Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kashe Anwar, an gano su kuwa.?" Ammi ta ce "Har yau dai shiru babu labari ba'a gano ko suwaye ba." Haneefah ta ce "Allah ya bayyana su cikin gaggawa." Suka amsa Amin gabad'aya. Kafin Magriba suka musu sallama suka tafi.








*After 2 weeks*




Su Dad sun kai kuɗin Auren Ameen gidansu Hafsat, inda a ka tsaida ranar biki wata huɗu masu zuwa. Maganganu sun yi ta yawo a cikin Family'n su Dad sosai, wasu na faɗin Ameen ya yaudari Hameedah, wasu kuma na faɗin Ameen kuɗin mahaifin Hafsat ya bi zai aure ta, wasu kuma suna faɗin ai gwara ma da ba Hameedah zai aura ba, dan sam ba su dace ba. Mommy'n Hameedah kuwa kamar za ta yi hauka, duk da an kai kuɗin amma ƙara kwantarwa da Hameedah hankali take da faɗin indai ta na raye Ameen ba shi da mata sai ita. Su Neehal da Haneefah da sauran cousins d'in Neehal murna suke sosai da baikon Yayansu. Next week su Neehal za su yi resuming school, ta na cikin d'akinta ta na guge hijabs ɗinta Mama ta shigo d'akin. "Neehal yau fa Muna da baƙi a gidan nan." Neehal ta ce "Suwa kenan Mama?" Mama ta ce "Ameen ya ce Hafsat za ta zo ta gaishe ni, ki bar gugar nan ki taso mu ki musu ɗan abun taɓawa." Neehal cikin murna ta ce "Yanzu kuwa Mama, ashe yau mu na da manyan baƙi." Mama ta ce "Ki dai yi sauri kar time ya k'ure." Sosai Neehal ta zage jikinta ta shiryawa su Hafsat kayan ciye_ciye kala_kala ita da su Dije da suka taya ta. Bayan sun gama aikin ta na nunawa Mama abubuwan da suka yi Mama ta ce. "Um lallai Neehal, da ni na saki wannan aikin na san har kuka sai kin mun, amma da yake budurwa Ameen ce za ta zo ko nuna alamun gajiya ba ki yi ba." Neehal ta yi murmushi kawai. Mama ta ce "Ki je ki yi wanka kafin su ƙaraso, su Dije za su jera musu abincin a dinning." Neehal ta ce "Toh."




