miyan ta wanke ta bata ta kai markad'e, ko tunanin bata abinci bata yi ba gashi har la'asar ta yi. Cikin mintuna ƙalilan Neehal ta dawo daga kai markad'en da yake anan mak'otansu ake babu nisa. Sai a sannan Aunty Fauziyya ta bata abinci a wani ɗan kwano, jallop ɗin shinkafa ce da cavage ce akai. Neehal ta kai abincin ɗaki ta ajiye a bayan kayanta, dan a koshe take. Aunty Fauziyya bata barta ta huta ba, sai da ta bata wankin uniform ɗin su Aiman, Neehal ta jijjik'a ta shanya dan ba wani iya wanki ta yi ba, sai dai tai ta goggoga sabulu ajikin kaya in ta ga ya yi kumfa sai ta d'auraye ta shanya. Bayan isha'i tana zaune a ɗaki tana yi wa su Aiman Homework, dan Yaran babu abun da suka iya sai dambe da zagi, ashar kala_kala sun iya narkawa kamar ƴaƴan maguzawa. Tun da Neehal ta zo gidan ita take musu Homework da Assignment ɗin islamiyya. Jin Uncle Umar ya shigo ta miƙe ta shiga falon ta gaishe shi, Allah ya so Aunty Fauziyya tana ɗakinta da sai ta k'ulla mata wani sharrin a gurinsa. Bayan ya amsa ta ce "Uncle Ina son na koma School da Islamiyya." Uncle Umar ya ɗan bata rai ya ce "To je ki sai na duba." Neehal ta tashi ta koma ɗaki ta cigaba da abun da take. Aunty Fauziyya ta fito daga ɗakinta tana yamutsa fuska ta ce "Me na ji yarinyar can tana ce maka ne?" Uncle Umar ya ce "Wai Makaranta take so ta koma." Aunty Fauziyya ta haɗe sosai ta ce "Kai kuma saka ta a makarantar zaka yi?" Ya ce "To ya zan yi, tunda Allah ya ɗora mun." "Ka dai ɗora wa kanka." Aunty Fauziyya ta faɗa tana keɓe fuska. Uncle Umar ya ce "Hmmm, tunanin ma makarantar da zan kaita nake, amma ina ga makarantar su Aiman zan kai ta." "Me? Makarantar su Aiman fa ka ce, dubu ashirin da biyar ɗin zaka biya mata? Tab'! To wallahi ka nemarwa kanka sauƙi, ka nemi Government School ka kaita." Uncle Umar ya ce "Ai na ga babu Government School a kusa ne shi ya sa." Aunty Fauziyya ta ce "Ga ta nan ana ginawa, ka bari idan an gama ginin sai ka kai ta mana." Daga haka suke rufe wannan chapter, suka kama wata. Washegari bayan Neehal ta gama shan akinta kamar kullum aka aike ta siyan kayan miya, yau ma ba ta ci abinci ba ta tafi, gashi abun da bata ci ma Aunty Fauziyya ta yi wato tuwo, tuwon ma miyar kuka.








