Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi bana ƙare ba ne ta taka masa burki ta ce bai isa ya takurawa Ƴarta ba, tun da ba shi ya haifar mata ita ba. Sannan fa Neehal ta samu salama ya ɗan sararara mata. Allah ya ba wa Neehal farin jinin samari tun da ta fara tasowa, amma bata kula su saboda ba a bata damar hakan ba a gida. Jameel shine saurayin data fara kulawa da sunan soyayya, ɗan Kano ne amma a Abuja suka haɗu a wani Mall, a lokacin ya takura mata da naci har sai da ta ba shi phone Number ɗinta. Tun yana kiranta tana ƙin d'aga wa har dai ta fara sake masa. Jameel matashi ne Black beauty, gashi da nutsuwa hakan yasa Neehal ta ji ya kwanta mata a rai. A hankali soyayyarsa ta fara mamaye zuciyarta. Tun kafin tafiyarsu ta yi nisa ta gabatarwa da Mama shi, Mama ta yi murna sosai ta kuma sanar da Daddy dan a san abun yi. Mahaifin Jameel ba boyayyen mutum ba ne kasancewarsa ɗan siyasa ne, Daddy ma ya san sa. Soyayya sosai Neehal suka sha da Jameel kamar ba gobe, sai dai bayan an yi Engagement ɗinsu ba jimawa ya fita aka bishi aka harbe sa ya mutu. Mutuwar Jameel ta girgiza duk wani makusancinsa ciki har da Neehal kuwa, dan tun daga lokacin da ya rasu ta zama so silent. A lokacin ne kuma Jamb ɗinsu ta fito, sai dai Neehal ba ta ci point sosai ba duk da Kasancewar tana da ƙoƙari, Haneefah kuwa ta ci point da yawa, amma ganin Neehal bata ci ba harma ta yi apply a Kano state polytechnic sai itama Haneefah ta ce can zata ta fasa zuwa University tun da besty'nta ba can zata yi ba, ita ma ta yi apply a poly. Sun fara karatu cikin nasara a Management kasancewar su duka ƴan art ne, department of mass communication suke, dama ita Neehal choice d'inta kenan, burinta a rayuwa ta ga ta zama Jonorlist. Da wata shekarar ta zagayo suka sake yin Jamb, wannan karan ma Haneefah ce ta ci Neehal ba ta ci ba. Dole tasa Haneefah ta yi apply a Bayero University Kano inda ta fara karantar law, Neehal kuma ta ci gaba da Polytechnic ɗinta. Tana siwes suka haɗu da Anwar, da farko shi ma ba ta kula shi sosai, sai daga baya ta saki jiki da shi suka fara soyayya fiye da ma wadda suka yi da Jameel. Cikin ikon Allah Neehal ta gama school ɗinta successfully, bata taɓa carry over ba balle spill, tun kafin ta gama ta siyi D.E Form a Bayero ta cike da waiting result. Bayan ta karb'i result ɗinta suka bata admission direct level two ta ɗora karatunta, lokacin ita ma Haneefah ta shiga level two ɗin, sai matakin karatunsu ya zo ɗaya. Ba jimawa da shigar ta Bayeron aka yi Engagement ɗinsu da Anwar. Duk kawo kuɗin Neehal ɗin da za'ai sai Mama ta aikawa ƴan'uwan Neehal, amma daga ƴaƴan Baffa har Uncle Umar babu mai zuwa, Kawu Musa ne kawai yake zuwa a karb'i kuɗin da shi, Uncle Usman kuma ya yi nisa ba ya samun zuwa, ya kance sai bikin Neehal ɗin zasu zo shida iyalansa.






A lokacin da aka yi engaged ɗin Neehal aka buɗe gidan Television na ASTV. Wani abokin Daddy ne ya buɗe, hamshaqin mai kuɗi ne kuma sananne ne a ƙasar nan. Da kwalin Deplomer aka ɗauki Neehal aiki a gidan TV'n, Haneefah kuma da S.S.C.E Daddy ya sa aka mata alfarma ita ma aka ɗauke ta. Neehal abun nema ya samu ta zama Jonorlist sai murna. Kafin Neehal ta fara aiki sai da aka kai ruwa rana da Ameen, dan da farko cewa ya yi baza ta yi ba. Mama ta ce, A nan bai isa ba kuwa, wanda zai aure ta ma bai hana ta ba sai shi ɗan karere. Har wannan lokacin dukiyar Neehal tana hannun Uncle Umar yana juya ta, babu wanda ya ce masa k'ala a kanta, su Fauziyya da aka ga Neehal a gidan TV baƙin ciki kamar ya kashe ta, musamman da ta ga yanda ta ƙara kyau ta zama ƴar gayu wanke hannu ka taɓa, gashi ko ta ina samun masoya take rututu a faɗin ƙasar nan.














