Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idonta tare da girgiza mata kai. Haneefah ta ce. "Are you sick? Ko kewar Maman ce kika fara tun yanzu?" Kamar zuga ta, ta yi sai ga hawayen da take ta ƙoƙarin mayarwa sun zubo. Cikin lallami Haneefah ta ce. "I'm sorry Besty, Dan Allah ki bar kukan nan kar hankalin mutane ya dawo kan ki." Ta share hawayen tare da gyaɗa mata kai. A hankali ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet ta yi brush, sannan ta fito ta tafi part ɗin Daddy, dan anan kayanta na sakawa suke. Mama da kanta ta kawo mata ruwan zafi da kayan haɗin tea, ta haɗa mata ita da su Afrah dake mak'ale da ita suka sha. Sannan ta kawo musu abubuwan toye_toye irin su, waina, sinasir, funkaso suka ci. Duk da ita Neehal kaɗan ta ci, dan da ƙyar suke iya wuce mak'oshinta, cusawa kawai take ganin idon Mama. Wajen ƙarfe tara Aunty Sadiya tasa ta, ta yi wanka, ta shirya cikin wani had'ad'd'en less ɗinkin riga da zani, ta yi kyau sosai duk da ba ai mata make up ba. Sai anjima mai make up ɗin zata zo har gida tay mata, tunda d'aurin Auren sai ƙarfe biyu na rana za'a yi, bayan an idar da sallar juma'a za'a daura. Ta dawo part ɗin Mama ta zauna suna ta yin pictures da su Haneefah. Abokan wasa nata tsokanarta. Ƙarfe goma na safe sai ga Aunty Fauziyya da Iman da Aiman sun zo. Neehal ta tarb'e su cikin fara'a, har da musu tsiyar shine tunda aka fara bikin ba su zo ba sai yau. Aunty Fauziyya ta bata haquri da cewar Iman ce bata jin daɗi shi yasa ba su zo ba. Neehal tay mata sannu cikin tausayawa, yarinyar duk ta rame ta d'ashe, ana kallon ta an ga mai ƙaramin ciki, itama Aunty Fauziyyan kamar me jinya ta k'anjale ta yi baƙi. Sai ga Hafsah ba kunya ta zo tana yiwa Neehal magana cikin fara'a, abun ya bawa Neehal mamaki, amma sai ta ɗauki hakan a matsayin fuska biyun da take mata. Kamar ta tambaye ta Ameen da kuma dalilin da yasa bai zo dinner jiya ba sai kuma ta fasa. Gida fa sai ƙara cika yake da baƙi mata da maza. Neehal har ta fara gajiya da gaisawa da mutane. Ƙarfe goma sha biyu na rana mai make up ta zo gidan ta fara yiwa Neehal kwalliya, wadda zuwa lokacin hankalinta gaba-ɗaya yana kan angon ta. Ta ƙara kikkiran sa bayan kiran da tay masa na safe amma bai ɗauka ba kuma bai kira ta ba har yanzu. Duk da ta masa uzurin may be ya shiga cikin hada_hada da mutane ne. A dai-dai lokacin Mama tana bedroom ɗin Daddy tana shiryawa cikin shigarta ta biyu a ranar, fuskarta ɗauke da farincikin nuna mata ranar D'aurin Auren Neehal da Allah ya yi. Tana zira sark'a Daddy ya shigo dakin kamar an jeho shi, kallo ɗaya tay masa ta cikin mudubi ta san akwai matsala. Gabanta ya yi mummunar fad'uwa, ta miƙe tsaye har wayarta dake kan cinyarta na faɗuwa a ƙasa ta juyo tana kallon Daddy dake ta goge gumin fuskarsa, in ba gizo idanunta ke mata ba har yar rama ta ga ya yi. A ruɗe ta ce. "Gen. Lafiya kuwa?" Daddy ya sauke zazzafan numfashi cikin tsananin damuwa ya ce. "Akwai matsala Doctor." Wani irin sarawa Mama ta ji kanta yay mata, jikinta har rawa ya fara, cikin rawar murya ta ce. "Matsalar me?" Daddy ya kamo hannunta kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu Mahifin Sadik ya kira ni, wai an neme shi an ransa." Mama ta waro Ido waje tare da k'wace hannunta daga na Daddy, cikin matuƙar tashin hankali ta ce. "Kamar