Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da saman ƙirjinta. Hakan yasa ta cire mayafin jikinta ta ɗauko hijabin da zai shiga da kayan jikinta ta saka. Ta ɗauki jakarta wadda wayoyinta ke ciki ta nufi ƙofa, har ta buɗe ƙofar zata fita ta dawo ta ɗauki wata ƙaramar wayarta keypad wanda bata fiya amfani da ita sosai ba, ta saka ta a cikin aljihun rigar jikinta sannan ta fita. A falo suka ci karo da Mama, Mama ta yi murmushin jin daɗin yanda ta gan ta. Ta kama hannunta ta ce. "Kin tashi lafiya Daughter." Neehal ta ce. "Lafiya k'alau Mamana, ina kwana." Mama ta ce. "Lafiya k'alau, ko kefa Neehal har na ji daɗi da zaki koma aikin nan, zai ɗebe miki kewa ba kaɗan ba, jiya da Ameen ya zo kin yi bacci yay ta faɗa wai iskancin me ya hana ki komawa aiki." Neehal ta yi murmushi ta ce. "Mama ɗan nan naki halinsa sai shi, Yaushe ya daina masifar zuwa na aikin, amma yanzu dan bana zuwa zai ce in koma." Mama ta ce. "Nima na yi mamakinsa, wai zama guri ɗaya babu fita gara kina fita kina ganin jama'a hakan zai rage miki damuwa." Neehal ta ce. "Haka ne, shi yasa yau na shirya komawa, Daddy ya fita ne?" Mama ta ce. "Yana nan yanzu dai zai fitan." Neehal ta ce. "Bari na je na gaishe shi." Mama ta ce. "Okay." A falo ta tarar da Daddy zaune yana waya, ta zauna a ƙasan kujerar da yake a zaune, sai ya katse wayar ya dube ta da murmushi ya ce. "Daughter an fito? Ta ce "Eh Daddy ina kwana?" Ya ce. "Lafiya k'alau ƴar albarka, dafatan kin yi breakfast?" Ta ce. "Na yi Daddy." Ya ce. "To Masha Allah, sai yaushe zaki dawo?" Ta ce. "Zan kai yamma saboda cike_ciken da zan yi." Daddy ya ce. "To Allah ya taimaka, ki kula fa sosai kin ji." Ta ce. "Insha Allah Daddy." Sannan ta miƙe tay masa sallma ta fita, ta koma ta yiwa Mama Sallama ta tafi.








Ta ji daɗin fitar da ta yi yau sosai, sai ta ji duk rabin damuwarta ta kau, tana ta hada_hada cikin jama'a ko time ɗin tunani bata samu ba, balle ta tunano abun da zai dame ta. Duk inda ta gilma ma'aikata na yi mata magana, wasu na tsokanarta da wata sabon gani wasu kuma suna yi mata ya jiki, saboda abun da ta cewa Manager ɗinsu kenan da bata zuwa bata da lafiya ne. Sai yanzu ta ƙara tabbatar da abun da Mama take faɗa mata kullum akan ta dinga fita zata ji sauƙin damuwar dake ranta. Sai yamma ta baro gurin aikin tana jin zuciyarta wasai. Ta shigo farkon layin su ta ga wata Mota tana tahowa daga cikin layin, ta yi b'arin left inda masu shiga suke bi, masu fita kuma right side suke bi, amma sai ta ga Motar saitin da take bi nan ita ma take bi, kuma layin nasu yana da faɗi sosai, three motors zasu iya wucewa a lokaci ɗaya ba tare da sun takura ba, kuma babu kowa a layin balle ta ce an tsare masa hanya ne. Ta cigaba da tafiya slowly tana kallon ikon Allah, sai ta koma right side ta bar masa left side ɗin, sai ta ga shi ma ya canza ya koma inda ta koma. Ta yi tsaki ta cigaba da tafiyar ta, a ranta tana faɗin baza ta kuma matsawa ba, sai dai shi in ya ga zasu yi karo ya matsa. Amma me, sai kawai ganin Motar ta yi ta sha gaban ta kamar zata buge ta. Ta taka burki cikin sauri gabanta na fad'uwa. Kafin ta yi wani yunkurin ta ga maza guda biyu sun fito daga cikin Motar cikin sauri, ta yi looked Motar ta_ta da sauri cikin mamakin dalilin da yasa waɗan nan mutanen zasu tare mata hanya, ta shiga ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a cikin zuciyarta. Suka