Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hankali, ta ce ya je ya dage da addu'a Allah ya zaɓa masa abun da ya fi Alkhairi.






Har bayan Magriba Neehal bata daina kuka ba, Mama ta yi rarrashin ta yi nasihar ta yi faɗan amma ta ƙi barin kukan, har ta gaji ta ƙyale ta. Tana jin wayarta nata vibrate ana ta kiran ta amma ta ƙi bi ta kanta. Ga kanta dake ciwo saboda kukan da take. Bayan Magriban ne Ameen ya zo gidan, lokacin tana ɗakinta a kwance akan gado. Bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta Neehal ɗin, ta sanar masa tana ɗaki tana kuka, ko abinci bata ci ba tun safe. Bai tambaye ta dalilin kukan ba ya tashi ya shiga ɗakin. Ya zauna a gefen gadon ya kira sunanta, ta tashi zaune da ƙyar tana goge hawayen fuskarta, idanunta sun yi jajur. Cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi yay mata Ƴar nasiha, akan kuka ba maganin damuwa ba ne, komai yake damun ka, ka kaiwa Allah kukan ka, shi zai maka magani. Sai gashi ta yi shiru, ya ce ta je ta wanke fuskarta ta zo ta ci abinci. Bata musa ba, ta tashi ta yi abun da ya ce. Mama ta cika da mamakin ganin cikin mintuna ƙalilan ta saki ranta, Alhalin ita tun yamma take fama da ita. Sai da ta ci abincin ta sha maganin ciwon kai sannan Ameen ya bar gidan.










Washegari kamar yadda Dad ya ce, Sadik ya zo gidan da yamma. Har part ɗin Daddy'n akai masa iso ya je ya same shi. Daddy yay masa ƴan tambayoyi, sannan ya ce ya bashi auran Neehal ya turo magabatansa. Ai Sadik ji ya yi kamar ya rungume Daddy dan tsananin farin ciki, yay ta zuba masa godiya. Ranar Neehal ta sha kalamai da soyayya a gurin shi kala_kala, ita kuwa tay ta masa dariya tana tunanin ranar da aka ɗaura musu aure kuma sai ya kusa mutuwa dan farinciki. Bayan sati ɗaya mahaifinsa da abokinsa da Yayan Maamah suka zo nema masa auren Neehal, tare da kuɗin na gani ina so. Daddy da Kawu Musa da Uncle Mahmud, da mijin Aunty A'isha, su suka karb'i kuɗin, aka saka ranar biki bayan ƙaramar Sallah da yardar Allah, lokacin Neehal sun yi graduation ba jimawa. Su Sadik baki ya ƙi rufuwa, saboda farincikin nan da watanni biyar zuwa shida zai angonce da masoyiyarsa. A ɓangaren Ahmad kuwa a washegarin ranar da ya zo ya koma Abuja, yana zuwa ya sanar da su Ummi abun da yake faruwa. Sun ji ba daɗi sosai har Abban su Ahmad, amma suka ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Ahmad ya bawa zuciyarsa haquri, bai bari damuwa ta masa illa ba, duk da ko d'igo babu abun da ya ragu na son Neehal a cikin zuciyarsa. Daga ya ji abun zai dame sa sai ya dinga maimaita kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un da hasbunallahu'wani'imal'wakil, ga zuciyarsa kullum cikin ƙarfafa masa gwiwar Neehal tasa ce take, kar ya fidda rai da samun ta. Kuma babu abun da ya canza wa Neehal daga yanda suke before, idan ya kira wa su Afrah ita a waya, ta ce su ba shi wayar yana karɓa su yi magana har da ƴar tsokana wani lokacin, sai dai ba ya mata zancen soyayya ko kaɗan, zumunci kawai suke yi. Itama Neehal ɗin ta yi ƙoƙari ta cire damuwar rabuwa da shi daga ranta. Ta yadda cewa Allah ya yi Sadik ne mijinta tun fil azal, ba Jameel, Anwar da Ahmad ba, tunda su sun rasu, Ahmad kuma shi yasa Allah ya raba su tun a farko, dan da ace ba su rabu da shi ba a lokacin da take gidan Aunty Fauziyya, da ko soyayya ba zata yi da Jameel da Anwar ba, tunda ga shi kuma tun lokacin yake son ta. Ta