Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin itama Aunty A'isha ta ƙaraso gidan, bayan sun gaggaisa suka rankaya suka tafi a Motar Mama wanda direban Maman ne zai kai su. Suna tafe suna ƙara jimanta al'amarin a tsakanin su. Neehal dai ta yi shiru kawai tana sauran su. Aunty A'isha ta dube ta, ta ce "Daughter baki da lafiya ne?" Mama ce ta bata amsa da faɗin "Tun jiya dana faɗa mata zancen nan shine duk ta koma haka." Aunty A'isha da itama dauriya kawai take dan mutuwar tsohon Mijin nata da abokiyar zamanta ta dawo mata sabuwa a ranta. Ta kwantar da kan Neehal a ƙafaɗarta bata ce komai ba. Mama ta ce "Na kira Hajiya na faɗa mata, ta ce zata zo kafin Monday a yi zaman kotu da ita." Aunty A'isha ta ce "Allah ya kai mu, ya kuma sa a ƙarƙare shari'ar a ranar, kin san shari'ar ƙasar nan tsaf zasu iya cewa sun d'age shari'ar." Mama ta ce "Ai tunda waɗanda suka yi laifi sun amsa babu buƙatar wani jan magana na daban, hukunci kawai za'a yanke musu dai_dai da abun da suka aikata." Aunty A'isha ta ce "Haka muke fata dama." Bayan sun ƙarasa gidan Alh Ali Aunty A'isha ta kira shi ta sanar masa, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidansa ya aiko ya shigar da su. A wani babban falo aka sauke su, dattijuwar matarsa ta karɓe su hannu bibbiyu dan ta san da zuwan nasu. Alh.Ali ya yi mata bayanin komai. Kuma ta shaida fuskar Aunty A'isha dan kafin Abba ya rasu suna ɗan zuwa tsohon gidansu idan abu ya samu. Tana ganin Neehal ta ce "Wannan yarinya kamar an tsaga kara ita da mahaifiyarta." Da kanta ta musu jagora har falon Alhaji Ali. Yana zaune shi kaɗai a falon yana kallon labarai suka yi sallama, ya amsa musu cikin sakin fuska. Suka ƙarasa suka zauna matar tasa ta ce "Ga iyalan Alh.Muhammad sun ƙaraso." ya yi murmushi yana duban Neehal ya ce "Masha Allah, wannan ce Amaryar tawa?" Suka yi murmushi dukan su, Neehal ta ƙarasa ta tsugunna a gabansa ta gaishe shi. Ya amsa mata cikin fara'a da kulawa, su Mama ma suka gaishe shi, ya amsa musu. Aunty A'isha ta ce "Ya jiki kuma Alhaji? Ashe cuta ka sha Wlh ba mu da labari." Ya nuna ƙafarsa ya ce "Ciwon Ƙafa ne ya sako ni a gaba, na fi shekara biyar a zaune bata takuwa, kuma tunda muka je Saudiyya ake ta maganin, sai yanzu Ubangiji ya kawo sauqi." Mama ta ce "Subhallahi, Lallai kasha jinya Alhaji, Allah Ubangiji ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Suka amsa da "Ameen." Ya dubi Aunty A'isha ya ce "Ya ƙarin haquri rashin su Alhaji Muhammad, tun bayan rasuwar su ba mu ƙara haɗuwa ba, na samu labarin ma kin yi aure." Aunty A'isha "Haquri Alhamdulillah, ai tun bayan dana gama takaba na yi aure." Ya ce "Masha Allah, Allah ya raya zuri'a ya ƙara haqurin zama da juna. Su kuma Alh. Muhammad Ubangiji Allah ya ji k'ansu ya gafarta musu." Suka amsa da Ameen gaba_ɗaya. Daga nan suka shiga tattaunawa akan abun da ya kawo su. Inda Alhaji Ali ya sanar musu da cewa. "Bayan ya dawo daga Saudiyya ne ya bibiyi