Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan tana bin ta a baya. Kamar ɗazu addu'a ta shiga yi a ranta har suka ƙarasa. Haneefah ta yi murna sosai da ganin sabuwar Motar Neehal, kamar ita yi Motar. Bayan ta gama tsallen murna suna zaune a kan gadonta su Afrah kuma suna falo gurin Momy, Neehal ta cewa Haneefah "Me kika ce zaki faɗa mun idan na zo?" Haneefah ta ce "Hmm, jiya Abban Abuja ya zo (wan mahaifinta kenan) ya cewa Mommy Iyayen ya Faruq sun je sun tsaida ranar bikinmu nan da three months masu zuwa." Neehal ta waro ido tana murmushi ta ce "Dagaske kike Haneefah?" Haneefah ta ce "Zan miki ƙarya ne to." Neehal tana dariya ta ce "Ban iya guɗa ba dana rangad'a ta yau, Ya Faruq ya ga ji da iskancinki kenan na ja masa rai da kike, amma na ji daɗi sosai ƙawata, Allah ya kai mu lokacin ya sanya Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin, ni kuma ban ji daɗi ba, na so an fara bikinki kafin nawa na rak'ashe son raina." Neehal ta mata gwalo ta ce "Sai kuma Allah ya yi ni zan rak'ashe ɗin a bikinki." Haneefah ta ce "Ba komai, idan bikin naki ya zo nima aje auran zan yi a gefe in sha sha'ani na." Neehal ta ce "Allah ya sa lokacin kina da tsohon ciki ma, sai mu ga ta tsiya." Haneefah ta jefe ta da filo tana faɗin "Ba Amin ba muguwa ƴar buk'ulu." Sai bayan Magriba suka koma gida, a koma wa gida dai Neehal bata ga Motar nan tana binta ba, in ma tana binta ɗin ita dai bata gan ta ba, ko dan duhu ya fara ne oho. Washegari Friday bayan Neehal ta dawo daga school da yamma Mama ta ce ta shirya su je ita da su Afrah ta yi musu shopping ɗin kayan sawa da duk wani abun buƙata. Suka shirya suka tafi, kaya sosai Neehal ta jidar wa su Afrah, sannan suka biya suka sha Ice cream sannan suka dawo gida. Yau dai ba ta ga Motar nan ta bi ta ba kwata_kwata, ko da safe da zata school. Hakan yasa ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ba kamar jiya ba da ta kwana cikin zullumi da fargaba.







