Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba." Yarinyar ta ɓata fuska. Neehal ta bi ƙasan Falon da kallo, tiles ɗin ta gani kamar da datti. A hankali ta tashi ta shiga duba falon ko za ta ga tsintsiya, a bakin ƙofa ta ganta tare da mopper, ɗauka ta yi ta shiga share falon, bayan ta gama ta yi mopping ɗin shi, tana cikin yi Hafsah ta sakko, da mamaki take duban Neehal, can kuma ta tab'e baki ta ce "Ina kika samu ruwan da kike mopping?" Toilet ɗin dake falon Neehal ta nuna mata da hannunta ba tare da ta yi magana ba, Hafsat ta wuce kitchen tana tab'e baki. Amrah ta dubi Neehal ta ce "Aunty zan ci abinci." Neehal ta mata shiru, har sai da yarinyar ta ƙara maimaita mata sannan ta ce "Ba ki ci abinci ba ne a gida?" Amrah ta gyaɗa mata kai tana keɓe fuska, Neehal ta yi shiru kawai dan bata san me zata ce mata ba. Hafsah ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da lemo ta ajiye a gaban yaran, ta dubi Neehal a yatsine ta ce ki shiga kitchen ki dafa muku abin da zaku ci. Neehal ta mata wani kallo sannan ta ce "Toh." a ranta tana faɗin 'Ai ba yunwa na ce miki ina ji ba.' Daga haka Hafsah ta koma sama, ashe Ameen ne ya mata waya yana hanya shi yasa ta yi sauri ta sakko ta kawo wa su Neehal drinks dan kar ya dawo ya ga bata basu ba. Bayan Neehal ta gama mopping ɗin ta koma ta zauna tana duban su Afrah dake shan lemo, Hafsah ta ƙara sakkowa hannunta ɗauke plate ta ajiye a gaban Neehal, A hankali Neehal ta ce "Thank you." Hafsat ba ta ce komai ba ta juya ta koma sama. Cake ne da cin_cin da Donot a cikin plate ɗin, Neehal ta ce su Amrah su sakko su ci, ita kuwa ko kallon snacks ɗin bata ƙara yi ba. Su ma kaɗan suka ci suka ce sun k'oshi. Neehal ta duba time a wayarta ta ga uku saura, lumshe idonta ta yi ta kwanta akan kujera tana jin cikinta na juya mata, zuciyarta kuwa cike take da mamakin dalilin ya sa Hafsah ba ta k'aunarta, dan ita ba ta taɓa tunanin irin wannan tarb'ar daga gare ta ba, yanda tasan amare idan ka je gidajensu kamar su mai da mutum ciki dan murna amma..... Ƙarar buɗe ƙofar falon ya katse mata tunanin da take. Da Sallama ya shigo falon duk da be yi tunanin da mutane a ciki ba, dan yasan Hafsah ba ta zaman ƙasa. Waro ido ya yi ganin Twins fuskarsa na nuna mamakinsa na ganinsu. Su ma suna ganinshi suka nufe shi da gudu suna faɗin "Uncle !." Dan ɗan zuwan da Ameen yake gida sun saba da shi. Ameen ya d'aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi, yaran suka shiga ƙyalƙyala dariya sannan suka gaishe shi, ya amsa musu cikin kulawa. Afrah ta ce "Uncle nan gidanka ne?" Ameen ya mata murmushi tare da gyaɗa mata kai. Neehal wadda ta tashi zaune tun shigowar shi, cikin boye ɓacin ran Hafsah da dauriyar ciwon cikin da take ji ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Ameen ya zauna a gefen ta yana kallonta cikin nazarta yanayinta ya ce "Yawwa." Neehal ta yi ƙasa da kanta ganin yana binta da wani irin kallo, a sanyaye ta ce "Ina yini." Ya amsa da "Lafiya k'alau, ya aiki?