Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake maimaitawa cikin tsananin d'imuwa. A ruɗe ya ce. "Subhallahi, wanne irin mugun aboki Alhaji yake tarayya da shi? gaskiya ya cika cikakken mara imani, matsiyaci ne na ƙarshe amma." Abba ya ce. "Ai Ginyau ba ƙaramar cuta ya yi mana ba, dan ya yi sanadiyar ɓacin sunan zuri'armu." Mama ta ce. "Hmm, idan bera da sata daddawa ma da wari, da a ce Yaya Tafidan bai bi shi ba ai bai isa ya ɗauke shi ya kai shi ba, ko kuma yana zaune a gida ya saka shi a cikin ƙungiyar ba." Kawu Musa ya ce. "Kar ki ce haka Hajiya, babu ta yanda za'a yi dan mutum ya ce maka ka zo ku je wani guri ka yi tunanin a wannan mummunar hanyar zai saka ka, ko da zai kaika gurin irin waɗannan mutanen baza ka taɓa kawowa a ranka saka a cikinsu za'a yi ba, kuma idan har gaskiya ne abun da Alhaji Tafida ya faɗa to duk abun da ya aikata a cikin wannan ƙungiya ba'a hayyacinsa ya yi ba, tunda tsaface shi suka yi. Duk abun da ya aikata na saɓon Allah alhakin yana kan waɗanda suka saka shi a ciki ko a gurin Ubangiji, domin ba shi da yanda zai yi ne a dole yake aikatawa, kuma shi ma ya ce abun yana damun sa. Dan haka yanzu dole mu san yanda za'a yi ya fito daga hannun hukuma sannan kuma ya bar cikin wannan ƙungiyar. Ita kuma Neehal wannan abubuwan da suka dinga samun ta sanadiyyar shi Alhaji Tafidan ba laifin kowa ba ne sai mu danginta, domin da mun riƙe ta a hannunmu babu ta yanda za'a yi wannan al'amarin yakasance a gare ta. Watsi da ZUMUNCI da gudun wahala na ƴan'uwan mahaifinta da mahaifiyarta duk shi ya janyo mata, banda haka ta yaya har za'a ce yayar kishiyar mahaifiyarka ce zata riƙe ka banda ma da mutunci sosai a tsakani, alhalin da danginka a raye. Su suna can sun saki baki tunda yarinya ba'a hannunsu take ba babu ruwansu da wahalarta koma me zai faru da ita ya faru basu da asara. Bacin su kuma wahalar da mahaifinta ya yi da su." Uncle Mahmud ya ce. "Malam Musa da zancenka gaskiya, amma duk da haka Ubangiji ne ya ƙaddara mata hakan zata faru da ita." Kawu Musa ya ce. "Haka ne, amma komai yana da sanadi a rayuwa, rashin ZUMUNCI ba ƙaramin abu ba ne, wanda bai yi shi a duniya ba fa aka ce zai yi shi a wuta. Yanzu da ace tana hannunmu mu danginta da Alhaji Tafida ya faɗa wannan harkar ai baza su ce ya je har inda take ya cutar da ita ba, tunda kamar yadda suka faɗa ba shi yake ciyar da ita ba da sauransu." Abba ya ce. "Haka ne Malam Musa zancenka dutse, na fahimci abun da kake nufi da maganar ka da kuma abun da kake son faɗa. Mutane ne yanzu sun mayar da zumunci na ganin ido da kuɗi, zumuncin Allah amma ba'a son yin sa, kuma an mayar da hakan kamar ba komai ba." Kawu Musa ya ce. "Ƴar guda ɗaya tal a duniya amma su kasa riƙe ta, bacin tarin Alkhairin da mahaifinta yay musu da yana raye. Amma kuma da yake Allah mai ƙudura ne ba ka ga yanda su Salisun suka koma ba yanzu gaba-d'ayansu. (Ƴaƴan Baffa, wanda ya riƙe Umma da Abba.) Sun zama abun tausayi, abun da zasu ci ma gagarar su yake yi, ita ɗin da suka so ta tagayyara gashi Ubangiji sai d'aga ta yake, wannan ƙaddarar data same ta ma Insha Allahu komai ya zo ƙarshe, kuma da ma rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa. Wallahi idan kuka ga halin matsin rayuwar da Umar yake ciki sai kun tausaya masa, kuma shi ma duk alhakin marainiyar Allah da ya zalunta ne ya fara kama shi." Mama ta jinjina kai ta ce. "Na gani tabbas, lokacin bikin Neehal da Sadik kamar ba shi ba, har wani tsufan dole ya yi." Kawu Musa ya ce. "Ba dole ba, zaluntar Maraya ai ba wasa ba ne, ga kuma watsi da ZUMUNCIN Allah." Uncle Ahmad ya ce. "Mutanen duniyar nan sai addu'a, ita dai wannan yarinya Allah yasa iya wahalarta kenan duniya da lahira, Allah ya bata miji na gari da zai riƙe ta da amana." Gaba-ɗaya suka amsa da "Amin ya Allah." Sannan suka koma hirar Daddy da yanda za'a yi ya fito, inda suka k'ark'are akan matsayar za su nemi abokin Ameen waɗanda suka tafi da Daddy dan su san ya za'a ɓullo wa abun.