ƙaraso inda take suka yi mata knocking glass ɗin Motar. Da farko ta tsorata sai ta ƙi buɗe musu, amma daga baya kuma da ta ga suna bata mata time sai ta zuge glass ɗin Motar ƙasa ta dube su cikin dakiya da son ɓoye tsoron da take ciki ta ce. "Me kuke buƙata a gurina, da zaku taren hanya and then ku zo kuna mun knocking?" Ɗaya daga cikin su ya juya yana kallon layin da babu kowa sai su kaɗai, ɗayan kuma ya bata amsar tambayar ta da watsa mata wani abu a fuska. Ta rufe idanunta tare kare fuskarta_ta da hannunta tana jujjuya kanta saboda juyawar da ta ji ya fara mata, cikin wasu sakanni kanta ya langwab'e a jikin kujerar da take. Da sauri wanda ya watsa mata abun ya zira hannunsa ta saman glass ɗin ya yi unlocked ɗin Motar, sannan ya ja murfin ya buɗe ya shiga, ya mayar da Neehal kujerar mai zaman banza sannan ya zauna a driver seat ya rufe Motar ya tayar da ita ya yi reverse ya fice daga layin da mugun gudu. Ɗayan wanda ya kasance kamar mai yi masa gadi ya juya cikin gudu ya shiga Motar da suka fito daga ciki ya kunna ta ya bi bayan ɗan'uwansa a guje.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












........."Ya...ya... Al...lah kasa mafarki nake ba gaske ba ne abun da yake faruwa." Ta sauke hannunta tare da runtse idonta tana girgiza kai, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido ta ga babu shi a gurin, Allah yasa idan ta buɗe idon ba shi zata gani ba wani daban zata gani idanunta ne ke mata gizo. Ta buɗe idonta a hankali kamar mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙaruwa. Shi ɗin ne dai tsaye a gaban ta yana kallon ta. Ta sake nuna shi tana ƙoƙarin yin magana amma ta kasa sarrafa harshenta ta yi maganar, sai rawar baki kawai take. Ta juya cikin fitar hayyaci ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice da gudu, ƙofar dake kusa da dakin ta murd'a ta buɗe ta shiga, cikin ikon Allah kuma ƙofar a buɗe take. A cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki da babu komai a cikinsa ta tsinci kanta, ta zube a bakin ƙofar cikin matsanancin tsoro da fargabar wanda ta gani, shirun sa da yanda ya tsaya yana kallon ta ya tabbatar mata da shine wanda yake ƙoƙarin keta mata haddi, me ya haɗa shi da wannan ƙungiyar wadda bata tantama ta matsafa ce? Ko shi ma member ne a cikinta? Ta tambayi kanta. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Ta shiga maimaitawa a fili cikin sark'ewar numfashi. Addu'a da fatanta ɗaya Allah ya farkar da ita daga wannan mummunan mafarkin da take, dan ta kasa yarda a gaske ne wannan baƙin al'amarin yake faruwa da ita. Wanda take masa kallon jigon rayuwarta anya zai aikata mata haka? Wanda take kallo a matsayin bangon rayuwarta a ce da shi ake ƙoƙarin gurɓata mata rayuwa, wannan wacce irin ƙaddara ce ta kuma samun ta? Wacce irin rayuwa take yi ne a duniyar nan? A fili ta furta. "Ya Allah idan wani laifin nai maka kake jarabta ta Allah ka yafe mini ka sassauta mun wannan jarabawar, Ya Allah karka tabbatar da abun da nake zargi, Allah karka ɗora mun abun da ya fi ƙarfi na." Ta zauna akan gwiwoyinta ta shiga bubbuga kanta a jikin kofar ɗakin cikin rashin sanin mafita da abun yi, ƙwaƙwalwarta_ta ta tushe gaba-d'aya ta ƙi bata space ɗin ma da zata yi tunani, idanunta kamas ko k'walla babu a cikinsu, kukan ma ya ƙi zuwar mata balle ta ji sauqin yaƙin wutar da ake a cikin zuciyarta.......