kwantar da hankalinta suna shan soyayyar su da Sadik. Sai dai tunda aka tsayar da lokacin bikin su take jin wani irin feeling a cikin zuciyarta, feeling ɗin data kasa tantance ko na mene ne, sai dai yana mata yanayin kamar tsoro ko fargaba, amma kuma tsoron da fargabar na mene? Sai kuma wani abu guda ɗaya, ɗan sakin fuskar data fara samu daga gurin Ameen da kulawa ya daina mata yanzu, sai ta gaishe shi ma ya ƙi amsawa, ita kuma hakan na damunta matuƙa, bata son ta ga yana yi mata irin wannan shariyar, sai ta ji duk ranta babu daɗi........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣0️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












...........Da yamma Haneefah ta zo gidan, duk da tana fama da laulayi amma ta ce ba zata iya kwana bata ga lefen Besty ba. Bayan sun gaisa da su Mama ta hau sama gurin Neehal. A falo ta tarar da ita idanunta a lumshe tana sauraren karatun Alkur'anin da tasa a speaker. Haneefah ta ƙarasa inda take ta taɓa ta, tare da faɗin. "Amarya." Neehal ta buɗe idonta ta dube ta, ta yi murmushi ta ce. "Na'am Ango." Haneefah ta zauna a kusa da ita, ta ce. "Ya na ganki wani iri, ko baki da lafiya ne?" Neehal ta ce. "A'a k'alau nake, kawai yanayi ne." Haneefah ta ce, "Yanayin me? Ke da ya kamata a zo a tarar kina cikin farinciki da annashuwar kin kusa aure." Ta ƙarashe maganar da dariya. Neehal ta harare ta, ta ce. "Zan bar Maman shine zan dinga farinciki?" Haneefah ta ce. "Wannan duk na ɗan lokaci ne, kina jin zaƙin auren zaki ware, wuyarta ki shiga daga ciki, ke Auran fa da daɗi." Neehal ta ƙara hararar ta, ta ce. "Allah ya shirye ki, kin fi ƙarfi na." Haneefah ta yi dariya ta ce. "Ina Barrister? Na ɗauka zan shigo in same ki kina waya da shi kuna soyewa." Ta sauke numfashi ta ce. "Yana nan k'alau, ba mu jima da yin waya ba, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce. "Yana can Kogi State." Neehal ta ce. "Yaushe zaki koma ke?" Ta ce. "Next week insha Allah, tunda by Monday zamu gama exam." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin ƙoƙarin ganin ta ɓoye Mood ɗin da take ciki. Ta tashi ta sauka ƙasa ta ɗebo mata snacks ɗin da akaiwa masu kawo kayan lefen, ta haɗo mata da drinks.








Bayan Magriba kamar yadda aka ce, su Daddy suka karb'i lefen Neehal a gurin magabatan Sadik, suka kuma saka lokacin biki sati takwas, bayan Babbar Sallah da sati biyu kenan. Ba su wani jima ba suka tafi, Daddy yasa ma'aikatan gidan suka shigar da kayan part ɗin Mama, aka baje su a falon ƙasa. Aunty Sadiya ta rangad'a guda, gudar da Neehal dake ɗakinta ita da Haneefah sai da suka jiyo. Wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta runtse idanunta ta shiga ambaton Hasbunallahu'wani'imal'wakil a cikin ranta. Haneefah dake gwagwiyar goruba ta ajiye ta miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki ta fice daga ɗakin da saurin ta. Neehal ta ji wasu hawaye masu d'umi sun zubo a kan kuncinta, wanda ta kasa tantance na farinciki ne ko akasin haka, yau ita ce aka kawo lefen ta, hakan ya nuna mata ta kusa zama mallakin Sadik kenan? Ta kusa aure itama? Kamar amsar tambayar ta sai ga kiran shi ya shigo wayarta. Ta saka hannu ta ɗauki wayar tare da buɗe idonta, ta ƙura wa screen ɗin wayar ido da idanunta dake ganin dishi_dishi saboda hawayen dake cikin su, ganin Sadik ne yake kiran sai ta mayar ta ajiye wayar, haka kawai ta ji bata son yin wayar da shi.






