Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta da kallo kawai yana sakin wani munafukin murmushi. A balcony suka ci karo da Mama, garin saurin da take har da tuntube ta yi. Mama ta ce. "Subhallahi, ki dinga kallon gabanki mana kina tafiya a hankali, kuma lafiyarki kuwa na gan ki kamar a firgice?" Tana sassauke numfashi ta ce. "Babu komai." Tare da shigewa falo. Mama ta tab'e baki ta sauka ƙasa abinta. Ta tarar Ameen ya zauna har lokacin bai bar murmushin da yake yi ba, ta yi masa wani kallo sannan ta zauna a kujerar dake facing ɗinsa. Suka ƙara gaisawa sannan Mama ta ce masa. "Ya na ga ka dawo?" Ya kama haɓa da hannunsa ɗaya ya ce. "Oh Mum, dan na dawo gidanmu laifi ne?" Mama ta ce. "Baka da gaskiya ne shi yasa na tambaya." Ya waro ido ya ce. "Rashin gaskiya kuma Mum?" Mama ta ce. "Ka fi ni sanin me ka yi ai." Ya yi murmushi ya ce. "I don't know fa." Mama ta ƙara ta tab'e baki ta ce. "Ai baza ka taɓa sani ba, wannan muskilancin naka yana k'ona mun rai, ka turo a sanar mana abu kuma ka san an sanar manan and still you can't say anything about it." Ya shafa kansa yana murmushi sosai ya ce. "Mum, what do you want me to say?" Mama ta ce. "Abun da ka je ka faɗa a zo a faɗa mana." Ya yi shiru still yana murmushi bai ce komai ba. Mama ta shiga mitar abun da yake ranta, harda ce masa alfarma ta yi kawai ta ba shi Neehal amma ba dan halinsa ba, babu yanda zata yi da Kawu Musa ne kawai. Shi dai murmushi kawai yake yi. Daga baya kuma ta koma yi masa faɗa da faɗin. "Ga Neehal nan Ameen, idan Allah ya yi auranku na baka amanarta, ka riƙe ta da amana dan Allah, ka ga yarinyar nan bata da kowa sai Allah, marainiyar Allah ce, idan ka zalunce ta Ubangiji bazai bar ka ba." Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, soyayyar Neehal da k'aunarta gami da tausayinta na ƙara narkar masa da zuciya. Daga nan part ɗin Daddy ya je wanda dama shi ya kira shi yana son ganin sa, shi ma faɗa da nasiha ya yi masa duk akan ya riƙe Neehal da amana ne. Neehal kam bata kuma fitowa ba tunda ta shige ɗaki dan bata san ta fito su haɗu kar ta je bai tafi ba. Wani irin tsoronsa da kunyarsa Ubangiji ya ɗoro mata tun daga lokacin data fara tursasawa zuciyarta karɓar sa a matsayin mijin da zata aura.








A daren Daddy bai jira komai ba ya kira Abba da wasu cousins ɗinsa ya sanar musu abun da yake faruwa, ya kuma faɗa musu a cikin week ɗin nan yake son akai kuɗin Auren Neehal gidan kawunta. Mama ta ce masa saurin me yake har haka? Ya ce mata baza ta gane yanda yake d'okin abun ba ne, a yanzu ba shi da wani sauran buri a rayuwarsa bayan ya ga Auran Neehal da Ameen..... Kamar yadda ya faɗa ranar Asabar wanda ya kama kwana biyar da yin maganar da yamma suka kai kuɗin na gani ina so gidan Kawu Musa. Ranar Neehal ji ta yi gaba-d'aya kamar ba ita ba, ita ce yau aka karb'i kuɗin Auranta da Ameen? Sai ta dinga jin abun kamar a mafarki, ta tabbata dai Auransu za'a yi da Ameen, ɓoye kanta ta yi a ɗaki ta ci kuka ta k'oshi. Su Daddy ba su baro gidan Kawu Musa ba sai da aka tsayar da lokacin biki wata uku masu zuwa, a haka ma da ƙyar Kawu Musa ya yarda, ya ce abun tunda duk na gida ne no need a ja lokaci, in san ransa ne bai ƙi a yi bikin a cikin two weeks masu zuwa ba. Da Daddy ya zo yana faɗawa Mama ta ce, ta san wannan duk shirin Ameen ne, shi yake zuwa yana zubawa Kawu Musa sintiri akan maganar bikin. A ranar bayan Magriba Ameen ya zo gidan kamar kullum, sai dai tun daga ranar da Neehal ta zura masa da gudu bai kuma ganin ta ba, dan b'uya take yi a ɗaki, ana yin Magriba zata shige ɗakinta ta kulle dan ta san shine time ɗin zuwansa gidan, bata fitowa har sai ta tabbatar ya tafi. Shi kuwa yana sane da ita da duk b'uyan da take, kuma ya san duk saboda shi ne, ƙyale ta kawai ya yi ya ga iya gudun ruwanta dan ya san akwai ranar ƙin dillanci. A ranar Mama ta ce masa ya sanar da Hafsat maganar bikin, ya amsa mata duk da bai so hakan ba, da ya so sai abun ya matso daf sannan ya sanar mata, amma yaya zai yi tunda Mama ta bayar da umarni dole ya bi. Bayan isha'i ya koma gidansa, ya tarar da Hafsat Hakimce a falon ƙasa ta ci uwar kwalliya ta tarb'arsa..........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._












