Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kam, bari na ci abinci nay wanka sai nay miki bayani." Mama ta yi murmushi ta ce. "Ga dukkan alamu dai baka da labarin an ga Sadik." Daddy ya ce. "What? Yaushe? Wallahi ban sani ba." Mama ta ce. "Tun yamma aka gan shi ko in ce ya dawo, dan Mamansa ta ce mun da kansa ya shigo gida cikin k'oshin lafiya." Daddy ya ce. "Alhamdulillah, kai Masha Allah for this nice story, to ya akai ya dawo?" Mama ta ce. "Bata faɗa mun ba, da zamu je gidan kuma rashin dawowar ka da wuri yasa bamu je ba, su Sadiya ma duk sun zo d'azun, amma gobe da safe Insha Allah zamu je gaba-d'ayan mu." Daddy ya zauna yana murmushin farinciki. Mama ta ce. "Kwanan masallaci ana sauka ya ƙare, yau sai ka more bacci ko zaka ciko, dan ba ƙaramar rama ka yi ba a Ƴan kwanakin nan." Daddy ya yi murmushin dake bayyanar da farin cikinsa ya ce. "Dole ai, bari na kira baban yaron na fara yi masa murna." Mama ta ce. "Toh, bari na kawo maka abincin ka nan ka ci." Daddy ya ce. "Ina Daughter ɗin ne da Hajiya?" Mama ta ce. "Sun kwanta tuntuni, Neehal ta sha kuka kanta sai ciwo yake mata." Daddy ya ce. "Sarkin kuka kenan, ta cancanci award ta wannan fannin." Mama ta ce. "Rashin duka ne da iskancin banza, abun kuka da bana kuka ba ita duk kuka take musu." Daddy ya yi dariya ya ce. "Duka kuma Doctor? Tab' ai ba me taɓa mun ƴa ya kwana lafiya, saurin kukanta kuma ai halitta ce, da yawan mutane haka suke musamman ku mata." Mama ta ce. "To Allah ya yaye mata."








Tun bayan isha'i Neehal take saka ran ganin kiran Sadik a wayarta amma ta ji shiru, tun tana jira har bacci ya ɗauke ta. Data tashi da asuba ta ɗauka zata ga text ɗinsa ko missed call ɗin sa, amma ko ɗaya bata gani ba. Bata yi tunanin komai ba sai ta yi tunanin ko yana cikin dangi ne anata murnar ganin sa, ko kuma a gajiye ya dawo ya yi bacci da wuri. Kafin ƙarfe goma na safe sun gama shirin su na zuwa gidansu Sadik dukan su, Aunty Sadiya ma ta zo, Aunty A'isha ce dai tunda a unguwar take sai dai su biya gidanta su ɗauke ta.










Mama da Daddy da driver a Mota ɗaya, Neehal da Hajiya kuma suna Motar Aunty Sadiya. Sun fara tafiya Mama ta dubi Daddy ya ce. "Jiya Ameen bai zo gida ba, yanzu kuma na kira shi ya zo mu je gidansu Sadik da shi wai ba zai samu damar zuwa ba, sun fita operating tun safe wani ƙauye." Daddy ya ce. "Allah sarki Son ba dai jajircewa a aiki ba." Mama ta tab'e baki ta ce. "Ni ban ma yarda da sun fita wani aiki ba, yau fa Saturday." Daddy ya ce. "Ina ruwan aikin tsaro da weekend Doctor, ko kin manta yanda na yi da ne, sai kina kira na kina Hamma Tafida wai baza ka dawo gida ba, idan ma kin same ni a wayar kenan." Mama ta yi murmushi tana tuna lokacin farkon Auren su ita da Daddy, lokacin suna faman yawon gari_gari a Nigeria idan an yi posted ɗinsa, wani gurin ma ba zai yiwu ya tafi da ita ba sai dai ya bar ta a gida. Cikin mintuna ashirin suka ƙarasa gidansu Sadik. A compound ɗin gidan suka tarar da Abban Sadik shi da Kawu. Suka gaisa cikin mutuntawa tare da yi musu murnar bayyanar Sadik da addu'ar Allah ya tsare gaba, Sannan su Neehal suka shige cikin gidan suka bar Daddy a gurin su Abba. Da fara'a sosai Maamah da