Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

for you kamar yadda kake buƙata." Ta miƙe tana sauke numfashi da sauri alamun ranta a matuƙar ɓace yake. Ya miƙe shi ma tare da kamo hannunta cikin tsananin damuwa ya ce. "Bana son na ga kina ɓata ranki a kaina Mum, sai in ji gaba-d'aya na tsani kaina, dan Allah ki koma ki zauna mu yi magana." Mama ta ce. "I think five minutes Ka ce, kuma ta yi har ma ta wuce." Ya ce. "Please Mum." Mama ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce. "Ameen! Ni mahaifiyarka ce?" Ya ce. "Yes you are." Ta ce. "To meyasa baka son faɗa mun damuwarka? Ameen barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, ni na san akwai abun da yake damun ka, kuma ba ƙaramin abu ba ne, yanayinka ya tabbatar mun da haka, amma ban san dalilin ka na ƙin sanar mun ba, ni kuma indai zanke ganin ka a haka bazan taɓa iya haquri ba sai na tambaye ka. Ameen da damuwarka zan ji ko da ta Neehal?" Ya zaunar da ita shi ma ya zauna cikin damuwa ya ce. "Mama! wani abun da yake cikin ciki wuta ne, wanda idan ya fito zai cinye mutane da yawa, barin shi a cikin shi ya Alkhairi." Mama tay masa wani kallo ta ce. "Tunda ka san wutar ne me yasa kai zaka bar shi a cikin cikinka? ya cinye ka kenan?" Ya ce. "Ba zai cinye ni ba Insha Allah, I know." Mama zata kuma magana ya katse ta da faɗin. "Just pray Mum." Mama ta jinjina kai cikin raunin murya ta ce. "Shikenan Allah yasa mu dace, Amma Ameen ina jin wani iri a raina something so bad, bana son na rasa ka kai da Neehal a rayuwata, ku kaɗai ne garkuwata a duniyar nan, ku kaɗai nake kallo in ji sanyi a raina bayan mahaifiyata, more especially You!" Ya kwantar da kansa akan ƙafaɗarta bai ce komai ba, sai lumshe idonsa da ya yi. Mama ta shafa lallausar bak'ar sumar kansa ta ce. "Ameen! ka ji ƙaddarar data kuma samun mu ko? ban san me marainiyar Allah nan tay musu suke cutar da ita." Can ƙasan mak'oshi ya ce. "Akwai Allah!" Mama ta ce. "Da shi muka dogara." Ya janye kansa daga jikin Mama ya ce. "Where is she?" Mama ta nuna masa ɗakin Daddy da hannu dan ta gane Neehal yake nufi ta ce. "Tana can." Ya miƙe ba tare ya yi magana ba ya nufi ɗakin. Mama ta bi shi da kallo zuciyarta cike da son sanin abun da yake damun tilon ɗan nata k'waya ɗaya jal a duniya da ya sanyaya shi over haka. Ta miƙe tana sauke ajiyar zuciya ta fice daga falon.