Tunda bayan fitar Daddy su Mama suke ta amsa kiran wayar mutane, ƴan'uwa da abokan arzik'i ana ta tambayar ko an ga Neehal. Mak'ota da wasu mutanen suna ta zuwa jaje. Ƙarfe sha ɗaya da mintuna Hajiya ta ƙaraso gidan, ta zube a falon ƙasa inda su Mama suke da Abba yayan Daddy wanda bai jima da zuwa gidan ba shi ma. Salati kawai Hajiya take yi tana hawaye. Mama tay mata sannu da zuwa cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsananin damuwa. Su Aunty ma suka gaishe ta tare da bata baki akan ta yi haquri. Hajiya ta ce. "Wanne irin haquri zan yi? Ku daina bani wani haquri ni, ku bar ni in yi kukana, wannan wanne irin bala'i ne yake bibiyar yarinyar nan? Dan na tabbatar sace ta aka yi." Mama ta jinjina kai tare da sauke numfashi. Dan itama zuwa yanzu ta fi zargin sace Neehal ɗin akay. Gashi Daddy shiru tunda ya fita bai dawo ba, ana ta trying Numbers ɗinsa basa tafiya.








Gajiya Neehal ta yi da bubbuga kan nata ta zauna dab'as tana sauke numfashi, sai ta ji kamar wani abu yana tokarinta a cinya. Ta kai hannu ta taɓa gurin sai ta ji abu a cikin aljihun rigarta. Cikin sauri ta dage hijabin jikinta ta zira hannu ta zaro ƙaramar wayarta da tashin hankali ya mantar da ita tana jikinta. Hannunta har rawa yake wajen kunna wayar, sai kuma ta kama waige_waige kamar mai tsoron kar wani ya gan ta. Numbern Mama ta lalubo da ƙyar saboda ko gani bata yi sosai ta yi dialing, amma sai kiran ya ƙi tafiya, tay ta trying kusan sau 20 amma ya ƙi tafiya, wayar ma gaba-d'aya emergency ta koma, sim ɗin ya ɗauke alamun babu network. Cillar wayar ta yi gefenta cikin takaici, ta zauna sosai ta jingina kanta dake barazanar fashewa saboda ciwo a jikin ƙofar ɗakin, bata san kuma mai zai faru da ita next ba, ko zasu biyo ta har nan ɗin ne su cimma buƙatarsu a kanta? Ko kuma wani sabon shirin muguntar suke kuma yi a kanta? Duk wannan ba shine abun da ya fi damunta ba a yanzu, damuwarta me ya kawo mutumin data gani a ɗakin da aka kaita? Ko fitar da ita ya zo yi daga gidan? Amma me yasa da ya gan ta ya ƙi magana? Ya ƙi ce mata komai? Me yasa data fito bai biyo ta ya kama hannunta sun fice daga gidan nan ba? Me yasa? A fili ta ce. "Dan Allah ka zo ka ce mun zuwa ka yi ka cece ni ba wai da kai ake ƙoƙarin cutar da ni ba, idan har hakan ta kasance ƙwaƙwalwarta baza ta ɗauki wannan al'amarin ba, zuciyata bugawa zata yi in mutu......!"