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ina Haneefah fa, kika zo ke kaɗai?" ta ce "Tana Abuja ta je gidan Yayan Abbansu sai Sunday zata dawo." Ameen ya gyaɗa kai tare da bin falon da kallo, sai kuma ya dawo da dubansa ga Neehal ya ce "Ina matar gidan?" Neehal ta ce "Yanzu ta hau sama." Ameen ya miƙe hannayensa riƙe dana Twins suka hau saman, Neehal ta bi su da kallo tare da jan numfashi. Duk murna da d'okin ganin Yayan nata da take takaicin Hafsat ya sa ta ma dena. Ko minti biyar Ameen be yi da hawa saman ba suka sakko tare da Hafsah, wadda ta faɗaɗa fara'a akan fuskarta. Tana duban Neehal ta ce "Sister na bar ki ke kaɗai ko? Sorry toilet na shiga ne." Mamakin Hafsat ne ya kusa kashe Neehal, shanye mamakinta ta yi ta kirkiro murmushi ta ce "Ba komai Aunty." Hafsah ta dubi Ameen da ya zauna yana kallonsu ta ce "Honey Ka ga hira da Sister ta ɗauke mun hankali ko girki ban daura ba, duk da ma na tambaye ta mai za su ci ta ƙi faɗa mun, na ce kuma ta shiga ta girka da kanta ta ƙi, sai ka ce wata bakuwa." Ameen yana duban Neehal ya ce "Why?" Neehal ta ce "Yaya mun ci fa snacks mun k'oshi." Ameen ya ce "Snacks ai ba abinci ba ne, ki shiga kitchen ki dafa muku abun da zaku ci." Neehal ba za ta iya musu da Yayan nata ba, hakan yasa ta miƙe ta nufi kitchen ɗin." Hafsah na murmushi ta ce "Ko ke fa yar ƙanwata, amma da kin ƙi sakin jiki kamar wata baquwa." Neehal dai bata yanka mata ba ta shige kitchen zuciyarta cike da mamakin kissa irin ta Hafsah. Duk da bata jin dadi haka ta dafa musu jallop ɗin sphagetti, kafin ta gama an shiga sallar Asr, hakan yasa da ta gama ta juye a warmer sannan ta dawo falon, Twins ne kawai a falon suna kallon cartoon ɗin da Ameen ya kunna musu, Ameen ya fita Masallaci ita kuma Hafsat tana sama. Ɗakin dake falon Neehal ta shiga ta yi Sallah, bayan ta idar ta fito falo ta tarar har Ameen ya dawo, Hafsah ma ta sakko. "Sannu da aiki my sister, Allah ya saka da Alkhairi ya baki miji na gari, bari na je na ga me aka girka mana haka ne, duk muna nan k'amshi ya buɗaɗe mu yawun mu sai tsinkewa yake." Hafsah ta faɗi haka cikin iyayi tana murmushin da be kai zuci ba. Neehal ta yi ɗan murmusa kawai, dan mgn ma bata son yi saboda yanda take jin cikinta. Hafsah ta miƙe ta shiga kitchen ɗin, ɗauko warmer ta yi gaba-d'aya tare da plates da pork ta ajiye akan dinning, sannan ta ɗauko drinks shima ta aje. Ta dube su duka ta ce "Ku taso mu ci abincin." Neehal dai kamar ta ce ta k'oshi, amma ta san ko ta faɗa Ameen ba kyale ta ze yi ba sai ta ci, hakan yasa ta miƙe tana taune lips d'inta ta nufi dinning ɗin. Ameen dai kallonta kawai yake amma ya gane akwai abun da ke damunta. Duban Hafsah ya yi ya ce "Ku ci kawai am full." A karamin plate Hafsah ta zuba wa Twins na su abincin ta ajiye musu ƙasan carpet ɗin dake tsakiyar falon. Da kanta ta zuba wa Neehal abincin sannan ta zuba nata itama, ba kunya ta shiga durawa cikinta taliyar dan ta mata daɗi ba kaɗan ba. Neehal ta kasa cin abincin sai juya pork ɗin take a cikin taliyar, har taliyar ta fara sanyi. Da ƙyar dai ta daure ta tsakura ta kai bakinta, a hankali ta shiga taunawa cikin