Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya katse wani ya ƙara shigowa. Mama ta yi mata sallama. Mom bata bi ta kan sallamar ba ta ce. "Hajiya Fateemah kin aura wa ɗanki ƴarki ni kuma ya sakar mun tawa." Cikin shock Mama ta ce. "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, Ameen ɗin? Yaushe?" Mom ta ce. "Ki riƙe sallallaminki zai miki amfani wani lokacin ba'a nan ba, munafurcin banza munafurcin wofi, amma ki sani wallahi Ameen sai ya san ni ya wulaqanta." Ta ja tsaki sannan ta katse kiran. Aunty Jamila ta dube ta, ta ce. "Haba Yaya, ya zaki kira........" A zazafe Mom ta katse ta, ɗaga mata hannu ta yi ta ce. "Dahalla Jamila saurara mun, bana son wani dogon jawabinki na banza, ko dan ba ƴarki aka saka ba ne." Girgiza kai kawai Aunty Jamila ta yi. Mama kuwa bin wayar ta yi da kallo bayan ta katse, ta zauna a bakin gado tana jin zuciyarta babu daɗi sosai akan sakin Hafsah da Ameen ya yi, ba ta ji daɗin kalaman mahaifiyar Hafsah ba, amma duk da haka ta fi jin zafin sakin Hafsah da Ameen ya yi. Numbern sa ta lalubo ta yi dialing, komawarsa gida kenan ya tarar Neehal tana bacci a falo, da alama bata ma san lokacin da baccin ya ɗauke ta ba. Ya ɗaga wayar ya kara a kunne. Mama ta ce masa "Ameen where are you?" Ya ce. "Ina gida." Ta ce. "To ka zo yanzu ina son ganin ka." Ya ce. "Gani nan insha Allah." Ɗakinsa ya shiga ya yo alwala ya fito ya fice ba tare da ya tashi Neehal ba, tunda ya san ba Sallah zata yi ba.










Zaune yake a gaban Mama yana sauraren faɗan da take yi masa. Ta ce. "Ban ji daɗi ba ko kaɗan Ameen, gaskiya baka kyauta ba, duk tausar kan dana dinga yi jiya amma sai da ka aikata wannan d'anyen aikin? Bana son ka kasance cikin mazan da dan sun samu wata matar su rabu da wadda suke tare da ita." Cikin ladabi ya ce. "Mum ba haka ba ne kema kin sani, dan na samu Neehal haka kawai bazan rabu da Hafsah ba, halinta ne ya janyo mata. Kuma ina son hakan ya zama kamar jan kunne a gare ta. Mama ta sauke numfashi ta ce. "Saki nawa ka yi mata?" A hankali ya ce. "Ɗaya ne." Mama ta ce. "Shikenan, Allah ya dai-daita ku, ya kiyaye faruwar hakan a gaba." Ya amsa da Amin sannan ya tashi ya yi mata sallama ya tafi. Har kusan isha'i su Hafsat suna falo, mahaifiyarta na faman kumfar baki Aunty Safiyya data zo gidan tana taya ta, Hafsat kuma tana ta aikin kuka. Ko sallar Magriba ba su yi ba, ba su ma da niyyar yi, Aunty Jamila ce kawai ta yi. A haka mahaifin Hafsah ya shigo ya same su, ya zauna tare da tambayar ba'asi. Mom ta kora masa bayani, ta ƙara da faɗin. "Yanzu Alhaji sai ka san matakin da zaka ɗauka ga Ameen da iyayensa na wulaqanta maka ƴa da suka yi." Dad ya haɗe rai ya ce. "Hafsah 'yata ce wadda nake k'aunarta kamar raina, bana jin bayan iyayena akwai abun da nake so a duniyar nan sama da ita. Na san halinta na san abun da zata yi, haka na san mijinta Ameen yaron kirki ne shi da iyayensa, ya samu ingantacciyar tarbiyyar da nake da tabbacin bai saki Hafsat haka kawai ba tare da wani dalili ba, face ta yi masa wani abun. Dan haka i will never