Hafsat 'Ya mace ɗaya tilo a gurin mahaifinta wanda ya kasance hamshaqin mai kuɗi, Hafsat ta so Ameen kamar ba gobe, amma Ameen ya nuna sam ba ya ra'ayinta. A wancan lokacin haka za ta yi ta zarya gidan Mama tun suna Abuja ta na gaishe ta, daga baya ne da ta ga Ameen ɗin dai ba ya k'aunar ta sai ta hak'ura ta k'yale shi amma ba don ta dena k'aunar shi ba. Cikin wata rantsatstsiyar Mota suka ƙaraso gidan, driver'nta a gaba ya na driving ɗinsu sai ita da k'awarta mai suna Fadeela a bayan Motar. Bayan ya yi parking Motar ya fito da sauri ya buɗe mata mota, cikin izzarta ta fito ta na kallon harabar gurin. Duk da kasancewar mahaifinta ya fi Dad kuɗi amma babu abun da gidansu zai nunawa gidansu Ameen a kyau da tsaruwa, sai dai ya fishi girma. Cikin takunta ɗai_ɗai ta fara tafiya k'awarta na bin bayanta. D'aya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya musu jagora zuwa part ɗin Mama. Hafsat sosai take farin ciki da zuwanta gidansu Ameen ɗin, domin wannan zuwan ta zo ne a matsayin suruka ba kamar baya ba da take zuwa dan neman samun guri. Fadeelah ta dube ta tace "Hafsy na lura yau wani farin ciki ki ke na musamman kamar yau ne ranar auran naku." Hafsat ta faɗaɗa fara'ar fuskarta ta ce "Hmmm Fadeelah kenan, wannan zuwan fa da na yi gidansu Ameen a matsayin suruka na zo, saɓanin da da nake zuwa da k'ok'on barata." Fadeelah ta ce "Gaskiya ki na son Ameen da yawa."Hafsat ta ce "Faɗar irin son da na kewa Ameen ms ɓata baki ne saboda tarin yawansa a cikin zuciyata." Fadeelah ta ce "Amma me yasa be bari sai ya dawo daga Lagos ki zo yana nan ba?" Hafsat ta ce "Ni na matsu sai na zo na gaida Mum ɗinsa, shi ma da yaso na bari sai ya dawo na ce ni dai sai na zo......." Buɗe k'ofar da Zulai ta yi ya katse mata maganar da take. Zulai ta ce "Sannunku da zuwa, ku shigo." Fadeelah ce kawai ta amsa da "Yawwa" amma ita Hafsah ɗan yatsina fuska ta yi ta wuce ciki. Gurin zama Zulai ta nuna musu sannan ta haura sama domin ta sanarwa da Mama zuwansu. Hafsat ta dinga satar kallon falon dan ba ƙaramin kyau da burge ta ya yi ba, ga wani sassanyan k'amshi da yake tashi a cikin sa. Neehal Mama ta turo ta hawo da su sama. Neehal da murnarta ta taho dan tarar Aunty'n tata. Tun da ta fara sakkowa Hafsat ta ƙura mata ido cikin fad'uwar gaba, domin ta gane ita ce Neehal ɗin da kullum sai Ameen ya yi zancen ta, dama ta santa a ASTV amma sai ta ga kamar a TV'n ma rage mata kyau a ke a fili ta fi kyau. Haɗe rai ta yi sosai tare da ɗauke kanta daga kallon Neehal ganin ta ƙaraso cikin falon. Da fara'a sosai Neehal ta ce "You are highly Welcome Dear, sai dai ban san Aunty'n tawa ba da nake ta ɗokin zuwan ta, wacece acikin ku?"." Fadeelah ta yi murmushi dan ita kam yanda Neehal ta musu ta burgeta, nuna Hafsat ta yi ta ce "Gata nan, tunda kin kasa hak'uri na gabatar miki da ita." Neehal ta yi murmushi ta na kallon Hafsat ta ce "Masha Allah, gaskiya Yayanah ya iya zaɓe." Ta ƙarashe zancen tare da ƙoƙarin rungume Hafsat ba tare da ta damu da ɗauke kan da ta mata ba. Wani kallon wulak'anci Hafsat ta jefa wa Neehal ta na yatsina fuska kamar ta ga kashi..............✍️






*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL ⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_










1️⃣5️⃣












Ina ma'abota karatun littattafan HAUSA masu ilimantarwa ,nishaɗantarwa,wa'azantarwa gami da sa canjin rrayuwa🗣️🗣️🗣️.


AƘIDATA! AƘIDATA!! AƘIDATA!!!.




Idan baki karanta ba inason nabaki shawarar ki nemi naki
.


AƘIDATA! Labarin wata haɗaɗɗiyar hamshaƙiya ƴar hamshaƙin mai kuɗi ce😍gata da izzah, taƙama,gadara,iko,ilimi,wayo da sauransu🥳Amma duk da wannan halaye nata tana da wasu wanda taɗaukesu AƘIDARTA, Akwai takun saƙa tsakaninta da matar babanta da kuma agololin da tazo dasu🥺


Ana bibiyar rayuwarta ta ko'ina hakan yasa rayuwarta taƙare aƙasar waje🥳
Bata da abokai da suka wuce dabbobi zomaye,maguna,tattabaru,dasauransu🥳sune abokan dariyarta da kukanta kuma suke ɗebe mata kewa🥳🥳🥳🥳


Bata tausasa lafazi ga kowa ciki kuwa hadda ma'aifinta ciki 🥳🥳🥳




🥳🥳🥳🥳Cikin rashin yaddarta tasaki jiki da direbanta wanda shine masomin ƙaddararsu 😳😳bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koyaci amanarta🥳🥳shin mezai faru idan tasan direbanta ma'aikacin sirri ne❔❔❔❔❔