ƴan'uwanta suka tarb'e su, suka gaisa cikin mutunta juna tare da ƙara jajanta abun da ya faru, su Mama sukay musu murnar bayyanar Sadik. Neehal dai tana ƙasa zaune akan carpet kanta a ƙasa, Hajja tana ta tsokanar ta, sai dai ta yi murmushi kawai, wata ƙanwar Maamah na tare mata. Ƴan'uwan Maamah suna da kirki sosai, kuma suna son Neehal da ɗansu, kawai babu yadda zasu yi dan su kansu al'amarin na ba su tsoro. Batul ƙanwar Sadik ce ta shigo falon, ta gaishe da su Mama sannan ta zauna a kusa da Neehal ta gaishe ta. Murya ƙasa_ƙasa yadda Neehal ɗin ce kaɗai zata ji ta, ta ce. "Aunty Neehal Yaya ya ce ki zo." Cikin d'oki Neehal ta ce. "Yana ina?" Batul ta ce. "Yana bayan gida nan." Neehal ta yi shiru dan bata san ta yanda zata iya tashi ta tsallake su Maamah da Mama ta tafi gurin Sadik ba. Maamah data fahimci abun da ke faruwa sai ta cewa Neehal. "Ƴata ku je da Batul ki ga jikin Sadik ɗin." Cikin jin kunya ta ce. "Toh." Sannan ta miƙe a hankali ba tare da ta kalli kowa ba ta bi bayan Batul wadda ta riga ta tashi. A wata rumfa dake bayan part ɗin Maamah suka same shi zaune akan ɗaya daga cikin kujerun robar dake gurin. Ta ƙura masa ido kamar yadda shi ma ya zuba mata nasa, sai ta ga ya rame ya ƙara haske. Ta zauna a kujerar dake fuskantar wadda yake kai, Batul kuma ta juya ta koma cikin gida. Sadik ya yi murmushi ya ce. "Neehal!" Ta mayar masa da matarnin murmushin ta ce. "Sadik!" Ya ce. "Na'am da fatan kina lafiya?" Ta ce. "Lafiya k'alau, Alhamdulillah Yaya Sadik, na gan ka cikin k'oshin lafiya ba kamar yadda muka yi zato ba, na ji daɗin hakan sosai sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba." Sadik ya ce. "Amin ya Allah, Are you sick?" Ta ce. "Lafiya ta k'alau, me ka gani?" Ya ce. "Duk kin rame Neehal." Ta ce. "Tashin hankalin ɓatan ka ne kawai amma yanzu ai komai ya wuce, tunda Allah ya dawo mana da kai lafiya." Sadik ya danne duk wata damuwa dake cikin ransa suka cigaba da hira da Neehal, har yake bata labarin yanda aka sace shi da inda aka kai shi.








A Parlour'n Maamah kuwa bayan fitar su Neehal ba jimawa Hajiyarsu Sadik ta shigo Parlour'n. Bacci take a part ɗin Umma aka taso ta aka ce mata iyayen Neehal sun zo. Su Mama suka gaishe ta cikin girmamawa. Ta amsa ba yabo ba fallasa sannan ta ce. "To Alhamdulillah, yaron mu ya dawo lafiya, mun gode da zuwar mana murna da kuka yi, amma ku sani babu batun Aure yanzu a tsakanin sa da ƴarku." Cikin mamaki Hajiya ta ce. "Saboda da me kuma?" Ta ce. "Saboda mu tsiratar da rayuwarsa daga faɗawa halaka mana, dan wannan yar taku ba matar aure ba ce, yawwa, dan haka baza mu ɗauki ɗanmu mu aura masa ita watarana kawai mu wayi gari mu ga an kashe mana shi ba." Mama ta kalli Aunty A'isha dake gefen ta da sauri suka haɗa ido. Cikin rashin jin daɗin abun da Hajiyarsu Sadik ta faɗa, Hajja ta ce. "Haba Hajiya, wannan wacce irin magana ce?" Hajiya data saki baki tana kallon ta, ta ce. "Ko mutuwa tana kunyar idon iyaye, amma ke matar nan ki dubi tsabar idon mu ki faɗa mana haka? Saboda mun zo inda kike." Maamah ko kaɗan bata ji daɗin abun da Hajiyar ta ce ba, ta dubi su Mama ta ce. "Dan Allah ku yi haquri." Hajiyarsu Sadik ta ce. "Haqurin me zaki ba su, kar