Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Ayya, ai ban sani ba sisina, mu je na baki abinci ki ci" Neehal zata yi magana wayarta dake hannunta ta hau vibrate, ta duba tare da d'agawa ganin Mama ce. Mama ta ce "Kin je gidan Ameen ɗin." Neehal ta ce "Ehh." Mama ta ce "Ya jikin nasa." Ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Is he sleeping?" Neehal ta ce "A'a, idonsa biyu yana ma zaune." Mama ta ce "Okay, bashi wayar." Neehal ta miƙa masa ba tare da ta yi magana ba, ya karb'a tare da kara wayar a kunnensa, ko da ba'a faɗa masa ba ya san Mama ce. Gaisawa suka yi, Mama ya masa ya jiki? Sannan ya bawa Neehal wayar. Ameen ya dubi Hafsah wadda ke kallonsa ya ce "Ina kika ajiye mun my phone's? Mum said ta kira ni ban yi picking ba." Hafsah ta ce ,"Suna Bedroom dina, bari na ɗauko maka." Sai kuma ta marairaice fuska ta dafa kafaɗunsa tare da faɗin "Babyna duk ka rame, ciwon nan yana wahalar mun da kai, nice mai cikin amma kai ne da laulayin." Neehal ta ɗan tab'e baki tare da fita daga ɗakin. Ameen bai cewa Hafsah komai ba, sai idanunsa da ya mayar ya lumshe. Neehal ta fito falo ta zauna ta ɗauko wayarta ta shiga latsawa, su Fadeelah kuwa sai hirarsu suke. Hafsah ta fito ta shiga bedroom ɗinta ta ɗauko wayoyin Ameen ta kai masa, sannan ta fito ta zauna kusa da k'awayenta ba ta ko kalli inda Neehal take ba. Fadeelah ce ma take ɗan sako ta a cikin hirar tasu, ita kuma sai dai ta yi murmushi kawai. Ganin Magriba ta kusa ta miƙe ta dube su ta ce "Aunty Hafsah zan wuce Allah ya ƙara sauƙi." Bata jira amsarta ba ta mai da dubanta ga su Fadeelah tana murmushi ta ce "Sai anjimanku." Fadeelah ta ce "Har zaki tafi Neehal? To ki gai da gida da Mama." Neehal ta ce "Mama zata ji." Sannan ta juya ta fice daga falon. Hafsah ta bita da harara tare da jan dogon tsaki bayan ta fita. Fadeelah ta kalle ta ba ta ce komai ba, a ranta tana mamakin wannan hali na ƙawartata. Neehal tana koma wa gida Mama ta kalle ta, ta ce "Kuka kika yi ko Neehal?" Neehal ta yi shiru, Mama ta ce "Allah ya shirye ki, ya jikin nasa?" Kamar zata kuma wani kukan ta ce "Da sauqi, amma Mama daga gani Yaya yana jin jiki sosai, duk ya rame." Mama ta ce "Ki masa addu'a, ba kuka ba." Ganin idanunta har sun fara ƙyallin k'walla. Da daddare Sadik ya zo suka sha zancensu, sun daɗe suna hira wanda kusan gaba-ɗaya hirar a kan bikin Haneefah suka yi ta. Lokacin da Sadik ya koma gida kamar kodayaushe idan mahaifinsu yana gari, iyayensa duka suna zaune a main Parlour, sai dai yau babu k'annensa. Ya shigo da sallama kan sa a ƙasa, suka amsa masa baki ɗaya. Umma ta ce "Um su Sadik yanzu kullum sai an je zancen ne?" Ran Maamah ya ɓaci amma ba ta ce komai ba. Abbansa ya ce "Idan ya je zance laifi ne?" Cikin kissarta da son ɓata Sadik ɗin a idon mahaifinsa ta ce "Ba laifi ba ne Abbansu, kawai dai na ga ya kamata a san inda yake zuwa zancen ne, domin a tabbatar da tarbiyyar yarinyar." Abba ya kalli Sadik dake tsugunne ya ce "A ina gidansu yarinyar da kake zuwa yake?" Cikin ladabi Sadik ya ce "A Nasarawa gidansu yake, sunan mahaifinta Alh. Muhammad Tafida." Abba ya maimaita sunan kamar mai son tuno wani abu "Alh. Muhammad TAFIDA? kamar na san sunan nan, amma dai zan bincika, dan kamar Yadda Ummanku ta faɗa ya kamata mu san inda kake zuwa ɗin, idan gidansu yarinyar gidan tarbiyya ne sai ka cigaba da zuwa, idan kuma akasin haka ne kasan sauran." Ya ƙarashe zancen yana kallon Sadik. Sadik ya gyaɗa masa kai zuciyarsa babu fargabar komai, dan yasan babu wani abu bad da za a samu a gurin Neehal ko iyayenta Insha Allahu.