nutsuwa, Hafsat kuwa tana zuba lauma tana harararta a fakaice. Cokali uku Neehal ta ci ta ajiye pork ɗin da sauri saboda murd'awar da cikinta ya mata, dafe cikin ta yi tare da taune lips ɗinta sosai, duk yanda taso daurewa amma ta kasa, Ameen dake latsa wayarsa amma hankalinsa gaba-d'aya yana kanta ya ce "What happened?" Hafsah cikin nuna damuwa itama ta ce "Sister me ya faru?" Neehal cikin sanyi ta ce "Cikina." Ameen ya miƙe da sauri ya ƙaraso dinning ɗin yana mata sannu, miƙewa ta yi ta nufi toilet ɗin dake falon da gudu ta fara kela amai. A rude Ameen yake faɗin "Sannu, Sorry, dama ba ki da lafiya?" Neehal dai bata samu damar ba shi amsa ba, bayan ta gama ya taimaka mata ta fito tana numfarfashi ta kwanta a ƙasa, Twins suka bita da kallo. Sai da ya tsaftace toilet ɗin sannan ya fito, sai a sannan Hafsah ta yiwa Neehal sannu, tana pretending kamar ta damu, nan kwa a zuciyarta ji take kamar ta ƙarasa ta dan tsanar da take mata. Neehal ta fara nuk'urk'usu a ƙasa tana hawaye, sosai Ameen ya rude dan ya san wahalar da take sha a ciwon ciki, hakan ya ƙara konawa Hafsah rai, dan ko first night ɗinsu da bata da lafiya be rude haka ba sai a kan wannan figaggiyar yarinyar. Neehal ta riko hannun Ameen a wahalce ta ce "Yaya cikina kamar zan mutu, ka kai ni gurin Mama Please." Ameen ya tashi ya haura sama da sauri ya ɗakko car key ɗinsa ya ɗauki Neehal kamar jaririya ya yi waje da ita, Twins da ganin halin da Auntinsu take ciki yasa su kuka suka bi bayanshi da gudu. Takaici kamar ya kashe Hafsah ganin yanda Ameen ya wani gigice, tsaki ta ja ta ɗauki handbag da takalman su Neehal ta bi bayansu. Har ya kwantar da Neehal a bayan Motar su twins kuma yasa su a front seat. ajiye takalman ta yi a gaban Motar fuskarta ɗauke da jimamin ƙarya, Ameen bai bi ta kanta ba ya ja Motar ya danna horn, mai gadi ya taso da sauri ya buɗe masa gate ya fice daga gidan...........✍️


















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:43] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL ⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_










*2️⃣2️⃣*














.........A ɓangaren Ango da Amarya kuwa komai ya tafi yadda ya kamata a daren da aka kaita, sai dai Ameen ya sha rawar kai a gurin Hafsat, daga baya kuma ta koma raki da shagwab'a. Sai dai abu na farko da Ameen ya fuskanta dangane da Hafsat tana da ƙarancin ilimin Addini da shi kanshi addinin ma, dan Sallah ma da asuba har ya je masallaci ya dawo ba ta yi ba tana kwance, da ƙyar ya tashe ta ta yi, duk ya san bata jin dad'i amma ai ba cutar da zata hanata Sallah take ba. Haka ɓangaren gyaran gida ma babu abun da ta taɓa da sunan gyara,duk da jikin nata ya warware, sai da ƴan'uwanta suka zo da yamma ne ma suka gyara mata gidan. Da daddare Mama ta aiko musu da dinner, bayan sun gama ci ta tashi ta bar kayan a wurin, Ameen ya bita da kallo cikin mamaki zuciyarsa cike da takaicinta, amma ya danne bai nuna ba ya kwashe kayan ya kai kitchen, wurin da suka ci abincin kuwa ko arzik'in tattarewa bai samu ba haka ya kwana.