ma su yi haqurin gaskiya ce dole a faɗe ta, ƴarsu annoba ce wadda zaman ta ma a cikin al'aumma bala'i ne, wa ya sani ma ko mayya ce take lashe kurwar samarin nata." Wannan kalmar ta maita da Hajiya ta danganta Neehal da ita ta bala'in k'ona ran su Mama ta yi ba. Hajiya ta ce. "Insha Allahu sai dai ki ga maita a zuri'arki ba dai a tamu ba, kuma Allah sai ya sakawa yarinyar nan k'azafin maita da kikai mata, ɗanku kuma ku kwad'anta shi ku cinye ko ɗan gold ne Neehal baza ta aure shi ba." Ganin abun yana neman ya zama babban faɗa Maamah ta yiwa Abba text akan ya zo, dan duk haqurin da Hajja take ba su akan ɗan Allah su bar maganar haka amma sun ƙi saurarar ta. Aunty Sadiya da baza ta iya jure cigaba da sauraren munanan kalaman Hajiyarsu Sadik akan Neehal ba ta miƙe tana duban Hajiyar ta ce. "Yarinyar nan ƙaddara ce Allah ya ɗora mata wadda babu wanda ya fi ƙarfin ya ɗora masa ita, ita ma ba yin kanta ba ne. Dan haka karki sake danganta ta da maita, idan kin manta bari in tuna miki shari'ar maita ba ƙaramin abu ba ne, wallahi idan kika sake alaƙanta Neehal da maita zaki sha mamaki." Tana gama faɗar haka ta ɗauki jakarta a fusace, ta cewa su Mama su tashi su tafi. Kafin su kai ga tashin Abban Sadik ya shigo falon a ruɗe, bai tambayi ba'asi ba dan ya san halin mahaifiyarsa ya shiga ba su haquri. Hajiyarsu Sadik kuma sai ta saka kuka wai ƴar cikinta wadda ta yi jika da ita ta zage ta amma ya zo yana ba su haquri.










Su Neehal suna can suna hira ba su san me yake faruwa ba, ita Neehal kanta gaba-d'aya ya kulle da labarin da Sadik ya bata, a yanda ta fuskanta waɗanda suke kawo masa abinci a inda aka ajiye shi su suka fito da shi suka dawo da shi gida. Kenan wanda yasa aka ɗauke sa shi ya saka aka dawo da shi, sai ta shiga tambayar kanta ta yaya Ameen ya fito da Sadik? Ko kuɗi ya bawa masu tsaron nasa fiye da yadda wanda ya saka su aikin ya ba su suka fito da Sadik ɗin? Ko kuma ƙarfi ya nuna musu ya tsoratar da su? Ko da hukuma ya haɗa su? Amma idan da hukuma ya haɗa su ai hukumar ce zata fito da shi su kuma a kama su. To ko dai ya san wanda ya sace Sadik ɗin ne? Sai ta girgiza kai a ranta tana cewa hakan ma ba zai taɓa faruwa ba, ta bar yiwa kanta tambayoyin tun kafin ta fara rubbish ɗin tunani akan Yayan nata wanda ta san ba za'a taɓa haɗa baki da shi a satar Sadik ba, ta k'udurce a ranta zata tambaye shi ya warware mata yanda abun ya kasance, duk da ta san halinsa da ƙyar ya bata amsa. Sadik yana ƙoƙarin faɗa mata abun da yake ransa na raba sun da aka yi dan kar ta ga lefin sa ta ga kamar ya zalunce ta ya yaudare ta, amma zuwan Batul kiran Neehal ɗin ya hana shi yi mata zancen, Batul ta ce ta zo su Mama suna jiran ta za su tafi. Neehal ta miƙe suka yi sallama da Sadik, ta lura da yanda jikinsa ya yi sanyi k'alau da kuma yanda yake bin ta da wani irin kallo. Ta tafi tana jin ba daɗi a zuciyarta kamar kar su rabu, sai ta tarar su Mama har sun shishshiga Mota zuciyoyinsu babu daɗi. Ta buɗe Motar Aunty Sadiya ta shiga, bata lura da yanayin da suke ciki ba saboda bata bari sun haɗa ido da kowa ba, har suka je gida babu wanda ya ce k'ala, sun yi shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa.