Washegari da safe sai ga Hajiya ta zo wai ta zo duba Ameen ne. Neehal tana bacci ta ji Maganar Hajiya a kanta. A hankali ta buɗe idanunta dake cike da bacci, cikin muryar bacci ta ce "Kai tsohuwar nan baza ki bar mutum ya yi ƙiba ba, daga zuwanki ina baccina mai daɗi kin katse mini." Hajiya ta ce "Wanne irin baccin asara ne wannan har tsakar rana? Yaushe Faɗiman ta lalace har ta barki kike irin wannan baccin? Haka zaki je gidan mijin kina sakin baki kina sharar bacci." Neehal ta tashi zaune tana ƴar miƙa tare da yin salati. Hajiya ta ce "Ni ki yi ki tashi ki shirya ki raka ni gidan Aminu yaron kirki irin albarka in dubo sa, duk da ma sai jiya Uwartasa ta faɗa mun rashin lafiyar tasa, ban da haka da tuni ban zo ba." Neehal ta kalli agogon dake bangon ɗakin ta ce "Taɓ, sai dai direban Mama ya kai ki, ni school zan tafi yanzu ina da exam 12." Bata bi takan mitar Hajiya ba ta tashi ta shige toilet. Tana fitowa ta ga wayarta dake kan gado tana haske, ta ɗauka ta ga Ameen ne yake kiranta. Ta d'aga da sallama a bakinta, Al'ameen ya amsa mata. Ta ce "Ina kwana Yaya, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauqi, me yasa jiya kika taho baki mun sallama ba?" Ta ce "I thought ka yi bacci ne lokacin." Ya ce "Ko dai kina sauri ki tafi saboda saurayinki zai zo?" Neehal ta ce "Allah ba haka ba ne Yaya" ya ce "Amma ai yazo ɗin ko?" Neehal ta yi shiru tana murmushi ƙasa ƙasa, ya ce "Uhm, to me yasa yau baki kira ni kin ji lafiyata ba?" Sai ta ji abun wani iri, ita da tun yana gida ma basa wata waya balle yanzu da ya yi aure, ko yana nufin dan bashi da lafiya ne bata kira ta ji jikin nashi ba? ta ce "Yanzu na tashi daga barci ne am sorry" Ya ce "Alright, i will call you later" Daga haka ya kashe wayar. Ta bi wayar da kallo kamar zata gan shi a ciki, daga baya kuma ta ajiye ta cigaba da sabgarta.