al'amarin, inda aka tabbatar masa har yanzu ba a gano wand'anda suka yi kisan ba, hankalinsa ya tashi ya dinga faɗa akan rashin tsaurarara bincike na ƙasar nan da ba'ayi, sannan ya saka lauyoyi da jami'an tsaro su binkito masa. To ana cikin haka ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kisan su Abba ya fito daga gidan yari bayan shekaru takwas daya shafe a gidan yarin, bisa laifin fashi da makami da aka kama shi da shi, dama irin ƴan daban nanne da masu kuɗi da ƴan siyasa suke amfani da su dan cimma wata buƙata ta su, daga zarar buƙatar tasu ta biya kuma da su da banza duk ɗaya ne a gurinsu. Bayan ya fito ya nemi wanda sukay kisan su Abban tare wanda shine yakasance kamar babbansu a jan ragamar aikin, ya buk'aci daya ba shi cikon kuɗin aikinsa, shi kuma wancan ɗin sai ya hana shi ya ce ya cinye. To saboda baƙin cikin cinye masa kuɗin da aka yi shine ya ɗauki alwashin sai ya tona musu asiri in ya so kowa ya rasa duk a kama su. Da kansa ya kai kansa Police station ya faɗi laifinsa, aka kuwa yi ram da shi nan take, sannan ya faɗi inda sauran biyun suke su ma aka je aka kamo su. Da farko su sun musa, amma da suka ji duka sai suka fadi gaskiya, suka ce tabbas su sukai kisan amma su ma wani mutum ne ya ba su kwangilar yin kisan. Yanzu haka suna Bamfai a tsare, Ranar Monday Insha Allahu za'a yi shari'ar a babbar kotun jiha, dan yanke musu hukunci dai_dai da abun da suka aikata. Sai dai har yanzu sun ƙi faɗar wanda ya saka su aikin, dan su yaran biyun dama ba su san shi ba, babban nasu ne ya san shi. Amma ana saka rai Insha Allah za su faɗi koma waye a zaman kotu, lauyoyinmu suna ta faɗi tashi akan haka. Na samu duk wannan bayanan ne ta bakin amintaccen lauyana wanda shi ne lauyan da zai tsaya a gaban kotu a matsayin lauyan iyalan Alhaji Muhammad Gabasawa dan ganin kotu ta bi musu hak'k'in su." Sai bayan Azhar su Neehal suka baro gidan nasa zuciyoyinsu cike da al'ajabi.








Ranar Asabar sai ga Hajiya ta zo Kano kamar yadda ta faɗa. Kwanakin nan da zazzaɓi mai zafi Neehal ta yi su, dan ko falo bata iya takowa ba tana kwance, ko toilet zata sai Mama ta taimaka mata. Ranar Monday ranar shiga kotu ta tashi jikin nata da ɗan dama, har ta yi wanka da kanta ta shirya. Daa Mama ta ce ta zauna a gida ba sai ta je court ɗin ba, amma ta ce zata iya zuwa ai ta ji k'warin jikin nata. Ƙarfe tara da ƴan'mintuna suka bar gidan gaba-ɗayansu har su Dije da Daddy zuwa court, dan ƙarfe goma za'a saurari ƙarar. Duk wannan abun da yake faruwa Ahmad da Sadik ba su sani ba dan Neehal bata sanar da su ba, tunda ko waya bata yi da ɗayan su ba saboda rashin lafiyar da take. Idan sun kira ta Mama ce take d'agawa. Sadik ya zo har sau biyu ya duba ta, Ahmad ma ya zo sau ɗaya ranar Sunday. Mama ta ce masa, dama bai wahalar da kansa ya zo ba tunda yana da nisa kuma dududu kwanansa uku da barin garin. Ameen kuwa tun ranar Friday da ya dawo garin every morning and night sai ya zo ya duba ta....