Neehal tana kwance a ɗakinta tana tunanin rayuwa da bata rabo da shi Mama ta shigo ɗakin. Ta tashi zaune tana amsa sallamar da ta yi. Mama ta zauna a gefenta ta ce. "Neehal ban ga kin fito kin ci abinci ba." Kamar zata yi kuka ta ce. "Mama bana jin yunwa ne, wai yaushe Daddy zai dawo?" Mama ta ce. "Ban sani ba Neehal." Ta fara hawaye ta ce. "Mama dan Allah ki cewa su Abba kar su bari a kashe shi, ko kuma su cewa Yaya yasa waɗanda suka kama shi su sake shi." Mama ta ce. "Al'amarin ba ƙarami ba ne Neehal, ke dai ki tay masa addu'a kin ji." Neehal ta d'aga mata kai. Mama ta ce. "To share hawayen mu je ki ci abinci, ai ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba."






Bayan Azhar sai ga Mommy'n Hameedah fakal_fakal ta zo gidan, duk zaman da Mama ta yi a asibiti bata zo ba sai yau, yauma dan ta ji labarin abun da ya faru da Daddy ne a wajen Kawunsu k'anin mahaifinsu. Ta zo tay ta ƴan koke_kokenta akan abun da ya samu Daddy tare da borin kunyar abun da suka yiwa Neehal na mutuwa da samarinta suke yi. Daga Mama har Neehal babu wanda ya kula ta, sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru. Da yamma Ahmad ya zo gidan. Lokacin Neehal bacci ma take Mama ta tashe ta. Tunda ta sakko ya ƙura mata ido ganin yanda ta rame ta ƙara haske, idanunta duk sun jeme alamun suna shan kuka. Ta zauna a ƙasa nesa da shi a hankali ta ce. "Ina yini?" Ya ce. "Lafiya k'alau Princess ya jiki? Ashe Mama ma bata da lafiya?" Ta ce. "Da sauqi, ita ma Maman ta ji sauƙi Alhamdulillah." Ya ce. "Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa, wallahi ban sani ba ai da tuni na zo. Su Ummi suna muku ya jiki." Ta ce. "Amin, ba komai, muna amsawa, ina Yarana?" Ya ce. "Yaranki suna nan k'alau, kullum sai rigimar zasu gurin Aunty suke yi." Ta yi murmushi kawai. Ya gyara zama sosai cikin kulawa ya ce. "Princess bacin rashin lafiya akwai wani abu da yake damun ki, dan Allah ba dan ni ba ki rage saka samuwa a cikin ranki, ki miƙawa Allah dukkan alamuranki shi zai shige miki gaba, amma damuwa bata haifar da komai sai matsala, Please Princess ki mun wannan alfamar." Gyaɗa masa kai Neehal ta yi cikin gamsuwa tare da yi masa godiya. Ya ɗan jima a gidan suna hira, anan yake sanar mata next week za kai kayan lefensa, tay masa fatan Alkhairi tare da fatan zaman lafiya a rayuwar auransu. Bayan Magriba su Abba suka gana da Kamal abokin Ameen, suka faɗa masa buƙatarsu da labarin da Daddy ya ba su na shigar sa cikin ƙungiyar. Ya jinjina abun sosai ya kuma yi musu alƙawarin zai yi iya yinsa na ganin hakan ya yiyu duk da hakan da matuƙar wahala, dan case ɗin ya bar hannunsu yana gun manyansu. Daɗin abun da ba'a fito da zancen ba ga al'ummar gari ba, amma dai ya ce su dage da addu'a. Da daddare bayan isha'i Neehal tana kwance a falon ƙasa suna chatting da Haneefah Ameen ya shigo