ya an neme shi an rasa? Ina kuma zai tafi ranar Auren sa?" Daddy ya ce. "A yadda ya sanar mun ya ce, suna zargin sace shi aka yi, dan jiya har cikin dare yana gida cikin ƴan'uwa, amma tunda asuba mahaifin nasa ya shaida mun aka lura baya gidan, kuma ga wayoyinsa duka da komai nasa a ɗakin da ya kwana, harta silifas ɗinsa gashi nan a bakin toilet." Mama ta ji wani abu luuu ya gilma ta ƙwaƙwalwarta, zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfin gaske, cikin sark'ewar numfashi ta ce. "Me hakan yake nufi Daddy? Dan Allah karka ce mun an sace Sadik a yau ranar Auransa da Neehal, dan Allah Daddy kace mun kunnena ne bai ji dai-dai ba." Daddy ya riƙe ta ganin tana ƙoƙarin faɗuwa suka zauna a bakin gado. A gigice ya ce. "Calm dawn Doctor, jikina yana ba ni Insha Allahu za'a gan shi kafin time ɗin d'aurin Auren, may be wani gurin ya tafi zai dawo." Mama ta girgiza kai cikin hawaye ta ce. "Tunda har Mahaifinsa ya kira ka ya sanar maka to da akwai babbar matsala." Bata jira cewar Daddy ba, ta tashi cikin sauri ta ɗauki wayarta data faɗi ƙasa, ko gani bata yi sosai saboda tashin hankali ta shiga contact ta lalubo Numbern Maamah ta yi dialing. Kamar yadda ta yi zato bata ɗauki kiran ba. Ta juyo tana duban Daddy amma bata ce komai ba, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai take maimaitawa a cikin ranta. Ta dafe bango saboda jirin da take ji yana ɗibar ta. Aunty Sadiya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a tunaninta Mama ce kaɗai a ciki kamar yadda ta fita ta bar ta. Da mamaki take kallon su, ganin fuskokinsu cikin tashin hankali. Da mamaki ta ce. "Yaya Tafida lafiya?" Daddy ya sauke numfashi ya ce. "Babu lafiya Barrister, an sace Sadik." Aunty Sadiya ta yi jimm tana kallon Daddy sannan ta ce. "Sadik dai Ango wanda za'a d'aura musu aure da Neehal yau? Na ma kasa gane wane Sadik ɗin." Daddy yay mata bayanin abun da Abban Sadik ya sanar masa kamar yadda yay wa Mama bayani. Aunty Sadiya ta dafe kai tana ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un a fili. Kusan 5 minutes suna haka babu wanda ya kuma magana, Mama dai sai addu'a take a ranta Allah yasa mafarki take, ba gaske ba ne abun da yake faruwa yanzu. Wayar Daddy ce ta dau ƙara, suka kalle shi gaba-ɗaya cikin alamar tambaya. A sanyaye ya zaro wayar ya duba, sannan ya dube su ya ce. "Alhaji Suraj ne." A hanzarce Mama ta ce, "D'aga mu ji ko an gan shi ne." Daddy ya yi picked ya saka wayar a handsfree. Cikin damuwa ya ce. "Alhaji Suraj an gan shi ne?" Cikin muryar dake nuna tsantsar damuwa Abba ya ce. "Har yanzu dai babu wani labari ranka ya daɗe, duk inda muke tunanin zai iya zuwa an je baya nan, ga dukkan alamu fa sace Abubukar akai, dan ƙofar ɗakin da ya kwana a ciki a ɓalle muka tarar da ita." Daddy ya ce, "A ɓalle kuma? Kenan ɓalla ta akai aka shiga?" Abba ya ce. "Haka muke tunani, ga darduma nan a shimfid'e alamun abu na ƙarshe da ya yi sallah ce." Daddy ya ce. "Hasbunallahu'wani'imal'wakil, Alhaji gani nan zuwa gidan naka, wannan maganar bata waya ba ce, bari na kira a haɗa mun jami'an sojoji su zo mu san abun yi, Insha Allahu za'a gan shi." Mama ta durk'ushe a gurin da take tsaye numfashinta na fita da ƙyar. Ta rasa tunanin me ma zata yi, ƙwaƙwalwarta gaba-ɗaya ta toshe, ta ma daina fahimtar abun da Daddy yake faɗa. Aunty