*CIGABAN LABARI.............✍️*












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:48] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_








*3️⃣4️⃣*














Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












.............Washegari bayan an yi sallar asuba, Daddy ya dawo daga masallaci Mama ta sanar masa abun da Aunty Sadiya ta faɗa mata, dan jiya bai dawo da wuri ba shi ya sa bata faɗa masa ba. Zarya yake ta yi a ɗakin baccinsa, Mama kuma tana zaune a gefen gado ta yi tagumi cikin tunanin mafita. A hankali ta ɗago da idanunta da ba su samu isasshen bacci ba a daren jiya saboda fargaba ta dubi Daddy ta ce "Daddy ka zauna mana, ka bar wannan safa da marwar ka zo mu nemi mafita akan wannan al'amarin." Daddy ya sauke numfashi tare da goge gumin da ya kwanta a kan goshinsa ya ce "Al'amarin ne ya girgiza ni ba kaɗan ba Doctor." Mama ta sauke tagumin data rafka bata ce komai ba. Daddy ya zauna a kan bedside locker yana fuskantar Mama ya ce "Zuciyata ta kasa yarda da wannan abun Doctor, ba zan taɓa yarda saboda Daughter ake wannan kisan ba gaskiya." Cikin karaya Mama ta ce "Saboda me zaka ce haka? Kar fa ka manta mahaifan Neehal ma fa kashe su a kai, kuma har yau an kasa gano waɗanda suka yi kisan da kuma dalilin da yasa aka kashe sun. Haka su Jameel suma har yau an kasa gano waɗanda suka kashe su, ai ko aljanu ke kisan nan ya ci ace zuwa yanzu asirinsu ya tonu." Daddy ya ce "Ka da ki la'akari da haka, zata iya yiyuwa mahaifan Neehal b'arayi ne suka kashe su ko kuma wani mak'iyin Abbanta, kin san idan mutum ba ya k'aunar ka a shirye yake da ya aikata komai a kanka. Sannan na biyu kuma Jameel, mahaifinsa ɗan siyasa ne abokan hamayya babu abun da baza su iya ba suma a kan mutum, tun lokacin da aka kashe Jameel tunanin da kowa ya yi kenan ciki har da mahaifinsa. Sai kuma Anwar, wanda shi kaɗai ne ma babu wani dalili a rayuwarsa da a yi tunanin zai sa a kashe sa." Mama ta sauke numfashi ta ce "Yanzu dai a takaice kana son ka ƙaryata abun da Sadiya ta faɗa kenan? Ko kuma kana son ka kwantar mun da hankali ne kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ganni a cikin damuwa? Daddy! Wannan maganar ba fa ƙaramar magana ba ce, ina tsoron abun da Sadiya ta faɗa ya tabbata." Daddy ya ce "Ko kaɗan ba ina nufin na ƙaryata Sadiya ba ne domin akan aikinta take, kuma ban san hujjar data gani ta faɗi haka ba, kawai dai ina son nusar dake wani abu ne." Mama ta ce "Wanne abu zaka nusar da ni? Hmm Daddy kenan, ni fa na riga na gano ka, kawai kana san kwantar mun da hankali akan wannan al'amarin ne." Daddy ya yi