Tun daren jiya da Ameen ya bar gidan Mama ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗakinsa dan a halin da yake ciki ba ya buƙatar takurar Hafsat. Wata ƴar ƙaramar laptop ya ɗauko ya shiga operating, ga dukkan alamu aikin da yake yi mai matuƙar mahimmanci ne duba da yanda ya bayar da hankalinsa duka a kan aikin, yana yi yana kiran Numbobin Neehal tare da addu'ar Allah yasa su shiga, ya ɗaukarwa kansa alƙawarin duk inda Neehal take sai ya nemo ta ko da zai rasa ransa a gurin yin hakan, saboda dalilai guda biyu. Na farko saboda Mahaifiyarsa, ba zai iya jurar ganin Mama cikin wannan tashin hankalin da take ciki ba, wanda bai taɓa ganin ta a cikin irinsa ba tsawon rayuwarsa, dan haka dole sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Na biyu kuma yana son sanin gaskiya akan wani al'amari da yake zargi, al'amarin da idan abun da yake zargi ya tabbata to tabbas da akwai babbar matsala, matsalar da zata girgiza rayukan mutane da yawa. Har asuba yana operating system, sai da aka kira sallah sannan ya tashi duk ya haɗa zufa duk da A.C dake ɗakin, sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwala ya fito ya tafi masallaci. Hafsah ta cika ta yi fam akan shiga ɗaki da Ameen ya yi ya kulle, kishi ya cika ta dan ko tantama bata yi saboda ɓatan Neehal ya aikata hakan. Kwana ta yi tana jan tsaki da ƙwafa tare da addu'ar Allah yasa kar a ga Neehal ɗin shegiyar yarinya, ko kuma in an gan ta a gan ta a mace kowama ya huta. Dan tun gabatowar bikinta da Sadik ta rasa gane kan Ameen, har yanzu kuma bai dawo dai-dai ba, kullum cikin damuwa da shegen bincike_bincike yake, wanda ta san duk akan al'amarin Neehal ɗin ne. Bayan ya dawo daga Masallacin ɗakin Hafsat ya zarce, ya tarar da ita kwance lullub'e da bargo babu alamun ta tashi ta yi Sallah. Ya shiga tashin ta a hankali. Ta buɗe ido da yake baccin nata ba wani nisa yay ba, sai da aka shiga sallah ya ɗauke ta. Ta riƙe hannunsa idanunta ƙur a kansa, cikin kissa ta ce. "Baby." Tana tashi zaune. Bai amsa mata ba sai zare hannunsa da ya yi daga cikin nata yana haɗe rai, ta kuma san dalilin hakan saboda bata tashi ta yi Sallah akan lokaci ba ne. Sai ta ƙara riƙe hannunsa cikin damuwa ta ce. "Baby a kwana ɗaya har ka faɗa, nima jiya kwata_kwata ban samu bacci ba, saboda damuwar ɓatan sister, sai yanzu gab da Asuba na ji ya ɗauke ni, dan Allah ka kira Mum ka tambaye ta ko an ga Neehal ɗin, ko kuma an samu labarin inda ta je, hankalina gaba-d'aya a tashe yake." Ya saka ɗayan hannunsa ya shafi gashin kanta cikin sanyin murya ya ce. "Go and pray First." Ta gyaɗa masa kai cikin nuna tsantsar damuwa. Ta sakar masa hannunsa ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet zuciyarta fal da murna, dan yanda ta ga yanayin Ameen ta san babu wani daddaɗan labari, ta k'udurce a ranta tana idar da Sallah zata kira Mama dan jin ƙarin bayani, a zuwan da damuwar abun ta kwana kamar yadda ta nunawa Ameen. Shi kuwa da ya koma ɗakinsa ɗorawa ya yi daga inda ya tsaya a aikin da yake yi, babu alamun yana da niyyar fita yau.....