falon, ko sallamarsa bata ji ba sai k'amshin turarensa. Saurin kifa wayar ta yi a ƙirjinta tare da lumshe idonta kamar mai bacci, dan haushin shi take ji akan kama Daddy da ya saka a yi, a ganin ta ya kamata ya yi bincike kafin ya yi saurin zartar da hukunci. Shi kuwa tsayawa ya yi yana kallon ta, ta turo baki domin tana jin idanunsa na yawo a jikinta, tsawon three minutes yana kallon ta sannan ya wuce sama. Ta buɗe ido jin takun sa akan steps tana kallon bayansa. Tana ganin ya haye ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta shige ɗakin su Dije dan kar ya fito su ƙara haɗuwa. Washegari da safe ta je school ta dubo result ɗinsu da aka kafe musu tun week ɗin da ya wuce. Alhamdulillah kamar kodayaushe ya yi kyau successfully. Sai a lokacin ta ji haushin rashin apply ɗin N.Y.S.C da bata yi ba, a lokacin classmates ɗinta suna ta yi ita kuma ta ƙi yi saboda auranta da Sadeek, dan ba zai yiyu daga yin aure ta fara da bautar ƙasa ba. Shine Mama ta ce ta bari sai next year ta yi. A cikin week ɗin nan ta fara bucking karɓar result ɗinta. Sati biyu da sallamo Mama bayan cuku_cuku da shan gwabarmaya su Abba suka samu aka fito da Daddy, dan ma Daddy'n na manya mutane ne a ƙasar shi yasa abun ya ɗan zo musu da sauƙi, amma duk da haka sun sha wahala ba kaɗan ba. Ana i gobe ranar ne kuma jami'an tsaro suka yi nasarar k'one gidan tsafin ƙungiya bisa jagoranci Daddy. Bisa Ikon Allah sai abun da ya zo da tsautsayi ashe duka ƴan ƙungiyar suna cikin gidan suna meeting akan yanda za su yi Daddy ya zo hannunsu a wannan lokacin, tunda Sarauniya ta hana a kashe shi, su kuma jami'an tsaro basu san suna cikin gidan ba, gidan kawai suka zo da niyyar k'onewa aka haɗa da su. Sai da wutar ta mutu sannan aka dinga zak'ulu k'onannun gawarwakinsu. Jami'an tsaro ba su so haka ba, sun so su kama su a hannu. Amma al'ummar gari da labarin ya bazu kowa cewa yake yi gwara haka, dan halin ƙasar nan tsaf za'a kama su a tsare kuma a ƙi yi musu hukuncin komai a yi ta jan abun har a manta da maganar, musamman da ya kasance da wasu daga cikin manyan ƙasa a cikin ƙungiyar. Ranar ƙasar nan da kewaye rud'ewa aka yi da zancen kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Daddy ya yi kuka sosai tare da ƙara godewa Allah da ya bar shi da imaninsa, shigarsa cikin ƙungiyar nan bai ruɗe shi yasa ya manta da Ubangiji ba, ya kuma gode masa akan fitar da shi da ya yi, domin yasan wannan ikonsa ne kawai da rahamarsa yasa ya cece shi. Ranar ji ya yi tamkar an sauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa, ya ji jikinsa da kansa yay masa wasai kamar wanda ya tashi daga doguwar cuta, nutsuwarsa ta dawo cikin jikinsa. Ya ƙudure a ransa yanzu bautar Allah da istigfari kawai zai duk'ufa yi akan abubuwan da ya aikata, duk da bayin kansa ba ne amma ba zai dogara da hakan ya ƙi tunatarwa Allah ba.