Sadiya ta yi wani murmushin takaici ta ce. "An canza salo kenan? saboda a ɗauke hankalin mutane." Cikin rashin fahimta Daddy ya ce. "Kamar Yaya?" Aunty Sadiya ta ce. "Lokaci da ikon Ubangiji na tonar asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari zai bayyana." Daddy ya ce. "Me kike nufi ne Barrister, dan Allah karki danganta ɓatan Sadik da mutuwar su Anwar." Aunty Sadiya ta ce. "Ban danganta ba, amma ina zargin haka." Daddy ya miƙe yana gyara hular kansa ya ce. "Bari na je na dawo sai mu yi magana, yanzu hankalina ba ya jikina." Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin. Dan shi damuwar Daddy ɗaya kar a ce an fasa d'aurin Auren nan a yau. Aunty Sadiya ta ƙarasa inda Mama take ta riƙo ta, Mama tana duban ta, ta ce. "Sadiya an sace Sadik kamar yadda aka kashe Jameel da Anwar, kenan hakan yana nufin akwai wani da yake bibiyar rayuwar Neehal da wata mummunar manufar? Me tay masa haka da ya zaɓi cutar da ita da mu da iyayen yaran da yake kashewa? Akan me ba'a son aga ta yi Aure kamar kowacce mace?" Aunty Sadiya ta ce. "Yaya Fateemah yanzu duk ba wannan ne a gaban mu ba, addu'a kawai zamu yi Allah ya bayyana mana Sadik a duk inda yake. Kila ma abun da muke tunani ba haka ba ne, wani gurin Sadik ɗin ya je. Ko kuma idan ma sacen shi aka yi hakan ba shi da alaƙa da Neehal." Mama ta sauke wani gwauron numfashi mai tattare da tsantsar damuwa ta ce. "Ya Allah ka bayyana mana yaron nan, ya Allah ka kare shi a duk inda yake, Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan al'amari." Aunty Sadiya ta ce. "Ameen ya Allah."










A gidansu Sadik kuwa, tun bayan da k'aninsa Bashir ya je tashin sa da asuba dan su tafi masallaci kamar yadda suka saba kullum, duk wanda ya riga ɗan'uwansa tashi shi zai je ya tashe sa. Tun daga ganin ƙofar ɗakin a ɓalle a ƙasa ya san da matsala, cikin mamaki ya shiga ɗakin yana k'wala masa kira da tambayar sa dalilin ɓalle ƙofar. Jin shiru kusan mintuna biyar yasa ya lek'a toilet inda yake tunanin Sadik ɗin yana ciki, amma sai ya ga wayam babu kowa. Ya fito ya dinga dudduba ɗakin har bayan labule amma babu shi babu alamar sa. Ya fito hankali a tashe ya duba bayan ɗakunan, nan ma babu shi. Sai ya yi tunanin ko masallaci ya tafi ya bar shi, duk da wata zuciyar na faɗa masa ba haka ba ne, amma dai ya nufi masallacin. Yana ta dube_dube amma ko mai kama da Sadik bai gani ba har aka idar da Sallah. Bayan sun fito daga Masallacin sun gaisa da Abban su ya sanar masa. Ba tare da damuwar komai ba, Abban ya ce masa su duba ɗakinsa na part ɗin Maamah may be yana can, tunda dama a can suke kwana saboda baƙi ne yasa suka dawo BQ. Wasa_wasa dai Bashir da Abba sai da suka duba ko'ina na gidan amma ba su ga Sadik ba. Suka dinga kiran wayar shi amma bai ɗauka ba, sai da suka koma ɗakin da ya kwana suka gan ta. Tun daga nan Abba ya san da matsala, Bashir ya ɗauki wayar da yake ya san pin ɗin Sadik ya buɗe wayar, ya duba last wanda suka yi waya ya ga Neehal ce. Har zai kira ta amma ya hana shi, dan ya san Sadik ba zai je gurinta ba tun asuba. Abokanansa suka dinga kira ana tambaya ko suna tare amma kowa sai ya ce A'a. Duk inda Abba yake tunanin Sadik zai je sun kira baya nan. Hankalin su fa ya ƙara tashi, Bashir ya fara kuka. Abba ne ma mai dauriya, ya fita ya tambayi mai gadi ko ya ga alamar