Neehal tana nan zaune a bakin ƙofa ta ji ana taɓa handle ɗin ƙofar ta waje. Ta zabura ta miƙe tsaye ta manne a jikin bango jikinta na ƙyama, jin an turo ƙofar ɗakin ta runtse idanta a tunaninta sun biyo ta nan ne domin su far mata. Jin shiru har na wasu sakanni bayan turo ƙofar yasa ta buɗe ido, farin saurayin nan da ya kawo mata abinci d'azu ta gani yana kallon ta. Ya tako a hankali zuwa gaban ta ya kama hannunta ya ce. "Ki nutsu ƴan'mata, zan fitar dake daga gidan nan yanzu amma sai kin nutsu kin kuma yi komai cikin lura. Da sauri Neehal ta gyaɗa masa kai alamun gamsuwa. Ya ce. "Ki zauna anan, yanzu zan je na lalata wutar gidan haske ya ɗauke, kafin su gyara Insha Allahu zan fitar da ke. Cikin marainiyar murya Neehal ta ce. "Na gode, na gode sosai bawan Allah." Ya jinjina mata kai sai kuma ya juya da niyyar fita idanunsa suka sauka akan wayarta dake tsakar ɗakin, ya waro Ido cikin alamun mamaki. Da sauri Neehal ta zo ta tattare wayar data tarwatse ganin yanda yake kallon ta, ta haɗa ta ta kunna ta. Bai ce komai ba ya juya ya fita. Neehal ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ƙara dialing Numbern Mama, amma still bata tafiya network is not available ake rubuta mata. Kamar ta yar da wayar sai kuma ta zira ta a cikin aljihun rigarta. Ta koma ta rakub'e a kusurwar ɗakin tare da rafka tagumi da hannu biyu. Bayan mintuna biyar ta ga hasken ɗakin ya ɗauke sai duhu dumɗum, ta ƙara mannewa a cikin bango jikinta na ƙyarma. Ko minti biyu ba'ai ba ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo, muryar saurayin ta ji yana faɗin. "Taso da sauri ba mu da ishashshen time." Neehal ta tashi cikin sauri kamar yadda ya ce ta yi inda ta ji sautin muryarsa saboda bata ganin sa, sai da ta matso kusa da shi ne ma ta ga alamar duhun mutum a tsaye, ya kamo hannunta cikin raɗa ya ce. "Duk inda nasa ƙafata ki saka taki, amma sai kin yi sauri fa dan yanzu zasu gyara wutar, kuma gidan nan gaba-d'aya a zagaye yake da CCTV camera, duk inda muka gilma akwai masu kallon mu." Neehal ta gyaɗa masa kai. Ya buɗe ƙofar suka fita yana jan ta, dan gudun ma gagarar ta ya yi ta kasa yin sa, sai faɗuwa take musamman idan suka zo gurin shan kwana, amma kuma sai ta miƙe zumbur saboda tamkar gudun ceton rai take. Suna fitowa daga corridor ɗin gidan wutar gidan ta dawo, saurayin ya waro ido waje cikin alamun tsoro, dan ya san kafin sukai bakin gate waɗanda suka gyara wutar sai sun gan su, ya tsaya ya fara tunanin mafita. Neehal ta shiga kalle_kalle a makeken harabar gidan. Bai gama tunanin ba ya ji alamun tafiya, ya yi saurin jan hannun Neehal suka zagaya baya, suna zuwa bayan ya hangi mutum uku suna tahowa, ya yi saurin yin ƙasa tare da jan Neehal suka b'uya a bayan wani gini. Ta daf da ginin mutanen ukun nan suka zo suka wuce, ɗaya daga cikinsu har da juyowa, ai kaɗan ya rage Neehal bata saki fitsari ba. A tare suka saki ajiyar zuciya bayan mutanen sun ɓace