Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya ba, dan ba zai iya rayuwa babu ita ba, ya ƙi ci ya ƙi sha, ya tada hankalinsa, damuwar da ya sanya wa ransa gami da yunwa suka taru suka haifar masa da ciwo mai tsanani, wanda har ya kai shi ga kwanciya a gadon asibiti. Hankalin Maamah dana Abba ya tashi ba kaɗan ba, Maamah ta kira iyayenta ta sanar musu halin da ake ciki. Mahaifin Maamah da ya zo duba Sadik ya ji abun da yake faruwa yay ta faɗa, ya ce wannan ba hujja ba ce wadda za'a hana Sadik auren Neehal, da mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke, sai ya rabu da Neehal ɗin kuma idan kwanansa ya ƙare dole ya tafi, dan haka shi zai tsayawa Sadik ɗin a auransa da Neehal, tunda ita yake so. Wannan magana ta Abeey (mahaifin Maamah) ita ta sanyayawa Sadik rai gami da ƙwarara masa gwiwa, har ya fara kwantar da hankalinsa ya samu lafiya. Hajiya da Kawu kuwa suka ce babu saka hannunsu a wannan al'amarin, dan haka duk abun da ya faru da Sadik babu ruwan su. Abeey ya ce "Babu abun ma da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi." Abbansa kuwa bin al'amarin kawai ya yi da addu'a, dan ita ce mafita. Sadik ya so tun lokacin a zo a yi maganar auran su da Neehal, amma Maamah ta dakatar da shi ta ce, ya bi komai a sannu, ya bari ya ƙarasa ginin gidansa and kuma akwai lefe, dan haka idan ya gama shiryawa sai aje a yi maganar auren, a saka lokaci ƙanƙani a yi a wuce gurin.








A month ɗin da ya wuce ne asirin Safeenah wadda tasa aka sace su Afrah ya tonu. Ta hanyar Gaye wanda jami'an tsaro suka samu nasarar kama su shi da yaransa akan dukan da suka yiwa Saudart. Bayan an kama sun ne ya yi bayanin dalilin dukan da sukay mata. Daga Zariya aka je har Abuja aka kamo Safeenah, wadda zuwa lokacin duk ta fige ta rame saboda zullumi da tsoro. Babu wanda bai yi mamakin jin Safeenah ce ta saka a sace su Afrah ba, kasancewar ta ƙanwar Mahaifiyarsu ta jini. Mamanta tay ta kuka tana Allah wadai da halin ta, duk da ba shiri suke da Ammi kishiyar ta ba, amma bata taɓa tsammanin ƴarta zata cutar da ahalinsu har haka ba. Ahmad ma ya sha mamaki ba kaɗan ba, duk da ya san Safeenah tana sonsa amma bai taɓa tunanin son zuciyarta har ya kai haka ba, dan shi a gurinsa wannan hauka ne da jahilci ba so ba, dan duk mutumin da yake k'aunarka to zai so ƴaƴanka. Safeenah ta yi nadama mara amfani ita da ƙawarta Saudat, dan har ita Alk'ali ya tisa prison bayan an gabatar da su a gaban kotu bisa laifin bayar da kwangilar kisan kai, duk da bata gama warkewa daga jinyar dukan da yaran Gaye sukay mata, sai dai an cigaba da ɗora ta akan magani a gidan kason.