A Parlour'n Mama suka zauna gaba-ɗayan su, sai a lokacin Neehal ta lura kamar duk suna cikin ɓacin rai. Daddy ya sauke wani gwauron numfashi yana duban Neehal cike da tausayawa. dan shi ma Abba ya faɗa masa komai akan fasa Auren ta da Sadik. Mama ta janyo ta jikinta cikin damuwa ta ce. "Ya kika ga jikin Sadik ɗin?" A hankali ta ce. "Lafiyar sa k'alau." Mama ta sauke numfashi ta ce. "Ki yi haquri Neehal da rayuwa a duk yanda ta zo miki, duk abun da kika ga kin rasa ba Alkhairi ba ne a gare ki, idan kika yi haquri da tawakkali sai ki ga Ubangiji ya sauya miki da wanda ya fi wanda kika rasa ɗin, komai lokaci ne da shi kuma komai mai wucewa ne, na daɗi ko na wahala. Neehal iyayen Sadik sun ce ba zai aure ki ba." Ai Neehal ji ta yi kamar Mama ta soka mata mashi a ƙirjinta, ta runtse idanta a ƙoƙarin ta na ganin hawaye sun zubo mata kamar kodayaushe idan tana cikin damuwa ko zata ji abun da ya tokare mata ƙirji ya yi ƙasa, amma sai hawayen suka ƙi zuwa wannan karon. Ta buɗe idonta tare yin murmushi mai ciwo wanda ya matuƙar bawa su Mama mamaki ta ce. "Shikenan Mama, Allah yasa haka shi Alkhairi, dama na san haka zata iya faruwa." Bata jira amsa ba ta miƙe dak'yar ta nufi upstairs, ko ganin gaban ta bata yi sosai saboda tsananin damuwa. Suka bi ta da kallo gaba-d'ayan su cike da tsantsar tausayawa Aunty A'isha har da k'walla. Hajiya ta fashe da kuka ta ce. "Gaskiya duk mai aikatawa yarinyar nan wannan abun Allah ka wulaqanta rayuwarsa ta duniya da lahira, Allah ka saukar masa bala'in da ya fi ƙarfin sa." Mama ta lumshe idonta wani tunani na d'arsuwa a cikin ranta wanda take ganin Insha Allahu shine ƙarshen matsalar Neehal. Aunty Sadiya ta ce. "Komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah." Aunty A'isha ta ce. "Allah yasa." Suka cigaba da jimanta al'amarin, suna jinjina wulaqanci irin na Hajiyarsu Sadik. Aunty A'isha ta ce. "Ni ban ji daɗin maganganun da kika faɗa mata ba Sadiya, tunda babbar mace ce ta haife ki." Aunty Sadiya ta ce. "Ai bata da wani girma sai na jikinta, dan abun da ta yi halin ƙananun mutane ne." Hajiya ta ce. "Gwara da kikai mata hakan ai, da za ji zancen Shari'ah ai shiru ta yi ta kama kukan munafurci, yanzu sai a tattara musu kayansu da kuɗaɗen su a mayar musu." Daddy ya ce. "Insha Allahu gobe zan kira Alh. Musa da su Usman sai su zo mu mayar musu." Suka amsa da Allah ya kai mu. Su Aunty's ba su wani jima a gidan ba suka tafi, saboda yanda zuciyoyinsu gaba-d'aya babu daɗi, Hajiya ma ta ce gobe zata wuce Gombe.