Ƙarfe goma dai_dai court ta cika ta tunbatsa da mutanen Daddy da suka samu labari da mutanen Alhaji Ali gami da wasu daga cikin abokan Abba, sai ƴan jarida da sauran mutane, har da su Uncle Umar da iyalansa da Kawu Musa. Uncle Usman ne bai samu damar zuwa ba. Shigowar Alk'ali yasa kotun yin tsit daga hayaniyar dake tashi a cikin ta, hakan kuma ya yi dai_dai da shigowar jami'an tsaro da waɗanda ake ƙara akan laifin kisan su Umma........✍️












_*Page ɗin yau bana soyayya ba ne, bare a cika mana kunne da team ɗin anace dana k'anin kurma.*_🏃‍♀️😉










*By*
*zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣9️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












...........Bayan Alk'ali ya zauna a mazauninsa aka miƙo masa wani ɗan abun rubuta da pen. Bayan 2 minutes wani mutum ya miƙe ya ɗan rankwafawa ya yi gaisuwa ga Alk'ali sannan ya fara karanto takardar dake hannunsa kamar haka "Zamu saurari shari'a ta gaba akan gisan gillan da wasu mutane suka aikata wa marigayi Alhaji Muhammad Gabasawa tare da mai ɗakinsa, shekara goma sha ɗaya da watanni da suka wuce." Sannan ya koma ya zauna. Neehal ta lumshe idonta bayan ta gama ƙarewa wadanda suka yi kisan kallo, zuciyarta na mata k'una. Barrister Murtala Gaya (Lauyan Alhaji Ali) ya miƙe ya kai gaisuwa ga Alk'ali sannan ya fara magana. "Sunana Barrister Murtala Gaya, Ni ne lauyan masu ƙara, ina roƙon wannan kotu mai adalci da ta yankewa waɗan nan azzaluman mutanen da suka yiwa Alhaji Muhammad Gabasawa da mai ɗakinsa gisan gilla hukunci dai_dai da abun da suka aikata." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Alk'ali ya ɗan yi rubuce_rubuce sannan ya d'ago ya dubi mutane ya ce "Ko akwai lauyan da yake kare masu ƙara?" Wani Barrister ne ya miƙe cikin girmamawa ya ce "Eh akwai ya mai girma mai shari'a. Sunana Barrister Garba Dan_ladi, nine lauyan dake kare waɗanda ake ƙara." Sannan shi ma ya ɗan rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya koma ya zauna. Barrister Murtala Gaya ya miƙe a karo na biyu yana duban Alk'ali ya ce "Ya mai girma mai shari'a ina son zan yi magana da waɗanda ake ƙara." Alk'ali ya ce "Kotu ta baka dama." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya yi fito daga gurin da yake ya ƙarasa inda masu laifin suke ya ɗan kare musu kallo na wasu sakanni sannan ya ce. "Kotu tana son sanin sunayenku da kuma yanda kuka gudanar da kisan kai ga Alhaji Muhammad Gabasawa da iyalinsa, tare kuma da son sanin wanda ya turo ku aikata hakan." Da sauri Barrister Garba ɗan ladi ya miƙe ya ce "Ina da ja ya mai shari'a, bai kamata Barrister Murtala ya dinga tambayar waɗanda ake ƙara wanda ya turo su aikata laifin da sukay ba, saboda ba don haka ake zaman wannan kotun ba." (Da alama dai wanda ya turo a kashe su Abba shine ya ɗauki Barrister Garba.) Barrister Murtala ya tari numfashinsa da faɗin "Dole ne in musu wannan tambayar ya mai girma mai shari'a, saboda waɗanda ake ƙara sun sanar da jami'an tsaro cewar turo su akay, amma sun ƙi faɗar ko waya ne, da alama an musu babban gargadi' ko barazana mai tsoratarwa. Mu