wa ganin su. Saurayin ya miƙe hannunsa cikin na Neehal ya ce. "Gudu zaki yi sosai mu samu ki fita daga gidan nan, dan na san zuwa yanzu sun fara nemanki, mintuna kaɗan kuma ya rage ragowar ƴan ƙungiya da sarauniya su ƙaraso gidan nan dan bikin murna." Neehal da zuwa yanzu ta fara sarewa ta gyaɗa masa kai numfashinta na fita da ƙyar. Ya ja hannunta suka falfala da gudu yana yi yana waiwaye, cikin ikon Allah har suka ƙarasa gate ɗin gidan babu wanda ya gan su. Sai dai gate ɗin a kulle yake da gark'amemen ƙwado. Saurayin ya dafe kansa cikin takaici dan gaba-d'aya ya manta da akwai sauran rina akaba, wato ta yanda zasu fice daga gidan. Kallon ɗakin mai gadi ya yi sannan ya juyo ya kalli Neehal wadda ke ƙoƙarin sumewa. Ya ja ta dan tafiya ma neman gagarar ta take, a bakin ƙofar ɗakin mai gadi suka tsaya, ya zaunar da ita shi kuma ya tura ƙofar ya shiga. Mai gadin yana zaune kishingid'e, jin an shigo ya tashi zaune sosai. Saurayin ya ƙaƙaro murmushi ya ce. "Malam Buba ana hutawa ne?" Malam Buba ya washe baki ya ce. "A'aa, Malam sagiru kai ne, sannu da zuwa farin mutum ganin ka Alkhairi ne." Sagir ya ce. "Yau an gama abinci da wuri, kuma baka zo ka kawo kwano ba." Buba ya ce. "Ai na ga lokaci bai yi ba ne shi yasa." Sagir ya ce. "Ka san yau muna da shgali fa shi yasa aka gama da wuri, yanzu dai ɗauko kwanan naka kar wanda ya fi maik'on ya ƙare." Buba ya ƙyalƙyale da dariya ya tashi ya ɗauko flaks ɗin da ake zuba masa abinci ya miƙawa Sagir, Sagir ya karɓa ya buɗe ya ce "Dan daurayo shi dai a bayan gida Malam Buba, na ga da ɗan maik'o a cikinsa." Buba ya ce. "Toh Sagiru daɗina da kai akwai tsafta." Sagir ya yi murmushi kawai yana wurwurga idanunsa a ɗakin yana neman inda zai ga makullan gidan. Cikin sa'a ya ga malam Buba ya ajiye su akan wani ɗan table ya shige toilet. Jikinsa har rawa yake ya ɗauka tare da juyawa ya fice daga ɗakin da mugun gudu, inda ya bar Neehal anan ya tarar da ita. Ya kama hannunta suka nufi get ɗin da gudu, ya lalubo key ɗin ƙofar ya shiga bubbud'e makullan gidan kusan guda goma, yana yi yana waiwaye. Yana gama buɗewa ya hango Buba ya fito daga ɗakinsa a gigice, ya kama ƙaramar ƙofar gate ɗin ya buɗe ya tura Neehal waje sannan shi ma ya fita, ya damk'i hannunta suka falfala suka yi gabas da mugun gudu. Tafiya sosai suka yi sannan Neehal ta faɗi tana numfarfashi, cikin magana da ƙyar ta ce. "Ruwa, ruwa." Sagir ya ce. "Ki yi haquri ban san inda zan samu ruwa in baki ba, kuma dole anan zan barki in koma gidan da muka fito in karɓi hukunci na." Neehal ta ƙura masa ido ta ce. "Me yasa ka san za'a hukunta ka, ka taimake ni? Me yasa zaka koma gidan da da mutanen cikinsa babu Allah a ransu? Ka zo mu gudu tare mana." Sadik ya girgiza mata kai ya ce. "Duk inda na shiga a faɗin duniyar nan sai sun nemo ni, idan ban koma ba a yanzu za su tsotse jinin mahaifiyata wadda ita kaɗai ta rage mun a duniya, ni kuma da haka ta faru gwara ni su kashe ni." A