blame him akan abun da ya yi, balle har na ɗauki wani mataki kuma ban bawa kowa ikon ɗauka ba. Ban da ma hauka daga mutum ya saki mace sai a ce za'a ɗauki mataki a kansa? Duk matan duniya da ake sakin su fa? Ko ma ba haka Ameen ya wuce matakin da za'a ce za'a ɗauki wani mataki a kansa, irin matakin da kuke nufi na a wulaqanta shi ko something like that." Ya nuna Mun da hannu ya ce. "Wannan ya ishe ki ishara, a da idan ina faɗa miki ɓata Hafsah kike yi ba gata kike yi mata ba sai kina ganin kamar k'arya ne, yau gashi nan ta yi aure Mijinta ya kasa ɗaukar halayenta ya sako ta. Ba fina son ta kika yi ba Amina, kuma nima ina nuna mata gata dai-dai gwargwado, amma ba irin naki ba, naki ya yi yawa. Kasancewar ni ba mazauni ba ne kullum ina tafe neman halak ɗina shi yasa tarbiyyar da kika yiwa Hafsah ta fi tasiri a gare ta akan tawa. Amma yanzu tunda ta dawo gidan, zan yi iya yina wajen ganin na gyara rayuwarta, duk da an ce ice tun yana d'anye ake iya tank'wara shi." Ya mayar da kallonsa ga Aunty Jamila ya ce. "Idan zaki tafi gidanki ki tafi da Hafsan ta yi zaman iddarta a can, domin ki koya mata ilimin zaman duniya da kuma yanda zata samu lahirarta, da rayuwar zaman Aure da haqqokinsa dan ganin ta gina rayuwarta ko dan gaba. Sannan kuma duk lokacin da Ameen ya zo domin mayar da ita ɗakinsa zan yi masa maraba in kuma bashi ita." Yana gama faɗin hakan ya miƙe ya nufi sashensa. Gaba-d'aya suka bi shi da kallo baki a sake, Aunty Jamila ce kawai ta ji daɗin maganganunsa ta kuma yaba masa. Mom ta saka kuka tare da surutan shiga tsakaninsu aka yi da Daddyn Hafsah, amma da ba zai faɗi haka ba. Bayan Daddy ya dawo gida Mama ta sanar masa da abun da ya faru, ya ji ba daɗi shi ma amma ya ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi.














Sai bayan isha'i Ameen ya koma gida, ya tarar da Neehal ta shirya tana jiransa ya zo su fita, kamar yadda ya ce zasu je gidan wani abokinsa. Wanka ya yi sharp_sharp ya shirya suka tafi. Satin nan da aka shiga gaba-d'aya kullum sai sun fita bayan Magriba, ya kai ta gidan wani daga cikin abokansa daga nan su biya su sha ice-cream cikin soyayya da k'aunar junansu. Ameen ya manta da Hafsat da babinta a cikin ransa, kula da tarairayar Matarsa kawai ya saka a gaba. Neehal tana son ta ji inda aka kwana a zancen komen Hafsah amma tana jin tsoron ta tambaye shi, tunda ya ce karta ƙara yi masa maganar data danganci Hafsah. Ranar yana bacci suka yi waya da Aunty Sadiya take sanar mata Ameen ya saki Hafsah, yanda sakin ya daki zuciyar Neehal ba zai misaltu ba, har hawaye sai da ta yi, ta ji a ranta Ameen bai kyauta ba. Suna gama waya da Aunty Sadiya ta kira Mama ta dinga roqon ta akan ta saka Ameen ya dawo da Hafsah. Mama ta ce mata, ita ma burinta da fatanta kenan, bari ta yi Ameen ɗin ya gana hucewa sai a san abin yi. Ranar Ameen kasa gane kanta ya yi, ta ƙi kula shi ta dinga yi masa k'unci. Ya rarrashe ta ya lallab'a ta amma duk a banza, sai haqura ya yi ya k'yale ta, daga baya kuma da karan kanta ta saki ranta suka koma normal.
