kuma muna so mu sani saboda shi ma a nemo shi a duk inda yake a hukunta shi." Alk'ali ya dubi Barrister Garba ya ce "K'orafi bai karbu ba Barrister Garba." Ya mayar da dubansa ga Barrister Murtala ya ce "Barrister Murtala cigaba da tambayarka kotu na sauraren ka." Ya yi murmushi ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya ƙara maimaita tambayar da ya yi wa waɗanda ake ƙara. Ɗaya daga cikinsu ya ce "Sunana Hakim ilyasu." Sai babban nasu shi ma ya ce "Sunana Bilyaminu saminu." Na ƙarshen kuma ya ce "Sunana Zakari Mu'azu." Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce "Kotu tana sauraren ku, Malam Zakari da Bilyaminu da Hakim." Wanda ya fara faɗar sunansa wato Hakim ya ce "Watarana muna zaune da yamma ni da abokina Zakari......ya nuna Bilyaminu sannan ya cigaba da magana. Bilyaminu ya zo ya same mu a kan yana so zamu yi wani aiki tare da shi, ya tabbatar mana da za mu samu kuɗi mai tarin yawa a wannan aikin, cikin zumud'i muka ce masa za mu yi ko wanne irin aiki ne. Da farko da ya sanar mana aikin kisan kai ne mun tsorata, muka ce gaskiya baza mu iya ba, domin ba mu taɓa aikata hakan ba, iyakacinmu k'wace da haurawa gidan mutane, ko kuma raka irin su Bilyaminu fashi da makami. Amma Bilyaminu ya nuna mana ruwan kuɗi ya ce, mutumin da zamu yiwa aiki hamshaqin mai kuɗi ne, zai ninka mana kuɗin da muka gani a gurin Bilyaminu sau goma. Nan fa muka ruɗe mun ji zamu kuɗi, muka je mun amince amma fa muna tsoron kar a samu matsala. Bilyaminu ya ce babu matsalar da za'a samu, koma da an samu wanda ya samu aikin zai tsaya mana dan Babba ne a ƙasar nan, dan haka mu kwantar da hankulanmu babu abun da zai faru. Da jin wannan batu sai muka amince." Hakim ya ɗan numfasa, Barrister Murtala ya ce "Dama already kum san shi Bilyaminun ne kuna da alaƙa dashi?" Hakim ya ce "Ehh, babba ne shi a daba kuma kamar oga yake a gurin mu." Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce "Cigaba kotu na saurarenka ka sanar mata yanda kuka gudanar da kisan." Hakim ya cigaba da magana. "Tun a ranar Bilyaminu ya fara ba mu kuɗaɗe masu kauri, ya ce sauran kuma sai aiki ya kammala zai ba mu. Muka amince cike da k'warin gwiwa da murnar za mu samu kuɗaɗe. Bayan kwana biyu da daddare Bilyaminu ya zo ya ɗauke mu a wata Mota shida wasu mutane guda biyu, gaba-ɗayansu fuskokinsu a rufe da baƙin k'yalle. Wani ɗan gida ya kai mu ya ba mu wasu kaya bak'ak'e muka saka a jikinmu tare da baƙin k'yallen muma muka ɗaure fuskokinmu. Sannan ya bamu bindigu muka zira a aljihun wandunanmu. Bayan dare ya tsala muka fita a wannan Motar zuwa gidan mutumin da muka kashe, ta bayan gidan Bilyaminu ya yi parking motar muka fito ya buɗe ƙofar dake bayan gidan muka shige, shi ya yi mana jagora har cikin ɗakin baccinsu. Dama Bilyaminu ya sanar mana za su yi magana da mutanen, idan sun amince da buƙatarsa wadda ba mu san ta mene ba kar mu yi musu komai, idan kuma mun ji sun yi gardama mu sakar musu harbi. Bayan ya gama rad'a musu maganar da zai faɗa musu muka ji mai gidan cikin ƙaraji yana cewa ba zai taɓa amincewa da buƙatar su ba, da ido Bilyaminu yay