Neehal tana kwance idonta a lumshe tana tunanin da bata san ranar daina shi ba. A hankali ya turo ƙofar dakint ya shigo, ya tsaya yana kallon ta tare da hard'e hannayensa a ƙirji. Bata ji shigowar shi ba saboda bata duniyar da yake, daddaɗan k'amshinsa da ba ya taɓa buya matuƙar yana guri shi yasa ta buɗe idonta, saboda yanda ta ji gaba-ɗaya ya mamaye mata hanci. Ta waro Idanunta waje waɗanda babu d'igon hawaye a cikin su, tunda ta kwanta take son ta yi kukan ko zata ji daɗin radadin da zuciyarta take mata amma kukan ya ƙi zuwa, sai yanzu ta gane ashe kukan ma rahama ne, ashe idan damuwa ta kai damuwa nemar shi ake a rasa? ta yunƙura tana ƙoƙarin tashi zaune cikin matuƙar dauriya. Ganin haka ya ƙarasa bakin gadon da sauri. Cikin marainiyar murya ta ce. "Yaya!" Ya rank'wafawa ya ce. "Na'am Miemerh!" Ta faɗa jikinsa da sauri tare da fashewa da kukan da take ta fatan ya zo mata tun d'azu sai yanzu ta ji sa. Ya runtse idanunsa tare da taune lip ɗinsa da ƙarfi, a hankali ya saka duka hannayensa ya zagaye bayan ta da su. Kuka take yi sosai mai taɓa zuciya gami da karyar da zuciyar mai saurarensa, wanda idan mutum mai saurin kuka ne zai iya taya ta. Numfashinta har wani sama_sama yake kamar zai ɗauke. Da sauri Ameen ya zare ta daga jikinta jin yanda take kukan kamar zata mutu, ya zauna akan gadon sosai sannan ya d'ago fuskarta yana fizgar da huci mai zafi ya shiga girgiza mata kai. Ta kwantar da kanta akan ƙafaɗarsa ta cigaba da rera da kukan ta. Ya jinjina bayansa da prame ɗin gado tare da lumshe idonsa zuciyarsa na wani irin bugawa. Bai ce mata komai ba kuma bai yi yunƙurin hana ta kukan ba, sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru ta shiga sauke ajiyar zuciya. Jin ta yi shiru ya buɗe idonsa ya zuba su akan fuskarta, wadda ta yi jajur saboda kuka. Ya ɗora hannunsa akan fuskar ya ji zafi zau kamar garwashi. Ta cire hannunsa daga kan fuskarta ta rike da nata hannun ta d'ago kanta daga jikinsa, cikin magana da ƙyar ta ce. "Yaya sun sace Sadik, Yaya me nay musu? Please Yaya ka karb'o mun shi dan Allah kar su cutar da shi, kar su kashe mun shi kamar sauran, ka ji Yaya." Ameen ya shiga goge mata hawayen fuskarta ya ce. "I promised to you Miemerh, zan nemo miki Sadik a duk inda yake Insha Allah." Ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tana ƙara riƙe hannunsa. "Thank you Yaya, dama na san kai kaɗai ne zaka dawo mun da shi, Yaya ka je ka karb'o mun shi yanzu_yanzu karka bari ya kwana su kashe shi, Yaya in ya mutu nima mutuwa zan yi, ka yi sauri ka ji Yayana." Ya ƙura mata ido ganin yanda take magana kamar bata cikin hayyacinta, ga dukkan alamu tashin hankalin da take ciki ya rud'ar da ita ba kaɗan ba. Ta saki hannunsa ta mayar da kanta ta kwantar a jikinsa tare da lumshe idanunta tana sassauke ajiyar zuciya akai_akai. A lokacin Mama ta dawo ɗakin da ledar drugs a hannunta, kallo ɗaya tay musu ta ɗauke kanta. A hankali Ameen ya zare Neehal daga jikinsa ta koma ta kwanta, wadda ta yi wani irin shiru jikinta kamar na wadda ta suma duk ya shika, sai numfashinta dake fita da sauri da sauri. Mama ta ɗauki mug ɗin tea tana faɗin. "Taso ki sha Daughter kar ya yi sanyi." Neehal ta buɗe idonta a hankali ta zubawa Mama su, Mama ta dubi Ameen ta ce. "Taimaka mata ta tashi zaune." Ya amsa mata da kai sannan ya tayar da Neehal zaune, ya saka mata pillow a bayan ta Sannan ya miƙe. Mama ta ce. "Ka je gurin matarka kuwa? Yarinyar nan yau gaba-d'aya cikin zullumi ta wuni." A hankali ya ce. "Yanzu zan je na gan ta, daga nan sai mu wuce gida." Mama ta ce. "Shikenan Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da Amin sannan ya fice daga ɗakin. Mama ta zauna a bakin gadon tare da miƙawa Neehal mug ɗin hannunta ta ce. "Take it." Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce. "Ki yi haquri ki daure ki sha ko kaɗan ne, baki da lafiya Neehal ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba." Ta buɗe baki da ƙyar ta ce. "Bakina ɗaci Mama, ba zan iya sha ba, ko na sha ma amai zan yi." Da ƙyar Mama ta lallaɓa ta, ta sha tea ɗin kaɗan, sai dai kamar yadda ta faɗa kurb'a uku kawai ta yi ta dawo da shi. Dole Mama ta haqura ta ƙyale ta, magungunan ma fasa bata ta yi, dan ta san su ma in tasha amansu zata yi. Tana son tay mata allura amma saboda cikin ta babu abinci yasa batai mata ba dan kar ta galabaitar da ita. Sai ruwa ta ɗebo ta goga mata a jikinta da towel saboda zafin da jikin nata ya yi, ta kuma kama mata kanta ganin yanda take ta dafe kan da hannunta. Goma saura Hafsat ta zo ta yiwa Mama Sallama, wai za su wuce gida ita da Ameen. Mama tay musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya. Neehal dai tana kwance idanunta a lumshe amma ba barci take ba, tunanin Sadik da rashin sanin halin da yake ciki a yanzu kawai take. Ko yana raye ko a mace sai Allah. Tana ji su Aunty A'isha da Aunty Sadiya da Hajiya suka shigo ɗakin suna tambayar jikinta tare da yi mata sannu, amma ko ido ta kasa buɗewa ta kalle su.










Sha ɗaya saura Daddy ya shigo ɗakin, Mama tana zaune ita kaɗai akan darduma tana jan carbi. Ya zauna a bakin gado yana duban Neehal ya ce. "Bacci take ne?" Mama ta ce. "Ehh." Daddy ya girgiza kansa ya ce. "Allah ya kawo miki ƙarshen wannan abun Daughter." Mama ta ce. "Amin, bari na kawo maka wani abun ka ɗan saka a cikinka, na san yau babu abun da ka ci." Ya ce. "Doctor bar abun cin nan, babu abun da zai iya shiga cikina a yanzu." Mama ta ce. "Daurewa zaka yi ka ci ko kaɗan ne, yau ɗaya amma ba ka ga yadda ka faɗa ba." Daddy ya ce. "Ina cikin tsananin tashin hankali ne Doctor." Mama ta ce. "Addu'a ce mafita Gen." Daddy ya ce. "Haka ne ita muke ta yi, yanzu ma masallaci zan tafi, na saka a kwana yau ana karatun Alkur'ani, to na san ko na zauna a gida ba bacci zan yi ba, shi yasa na ce gwara na je kawai a yi karatun tare da ni, ko na ji daɗi a raina." Mama ta ce. "Shikenan, Allah ya amsa mana addu'oin mu, ya bayyana mana wannan yaro." Daddy ya ce. "Amin Amin." Sannan ya shafa kan Neehal yay wa Mama Sallama ya tafi masallaci. Daren yau mutane da yawa ba su rintsa ba, Mama kwana ta yi tana Sallah tana kaiwa Allah kukan ta, haka ma Maamah mahaifiyar Sadik da Abbansa, Aunty Sadiya ma kwana ta yi tana bincike a system ɗinta da wayarta. Neehal kuwa wannan daren da tunanika ta raya shi. Ta fara tunanin farkon haɗuwar ta da Jameel har zuwa lokacin da ya rasu ya bar ta da tarin k'aunarsa a ranta, ta tuno Anwar shi ma da irin soyayyar da suka sha kamar babu gobe, ta tuno Ahmad da tarin k'aunar da ya nuna mata, ƙarshe kuma suka rabu. Sai Sadik wanda ta saka a ranta shine mutum na ƙarshe wanda zata yi soyayya da shi a rayuwarta, ta sakankance shi zai zamto abokin rayuwarta na har abada. Amma shi ma sai da *BAK'AR ƘADDARA* ta raba su a ranar d'aurin Auren su. Ta gane bata da sa'a a soyayya kamar yadda ta fitar da rai da yin aure a rayuwarta. Ta haqura da soyayya balle har ta yi tunanin yin aure, tunda aka sace Sadik a ranar Aurensu to babu makawa ko da ta yi