Kutsen ƙaddara ya kutso rayuwarta ba tare da ta shirya ba, rayuwarta takoma wani gari dako ruwan famfo babu, sedai kududdufi wanda ake wanka da wanki aciki shine ruwan amfanin garin.... 😳alhalin ita idanba ruwan jarka ba batasaba shan wani ruwaba🥳🥳🥳🥳🥳


Sabulun wanka kansa babu semai ƙarni alhalin tasaba wanka da shower jell🥳🥳🥳🥳🥳


Akwai tarin sarƙaƙiya da ƙulle ƙulle a cikin wannan labari me ban al'ajabi




ƘAƘA ƘARA ƘAƘA🥺🥺🥺






WIDAD🥳WIDAD🥳WIDAD🥳




Duk me son jin cikakken kabarin Widad da mahaifinta NASIR DAULA yanemi 2&3 akan farashi ƙalilan🥳🥳🥳🥳🥳daman part 1🥳🥳kyauta ne meso taimin magana nabata🥰🥰💞💞




LALLAI 🥳AYSHERCOOL ✍🏻ta dabance basirarta bazaka ganeta ba seka kranta AƘIDATA domin ta farantawa mu masoyanta fie da yadda tay AWATA KISSAR........! SAI MATA😊😊.


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻AƘIDATA TAYYI DABAN DATA KOWA🥳🥳


Normal gro duka littafi biyun #300
Idan kuma laya zaki siya #200


Vip #500.




Idan kuma se angama zaki siyi complete documment #700.




Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank


Se aturo evidence of payment through 07063065680.




Share please🙏🏻🙏🏻🙏🏻.






.......... Neehal ce zaune a office d'inta ta na operating system, sai sauke numfashi take akai_akai alamun wani abu na damunta. Haneefah dake zaune a kujerar da take fuskantar ta ta na latsa waya, lokaci zuwa lokaci ta na d'agowa ta na kallon ta. Ajiye wayar ta yi a kan table ɗin gabanta cikin kulawa ta ce "Wai Neehal meke damun ki ne.?" Ba tare da Neehal ta d'ago ba ta ce "Babu komai, me ki ka gani.?" Haneefah ta ce "Yanayinki ya nuna kamar wani na damun ki." Neehal ta ce "Babu gaskiya, idan ma da akwai ba zai wuce Rashin jin Ya Sadik ba ne da banyi ba yau." Haneefah ta ce "Kamarya rashin Ya Sadik.?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Tun jiya da yamma da muka yi waya har yanzu bai ƙara kira na ba, gashi last seen ɗinsa a WhatsApp tun 6:44 pm na jiya" Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ganin haƙansu ya kusa cimma ruwa ita da Sadik, domin ita ta bashi shawarar ka da ya nunawa Neehal ya na sonta a yanzu, ya bari sai ta shak'u da shi sosai sai ya sanar mata. Ita kuwa Neehal baiwar Allah, maganarta take bil hak'k'i ba tare da tunanin komai ba. "To ki kira shi mana ki ji ko lafiya." Cewar Haneefah cikin nazartar ta. Neehal ta ce "Kuma fa hakane, bari mu koma gida zan kira shi." Haneefah ta ce "To, Allah ya sa lafiya dai." Neehal ta ce "Amin." Bayan sun koma gida da yamma wanka kawai Neehal ta yi ta kira layukan Sadik amma duka ba sa tafiya. Zama ta yi a bakin gado tare da dafe kanta cikin damuwa, can kuma ta ja ɗan ƙaramin tsaki ganin damurwar na neman hanata sukuni. A fili ta ce "To mene ma na damuwar haka akan shi.?" "Sadik ya cancanci ki damu dashi fiye da haka ma, duba da tarin kyautatawarsa a gare ki, gami da kulawar da yake nuna miki." Wata zuciyar ta ba ta amsa da faɗin haka. Mik'ewa tsaye ta yi zumbur kamar an tsikareta ta na sauke ajiyar zuciya, saboda wani tunani da ya ɗarsu a ranta. Wata doguwar rigar abaya purple color ta ɗakko ta zira a jikinta, turarukanta ta mutstsika ta yane kanta da ɗankwalin abayar, wayoyinta kawai ta kwasa a hannunta ta fice daga d'akin. A falon ƙasa ta tarar da Mama. "Ke ina zaki haka ki ke sauri kamar za ki tashi sama.?" Mama dake kallon Neehal tunda ta fara sakkowa daga kan steps ta fad'i haka." Neehal ta tattaro nutsuwarta ta na ɗan sosa kanta ta ce "Gidan Aunty za ni, kuma sauri nake saboda in yi in dawo da wuri." Cikin mamaki Mama ta ce "Gidan Aisha kuma da wannan sakaliyar yammar? Daga dawowarki daga aiki ko abinci ba ki ci ba.?" Neehal ta yi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa. Mama ta ce "Me ma za ki yi a gidan A'ishan?" Neehal ta ce "Gaishe ta zan yi, na dad'e ban je ba." Mama ta mata kallon tsaf ta ce "Ki bari gobe kya je." Neehal ta ce "Gobe fa sai six zan dawo daga school." Mama ta ce "To kya je wani time ɗin." Neehal ta marairaice ta ce "Please Mama." Mama ta ce "Ba fa za ki fita ba Neehal a yamman nan, idan Dad ɗinki ya dawo me zan ce masa.?" Neehal ta turo baki gaba ta juya za ta koma sama. Mama ta katse ta ta hanyar faɗin. "Ki shiga kitchen ki zubo abinci ki ci." Neehal ta yi hanyar kitchen ba tare da ta ce komai ba, abincin ta ɗebo kaɗan ta koma sama. Ta na shiga ɗakinta ta ajiye shi a kan bedside ta hau gado ta kwanta, sosai ta ji takaicin hana ta zuwa da Mama ta yi harda 'yar k'wallarta, kiran Sallar Magriba ne ya tada ta. Bayan ta idar da Sallah ta ɗakko abincin ta fara ci, sai kuma yanzu take jin haushin kanta na damuwar da ta yi akan kawai yau rana ɗaya dan ba su yi waya da Sadik ba, tambayar kanta ma ta yi inda ta je unguwar su Aunty A'ishan gidansu Sadik ɗin za ta je neman sa ko kuma yaya? Sakin ranta ta yi ta cigaba da sabgarta duk da kewar Sadik ɗin na nuk'urk'usar ranta.