Washegari misalin ƙarfe Takwas da ƴan mutuna na safe Mama tana zaune a falonta tana karatun Alkur'ani da bata samu ta yi ba sai da ta gama haɗa musu breakfast saboda fitar da za su yi, Neehal ce ta shigon falon, tana ɓata fuska wai ita a dole fushi take ta zauna a kusa da Mama tana jiran ta gama karatun. Mama ta kai ƙarshen aya ta d'ago tana dubanta. A hankali Neehal ta ce "Ina kwana." Mama ta ce "Lafiya k'alau, Ina yaran?" Neehal ta ce "Bacci suke." Mama ta ce "Bacci kuma har yanzu? Kin san fa za mu fita." ta ce "Yanzu za su tashi sai na musu wanka." Mama ta ce "Ki sauka ƙasa ki yi break." Neehal ta miƙe ta ce "Bari na fara musu wankan sai mu yi tare." Tana komawa ɗaki ta tarar sun tashi duka suna zauna, ta ƙarasa gadon da sauri tana dubansu. Afrah ta ce "Aunty yau za mu gurin Daddy ko?" Neehal ta ce "Insha Allah." Amrah ta ce "Zaki bi mu ko Aunty?" Neehal ta ce "Ehh." Tana cire musu kaya ta ce "Wa yake muku wanka a gida?" Amrah ta ce "Baaba talatu, idan mun je gidan Mommy kuma Aunty zahrah." Neehal ta gyaɗa kai ta ce "Ku da wa kuke bacci." Amrah ta ce "Mu da Baaba Talatu." Neehal ta ce "A gidanku take itama?" Suka haɗa baki suka ce "Ehh." Bayan ta musu wanka tana shafa musu lotion Afrah ta ce "Aunty ba mu yi karatu ba, kuma kullum Daddy yana mana idan mun tashi." Neehal ta ce karatun me?" Afrah ta ce "Qur'an." Neehal ta ce "Ku biya mun naji to." Suka haɗa baki sukai basmala cikin karatun yara suka fara karanto Suratul Nas." Harta gama shirya su ba su gama karatun ba. Neehal ta jinjina wa yaran sosai a ƙananun shekarun su amma sun iya karatun, sai da ɗan gyararraki da ba za a rasa ba. Neehal ta kamo hannunsu suka sakko ƙasa suka yi break, suna gamawa ta haye sama dan yin wanka su kuma ta barsu a falon suna kallo tare da su Dije. Wajen ƙarfe tara Ameen ya kira Mama, ya gaisheta ta tambaye shi lafiyar Hafsah ya ce tanan k'lu. Kafin ƙarfe goma sun fita, duk inda ya kamata su je sun je dan bayar da cikiyar su Afrah, Neehal dai kamar ta zunduma ihu haka take ji, a hanyarsu ta dawowa kuwa suna Mota ta saka kuka, dan ji take kamar har anga ƴan'uwan su Afrah sun karɓe su, Mama ta mata tsawa ta ce "Ta rufe musu baki kar ranta ya ɓaci." Daddy kuma ya rarrashe ta. Wajen 1 suka koma gida, ɗakinta ta yi wucewarta da Twins ta kulle suka kwanta, hakan yasa baccin dole ya ɗauke su dukan su. Sai da 3 ta wuce Mama ta buga mata ƙofa dan su tashi su ci abinci. Bayan Sallar la'asar ma ta ƙara jan su daki ta samu game a wayarta ita kuma ta kwanta, Mama dai kallonta kawai take duk abun da take ba ta kuta ba. Har Ameen ya zo gidan da Yamma ya tafi ba ta sani ba tana ɗaki. Wunin yau ko kiranta aka yi a waya sai gabanta ya faɗi saboda tunanin ko ƴan'uwan su Afrah ne, dan Numbern'ta aka bada idan iyayen yaran sun