mana inkiya. Babu jira ni da Zakari muka sakar musu bullet bibbiyu a ƙirjinsu, Bilyaminu ya ƙara musu ɗai_ɗai. Sauran mutum biyun da su zo ɗaukar mu tare da Bilyaminu waɗanda ba mu san su ba, su ba su yi harbin ba. Suna dai tsaye riƙe da bindigu a hannunsu. Mu ukun nan mu kai kisan." Ya yi shiru yana jan numfashi. Neehal ta runtse idanta hawaye mai zafi na zuba daga cikinsu. Aunty A'isha ma runtse idanunta tay tana tuno sanda ta ji ƙarar harbin a cikin kunnenta. Hajiya kuwa tsinuwar Allah take ja musu a cikin zuciyarta. Barrister Murtala ya jinjina kai cikin k'warewar aiki ya dubi Zakari ya ce "Ka ji duk abun da ɗan'uwanka ya faɗa, gaskiya ne?" Zakari ya ce "Eh haka ne." Barrister Murtala ya mayar da dubansa ga Bilyaminu wanda ko cikin duhu mutum yay gamo da shi zai tabbatar da rikak'k'en ɗan ta'adda ne. Saboda zubinsa da yanke yake muzurai da ido da kuma tabo_tabon yanka dake jikinsa. Ya ce "Malam Bilyaminu ka ji duk abun da Hakim ya faɗa haka ne?" Cikin shakak'k'iyar murya ya ce "Eh Haka ne." Barrister ya jinjina kai ya ce "Kotu tana san sanin wanda ya turo ku ku kay wannan ɗanyen aikin da kuma sanin ina sauran mutum biyun da ku kay aikin tare?" Bilyaminu ya ce "Sauran mutum biyun da mukay aiki tare ɗaya ya shek'a barzahu a cikinsu, ɗayan kuma yana kurkuku a halin yanzu sakamakon wani kisan da yay aka kama su, an yanke masa hukuncin d'aurin rai da rai. Batun wanda ya samu wannan aikin kuma wani babban mutum ne kuma sananne a ƙasar nan. Shi ya bani address ɗin gidan da za mu yi kisan, har yanda tsarin gidan yake da hanyoyin da zamu bi har zuwa ɗakin baccinsu, kuma shi ya ba ni mukullin da na yi amfani da shi na buɗe ƙofar gidan ta baya. Ban san dalilin da yasa ya ce mu je mu kashe mutumin da matarsa ba, ya dai faɗa mun kawai idan na je na nuna musu hotonsa, na ce masa za su amince da buƙatar da yake da ita a kan ƴarsu ko a'a? Idan sun je za su amince kar mu yi musu komai, idan kuma sun ƙi amince mu kai su k'iyama, dan za su iya tona masa asiri. A halin yanzu mutumin ba ya numfashi a doron ƙasa ya mutu shi ma. Kuma na riga na yi masa alƙawari bisa wani sharad'i namu na sirri ba zan taɓa faɗar sunansa ba a cikin wannan aikin ko me za'a mun kuwa." Barrister Murtala ya jinjina kai cikin gamsuwa ya ce "Ko zaka iya faɗawa kotu alaƙar dake tsananinka da mutumin da ya saka ku aikin." Ya ce "Eh, alaƙa ce kawai irin ta mai kuɗi da ƴan hark'alla irin mu, idan suna buƙatar aiki irin wannan su saka mu su biya mu da ƴan silalla." Barrister Murtala ya juyo ya kalli Alk'ali ya ce "Ya mai girma mai shari'a, ina son wannan kotu ta bani dama in gayyato wani bawan Allah wanda yake da masaniyar komai akan wanda yasa su Bilyaminu kashe su Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa. Tunda shi Bilyaminu ya ƙi faɗa" Alk'ali ya ɗan yi rubuce-rubuce ya d'ago ya ce "Kotu ta baka dama Barrister Murtala." Ya rank'wafawa ya ce "Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya ce "Ina son gayyato *Hashim Isma'il na_kowa* ." Alk'ali ya dubi mutane ya ce "Kotu na san ganin Hashim Isma'il na_kowa a gabanta." Alhaji Ali ya maimaita