Hajiya tana duban Mama bayan ta gama rattabo mata yanda suka yi da Neehal ta ce "Wai niko Faɗima har yanzu yaran nan shiru babu labarin wani nasu?" Mama ta ce "Babu Hajiya har yanzu, tun muna zuba idon ganin kira har mun gaji." Hajiya ta ce "Ikon Allah, to ko dai ba ƴan ƙasar nan ba ne?" Mama ta ce "Waya sani ne, sai Allah." Hajiya ta ce "Allah ya kyauta, suna inane ma ban gansu ba." Mama ta ce "Suna makaranta, sai yamma suke dawowa." Hajiya ta ce "Allah sarki Janar, Allah ya saka masa da Alkhairi, shi da ba ya gajiya da aikin Allah"








Har Neehal ta shirya ta fito Hajiya bata tafi gidan Ameen, Mama ta tsayar da ita, ta ce idan ta gama girki sai ta raka ta da kanta. Tana falon ƙasa tana kallo, da Neehal zata wuce ta ce "Au baki tafi gidan Yayan ba?" Hajiya ta ce "Ban sani ba, tunda baza ki raka ni ba meye naki na tambayata na je ko ban je ba?" Neehal ta ce "Allah ya baki haquri, amma dai zaki zaunar mana har bikin Besty ko?" Hajiya ta ce "Gobe goben nan zan koma inda na fito, dubiya ce ta kawo ni dama." Neehal ta ce "Kai Hajiyarmu ki zauna ki yi babbar Sallah a nan." Hajiya ta ce "Um'um, in zauna ku ce na cinye muku nama, gidana zan tafi in yi sallah ta a can." Neehal ta ce "Tom Shikenan, Ni na wuce school." Hajiya ta ce "Allah ya tsare." Washegari kuwa kamar yadda Hajiya ta faɗa ta koma Gombe, ko gidansu Aunty Sadiya ba ta je ba sai su suka zo gidan Maman suka gan ta. Babbar Sallah saura kwana Biyar aka kawo lefen Haneefah, Masha Allah kaya sun yi kyau, Faruq ya yi ƙoƙari sosai, kaya masu tsada ya zuba mata, akwati goma ya mata cike taf da kaya. Ranar Haneefah ta sha tsokana gurin Neehal, tun tana biye mata tana ramawa har jikinta ya fara yin sanyi ta yi shiru. Ana i gobe Sallah mai ƙunshi ta zo har gida ta yiwa Mama da su Afrah, Neehal dai ba ta yi ba saboda kar ya ƙi fita kafin bikin Haneefah. An yi bukukuwan Sallah lafiya an gama Lafiya, Neehal kam babu inda ta je saboda aikin nama, gashi hutun school kwana uku ne kacal, dan ran huɗu ga Sallah ma tana da exam. Kuma ta so wannan Sallar ta zazzaga danginta, duk da basa nemanta amma ita baza ta biye ta su ba, kamar yadda Mama take faɗa mata a kodayaushe, Ta yi zumuncinta dan Allah ba dan su ba, shi zumunci dole ne. Ranar Asabar ɗin data kama saura kwana huɗu a fara bikin Haneefah su Neehal suka gama exam, hakan yasa ta kama hidimar bikin ƙawarta gadan_gadan. Ranar Thursday akai bridal shower, Amarya ta yi kyau sosai ita da k'awayenta, an yanka Cake an cashe. Ranar Friday kuma Kamu, shima Ranar Amarya ta yi kyau har tafi jiya ma. Su Neehal ƙirjin biki an cashe sosai, dan ma Sadik yana hana ta rawar gaban hantsi duk inda ta yi yana biye da ita, wai dan kar wani ya kula ta. Ranar Asabar kuma akai Mother's Day da yamma, da daddare kuma akai Dinner. Tunda aka fara bikin Ameen bai je ba sai ranar Dinner suka je shi da Hafsah. Aiko ranar Neehal ta ga takura, dan hana ta sakat ya yi. Tana shiga filin rawa zata hango idanunsa yana banka mata harara, ga shi ita ma kamar an mata asiri sai tay ta kallon inda yake. Ƙarshe ma tashi yay ya ja hannunta ya fara mata masifar wai tana ganin Maza a gurin amma sai Safa da Marwa take, gashi kayan jikinta sun kama ta. Allah ya taimake ta ranar Sadik bai zo ba, da bata san a gurin wa