ji cikiyar su kira. Bayan Magriba Mama ta kwankwasa mata ƙofa, ta taso ta buɗe, Mama ta ce mata "Ki sauka ƙasa Sadik yana jiranki, ya kira wayarki dan iskanci kika ƙi d'agawa." Neehal ta ce "Ban gani ba wayar na silent." Mama ta ce "Ke kika sani, kuma ki fito da Yara su shaƙata in ke kin zaɓi zaman ɗaki su ba za su yi ba." ta ce "Toh." Mama ta yi wucewarta. Hijabi ta zira ta kamo hannunsu suka fito, suna ta murna sun ɗauka fita za su ta yi. Sadik yana zaune yana latsa waya, k'amshinsa ya cika falon gaba-d'aya, Mama ta sa su Dije sun kawo masa drinks da abinci. Neehal ta yi masa sallama tare da zama a kujerar dake gefen ta sa, ya amsa mata yana kallonta. Su Afrah kuwa suna can gefe sun samu kallo. Sadik ya ce "Ya gajiyar biki kuma?" Neehal da ta ƙi d'agowa ta ce "Babu gajiya, ya kaje gida.?" Ya ce "Lafiya k'alau." Suka yi shiru, ita tana wasa da yatsun hannunta shi kuma yana danna waya, can dai ya katse shirun da faɗin "Na yi tunanin ma bakya nan dana kira wayarki ba ki ɗauka ba, shigowa na yi in gaida Mama sai ta ce kina ciki." Neehal ta ce "Uhm ina kwance ne." Ya ce "Ba ki da lafiya ne?" Ta ce ",Lafiyata k'alau." Ya yi shiru yana kallonta na wasu sakanni, duk ta ƙi d'ago kanta amma ya fahimci tana cikin damuwa. Murya ƙasa_ƙasa seriously ya ce "Me ke damunki to?" Numfashi ta ja jin yadda ya yi maganar ta girgiza masa kai, ya ce "Neehal!." Ta d'ago da kanta a hankali ta ce "Na'am." Ya ce "Har yanzu baki saki jikinki da ni ba, baki ɗauke ni a matsayin brother ɗinki ba kamar yadda na ɗauke ki as my sister." Neehal ta yi shiru, Sadik ya ce "Okay thank you." Ganin yana ƙoƙarin miƙewa ta marairaice ta ce "I'm sorry ya Sadik, dan Allah kar kace haka, wlh ba haka ba ne." Ya ce "Ya ya ne?" Ta sauke numfashi cikin rashin sanin ta ina zata fara masa bayanin damuwarta, dan tabbas tana buƙatar share problem ɗinta da wani ko zata ji sauƙi a ranta, ita kanta tana mamakin yanda aka yi take son yaran haka." Sadik ganin ta yi shiru ya ce "Kar ki damu ba sai kin faɗa mun abunda ke damunki ba, but i promise you zan taya ki da addu'a." Neehal ta ce "No I will tell you now." A hankali ta shiga bawa Sadik labari tun daga time ɗin data tsinci su Afrah har zuwa yau. Sadik dake kallon ta ya ce "Gaskiya Mama take faɗa Neehal, ki yi imagine ace yaran nan yanda suke hannunki yanzu kawai ki tashi ki neme su ki rasa, na san hankalinki zai tashi ba kaɗan ba, to duk tashin hankalin da zaki yi ba za ki kai iyayensu ba, dan haka Mama ta fiki gaskiya. And please kuma ki dena damuwa akan hakan, yaran nan ko da sun koma gurin iyayensu ai hakan ba yana nufin kun rabu ba kenan, duk time ɗin da kike son ganinsu zaki je ki gan su kin ji." Neehal ta jinjina kai cikin gamsuwa da bayaninsa, ya ce "Yawwa sisina, ki kuma je ki bawa Mama