Set ɗin akwati ɗai ɗai ɗai har goma sha biyu Sadik ya yo, sai kuma takalma da jakunkuna a cikin manyan basket ɗin kaba da ake yi yanzu. Su Aunty A'isha fa suka shiga bubbud'ewa suna dubawa cikin farinciki, Haneefah kuma ta shiga yiwa kayan video. Kaya na gani na faɗa masu tsada da kyau aka zuba a lefen, Sadik ya yi ƙoƙari sosai, dan ya kashe kuɗi ba kaɗan ba. Mama ta rasa inda zata saka ranta dan farinciki, ashe za ta ga lefen ƴarta_ta kafin ta mutu, ta shiga addu'ar Allah ya nuna musu ranar bikin lafiya. Har bayan isha'i suna ta aikin kallon kayan, ba su kuma da alamar dainawa, su Dije ma sun fito suna kallon kayan. Sai kod'a kayan da faɗar kyawun su suke. Haneefah dai tana tsakiyar kayan zaune tana ta aikin ɗaukar hotunan su. Suna cikin duba kayan Haneefah ta dubi Mama ta ce. "Mamana yau kina cikin farinciki, dan haka bari na yi amfani da wannan damar na ƙara roƙar ki abun da nake ta nacin roƙon ki in ƙi yarda." Mama ta yi murmushi ta ce. "Haneefah da naci kike amma." Ta yi dariya ta ce. "Ni dai Mama ki amince mu ɗan warwasa, biki lami ai babu daɗi, kamar wadda za ai wa auren dole." Aunty Sadiya ta ce. "Gaskiya Ya Fateemah ki bar su, su warwasa, muma ma je a warwasa da mu." Aunty Aisha ta ce. "Gaskiya dai." Mama ta ce, "Shikenan tunda kun dage, sai a yi kamu kawai." Haneefah ta ce. "Yeee, yawwa Mamanmu, thank you so much, bari mu zo mu zaɓi atamfa mai kyau mu fitar da anko, dan event da anko ya fi kyau." Mama ta ce, "Kina fama da kanki, amma sai shegen son bidiri." Haneefah ta yi murmushi ta ce. "Mama bikin Besty ne fa, aiko jego nake na ajiye ɗan a gefe na wasu kwanaki in sha shagali na." Suka yi dariya Gaba-d'aya, Aunty Sadiya ta ce. "Allah ya shirya ki Haneefah." Suka ci-gaba da tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, a nan Haneefah ta sanar musu Sadik ma ya ce za'a yi dinner, Aunty Sadiya ta ce, itama Dinner ya kamata a fitar mata da nata ankon. Anan suka zaɓi atamfar da za'a yi ta kamu da kuma kalar yadin da k'awayen amarya za su yi na ranar Dinner." Haneefah ta haɗa video na kayan lefen da ankunan bikin ta saka a story. Tare da yin ɗan note na Allah ya sanya Alkhairi da kuma nuna farincikin da take ciki. Har da cewa, Yau tana cikin farinciki bikin besty ya kusa, dan haka ko marin ta akai ba za ta ji haushi ba. Neehal dai tana ɗaki bata san me suke ba, Sallar isha'i ce kawai ta tashe ta, ta tashi ta yi sannan ta koma ta yi kwanciyarta.