zata fi shan takura ba tsakanin shi da Ameen. Hafsah kuwa bata ma san me ake yi ba, tana can tana bawa idanta abinci, da Ameen ya tashi ma ta ɗauka waya ya tafi yi. Wata cousin ɗin su Haneefah ta cewa Neehal "Kai amma guy ɗin nan naki ya haɗu, kuma daga gani yana sonki sosai, gashi kun dace." Neehal ta yi murmushi tace mata "Yayana ne fa, kin ga matarsa can a gefensa." Yarinyar ta jinjina kai kawai, amma ita ta hango tsantsar kishin Neehal a tattare da Ameen. Washegari Ranar Lahadi da misalin ƙarfe Sha ɗaya na rana aka ɗaura Auran Haneefah da Angonta Umar Faruq. Tun lokacin ta fara kuka saboda tsokanarta da abokan wasa suka fara yi, jikinta ya yi sanyi duk rawar kan nan babu. Neehal ta ce "Ashe zan ga ranar da bakin tsiwar nan zai mutu." Duk da itama jikinta ya yi sanyi dauriya kawai take. Ranar kiɗan ƙwarya aka sha a cikin gida. Kafin Magriba ƴan ɗaukar Amarya sun zo, a lokacin kukan Haneefah ya tsananta kamar zata shid'e, Neehal ma tuni ta fara kuka. Mommy ma duk yadda taso daurewa amma sai da ta yi Hawaye da za'a fita da ƴartata tilo ɗaya a duniya. Sadik ne ya kai su Neehal gidan Amarya ita da wasu k'awayen Haneefah guda biyu, sai Ameerah ƴar Uncle Mahmud da ta zo bikin itama. A lokacin Neehal ta yi ƙoƙari ta daina kukan, amma kana ganinta ka san tana cikin bad mood, Suna Mota Sadik yana mata magana ma bata responding, ta kwantar da kanta a jikin kujera idanunta a lumshe. Sai da su Afrah dake kan cinyarta yake hirar. Sune na ƙarshen barin gidan Amarya, a haka ma da dabara suka fito saboda Haneefah riƙe Neehal ta yi wai ba za su tafi ba. Gidan Amarya ya yi kyau Masha Allah, Mommy da dangin Abban Haneefah sun mata kaya na ƴaƴan gata, komai ya ji Masha Allah. Sai fatan Allah yasa gidan zamanta ne na har abada, ya kuma ba su zaman lafiya ya kau da fitina a tsakaninsu. Da wani irin ciwon kai Neehal ta dawo gida, sallah kawai ta yi ta bi lafiyar gado, ba jimawa bacci ya ɗauke ta saboda tarin gajiyar dake addabar jikinta.












Yau Laraba misalin ƙarfe huɗu da mintuna Neehal ce zaune akan darduma, ta idar da sallar la'asar. Tunanin besty'nta da ta yi kewarta take yi, tana tuna yanda suke yin komai tare, idan ɗaya zata unguwa sai ta kira ɗaya ta raka ta, idan yau wannan bata zo ba gobe sai wannan sai ta zo, su je gurin aiki tare su dawo tare. Yanzu gashi aure ya raba su, tunda Haneefah baza su wuce 1 month a Kano ba, zasu koma Kogi state, a can mijin nata yake aiki. Wayarta ce ta shiga ruri ta kai hannu ta ɗauka, murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta. Bayan ta yi picked ta ce "Ƴar halak, tunaninki nake a raina sai gashi kin kira ni." Haneefah ta ce "Ba wani nan, ba cin ma kin manta da ni, ko kirana akai_akai bakya yi." Neehal ta ce "So kike Yaya Faruq ya fara jin haushina kenan, yana tsaka da cin amarcinsa ni kuma ina damunsa da kira." Haneefah ta ce "Na ji, yaushe zaki zo?" Neehal ta ce "Ran Friday Insha Allahu." Haneefah ta ce "Allah ya kai mu, ina Mamana da twins?" Neehal ta ce "Duk suna nan lafiya k'alau." Haneefah ta ce "My regard to them." Neehal ta ce "Za su ji insha Allah." Sun ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama. Neehal ta miƙe ganin biyar ta kusa ta ɗauki car key ɗinta ta fita dan ɗauko su Afrah, Mama bata nan tana gurin aiki.