shiru domin tabbas abun da Mama ta faɗa haka ne, yana son ya kwantar mata da hankali ne kawai amma tabbas shi ma maganar ta girgiza zuciyarsa ba kaɗan ba, ya manta rabon da ya ji abun da ya firgita zuciyarsa irin wannan. Mama ta ce "Ya Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan abun, ka tona asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari da gaggawa." Daddy ya ce "Ameen ya Allah, abun da ya dace dama mu dage da yi kenan addu'a, Insha Allahu gaskiya zata bayyana." Kusa da Mama Daddy ya dawo ya kama hannunta ganin damuwa ƙarara a fuskarta ya ce "Please Doctor ki rage damuwar nan da kike, kin san Neehal ɗin ma idan ta ganki a haka itama zata shiga damuwar ne, ina jarumtar dana san ki da ita ne? Haba matar soja uwar soja." Mama ta sauke numfashi ta ce "Idan ka ga na daina damuwa to naga na aurar da Neehal, shine kawai hankalina zai kwanta." Daddy ya miƙe ya ce "Insha Allahu zaki gani, ai shi aure hab'o ne idan lokacinta ya yi dole sai ta yi, fata kawai Allah ya kawo mata miji na gari, wanda zai riqe mana ita da amana ko bayan ranmu." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Daddy yana buɗe wardrobe ɗinsa ya ce "Yanzu ita Neehal ɗin akwai wanda take kulawa ne?" Mama ta ce "Gaskiya a sani na babu kowa." Daddy ya ce "Wannan yaron da yake zuwa fa wani ɗan fari dogo haka?" Mama ta ce "Sadik kake nufi wai?" Daddy ya ce "Ehh, Barrister ne shi ko?" Mama ta ce "Ehh, a unguwar su A'isha gidansu yake." Daddy ya ce "Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Mama ta ce "Ameen." Car key Daddy ya miƙawa Mama ya ce "Gashi ki ba wa Daughter." Mama ta karb'a cikin mamaki ta ce "Mota ka sai mata?" Daddy ya ce "Ehh mana, alƙawarin dana mata ne tun sanda ta gama Polytechnic kika hana a bata a time ɗin." Mama tana murmushi ta ce "Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi ya tsare, ai yanzu ta ƙara hankali zan bar ta ta yi driving ɗinta. Mun gode sosai fa Allah ya ƙara buɗi mai albarka" Daddy ya ce "Ameen ya Allah. Mama ta miƙe ta ce "Bari in je inwa Daughter albishir, na san zata yi farin ciki sosai." Daddy ya yi murmushi cikin jin daɗin ganin Mama na murmushi, saɓanin d'azu da damuwa ke kwance a kan fuskarta. A duk duniya abun da ke d'aga masa hankali kenan ya ga iyalinsa a cikin damuwa, da yana yanda zai yi da sai ya magance wa Neehal wannan K'ADDARAR data shigo cikin rayuwarta, amma babu yanda zai yi komai rubutacce ne tun fil'azil daga Ubangiji Mai girma da ɗaukaka, amma ya ɗaukar wa kansa alk'awari sai inda ƙarfinsa ya ƙare a game da binkicen wannan al'amari, a matsayinsa na k'wararren soja.