Yau ta kama ranar Alhamis, misalin ƙarfe huɗu da mintuna na yamm Neehal ta dawo gida daga school. A falo ta ajiye handbag ɗinta da sauran tarkacen school, kitchen ta nufa saboda hango Mama da ta yi a ciki. "Mama sannu da aiki, am back." Ta faɗi haka bayan ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce "Sannunki da zuwa, shine zaki shigo mun babu sallama." Ta ƙarasa ta rungume Mama ta baya a shagwab'e ta ce "Na yi sallama fa ba ki ji ba ne. Mama duk na gaji yau ɗin nan." Mama ta shafi kuncinta ta ce "Ki je ki yi wanka ki sakko ki abinci, idan kin huta akwai maganar da za mu yi." Ta bar jikin Maman tare da faɗin "Tom Mamana, Yaya ya kawo miki saqo ki bani?" Mama ta ce "Ya kawo tun safe, ki duba kan mudubi zaki gani." Ta ce "Me ya kawo mun?" Mama ta ce "Ban duba ba, ki je ki gani, zaki gan shi a cikin leda." Ta juya cikin murna ta fice daga kitchen ɗin. Ɗakinta ta fara shiga ta yi wanka, bayan ta shirya ta je ɗakin Mama ta ɗauki ledar da Ameen ya kawo mata ta buɗe. Kwalin sabuwar waya ta gani kamfanin iPhone, ta shiga buɗe kwalin da sauri ta zaro sabuwar wayar ta shiga jujjuya ta a hannunta cikin tsananin murna, da sauri ta tashi ta sauka ƙasa ta shiga kwad'awa Mama kira. Mama ta fito falo da sauri jin kiran tana faɗin, "Ke lafiya kike mun wannan kiran?" Ta rungume Mama tana murmushin farinciki ta ce "Mama Yaya ya siyo mun sabuwar phone." Mama ta yi murmushi tare da zare ta daga jikinta ta karɓi wayar tana kallo ta ce "Congratulation Dear, Ameen ya hutar da ni, na huta da mitar kullum Mama anyo sabuwar waya kaza ki siya mun ko ki sa Dad ya siya mun." Neehal ta yi dariya ta ce "Mama tun sanda result ɗinmu na last semester ya fito na nuna masa, da ya gani shine ya ce na yi ƙoƙari sosai me nake son na siya mun? Na ce masa kome ne ma ina so. Ni har na manta mun yi haka da shi, ashe shi bai manta ba yana sane. Jiya da ya zo da daddare shine ya ce mun zai kawo mun sak'ona yau na alƙawarin da yay mun." Mama ta ce "Ya kyauta sosai, sai kira shi ki yi masa godiya." Ta ce "Toh Mama bari na saka wayar a chaji." Mama ta bata wayar ta koma sama. Bayan ta saka chajin ta sauko ƙasa ta ɗebo abinci ta ci.








Tana gama cin abincin ta ɗauki wayarta ta kunna data, ko 5 minutes ba ta yi da ɗaukar wayar ba kiran Ahmad ya shigo. Ta yi murmushi sannan ta d'aga ta kara a kunnenta, muryar su Afrah ta ji a maimakon ta Ahmad, suna kiran sunanta cikin karaɗin su. "Aunty! Aunty!" Ta ce "Na'am, Yaran kirki dafatan kuna lafiya?" Amrah ta ce "Lafiya k'alau Aunty." Ta ce "Ina Ummi da Aunty Zahra da Abba?" Suka ce "Suna gida." Ta ce "To ku gaishe su." Suka shiga yi mata hirar makarantarsu da bata labarin kayan wasan da Daddy ya siyo musu. Ta ce "Lallai ƴan gatan Daddy, ina Daddy'n yake?" Amrah ta ce "Gashi nan a kwance, bashi da lafiya." Cikin damuwa ta ce "Bashi da lafiya kuma, me yake damunsa?" Ahmad dake kwance yana sauraren su ya tashi zaune tare yi musu alamar su kawo masa wayar. Amrah ta ce "Ya tashi Aunty, ya ce na bashi wayar." Yarinyar ta miƙa masa wayar, ya karɓa ba tare da ya cire ta a speaker ba ya ce "Princesss.!" Cikin kasalalliyar murya. Ta ce "Na'am Uncle, meke damun ka?" Ya sauke numfashi ya ce "Babu komai." Cikin shagwab'a ta ce "Please Uncle ka faɗa mun, hankalina gaba-d'aya ya tashi da aka ce mun baka da lafiya." Ya ce "Ba ciwo nake ba Princess, kawai ina jin wani iri a cikin zuciyata kamar zan rasa ki." Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Twins dake kallon sa suna sauraren su duk da ba fahimta suke ba, Afrah ta ce "Daddy Aunty ta yi shiru, ko ta kashe wayar ne?" Ya ce "A'a bata son magana da ni ne, Aunty ku kaɗai take so bata so na." Yarinyar ta waro Ido ta ce "She like you Daddy." Ya ce "No, ask her?" Yarinyar ta ɗauki wayar da sauri tare da ɓata fuska ta ce "Aunty wai bakya son Daddy'n mu?" Amrah ta tari numfashin ƴar'uwarta da sauri da faɗin "Daddy yana da kirki fa Aunty." Neehal ta sauke numfashi tare yin murmushi domin ta gane wayo Ahmad ya shirya mata. A hankali ta ce "Ina son Daddy sosai Yarana, wasa yake muku." Ahmad ya lumshe idonsa tare yin wani sassanyan murmushi, duk da ba direct shi ta faɗa wa tana son shi ba amma kalmar ta doki zuciyarsa. Afrah ta kama hannunsa ta ce "Daddy Aunty ta ce tana sonka." Ya girgiza kai ya ce "Ai bata faɗa mun ba, ku ta faɗa wa." Cikin shagwab'a Amrah ta ce "Aunty please ki cewa Daddy kina son shi, tunda kina son mu ai kina son Daddy'n mu ko?" Ta ce "Eh mana, bawa Daddy wayar za mu yi magana da shi." Ya karɓa ya cire ta a speaker sannan ya kara a kunnensa ya ce "Uhm? ina jin ki." Ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, ta ce. "Uncle meke damun ka?" Ya ce "Babu komai sai son ki Princess." Ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Ya yi ƙasa da murya ya ce "Princess please say you love me, baki taɓa faɗa mun ba fa." Ta ce "Gashi nan kai ka faɗa, kuma already You know I....." Sai kuma ta yi shiru. Cikin zak'uwa ya ce "Please Princess say it, ko zan ji daɗi a raina." Ta lumshe ido cikin shauƙi tare da yin ƙasa da murya sosai ta ce "I Love You Doctor Ahmad!" Sai kuma ta yi saurin zare wayar daga kunnen ta, ta yi hanging up. Sai jin ɗil ya yi alamun ta kashe wayar. Ya yi murmushi cikin tsananin farinciki ya ajiye wayar a gefen sa, sai ya tuno lokacin da tana ƙarama da ya ce mata I love You, ta ce "Love You too Uncle." Ya janyo ƴaƴansa da suka fara wasan su da sabbin teddy's ɗin da ya siyo musu ya rungume su a jininsa ya ce "Aunty ta kusa dawowa nan gidan mu zauna tare da ita." Yaran suka waro suka ce "Daddy When?" Ya ce "Soon Insha Allah." Sai suka bar jikinsa suka fara murnar Aunty zata dawo gidansu." Ahmad ya bi su da kallo yana tunanin farincikin da kids ɗinsa za su yi idan ya auri Neehal, da shi da his kids suna buƙatar ta a cikin rayuwar su, yaran suna sonta sosai dan har mamakin hakan yake, dan yanzu komai za su yi sai sun ambaci sunan Aunty, in unguwa suka ce suna dawowa za su je akira musu Aunty su bata labari, idan makaranta ce ma haka ne. Ya koma ya kwanta tare da janyo pillow ya rungume a ƙirjinsa gami da lumshe idonsa. A daa ya bar Neehal ta ƙarasa school ɗinta kafin ya tura a yi maganar auransu, amma a yanzu sai yake ganin kamar ba zai iya jiran watannin da suka rage mata ba ta ƙarasa karatun, ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba. A ɓangaren Neehal itama lumshe ido ta yi ta kwanta a jikin a kujera bayan ta katse wayar da murmushi ɗauke akan fuskarta. 'Uncle rigima.' Ta faɗi haka a ranta. Ƙarar shigowar text message cikin wayarta yasa ta buɗe ido ta ɗauki wayar ta duba, kamar yadda ta zata shine yay mata text ɗin, ta shiga karantawa a zuciyarta kamar haka. _Thank You so much Princess, you make me Happier, I love you so much._ Ta yi murmushi ba tare da ta yi masa reply ba ta tashi ta haye upstairs.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣7️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