Yau Monday wanda ya kama kwana goma sha bakwai da Auran Neehal da Ameen. Da safe yana shiryawa zai tafi aiki da yake hutun 2 weeks aka bashi. Neehal tana tsaye tana kallon sa ta yi kalar tausayi da fuskarta kamar zata yi kuka. Ya ƙarasa saka talalmin ƙafarsa sannan ya ɗago ya kalle ta. Hannunsa ya miƙa mata ta ɗora nata akai a hankali. Ya riƙe hannun tare da janyo ta jikinsa ya zaunar da ita akan cinyarsa ya ce. "Mene ne." Ta ɓata fuska ta ce. "Ni bana son ka fita." Shafa bayanta ya shiga yi a hankali ya ce. "Ki yi haquri Baby, bazan dad'e ba fa zan dawo." Ta ce. "Ai na san baza ka dawo da wurin ba." Ganin tana shiri fara hawaye ya ce. "To ko in tafi dake ne?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya yi murmushi sannan ya sauke ta ya miƙe. Tun jiya da yake shirye-shiryen zuwa aiki yau take haka, jikinta gaba-d'aya ya yi sanyi, a yanda take jin sa yanzu a cikin zuciyarta bata k'aunar abun da zai rabata da shi ko na awa ɗaya ne balle na awanni. Ya ɗauki briefcase ɗinsa suka fita ta yi masa rakiya zuwa bakin ƙofar parlour. Ya ɗan tsaya yana kallon ta sannan ya kama fuskarta da hannunsa ya ce. "I will miss you Darling." Ƙasa ta yi da kanta bata ce komai ba. Rungume ta ya yi ya ce. "Please Baby ki saki ranki, idan na tafi kina haka ai babu abun da zan iya ko na je gurin aikin, ko kuma in zauna in fasa zuwa ne?" Ta girgiza masa kai tare da d'agowa ta yi masa murmushi ta ce. "Ka je Yayana, ya za'ai ka ƙi zuwa aiki? Allah ya kiyaye hanya ya kare mun kai." Murmurshin ya yi shi ma ya ce. "Amin, thank you so much dear, ko ke fa, harna ji daɗi." Ta bar jikinsa ta ce. "Ka tafi kar ka yi late." Ya ce. "Shikenan Baby, karfa ki damar mun kanki ki yi ta tunani, ina ƙarasawa office zan kira ki." Ta ce. "Insha Allah Yaya, Allah ya kaika lafiya." Ya ce. "Amin." Sannan ya yi mata pick a kuncinta ya fice tana ɗaga masa hannu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin Ameen da Neehal cikin kwanciyar hankali da farinciki da tattali gami da kula da juna. Duk wanda ya zo gidansu sai sun burge shi sun ba shi sha'awa, zamansu gwanin sha'awa. Bayan sati biyu ita ma Neehal hutunta ya ƙare na gurin aiki da yake wata ɗaya aka bata. Ameen ya ce bai san zancen ba baza ta koma wani aiki ba, aikin ma na Jarida na gidan TV wanda ya dace da wanda bai dace ba ya kalle masa mata. Neehal har da Kukanta dan tana matuƙar k'aunar aikinta amma ya yi biris ya ƙi yarda, sai da ta kira Mama ta faɗa mata sannan ita kuma ta kira shi ta yi masa magana akan hakan, dole ba don son ransa ya yarda ta koma aikin, amma ta sha sharad'ai da dokoki, duk da yawan hijaban lefenta haka ya ƙara jibgo mata wasu dogaye har ƙasa da socks na ƙafa ya ce da su zata na fita. Ita dariya ma ya bata dan ita ma tafi son tana saka hijabin akan mayafi. Ranar data koma bayan ta dawo ya tasa ta a gaba da mita kamar zai