Bayan Sallar Magriba Neehal tana sama tana yin wani Assignment Amrah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama, Neehal ta amsa mata ba tare da ta ɗago ba. Amrah ta ce "Aunty Mama ta ce ki zo Uncle Sadik ya zo." 'Sadik kuma?' ta tambayi kanta gabanta na fad'uwa ba tare da ta san dalili ba. A hankali ta dubi yarinyar ta ce "Ki ce ina zuwa." Amrah ta juya ta fice daga ɗakin da gudunta. Neehal ta tattara takardun gabanta ta ajiye akan bedside locker sannan ta ɗauko mayafi ta yafa ta fito falo. Mama tana zaune tare da su Afrah suna kallo a Falon. Neehal ta dube ta, ta ce "Mama wai Ya Sadik ne ya zo?" Mama ta ce "Eh, yana ƙasa yana jiran ki." Bata kuma cewa komai ba ta nufi ƙasa. Yana zaune a kan kujera as always idan ta sakko gurinsa yana ta latsa waya, k'amshinsa ne ya ziyarci hancinta, ta lumshe ido tana jin wani irin yanayi na bin jikinta tare da canzawar bugun zuciyarta. Sosai Sadik ya mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananun kaya, sumar kansa baƙi sidik sai k'yalli take. Cikin sanyin jikin data rasa na mene ta ƙarasa ta zauna a kujerar kusa da shi tare yin ƙasa da idonta tana sauke numfashi a hankali. Murya ƙasa_ƙasa ta yi masa sallama. Ya d'ago kansa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da mayar da wayarsa cikin aljihu. Kamar bata son magana ta ce "Ina yini." Idanunsa na kanta Ya ce "Lafiya k'alau, ya study?" Ta ce "Alhamdulillah, ya su Maamah?" Ya ce "Suna lafiya, ta ce na gaishe ki ma." Still kanta na ƙasa ta ƙi d'agowa ta ce "Ina amsawa, ya aiki?" Ya ce "Aiki gashi nan muna ta fama Alhamdulillah." Ta yi shiru ba ta ce komai ba, shi ma shirun ya yi yana jiran ya ji ko zata tambaye shi dalilin yasa kwana 2 bai kira ta ba kuma bai zo ba. Tsawon three minutes suna haka, katse shirun na su ya yi da faɗin "Neehal !Kamar wani abu na damunki ko?" Lumshe idonta ta yi tana jin yanda sunanta ya ƙara daɗi a cikin muryarsa, sai ta ji kamar ta ce ya ƙara maimaitawa. Girgiza masa kai ta yi alamun a'a. Ita kanta ba zata ce ga abun da yake damunta ba, amma tabbas daga lokacin da Amrah ta zo ta faɗa mata Sadik ya zo ta ji sauyi a zuciyarta wanda bata san ko na mene ba. Sadik ya yi ƙoƙarin jan ta da hira amma ta ƙi sakin jikinta, ko d'ago kanta ta kasa yi, amma sai ta tsinci kanta da son jin muryarsa a wannan lokacin, ta ji bata son ya yi shiru da magana ko na second ɗaya ne. Shi kuwa Sadik jikinsa ne gaba-d'aya ya yi sanyi, dan yau da shirinsa ya taho na bayyana wa Neehal abun da ke zuciyarsa game da ita, amma kuma yanayin da ya ganta a ciki ya kashe masa gwiwa. Suna haka kamar a mafarki Neehal ta ji k'amshin Ameen, da sauri ta d'ago kanta ta kalli ƙofa. Shine kuwa yake ƙoƙarin shigowa falon, samun kanta ta yi da ƙura masa ido fuskarta ɗauke da murmushin da bata shirya masa ba, rabon data gan shi tun ranar da ta je gidansa, sati ɗaya kenan yau, sai ta ga ya ƙara mata kyau da haske ya yi wani fresh abunsa, alamun angoncin ya karɓe shi. Ameen ya ƙaraso inda suke fuskarsa ba yabo ba fallasa ya yiwa Sadik sallama tare da miƙa masa hannu. Cikin fara'a Sadik ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha sannan ya gaishe shi. Ko kallon inda Neehal take bai yi ba ya nufi sama, Neehal data kasa ɗauke idonta daga kansa cikin sanyin murya ta ce "Yaya ina wuni." Ba tare da ya juyo ba ya ce "Fine." Tare da wucewa sama abinsa ya bar musu daddad'an k'amshinsa a falon...........✍️












_*Yanzu labarin zai fara sauya salo, sannu_sannu bata hana zuwa.......*_












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:51] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*3️⃣6️⃣*












............Runtse idanunta ta yi tana jin ba daɗi akan abun da Ameen yake mata, ta rasa wanne irin mutum ne shi da ba'a gane gabansa balle bayansa, tamkar mai aljanu wata rana faran_faran, wataran kuma akasin haka. Buɗe idonta ta yi tare da daidaita nutsuwarta jin muryar Sadik yana mata magana.