Zaune a kan darduma Mama ta tarar da Neehal ta jingina jikinta a jikin gado, Sallamar Mama yasa ta ɗago da kanta tare da amsa mata. Mama ta zauna a bakin gado tana dubanta. Neehal ta ce "Ina kwana Mama." Mama ta ce "Lafiya k'alau, me ya samu idanki?" Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce "kuka kika yi ko? kuka dai ba ya maganin duk wata damuwa, addu'a ita ce kawai mafita." Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta kalli su Afrah dake bacci ta ce "ƴan rigimart taki ba su tashi ba kenan?" Neehal ta ce "Ehh ni Mama dama ina son na faɗa miki me zai hana a saka su a makaranta kafin Allah ya bayyana iyayensu, kin ga idan na tafi school ko aiki kema in kin tafi asibiti sai su kaɗai fa a gidan, su Aunty Dijee ma kin ga suna zuwa islamiyya da yamma." Mama ta ce "Hakane kin kawo shawara mai kyau, ranar Asabar in Allah ya kai mu sai a kai su tahfiz, ranar Monday kuma sai na kai su school." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Mama ta ce Ameen, ga saqo in ji Dad ɗinki." Neehal ta miƙa hannu dan karɓar abun da Mama take miƙo mata tana faɗin "Saqon mene?" Kafin Maman ta bata amsa ta gani da idonta, waro ido ta yi waje tana murmushi ta ce "Mama kar dai ki ce mun wannan nawa ne Dad ya siya mun Mota?" Ita ma Mama tana murmushin ta ce "Ban ce ba to, amma ni dai saqo aka bani kuma na isar." Neehal ta rungume Mama da sauri cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah, amma fa Dad ya iya surprise." Mama ta ce "D'aga mun jiki ni, sai a kula da titi sosai tare da kasancewa cikin addu'a a kodayaushe." Neehal ta ce "Insha Allah Mamana." A take Neehal ta tafi part ɗin Daddy ta masa godiya sosai, Mama ce ta yi musu breakfast yau dan ta san murna ba zata bar Neehal ta musu cikin nutsuwa. Ƙarfe tara da ƴan mintuna Neehal ce zaune a gaban mudubi tana ɗaura d'ankwalin atamfar dake jikinta, ɗinkin riga da skirt ne ya mata das a jikinta. Bayan ta gama ɗaura d'ankwalin ta saka ɗan kunne fashion mai kyau kalar one colour na jikin atamfar, sannan ta ɗaura agogo a left hand d'inta, ta zira abun hannu a right. Masha Allah ta yi kyau sosai small pink lips ɗinta sun sha white lipstick sai k'yalli suke. Su Afrah dake zaune a kan carpet ɗin bakin gado suna break, ganin ta miƙe ta ɗauki mayafinta dake kan gado suka miƙe su ma da sauri suna haɗa baki gurin faɗin "Zan biki Aunty." Neehal ta kalle su ta yi murmushi sannan ta kama hannuwansu ta ce "Bana faɗa muku school zani ba, ku bari idan na dawo da yamma za mu je unguwa Insha Allah." Suka gyaɗa mata kai ba dan ransu ya so ba. Neehal ta yi picking goshinsu sannan ta ce su tafi ɗakin Mama ta musu wanka idan sun gama break ɗin. Ta yafa mayafinta wanda ya kasance babba ne amma ba me kauri sosai ba, sannan ta ƙara fesa perfumes ɗinta ta zira plate shoe d'inta ta ɗauki jakarta da car key ɗinta ta fice daga ɗakin tana yi wa su Afrah bye_bye. A falo ta tarar da Mama ta ce mata "Mama zan tafi sai na dawo." Mama ta ce "Allah ya kiyaye ina yaran fa?" Ta ce "Suna ɗaki suna break in sun gama na ce su zo ki musu wanka." Mama ta ce "To Allah ya bada sa'a, ki kula da titi fa kuma kar ki manta da addu'a." Neehal tana fita daga falon ta ce "Insha Allah Mamana, bye." A parking space kamar yadda Daddy ya ce mata Motar ta tana can, a nan ta ganta. Ta sa key ɗinta ta buɗe murfin Motar da bismillah sannan ta yi addu'a ta shiga zuciyarta cike da farin ciki, gaba-d'aya damuwar data kwanta da ita daren jiya a ranta ta ji duk ta gushe, Daddy ya faranta mata ba kaɗan ba, a rayuwarta tana son ta ga tana driving, tun da Daddy ya so siya mata Motar amma Mama ta hana. A hankali take driving ɗin cikin nutsuwa da kula, sai dai ba ta yi nisa da tafiya ba ta ga wata Motor kamar tana binta a baya, ba ta kawo tunanin komai a ranta ba, tafi zaton may be hanya ce ta haɗa su ɗaya da mai motar, sai dai yanda take driving ɗin a hankali ya ci a ce mai Motar ya zo ya wuce ta kamar yadda wasu motocin ke yi. Cikin ikon Allah ta ƙarasa har cikin Bayero lafiya, kuma har ta zo bakin gate ɗin makarantar Motar na biye da ita a baya. Ƙarfe biyu suka gama last lecture ɗinsu, ko Sallah bata tsaya yi ba ta yi wa Freinds ɗinta sallama ta yo gida, saboda tana son ta je gidansu Haneefah ta nuna mata sabuwar Motarta.Tana fita daga get ɗin makarantar ta hau kan titi kenan ta mudubi ta ga kamar motar d'azu ce ke kuma binta, ita tama manta da batun wata motar d'azu, dan ta yi tunanin mai Motar shima Bayeron zai je a d'azun. Gabanta ya yanke ya faɗi tsoro ya fara ziyartar zuciyarta, hakan yasa ta shiga karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da hasbinallahu'wani'imal'wakil. Har ta ɗan samu nutsuwa a ranta ta cigaba da driving ɗinta. Wata zuciyar na faɗa mata ƙila ma ba Motar d'azun ba ce irinta ce kawai. Sai dai kuma kamar ɗazun duk inda ta yi nan Motar itama take bi, har tafiya ta fara yi a slow wai dan ta ga ko Motar zata zo ta wuce ta amma still dai motar tana bayan tata..........✍️