A bakin gate ɗin makarantar ta yi parking motar, sai da ta duba agogon hannunta sannan ta fito ta shiga cikin school ɗin. Tana shiga ana kaɗa musu beil, yara suka fara fitowa daga classes ɗinsu da gudu. A bakin class ɗin su Afrah ta hango su, ta ƙarasa ta kama hannuwansu. Suka juyo suka kalle ta, Afrah ta ce "Aunty yau ke kika zo ɗaukar mu?" Neehal tana karɓar lunch box ɗinsu ta ce "Gashi ko kin gani." A hankali suke tafiya har suka fito daga school ɗin, ta nufi inda ta yi parking Motarta. Wani matashi dake waya a gefe ɗaya ya ƙurawa su Afrah ido cikin tsananin mamaki. Katse wayar ya yi bayan ya cewa wanda suke wayar yana zuwa, ya nufo inda Neehal take. Neehal ta buɗe bayan Motar ta ajiye lunch box ɗin sannan ta shigar da su Afrah cikin Motar. Tana rufe musu murfin Motar matashin ya ƙaraso, kawai sai ganin mutum ta yi a gabanta. Ta ɗan ja baya ta ce "Malam lafiya?" Matashin ya mayar da dubansa ga su Afrah dake cikin Mota ta glass ya ce "Dan Allah ina kika samo waɗannan yaran?" Gaban Neehal ya faɗi amma ta dake ta ce "Kamarya? Wannan wacce irin tambaya ce." Matashin ya ce "Na san su ne shi yasa na tambaye ki." Neehal ta ɓata rai sosai ta ce "To ba su ka sani ba gaskiya, watakila ɓatan kai ka yi." Bata jira amsar sa ba ta juya ta buɗe gaban Motarta ta shige, ta bar shi nan tsaye. Matashin ya matso da nufin ƙara yi mata magana, amma ganin ta yi reverse yasa shi yin baya da sauri, sai kuma ya nufi titi da gudu ya tsayar da na mai napep ya shiga, cikin sauri ya ce "Dan Allah malam waccen Motar zaka bi mun bayanta duk inda ta yi, zan biya ka ko nawa ne." Mai napep ɗin ya ja suka tafi da sauri dan kar motar Neehal ta ɓace musu. Suna shiga layin su Neehal ita kuma ana buɗe mata gate ta shige cikin gidan. Matashin ya cewa mai napep ɗin ya tsaya, ya sauko tare da Sallamar mai napep ɗin. Sannan ya nufi gidan da ya ga ta shiga. Sai da ya fara Ƙarewa gidan kallo sannan ya nufi gate ɗin gidanya fara knocking, mintuna biyu ya ga wani soja ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan. Ya dubi sojan dake masa kallon tara saura k'wata ya ce "Barka da yamma yallaɓai, dan Allah idan babu damuwa ka mun magana da mai_gidan nan." Sojan ya bishi da kallo daga sama har ƙasa sannan ya ce "Baya nan." Matashin ya ja numfashi ya ce "Matar gidan fa? Dan Allah ka mun magana da ita to." Sojan ya ja tsaki ya ce "Malam kafin na yi counting ten ka bar gurin nan, ko kuma yanzu jikinka ya faɗa maka." Matashin ya ce "Please I have important t...." Sojan yana jijjiga kai ya ce "Baka ji ba kenan? To ka cigaba da tsayawa." Ya juya ya rufo ƙofar da ƙarfi. Dafe kansa matashin ya yi sannan ya juya ya fara tafiya, yana tafe yana waigen gidan, a ransa yana faɗin daga ganin wannan tamfatsetsen gidan mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne. Sai da ya bar layin sannan ya ɗauko wayarsa ya shiga kiran wata Number......