yi kuka, wai ta yi kyau sosai da ya kalli labaran data gabatar, yanzu ya san wasu ma da suka kalla sun yaba kyawunta. Rarrashinsa ta yi da abun da ta son yana matuƙar so, da haka ta samu ya bar yi mata mitar. Bayan wata ɗaya wanda ya kama wata biyu da Auransu suka je Gombe aka sha shagalin bikin Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud. Duk wanda ya ga Neehal a bikin sai ya tanka kyawun da ta yi da irin canzawar da ta yi. Ta ƙara haske da ƙiba abun ta. Hajiya sai faman nan_nan take da ita tana cewa ciki gare ta, ita kuma sai ta ɓata fuska ta ce bata da komai ita. Ana shagalin biki amma suna manne da Ameen kodayaushe a waya. Har tsokanarta ake yi ana ce mata Cingam ne ita da shi. Daf da za su je bikin Ahmad ya kawo mata twins sun yi mata kwana biyu. A bikin ne labarin mutuwar Hafsat ya bazu a dangin su Mama, sakamakon rashin zuwanta bikin, daga masu cewa Allah ya raka taki gona sai masu cewa Allah yasa haka shi Alkhairi.












Bayan sun dawo daga Gomben sai zancen Hajiya ya zamto gaskiya, dan tunda suka dawo Neehal bata da aiki sai bacci, sai ta ɗora girki tana shiga d'aki ko ba da niyyar bacci ba sai ta kwanta ta yi bacci. Ga shegen kwad'ayi da ƙin cin abinci, ita dai ta wuni tana taunar abu a bakinta shine kwanciyar hankali. Daga ita har Ameen ba su gane ciki ne da ita ba, saboda bata laulayi kwata_kwata, ciye_ciye ne kawai da Bacci. Shi Ameen ya ɗauka zirga-zirgar zuwa gurin aiki ne take sanya mata gajiya take wannan baccin, ciye_ciye kuma dama ya san gwana ce ita a wannan fannin duk da na yanzu ya yi yawa, amma duk da haka bai kawo komai a ransa ba..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*
















_By_
_Zeey Kumurya_












*8️⃣9️⃣*














*ELEGANT ONLINE WRITER'S*












..........Yau ya kama weekend, ranar Sunday da rana Ameen yana parlour yana operating laptop, Neehal kuma tana d'aki tana aikin bacci. A hankali ta buɗe idonta dake cike da bacci, baccin bai ishe ta ba yunwace ta tashe ta. Miƙewa ta yi ta shiga toilet ta wanke bakinta tare da d'auraye fuskarta ta fito. Ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali ta lek'a kamar mara gaskiya, ganin Ameen zaune akan kujera yana aiki sai ta saki ajiyar zuciya ta mayar da ƙofar ta rufe ta koma ciki. Wardrobe ɗinta ta buɗe ta lalubo choculates ɗinta a inda ta b'oye su ta zauna a ƙasa ta fara sha tana lumshe idanu saboda daɗin dake ratsa ta. Sauri take yi ta yi ta shanye kar Ameen ya shigo ya gan ta, dan ya hana ta shan zaƙi saboda yanda ta mayar da su sweets abincinta, ba dare ba rana a ƴan kwanakin nan. Shi yasa ta koma sha a b'oye, kullum idan ta je gurin aiki sai ta bayar an siyo mata da yawa sai ta zo ta b'oye in ba ya gidan ta yi ta shan abin ta. Sai da choculate ɗin ta ishe ta sannan ta mayar da sauran ma'ajiyarta ta goge bakinta da tissue ta fita parlour.