Ta zo dai_dai layin da suka haɗu da mutumin jiya wanda ta rad'a masa suna *Uncle mai kirki* , har ta wuce gidan ta dawo ta tsaya a ƙofar gidan tana kallon gidan, a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta fara knocking, 2 minutes tana tsaye sannan aka buɗe ƙofar. Faɗaɗa fara'a ta yi sosai kamar yadda shi ma yake fara'ar cike da mamakin ganin ta, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka masa kyau sosai, sai tashi daddad'an k'amshinsa yake. Neehal ta ce "Ina yini." Yana murmushi ya ce "Lafiya k'alau." Juya wa ya yi ya ce "Come in." Neehal ta tsaya ba tare data bishi ba, ya juyo ya ce "Ya kika tsaya? Ki shigo mana." Neehal ta girgiza masa kai alamun a'a, ya ce "Why?" Ta ce "Ina jin tsoro." Da ƙyar ya lallaɓa ta ta shiga gidan, a BQ yake har ciki ta shiga ta zauna a falo a d'arare, haɗadd'iyar pride rice ya kawo mata a plate da bottle water da juice, da murna Neehal ta karb'a ta fara ci. Zama ya yi yana kallonta cikin tausayinta. Sai da ta ci ta yi ƙat sannan ta ce "Uncle ina Mamanka?" Ya ce "Tana cikin gida." Ta ce "Nan part ɗinka ne?" Ya ce "Ehh." Shiru ta yi tana ƙarewa falon kallo, cikin kulawa ya ce "What is your name?" Neehal ta ce "Neehal." Ya ce "Wow Nice name, real name ɗinki fa?" Ta ce "Fateemah." Ya ce "Wow! My mother's name." Neehal ta ce "And you?" Ya yi murmushi ya ce "Ahmad." gyaɗa kai ta yi tare da tashi da sauri ta ce "Zan tafi Uncle, zan siyo wa Aunty kayan miya, idan na daɗe zata zane Ni." Ya ce "To Princess, gobe ma zaki zo ko?" Neehal ta yi shiru can kuma ta ce "Ehh." Har bakin titi ya raka ta sannan ya dawo gida. Yau ma data koma gida sai da ta sha bala'in Aunty Fauziyya. Tun daga wannan ranar kullum sai aka aike ta sai ta biya gidansu AHMAD, ya bata lafiyayyen abinci ta ci da drinks, wataran kuma ice cream da snacks yake bata, choculate da sweet kam kullum sai tasha su ta more, idan ta koma gida kuma Aunty Fauziyya tay ta mata masifa, wataran har da duka akan dad'ewar da take, amma ko sau ɗaya bata taɓa tambayarta inda take zuwa ba. Idan ta bawa Neehal abinci sai ta k'ulle a leda ta faki idon Aunty Fauziyya ta fita ta bawa almajiri, tunda yanzu kullum a k'oshe take wuni, abincin dare ma kullum sai ta rage kaɗan take ci. Breakfast kawai take yi full a gidan. A hankali shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Ahmad, kullum ta zo yana mata tambayoyi a game da rayuwarta, a haka ya gane marainiya ce kuma bata haɗu da uwar riƙo ta gari ba, hakan ya ƙara masa tausayinta a zuciyarsa sosai, kullum yana mata ƙarin haddarta na Alqur'ani tunda Uncle Umar ya ƙi saka ta a Islamiyya da School, haka karatun boko kullum yana mata lesson, sai ta yi fiye da awa biyu a gidansu, ta koma gida kuma ta ci duka, amma duk da haka gobe sai ta karsi zuwa.