aure mijin data aura ma ba zai tsira ba, za'a iya biyo shi har cikin gidansu a kashe shi. Ita kuma abun da zuciyarta baza ta kuma ɗauka ba kenan, ta san idan hakan ta faru bugawa zuciyarta_ta zata yi ta mutu. Ta gaji da sai ta shak'u da mutum sannan a raba su, rabuwa ta har abada. She accepted her destiny, zata k'are rayuwarta a haka babu aure, wannan ita ce *ƙaddarar ta*. Tana fata da kuma addu'ar Allah ya bayyana Sadik cikin k'oshin lafiya, amma ba dan ya dawo su yi aure ba, sai dan farincikin ahalinsa. Sai wajen asuba bacci mai kama da suma ya ɗauke ta, a cikin barcin mafarkai ta dinga yi barkatai, wani wai gashi an ga Sadik cikin mawuyacin hali, wani kuma gawarsa aka gani an kashe sa, wani kuma ya dawo cikin k'oshin lafiya har an yi auransu suna rayuwarsu cikin farinciki. Duk mafarkan nata dai akan Sadik ne da kuma halin tashin hankalin da ake ciki game da ɓatan sa. Da asuba da Mama ta tashe ta da ƙyar ta iya tashi ta yi Sallah a zaune. Kafin safe jikinta ya rikice sosai da zazzafan zazzaɓi, jikinta har rawa yake ga matsanancin ciwon kai. Hankali a tashe Mama da Aunty A'isha suka ɗauke ta suka nufi asibiti da ita. Suna zuwa aka ba su gado, wanda zuwa lokacin Neehal ta galabaita matuƙa. A asibitin suka wuni, yayin da ƴan dubiya da suka samu labarin ciwon nata suke zuwa ko ta ina duba ta. Ahmad da su Ummi ma sun zo sun duba ta, Ahmad ya tsaya a bakin gadon marasa lafiyar da take kwance yana kallon ta cikin tsananin tausayin ta. Ya shafi gefen kuncinta ya ce. "Allah ya baki lafiya Princess." Kamar kar ya tafi ya zauna yay jinyar ta haka yake ji. Sai can yamma Ameen da Hafsat suka zo asibitin amma har dare ba su tafi ba. Da daddaren Mama ta matsa aka sallame su daga asibitin, ta ce zata cigaba da kula da ita a gida. Neehal dai bata um bata Um'um, sai dai tay ta kallon mutane. Hajiya ta ce, al'amarin nan nata fa sai an haɗa mata da rubutun dangana ta sha. Haka kuwa aka yi Daddy yasa akai mata rubutun ya zamto ruwan shan ta. Kwana uku da ɓatan Sadik amma shiru babu wani labari har yanzu, addu'a kam an dage yinta ake, a gefe guda kuma jami'an tsaro suna ta aikin nasu binciken. Zuwan su biyu gidan Mama domin yiwa Neehal tambayoyi a matsayin ta na wadda suka yi wayar ƙarshe da Sadik kafin a sace shi, amma halin da take ciki yasa ba su samun damar yin magana da Ita ba. Baƙin da suka yi saura a gidan tuni kowa ya koma gidan sa, su Aunty ma sun koma gidajensu amma kullum sai sun zo, dan ita kanta Maman tausayi take ba su, dan za'a bata gado tsaf Ita ma zata kwanta, dauriya da ƙarfin hali kawai take. Hajiya ce kaɗai bata tafi ba. Mommyn Hameedah ma ta gama yada habaibaice_habaicen ta tasa tuzuruwar ƴarta a gaba sun tafi. Uncle Usman da iyalansa ma basu koma Nijar ba, suna gidan Uncle Umar, a part ɗin Aunty Fauziyya suke zaune tunda bata gidan. Neehal ta fara magana kaɗan_kaɗan, idan aka yi mata magana yanzu tana amsawa da um ko um'um. Doguwar maganarta kuwa sai idan Ameen ya zo gidan, ta dinga ce masa. "Yaya ka karb'o mun Sadik ɗin? dan Allah Yaya ka karb'o shi kar su cutar da shi." Shi kuma sai ya lallaɓa ta tare da tabbatar mata da Insha Allahu Sadik zai dawo cikin k'oshin lafiya. Sai karatun Alkur'ani da kullum suke yi tare da Mama safe da dare, shine yake ɗan sanyaya mata zuciya yasa ta ji damuwarta na raguwa. Haneefah ma idan ta zo gidan tana iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta rage mata damuwar dake ranta, ta hanyar yi mata hira da nasihar yadda da ƙaddara cikin sigar rarrashi.