sunan a cikin zuciyarsa "Hashim Isma'il na_kowa?" Mamaki bai gama kashe shi ba sai da wani magidancin mutum da aƙalla zai yi shekaru arba'in a duniya ya fito gaban kotu, domin kuwa ɗan amininsa ne Alhaji Isma'il na_kowa, tsohon sanatan Kano ta tsakiya, kuma mutumin da yake matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Aunty A'isha ma mamakin ne ya kusa kashewa domin ta san mutumin a gurin Abban Neehal, mutuminsa ne sosai. Ba iya Aunty A'isha da Alhaji Ali kawai ambatar sunan Isma'il na kowa ya bawa mamaki ba, mafi yawan mutanen gurin sun cika da mamakin ganin ɗan *senator Na_kowa* a matsayin wanda zai ba da shaida. Wata mata kuwa har zabura ta yi ta miƙe, na kusa da ita su kay saurin mayar da ita ta koma ta zauna. Barrister Garba ɗan_ladi ma ya firgita ba kaɗan ba, dan har gumi ya fara gogewa, sai dai babu bakin magana tunda ba shi da abun cewa da kotu zata saurara. Bilyaminu ma ido k'walalo waje alamun razana yana kallon Hashim. Cikin nutsuwa Hashim ya faɗi sunansa kamar yadda Barrister Murtala ya ce masa. Sannan ya buk'aci da ya ba da shaida kamar yadda ya fito da nufin hakan. Ya gyara tsayuwa ya ce "Mahaifina Senator Na_kowa shine wanda ya saka su Bilyaminu yin wannan kisan." Kafin ya gama rufe bakinsa kotu ta barke da hayaniya gami da sallallamun jama'a. Alk'ali ya buga gudu ma tare da faɗin "Order." Nan dan kotun ta ƙara yin tsit kamar ba mutane a ciki. Alk'ali ya dubi Hashim ya ce "Cigaba da baya nanka kotu na sauraren ka." Ya cigaba da magana. "Watarana tun ina saurayi kafin na yi aure na je part ɗin mahaifina dan amsa kiran da yay mun. Ina shiga falonsa na ji yana waya a balcony inda yake cewa. "Kar ka damu mutumina, ko Alhaji Muhammad Gabasawa ya yarda ko kar ya yarda sai na biya buƙata ta da ƴarsa tunda zuciyata ta ƙwadaitu da ita, kasan bana had'iyar yawu a banza. Ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya kece da dariya ya ce, Kar ji komai na waje na kamar kaima ka huta da wannan yarinyar nan ne, kasan dama muna neman yarinya ta cikon goma kamar yadda boka ya ce mana akan aikin mu, to ina tabbatar maka da ita za'a za mu cike, zan biwa Gabasawa ta tallama ya bani ƴarsa in cika shi da ƴaƴan banki, idan kuma ya yi taurin kai kawar da shi a doran ƙasa ba wahala zai mun. Ya ƙara yin shiru na wasu sakanni sannan cikin dariya ya ce, Ah, to dan yana mutumina ai bai kai ya biyan buƙata ta ba a gurina. Ni fa dama dan na yi mu'amalar jin daɗi da shi na shiga cikin rayuwarsa, to kuma na fuskanci ba zai taɓa amincewa da buƙata ta ba, wai shi mai tsoron Allah, dan haka kawai zan huta ƴarsa ma ya wadatar. Wani irin juyawa na ji kaina yana mun, na yi baya da sauri na fice daga falon cikin tsananin tashin hankalin jin abun da mahaifina yake aikawa. Da ƙyar na iya ƙarasawa part ɗina na zube a kan kujera. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa ba tare da ya sani ba. Anan na gane mahaifina cikakken ɗan luwaɗi ne sannan kuma k'wararre a rapping ƙananan yara mata, duk a saboda neman duniya da mulki. Lokacin dana samu labarin rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa ko tantama ban yi ba na san aikin mahaifina ne, amma ban sanar da kowa ba saboda yanda idonsa ya rufe a neman duniya nima zai iya sawa a kashe ni matuƙar na faɗa. Sai dai cikin ikon Allah bayan rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da wasu kwanaki shima Dad Allah ya saukar masa da ciwo wanda aka rasa gane kansa da gindinsa. Ciwo kullum ƙara tsanani yake ana magani amma kamar ba'ayi. Ya shafe fiye da shekara biyu yana jinya kafin ya mutu, mutuwar da bana fatan duk wani wanda na sani a duniya ya yi irin ta. Domin kuwa babu alamar dacewa a tafiyar." Sai kuma ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. "Ganin ya rasu sai na bar abun a raina ban sanar da kowa ba, sai a cikin satin nan muka haɗu da Barrister Murtala ta sanadin wani abokina wanda shi ma Barrister ne, a nan ya ji yana bashi labarin case ɗin dake gabansa. Gabana ya faɗi amma ban sanar da shi komai ba a lokacin har muka rabu, sai daga baya dana koma gida na kasa zaune na kasa tsaye, na rasa abun da yake mun daɗi. A jiya ne na yanke shawarar na nemi Barrister Murtala na faɗa masa gaskiyar cewa mahaifina ne ya saka a yi wannan kisan, ko iyalan mamacin za su yafe masa dan ya samu sassauci daga azabtar Ubangiji. Da taimakon abokina kuma abokin Barrister Murtala na gano inda Barrister Murtala yake da zama na je na ba shi wannan labarin, shine ya buk'aci dana zo kotu yau na faɗa a gaban Alk'ali."






Kotun ta yi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen ciki, ba ƙaramin tashin hankali Alhaji Ali ya shiga ba da jin wannan labarin, tabbas da wanine ya faɗa masa wannan maganar ba ɗan cikin Senator na_kowa ba, ba zai taɓa yarda ba. Saboda yanda yake mutum na k'warai a idon al'umma, da kuma yanda yake nuna yana matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Lallai ka ji tsoron ɗan Adam ka kalle shi kawai, domin ba kowa ka san abun da ke cikin zuciyarsa ba. Neehal kuwa toshe bakinta ta yi saboda kukan da ya taho mata, kifa kanta ta yi hawaye na zuba a kan kuncinta kamar an buɗe famfo. 'Dan kare mutuncinta da ganin bata tozarta ta wulaqanta ba, aka kashe Ummanta da Abbanta? Tabbas babu wanda ya kay iyayenka k'aunarka a duk duniya, har abada ba zata yafewa Senator na_kowa ba da su Bilyaminu, ko da kuwa zata ga ana babbaka naman jikinsu a gabanta. Aunty A'isha ma kuka take yi, Mama kam ta daure zuciyarta sai jujjuya kai take tana da Allah wadai da wannan halin rashin imanin da zallar zalunci. Hajiya kuwa sai matsar hawaye ake tana ƴan maganganunta ƙasa_ƙasa. Sauran mutane wanda suka san yanda Abban Neehal suke mutunci da Senator na_kowa abun ya girgiza zuk'atansu. Barrister Murtala ya dubi Hashim ya ce "Kotu tana godiya bisa ga shaidar da ka bayar, zaka iya komawa ka zauna." Sannan ya dubi Bilyaminu dake ta aikin zazzare ido ya ce "Ka ji abun da Hashim ya faɗa, gaskiya ne Senator Na_kowa ne yasa ku wannan aikin?" Bilyaminu ya ce "Eh shine." Barrister Murtala ya yi murmushi ya mayar da dubansa ga Alk'ali ya ɗan rank'wafawa ya ce "Ya mai girma mai shari'a, ina roƙon wannan kotu

Please Login or Register in order to submit comment