Da Sallama Ameen ya shiga falon sama, Mama ta d'ago tana dubansa tare da amsa masa. Su Afrah suka tashi da sauri suka nufe shi suna faɗin "Oyoyo Uncle." Ameen ya kama hannuwansu yana murmushinsa mai k'ayatarwa. Shafa kansu ya yi ya ce "How are you?" Amrah ta ce "We are fine Uncle." Ya shafa fuskarta ba tare da ya kuma cewa komai ba sannan suka ƙarasa ya zauna a gefen Mama. Cikin kulawa Mama ta ce "Welcome." Ya gyaɗa mata kai tare da faɗin "Ina yini Mum." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ya Hafsah?" Ya ce "Tana nan k'alau." Mama ta ce "Komai dai lafiya babu wata matsalar ko?" Ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa sannan ya ce "Babu matsalar komai, Dad ba ya nan ne?" Mama ta ce "Bai dawo ba, ka san sai ya yi isha'i yake shigowa." Ameen ya jinjina kai tare da mai da kallonsa ga Twins wanda suka ba da hankalinsu a kan kallon cartoon ɗin da suke. Mama ta ce "Bari na zubo maka abinci." Ya ce "No, am full." Mama ba ta kuma cewa komai ba ta cigaba da latsa counter ɗin dake jikin finger d'inta bakinta na ɗan motsi alamun lazimi take. Ameen ya dawo da dubansa gare ta ya ce "Who is that boy?" Mama ta ce "Wanne yaron kenan?" Ya ɗan yi shiru na sakanni sannan ya ce "Wanda na gan shi a downstairs yanzu." Mama ta ce "Sadik ɗin ne baka sani ba ko ya?" Ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ma kawar da zancen da ya yi da faɗin "Ya wajen su Hajiya, da Uncle?" Mama ta ce "Sunan nan k'alau, Next week ma Insha Allahu zani Gomben." Ameen ya ce "Allah ya kai mu, nima Sunday Insha Allah zan tafi Lagos." Mama ta ce "Da Hafsah zaka tafi amma?" Ya ce "No." Tare da ɗan girgiza kansa. Mama ta ce "Kamar ya No? Zaka bar ƴar mutane ita kaɗai k'wal ne a gida? Ai ba zai yiyu ba." Ya ce "Za'a zo a taya ta kwana daga gidansu." Mama ta ce "Alright, Allah ya kai mu." Ameen ya ce "Amin, but in kin je Gomben tare zaku dawo da Hajiya ko?" Mama ta ce "Da ƙyar gaskiya, dan ta ce ita da Kano sai bikin Neehal kuma." Ya ɗan kalli Maman kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mai da dubansa ga agogon hannunsa ya ce "Mum ni zan koma, ki gaishe da Dad." Mama ta ce "Zai ji, Allah ya kiyaye hanya, ka gai da Hafsan." Ya amsa mata yana miƙewa sannan ya fice. Mama ta bishi da kallo a ranta tana cewa 'He will never change daga shegen muskilancinsa, ta yi zaton idan ya yi aure abun zai ragu, amma kamar ma ƙaruwa ya yi. Da ya sakko zai wuce Sadik kawai ya kula, shi ma dan ya masa sai da safe ne. Ganin lokacin Sallah ya yi Shi ma Sadik ya yi wa Neehal sallama ya tafi, bayan ya sanar mata zai turo mata da saƙo ta waya anjima, ba ta yi tunanin komai ba ta ce sai ya turo tana jiran shi. Lokacin data koma sama Mama bata falo, sai su Afrah da bacci ya kwashe su, dama lokacin baccin nasu yayi, dan da wuri suke bacci, amma asubar fari sun tashi. Neehal ta shiga ɗakin Mama tana turo baki gaba, Mama dake shimfid'a Darduma ta dube ta amma ba ta ce komai ba. Neehal ta zauna a bakin gado kamar zata yi kuka ta ce "Mama yau Yaya bai kula ni ba, ban sani ba ko wani laifin na masa." Mama ta ce "To nice shi da zaki zo kina cuno mun baki, ko kuma halin Ameen ɗin ne baki sani ba?" Neehal ta ƙara bata fuska ba ta ce komai ba. Mama ta ce "Tashi ki je ki yi Sallah ki ci abinci, in kin gama ki zo i want took to you." Neehal ta ce "Toh." Tare da tashi da fita. Bayan ta idar da Sallah ta ci abinci ta kai su Afrah ɗaki sannan ta koma ɗakin Mama. Ganin yanda Mama ta yi serious alamun magana za su yi mai mahimmanci sai ta bata duka hankalinta. Mama ɗan numfasa ta ce "Neehal! Zan tambaye ki wani abu, kuma ina son ki faɗa mun gaskiya." Ta ɗan ji gabanta ya faɗi, amma ta daure ta ce "Insha Allah Mama zan faɗa miki gaskiya in dai na sani." Mama ta ce "Wanne matsayi Sadik yake a gurinki?" Neehal ta dubi Mama da sauri cikin mamakin tambayartata sannan ta ce "Like Brother or Friend." Kamar Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa. Neehal ta ce "Wani abu ya faru ne?" Mama ta ce "Babu komai." Neehal ta ce "Daddy bai dawo ba ne?" Mama ta ce "Ya dawo yanzun nan." Neehal ta yi murmushi ta ce "Bari na je part ɗinsa mu yi hira." Ta miƙe ta fita, Mama ta bita da kallo cikin tausayinta. Ba dan ta mata maganar Sadik ta kira ta ba, ta kira ta ne ta mata wata tambayar daban akan abun da yake damun a zuciyarta a kwanakin nan, amma kuma da ta yi wani tunani a yanzu sai ta fasa.