*Na so page ɗin ya fi haka tsawo, amma tun daren jiya ban jin daɗi, yanzu ma dauriya na yi na muku wannan ɗin*












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:50] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_








*3️⃣5️⃣*














Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














...........Har ta ƙarasa gida Motar tana biye da ita a baya. Sunayen Allah tsarkaka take ambata a ranta, kuma cikin k'udurarsa da ikonsa ya kawo ta gida lafiya. Sai da ta shiga layinsu sannan ta ga Motar ta daina bin ta. Tab'e baki ta yi a fili ta ce "Allah kai ne sarki, Allah ka kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri, Allah da kai na dogara kuma kariyarka nake roqa a kodayaushe." Da haka ta shiga cikin gida ta yi parking motar sannan ta fito a gajiye ta yi cikin gidan. Zulai ce ta zo ta buɗe mata ƙofa, "Sannu da zuwa." Ta faɗa tana bata hanya. Neehal ta ce "Yawwa Aunty zulai, ya gida." Zulai ta ce "Lafiya k'alau." Daga haka Neehal ta wuce sama. Ɗakinta ta nufa ta ajiye handbag ɗinta, ganin su Afrah ba sa dakin ta fito ta nufi ɗakin Mama. A kan gado ta tarar da su sun baje suna bacci, da alama kaɗaici ne ya ishe su, tunda ta san ba su fiya baccin rana ba. Mama bata nan ta je aiki, dama ta san ba zata dawo ta same ta ba. Ɗakinta ta koma ta shiga toilet ta ɗan watsa ruwa tare da yin tsarki ta ɗauro alwala, bayan ta idar da Sallah ta sauka ƙasa ta zuba abinci a ƙaramin plate ta ci. Ganin har uku ta wuce yasa ta koma sama da sauri dan shiryawa. Wayarta ta ɗauka ta ga missed call na Uncle Usman, murmushi ta yi sannan ta siyi kati daga banki a sim ɗinta na 5k sannan ta kira shi. Yana d'agawa ta ce "Assalamu alaikum." Uncle Usman ya amsa mata, ya ƙara da faɗin "Daughter kin manta da ni ko?" Neehal ta shagwabe fuska kamar yana ganin ta ta ce "Haba Uncle ni na isa in manta da kai a rayuwata? ai ɗiyar kirki bata taɓa mantawa da ubanta ko dan neman albarkarsa." Uncle Usman ya yi murmushi mai sauti ya ce "To ƴar gidan Uncle, ya school ya office." Neehal ta ce "Lafiya k'alau Alhamdulillah, ina Auntynah da takwarata?" Ya ce "Suna nan k'alau, dafatan dai komai lafiya ko Neehal?" Ta ce "Lau lau my Uncle, ya kasuwa?" Ya ce "Kasuwa Alhamdulillah, gashi ma ta hana ni zuwa in ga ƴata." Neehal ta ce "Babu komai Uncle, Allah ya taimaka. Nima Insha Allahu wannan hutun da zamu yi zan yi ƙoƙari in zo Niger ɗin." Uncle Usman ya ce "Allah ya kai mu ya kawo ki lafiya." Neehal ta ce "Ameen." Ya ce "Ya Mama da Daddy da Aunty A'isha da Aunty Sadiya da wajen su Hajiya?" Ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau." Uncle Usman ya ce "Masha Allah, haka ake so Allah ya yi mana jagora. Ni kwa na ce Neehal har yanzu ba kya zuwa gidan Ya Umar da Gabasawa?" Neehal ta had'iye wani abu da ya tsaya mata a mak'oshi ta ce "Bana zuwa Uncle, tun da duk sun nuna ba sa son na rab'e su, kowa na je inda yake sai ya dinga wulaqanta ni kamar wadda ba jininsu ba, na rasa me nay musu, mutuwar iyayena ce lefi a gare su ko kuma riqona da Mama take yi? Dama Uncle idan iyayen mutum sun rasu sai ya zama abun ƙyamar a cikin zuri'arsu?" Ta ƙarashe zancen hawaye na zuba akan kuncinta. Uncle Usman ya danne ɓacin ransa ya ce "Don't cry Daughter please, ba dan na saki kuka na tambaye ki ba, na tambaye ki ne saboda ina son sanin ko an samu cigaba sai dai kash bayananki sun tabbatar