Yau Sunday da misalin ƙarfe biyu na rana Neehal tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana bitar haddarta, su Aiman kuma sun tafi Islamiyya. Uncle Umar ma baya nan, duk da yau Sunday amma ya fita tun safe shagonsa da yake sayar da kayan masarufi, kuma ba ya dawowa sai dare, kullum haka yake dama, Monday to Friday ma bayan sun tashi daga School ɗin da yake koyarwa can shagon yake wuce wa. Aunty Fauziyya ta tak'wala wa Neehal kira, Neehal ta miƙe da sauri ta fito waje. Aunty Fauziyya tana mata wani mugun kallo ta cilla mata kuɗi ta ce "Ɗauki kuɗin nan, ki je ki siyo mun kayan miya, kuma yau ma ki biya yawon naki da kika saba, wallahi dukan dana miki jiya Nafila ne akan wanda zan miki yau idan kika daɗe. Neehal ta ɗauki kuɗin ta koma ɗaki ta ɗauko Hijab da hula ta saka sannan ta fito ta tafi. Duk da gargadi'n da Aunty Fauziyya ta mata sai da ta biya gidansu Ahmad, dan dukan Aunty Fauziyya zuwa yanzu har jikinta ya saba da shi. Kamar kullum bayan ta yi knocking ya zo ya buɗe mata ƙofa ta shiga. Yau ba BQ ya kai ta ba, ainihin cikin gidan ya nufa da ita. A falon gidan ya zaunar da ita sannan ya nufi kitchen yana kiran sunan Mamy, Mamy wadda takasance ƙanwar mahaifiyar Ahmad ta fito daga kitchen tana amsa masa. Ya tsaya tare da faɗin "Sannu da aiki Mamy." Mamy ta ce "Yawwa son." Nuna mata Neehal ya yi ya ce "Ga yarinyar da nake baki labarinta na kawo miki ita." Mamy ta washe baki tana duban inda Neehal take ta ce "Ita ce wannan, Masha Allah, ga ta kyakkyawa da ita." Ta ƙarasa kusa da Neehal ɗin, Neehal ta durqusa ta ce "Ina yini Mama." Mamy ta ce "Lafiya k'alau, sannunki yarinya ya sunanki?" Ta ce "Neehal." Mamy ta ce "Masha Allah, Allah ya miki albarka ya inganta rayuwarki." Ahmad dake tsaye yana fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa da "Ameen." Mamy ta kawo wa Neehal lafiyayyen abinci da ruwa da juice, Neehal ta mata godiya sannan ta zauna ta ci. Mamy sai kallonta take cike da tausayawa, dan Ahmad ya tsakura mata labarin Neehal. Bayan Neehal ta gama cin abinci ta dubi Mamy ta ce "Please Mama ki tsefe mun kaina, na ce Aunty ta tsefe mun ta ce inyi da kaina, ni kuma ban iya ba." Mamy ta yi murmushi ta tashi ta ɗauko kibiya ta ce Neehal ta cire hijabin jikinta ta tsefe mata, Neehal tana cire Hijab sai ga shatin bulalar jiya ruɗu_ruɗu a jikinta, kasancewar hannun rigar jikinta k'arami ne. Mamy tay salati ta ce "Neehal wa ya dake ki haka?" Neehal ta ce "Aunty ce." Mamy cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Amma kuwa wannan matar bata da imani ko kaɗan, yanzu wannan yar yarinyar ita akewa irin wannan dukan kamar wani qaton gard'in? Wai duniya ina zaki da mu ne, dan bake kika haifi 'ya ba sai ki dinga zaluntar ta, menene abun damuwa a riqon ƴar wannan yarinyar da za'a dinga azabtar da ita haka?" Cikin takaici Ahmad ya ce "Hmm, kin ga wannan dukan kullum sai an mata shi, kuma Mamy wanke wanke, shara, mopping, wanki ta ce mun kullum ita take yi, sannan tai aike, kuma sun ƙi sata boko da islamiyya." Mamy ta ce "To kuwa wannan mata ta kiyayi duniya, dan wallahi cutar da Maraya ba ƙaramin abu ba ne, ta kiyayi randa Hakkin yarinyar nan zai kamata, kuma itama uwa ce ta haifa ko zata haifa nan gaba, kuma ba ta san inda ƴaƴanta zasu ƙare rayuwarsu ba, tunda ba'a mata alƙawari zata rayu da su har abada ba." Sosai ran Mamy ya ɓaci tai ta faɗa kamar zata ari baki, da gidan Fauziyyan ma ta ce zata je ta mata tatas duk da bata san ta ba, da ƙyar Ahmad ya taushe ta ta haqura ta fasa zuwan. Tass ta tsefe wa Neehal daddaud'an kanta da tunda ta dawo gidan Uncle Umar kusan 2 months Sau ɗaya wata mak'ociyarsu ta taɓa mata kitso. Mamy ta wanke mata kan tass ta busar da shi ta shafa wa gashin mai, ta mata wanka ta shafe mata jiki da mai, har yankan farce da cire dattin kunne sai da Mamy ta mata ranar. Tana yi tana mitar baƙin ciki Aunty Fauziyya take dan ta ga Neehal kyakkyawa ce shi yasa bata kula da ita. Ahmad kam daga baya dariya Mamy'n ta fara ba shi da mitartata, sai ga Neehal ta fito fess da ita sai k'amshin turaren da mamy ta saka mata take. Sai wajen ƙarfe biyar Ahmad ya raka Neehal ta siyo kayan miyan, suna tafe yana ta aikin maimaita mata "Ta yi kyau sosai." Dan har cikin zuciyarsa ta masa kyau ba kaɗan ba. Ita kam Neehal sai dai tay masa murmushi kawai. Har kusa da layinsu ya rakata sannan ya juyo, ita kuma ta ƙarasa gida..........✍️