..........Ranar Friday da yamma wanda ya kama bikin Neehal saura 4 weeks cif, tana zaune a ɗakin Mama suna hira dawowarta kenan daga gidan Alhaji Ali da ta je ta gaishe shi. Wayarta dake kan cinyarta ta fara ringing, ta ɗauka ta duba, ganin Sadik ne yake kiranta ta waro Ido cikin mamaki, duk da ta yi loosed wayoyinta a gidan ƙungiya amma Daddy yana fitowa ya siya mata sabbi dal guda biyu, ita kuma ta yi welcome back na Sims ɗinta. Amma da yake a email take sarving Numbers ɗinta tana ɗora shi akan wayar numbobinta suka dawo, that is why Numbern Sadik ta fito a wayarta with saved tunda bata goge ta ba ko bayan sun rabu. Ta d'aga tare yin sallama cikin sanyin muryarta. Sadik ya amsa mata tare da faɗin. "Neehal kwana dubu kin manta da Yayanki ko? Ko ɗan kira na mu gaisa ma ba kya yi." Ta ɗan murmusa ta ce. "Ka yi haquri Ya Sadik dan Allah, na san bani da bakin da zan kare kaina a gurinka." Ya ce. "Shikenan ya zan yi tunda kin ce Allah amma da ban yi niyyar haqura ba." Ta ce. "Toh Na gode, ya su Maamah da Batul?" Ya ce. "Suna nan k'alau, ya Mama da Daddy?" Ta ce. "Duk suna lafiya." Ya ce. "Masha Allah, ki gaishe su Please." Ta ce. "Za su ji Insha Allah." Ya ce. "Na manta lefin naki biyu ne ma a gurina, ashe bikinki ya taho amma babu labari Neehal?" Cikin mamaki ta ce. "A ina ka ji Ya Sadik?" Ya ce. "Zancen duniya yana b'uya ne? Amma dai Neehal baki kyauta mun ba da baki faɗa mun ba sai da abun ya zo daf nake ji." Ta ce. "To ka yi haquri, wannan ma na karb'i laifina." Ya ce. "Na ƙi yin haqurin." Ta shagwab'e ta ce. "Haba Yayana ni ce fa, ka haqura Please." Ya sauke numfashi ya ce. "Shikenan na haqura, Insha Allahu a cikin satin nan zan zo in gaishe da Mama." Ta ce. "Toh Shikenan sai ka shigo, Allah ya kawo ka lafiya." Ya ce. "Amin, sai anjima." Sai ta ji kamar ta tambaye shi yaushe ne nasa bikin, amma dai ta fasa ta ce. "Allah ya kai mu." Tare da katse wayar. Ta kalli Mama da hankalinta yake kan wayarta tana latsawa, can ƙasan ranta moment ɗin soyayyarsu da Sadik yana dawo mata. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta ce. "Mama Ya Sadik ne ya kira ni, ya ce yana gaishe ki." Mama ta ce. "Ina amsawa." Da daddare kamar haɗin baki sai ga kiran Ahmad ya shigo wayarta. Sai da gabanta ya faɗi saboda rabon da su yi waya da shi tun satin bikinsa da ya yi mata ban gajiya. Ta d'aga tare da ɗan bata fuska kamar yana ganin ta. Ya yi mata sallama ta amsa can ƙasan mak'oshi. Cikin taushin murya ya ce. "Princess!" Ta lumshe ido a hankali ta ce. "Na'am Uncle." Ya ce. "How are you?" Ta ce. "Lafiya k'alau." Ya ce. "Uhm, me Ahmad ya yi aka daina kula shi? babu kira babu magana a chat, sai dai in na je gidan Ummi ta ce mun kun yi waya da yaranki." Ta turo baki bata ce komai ba, a ranta tana cewa. 