mun jiya i_yau ake bata sauya zani ba, amma har su Mubarak ɗin Ummi suma ba kya zuwa wajensu?" Neehal ta ce "Ai Ka san yanzu ba sa Gabasawa suna Lagos acan suke neman kuɗin su, amma Mama ta ce Insha Allahu watarana zata kai ni gurinsu da kanta, tunda ba ni da kamar su a duk faɗin duniyar nan." Uncle Usman ya ce "Allah ya ba da iko." A ransa yana jinjina ƙoƙari irin na Mama da kullum ita dai burinta ta ga Neehal tana zumunci da danginta kamar kowa, wani b'arin na zuciyarsa kuwa cike yake fal da tausayin Neehal. Ganin har yanzu kamar bata saki ranta ba da zancen su Uncle Umar da yay mata sai ya kawar da zancen inda cikin sigar tsokana ya ce "To a bani labarin sabon surikina." Murmushi ne ya zubce mata ba tare da shirya yin sa ba sai dan yanayin yanda Uncle Usman ya yi maganar, don sosai take jin k'uncin da ɓacin rai a duk lokacin data tuno da yanda danginta suka manta da rayuwarta a cikin tasu rayuwar. Uncle Usman ya ce "Ko baza a bani ba, na ji kin yi shiru!" Neehal ta ce "Ai babu ne Uncle." Ya ce "Kai haba, Ni dai na san my Daughter bata da baƙin jini, sai dai idan korar surukan nawa take." Neehal ta ce "Dagaske babu Uncle." Uncle Usman ya ce "Allah ya kawo na gari to, mu sha biki mu rak'ashe." Neehal ta yi murmushi cikin jin kunyarsa, wani b'arin na zuciyarta kuma fargaba ce fal a ciki, dan ita ba ma ta kawo wa kanta aure a yanzu, to idan ma zata yi auren wa zata aura? Sun ɗan taɓa hira kaɗan wanda gaba-d'aya zolayarta Uncle Usman yake, har sai da ya ji ta ware tana ƙyalƙyala dariya sannan suka yi sallama bayan ya ce ta gaisar masa da Mama da kyau. Bata ajiye wayar ba ta kira layin Haneefah sai da ta katse wa sannan Haneefah ta d'aga. Neehal ta ce "Matar nan kin yar da ni." Haneefah ta ce "Faɗi da babbar murya, bacin yarwa ma har bi takanki na yi na take ƴar rainin hankali kawai." Neehal ta yi murmushi ta ce "Me yay zafi haka Besty?" Haneefah ta ce "Abun kan wuta mana, tun jiya na kira ki amma sai yanzu zaki kira ni." Neehal ta ce "Ki yi haquri ƙawata, yanzu dai ba ma wannan ba kina gida in zo in nuna miki wani abu." Haneefah ta ce "Ina gida, Nima da ma akwai abun da nake son faɗa miki." Neehal ta ce "To gani nan zuwa." Daga haka ta katse wayar. Kukan twins ta jiyo a falo, da sauri ta fita dan ganin mene ne. Abun da bata taɓa gani sun yi ba wato faɗa shi ta tarar suna yi, Amrah tana ta dukan Afrah ita kuma tana kuka. Ɗaukar Afrah ta yi tare da hararar Amrah ta ce "Me tay miki kike dukanta?" Amrah ta ce "Ita ta fara duka na." Afrah cikin ta ce "Ƙarya take ban dake ta ba." Neehal ta sauke Afrah ta tsugunna ta rungume su duka a jikinta ta ce "Ku daina faɗa kun ji babu kyau." Suka gyaɗa mata kai, Amrah ta cewa Afrah "Am sorry." Afrah ta ce "Me too." Neehal ta rungume su cikin k'aunarsu tana murmushi. A hankali kuma ta raba su da jikinta ta miƙe tsaye tana faɗin "Mu je in shirya Ku mu tafi unguwa." Afrah ta ce "Aunty gurin Daddy'nmu za mu?" Neehal ta ce "A'a ai ban san inda yake ba." Cikin sauri Amrah ta ce "Abuja, a Abuja yake." Neehal ta ce "Tom Shikenan, soon za mu je Insha Allah." Wanka ta musu ta shirya su sannan itama ta shirya tay wa su Dije sallama suka tafi. Ta kira layin Mama bata d'aga ba sai text message ta mata ta sanar mata ta tafi gidansu Haneefah. Abun mamaki da ɗaure kai gidansu Haneefan ma sai da ta ga Motar

Please Login or Register in order to submit comment