Sai da tara ta wuce sannan Haneefah ta shigo ɗakinta. Ta rungume ta cikin murna tare da faɗin. "Besty kin ga lefen ki kuwa, ya haɗu Masha Allah, Yaya Sadik ya yi ƙoƙari sosai wallahi, Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya." Neehal ta janye jikinta daga nata tana murmushi amma bata ce komai ba. Haneefah ta latsa wayarta ta miƙa mata. Ta karɓa ta shiga kallon videon kayan. Sai ta ji wani irin daɗi ya lullub'e zuciyarta, yanzu duk wannan uban kayan nata ne? Gaskiya dole duk wacce aka kaiwa lefe ta yi farinciki. Ta d'ago ta dubi Haneefah ta ce. "Yanzu har kin musu video?" Haneefah ta ce. "Me zan jira, har na watsa su a media ma." Neehal ta ce. "Sannu uwar azarbabi." Haneefah ta ce, "Na ji ɗin, ki yi gaba akwai wanda na haɗa da atamfar ankon da muka zab'a yanzu a wayar Aunty Sadiya, ta ce next week zata yi order, duk mai so sai ya siya. Ki tura videon sai ki yiwa duka friends ɗinki sending, ki faɗa musu date ɗin bikin, 8 weeks aka saka." Neehal ta ce. "Toh." Tare da ƙara kallon videon. Ta janyo wayarta, first abun da zata yi kafin sending videon ta fara yiwa Sadik godiya. Ta shiga contact ɗinsa ta rubuta masa text mai cike da tarin godiya da kuma addu'oi, sai kuma kalaman soyayya. Sannan ta tura video's ɗin ta shiga yiwa k'awayenta sending. Nan fa mutane aka yi caaa a kanta, "Dama bikin ki za'ai Neehal babu labari? Wow kaya sun yi Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi. Ai dole mu yi anko bikin ki guda." Maganganun da ta yi ta sha kenan, ta dinga murmushi kawai. Haneefah tay ta tsokanarta bayan ta yi Sallah. Mama da kanta ta zo ta kama hannunta suka sauka ƙasa ta ga kayan, su Aunty nata tsokanarta. Ita kuma wata irin kunya take ji, bata ma san tana da kunya haka ba sai yau. Ganin yanda Mama take cikin farinciki, sai hakan ya ƙara mata nata farincikin itama. Ta dinga kallon kayan a cikin ranta tana ƙara yabawa Sadik gami da jinjina masa. Sai kusan ƙarfe goma su Aunty A'isha suka tafi gidajensu, Haneefah kuwa ta yiwa Faruq waya, ta ce masa ta yi dare a gidansu zata kwana. Da Daddy ya shigo gidan ya zauna Mama tana bubbud'e masa kayan yana gani, shi kuma yana ta tsokanar Neehal dake cin abinci. Sai dai ta yi murmushi kawai kanta a ƙasa, sosai take jin farinciki, bata jin ko baccin kirki zata iya yi yau, duk wani feeling na damuwa da take ji kusan rabi ya tafi. Ranar kusan raba dare suka yi suna tattauna yanda bikin zai kasance ita da Haneefah, bayan kowacce ta gama shan waya da masoyinta. Da yake Neehal har Zahra ƙanwar Ahmad ta tura wa lefen, data kunna data sai ta ji voice ɗin su Afrah wanda ya sata dariya ba kaɗan ba. Dan gaba-d'aya yaran sun ruɗe da murna ganin kayan, sai zaɓar abubuwan da suke so a cikin kayan suke tun kafin su zo. Washegari tun safe mak'ota suka fara shigowa ganin kayan, ranar wuni su kay cikin karɓar baƙi ƴan ganin kaya, k'awayen Neehal da k'awayen Mama gami da ƴan'uwa, cikin baƙin har da Hafsat da Hajiya da Matar Uncle Mahmud, da matar Kawu Musa. Neehal dai ta sha tsokana a gurin mutane. Ummin su Ahmad da Mamy sun kira ta a waya sun mata Allah ya sanya Alkhairi. Shima Ahmad ɗin ya kira ta, yay ta tsokanarta kuwa. Da daddare Ameen ya zo gidan, Mama ta bubbud'e masa kayan ya gani, duk da, da farko cewa ya yi ba sai ya gani ba. Amma Mama ta