'Kai da ka yi auranka ka manta da ni amma kai kake mun complain.' Ya ce. "Hello, Princess." Ta ce. "Na'am." Ya ce. "Why are you silent?" Ta ce. "Nothing, Ka yi haquri Uncle." Ya ce. "No prob, na ji wani labari a gurin Ummi." Ta ce. "Labarin me?" Ya ce. "Na auranki mana." Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya ce. "Hmm, dole ki yi shiru tunda ke ma kin san baki kyauta ba, yanzu Princess ace za'a yi bikinki amma You can't tell me, sai da Mama ta kira Ummi ta faɗa mata sannan nake ji a gurinta." Yanda yake maganar ta gane ya ji haushi sosai, kamar zata yi kuka ta ce. "Ka yi haquri Uncle." Ya ce. "No, ai I'm not your Uncle right? Shi yasa baki faɗa mun bikinki ba" A shagwab'e ta ce. "You Are." Ya ce. "To me yasa baki faɗa mun ba." Ta ce. "Babu komai fa da gaske, I'm sorry." Ya ce. "Ba zan haqura ba, dan na san da ban kira ki ba yanzu baza ki kira ni ba." Ta ce. "Zan kira ka mana." Ya ce. "Eh zaki kira ni, amma sai nan da kamar 2 weeks haka ki ce na kawo miki twins ko?" Ta yi murmushi ta ce. "To yanzu tunda ka kira ni ai shikenan my Uncle sai ka yi haquri." Ya ce. "Na haqura, amma duk da haka I will punish you, punishment ɗin kuma shine bazan kawo miki twins ba." Ta ce. "Tab', aikuwa da kiranka zan yi inta maka kuka." Ya yi murmushi mai sauti ya ce. "Zaki iya ai, cry cry Baby." Ta ce. "Yanzu na girma na daina kukan ai." Ya ce. "Na san baki daina ba, zaki dai ki daina." Ta ce. "Ya Auntynah?" Ya ce. "She is fine." Ta ce. "My regard please." Sun daɗe suna hira da shi wadda ta saka su duka su biyun a cikin nishad'i, sai da ta ga goma ta wuce sannan ta yi masa sallama ta kashe wayar ganin ba shi da niyyar barin wayar, ta rungume wayar a ƙirjinta tana jin tsohon tsumin Ahmad na ƙoƙarin tasowa daga cikin zuciyarta, she missed him alot in her life. Ta lumshe idonta da ya ciko da k'walla. Shi kuwa Ahmad bin wayar ya yi da kallo bayan ta kashe kamar zai gan ta a cikin screen ɗin wayar, har yanzu yana son Neehal babu yadda zai yi ne kawai tunda ƙaddara ta raba su. Ya lumshe idonsa yana hango ta a cikin zuciyarsa tana murmushinta mai kyau, ba ya jin akwai macen da zai kalla a duniyar nan ya ga kyawunta kamar yadda nake ganin na Neehal. Ya buɗe ido a hankali yana sauke numfashi sannan ya tashi ya nufi ɗakin da Matarsa take bacci, wadda take fama da laulayin ɗan ƙaramin cikinsa.