_*Yau ban yi edit ba, sorry for the typed error.*_














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










*3️⃣0️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














.........Sosai Ahmad yake jin nishad'i da farinciki a duk lokacin da suka kasance tare da Neehal, sai ya ji kamar kar ta tafi ta zauna tay ta masa hirarta da muryarta mai daɗin sauraro gami da sassayan murmushinta. Har cikin ransa yake jin wani abu game da yarinyar, a da yana tunanin tausayi ne kawai, amma yanzu duk da da akwai tausayin amma da wani abu daban da ya kasa gane ko menene. Babban tashin hankalinsa yanzu befi 1 month ya rage masa ya koma gidansu ba, dama a Abuja suke wani course ne ya kawo shi Kano, dan shi bai taɓa zuwa Kano ba sai wannan time ɗin, saboda duk Relatives ɗinsu a Abuja suke both na Mamanshi dana Dad ɗinsa. Mamy ma da a Abuja take, a wurin aiki ne aka yi posting ɗin mijinta zuwa Kano shine suka dawo, itama ba tafi two years da dawowa ba. Zuciyarsa babu daɗi ya ƙaraso gida, zama ya yi akan kujera yana sauke numfashi, a hankali ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ya latsa ya shiga kallon pictures ɗin da yay wa Neehal d'azu, ta yi kyau sosai tana ta zuba murmushi.