hak'uri." Neehal ta ce "Insha Allah, na gode." Ya yi mata murmushi mai taushi yana jin sonta tamkar zai fasa masa zuciya. Cikin kankanin lokaci Neehal ta saki jikinta suka shiga hira da Sadik, sai gata tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ce take ta k'unci ba d'azu." Har kusan Tara da rabi Sadik bai tafi ba, duban agogon hannunsa ya yi da waro ido cikin mamaki ya ce "Haka dare ya yi ba mu yi Sallah ba, lallai yau hira ta yi daɗi." Neehal ta turo baki gaba ta ce "Yanzu sai ka ce zaka tafi ko?" Ya ce "Ehh mana, ko so kike Maamah ta rufe mun gida." Neehal ta ce "Sai ka kwana anan." Ya mata wani kallo ya miƙe ya ce "Wataran zan kwana not now." Miƙewa ta yi itama ta ce "Allah ya kai mu wataran ɗin, mu je in raka ka." A bakin part ɗin Mama suka tsaya suka yi sallama, har cikin ranta take jin dama kar ya tafi, dan yana ɗebe mata kewa ba kaɗan ba." Tana dawowa falo ta lek'a ɗakin su Dije ta ga ba su yi bacci ba hirarsu suke yi hakan yasa ta ce musu su kawo mata su Afrah sama, wanda tuni sun yi bacci. Ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana operating system. "Sannu da aiki Mama." Ta faɗa lokacin da take zama a kusa da ita, Mama ta ce "Yawwa sai yanzu ya tafi?" Ta ce "Eh." Mama ta ce "Ina yaran?" "Sun yi bacci." Neehal ta amsa, Mama ta ce "Sun dai ci abinci ko?" Neehal ta ce "Na basu popcorn kafin mu fito." Mama ta ce "Popcorn abinci ne?" Neehal ta ce "Da yawa suka ci ai, kuma da suna jin yunwa za su faɗa mun." Mama ta ce "Alright." Neehal ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Mama ki yi haquri akan abin da na yi, na gane gaskiya kika faɗa." Mama ta ce "Shikenan na ji dad'i da kika gane haka, wai har yanzu ba'a kira ki ba akan Yaran nan? tun d'azu nake so na tambaye ki kuma sai na sha'afa." Neehal ta ce "Ba a kira ba." Mama ta d'ago ta dube ta karon farko tun shigowar ta ɗakin ta ce "Bana son ƙarya fa Neehal kin sani, ki faɗa mun gaskiya ko sun kira." Neehal ta ce "Allah Mama ba'a kira ba, sai dai ko yanzu da na sauka ƙasa." Mama ta ce "Amma na yi mamaki, more than five Radios banda Televisions amma a ce ba'a samu wanda ya san su ba, Sadiya ma ta kira ni ta tambaye ni, Dad ma haka." Neehal ta ce "Nima Mama na yi mamaki, dan ko kirana akai sai na yi tunanin ko su ne." Mama ta jinjina kai kawai, Neehal ta ce "Mama kun yi waya da Yaya kuwa?" Mama ta ce "Ya zo ma d'azu." Neehal ta waro Ido ta ce "Amma shine bai neme ni ba." Mama ta ce "Ya tambaye ki na ce kina ɗaki a kwance, ko kina ta k'uncin zan je in kira ki ne." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta fice tana turo baki gaba, cikin takaicin Ameen ya zo amma ba su haɗu ba, shima kuma ko ya shigo ɗakin ya ganta. Gyarawa su Amrah kwanciya ta yi ta cire Hijab ɗin jikinta ta shiga toilet dan ɗauro alwala.