Washegari da safe sai ga Aunty Hauwa matar Uncle Umar ta zo gidan Mama, da tarkadu na kadarorin Neehal da littafi dake ɗauke da record ɗin duk wata dukiya ta Neehal da inda take da yanda ake juya ta. Mama ta yi mata godiya sosai tare da d'unbin Alkhairi. Ta sanarwa Neehal Uncle Umar ba shi da lafiya, cutar hawan jini na damun shi. Mama ta cewa Neehal ta shirya su koma tare da Aunty Hauwa ta dubo jikin nasa. Bayan sun je Neehal tana ganin shi ita sarkin kuka sai da ta yi kuka saboda yanayin jikin nasa da halin da yake ciki. Shi ma kukan ya saka cikin numfarfashi yana roƙon ta gafara akan zaluntar da ya yi a rayuwa. Ta ce ita ta yafe masa dama kuma bata riƙe shi a ranta ba. Ta kira Mama ta sanar mata halin da ake ciki, Mama ta ce ta saka shi a Mota su kay shi asibiti zata je asibitin yanzu ita ma. Suna zuwa aka bashi gado, zuwan su ba jimawa Mama ta ƙarasa asibitin, ita ta biya dukkan wani charges da akay musu. Washegari Sunday da daddare aka kay lefen Neehal gidan Kawu Musa, a daren Kawu Musa yasa aka juyo da kayan zuwa gidan Mama ya ce ai nanne gidan iyayen Neehal mene sai sun wahalar da kansu sun kay gidansa. Kaya masu kyau da tsada na gani na faɗa sune a cikin lefen Neehal, ba ƙaramin tatsar Ameen kuɗi su Aunty su kay ba, dan ma kusan rabin kuɗin Daddy ne ya bayar. Akwatuna goma sha biyar ne cif manya masu tsada, su kansu abun kallo ne. Banda wasu abubuwan da aka zubo a cikin Basket ɗin kaba da kuma wasu manyan jakunkunan leda guda biyu.