Bayan ya fito daga wanka ya shirya ya ci lafiyayyen abincin da Mama tay masa da sassayan lemo wanda rabon da ya ci ya manta saboda rashin kwanciyar hankali. Gashi duk ya rame ya yi duhu sakamakon tsaren shin da aka yi. Su Abba sun zo ana ta ƙara jajanta abun tare da murnar kub'utar da shi da Allah ya yi, domin sun san ba iyawarsu da dabararsu ba ce Ubangiji ne ya dubi zuciyar Daddy ya tseratar da shi bai mutu yana aikata wannan mummunan saɓon ba. Abba ya dubi Daddy ya ce. "Toh Alhamdulillah, Masha Allah, komai ya yi farko yana da ƙarshe, Muhammad wannan ita ce taka jarrabawar kai kuma, fatanmu Allah kar ya kuma maimaita mana irin wannan musifa ga zuri'armu da ma dukkan Musulmi baki ɗaya, wannan kuma ya isa ya zama izna ga ƴan baya akan mu'amala da abokai wanda bana gari ba ne. Dan shi aboki kullum burinshi ya ɗora ka akan hanyar da yake, musamman in bata ta gari ba ce." Daddy ya ce. "Gaskiya ne, ai na yi dana sanin sanin Kabir Ginyau a rayuwata, shi yasa Fateemah tun farko kamar ta sani ta dinga ƙoƙarin raba ni da shi, Allah ya yi dai wannan abun sai ya faru. Amma kuma sanadin haka gashi an yi nasarar kawar da mugun iri daga doran duniya, an rage masu saɓon Allah." Abba ya ce. "Allah ya kyauta, ya cigaba da tonawa masu irin wannan munanan d'abi'un asiri." Suka amsa da Amin. Dai-dai lokacin Ameen ya shigo falon. Daddy ya tashi da sauri ya tarye shi tare da rungume shi yana murmushi ya ce. "Da fatan yanzu zuciyar gwarzon ɗana ta yi fari da mahaifinsa akan baƙin da ta yi a da?" Ameen ya yi murmushi cikin wasa ya ce. "Kamar da saura dai Dad." Daddy ya marairaice fuska, gaba-d'aya Falon suka saka dariya. Neehal kam ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murnar Allah ya fito mata da Dad ɗinta lafiya. Sai Hamdala ga Ubangiji take. Alhamdulillah rayuwar gidan Mama ta koma kamar da ita da Daddy wanda a da ta fitar da ran samun hakan. Suna fatan kuma matsala ta ƙare musu haka daga su har Neehal. Hankalin ƴan'uwa ya kwanta akan problem ɗin Neehal tunda an gano bakin zaren har ma an yi maganin abun, yanzu sai fatan Allah ya kawo miji na gari ta yi auranta. Bayan sati biyu wanda ya kama farkon watan maulud aka yi bikin Ahmad wanda har yanzu bai san an fasa Auran Neehal da Sadik ba, dan Neehal ce masa ta yi d'aga bikin aka yi. Neehal ta je ta yi kwana uku da ita aka sha biki aka rak'ashe. Ƴan'uwan Ahmad sun nuna mata k'auna, kowa ya zo Ummi ta nuna masa ita ta ce ga Aunty'n su Afrah wadda ta tsince su ta riƙe su. Ranar D'aurin Aure da Mama da Daddy suka je ta biyo su suka dawo gida tare. A daren ranar ta ci kukan da bata san dalilinsa ba, ta ji dai kawai tana jin ba daɗi akan Auran da Ahmad ya yi, amma ta daure bata bari kowa ya fuskanci halin da take ciki ba. Ta koma bakin aikinta wanda aka ƙara mata girma bayan karɓar result ɗinta da ta yi. Ameen bai yi magana ba akan yana son Neehal ko wani abu makamancin haka, ko nuna alamar hakan ma bai yi ba. Mama kuma ta zuba masa ido ta ga iya gudun ruwansa da ƙarshen muskilancinsa. Da Daddy yay mata zancen ta ce masa kar ya kuma balle Ameen ɗin ya ji, sai ya zo da kansa ya ce yana son abun, tunda bai isa tay masa tallar ƴarta kota ba shi ita a bagas ba. Daddy ya yi dariya kawai. Mama ta dage da yiwa Neehal addu'ar samun miji na gari tare da neman zaɓin Allah mafi Alkhairi a gare ta. Ita ma ta ce mata ta dage da yin addu'ar hakan...........✍️