wasu sun shigo gidan ko kuma ya ga Sadik ya fita? Mai gadi ya ce, Gaskiya babu wanda ya shigo ko ya fita daga cikin gidan, dan shi ya buɗe gidan ma da kansa da asuba. Hankali a tashe Abba ya kira ƴan'uwansa maza ya sanar musu dan su san abun yi, amma ya roƙe su kar su sanar da kowa, Bashir ma ya gargad'e shi kar ya sake ya sanar da Maamah, Insha Allahu za'a ga Sadik ɗin. Babu jimawa Ƴan'uwan Abba suka zo cikin tashin hankali, kowa na tambayar ina yaron nan ya tafi shi kuwa da sassafe ranar Auransa? Duk wani gidan abokan Sadik da Abba da Bashir suka sani sai da suka je neman sa, duk da sun kira su a waya sun ce basa tare, amma Abba sai yake ganin kamar ɓoye masa suke, Sadik ɗin yana tare da su. Har gurin telan dake masa ɗinki suka je, akan ko nan ya je can karɓar ɗinki, amma telan ya ce bai zo ba, dan tun last week ya gama masa ɗinkunansa duka ya ba shi. Mata na gida suna can suna cigaba da harkar girke_girke da harkokin biki basu san mai yake faruwa ba. Sai Maamah ce ma da ta ga har kusan 11 bai shigo cikin gidan ba ta yi mamaki, amma ko kaɗan bata yi tunanin wani abu ba. Duk wani abu da zai tabbatarwa da su Abba sace Sadik akai ya bayyana, dan haka wani k'ani a gurin Abba ya ce ya kamata a kira iyayen Amaryar a sanar musu halin da ake ciki. Shine Abba ya kira Daddy ya sanar masa. Bashir yana kuka wiwi ya shiga cikin gidan ya sanar da su Maamah abun da yake faruwa, faɗar irin rud'ewa da tashin hankali da Maamah ta shiga ba zai misaltu ba, ƙarshe ma sumewa ta yi saboda tsabar firgici. Cikin lokaci k'ank'ani zancen ɓatan Sadik ya baza gidan, nan fa aka fara koke_koke gidan biki ya koma kamar na zaman makoki. Umma ta dinga faɗin dama ta san haka zata faru, shi yasa ta ce kar a yi bikin nan amma Sadik ya dage, gashi nan ai. Hajiya kuwa iska ta tayar tana faɗin sai ta je gidansu Neehal sun fito mata da jika, kurwar jikanta ta fi ƙarfin su in ma su mayu ne. Da ƙyar aka riƙe ta dan sai fizge_fizge take tana ƙoƙarin k'wacewa ta fita. Ana cikin haka Su Abby (Mahaifin Maamah) suka ƙaraso gidan, sun taho da shirin d'aurin Aure suka tarar da wannan abun tashin hankalin. Daddy da shi da Yayansa da Kawu Musa da Uncle Usman da Uncle Mahmud suka je gidansu Sadik hankali a tashe. Har ƙarfe ɗaya ta wuce lokacin masallaci ya yi babu labarin Sadik, tuni Daddy Ya yi report ga Police da duk wani gurin da ya dace. Tashin hankalin da ahalin Sadik suke ciki a wannan rana ba zai misaltu ba.














Kamar yadda ahalin Sadik suke cikin tashin hankali haka su Mama suke ciki, sai dai su har wannan lokacin ba su bayyana labarin ɓatan Sadik a gidan ba. Daga ita sai Aunty A'isha, da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud sai Umma matar wan Daddy ne kaɗai suka sani, dan ko Hajiya ba su sanarwa ba, ita Mama Babban tashin hankalinta bata san ya Neehal zata yi ba in ta ji labarin ɓatan Sadik. Mama ta kira Daddy yafi sau 20 tana tambayar sa ko an ga Sadik, amma amsar ɗaya ce yake bata A'a. Sauran ƴan biki kuwa suna ta harkokin su, duk da ana ta neman Mama da tambayar ta dan tana part ɗin Daddy bata fito ba, saboda ana kallon ta za'a gane tana cikin tashin hankali. Mommyn Haneefah data fuskanci da akwai wata matsalar ita take replacing ɗinta, tana faɗawa masu tambayar ta cewa suna ɗan tattaunawa ne da ƴan'uwanta, yanzu zata fito.