...........Bayan Sallar Magriba Neehal tana zaune a falon ƙasa tana sauraren karatun Alkur'anin dake tashi a cikin speaker, wanda ta yi connecting ɗinsa da wayarta. A hankali take bin karatun idanunta a lumshe. Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo tare da yin Sallama cikin kamilalliyar muryarsa. Bata ji sallamar ba ma hankalinta yana kan karatun, har ya nemi guri ya zauna, k'amshin turarensa ne ya fargar da ita zuwan sa. Ta buɗe idonta da sauri tare da tashi daga kishingid'en da take. Ta waro Ido cikin murmushi tana kallon sa, kamar yadda shima yake kallon ta. Ta saka stop a karatun, sannan ta tashi ta koma ta zauna a kusa da shi. A hankali ta ce "Ina yini Yaya." Ya ce "Lafiya k'alau." Ta ce "Ya Aunty Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Ta murmusa ta ce "Yaya na ga sak'on ka, thank you so much, Allah ya ƙara buɗi mai albarka." Ya lumshe ido ya buɗe a kanta ya ce "Amin." Ta miƙe tare da faɗin, "Bari na kira Mama." Bai ce komai ba har ta haye upstairs. Ta shiga ɗakin Mama da sallama, Mama dake shiryawa ta amsa mata, ta ce "Mama Yaya ya zo, yana ƙasa." Mama ta ce "Okay I will come." Ta juya ta koma ƙasa ta zauna a kusa da shi, ta shiga aikin kallon sa, shi kuma yana ta aikin latsa waya. Sai ta ga kamar ƙara kyau yake, ko dan ƙarshe ne shi a iya wanka da iya ɗaukar dressing. Ta kalli bak'ar sumar kansa wadda daga gani babu tambaya ba ƙaramin kuɗi ake kashe mata ba. Ta lumshe ido a ranta tana faɗin 'Ba a ƙasa ya ɗauki gayu ba, dan Mama ƙarshe ce itama a wannan fannin. Mama ta shigo falon tare da faɗin, "Neehal ki kawo masa abinci mana." Ta miƙe tare da amsawa ta nufi kitchen ɗin. Mama ta zauna a kujerar dake fuskantar sa, fuska a sake ya ce "Ina yini Mum." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ya Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Mama ta ɗan ƙura masa ido na wasu sakanni sannan ta ce "Ameen! Is everything okay?" Ya ce "Komai lafiya Mum, me kika gani?" Mama ta ce "You look so worry." Ya yi murmushi ya ce "Nothing Mum, idan ma da akwai wani abu yanayin aiki ne kawai." Mama ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a, sai a cigaba da dagewa da addu'a." Ya ce "Insha Allah Mum." Dai-dai lokacin Neehal ta fito daga kitchen ta ajiye tray a gabansa, ta tsugunna dan sarving ɗinsa, Mama ta dakatar da ita da faɗin. "Barshi Daughter, je ki gyara mun bedroom i will save him." Ta ce "Toh Mama." Tare da nufar sama. Mama ta sakko ta zuba masa abincin a plate, ta dube shi ta ce "Sakko ka ci, and no more excuse or saying you are full." Ya yi murmushi tare da saukowa ya zauna a kusa da ita, ya jawo abincin gaban sa ya ce "Yaushe da rabon da ki yi save ɗina Mum?" Mama ta harare shi ta ce "Kasan jariri ne ai kai, da sai na zuba maka abinci zaka ci." Ya yi murmushi ya ce "Before you getting a Daughter ai kina mun, tunda kika yi ƴa kika daina yayi na." Mama ta yi murmushi ganin yanda ya wani marairaice ta ce "Au har wani daina yayin ka na yi?" Ya lumshe kyawawan idanunsa ya buɗe ya ce "Eh mana." Mama ta ce "Never Ameen, ai babu wani abu da zai yi replacing ɗinka a zuciyata, kai ɗin ne sometimes nima ba gane kanka nake ba." Ya yi murmushi bai ce komai ba ya yi Bismillah ya fara cin abincin sa. Mama ta bishi da kallo cike da k'auna, a ranta ta ce "My Son you will never change daga miskilanci." Ta yi zaton idan ya yi aure zai rage, amma sai ta ga jiya i yau, kamar ma ƙara masa a kay. Kaɗan ya ci abincin ya ajiye spoon ya ce ya k'oshi, sannan ya sha ruwa yay mata sallama ya tafi. Mama ta tattara kayan ta kai kitchen bayan ya fice.