_*Ga Barka da Sallah nan har 3 pages, sai dai ni ban ji nawa ba har yanzu.😒😥*_












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣4️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
















.........Yau ta kama ranar Asabar, da yamma Mama da Daddy suna zaune a falon ƙasa na part ɗin Mama suna hira door beil ta yi ƙara. Neehal bata nan ta je gidan Haneefah tun Azhar. Daddy ya tashi ya je buɗe ƙofar. Kawu Musa ya gani, da fara'a ya tarb'e shi tare da yi masa iso zuwa cikin falon. Ya shigo ya zauna a kujerar dake fuskantar wadda Mama take, Daddy kuma ya koma ya zauna a gefenta. Cikin girmamawa da muntuntuwa Kawu Musa suka gaisa da Mama. Zulai ta shigo falon ta kawo masa drinks a cikin plate tare da gaishe shi. Bayan ya ɗan kurb'i juice ɗin ya dubi Daddy ya ce. "Na ji daɗi dana same ka a gida, dan har na yi tunanin baka nan sai Hajiya kawai." Daddy ya ce. "Ai yanzu yawanci da yamma ina gida, da rana ne nake ɗan fita idan ta kama." Kawu Musa ya ce. "Allah sarki, dama wata magana ce mai muhimmanci ke tafe da ni." Mama ta bayar da duka hankalinta a kansa, Daddy ya ce. "Toh muna sauraren ka Malam Musa." Malam Musa ya gyara zama ya ce. "Jiya da yamma Ameen ya zo ya same ni har gida mun gaisa, to na zata zuwan nasa kamar na kodayaushe ne da yake zuwa lokaci zuwa lokaci muna gaisawa, sai dai bayan mun gama gaisawar na fuskanci akwai magana a bakinsa sai ce masa, Aminullah kamar akwai magana a bakinka, meke tafe da kai ne? Sai ya sunkuyar da kai ya faɗa mun abun da ke ransa, wato yana son Auran NEEHAL. Shine na ce to bazan yi ƙasa a gwiwa ba yau na taho ƙafa_ƙafa domin sanar da ku wannan abun farincikin, tunda ya ce mun bai sanar muku ba." Ya ƙarashe zancen cikin murmushin farinciki wanda ke nuni da yana jin daɗin al'amarin sosai. Mama ta kalli Daddy wanda shi ma yake murmushin sannan ta jinjina kai ta mayar da kallonta ga Kawu Musa cikin mamaki ta ce. "Lallai na gaishe da Ameen na jinjinawa halinsa, wato dan ya san idan ya zo ya same ni bazan amince ba ko kuma Dad ɗinsa shi yasa ya je ya same ka, saboda bashi da kunya ba zai faɗa da bakinsa ba sai dai ya turo ka, to bazan amince ba duk da haka." Kawu Musa ya yi ƴar dariya sannan ya ce. "To ai wannan shine ƙa'ida, abun da ya yi shine dai-dai, idan kana son yarinya ka je ka samu magabatanta ba wai ka je kai ta hure mata kunne kana cika ta da surutun kawai ba." Daddy ya ce. "Faɗa mata dai, ita tafi son ya zo su yi ta ja masa aji ana ƴank'wana shi." Kawu Musa yana dariya ya ce. "Ai ɗan nawa ba irin waɗannan mazan da ake yiwa haka ba ne." Ganin sun mayar da abun wasa cikin seriously Mama ta ce. "Koma yaya ɗan naku yake dole ya ajiye duk wani ji da kai ya zo ya nemi yarda da amincewar yarinya, domin bazan yi mata Aure ba tare dana tabbatar tana so ko bata so ba." Kawu Musa ya yi murmushi ya ce. "Haba Hajiya, abu na gida abu tuwona maina ai bama buƙatar wani jan abubuwa, yarinyar nan tunda Ubangiji ya kawo mata ƙarshen matsalarta burinmu yanzu kawai mu gan ta a ɗakin mijinta, hankalinmu sai ya fi kwanciya." Daddy ya ce. "Wannan gaskiya ne Malam Musa." Mama ta ce. "Nima ban ƙi ta taku ba, hasalima abun da na kasa da addu'a a gaba kenan Allah ya kawo mata miji na gari ta yi auranta. To amma dan Ameen ya ce yana son ta baza mu amince masa ba ba tare da mun ji ra'ayin yarinya ba, idan bata so duk sonmu da abun