Goma saura Sadik ya ƙarasa gida, kamar yadda ya yi zato duka ƴan gidan nasu suna zaune a falon har Abbansu, bakinsa ɗauke da Sallama, gaba-d'aya suka zuba masa ido tare da amsa masa sallamar. Kusa da mahaifiyarsa ya je ya zauna a ƙasan kujerar da take ya mata sannu da gida, sannan ya gaishe da Abbansa da kishiyar Maamah wadda suke kira da Umma, k'annenshi kuma suka gaishe shi. Abbansa ya ce "Abubakar daga ina haka?" Sadik ya yi ƙasa da kansa tare da shafa sumar kansa, Abban ya kalli Maamah Wadda ke murmushi ƙasa_ƙasa yana murmushin shima, Umma kuwa tab'e baki ta yi ta ce "Hmmmm, Sadik dai ya soma ɓata wayonsa da yawon dare, da dai ba ya yi amma yanzu....." "Wacce irin magana ce wannan Ruqayyah kike yi?" Abba ya katse Umman a ɗan fusace, Maamah da annurin fuskarta ya ɗauke lokaci ɗaya jin kalaman Umma ta sauke numfashi cikin jin daɗin yanda Abban ya katse Umman ga aikabata mata ɗa da take ƙoƙarin yi." Sadik ma ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin yanda zugar Umman bata samu shiga ba a gurin Abban kamar yadda ta saba kodayaushe. Umma ba ta da aiki sai yi masa sharri a gurin Abbansa, kuma Maamah ba ta isa ta yi magana ba sai ta saka kuka ta ce tana nuna mata iko akan Sadik dan ta ga ita ba ta ƴaƴa maza, ai itama ɗanta ne ba zata cutar da shi ba. Shiru Umma ta yi ganin yanda Abban ya haɗe rai. Shima Abban shiru ya yi ganin yaransu na falon, miƙewa Sadik ya yi ya nufi bedroom ɗinsa dan yana da aikin da zai yi akan wani case da yake bincike akai.








Asalin Mahaifin Sadik mutumin Kano ne, ɗan kasuwa ne da yake da rufin asirinsa dai_dai gwargwado. Mahaifiyar Sadik kuma ƴar asalin garin Maiduguri ce kabilar Shuwa, aure ne ya kawo ta Kano. Fara ce kyakkyawa ga gashi har baya, a gurinta su Sadik suka gado kyau. Umma kuwa ƴar asalin jihar Kano ce, iyayenta a cikin gari suke, Maamah ba ta fi shekara 5 da aure ba Abba ya auro Umma, lokacin an haifi Sadik yana yaro. Ana zaton wuta a mak'era sai aka same ta a masak'a, domin kuwa Umma ce take da tsananin kishi da shegen makirci, ita kuwa Maamah da zuciya ɗaya take zaune da Umma, kuma duk kasancewarta Shuwa ba ta nuna wannan kishin na hauka, ga ta da haquri da addini. Su Sadik su biyar ne kawai a gurin mahaifinsu, a ɗakinsu su uku ne, Shine babba sai k'aninsa mai bi masa Bashir, sai autarsu Batul. Ita kuma Umma ƴaƴanta biyu kuma duk mata ne, kuma ta fi shekara goma kafin Allah ya bata haihuwar. Makirci kala_kala Umma ta dinga haɗawa Maamah a gurin Abba kafin ta haihuwa, wai Maamah tana mata gorin haihuwa. Hakan yasa Abba ya ce ƴaƴan Maamah itama ƴaƴan ta ne tunda Ƴaƴansa ne dan haka tana da iko akansu. Tun daga wannan rana fa Umma ta samu damar yiwa Sadik sharri iri_iri a wajen Abbansa, a matsayin tana faɗa masa gaskiya wadda Maaman take bo'yewa a cewar ta, kasancewar Abba matafiyi ne bai fiya zama a gari ba, saboda sha'anin kasuwancinsa. Haka Abba zai samu Sadik yay ta masa faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, itama Maamah bata tsira da faɗan Abban. Inda Allah ya taimaka kakarsu Sadik mahaifiyar Abba tana son su sosai, to wani sharrin idan Umma ta k'ulla ita take taka

Please Login or Register in order to submit comment