Sai da suka yi Sallar isha'i sannan Mama ta zaunar da Neehal a ɗakinta akan maganar da ta ce zasu yi. Tana duban ta seriously ta ce "Neehal ɗazu kawunki Malam Musa ya zo, yaso ya zauna ya jira ki dawo ku gaisa amma akai masa kiran gaggawa a gurin aikin su. Kuma dalilin zuwan nasa ya zo ne akan ya kamata idan kina da tsayayye ya fito a yi maganar auran ku." Ta d'ago ta dubi Mama da sauri amma batai magana ba. Mama ta cigaba da magana da faɗin, "Na ce masa akwai wanda yake zuwa gurin ki, dan kun ma daɗe kun kusa shekara tare, amma mu da muna jiran ki kammala karatun ki ne sai mu yi masa magana idan da gaske yake sai ya fito a yi maganar biki." Neehal ta sauke numfashi tare da yin ƙasa da kanta, Mama ta ce. "Ya ce duk wannan ba matsala ba ce, idan gasken yake ya turo a yi maganar auran naku, bayan kin kammala karatun naki sai a yi bikin." Neehal ta d'ago ta dubi Mama gabanta na fad'uwa ta ce "Mama duk yanda kuka yanke dai-dai ne, kuma duk abun da kuka ce shi zan bi." Mama ta ce "Haka ne Daughter, Allah yay miki albarka, yanzu idan Daddy ya dawo zamu tattauna ni da shi, yanda muka yi zan sanar miki sai ki faɗawa Sadik ɗin." Neehal ta gyaɗa mata kai, tana son tay mata maganar Ahmad amma kuma ta rasa ta ina zata fara. Mama dake nazartar ta, ta ce "Neehal me kike son cewa? Ko baki son Sadik ɗin ne?" Ta girgiza mata kai cikin sanyin jiki. Mama ta ce "To ya na ga gaba-ɗaya yanayinki ya sauya, kamar ba ki yi farinciki ba, kin ga Daughter idan da akwai wata matsalar ki faɗa mun." Ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce "Uncle Ahmad." Mama ta yi murmushi ta ce "Me ya faru da shi?" Ta buɗe baki kamar zata yi magana sai ta fasa. Mama ta ce "Na san soyayya kuke yi da shi ai, na zuba miki ido ne kawai in ga iya gudun ruwanki." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunya. Mama ta ce "Amma Neehal me yasa kina tare da Sadik kike kula Ahmad da sunan soyayya? Hakan ba dai-dai ba ne." Ta sauke numfashi ta ce "Mama i can't reject him, saboda shi ma ya taimake ni a lokacin da nake buƙatar taimako." Mama "You are right, but you did a mistake." Ta ce "Mama na sani, amma ban san yaya zan yi ba ne a time ɗin." Mama ta ce "Shikenan, yanzu shi kike so ko Sadik ɗin. Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama ta ce "Uhm? Ke nake sauraro." Ta ce "Mama na rasa wanda zan zab'a a cikin su, kowanne a cikin su yana da good quality, amma Mama ki zaɓar mun ɗaya a cikin su Please, duk wanda kika zaɓar mun i will accept him." Mama ta girgiza kai tare da dafa ƙafaɗarta ta ce. "Neehal miji fa, abokin rayuwarki wanda zaku yi rayuwar da baku taɓa yin irinta da kowa ba a duniyar nan. Dan haka ke ya kamata ki zab'arwa kanki wanda hankalin ki ya fi kwanciya da shi. Wanda kika yaba nagartar shi kuma kuka fahimci juna, wanda kike ganin zai baki farinciki ya kuma riƙe ki amana. Duk da mazan yanzu sai addu'a, amma ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, akwai nagari wanda muke fatan Allah ya haɗa ku da su. Dan haka ki je ki nutsu ki yi shawara ki tantance wanda kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi, kafin mu gama magana da Dad sai ki sanar mun wanda kika fitar, sai na faɗa musu a san abun yi. Sannan kuma ki dage da addu'a da neman zaɓin Allah." Neehal ta sauke numfashi cikin rashin sanin abun yi ta gyaɗawa Mama kai. Mama ta tashi tana faɗin. "Bari na je part ɗin Daddy." Ta gyaɗa mata kai kawai still bata yi magana ba. Bayan fitar Mama ta kwanta akan gado ta faɗa duniyar tunani. Ta fara tuno farkon haɗuwar su da Sadik da irin mutuncin da yay mata, ta kuma tuno irin tarin soyayyar da yake mata, da kuma damuwar da yake shiga a sanadin ta, domin ta san komai da ya faru a gidansu ya sanar mata babu abun da ya ɓoye mata. Ta tuna alkawarin da tay masa lokacin da ta je asibiti dubo shi da ba shi da lafiya, ya kama hannunta ya ce mata. "Neehal dan Allah duk runtsi karki bari a raba mu, Wlh idan na rasa ki mutuwa zan yi." Tana hawaye ta ce masa "Baza ka mutu ba Ya Sadik ɗina Insha Allahu kai ne mijina, na maka alƙawarin indai kana raye ba zan taɓa aurar wanin ka ba." And then ta komar da tunanin nata kan Ahmad, mutumin da yay ta dakon soyayyarta tsawon shekaru, kuma ya taimaka mata a lokacin da take da buƙatar taimako, ga kuma Ƴaƴansa wanda suke k'aunarta take k'aunar su, zata so ta auri Ahmad ko dan ta kula da twins, ta maye musu gurbin mahaifiya da suka rasa. Ta gyara kwanciyarta tana son ta tantance wa tafi so a tsakanin su amma ƙwaƙwalwarta ta kasa yi mata wannan aikin. Ganin ta kasa samun mafita sai ta yanke shawarar zata tunkari ƴar'uwa kuma Aminiyarta wadda bata da kamar ta wato Haneefah da wannan maganar, domin ta bata shawara. Da wannan tunanin ta miƙe ta koma ɗakinta.