Neehal na na kitchen ta na yiwa Dad pepper chicken Mama dake falon a zaune ta na kallon labarai ta shigo kitchen ɗin ta na faɗin. "Neehal kin kusa gamawa.?" Neehal ta ce "Ehh na kusa." Mama ta ce "Kawo in ƙarasa ki je falo Sadik ya zo." Neehal ta juyo da sauri ta na duban Mama cikin fad'uwar gaban da ba ta san dalilin ta ba." Mama ta ƙaraso cikin kitchen, Neehal ta na Ƙoƙarin fita Mama ta ce "Ki zuba masa abinci mana." Neehal ta ce "Toh, hijab zan ɗauko." Jiki a sanyaye ta ƙaraso ta zauna a kujerar kusa da shi bayan ta ajiye masa abinci a gabansa. Kanta a ƙasa ta ce "Ina yini." Sadik da yake ta binta da kallo ya ce "Lafiya k'alau ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Sadik ya gyara zama cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya ne na ganki wani iri.?" Neehal ta ce "Lafiya ta k'alau." Sadik ya ce "Uhm, ko ki tambaye ni yau ina shiga.?" Neehal ta ce "Ai zan tambaye ka, dafatan dai Lafiya.?" Sadik ya ce "Lafiya lau, sha'anin aiki ne ya kawo haka." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Sadik ya yi murmushi cikin tsokana ya ce "Fushin me ki ke yi to.?" A shagwab'e ta ce "Ni ba fushi nake ba."




"Uhm rigimar autanci ce ta motsa kenan."