ce, ya dai gani ɗin yasa Albarka. Haka su kay ta shan baƙi ƴan ganin kaya, ƴan aikin gurin su Neehal dana gurin su Mama. Amaryar Uncle Umar ta zo, amma banda Aunty Fauziyya. A gurinta Neehal take jin ashe Uncle Umar ɗin ya saki Aunty Fauziyyan, a dalilin cikin shegen da Iman ta yi, ya haɗa su duka ya kore su. Neehal bata ji daɗi ba har da kukan ta. Shi kuma Uncle Umar ya gama haɗa kuɗaɗen sa zai yo sarin kaya ya zuba a shago b'arayi suka tare shi suka k'wace kuɗaɗen. Aunty Hauwa tana faɗawa Neehal har cuta ya yi saboda tashin hankali da damuwa. Ita kuma ta k'wace duk wasu takardun kadarorin Neehal, kuɗaɗen ta kuma suna account ɗinta. Ta ce ba zai ci kuɗin marainiyar Allah ba, sai dai ya fita ya nemi nashi ko dako ne ya yi. Neehal ta cewa mata ta ba shi dukiyarta ita ta bar masa duniya da lahira, Aunty Hauwa ta ce. Abun da ba zai yiyu ba kenan, dan ta gama yanke shawara ana yin bikin Neehal ɗin zata tattaro mata dukiyarta ta damk'a mata a hannunta, ta juya abunta ta nemi kuɗi. Shi kuma Uncle Umar tunda yana koyarwa zasu cigaba da jalautawa a haka. Neehal dai bata ji daɗin abun ba sam, dan sosai tausayinsu ya cika mata zuciya.






Babbar Sallah saura sati ɗaya Mama ta ɗauko matar da zata yiwa Neehal gyaran jiki daga Maiduguri, sunan matar Hajja Gana, dan Mama so take a gyare mata ita sosai ciki da waje. Da ƙyar Neehal take zama a yi mata gyaran jikin, sai Mama ta mata jan ido tukunna, mai gyaran jikin tay ta dariyar dramar Mama da Neehal, wadda tunda bikin ya matso ta koma so silent, abun kaɗan sai kuka da k'unci. Mama kuwa ta tattara ta, ta watsar shirye-shiryen biki kawai take ba kama hannun yaro. Siyayya ba kaɗan ba take jibgowa Neehal ta kayan kitchen. Daddy kuwa ya ce, a je a duba gidan Sadik sannan Neehal da Mama su je duk inda take so ta zaɓi kayan ɗakinta da kanta wanda zai cika gidan. Ameen kuma Mama ta ɗaura masa nauyin siyayyar duk wani kaya da Neehal zata saka na fitar biki shi zai siya mata, tun daga kan ɗan'kunne da sarka har zuwa takalma, ta ce ba zata saka komai a cikin kayan lefen ta ba. K'awayen Neehal da ƴan'uwa suna ta kara suna ta siyen anko, ƴan NEEHAL FAN'S GROUP ma ba'a bar su a baya ba, sun ce ba'ayi ba su ba. Neehal ta kasa tantance yanayin da take ciki, bikin na ƙara kusantowa tsoron da zuciyarta take ciki na ƙara tsananta. Ta rasa tantance tsoron ko na mene ne, tana jin kamar wani abu mara daɗi na shirin faruwa, duk da kullum Aunty Sadiya cikin rarrashin ta da ƙara jaddada mata cewar haka kowacce amarya haka take jin irin wannan feeling ɗin, ta kwantar da hankalinta ba wani abu ba ne. Ita dai ta ƙara k'aimi gurin dagewa da addu'a, kamar yadda Mama take tunatar da ita a kullum. A ɓangaren Sadik kuwa zai iya cewa tunda ya zo duniya bai ɓata riskar kansa a farinciki irin na wannan lokacin ba, kullum cikin lissafin kwanakin bikin da suka rage yake, tare da ƙara dagewa gurin farantawa Neehal da nuna mata k'auna. Zuwa yanzu Ahmad ya cire rai da samun Neehal, kuɗi masu kauri ya turo mata a matsayin gudunmawarsa, dan ya rasa mai zai sai mata. Da tay masa complain ɗin kuɗin ya yi yawa sai ya yi fushi ya ce bata ɗauke shi a matsayin Uncle ɗin da take kiran shi ba kenan. Da ƙyar ta lallaɓa shi ya haqura sannan tay ta zuba masa godiya kamar ba gobe, Mama ma ta kira shi tay masa godiya.