Mama kuwa sai da ta zubawa Daddy abinci ya ci sannan ta sanar masa da zuwan Kawu Musa da kuma yanda suka yi da shi. Daddy ya numfasa ya ce "Haka ne, kuma abun da ya faɗa gaskiya ne, nima da na so na ce ta turo mun shi yaron mu yi magana, amma sai na ce mu bari ta gama karatun ta, ta ɗan huta tukunna. Ko dan damuwar da ta shiga kwanaki akan rasuwar sauran samarinta." Mama ta ce "Haka ne, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya kawar da duk wata fitina a wannan karon a yi lafiya a gama lafiya." Daddy ya ce "Amin, yanzu ta fara turo mun shi yaron mu yi magana da shi, kafin akai ga maganar turo magabatansa." Mama ta ce "To ai ita yanzu wai ta rasa wa zata zaɓa, ka san baban Twins shima son ta yake." Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Neehal ta sanar masa. Daddy ya yi murmushi ya ce "Daughter mai farin jini." Mama ta ce "Hmm, Allah ya kyauta, amma ni nafi mata sha'awar Ahmad ɗin, tunda shi babba ne, ga kuma yaransa suna buƙatar kulawar uwa, amma kuma idan ta zaɓe shi ta bar Sadik shi kuma bata kyauta masa ba, tunda ya riga Ahmad ɗin zuwa." Daddy ya ce. "Allah ya zaɓa mafi Alkhairi kawai." Mama ta ce "Amin Amin." Dad ya ce "Ɗazu Saratu ta kira ni, tana mun shirmen ku na mata." Mama ta ce "Shirmen me kuma?" Dad ya ce "Ita fa har yanzu bata haqura da batun Ameen da Hameedah ba, na ce mata ban da abunta Ameen fa ko shekara bai rufa da yin aure ba, idan ma auran zai ƙara ai ba yanzu ba, ballantana ma na san halin Ameen da ƙyar zai yarda ya ƙara aure." Mama ta ce "Allah ya kawo mata miji nagari ta yi auranta, amma Ameen a farko ma ya ƙi auren ta balle kuma yanzu." Daddy ya ce "Nima shi na gani dai Doctor." Mama ta ce "Allah ya kyauta."










Washegari ta kama Friday lecture ɗin safe gare ta 8_12. Kafin ɗaya ta dawo gida, bayan ta yi Sallah ta ci abinci ta shirya tay wa Mama Sallama ta tafi gidan Haneefah kamar yadda ta k'udurta. Haneefah tana kitchen tana suyar wainar fulawa ta ji ana knocking ƙofar falo, bata fita ta falo ba ta buɗe ƙofar kitchen ta baya ta lek'a dan ganin waye. Hango Neehal da ta yi yasa ta waro ido da ƙarfi ta ce, "Kan uban nan, zuwa babu sanarwa." Neehal ta yi murmushi tare da ƙarasowa ƙofar kitchen ɗin ta juya ido ta ce. "Ko in koma ne?" Haneefah ta rungume ta cikin murnar ganin ta ta ce, "Wa ya isa ke da gidan ki." Neehal ta ce "Shi na gani dai." Haneefah ta jata suka shiga kitchen jin wainar data bari akan wuta tana kamawa. Neehal ta riƙe hab'a ta ce "Unborn me cin wainar fulawa ne kenan?" Haneefah ta ce "Rufa mun asiri da wani batun unborn, ina da sauran shekara biyu da watanni

Please Login or Register in order to submit comment