Neehal ta yi murmushi saboda yanda yay maganar ya bata dariya. Hirar su suka cigaba da yi cikin nishad'i, wani irin daɗi take ji saboda ganin Sadik, cikin lokaci kaɗan ta ware suka shiga hirarsu. Sadiƙ mutum ne da ya san takan bi da duk wanda yake mu'amala da shi, mutum ne mai tsananin kirki da hak'uri, gashi da sanyi kamar ba lawyer ba, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu, ga uwa uba nutsuwa da addini. Abun da yake ƙara burge Neehal da shi nasiha da faɗin gaskiya a kodayaushe, ko yaya kuka ɗan zauna dashi sai ya tunatar da kai wani abu na addini da mu'amalar rayuwa. Mama ma yaron ya na burgeta, ta yaba da hankalinsa da nutsuwarsa, shi yasa ba ta hana mu'amalar su da Neehal.




Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, yau gashi bikin Ameen ya matso saura satittika, shirye-shiryen biki ake ba kama ƙafar yaro, ɓangaren gidan amarya da gidan Ango, ba yama kamar gidan su Amarya, dan su yanda suke tsara bikin ma sai anfi sati ana shagali, ango ne yake neman ba su cikas dan shi ya ce bashi da lokacin ɓatawa a yawon zuwa events, amarya dai ta na ta lallab'ashi a kan ya amince amma ya ƙi. Su Mama shirin su suke sosai ita da 'yan'uwanta, Ameen ya saki kuɗi an haɗa lefe na gani na faɗa, Aunty Sadiya da Aunty A'isha ne suka haɗo masa. Ƴan'uwan Dad ma masu murna da auren ba a barsu a baya ba gurin nasu shirin.








Yau Saturday Misalin ƙarfe goma na safe Neehal ta na kwance a kan gadonta ta na bacci ta ji ana tashin ta, a hankali ta buɗe idanunta dake cike da barci ta na karanta addu'ar tashi daga bacci a zuciyarta. Ameerah 'yar gidan Uncle Mahmud ta gani tsaye a kanta, yunk'urawa ta yi ta tashi zaune ta na mutsitstsika ido, Ameerah ta na murmushi ta zauna a bakin gadon ta na faɗin. "Bacci har wannan ranar Yaya Neehal." Cikin murya mai cike da bacci Neehal ta ce "Kin san jiya muka gama exam, baccin da ban yi ba ne kwana 2 saboda karatu nake ramawa, yaushe ku ka zo?." Ameerah ta ce "Yanzun nan, Mama ta ce in shigo in tashe ki." Neehal ta ce "Welcome, ke da Ammi ku ka zo.?" Ameerah ta ce "Ehh, suna falo suna kallon lefe." Neehal ta sauka daga kan gadon ta na faɗin, "Kin san nima har yau ban samu nutsuwar ganin lefen nan ba, saboda exams d'in da muke, gashi har za a kai gobe." Ameerah ta ce "Ai dama exam akwai caza wa mutum kai, Allah dai ya ba da sa'a." Neehal ta amsa da "Amin" tare da shigewa toilet.