Bayan Babbar Sallah da sati ɗaya an gama soyasoyen nama da shan bukukuwan Sallah wanda ya kama bikin Neehal saura sati ɗaya. Ranar Alhamis da daddare Neehal tana ɗakinta tsaye a gaban mudubi, fitowarta kenan daga wanka bayan da aka gama mulke mata jikinta da haɗin gyaran jiki da ake mata. Tana shafa mai amma kallon fatar jikinta kawai take yi, yanda ta canza ta yi wari irin laushi hami da haske, har wani pink_pink jikinta yake yi saboda an mata halawa. Ita kanta bata gajiya ta taɓa jikinta, dan ji take kamar ba jikinta ba tsabar sulb'i da kyau, dan tana shan gyara bana wasa ba. Ga wani irin fitinannen k'amshi dake tashi a jikinta, duk inda ta gilma kuwa sai an ji shi. Dan ma bata fita yanzu kwata_kwata, tun satin da za'a fara mata gyaran jiki ta ɗauki hutu a gurin aiki. Jiya da Sadik ya zo kawo mata invitations card kamar zai cinye ta saboda santi da kyawun da tai masa.








A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakin tare da yin Sallama, ta juyo ta kalli ƙofar da sauri. Ganin Ameen ne ta yi saurin tashi ta ɗauki hijabin dake gefen gado ta zira a jikinta cikin rawar jiki. Shi ko bai ko kalli inda take ba, ya ajiye ledodin hannunsa a kusa da ƙofa. Ya juya yana ƙoƙarin fita ta ce. "Yaya!" Ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Ta ƙarasa ta tsaya a kusa da shi. A hankali ta ce. "Thank you so much, Allah ya ƙara buɗi." Ya juyo ya zuba mata ido, itama idanun ta zuba masa ganin yanda yake kamar wani mara lafiya. Lokaci ɗaya idanunta suka kawo ruwa, cikin damuwa ta ce. "Yaya baka da lafiya ne? ko kuma wani abun ne yana damun ka?" Ya yi mata ɗan murmushi tare da girgiza mata kai. Ta fara hawaye ta ce. "Yaya i know baka da lafiya, ko kuma wani abun yana damun ka, Yaya You look so worry." Ya tako a hankali ya matso daf da ita, a hankali ya kama fuskarta da hannuwansa duka ya saka idanunsa cikin nata ya ce. "Nothing Miemerh, Just pray for yourself and me." Ta gyaɗa masa kai a hankali cikin rashin fahimta. Ya saki fuskarta sannan ya kuma yi mata murmushi ya juya ya fita. Ta bi shi da kallo tana maimaita abun da ya faɗa a cikin zuciyarta, a ƙoƙarin ta na ganin ko zata gane mai yake nufi amma bata gane ba. Addu'a abu ne mai kyau akan kowanne mutum, may be shi yasa ya ce tay musu addu'a ita da shi. Ta sauke numfashi ta ƙarasa inda ledodin da ya ajiye suke ta tsugunna ta shiga fito da kayan ciki tana dubawa. Kayan da zata yi fitar biki ne da su, kuma gaba-d'aya kalolin da ta ce masa tana so ya siyo. Babu abun da zata saka wanda bai sako ba, har da su undies da pant da bra. Ta yi murmushi ita kaɗai cikin jin kunya. Wedding gowns ɗin da zata saka ranar kamu, Dinner da ranar D'aurin Aure da safe. sun fi komai burge ta da yi mata kyau a cikin kayan, gashi daga ganin su masu tsada ne. Ta cire hijabin jikinta cikin murna ta fara gwada kayan.








Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga bayan ya fita, ya tarar da ita da Aunty Sadiya suna haɗa kayan da suka siyo d'azu a kasuwa. Tunda bikin ya gabato ba'a kwana biyu ba su je kasuwa ba. Bayan ya yi sallama ya zauna a kujerar dake gefen gado. Suka bi shi da kallo, Ba tare da Mama ta amsa gaisuwar da yay mata ba ta ce. "Al'ameen! Meke damun ka ne?" Ya lumshe idonsa bai ce komai ba. Mama ta shiga yi masa masifa akan wannan shegen muskilancin nasa da zurfin ciki, idan wani abu ke damun shi ai sai ya sanar mata, ko baza ta magance masa ba sai tay masa addu'a, amma ya gwammace ya bar abu a ransa yay ta damun sa, ita mahaifiyarsa ce baza ta so ta dinga ganin shi cikin damuwa ba, idan ma wata matsalar ce tsakanin sa da matarsa ai ya kamata ya sanar mata a san abun yi. Tunda ba shi da kamar ta a duk duniyar nan. Faɗa sosai Mama tay masa, Aunty Sadiya na bata haquri amma bata yi shiru ba sai da ta kai aya. Ganin yanda ran Mama ya ɓaci ya dinga bata haquri, ya sanar mata yanayin aiki ne kawai. A k'ufule Mama ta ce. "Aiki, aiki. Daga an yi magana ka ce aiki, kamar kai kaɗai ke aikin duk duniyar nan, a gurin aikin yankar naman jikinka ake ai. Amma ka cigaba idan ganin ka cikin damuwa ya haifar mun da wata damuwar nima ai ka ji daɗi." Bata jira amsar shi ba ta tashi ta fice daga ɗakin, Ya bita da ido. Aunty Sadiya ta dawo kusa da shi ta zauna cikin rarrashi ta ce. "Ameen! Rayuwar nan cike take da k'alubale da kaddda kala_kala, kowa ka gan shi ka kalle shi kawai, amma shi kaɗai ya san abun da ke damun sa, kuma bawa ba ya taɓa kaucewa ƙaddarar sa, ka saka wannan a ranka, sannan kuma ka rage damuwa, Please Ameen." Ya sauke numfashi ya ce. "Insha Allah Aunty Sadiya I will try." Aunty Sadiya ta tsaya kawai tana kallon sa kamar yadda shi ma yake kallon ta, kallo mai kama da na tausayi tare da jiman ta wani al'amari." Ta ɗauke idonta daga kallon sa cikin raunin murya ta ce. "Ka je ka bawa mahaifiyarka haquri, ka ga ranta ya ɓaci sosai." Ya ja numfashi mai huci ya sauke sannan ya miƙe bai ce komai ba ya fice, Aunty Sadiya ta girgiza kanta cikin damuwa, alamun something is hurting her heart. Bayan ya tafi Aunty Sadiya suna falo zaune ta cewa Mama. "Ki yi haquri Yaya Fateemah akan al'amarin Ameen, na ga kamar har yanzu ranki a ɓace yake." Mama ta girgiza kai cikin sanyin jiki ta

Please Login or Register in order to submit comment