Zuciyar Neehal cike da tsananin tsoro da fargaba ta ƙarasa gida, ba ta ga Aunty Fauziyya a tsakar gida ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙarasa kitchen ta ajiye kayan miyan sannan ta nufi falo, nan ma ba ta ga Aunty Fauziyyan ba, hakan ya sa ta wuce ɗakinsu tana sauke ajiyar zuciya. Yau wani daɗi take jin jikinta ya mata, to mamy ta dirje ta tass ta fitar mata da duk wani datti da daud'a dake jikin nata. Sai wajen magriba time ɗin su Aiman sun dawo daga islamiyya ta ji maganar Aunty Fauziyya, gabanta ya yanke ya faɗi saboda tsoro. Fauziyya wadda tun kafin la'asar ta kwanta take baccin asara sai yanzu yaranta suka tashe ta, ko sallar la'asar ba ta yi ba. "Neehal! Neehal!!" Ta shiga ƙwalawa Neehal kira, Neehal ta fito da sauri tana faɗin "Na'am Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta jefe ta da shi kamar kodayaushe, ta ce "Ina aiken dana miki?" Neehal ta ce "Na ajiye a kitchen." Aunty Fauziyya ta ce "Yau ma sai da kika gama yawon naki sannan kika dawo ko?" Neehal ta girgiza mata kai cikin tsoro. Aunty Fauziyya ta ce "Hmm, munafukar yarinya, zaki yi bayani ne idan wanda ya ajiye ki ya dawo gidan, zaki faɗa masa inda kike zuwa ne, in ma iskanci kike zuwa ki yi duk za ki masa bayani." Neehal dai tay shiru kanta na ƙasa. Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ƙara cewa "Taso ni mu je ki mun tsinta." Neehal ta tashi ta bi bayan ta, a k'aton farantin silver ta zubo shinkafa yar Hausa ta ajiye a gaban Neehal ta ce ta tsince mata, Neehal ta kalli shinkafar ta kalle ta, ta ce "Aunty ban iya ba." Rank'washinta Aunty Fauziyya ta yi sannan ta nuna mata yanda zata yi. Neehal fa ta duk'ar da kai ta fara tsinta, ga duhun Magriba ya kawo kai da ƙyar take gani. Fitila Aunty Fauziyya ta bata ganin magriba ta yi, Neehal ta ce "Aunty bari na yi sallah sai na cigaba." Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce "Dalla ni ki cigaba da mun aikina, algungumar yarinya kawai, sai ka ce da Sallar kike, ko kuma in kin yi lada zaki samu." (Allah ka raba mu da jahilci.) Neehal ta turo baki gaba ta cigaba da tsintar, Nasihar Abbanta da yake mata a kodayaushe ta tuno, inda yake ce mata "Ƴar albarkata ko me kike yi idan kika ji an kira Sallah ki bar shi ki je ki yi Sallah, idan kin idar sai ki ci gaba." Tun tana ƴar k'ank'anuwarta yake faɗa mata haka. Hawaye ne ya zubo daga cikin idanunta, da sauri ta share su dan kar Aunty Fauziyya ta gani, Allah ya rufe wa Aunty Fauziyya ido ba ta ga canzawar da Neehal ta yi ba na gyara ta da Mamy ta yi, gashi kanta da hula shi yasa ba ta lura da gashinta da ya sha gyara ba, da yau Neehal ta shiga uku. Sai wajen isha'i ta gama tsintar, duk da shinkafar bata da tsinta sosai, amma saboda bata saba ba shi yasa ta daɗe, aiko da ƙyar ta iya tashi dan bayanta ya k'age, ga cizon sauro da ta sha, Aunty Fauziyya kuwa ko sannu sai ma tukwuicin harara ta samu. Kan kujera ta je ta kwanta, yau ta ci sa'a ba'a ce ta sauka ba. Bayan Uncle Umar ya dawo yana ɗakin baccinsu yana marking papers Aunty Fauziyya dake goge Uniform ɗin su Aiman ta dube shi ta ce "Baban Iman inata zuci_zucin ka dawo in faɗa maka wani hali da yarinyar can ta tsira." Ba tare daya d'ago ba ya ce "Wacce yarinya kenan?" Ta ce "Neehal mana." Ya ce "Me kuma ta yi." Ta tab'e baki ta ce "Hmm, yawon banza ta koya, idan na aiketa sai ta yi awa uku a waje, ƴar ƙarama da ita har ta san wani bin maza." Da sauri Uncle Umar ya d'ago ya dubi Aunty Fauziyya ya ce "Haba Fauziyya, yarinyar da ba ta fi shekara goma sha ɗaya ba ita zaki ce tana bin maza? Ki dai sake wata maganar ba wannan ba gaskiya." Aunty Fauziyya ta ce "Lallai Umar me kake nufi? Sharri zan mata ko me? Kuma idan ba maza take bi ba gidan ubanwa take zuwa idan na aike ta, har ta yi awanni." Uncle Umar ya ajiye red biron dake hannunsa tare da miƙewa a fusace ya ya fito falo. Neehal dake kwance rub da ciki akan kujera har lokacin, ta ɗan samu baccin gajiya ya ɗauke ta ji murya Uncle Umar a tsawace yana cewa "Ke Neehal! Neehal!" A firgice ta farka tare da buɗe ido, cikin muryar bacci ta amsa masa tana ƙoƙarin tashi zaune cikin tsoro. "Gidan uban wa kike zuwa idan an aike ki?" Uncle Umar ya tambaye ta cikin tsawa, Neehal ta manne jikinta ba ta ce komai ba, Uncle Umar ya ƙara daka mata wata tsawar da faɗin "Ba dake nake ba." Neehal bata iya ƙarya ba, hakan yasa ta fashe da kuka dan ta san idan ta faɗawa Uncle Umar inda take zuwa sai ya kusa kashe ta da duka. Masifa ya dinga surfa mata, ya kuma ce aka kuma aiken ta ta daɗe sai ya karya k'afarta. Ba ƙaramin tsorata Neehal ta yi da Uncle ɗin nata ba, hakan yasa washegari bata biya ta gidansu Ahmad ba. Shi kuwa tun da ya yawo daga inda yake zuwa aiki yake ta zuba idon ganinta amma ya ji ta shiru har yamma. Yau data koma da wuri Aunty Fauziyya ta ce "Ehh lallai, wato ni kika raina shi yasa ba kya jin maganata, shi da kike tsoronsa gashi ai kin ji faɗan sa." Ta ƙarashe zancen tare da jan k'wafa. Neehal kam tunanin Uncle ɗinta Ahmad ta shige ɗaki tana yi, ta san yanzu ya siyo mata kayan daɗinta yana jiran ta je ta ci. Yau kwana uku Neehal bata je gidansu Ahmad ba, kullum sai dai ta kalli gidan ta wuce.








Misalin ƙarfe 2/30mp Aunty Fauziyya ta aiki Neehal siyan kayan miyan gado, dan shi kaɗai ne aikenta tunda komai na abinci Uncle Umar ya siyo ya dire, sai kuma markad'e idan babu wutar Nepa. Babu musu ta karb'a kamar kodayaushe ta tafi. Yau ma kallon gidansu Ahmad ta yi ta wuce duk kuwa da yanda zuciyarta take azalzalarta akan ta shiga, amma tsoron abun da Uncle Umar zai mata idan Aunty Fauziyya ta faɗa masa yasa take ƙin shiga. Tana shan kwana Motar Ahmad na shigowa layin, cikin tsananin murnar ganinta Ahmad ya taka burki wanda har yasa

Please Login or Register in order to submit comment