Bayan ta shirya suka sauko ƙasa inda suka tarar da Mama,Hajiya,Ammi,Aunty Sadiya da Aunty A'isha sun baje kayan lefen a falon suna kalla, Ammin su Ameerah sai yaba kayan take ta na faɗin "Masha Allah kaya sun yi sosai". Neehal ta ƙarasa ta rungume Hajiya cikin murnar ganinta ta ce "Hajiyata Oyoyo na yi miseed ɗinki." Hajiya ta ce "Kamar da gaske, ina ja'irar k'awarki.?" Neehal ta ce "Daɗina dake ba'a miki gwaninta sai ki gwale mutum." Hajiya ta ce "Na ji ɗin." Neehal ta sake ta ta ƙarasa kusa da Amminsu Ameerah ta rungume ta tare da gaishe ta, Ammi ta amsa mata cikin fara'a da kulawa. Gaishe da su Mama da Aunties ɗinta ta yi. Mama ta dubeta ta ce "Ki je ki haɗa break fast ki kaiwa Yayanki, kema ki haɗa ki ci." Neehal ta ce "Mama bari na ga kayan nan sai na kai masa." Hajiya ta tari numfashinta da faɗin "Kayan da sun kusa sati a gidan nan, mak'ota da ƴan'uwa duk sun zo sun gani amma ke ki na kwana a gidan baki gani ba." Mama ta bata amsa da faɗin "Ba ta wani gani sosai ba saboda ta na exam, kin san Neehal idan ta na exam ba ta da nutsuwa." Aunty Sadiya ta ce "Yanzu dai an gama, sai a bita da addu'a Allah ya ba da sa'a." Suka amsa gabad'aya da "Amin." Neehal bayan ta gama ganin kayan ta mik'e ta shiga kitchen ta haɗawa Ameen break fast kamar yadda Mama ta bata umarni, tunda Ameen ɗin a gida ya kwana yau. Ta ɗauki kayan ta na duban Ameerah da ta taya ta haɗa kayan ta ce "Mu je ki raka ni na kaiwa Yayan." Ameerah ta riƙe hab'a tare fito da idanunta waje ta ce "Wa? ki je ke kaɗai dai, kin san halin kayanki fa." Neehal ta ce "Kar ki je ɗin, kuma sai na faɗa masa in ce kince masa masifaffe." Ameerah ta ce "Allah ya na gani dai." Ammi ta bi Neehal da kallo bayan sun fito harta fice daga falon, Ammi ta sauke Numfashi ta ce "Neehal har yanzu ba ta maida jikinta ba tun ramar da tayi lokacin rasuwar Anwar." Mama ta ce "To bata son cin abinci, ba dole tai ta rama ba." Ammi ta ce "Duk da rashin cin abincin ma, amma mutuwar na damunta a rai har yanzu." "Ai dole ne ta damu Aunty Bilki, Samari har biyu sai an kusa bikinku duk su mutu." Cewar Aunty Sadiya cikin jimantawa. Mama ta ce "Wlh nima abun na damuna ina tsoron kar ace sanadin Neehal ake kisan nan." Cikin tarar numfashi Hajiya ta ce "Ashsha, faɗima ba na hanaki wannan zancen ba, yanzu idan wani ya ji ba sai ya samu abun ɗorarwa ba, tunda kema uwarta ki na faɗa, kun san mutane ba sa rasa abun fad'i, yanzu sai a gogawa yarinya baƙin fenti aita jifanta da sharruka kala_kala." Mama ta sauke numfashi ta ce "Shikenan Hajiya Insha Allahu na dena faɗar haka, shima Dad ranar da na faɗa masa haka sai ya hauni da faɗa wai a kan me zance haka, Neehal ɗin me taiwa wani da zai dinga bibiyarta ya na kashe mata samarinta?" Aunty A'isha da ba ta ce komai ba tunda suka fara maganar sai yanzu ta ce. "To mu dai muna ga Allah, kuma shi zai warware mana gaskiyar al'amari, duk ma mai nufin wani da sharri Allah ya mayar masa kansa." Suka amsa gabad'aya da "Amin."




Ameen ya na cikin bedroom ɗinsa ya na shiryawa ya ji a na knocking k'ofar falo, sai da ya ƙarasa shirinsa a tsanake sannan ya fito dan zuwa ya buɗe, zuwa lokacin Neehal ta gaji da tsaiwa ga kaya a hannunta. Ya buɗe k'ofar tare da yin baya dan bata damar shigowa, Neehal ta yi sallama sannan ta shiga. "Yaya a ina zan ajiye maka?" Ta tambaye shi bayan ya amsa mata sallamar. Kan carpet d'in dake tsakiyar falon ya nuna mata, ajiyewa ta yi ta na sauke numfashi. Juyowa ta yi Ameen dake kallonta yay saurin ɗauke kansa tare da zama a kan kujera 2 seater. Neehal ta zauna a kusa da shi ta na kallonsa a ranta ta na gulmarsa ganin kamar ƙara kyau yake ya yi wani fresh abinsa, Neehal a ranta ta ce "Tun kafin a yi auren, wannan ina ga anyi auren." "Ina kwana Yaya" ta faɗa cikin nutsuwarta. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Lafiya, Ya exams.?" Neehal ta ce "Mun gama jiya." Ameen ya jinjina kai ya na dubanta ya ce "Allah ya ba da sa'a." Neehal ta ce "Ameen." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta na son ta tambaye shi abu amma ta kasa saboda sanin halin halinsa, wannan ƴar sakewar da ta samu ya mata yanzu sai ta nemeta ta rasa. Wayarta dake cikin aljihun rigarta ce ta fara vibrate, hannu ta zira ta ɗauko a tunanin Mama ta ce amma sai ta ga Sadik ne. D'agawa ta yi ta na murmushi ta kara a kunnenta. "Wa'alaikassalam Yaya Sadik ɗina." Ta fad'i haka cikin murmushi mai sauti alamun ta na cikin nishad'in kiran da a ka mata. Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Lafiya k'alau and you." Ameen dake kallonta ya tab'e ɗan ƙaramin bakinsa tare da ɗauke kansa daga kallon nata, da sauri kuma ya juyo amma cikin basarwarshi yanda ba za a gane saurin nashi ba jin ta na magana cikin shagwab'a "Dan Allah da gaske kake Ya Sadik? Kar fa kasa na fito kuma ba ka zo ba." Sosai Ameen yake kallonta, Ƴar dariya ta yi sannan ta mik'e ta na faɗin "Gani nan to." Kallon Ameen ta yi ta ce "Yaya ina zuwa, bari in je in dawo." Ba ta jira amsarshi ba ta fara tafiya. Bin ta da kallo kawai ya yi cikin ransa ya na ƙissima abubuwa, har ta kai bakin k'ofa ya tsayar da ita ta hanyar faɗin...........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_