Sai wajen ƙarfe goma Neehal ta dawo part ɗin Mama daga gurin Daddy. Toilet ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito ta zira doguwar rigar bacci, ta kashe light ɗin ɗakin ta kunna bedside lamp sannan ta kwanta a kusa da twins. Wayoyinta ta ɗauko domin shiga yanar gizo. Message ta gani akan wayarta da Numbern Sadik, ta ma manta ita ya ce zai turo mata sak'o. Ta text ɗin kai tsaye ta fara karantawa kamar haka: _*Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake ma'abociyar kyawu da nutsuwa gami da hankali. Neehal! Na daɗe ina tunanin ta yanda zan Bayyana miki abun da yake raina game da ke, amma fargabar abun da zai biyo baya yasa na kasa bayyana miki tun tuntuni, na cigaba da dakon sa a cikin zuciyata. Neehal! Ina son ki! Tun kafin na sanki a zahiri mu fara mu'amala k'aunarki ta cika duk wani gurbi na zuciyata sai dai.......*_ Ai ba ta ƙarasa karanta message ɗin ba ta tashi zaune da sauri zuciyarta na wani irin dokawa da sauri da sauri. Ajiye wayar ta yi a gefenta ta runtse idanunta hannunta dafe a ƙirjinta, a ranta tana addu'ar Allah yasa mafarki take ba gaske ba ne Sadik ya mata text ya sanar mata wai yana sonta. Vibration ɗin da wayarta ta fara yi ne yasa ta buɗe idanunta da sauri ta ɗauki wayar ta duba, sunan Sadik taga yana yawo akan screen ɗin wayar. Kallon wayar take tare da girgiza kanta, a fili ta fara faɗin "No, no Sadik soyayyata da kai ba zata taɓa yi yu ba, dan ban shirya shiga wani tashin hankalin ba a rayuwata bayan wanda yake manne a cikin zuciyata, ban shirya ƙara rasa masoyi a karo na uku ba, ka yi haquri Sadik dan babu batun ƙara soyayya a rayuwar Neehal har abada." Tana gama faɗar haka ta kashe wayar gaba-d'aya ganin kiran ya katse wani ya ƙara shigowa. Komawa ta yi ta kwanta tana jin haushin kanta da har ta bari suka saba da Sadik sosai haka. Tabbas biri ya yi kama da mutum, ya kamata a ce tun kafin yanzu ta gane Sadik sonta yake, idan ta yi la'akari da yanda alaƙarsu ta fara, lokacin da farko da Haneefah suke mutunci ba ita ba. Amma tunda ya samu ta fara sake masa sai kuma suke shiri fiye da wanda suka yi da shi da Haneefan ma. Me yasa tun ranar da suka fara haɗa ido da shi ta ji sauyi a cikin zuciyarta, ko kuma hakan yana nufin shine wanda zai shigo cikin rayuwarta a karo na uku a matsayin wanda zai zamo abokin rayuwarta. Tabbas idan cancanta zata duba Sadik ya cancanta ya zamo abokin rayuwarta, domin yana da duk wasu qualities ɗin da take so mijin da zata aura ya kasance yana da shi. Sai dai bata tunanin *ƙaddarar* data raba ta da Jamil da Anwar zata bar mata Sadik. Bata son ta jefa rayuwarta data iyayenta a cikin wani tashin hankalin, shi yasa duk wata ƙofa da wani zai nuna yana sonta ta rufe ta a rayuwarta, da zarar ta ga take_taken mutum zata taka masa burki. Ita yanzu burinta a rayuwa taga ta yi karatu mai zurfi, domin ta san shikaɗai ne zai zama gatanta a nan gaba. Wasu zafafan hawaye suka ziraro daga idanunta.Ta lumshe ido tana jin hawayen na diga akan filon da tay matashi da shi. Fuskar Sadik, murmushinsa, tafiyarsa, su kawai idanunta suke hango mata, ga muryarsa dake mata kuwwa a cikin kunnenta. Wata irin fad'uwar gaba ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa. Tana ƙoƙarin cire Sadik daga rayuwarta amma zuciyarta tana hasaso mata komai nasa, kenan hakan yana nufin ta kamu da sonsa ne ita ma ko kuma dama can tana son shine ne? Ta tambayi kanta, a fili ta ce "Impossible!" Cikin muryar kuka. Ta san soyayya, tunda ta yi ta kar karo biyu, ta san daɗinta kamar yadda ta san ɗacinta. A rayuwarta tana son soyayya tana son ta ga masoya, a kullum addu'arta Allah ya bata mijin da ya iya soyayya, amma zuwa yanzu ta yiwa kanta alƙawarin koda zata yi aure ta ajiye babin soyayya a rayuwarta. Saboda ita bata iya so ba, idan tana son mutum tana son shi ne da dukkan zuciyarta, irin zufaffaffen son nan take yiwa mutum mai game jiki da zuciyar ɗan'Adam. Haka tay ta tunane_tunane da sak'e_sak'e a wannan daren, bacci kam yau duk iya satarsa ya kasa sure Neehal.






Washegari bayan ta yi Sallar Asuba ta ɗauko Alqur'ani ta shiga karantawa kamar kowacce Asubahi. Kafin ta gama karatun su Afrah sun tashi daga bacci, jikinta suka zo suka ɗane suna zuba mata surutu, ta ce su yi mata shiru ba su ga karatu take ba ne. Bayan ta gama ta musu wanka ta shirya su saboda yau Asabar Mama zata kai su Tahfiz. Ita ma wankan ta yi bayan ta gama shirya su dan ƙarfe tara zata fita gurin aiki. Ta kama hannunsu suka sauka ƙasa, a kitchen ta hango Mama tana haɗawa Daddy kayan karinsa. Su Afrah suka ƙarasa kitchen ɗin da gudu suna kiran sunan Mama. "Mama! Mama! kin ga Aunty ta saka mana sabon Hijabi, ta ce yau da mu zata fita." Mama tana dubansu da murmushi akan fuskarta ta ce "Kun yi kyau sosai ƴaƴan Aunty, ku je ga Aunty Dije can a falo ta zuba muku abinci ku yi breakfast, maza!" Da murnarsu suka juya suka fita, Neehal ta bi su da kallo sannan ta ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin jikinta a sanyaye. "Sannu da aiki Mama, ina kwana." Neehal ta faɗa tana duban Maman. Mama ta ce "Yawwa har kun fito kenan?" Neehal ta ce "Ehh, ina tunanin ma tafiya zan yi kar na yi late kya kai su Tahfiz ɗin kawai." Mama ta ce "Amma dai kya tsaya ki ci abinci ai." Neehal ta ce "A'a, yau na tashi da azumi ne, na manta ana bina wani guda ɗaya sai jiya na tuna ashe azumi bai fi saura 1 month ya rage ba, shi yasa na ga gwara in yi kar na manta kuma......" Kallon da Mama take bin ta da shi tunda ta fara magana ne yasa ta yin shiru ba tare da ta kai aya ba. Mama ta ce "Yaushe kika ko yi ƙarya Neehal ban sani ba?" Neehal ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba. Mama ta cigaba da Magana "Jiya kin tashi da kumburarrun ido alamun kin sha kuka kafin ki yi bacci, yau ma ga idanunki nan da alama ba ki yi bacci ba jiya, kuma still kin yi kuka, yanayinki da maganarki sun tabbatar mun da damuwar da na gani kwance akan fuskarki. Ba zan takura miki ki faɗa mun abun da yake damunki ba tunda ba ki yi niyyar faɗa mun ba tun farko, amma zan miki addu'a Allah ya yaye miki." Mama tana gama faɗar haka ta juya ta cigaba da abun da take fuskarta na nuna ɓacin ranta. Neehal ta matso kusa da ita ta rungume ta tare da sakin kuka, cikin kukan ta ce "Ki yi haquri dan Allah Mama kar ki yi fushi da ni." Mama ta sanyaya muryarta ta ce "Ba zan taɓa iya fushi dake ba Neehal, amma kin san ba zan juri ganin damuwarki ba ko?" Neehal ta gyaɗa mata kai. Mama ta ce "To share hawayen ki faɗa mun me yake damunki." Neehal ta share hawayen sannan ta ce "Babu komai Mama, kawai ki mun addu'a." Mama ta bita da kallo ba ta ce komai ba. Neehal ta kama hannunta ɗaya ta ce "Ki yarda Mamana seriously ba komai, idan ma da akwai ganinki da na yi yanzu ya shafe mun duk wata damuwata." Mama ta ce "Shikenan, amma dai always ina faɗa miki kuka ba maganin damuwa ba ne, addu'a ita ce magani, kin ji?" Neehal ta ce "Insha Allah zan daina kukan." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci to, sai ki je ki gaida Daddy." Neehal ta ce "Toh." Sannan ta juya ta fita, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta gami da k'aunarta. Neehal ta daure ta cuccusa bread da k'wai ta kora da ruwan tea, ba ɗan tana jin yunwa ba ko ɗan tana jin daɗin abincin a bakinta ba sai dan kar Mama ta mata faɗa. Bayan ta gama ta faki idon su Afrah ta shiga part ɗin Daddy, daga nan ta wuce gurin aiki. Sai dai wani ƙarin damuwar tana fita ta ga Motar data bi bayanta shekaran jiya tana bin ta yau ma still.








Tun daren jiya bata kunna wayarta ba saboda bata so ta kunna ta ga kiran Sadik ko text ɗinsa. Sukuku ta wuni yau, abokan aikinta kowa sai ya tambaye ta lafiya take kuwa? Ita kuma sai ta ce musu kanta ke ciwo, fatan samun sauqi su kai mata.Tare suka wuce gida yau da Haneefah, amma Haneefan bata jima ba ta wuce gidansu. Mama ta kai su Afrah Islamiyya kamar yadda ta ambata, islamiyyar weekend kawai ake yinta, 8_5. Babu nisa kuma daga gidan. Ɗaya daga cikin sojojin gidan Mama ta aika ya ɗauko su da time ɗin tashin su ya yi. Neehal tana kwance akan gado suka shigo, suka haye jikinta cikin murna suna ba ta labarin Islamiyyarsu, murmushin da bai kai zuci ba kawai take bin su da shi amma ta gaza ce musu ƙala, har suka haqura suka ƙyale ta suka koma gurin Mama suke ba ta labarin ita, tunda Auntin ta ƙi kula su. Da daddare tana gani Sadik yana ta kiran wayarta amma ta ƙi d'agawa, daga baya sai ga text ɗinsa, ta buɗe ta karanta amma ta ƙi yi masa reply.










Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal ta daina d'aga kiran Sadik kwata_kwata, shi kuma ba ya gajiya kullum sai ya kira ta ba a daɗi gami da yi mata daɗaɗan text, na kalaman soyayya addu'a da fatan Alkhairi. Duk text ɗin da ya turo sai ta karanta amma fa bata reply, kuma ba ta yi block ɗinsa ba, saboda babu block ɗin mutane a tsarin rayuwarta, in dai ba abun da bai dace ba mutum yake turo mata ba. Mama ta je Gombe ta yi kwana uku ta dawo, gidan Aunty A'isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, su Zulai da Dije kuma garinsu suka je. Da tana gidan Aunty A'isha sai ga Sadik ya zo, Allah ya so tana ɗaki ba falo ba. Ashe ya saba zuwa gidan yana gaishe da Aunty A'ishan ita ba ma ta sani ba. Da Aunty A'isha ta ce a kira ta, sai ta ƙi fitowa ta ce ace bacci take yi. Duk wannan abun da Neehal take dauriya kawai take yi a ƙoƙarinta na ganin ta cire Sadik daga cikin rayuwarta, sai dai zuciyarta ta ce sam bata san wannan batun ba, dan da tunanin sa take kwana take tashi. A kwanakin nan da ta yi babu Sadik ta tabbatar wa da kanta tana son Sadik, so ba na wasa ba ma kuwa, Amma ta yi alƙawari ko son nasa zai kashe ta ba zata taɓa bari su yi soyayya ba. Ameen kuwa tun ranar da ya zo ɗin nan bata ƙara sa shi a idanta ba, tunda ya koma aiki sai weekend yake gari, weekend ɗinma idan ya zo gidan ita tana gurin aiki, bare ma ta ji Mama ta ce sau ɗaya ya ƙara zuwa tun ranar. Sai dai ita Hafsah ta zo sau biyu ta wuni, bata nuna wa Neehal komai ba saboda ganin idon Mama, ita ma Neehal ɗin haka, sai dai ba sa shigewa juna sosai. Dan Munafurci Hafsah harda cewa Mama wai Neehal bata zuwa gidanta, kamar so take ta je ɗin, Mama ta ce bata da lokaci ne shi yasa ga aiki ga school. Kamar yadda Mama ta kai su Afrah Islamiyya ta kai su makarantar boko, wadda haɗe take da islamiyya itama, Monday to wednesday sai 5:pm ake tashin su, Thursday and Friday kuma 12: pm.










Yau Talata wanda ya kama azumi saura kwana shida ga mai rabon gani. Da yamma bayan Neehal ta dawo daga school tana ɗaki tana gugar Uniform ɗin su Afrah Haneefah ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Neehal ta d'ago tana

Please Login or Register in order to submit comment