Ranar juma'a wanda ya kama sati guda cif da ɓatan Sadik, da yamma Maamah suna zaune a main Parlour'n gidan ita da ƴan'uwanta da ba su koma gida ba har yau, sai Hajiya kakarsu Sadik. Suna zaune jigum_jigum kamar gidan zaman makoki, ko da yake su da mutuwa ma Sadik ɗin ya yi sai hankalinsu ya fi kwanciya tunda sun san ba ya raye, akan wannan zullumun da fargabar rashin sanin halin da yake ciki da suke. Mai gadin gidan ne ya faɗo Parlour'n yana ta zuba haki babu ko sallama. Hajiyarsu Sadik ta ce. "Lafiya kuwa malam Ayuba ka faɗo mana cikin gida a ruɗe babu sallama?" Sai a lokacin Maamah dake jan carbi ta d'ago kanta tana jin zuciyarta na wani irin bugu. Waje malam Ayuba yake nuna musu da hannunsa amma ya kasa magana sai rawar baki yake alamun yana so ya ce wani abu maganar ce ta ƙi fitowa. Hajiya ta buɗe baki zata kuma magana amma shigowar Sadik Parlour'n a matuƙar sanyaye ya hana ta faɗar abun da tay niyya........✍️










_*Na so page ɗin ya fi haka tsayi, amma rashin caji ya hana yiyuwar hakan, and ban yi edit ba a yi haquri da typing errors.*_












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣2️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















..........Kafin Yamma Labarin sace Sadik ya baza ko ina a cikin jihar nan da ma mak'wabtan ta. Sakamakon hotunansa dake ta yawo a social media tare da note ɗin ɓatan da ya yi. Abun da yake ƙarawa labarin nasa armashin yaɗuwa sace shin da akai a ranar D'aurin Auren sa, and kuma amaryar tasa wadda yake shirin angoncewa da ita fitacciyar ƴar jarida ce wadda duniya ta san ta. Su Daddy sun so a ɗaura Auran a yau ko dan jama'ar da aka tara amma dangin Sadik suka ƙi amincewa, haka suka dawo gida jiki a sanyaye. Kawu Musa ya ce, suna da gaskiya, kuma ko waɗanne iyaye ne ɗansu ya ɓata abun da zasu yi kenan, suna cikin zullumi da damuwar ɗansu baza su bi takan wani d'aurin Aure ba. Uncle Usman ya bayar da shawarar a ɗaurawa Neehal Aure da wani saurayin idan tana shi kowa ya huta da wannan fargabar. Amma Daddy ya ce baza a yi haka ba, domin Dangin Sadik zasu ga kamar ba su damu da ɓatan Sadik ba, tunda har suka iya ɗaurawa Neehal Aure a yau, idan suka yi haka ba su yi musu kara ba. Gidan bikin Mama ma ya koma kamar na zaman makoki like gidansu Sadik, Haneefah ta ci kuka ta k'oshi, haka ma Aunty A'isha da Hajiya. Aunty Sadiya mai ɗan dauriya a cikin su, Mama kuwa ko magana bata iya yi, tana zaune kawai ta tafka tagumi. Neehal kam tun bayan data suma aka dinga shafa mata ruwa a fuska da ƙyar ta farfaɗo tana ambaton sunan Sadik tare da roqon kar ya tafi ya bar ta. Ganin bata cikin hayyacinta kuma a firgice take yasa wata abokiyar aikin Mama tay mata allurar bacci, aka ɗauke ta aka kaita ɗakin Daddy aka kwantar.