Yana kwance rigingine akan makeken gadonsa, dawowarsa kenan daga office. Idanunsa a lumshe yana jin yanda zuciyarsa take bugawa a hankali, duk bugun da zata yi tana bugawa da tunanin kids ɗinsa a ransa. A kullum kewarsu na ƙara cika zuciyarsa, duniyar gaba-ɗaya ta yi masa zafi, yana jin gidan da yake ciki ya yi masa girma saboda rashin kids ɗinsa. Da suna nan da tuni yanzu suna jikinsa suna basa labarin abun da ya faru a school ɗinsu. Ya taune lips ɗinsa cikin k'unar zuci. "I missed you alot my kids." Ya furta hakan a fili cikin sassanyar muryarsa mai nuni da damuwar da zuciyarsa take ciki. Ɗaya daga cikin wayoyinsa da ya ajiye akan mudubi ce ta fara ruri, yana ji amma bai ko motsa ba da niyyar ɗauka har ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa. Tashi zaune ya yi yana sauke numfashi sannan ya sauko daga kan gadon ya je ya ɗauki wayar. Musbahu! Sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar kenan, ya yi picking tare da kara wayar a kunnensa. Daga ɗaya ɓangaren ba tare da gaisuwa ba Musbahu ya ce "Doctor! Na ga su Afrah yanzu." "What?" Ya faɗa cikin dokawar zuciya. Musbahu ya ƙara maimaita masa abun da ya faɗa, duk da ya san ya ji. "Musbahu! A ina ka gan su?" Ya tambaya cikin sark'ewar harshe. "A Kano." Shima Musbahun ya bashi amsa cikin hanzari. Ya ce "Kano kuma? A Kano a ina?" Musbahu ya bashi labarin duk abun da ya faru na ganin su Afrah tare da Neehal da bin bayanta da ya yi zuwa gida. Ahmad ya zauna dab'as a bakin gado ya ce "Soldier kuma? Kuma ya hana ka shiga gidan? Kuma ta tabbatar su Afrah ka gani?" Musbahu ya ce "Wallahi Doctor sune, ai na san su sosai, tunda kana zuwa da su gida gurin Yaya." (Musbahu k'anin wani Freind ɗin Ahmad ne mai suna Sagir.) Ahmad ya ce "Shikenan, gobe ƙarfe goma na safe Insha Allahu ina cikin garin Kano, idan na shigo zan kira ka." Musbahu ya ce "Shikenan Doctor sai ka zo, Allah yasa a dace." Ahmad ya ce "Ameen." Dafe kansa ya yi yana jin kamar mafarki yake, zuciyarsa ta kasa yarda da abun da Musbahu ya sanar masa, duk da idan hakan ya kasance bai san wanne irin farin ciki zai yi ba, his kids sun kusa dawowa gare sa kenan? Addu'ar da ake ba dare ba rana ita ce Allah ya amsa yau ya bayyana masa inda yaransa suke. 'Ya Allah! Ka tabbatar da abun da Musbahu ya faɗa.' ya faɗi hakan a ransa yana jin kamar ya zuk'o gobe ta yi........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:55] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_












*3️⃣9️⃣*














Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














............A ɓangaren Neehal kuwa bayan sun koma gida tana cire musu kaya Amrah ta ce "Aunty yaushe zamu gurin Daddy?" Neehal ta sauke numfashi har yanzu gabanta bai far faɗuwa ba ta ce "I don't know." Afrah ta ɓata fuska ta ce "Aunty We Missed him alot, please ki kai mu gurinsa." Ta yi shiru ba ta ce musu komai ba. Har ta gama cire musu kayan ta saka musu wasu zancen Daddy'nsu suke, suna ta lissafin abubuwan da yake siyo musu da abubuwan da yake musu, har wak'ar da yake musu idan za su yi bacci sai da suka bawa Neehal labari, ita dai kawai jin su take, amma zuciyarta cike take da fargabar da bata san ko ta mecece ba. Da Mama ta dawo bata faɗa mata gamuwarta da matashin nan ba, ta san idan ta sanar mata faɗa zata mata sosai akan rashin saurararsa da bata tsaya ta yi ba. Washegari da safe ta shirya su Afrah suka tafi school, ita kuma bayan ta gama breakfast ta koma ɗaki ta kwanta.......