Tunda ta fito ya ji ƙamshinta ya ɗago yake kallon ta, a gefensa ta tsaya tare da shagwab'e fuska. Ya saka hannunsa ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa. Ajiyar zuciya suka sauke a tare. Ya shafa fuskarta ya ce. "Har kin tashi daga baccin?" Gyaɗa masa kai ta yi. Ya ce. "Mene ne kuma ya faru Babyn Yaya?" Ta saka hannayenta ta zagaye bayansa ta ce. "Masara nake son ci dafaffiya." Ya ce. "Masara kuma Baby? a ina za'a samo ta?" Kamar zata yi kuka ta ce. "Koma a ina ne, ni dai ita nake son ci." Ajiyar zuciya ya sauke tare girgiza kai ya ce. "Bari na kira a kawo miki." Ta ce. "A'a ni dai ka je da kanka, ka taho mun da gyaɗa mai gishiri da kwakumeti." Tsayawa kawai ya yi yana kallon ta, ta fara yi masa shagwab'a. Ya rungume ta ya ce. "Yanzu dai kin ga aiki nake yi Baby ba sai na fita ba, ki bari na bayar a siyo miki, ni duk waɗan nan abubuwan ma ban san inda zan samo miki su ba." Ta ce. "Ni na sani mu je tare." Zai kuma magana ta fara yunk'urin kuka. Ya ce. "Shikenan bari na ɗan ƙarasa wani abu sai mu je." Ta turo baki alamun ba haka taso ba amma bata yi magana ba. A hankali ya kai hannu ya shafi cikinta ya ce. "Rigimarki da kwad'ayin da kika koya yanzu da yawan bacci ina tunanin fa na yi ajiya ne." Ta tura hannunsa bata ce komai ba ta lumshe idonta. Ya shafi saman idon yana murmushi, yana fatan a ce hasashen ya zama gaskiya. Kafin ya gama abun da ya ce zai ƙarasa har ta yi bacci a jikinsa. Bayan ya gama ya tashe ta dan su je su siyo abubuwan da ta ce, ɓata fuska ta yi ta ce. "Mafarki fa nake yi Yaya ina cin masarata ka tashe ni." Ya ce. "I'm sorry, yanzu ai zamu je mu siyo ki ci a reality ba'a mafarki ba."








Ga mamakin Ameen ta san ko ina da ake siyar da abubuwan data lissafa, suka je ya siya mata har da ƙarawa da wasu abubuwan. Sai da ya biya ta restaurant ya siyi abincin da zai ci, duk da ta ce masa zata iya girki idan sun koma gida, ya ce mata ya hutashshe ta, dan ya san girkin nan daƙyar zai yiyu. A daren yau kuma sai jikinta ya yi zafi zazzaɓi ya rufe ta, ko baccin kirki ba su yi ba. Washegari da sassafe kuwa suka shirya sai asibiti, dan ya ce ya kai ta gurin Mama ta ƙi yarda. Bayan an yi mata gwaje_gwaje da test aka tabbatar tana da shigar ciki na 7 weeks. Murnar da Ameen ya nuna ba zata faɗu ba, ya yi sujjada tare da yin godiya ga Ubangiji. Neehal kuwa sai kunya amma ita ma a cikin ranta farin ciki ne fal. Bayan sun dawo daga asibitin ya kwantar da ita akan gado ya ce. "Ki kwanta ki huta Baby zan je in yi gyaran gida, ko me kike so ki kira ni in miki karki wahalar mun da kanki da Small Babyna." Ta shafa sumar kansa ta ce. "Aikin fa? Baza ka je ba?" Ya ce. "Baki da lafiya ina na ga ta zuwa aiki Baby." Ta ce. "Na warware fa, zan iya yin komai." Ya ce. "No, ko toilet zaki shiga just call me in zo in ɗauke ki in kaiki, kar ki yi tafiya ki wahala." Ta yi murmushi kawai. Ya