Washegari misalin ƙarfe biyu na rana Ameen ya koma gidansa daga gurin aiki, bai shiga cikin gidan ba sai ya kira mai gadi da mai bawa flowers ruwa ya ce musu su shigar masa da akwatunan Hafsat na kayan faɗar kishiya dake cikin Motarsa. Suka amsa masa shi kuma ya shige ciki. Hafsat tana bedroom ɗinta tana shiryawa, fitowarta kenan daga wanka ta ji shigowar Motarsa gidan, a gaggauce take shiryawa dan kar ya shigo bata kammala shirinta ba. Bayan ya hau upstairs ɗin ma bai shiga ɗakin nata ba sai ya zauna a falo yana jiran su mai_gadi su shigo da kayan. Suna kammala shigowa da shi ba jimawa sai ga Hafsat ta fito cikin shirinta tana ta zabga murmushi. Ameen ya d'ago daga danna wayarsa da yake ya kalle ta. Turus ta tsaya murmushin fuskarta na ɗaukewa, da tsantsar mamaki take bin kayan da kallo, set na akwatuna mai shida sai ƙatuwar jakar leda guda ɗaya.












Ta dube shi cikin mamaki ta ce. "Baby wannan kayan fa, na wa ye?" A dake ya ce. "Naki ne, na faɗar kishiya ake cewa ko?" Ta tsaya kawai kamar status tana kallon shi na wasu sakanni, sannan kamar wata sabuwar kamu ta ce. "Wasa kake yi Baby, na san na wani ne ya kawo maka ajiya shine kake mun wasa." Ta ƙarashe zancen tana nufar kayan. Ya yi ɗan murmushi ya ce. "My dearest wife uwar gidan Ameen, babu maganar wasa anan, aure zan yi nan da three weeks da kwanaki, so waɗannan kayan naki ne, and kuma ki faɗi me kike so na canza miki a gidan nan, kafin lokacin bikin sai a canza." Ta saki baki tana kallon shi ganin yanda yake maganar babu alamar wasa a fuskarka. Wata irin bugawa ta ji ƙirjinta ya yi mata. Cikin raunin murya ta ce. "Dan Allah da gaske Al'ameen Aure zaka ƙara? Baka ce mun ka fasa ba?" Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Sai kuma ya miƙe ya yi ƙoƙarin janyo ta jikinsa ya rarrashe ta ganin ta fara hawaye. Ta yi baya cikin sauri a tsawace ta ce masa. "Karka kuskura ka taɓa ni, munafuki kawai macuci azzalumi." Sai kuma ta fashe da kuka. Ya tsaya kawai yana kallon ta cikin mamaki da ɓacin ran sunayen data kira shi da su. Ta juya ta shige ɗakinta da gudu tana kuka. Ya lumshe idonsa ya buɗe sannan ya ɗauki mukullin Motarsa dake kan kujerar da ya zauna ya juya ya fice daga gidan. Ba ya son ya cigaba da zama a gidan Hafsah ta yi masa abun da ba zai jure ba, ya ɗauki hukunci a kanta a zo a samu matsala. Yana fita Hafsat ta fito daga ɗaki kamar mahaukaciya tana kuka ta shiga bubbud'e akwatunan tana cilli da kayan ciki a tsakiyar falon. Tana yi tana faɗin. "Wallahi Ameen baka isa ba, ka yi kaɗan ka yi mini kishiya, zan ga ta yanda za'a yi auran nan ina raye." Sai da ta gama watsar da fiye da rabin kayan sannan ta sauka ƙasa a matuƙar fusace ta shiga kitchen, su Harirah suka bi ta da kallon mamaki ganin ta a haka babu maraba da mahaukaciya yanda take huci tana zazzaro ido. Taɓarya ta lalubo ta ɗauko ta fito falon ta fara faffasa abubuwa, ai da gudu su Harirah suka yi ɗakinsu suka banko ƙofa. Harirah ta dubi Baraka ta ce. "Mun shiga uku, Hajiya ko ta haukace ne?" Baraka ta ce. "Ko kuma dai ta tayar da aljanu ba, dan wannan aikin sai dai su." Dai-dai lokacin Hafsah ta rantab'awa show glass taɓarya, ji kake tassss gurin da ta dokawa taɓaryar ya yi ƙasa a dagargaje. Ai cikin rige_rigen gudu su Harirah har faɗuwa suke suka banka toilet suka rufo cikin tsoro tare da fargabar har Hafsat ta gama da falon ta dawo kansu. Duk wani abun fasawa a falon sai da Hafsat ta yi masa illa, sannan ta hau sama ta yiwa na saman ma. Tana zuba uban gumi da haki ta zaɓi jaka ta zira takalmi ta yi gidansu tana kuka. Su Harirah dai suna toilet rungume da bango ba su san ma ta fice ba, suna tsoron kar su fito aljanun su haɗa da su. Sai zazzare ido suke cikinsu na ƙugi.










Hafsah ce zaune a falon gidansu tana ta rusa kuka, tunda ta je gidan kusan minti talatin kukan kawai take yi, Mom har ta gaji da tambayar ta abun da ya faru. A harzuk'e Mom ta ce. "Daughter wai ba tambayarki nake yi abun da ya faru ba, kin taho a hargitse kamar wata korarriya kin zo sai kuka kike mun kin ƙi yin magana." Ta ɗan tsayar da kukan ta ce. "Mom ashe Ameen yaudarata ya yi bai fasa Auran da ya ce zai yi ba." Mom ta ce. "Kamar yaya kenan?" Cikin kuka ta ce. "D'azu ya kawo mun wasu tsinannun kaya wai kayan faɗar kishiya, wai saura 3 weeks bikinsa." Sai ta kuma fashewa da kuka. Mom ta ce. "Kan uban nan, lallai ma yaron nan ɗan iska ne, mu zai yiwa haka? To wallahi bai isa ba, zai zo gidan ya same ni ne, sai dai ya zaɓa ko ke ko auran da zai ƙara. Ki daina kukan nan haka da'alla, har wani shid'ewa kike kamar wadda aka cewa na mutu, yanzu zan kira Alhaji in sanar masa halin da ake ciki, dan yana dawowa ya san matakin ɗauka cikin gaggawa. Shi kuma mara kunyar zai zo ya same ni har inda nake, na san zai kwaso jiki zalalo_zalalo ya zo biko, anan zan masa wankin babban bargo in ci masa mutunci. Yaro da ana ganin ka kamar na Allah ashe ka ce na shaid'an ne kai, banda ƙaddara mai zai haɗaki aure da wannan ai kin fi ƙarfin ajin shi." Ita dai Hafsah kukanta kawai take yi, bata ma saurarar sababin Mom.