Duk da halin tashin hankali da ake ciki amma haka su Daddy da su Abba suka tafi masallacin Juma'a, masallacin da aka saka za'a yi d'aurin Auren a can. Ai kuwa masallacin ya cika ɗank'am da jama'a, mutanen Daddy da ƴan'uwa dana Abba kowa ya hallara ana jiran a ɗaura Aure bayan an idar da Sallah. Daddy ya dubi Abba ya ce. "Amma Alhaji ina fata dai ɓatan Sadik ba zai saka a fasa wannan d'aurin Auren ba? duba yanda muka tara wannan dubban jama'ar." Abba ya nuna Kawu dake gefen sa ya ce. "Ga waliyyin shi nan ku yi magana da shi, ni bani da ta cewa akan wannan maganar." Daddy ya ja Kawu da Kawu Musa wanda shine waliyyin Neehal ya faɗa musu abun da ya cewa Abba. Kawu da dama jiran k'iris yake tunda ba k'aunar Auren yake ba, ya shiga masifa yana faɗin. "Tunda dama ba ɗansu ba ne ya ɓata ai dole ya faɗi haka, to wallahi ko Allah ya bayyana Sadik a yanzu baza a yi Auren nan ba, su sun fasa, wannan tashin hankalin ma kaɗai ya ishe su, a yanzu ma an sace shi in aka ɗaura Auran kuma ai sai kisa kamar yadda aka yiwa na baya, tunda ƴar tasu ta zama annoba, duk wanda zata aura sai an kashe shi." Duk da ran Daddy ya ɓaci amma ya dinga ba shi haquri akan ya amince a ɗaura Auran, Insha Allahu Sadik ɗin zai bayyana a yau cikin k'oshin lafiya har su tare da matarsa. Duba da yadda jama'a suka taro dan halartar d'aurin Auren, yanzu kuma kawai sai a ce musu an fasa." Kawu ya ce, ai kamawa ta yi dan haka batun wani d'aurin Aure ma a bar shi bai taso ba, su yanzu ta ɓatan ɗansu suke bata wani d'aurin Aure ba. Kawu Musa ya lallmi Daddy ganin yanda ya damu, ya ce masa ya bari a idar da Sallah sai su san abun yi, Insha Allahu baza a tara wannan Jama'ar a banza ba.










A dai-dai wannan lokacin aka gama yiwa Neehal make up ɗin, ta shirya cikin wani rantsatstsen farin less, an yi masa ado da golden colour, an ɗaura mata head golden, ta ci ɗan'kunne da sark'a da awarwaro na gold sai walwali suke. An yafa mata wani farin mayafi mai kamar net, sai tashin k'amshi dake. Hajiya tunda aka fara kwalliyar take ɗakin tana ta zuba santin kwalliyar. Kowa na ɗakin sai faɗin. "Masha Allah, amarya kin yi kyau, anya kuwa wannan angon naki zai gane ki in ya gan ki." Neehal dai murmushin yaƙe kawai take, amma ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki. Gashi haka kawai ta ji ta fara damuwa da rashin kiran ta da Sadik bai yi ba, shi da kullum tun safe yake kiran ta, wataran ma shi yake tashin ta daga barci. Amma yau ranar farincikinsu a ce har yanzu bai kira ta ba, yanda yake ta zumud'in nan ta yi tunanin ba ƙaramin addabarta zai yi da kira ba, amma sai ta ga saɓanin haka.










Hafsah ce ta shigo ɗakin yanayin ta kamar tana cikin damuwa. Hajiya ta dube ta ta ce. "Ke wai ina mijin naki ne? ban gan shi ya zo yau ba." Cikin damuwa alamar an sosa mata inda yake mata k'aik'ayi ta ce. "Wallahi Hajiya ban sani ba, rabo na da shi tun jiya da yamma, dama ya ce mun dak'yar in zai je gurin dinner. To kuma yau tun safe nake kiran wayoyinsa duka a kashe." Hajiya ta ce. "Subhallahi, an shiga uku, kar dai baƙin halin Aminu har ya kai ya ƙi zuwa d'aurin Auren Yar'uwarsa guda ɗaya jal a duniya." Neehal tay karaf ta ce. "Ni Yayana ba shi da baƙin hali." Ta yi maganar cikin turo baki. Hajiya ta tab'e baki ta ce. "Toh mai Yaya, zamu gani ai in zai zo, halin Aminun ne ban sani ba, kaɗan daga cikin aikinsa ne ya ƙi zuwa." Hafsah dai bata kuma cewa komai ba. Neehal ta tsugunna ana musu hotu ita da twins ɗinta. Salma Ƴar ƙawar Mama wadda suka je gidansu Sadik tare tana gefen ta a bakin gado tana latsa waya, kallon status take. Da yake sun yi exchanging number ita da batul da suka je gidan sai ta ga ta yi story just now. Ta shiga da sauri dan ganin pics ɗin Namiji ne, a tunaninta kwalliyar Sadik ta ɗora ta angonci. Rubutun da ta gani akan hoton yasa ta waro Ido, ta kalli hoton tare da maimaita karanta rubutun kan hoton ya fi sau biyar. Da sauri ta taso ta miƙawa Neehal wayar tana faɗin. "Neehal! Duba mun hoton nan ba Sadik ɗinki ba ne?" Neehal ta karɓa cikin tashin hankali, hannunta har rawa yake tun kafin ta ga mene a hoton Sadik ɗin. Kowa na ɗakin ya zuba mata ido. Hajiya ta ce. "Me kuma ya samu Sadik ɗin?" Neehal ta zauna dab'as daga tsugunnen da take idanunwanta duka sun yo waje. A fili ta maimaita rubutun da ta karanta a jikin hoton Sadik. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Be safe Big brother, Allah ya bayyana mana kai ya kare ka a duk inda kake. Yan'uwa musulmai muna barar addu'arku, yau mun tashi cikin tashin hankalin ɓatan Yayanmu Barrister Abubakar Sadik, wanda wasu alamomi suka tabbatar sace shi aka zo akay har cikin gida. Dan Allah a taya mu da addu'ar Allah ya bayyana mana s....." Ta yarda wayar ba tare data ƙarasa karanta rubutun ba ta hau girgiza kanta kamar dolowa tana faɗin. "No, no ba Sadik ɗina take managa akai ba, wani mai kama da shi ne. Sadik ba zai taɓa ɓata ranar Auren mu ba." Sai ta fashe da kuka tare da miƙewa zumbur numfashinta na wani irin fuzga. Da sauri aka yo kanta aka riƙe ta, Haneefah ta zo ta ɗauki wayar ta duba ta ƙara karanta abun da Neehal ta karanta a fili cikin tashin hankali. Hakan ba ƙaramin ƙarawa Neehal tashin hankali da razani ya yi ba tare, lokaci ɗaya ta ji kamar an janye iskar da take shaƙar numfashi da ita, idanunta suka daina ganin komai sai duhu, kawai gani aka yi ta tafi luuu ta faɗi a gurin sumammiya. Yan ɗakin gaba-ɗaya suka yo kanta suna kiran sunanta, twins suka fashe da kuka. Hajiya wadda ita kaɗai ce bata motsa ba sai bin su da ido kawai take cikin tsananin shock, ta miƙe tsaye tare da rafka salati cikin d'imuwa.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣3️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















...........Mama ta ja baya da sauri tana kallon sa kamar yadda shi ma ya tsaya yana kallon ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Mama ta sauke ajiyar zuciya gaba-d'aya kwandon bala'in data tanada domin sauke masa idan ya dawo ta nemi shi ta rasa saboda yanayin tsantsar damuwar data gan shi a ciki. Cikin sanyin murya ya ce. "Mum.!" Mama ta haɗe rai ta ce, "Malam bani hanya in wuce, ka zo ka wani tsaya mun a kai." Ya sauke numfashi mai huci ya ce. "Please Mum I want to talk to you." Mama ta harare shi ta ce. "Bani da wannan lokacin, bani da lokacin magana da kai Ameen, So ka bani hanya in wuce ana jira na, and i have important something to do now." Ya kama hannunta tare da marairaicewa ya ce. "Please Mum, na san ni mai lefi ne a gurin ki, amma just 5 minutes ki tsaya ki saurare ni." Mama ta kalle shi tana sauke ajiyar zuciya, ko ba komai ta ji daɗi data gan shi cikin k'oshin lafiya. Ta zare hannunta daga nashi ta juya ta koma cikin falon, ya yi ɗan murmushi tare da bin baya ta sannan ya ce. "Thank you." Bayan sun zauna Mama ta fara magana cikin sanyin murya mai nuni da damuwa. "Yanzu Ameen abun da ka yi ka kyauta mana kenan? More especially ma ni da ka san zan damu over, muna cikin wannan halin tashin hankalin amma a nemeka a rasa, sannan ka kashe wayoyinka, bayan ka kunna kuma in an kira ka sai ka ƙi d'agawa." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce. "I'm sorry Mum."Mama ta ce. "I don't want your stupid sorry, ka riƙe haqurin ka, abun da nake so kawai just tell me what happened to you? Ina ka shiga through out today? And me yasa kuma ka kashe wayoyinka?" Ya kalli fuskarta ya ce. "Nothing Mum, kuma babu abun da ya faru da ni." A fusace Mama ta ce. "You are lier Ameen, like every time if I asked you to tell me what is wrong with you. Amma yanzu ma i will not force you to tell me kamar kodayaushe, zan barka tunda haka kake so, just i will pray

Please Login or Register in order to submit comment