Bayan Sallar la'asar gaba-ɗaya ƴan'uwa na jiki suka hallara a main Parlour'n Daddy dan tattaunawa akan al'amarin, tunda zuwa yanzu sun fuskanci saboda Neehal aka sace Sadik. Daddy, Kawu Musa, Uncle Usman, Uncle Umar, Uncle Mahmud, Uncle Ahmad (Mijin Aunty Sadiya) Abba, (Yayan Daddy) Mama, Hajiya, Aunty Sadiya, Aunty A'isha da Umma. Kawu Musa ya yi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka. "Zamu fara da Addu'ar Ubangiji Allah ya bayyana mana wannan yaro a duk inda yake, ya kuma kare shi yasa yana hannu na gari, idan kuma kamar yadda ake tunanin sace shi aka yi, to Ubangiji Allah ya toni asirin waɗanda suka sace shin cikin gaggawa." Gaba-ɗaya suka amsa da "Amin ya Allah." Daddy da hannunsa ke dafe da kansa ya d'ago yana girgiza kai ya ce. "Amma fa wannan abun akwai rikitarwa da tayar da hankali ba kaɗan ba." Mama ta sauke numfashi tare da janye tagumin data rafka, cikin sanyin murya mai nuni da tsantsar damuwar da take ciki ta ce. "Tabbas a yau na yarda da maganar Sadiya 100%, ko shakka babu wanda ya kashe Jameel shi ya kashe Anwar, haka nan kuma shi yasa aka sace Sadik yanzu ma, kuma duk saboda Neehal." Daddy ya ce, "Ni kuma bana tunanin hakan gaskiya." Cikin takaici Uncle Usman ya ce. "To idan ma hakan ne waye yake aikata hakan? kuma akan me? Me yarinyar nan tay masa?" Cikin dashashshiyar muryar da ta ci kuka ta k'oshi Aunty A'isha ta ce. "Na fi tunanin koma waye son ta yake, shi yasa baya son kowa ya aure ta." Aunty Sadiya ta ce. "So?" Sai kuma ta yi ɗan murmushi ta ce. "Hmm, duk wanda yake aikatawa Neehal wannan abun ba son ta yake ba, wata mummunar manufar ce da shi a gare ta." Uncle Mahmud ya ce. "Me yasa zaki ce haka Haleemah? Nima zuciyata ta fi yarda da abun da A'isha ta faɗa na wani ne yake son Neehal ɗin, shi yasa yake kashe duk wanda zata aura, yanzu kuma sai ya sace Sadik ya canza salo." Aunty Sadiya ta miƙe ta yi taku hannayenta cikin juna tana zira yatsunta a tare tana zarewa, sannan ta ce. "Idan har dagaske son ta yake son Allah ba ƙoƙarin cutar da ita ba me yasa ba zai bayyana kansa a gare ta ba? Me yasa ya san idan har ya bayyana kansa a matsayin wanda yake kashe mata duk wanda zata aura saboda yana son ta ya san baza ta taɓa amincewa da auren shi ba, amma kuma yake aikata hakan? Ya kamata Ku yi tunani da kyau akan wannan idan har son ta yake da gaske ba zai taɓa aikata mata haka ba, kamar yadda na faɗa wata mummunar manufar ce da shi a gare ta, ko kuma akwai wani abun da yake son gudanarwa da ita, amma kuma Allah bai ba shi sa'a ba har yau, kuma ga dukkan alamu mummunan kudirin sa a kan ta da zarar ta yi aure ba zai samu ba, shi