yi kissing goshinta da cikinta sannan ya fita. Yana fita ta miƙe ta je ta tsaya a gaban mudubi ta ɗaga rigar jikinta tana kallon cikin, murmurshin farinciki ɗauke akan fuskarta. Jin abun take kamar a mafarki, ita ce da ciki very soon da yardar Allah she will be come a Mother. A haka Ameen ya shigo ya same ta, cikin tsokana ya ce. "Wasa kike masa ne?" Saurin rufe cikin ta yi ta rufe fuskarta da hannunta. Ya ƙaraso ya rungume ta yana dariya ƙasa_ƙasa. B'oye fuskarta ta yi a ƙirjinsa tana murmushi. Ya jata suka faɗa kan gado ya ce. "Bari na duba lafiyar Babyn." Ya fara ƙoƙarin cire mata riga. Ta marairaice ta ce. "Bani da lafiya fa." Shi ma marairaicewar ya yi ya ce. "Nima haka." Ta ja karan hancinsa da ƙarfi bata ce komai ba........ Sosai Ameen yake kula da tattalin Neehal, dan sai yanzu kuma ta fara laulayi, idan ta ci abun da bai yi mata ko ta shak'i ƙamshinsa sai amai, ga zazzaɓi daren da take kwana da shi kullum. Kwad'ayi kuwa da bacci sai abun da ya yi gaba, shi yasa duk abun da Ameen ya gani a hanya ko bata ce masa tana so ba sai ya siyo mata, wani ta ci wani ta ƙi ci. A haka take lallab'awa take zuwa aiki, duk da ya hana ta ya ce ta ɗauki hutu ta ce masa ita bata son zaman gidan, ta fi son tana fita tunda ba wani jin jiki take sosai ba. Amma idan ta je gurin aikin ba wani abun arzik'i take yi ba rabi da rabi bacci ne, a yi ta tsokanar ta kuwa a gurin aikin, sai dai ta yi murmushi kawai cikin jin kunya. Ta ƙi barin Ameen ya faɗawa su Mama tana da ciki, wai ita kunya take ji. Ya yi dariya ya ce. "Indai Mum ce gani ɗaya zata yi miki ta gane, kin sani ke ma." Jin haka sai ta ƙi zuwa gidan Maman, sai dai kullum cikin faɗar tana son ganin Maman take, idan suka yi waya tay ta yi mata mitar ta ƙi zuwa gidanta. Ranar wata Sunday Daddy ya cewa Mama ta shirya ta je ta gano Neehal ɗin ta ga gidanta tunda bata taɓa zuwa ba. Ai kuwa ranar Neehal murna kamar me, ta shiga kitchen ta yiwa Mama abubuwa na tarb'ar ta. Sai yamma Maman ta je gidan. Neehal ta tafi da gudu ta rungume ta, Ameen ya bi ta da wani kallo data san ko na mene ne, juya masa ido ta yi tana murmushi. Mama ta zauna suka gaggaisa tana bin Neehal da ido, Neehal ta tashi ta je ta kawo mata abinci da drinks. Mama dai kallon ta kawai take yi tana noticing ɗinta, ta lura da yanda take yin komai a sanyaye da kuma yanda jikinta ya d'ashe ta yi wani irin haske. Ta yi sarving Mama ta koma kusa da ita ta zauna tana ta yi mata hira. Can ta kalli Ameen ta turo baki ta ce. "Mamana ta zo shine baza ka ba mu guri mu yi sirri ba?" Harararta ya yi bai ce komai ba. Ta kwanta a jikin Mama tana ɓata fuska. Kafin Mama ta tafi ta shiga ɗaki dan yin fitsari, bayan ta yi fitsarin ta fito daga toilet sai ta kwanta akan gado, duk yanda ta so daurewa kar ta yi bacci amma ina baccin ya ce bai san wannan zancen ba, saboda rabon ta da yi tun safe, tana kitchen tana ta