ruɗe Neehal ta ce. "Tsotse jini kuma? Suna shan jini ne?" Sagir ya gyaɗa mata kai ya ce. "Eh suna shan jini, matsafa ne, kuma nima ina cikin su." Neehal ta waro Ido ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, me ya kaika cikinsu? kuma gashi ba kai kala da marasa imani ba." Sagir ya ce. "Baza ki gane ba ƴan'mata, amma abun da zan faɗa miki rashin imanin yan ƙungiyar nan ya wuce duk inda kike tunani, ni zan koma kafin azzaluman ƙungiyar da sarauniya su ƙaraso." Neehal ta ce. "Me yasa ka taimake ni?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce. "Saboda Yayanki Al'ameen, ya taɓa mun wani taimako da bazan taɓa mantawa da shi ba a rayuwata, kalamanki na d'azu a lokacin da na kawo miki abinci su suka tunzura ni akan na taimake ki, domin na san kamar yadda kika faɗa da ƙanwata ce na ga ana ƙoƙarin keta mata haddi sai inda ƙarfina ya ƙare a ceton ta duk da bani da ƙanwar ban san daɗinta ba ni kaɗai iyayena suka haifa. Dan haka na yi amfani da wannan damar gurin sakawa Ameen da Alkhairin da yay mun na taimake ki, domin na san da zarar sauran ƴan ƙungiya sun zo babu abun da zai hana su aiwatar da ƙudirinsu a kanki sai dai wani ikon Allah. Ni ne na bar ƙofar ɗakin da kika shiga a buɗe saboda na san idan kin samu kin kub'uta nan zaki fara tunkara dan neman tsira." Ta ce. "Ta ya ya ka san ni ƙanwar Ameen ce?" Sagir ya yi murmushi ya ce. "Na sani kawai." Neehal ta ce. "Ya sunan ka?" Ya ce. "Sagir." Ta ce. "Na gode sosai Yaya Sagir da taimakon da ka mun, amma ina tsoron kar su kashe ka saboda ka fito da ni." Sagir ya ce. "Karki damu baza su taɓa kashe ni ba." Neehal ta sauke ajiyar zuciya numfashinta na fita da sauri_sauri. Sagir ya miƙe da niyyar tafiya Neehal ta tsayar da shi da faɗin. "One more question." Ya tsaya yana kallon ta bai ce komai ba. Ta ce "Wanda waɗannan mutanen suka kaini ɗakinsa shine wanda yake ƙoƙarin keta mun haddi? Shine wanda aka ce mun my virginity is for him? Shi ma ɗan ƙungiyar ne? Yana shan jini?" Sagir ya ce. "Kin ci sunanki ƴar jarida, Tamboyoyinki kuma amsar su gaba-d'aya *Eh* ce." A razane Neehal ta ce. "Real him ɗin shi fa, not fake face maks ɗin daya saka, kasan kuwa matsayin shi a gurina?" Sagir na ce. "Na sani kuma shi ne." Neehal ta dafe ƙirjinta da sauri saboda wata irin bugawa da zuciyarta ta yi a million. Hakan ya yi dai_dai da jin vibration ɗin wayarta da ta yi. Sagir ya juya ya tafi cikin sauri. Ta zaro wayar daga cikin aljihun rigarta da ƙyar saboda yanda kanta yake juya mata, ta danna gurin picking ba tare data duba mai kiran ba. Ameen wanda tun safe ya ɗora da kiran Numbobin Neehal sai yanzu cikin sa'a ya ji ɗaya ta shiga. A hanzarce ya ce. "Miemerh." Cikin magana da ƙyar ta ce. "Yaya...!" Ya ce. "Where are you?" Ta ce. "I dont know, please Yaya ka zo ka ɗauke ni." Ameen ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya ce. "Okay I will come

Please Login or Register in order to submit comment