*1️⃣4️⃣*














........... Neehal duk da ta ga irin kallon da Hafsat ta mata amma ta danne zuciyarta ta rungume ta, sai dai jikinta ya yi sanyi ba kaɗan ba. Kamar yadda ta rungume Hafsat haka ta rungume Fadeelah. Fadeelah da ba ta ji daɗin abun da Hafsat ta yi ba ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Ai na yi fushi, tunda Aunty'nki kawai ki ka sani ita ki ka fara tarb'a." Neehal ta yi murmushin yaƙe ta ce "Sorry ai kema Auntyna ce." Fadeelah ta yi murmushi dan sosai ta ji ta na son Neehal, yarinyar ta burgeta daga gani ba ta da d'abi'ar wulak'anta mutane duk da kasancewar ta celebrity. Neehal ta ce "Mama ta na sama mu ƙarasa." Fadeelah ce kawai ta amsa mata suka mik'e suka bi bayanta, Hafsat sai hararar bayan Neehal take. Neehal ta shiga d'akin Mama ta sanar mata da isowarsu sannan ta fito ta wuce ɗakinta. Kafin Mama ta fito Fadeelah ta ce wa Hafsat "Haba Hafsah, gaskiya ban ji daɗin abun da ki ka yi wa yarinyar nan ba ko kaɗan wlh." Hafsat ta mata wani kallo ta ce "Yarinyar ba ta mun ba ne shi ya sa." Fadeelah ta ce "Hmmmmm, me yarinyar nan ta yi da za ki ce ba ta miki ba? Yarinya ta taho da murnarta da ɗokin ganin ki ka amma ki mata wannan wulak'ancin, gaskiya ban ji dad'i ba." Hafsat ta tab'e baki ba ta ce komai ba, domin ita kaɗai ta san baƙin cikin dake cin ranta na ganin Neehal, ashe duk kyawunta da mutane suke faɗa na ganin da suke mata a TV a fili tafi haka, yarinya ga dirin jiki kamar ita ta yi kanta, tafiyar ta ma kaɗai abun kallo ce ga zazzak'ar murya.... Fitowar Mama ya katse mata tunanin da take. Cikin girmamawa suka ɗan zamo daga kan kujerar da suke suna amsa sallamar da Mama ta musu. Mama ta zauna ta na faɗin "Sannun ku da zuwa." Suka amsa da yawwa tare da gaisheta, Mama ta amsa musu cikin fara'a ta ƙara da faɗin. Ya mutanen gida.?" "Suna lafiya, suna gaishe ku." Cewar Fadeelah. Mama ta ce "Masha Allah, muna amsawa." Hafsat dai kanta na ƙasa ta na satar kallon Mama, domin Maman kamar ba ta tsufa,

Please Login or Register in order to submit comment