dole mu haqura." Kawu Musa ya ce. "Wannan ai duk ba wata matsala ba ce Hajiya, yaron nan kowa ya san halinsa ba shi da wani aibu, kowanne iyaye zasu so ƴarsu ta yi dacen miji da kamar Ameen yaron kirki. Ni dai dan Allah ina nema masa wannan alfarmar a gurinku, domin a ganina koda bata son shi idan aka yi auran zata so shi, za su fuskanci juna, bare ma Insha Allahu na san baza ta ƙi ba. Mu dai kawai mu bi su da addu'ar Allah yasawa abun albarka ya ba su zaman lafiya." Daddy ya ce. "Amin Amin, mun gode sosai Malam Musa, Allah ya bar zumunci." Ya ce. "Amin, amma mune da godiya akodayaushe Alhaji, Allah ya raya zuri'a ya ƙara buɗi." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Amin, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Malam Musa ya ce. "Amin, shine kawai dama, ina Neehal ɗin ne ban ga gilmawarta ba ko tana gurin aiki?" Mama ta ce. "Ta je gidan ƙawarta ne, yau ai Asabar bata da aiki." Malam Musa ya ce. "To Allah ya taimaka, ni zan wuce sai na kuma dawowa, duk abun da ake ciki sai ku sanar mun a waya." Mama ta ce. "To ka gaida gida da mutanen gidan, mun gode sosai fa, Allah ya bar zumunci." Ya ce "Gida zai ji." Tare da miƙewa, Daddy ya tashi ya bi bayansa dan raka shi. Bayan ya dawo Mama ta ce masa. "Ni fa Gen. bana son mu tursasa Neehal akan Auran Ameen, kuma ka san indai muka faɗa mata baza taɓa ƙi ba, ni kuma bazan so hakan ba gaskiya." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Bana jin zata ƙi Ameen Fateemah, a yanda Neehal abubuwa suka faru a baya akan aurarrakinta da Allah bai nufa an yi ba tana buƙatar ace ta samu miji na gari wanda baza ta yi kuka da shi ba ko bayan ba ma raye, ke kika haifi Ameen kin fi kowa sanin halinsa, Ameen ba shi da wata matsala da zata saka a hana shi Aure." Mama ta ce. "Hmmm, in aura masa ƴa ya cinye mun ita da masifa da faɗa." Daddy ya yi murmushi ya ce. "Wannan kuma aiba a ƙasa ya ɗauka ba gurinki ya gado, kuma tunda yana k'aunarta ai bazai mata ba. Kin ga Fateemah kamar yadda Malam Musa ya ce mu bi al'amarin nan kawai da addu'a, idan Alkhairi ne Allah ya tabbatar mana, Insha Allahu watarana sai mun yi alfahari da farincikin auransu." Mama ta ce. "Allah yasa." Sai kuma ta shiga mitar Ameen dan ya san baza ta iya cewa Malam Musa a'a ba shine ya turo musu shi, zai zo ya same ta ne har inda take." Daddy dai dariya kawai yake yi mata, zuciyarsa wasai, domin babban burinsa a yanzu Ameen ya auri Neehal, domin ya san bazai taɓa wulaqanta ta ba, ya yarda da ɗansa da irin tarbiyyar da yay masa. Ita kuma Mama anata ɓangaren tana son abun domin idan ya kasance sai ta fi kowa farinciki, amma gani take kamar tursasa Neehal zasu yi, ita kuma baza ta so hakan ba. Sai bayan Magriba Neehal ta dawo gida. Direct ɗakin Mama ta wuce, ta faɗa jikinta cikin shagwab'arta ta ce. "Wash Mama na gaji sosai." Mama ta ce. "Wani aikin kika yi ne?" Ta ce. "Driving mana." Mama ta ce. "Daga gidan Haneefah zuwa nan shine zai saka ki gaji saboda lalacinki." Ta turo baki bata ce komai ba. Mama ta ce. "Ki je ki ci abinci ki huta bayan isha'i Dad yana son ganinki." Ta ɗan waro Ido ta ce. "Lafiya Mama?" Dan haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Mama ta ce. "Ba wani abu ba ne tambayar ki kawai zai yi." Ta yi shiru a ranta tana kissima abubuwa da dama, ko kaɗan maganar aure bata zo cikin zuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment