Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tashi su ce mata ya wuce Abuja. Ba dan wayar da ake ta zabga masa ba a gurin aiki da babu abun da zai sa ya koma Abuja a yau, ko dan rashin lafiyar Neehal. Dan ma ciwon nata na lokaci ɗaya ne, ya san nan da anjima zata wartsake Insha Allah. Amma sosai tausayinta ya cika masa zuciya, na ganin tana cikin mata masu shan wahala a lokacin al'adar su.








Sai bayan Azhar ta farka, lokacin Mama ta kikkira wayarta bata ma sani ba. Ta tashi ta ɗauke bedsheet ɗin dake gaban gadon ta kay toilet, sannan ta dawo ta ɗauko wani ta shimfid'a. Ta ɗauki wayarta ta bi bayan kiran Mama, ringing uku ta d'aga da sallama. Neehal ta amsa mata tare da turo baki gaba kamar tana ganin ta, ta ce "Mama nay ta kiran ki baki ɗauka ba, kuma ban da lafiya na kusa mutuwa." Mama ta ce "Sorry dear, na shiga surgery ne, ciwon ciki ko? Ya jikin naki? Amma dai kin sha maganinki?" Ta ce "Ni ina kwance na kasa tashi, Aunty Zulai ta je ta duba ɗakin ki bata gani ba." Cikin damuwa Mama ta ce "Subhallahi, amma dai ciwon bai wahalar dake sosai ba?" Ta ce "Na wahala sosai, sai da Uncle Ahmad ya zo yay mun allura sannan ya lafa mun." Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki Doctor ashe ya zo? Allah ya biya shi." Ta ce "Amin." Mama ta ce ta je ta ɗauki magungunanta duka dake ɗakinta, ta dawo da su nata ɗakin. Daga yanzu a nan zata na barin su, saboda gaba kar irin haka ta kuma faruwa. Bayan sun gama maganar ta k'waso magungunan ta dawo da su ɗakinta. Duk second ɗaya zuciyarta na bugawa da tsoron punishment ɗin da Ameen ya ce zai mata. Ta sauka upstairs ta tarar da su Afrah baje akan carpet suna bacci, ga chocolate ɗin da Ahmad ya siya musu da suka fita barbaje a kusa da su. Dije ta fito daga kitchen tana duban ta, ta ce "Har kin tashi? Ya jikin naki?" Ta ce "Alhamdulillah, waɗannan bacci su kai kenan." Ta ce "Eh, da Babansu ya dawo da su zasu hau sama ya hana su, ya ce su zauna a nan kar su je su dame ki. Na kunna musu kallo, sun fara kuma bacci ya ɗauke su." Ta ce "Ya daɗe da dawowa?" Dije ta ce "Eh, ga magani ma ya kawo ya ce in kin tashi a baki shi ya wuce Abuja." Sai ta ji daɗin tafiyar tasa, dan idan suka ƙara haɗuwa a yau bata san da idon da zata kalle shi ba saboda kunya.








Sai la'asar Mama ta dawo gida, Neehal ta haye jikinta tay ta zuba mata shagwab'ar ita bata da lafiya, cikinta ciwo da ƙafarta da kanta. duk da ta ji sauqi sosai rigimarta ce kawai. Da Maman ta gaji da mitar ta_ta, sai ta ce bari ta ɗauko allura tay mata, zata ji sauqi. Sai ta bar jikin nata tana faɗin ta ita ta warke ai. Kafin Magriba ta ware abunta tana harkokin ta, sai ɗan abun da baza a rasa ba. Da yamma wasu daga cikin abokanan aikinta mata suka zo suka duba ta.












Bayan Magriba ta yi wanka ta shirya cikin wata brown abaya mai kyau, ta yi kyau amma fuskarta ta yi fayau saboda cutar ta da ta yi. Ta fesa sassanyan turarenta mai daɗin k'amshi. Su Afrah suka mak'ale mata dan a zaton su fita zata yi. Ta zauna tana latsa wayarta kafin Sadik ya ƙaraso. Amrah ta ce "Aunty Unguwa zamu?" Ta ce "A'a." Bayan abun da bai fi mintuna biyu ba Sadik ya kira ta ya sanar mata ya ƙaraso. Ta miƙe ta kama hannun yaran suka fita. A falon sama ta tarar da Mama tana operating system. Ta saki hannun yaran tare da faɗin "Mama ga ƴan tayin aiki na kawo miki." Mama ta d'ago ta dube ta, ta ce "Sadik ɗin ya zo ne?" Ta ce "Eh." Mama ta ce "Sai ki ɗauki drinks ki tafi masa da shi, tunda ke ki shiga kitchen ki yi masa ko da snaks ne ma baza ki iya ba saboda ganda, sai dai mutum yay ta zuwa yana tafiya haka." Ta turo baki ta ce "To Mama baki ga ban da lafiya ba." Mama ta ce "Haka ne, duk watannin da ya yi yana zuwa ma a cutar kike ai? Wuce ki tafi ni kar yay ta jiran ki." Ta ɓata fuska, Afrah ta ce "Aunty zan biki." Mama ta ce "Ku zauna a nan, zata je gurin Uncle Sadik ne." Suka koma suka zauna kusa da Mama ita kuma ta fice bayan ta ba su wayarta ta ce su yi game. Bayan ta ƙarasa inda suka saba zama, ta gaishe shi cikin mutuntawa ya amsa tare da tsokanarta kamar yadda ta saba har ta yi fushin wasa, shi kuma ya rarrashe ta. Sai da suka shirya sannan ya gyara zama yay mata tambayar dake damun sa a rai. "Neehal Please dan Allah karki ɗauki tambaya da wata manufa i want know something ne." Ba tare da tunanin komai ba, ta ce "Karka damu Ya Sadik, ka tambaye ni ko me kake so, ni kuma indai na sani Insha Allahu zan baka amsa." Ya sauke numfashi ya ce "Neehal kafin mu haɗu, na ga sanarwar rasuwar tsohon saurayinki wanda a lokacin ma an kusa bikinku, bayan mun haɗu da ku Haneefah ta ƙara tabbatar mun da hakan, lokacin dana nuna mata ina son ki. Already na riga na san wannan, amma kafin shi akwai wani saurayin naki da ya rasu ne?" Neehal ta ƙura masa ido cikin tsananin bugawar zuciya dan bata taɓa zaton tambayar da zai mata ba kenan. Hawaye masu d'umi suka fara zuba a kan kuncinta, cikin raunin murya mai haɗe da kuka ta ce. "Sadik! Har an kai maka wannan labarin? ko kuma in ce an kai muku kai da ƴan gidanku, har lokaci ya yi da za'a fara yawo da ni a gari ana duk wanda zai aure ni kashe shi ake, har lokacin ya yii?" Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi. Gaba-d'aya Sadik ya ruɗe cikin dana sanin tambayar tata ya shiga bata haquri da ban baki, amma ina kuka kawai take yi, dama ta san wannan ranar sai ta zo a rayuwarta, ranar da wani zai zo neman auranta a ce masa ya janye kar ya zama gawa. Da ƙyar Sadik ya rarrashe ta ta yi shiru, sai da ya yi kamar zai rungume ta sannan ta haqura. Cikin tsananin damuwa ya ce "Dan Allah Wifey ki yi haquri, wlh ba da niyyar ɓata miki rai na yi miki wannan tambayar ba, amma mu bar maganar kawai tunda har ta samun ke kuka haka." Ta ce "Na sani Sadik, na sani kuma ko kaɗan ban ga laifinka ba, tun kafin yau na shirya tarb'ar wannan ranar a rayuwata dan na san dole zata zo. Sadik! Kafin Anwar Jameel ya kawo kuɗin aurena, sai da bikinmu ya rage saura watanni aka kashe shi, aka harbe shi and shima Anwar haka." Sai ta kuma ta fashewa da kuka. Gaba-d'aya Sadik ya ruɗe ganin yanda take kukan da dukkan zuciyarta, kuka ne irin wanda an fama wa mutum wani gyambon ciwo a cikin zuciyarsa. At the first time a tarayyar su ya kama hannunta, tare da tsugunnawa a gabanta ya fara magana cikin rarrashi. "Dan Allah, Neehal ki yi shiru ki saurare ni." Ta yi iya yinta ta ga ta bar kukan da take, ya zaro handkerchief ɗinsa ya shiga share mata hawayen fuskarta zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta. Da yasan samarinta biyu ne kacal suka rasu Wlh ba zai tambaye ta ba, shi duk a tunaninsa sun kai irin biyar ɗin nan, amma saboda tsabar gulma irin ta mutane har an saka wa rayuwarta ido. Ba tare da ya saki hannunta ba ya ce "Neehal! Ina son ki fiye da yanda nake son kaina, komai rintsi komai wuya ba zan taɓa iya rabuwa dake ba, ki saka wannan a ranki." Ta kalle shi cikin wadataccen hasken dake wurin, cikin raunin murya ta ce "Bana son na rasa ka Sadik, bana son kaima a kashe mun kai." Ya ce "Allah ne mai rayawa da kashewa Neehal, kisa a ranki zamu yi aure kamar yanda kowanne masoya suke yin auransu, jikina yana bani zamu yi aure, mu rayu cikin farinciki da annashuwa, har ma da tuk'wucin kyawawan yara kamar ki da yardar Allah." Ta sauke ajiyar zuciya tare da zare hannunta daga cikin nasa, tana jin sanyi ya fara ratsa zuciyarta. Sadik ya cigaba da faɗa mata daɗaɗan kalamai masu kwantar da zuciya, gami da ƴar nasiha. Lokaci ɗaya ta ji ta samu nutsuwar zuciya, ta kuma tabbatar Sadik ya cancanci zama miji a gare ta, ko dan tarin Alkhairinsa da k'aunarsa a gare ta.








A part ɗin Mama kuwa, ba jimawa da fitar Neehal Mama ta miƙe ta shiga ɗakinta, a lokacin ne kuma kiran Ahmad ya shigo wayar Neehal dake hannun su Afrah. Suka dinga shafa wayar har Allah ya ba su sa'a su kay pick ba tare da sun sani ba. Amrah ta ƙara danna wayar a ƙoƙarin ta na ganin sun koma game ɗin da suke, ashe gurin speaker ta danna. Jin muryar Mahaifinsu yana sallama suka ruɗe da murna. "Daddy! Daddy! Daddy!" Kowacce na son ya yi magana da ita. Ya ce "Oh, sweethearts zaku kashewa Daddy kunne fa." Afrah ta ce "Daddy Aunty ta ce ka tafi ka bar mu." Ya ce "Ai zan dawo in ɗauke ku soon, ko baku san zama a gurin Aunty." Suka ce "Muna so." Ya ce "Yawwa yaran kirki, ina Aunty? Ko bacci take?" Amrah ta ce "Ta fita gurin Uncle Sadik." A kwance yake amma bai san sanda ya tashi zaune ba. A fili ya ce "What? who is he?" Ya yi maganar a gigice. Afrah ta ce "Daddy yana zuwa gida gurin Aunty, yana da kirki yana ba mu chocolates." Amrah ta karɓe zancen da faɗin "Shi ya kai mu gidan Aunty Haneefah da ana bikinta." Ahmad ya had'iye wani abu da ya tsaya masa a mak'oshi, da ƙyar ya iya cewa "Unguwa suka je?" Afrah ta ce "No, Mama ta ce suna waje a zaune." Ya cize lip ɗinsa da ƙarfi, tare da faɗin "Damm it." Yaran suka ce "Hello Daddy." Ya sauke numfashi ya ce "Bye Dear, I will call later." Ya kashe wayar ya cillar akan gado. Kansa ya dafe da hannunsa yana zancen zuci. Me yasa tun farko bai yi tunanin Neehal tana da wani saurayin ba? a age ɗinta dama dole a ce tana da samari ba ma saurayi ɗaya ba. Hankalin Ahmad fa in ya yi dubu ya tashi, ya maimaita sunan Sadik a cikin ransa ba a dadi, kamar mai neman wani abu a cikin sunan. Ji yake kamar ya yi tsintsuwa ya gan shi a Kano, ya ga wane Sadik ɗin nan da his future wife take kulawa. "Kenan tana son shi?" Ya faɗi haka a fili cikin tsananin damuwa. 'Tana son shi mana tunda har take kula shi.' Zuciyarsa ta ba shi amsa da haka. "Ya Allah!" Ya furta haka a fili wani irin kishi na nuk'urk'usar zuciyarsa.










Sai wajen 9 Sadik ya tafi, bayan ya gama wanke mata zuciyarta tass, ya kuma roƙe ta kar ta sanar da Mama abun da ya tambaye ta, bare itama hankalinta ya tashi. Tay masa alƙawarin ba zata faɗa mata ba. A bakin part ɗin Mama tana ƙoƙarin danna door beil, ta ji k'amshin Ameen ya cika mata hanci, ta juya bayanta da sauri suka yi 4 eyes da shi.........✍️














*NOTE: For just of you that are thinking Ameen zai yiwa Ahmad wani abu na rashin mutunci or something else, har da masu tunanin duka.🤔🤣 Let me tell you something, Namijin duniya baya hukunci da faɗa ko wani hargagi, da ido ma kaɗai ya isa ya hukunta mutum, ato, Mama bata haifi sakaran Namiji ba, Jarumi ta haifa mai dakakkiyar zuciya. Har na hango su oo suna washe baki na yabi gwaninsu, to ba Ameen na kare ba, dan Mama na yi.😎*














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣4️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












...........Gaba-ɗaya sai ta duburburce ta rasa ina zata saka ranta saboda tsoro da kunya. Ya ƙaraso ba tare da ya ce komai ba ya buɗe ƙofar da key ɗin part ɗin dake gurinsa ya shige. Ta turo baki tare da bin bayansa, a ranta tana faɗin. 'Ya bar gidan ma amma har yanzu yana tare da key ɗin part ɗinsu.' Ya tsaya bayan ya shiga falon yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya, Ya jikin?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Bai jira amsar ta ba ya nufi upstairs. Ta d'ago kanta tare da sauke ajiyar zuciya ta bi bayan shi zuwa saman. Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi bedroom ɗinta, a nan ta tarar da su Afrah kwance akan gado suna bacci. Ta ajiye mayafin jininta tare da kwanciya ta lumshe idonta ta faɗa duniyar tunani. Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga, bayan sun gaisa ta ce "Neehal ta ce mun ka zo da safe ina gurin aiki." Ya ce "Eh." Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Ta ji sauqi." Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi." Ya miƙe ya ce "Ameen, bari na je gurin Dad." Mama ta ce "Okay." Bayan fitar sa Mama ta ɗauki wayar Neehal data karɓa a hannun su Afrah ta nufi ɗakinta, dan dubawa ko ta dawo." Turo ƙofar ɗakin da Mama ta yi yasa ta buɗe ido, Mama ta ce "Har kin dawo kin kwanta kenan?" Ta ce "Ban jima da dawowa ba." Mama tana mata kallon tsaf ta ce "Are you Okay?" Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Kaina ke mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauqaqe sai ki tashi ki ci abinci ki sha magani." Ta ce "Toh." Tare da karɓar wayarta da Mama ke miƙo mata." Mama ta ce "Sai kiran ki ake, waye yake miki wannan kiran ne haka?" Tana latsa wayar ta ce "Uncle Ahmad ne, yaransa yake son magana da su." Mama ta ce "Sai ki kira shi ki sanar masa sun yi bacci." Ta gyaɗa mata kai, amma bata jin zata iya kiran nasa. Mama ta juya ta fita bayan ta ƙara jajjada mata ta fa tashi ta ci abinci ta sha magani. Ta fi awa bayan fitar Mama tana sak'awa da kuncewa sannan ta miƙe ta fito ta sauka ƙasa. Abinci ta ɗebo ta ci, sannan ta dawo ta sha magani. Har time ɗin bata kira Ahmad ba, shi ma bai ƙara kiran ta ba. Ta shiga toilet tay wanka ta fito ta shirya cikin kayan bacci masu taushi ta kwanta, text kawai ta yiwa Sadik ta yi addu'a ta tofa wa su Afrah sannan ta shafa a jikinta, ba jimawa bacci ya ɗauke ta.










Bayan kwana biyu ranar Juma'a da safe ta samu Mama a ɗakinta ta ce mata. "Mama Ya Sadik ya matsa wai sai na je gidansu na gaishe da Maamah." Mama ta ce "To ki shirya anjima ki je mana." Ta ce "Ni dai Mama kunya nake ji, kuma ba zan iya zuwa ni kaɗai ba." Mama ta ce "Maganin rashin zumuncin ki kenan, da kina zuwa ki kaiwa Freind's ɗinki ziyara da yanzu sai ki kira wata ta raka ki ku je." Ta ce "Bari in kira zee ta B.U.K." Mama ta ce "Tunda baki da kunya ba, yarinyar nan haka tay ta zuwa gidan nan amma saboda ba kya zuwar mata itama ta gaji ta daina zuwa, yanzu kuma sai ki kira ta ki ce ta zo ta raka ki ko? Tunda zaman ki take." Ta marairaice fuska ta ce "Allah sarki, Haneefah tah, ga ranarta ta zo." Mama ta ce "Bari na kira Hajiya Rabi, idan Salma tana free yau sai ta zo anjima ku je." Neehal ta yi murmushin jin daɗi ta ce "Yawwa Mamana." Mama ta ɗauko Wayarta ta kira Hajiya Rabi wadda ta kasance ƙawarta ce, Salma kuma ƴarta ce baza ta fi mate ɗin Neehal ba. Bayan sun gaisa Mama ta roƙe ta alfarmar zuwan Salman idan babu abun da take. Hajiya Rabi ta ce, zata zo insha Allah bayan an sauko daga masallaci. Mama tay mata godiya su kay sallama. Ta dubi Neehal ta ce "Sai ki kira shi ki sanar masa ya zo da yamma ya kai ku." Ta ce "Toh Mama, amma duk da haka ina jin kunya in na je me zance?" Mama ta ce "To ai ba zama zaku yi ba, gaishe su kawai zaki ku dawo." Ta ce "Tom, bari na je na kira shi." A safiyar Ahmad ya kira wayarta, ta d'aga ta saka a speaker sannan ta bawa su Afrah. Tun ranar Larabar nan da ya tafi ba su kuma magana ba, idan ya kira sai dai ta bawa ƴaƴansa, shima kuma ba ya cewa su bata wayar, ko zancen ta ba ya musu, sai dai su in sun masa maganarta yana biye musu. Ta yi shiru tana sauraren voice ɗinsa a cikin wayar, yana magana da ƴaƴansa cikin nishad'i. Sai ta ji ba daɗi sosai a ranta, na ƙin kulatan da yake kwana biyu, ta turo baki kamar yana ganin ta, jin yana cewa su Afrah ranar Sunday zai zo ya ɗauke su. Afrah ta kalle ta, ta ce "Aunty Daddy ya ce zai zo ya ɗauke mu ranar Sunday." Ba ta ce komai ba, sai lumshe idonta da ta yi. Ahmad ya ɗan lumshe idonsa cikin tsananin kewarta, ambatar sunan ta da Afrah ta yi kawai yasa ya ji ba zai iya jurewa ba sai ya ji muryarta a yanzu. A hankali ya ce "Ina Aunty?" Amrah ta ce "Gata nan, a kwance." Ya ce "Ku bata wayar." Suka matso jikinta suna kiran sunan ta, "Aunty, Daddy ya ce ki karb'i wayar." Tana jin su tay musu shiru, ta kuma ƙi buɗe idonta. Amrah ta ce masa. "Daddy ta yi bacci." Ya san ba baccin take ba, kawai wayar ce baza ta karɓa ba. Sai yay wa yaran sallama ya katse wayar ya tura mata text. Sai bayan sun gama surutunsu sun fita falo sannan ta tashi ta ɗauki wayar, a lokacin ta ga text da Numbern sa. Cikin sauri ta shiga karanta abun da ya turo. _Princess, ya jikin naki, da fatan kin samu lafiya. I MISSED YOU ALOT._ Ta ji wani murmushi ya subce mata, ko ba komai ya nuna care a kanta, duk da bata san me yasa 2 days ya daina kula ta ba, ita kuma tsananin kunyarsa ce tasa in ya kira take kasa pick. Tay masa reply da, _Ina lafiya Uncle, dafatan kai ma haka?_ Ta rungume wayar a ƙirjinta zuciyarta na azalzalarta akan ta kira shi, ta ji muryarsa. Duk da ta ji yanzu da suna waya da su Afrah, amma ta yi missed ɗin yanda yake mata magana da ita a cikin kunnenta cikin salo mai narkar da zuciya, tana ta tunanin nasa bata san bacci ya ɗauke ta ba. Sai ƙarfe ɗaya saura Mama ta tashe ta. "Ki tashi, ki shirya ki shirya su Amrah, ko kin manta zaku fita ne?" Ta tashi zaune cikin muryar bacci ta ce "Ban ma san sanda baccin ya ɗauke ni ba." Mama ta ce "Sai ki tashi yanzu, kafin Salma ta ƙaraso, gidan A'isha zaku fara zuwa sai ya je ya ɗauke ku a can." Tana sakkowa daga kan gadon ta ce "Toh."








Kafin ƙarfe biyu Neehal ta gama shiryawa cikin wani plan cotton material mai kyau, milk colour an masa ado da coffee colour, ɗinkin Baby gown ta yi das a jikinta. Ta yi simple d'auri da d'ankwalin material ɗin, sannan ta yafa mayafi coffee colour. Ta yi kyau sosai, hannunta ya ci zobuna da abun hannu, sai tashin sassayan k'amshinta take. Ta zira plate shoe coffee colour a farar ƙafarta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag itama coffee colour ta zira wayoyinta a ciki. Ta kalli kanta a mirror tana tambayar kanta 'Shigar jikinta ta dace data zuwa gidan surukai? Tun kafin tay wanka take ta tunanin kayan da zata saka a jikinta, da a niyyar ta Hijabi zata zumbula ta tafi, amma kuma data zo saka kayan sai ta fasa ta ɗauko na jikinta wanda bata taɓa saka su ba ta sa. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta wani iri akan zuwa gidansu Sadik ba tare data san dalili ba, ba yau ne first time ɗinta zuwa gidan surukai ba, ta je gidan su Anwar da Jameel, amma wannan sai ta ji kamar ta ce ta fasa zuwan. A hankali ta juya ta fice jikinta a sanyaye, a falon ƙasa ta tarar da Mama da Twins data shirya su tun d'azu, ta kora su gurin Mama dan ta samu damar shiryawa a tsanake. Afrah ce ta fara ganin ta, cikin kaud'inta ta ce "Aunty You look so beautiful." Neehal ta yi murmushi, Amrah ta juyo itama ta ce "Kin yi kyau Aunty." Tay mata murmushi ta ce "Thank you dears." Ta ƙarasa ta zauna a kusa da Mama dake kallon ta, ta ce. "Mama shiga ta bata yi komai ba?" Mama ta ce "Babu abun da ta yi, Daughter sai ma kyau da tay miki." Ta yi murmushi kawai, Mama ta ce "Na ga jikinki duk a sanyaye, ki saki jikinki Daughter babu abun da zai faru sai Alkhairi, Insha Allahu, wannan shine last zuwan ki another in-laws Family." Ta ce "Allah yasa." Ba jimawa da zamanta Salma ta iso gidan, cikin shiga ta mutunci. Mai kyau ce, Black beauty da ita. Ta gaishe da Mama sannan suka gaisa da Neehal, Neehal ta kawo mata drinks ta sha kaɗan bisa takurawar Mama. Kafin ƙarfe uku sun isa gidan Aunty A'isha, Salma da yake she is so friendly tay ta tsokanar Neehal da suna tafiya, dan Mama ta mata bayanin inda za su je, Neehal kam sai dai tay mata murmushi kawai.












Sai bayan la'asar Sadik ya zo ya ɗauke su dan kai su gidansu, har da Maryam ɗin Aunty A'isha suka tafi. Ta so barin su Afrah a gidan Aunty A'isha, amma suka saka ihun sai sun bita, Aunty A'isha ta ce ta je da su kawai. Duk uban warning da ta ja musu akan kar su yi surutun su in je gidan, amma tun a Mota suka fara yiwa Sadik zuba, shi kuma yana biye musu cikin fara'a. Parking ɗin Sadik a compound ɗin gidan su, ya yi dai_dai da fad'uwar gaban Neehal. Ta lumshe ido a ranta tana fatan wannan gidan ya zama na ƙarshe a zuwa gaisuwar surukai a rayuwarta.














Salma ce ta fara fita daga cikin Motar su Afrah suka bi bayan ta cikin zumud'in sun zo unguwa sai kuma Maryam. Sadik ya dubi Neehal ya ce "What happened Wifey?" Ta ce "Nothing, me ka gani?" Ya girgiza kai tare da faɗin. "Babu komai." Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata. Ta ɗan ɓata rai tana masa kallon bata so hakan ba. Ya yi murmushi ya ce "To naga sai jan aji kike, Maamah kuma na san zuciyarta ta cika taf da d'okin ganin ki." Ta fito tana faɗin, "Like me." Ya ce "Sure?" Ta ce "Sosai ma, waye ba zai so ganin Mamansa ba?" Ya yi murmushi, suka jera suka nufi cikin gidan, Salma na bin bayan su tare da tsokanar su tana faɗin. "Gaban dai Mama za'a je, a rage rashin ta ido." Neehal ta harare ta. Sadik ya ce "A'a gwara dai ta gani da idonta irin son da sirikar ta takewa ɗanta, ko Baby?" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kar ka sa in kasa shiga, ni ka yi gaba ma." Ya yi murmushi

Please Login or Register in order to submit comment