Ƙarfe goma da mintuna na safe Doctor Ahmad ya sauka a garin Kano, garin da ya yi shekaru masu yawa rabon sa da shi, sai yau sanadiyyar kids ɗinsa Allah ya kawo shi. Babu wanda ya faɗawa abun da zai je yi Kano, daga shi sai Musbahu ne suka sani, saboda ya fi so ya musu surprise, kuma ma baya so sai ya gama faɗar anga twins a Kano kawai ya zo ya ga ba su ba ne, duk da baya fatan haka. Yana sauka ya kira Musbahu ya sanar masa ya sauka yana airport ya zo ya ɗauke sa. Mintuna ƙalilan Musbahu ya je airport ɗin, saboda dama a shirye yake, kuma daga inda yake babu nisa zuwa airport ɗin. Bayan sun gaisa Ahmad ya shiga cikin motar da musbahu ya zo a ciki suka nufo gidansu Neehal. Suna tafe Ahmad yana tambayar Musbahu ƙarin haske akan ganin su Afrah da ya yi, har da nuna masa hoton su Afrah wai ya tabbatar su ɗin kuwa ya gani? Abun da ɗaure wa Ahmad kai da Musbahu ya ce masa cikin uniform ya ga su Afran, ɗaukar su ma aka zo yi daga school. Kenan waɗanda suka tsince su ne suka saka su a makaranta? Ko kuma dai ba su Afrah ɗin Musbahu ya gani ba wasu masu kama da su ne? Tunda gashi ya ce ya yiwa wacce ta zo ɗaukar tasu magana ta ce ba waɗanda ya sani ba ne. Tambayoyi dai barkatai Ahmad yake ta yiwa kansa wanda ba shi da amsoshin su, a gefe guda kuma yana jin wani irin sauyi a cikin zuciyarsa, a haka har suka ƙarasa gidansu Neehal. Horn Musbahu ya yi a bakin makeken gate ɗin gidan, Ahmad ya ƙurawa gidan ido cikin fad'uwar gaba. Ƙaramar ƙofar gidan wani dogon soja ya buɗe yana kallon Motar tasu, a hankali Ahmad ya bude murfin Motar ya fito Musbahu ma ya biyo bayansa. Ahmad yana zuwa ya miƙawa sojan hannu cikin kamilalliyar muryarsa ya ce "Good Morning." Musbahu ya saki ajiyar zuciya ganin ba sojan jiya ba ne, wanine daban. Sojan ya ce "Morning." yana bin Ahmad da kallo." Ahmad ya ce "Masu gidan suna nan?" Sojan ya ce "Mai gidan dai baya nan, amma matar gidan tana nan." Ahmad ya ce "Idan babu damuwa a yi mana iso a gurinta." Sojan ya ce "Wa za'a ce mata?" Ahmad ya ce "Baƙi ne daga Abuja." Sojan ya yi shiru yana ƙarewa su Ahmad kallo, sannan ya juya ya koma cikin gidan ba tare da ya yi magana ba. Musbahu ya ce "Hmm, Daga ganin gidan nan na wani babban Sojan ne." Ahmad ya sauke numfashi bai ce komai ba, yadda yake jin zuciyarsa kamar ya bi ta cikin gini ya shiga gidan saboda zak'uwa...... Mama tana falon ƙasa tana operating system Dije ta ƙaraso inda take bayan ta buɗe ƙofa, cikin ladabi ta

Please Login or Register in order to submit comment