Ameen bai koma gidansa sai bayan Magriba, a lokacin ya ga aika_aikar da Hafsah ta yi. Da farko gani ya yi kamar ba Falon gidansa da ya saba gani ba ne kodayaushe tsaf, ya tsaya yana kallon Falon kamar wanda aka yi yaƙi a cikinsa cikin mamaki. Ya tsallake abubuwan ya haura sama dan jin ba'asin faruwar hakan a gurin Hafsah. Sai ya tarar falon saman ya ci uban na ƙasa a haukacewa. Yanda aka yi da kayan da ya kawowa Hafsah shi ya tabbatar masa gaba-ɗaya wannan aikin nata ne. Ransa ya yi matuƙar ɓaci ba kaɗan ba, saboda kawai ya ce zai ƙara Aure? Mene matsalar mata da ƙara Auren Namiji ne? Ubangiji ne fa ya halatta a yi, da wannan haukan ba gwara ki dage da Sallah kina addu'a da kai kukanki gurin mai duka akan Allah ya baki kishiyar ta gari ba, idan mai sharri ce ki roƙi sharrin ya ƙare a kanta ke kuma ya tsare ki daga sharrin. Amma sai sabon jahilci da hauka zaki tsiro. Cikin tsantsar ɓacin rai ya nufi ɗakinsa ya yi wanka ya fito. Kamar yadda ya zata bata gidan, ya sauka ƙasa ya tarar su Harirah wanda jin shigowarsa yasa suka fito falon, amma duk da haka a tsorace suke. Fuska a cukule ya ba su umarnin gyara gidan sannan ya fice. A gurin gyaran ne su Harirah suka gane dawar garin, wato dalilin da yasa Hafsah ta yi wannan haukan.










Saura sati biyu biki Mama ta ɗauko mai gyaran jikin data gyarawa Neehal lokacin bikinsu da Sadik ta fara yi mata. Haramar biki fa ta ɗauka sosai, Daddy ya ƙara gyara gidan Mama, duk wani furniture's dake part ɗinta an canza shi an saka sabo, haka ma cotton's da carpet's. Ga contributions da Mama take samu ko ta ina, haka ma Neehal ɗin. A lokacin ne Neehal ta fara nuna damuwarta ta fara k'unci da koke_koke irin wanda ta yi lokacin bikinsu da Sadik, ganin dai da gaske auran nata za'a yi, tafiya zata yi ta bar Mamanta. Ameen ma shirye-shiryen bikinsa kawai yake yi ya ajiye batun wata Hafsat a gefe, ya ce idan ta gaji da zaman gidan nasu ta dawo, dan shi dai ko zata shekara ba zai je wani biko ba. Mama bata san Hafsat ta yi yaji ba dan bai faɗa mata ba, Daddy ma haka. Kuma ko kaɗan ba ya nuna alamar bata gidan nasa. Wannan karon Mama ta ce babu abun da za'a yi na events, Ranar d'aurin Aure kawai zata yi yini da daddare a miƙa Amarya gidanta. Haneefah da sauran mate ɗinsu na Familyn su Mama ba su so hakan ba, sai dai ita Neehal hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, dan bata son taro ko kaɗan. Aunty Sadiya dai ta ce sai sun yi Kamu ranar Alhamis ko a gida ne an kira masu kiɗan ƙwarya sun buga musu sun jajige baza'a yi biki lami ba. Tun ranar Sunday wanda ya kama saura kwana biyar d'aurin Aure Ahmad ya kawo twins, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Neehal ba. Ya kuma bata kuɗi masu kauri a matsayin gudunmawa, wanda sai da ya ɓata rai sannan ta karɓa. Uncle Usman ma ranar ya sauka shi da iyalansa. Ana i jibi biki gidan ya ɗinke da jama'a, dangin Mama dana Daddy da kuma na Neehal, wannan karon sun mata kara babu laifi sun zazzo, wasu ma bata san su ba sai an faɗa mata dangantakarta da su take ganewa, Kawu Musa ne duk ya yi musu tilas suka zo, da kansa ya je har Gabasawan ya kai musu abun gayyata. Matan Ƴaƴan Baffa ma sun zo da ƴaƴansu. Ranar aka yarfawa Neehal ƙunshi a fararen hannunta da ƙafarta, ƙunshin ya yi matuƙar kyau akan fatarta data sha gyara bana wasa ba. Sai walwali take tana hasakawa, ga wani k'amshi mai daɗin gaske dake tashi a jikinta. Ita akaran kanta ta san ta sauya, dan wannan gyaran jikin har ya fi wancan da aka yi mata kyau. Sai ta tsaya a gaban mudubi ta yi ta kallon kanta tana murmushi ita kaɗai..........✍️












*Wanga novel yaushe zaka ƙare ne?🤔😰*














*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣9️⃣*












Thank

Please Login or Register in order to submit comment