yasa yake aikata hakan." Gaba-ɗaya suka yi shiru suna kallon ta kowa yana auna maganganun ta a mizanin hankali. Ta koma ta zauna sannan ta dubi wani sashi na Falon ta ce. "A binciken da nake gudanarwa fiye da shekara akan al'amuran Neehal akwai wanda nake zargi, kuma a Ƴan kwanakin nan wasu alamomi suka ƙara ƙarfafa mun zargin nawa a kansa." A hanzarce Daddy ya ce, "Wa kike zargi Barrister? Ki yi gaggawar sanar mana in saka a damk'o sa a bincike sa." Uncle Umar ya ce, "Wannan haka ne, kuma shine abun yi, domin kuwa wannan abun ya yi yawa, mun gaji, muna san sanin gaskiyar al'amarin." Suka gyaɗa kai gaba-d'ayan su alamun haka ne. Aunty Sadiya ta ce. "Zargi nake ban tabbatar ba, shi yasa ba zan sanar muku a yanzu ba, na fi son sai na samu cikakken evidence k'wakwk'wara." Uncle Mahmud ya tari numfashinta da faɗin, "Amma ai a tsarin doka ma ana gudanar da wanda ake zargi a gaban shari'a, ko da ba'a tabbatar ya aikata lefi ba, ke me yasa baza ki faɗa ba?" Hajiya da bata yi magana ba tun d'azu sai yanzu ta ce. "Gaskiya ne, ya kamata ki faɗi wanda kike zargin, in ma ba shi ba ne wataƙila sanadiyyar hakan sai ki ga an gano gaskiya." Umma ta ce. "Haka ne, Sadiya ya kamata ki faɗa mana wanda kike zargi domin a san abun yi a kansa." Aunty Sadiya ta numfasa ta ce. "Ku yi haquri, na san zuciyoyinku a zak'e suke da sanin ko waye, amma ku sani wannan case ɗin na Neehal ya sha banban da case ɗin laifukan da muka saba ji da gani, idan har ban yi takatsantsan ba to zan iya kwana a ciki." Abba ya ce. "Kamar ya? Ba bincike ba ne? Ai idan aka gane mutum ba shi da hannu a ciki sakin sa za'a yi." Aunty Sadiya ta ce. "Ku dai yi haquri, Insha Allahu nan ba da jimawa komai zai bayyana, mu dai kawai mu dage da addu'a." Kawu Musa ya ce. "To Allah yasa mu dace, amma ba kwa tunanin ko akwai wani da suka samun saɓani da yarinyar nan ya k'ullace ta yake aikata mata wannan abun?" Mama ta ce. "Bana tunanin haka gaskiya, dan Neehal bata da abokin faɗa a rayuwarta, na san wani lokacin bata da haquri idan aka ɓata mata rai, amma bana jin zata yiwa wani babban abun da zai sa ya dinga bin ta da wannan mummunan abun a matsayin ɗaukar fansa ko hukunci." Kawu Musa ya ce. "To idan ba haka ba kuwa zata iya yiyuwa ko shi Gen. da ya kasance babban mutum mai tare da ƴan adawa a ƙasar nan saboda shi ake aikata wannan abun, domin a ɓata masa suna ko kuma dan wata manufar daban." Suka yi shiru cikin alamun nazari. Daddy yana jinjina kai ya ce. "Kuma fa Alhaji Musa zancen ka akwai k'amshin gaskiya, dole ne in tsaurara bincike akan wannan al'amarin, domin kuwa na san

Please Login or Register in order to submit comment