aiki. Mama ganin shida saura ta yi ta dubi Ameen ta ce. "Ina Neehal ɗin ne? Tafiya zan yi fa." Ya ce. "Tun yanzu?" Mama ta ce. "Tunda na zo na gan ku mai zan zauna yi kuma." Ya miƙe ya shiga ɗakin Neehal, mamaki ne ya kama shi ganin ta kwance tana baccinta hankali kwance. Ya juya ya fita ya ce wa Mama. "Kin ga Mum daga shigar ta har bacci ya ɗauke ta." Mama ta ce. "Bacci kuma?" Ya gyaɗa mata kai. Tashi Mama ta yi ta shiga ɗakin ta zauna a gefen Neehal, tafin hannunta ta kama ta dudduba sannan ta kalli Ameen dake tsaye a bakin ƙofa ta ce. "Wani abu yana damunta ne ko ta yi rashin lafiya?" Ameen ya ce. "Tana yin zazzaɓin dare dai, amma yanzu da sauƙi tana shan magani." Mama ta ce. "Kun je asibiti?" Ya ce. "Eh." Mama ta ce. "Me aka ce yana damunta?" Ya shafa gashin kansa tare da yin ƙasa da kansa ya ce. "She is pregnant." Mama ta mayar da kallon ta ga Neehal cikin tsananin farin ciki ta shafi fuskarta ta ce. "Allah ya sauke ki lafiya Daughter, ya baku lafiya ke da unborn." Can ƙasan mak'oshi Ameen ya amsa da Amin. Dama Mama tun zuwansu Gombe data ga yanayin Neehal ɗin ta fuskanta. Ta miƙe ta fita Ameen ya bi bayanta dan yi mata rakiya, suna tafe tana ƙara faɗa masa yanda zai kula da Neehal da abubuwan da zata yi da wanda baza ta yi ba, tana kuma tambayar sa abubuwan da Neehal ɗin take yi. Sai daf da Magriba Neehal ta tashi, ta dinga yiwa Ameen mita akan ƙin tashinta da ya yi da Mama zata tafi, shi dai bai ce mata komai ba har ta gaji ta haqura, kiran Maman ta yi ta ji ya ta koma gida, Mama ta sanar mata lafiya ƙalau, sannan ta faffaɗa mata addu'oin da zata dinga yi a matsayinta na mai juna biyu, cikin jin kunya take amsa mata. Suna gama wayar ta juyo zata yiwa Ameen complain ya yi saurin cewa. "Bani na faɗa mata ba, ita ta gane da kanta, ai dama na faɗa miki." Ta yi murmushi kawai a ranta tana hasaso irin farin cikin da Mama ta yi da ta ji labarin cikin. Bata ƙara nutsewa da jin kunya ba sai da Daddy ya kira ta ya yi mata ya jiki, dan ta san definitely Mama ta sanar masa da batun cikin jikinta.












A ɓangaren Hafsah kuwa kamar yadda Dad ɗinta ya faɗa a ranar ta bi Aunty Jamila zuwa gidanta tana gunjin kuka. Saboda kuka da damuwar data saka kanta a ciki har jinyar kwana biyu ta kwanta. Bayan ta warware Aunty Jamila ta fara koyar da ita abubuwa kamar yadda Dad ya buƙata daga gare ta, da farko bata mayar da hankali akan abubuwan ba sai dai ta zauna ta yi ta koke_koke da tunane_tunane. Daga baya cikin dabara Aunty Jamila ta ce mata idan bata gyara dabi'unta ta koyi zaman rayuwar duniya ba babu ta yanda za'a yi Ameen ya mayar da ita, sannan ta fara mayar da hankali. Ta kan addini Aunty Jamila ta fara yi mata dan sai ya gyaru sauran abubuwan za su gyaru. Wata yarinya ƴar mak'otansu Aunty Jamila ta ɗauko take yiwa Hafsan karatun addini, za su yi ƙarin

Please Login or Register in order to submit comment