Dak'yar Neehal ta iya ƙarasawa ɗakinta saboda juyawar da kanta yake mata. Ta faɗa kan gado tana maimaita Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un cikin sark'ewar harshe. Jikinta gaba-ɗaya rawa yake kamar yadda take jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi, ba rabuwa da Sadik ne yafi damun ta ba, *Baƙin tabon* da aka yiwa rayuwarta ne ya fi komai damun ta, ta san shikenan an fara kenan, duk wanda ya ƙara fitowa da niyyar Aurenta mutanen gari zasu hana shi ko kuma idan ya ƙi jin maganar mutane iyayensa wanda ya zama dole yay musu biyayya su hana shi, shikenan kuma wataƙila ita da Aure sai a lahira. Ta tuno gawar Jameel data gani lokacin da za'a kai shi makwancinsa na gaskiya, sannan ta tuno Anwar ma, ta tuno Ahmad ranar da suka rabu a soyayya sannan ta tuno moment ɗinsu da Sadik na d'azu, ta tuna yanda yake kallon ta da yanda ta ga jikinsa a sanyaye da damuwar data hango ƙarara akan fuskarsa, ashe duk na rabuwa da ita ne, hirar ƙarshe suka yi, kallon ƙarshe yake mata ashe. Sai a lokacin ta ji wasu hawaye masu d'umi suna bin kuncinta, wanda take jin kamar a zuciyarta suke sauka suna ƙara mata zafin da take ji a cikin zuciyarta_ta. Ta daɗe a cikin wannan halin mai wuyar fassaruwa, wanda ta kasa bambance a sume take ko a normal rayuwa saboda tsananin damuwa. Bata san mintunan data ɗauka ba ko awanni ba sai ji ta yi Mama tana mata magana. Ta d'ago kanta da yay mata nauyi ta dubi Maman, Mama ta taɓa jikinta ta ji ya yi zafi. Ta shafa fuskarta ta ce. "Ki tashi ki yi Sallah, ko baza ki iya ba?" Ta yunƙura ta tashi zaune dak'yar, a zaunen ma sai ta ji kamar jiri yana ɗibar ta, amma saboda kar tayar da hankalin Mama ta ce. "Zan iya." Mama ta ce. "Sannu kin ji, ki yi Sallar sai ki ci abinci ki sha magani, ki yi ta maimaita sunan Allah da Hasbunallahu'wani'imal'wakil, Insha Allahu zaki ji sauƙin zafin zuciyarki." Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta bi ta da kallon tausayawa sannan ta tashi ta fice. Bayan ta yi Sallar a zaune Mama ta kawo mata abinci, favourite ɗinta Mama ta yi hoping zata iya ci, amma lauma ɗaya ta yi ta ji abincin ya kasa wucewa ta mak'oshinta, sai ta ji kamar ƙasa ta watsa a bakin nata, ba shiri ta furzar da abincin. Sai tea Mama ta haɗa mata ta sha shi ma da ƙyar ta iya shan kaɗan. Mama tay mata allura ta kwanta ta samu bacci ya ɗauke ta. Tana cikin baccin ta ji muryar Haneefah a kanta. Ta buɗe ido sai ta gan ta zaune a gefen ta. Haneefah ta ce. "Yau kuma bacci ake, na ɗauka zan zo in tarar kuna hira da Habibin naki." Neehal ta tashi zaune bata ce mata komai ba ta sauka ta shiga toilet saboda fitsarin data ji ya ɗaure mata mara. Bayan ta fito ta cewa Haneefah. "Yaushe kika zo?" Haneefah ta ce. "Na kai 30 minutes, na gaji da jiran ki har sai kin tashi da kanki shi yasa na tashe ki." Neehal ta ce. "Kin kyauta ai, gashi nan kin ja mun ciwon kai." Haneefah ta ce. "Sharri kayan k'walba." Sai kuma ta yi murmushi ta ce. "Ashe an ga Ya Sadik, dan iskanci shine baki kira ni kin faɗa mun ba." Neehal ta ce. "Sorry ƙawata, wallahi babu wanda na faɗawa, farinciki ya mantar da ni." Haneefah ta ce. "Sai fa Mommy ce da muka yi waya d'azu take mun zancen, ta ɗauka ma na sani. Na ce mata ban sani ba wallahi, ta ce mun Mama ce ta kira ta, ta faɗa mata." Neehal ta ce. "Ya dawo, cikin k'oshin lafiya ma." Haneefah ta ce. "Masha Allah, haka muke fata dama, yanzu sai k'unci da damuwa su ƙare Tunda Ango ya dawo." Haneefah ta ƙarashe zancen cikin sigar tsokana. Neehal ta yi murmushi mai ciwo ta ce. "Mu fara yin Sallah Haneefah, na ji an shiga a masallaci sai in baki labari." Haneefah ta ce. "Toh."












Duk yanda Neehal take tunanin Haneefah zata ruɗe idan ta ji an fasa Auren su da Sadik sai ta ruɗe fiye da haka, ta miƙe tsaye kamar wata zautacciya tana ambaton Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Idanunta a waje. Neehal ta kama hannunta ta zaunar da ita ta ce. "Karki tada hankalin ki Haneefah nina barwa Allah komai, domin shi yake tsara mun rayuwa kuma ya fi ni sanin dai-dai a cikin ta, ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar tawa." Ta ƙarashe maganar cikin matuƙar raunin murya. Haneefah ta girgiza kanta idanunta fal da hawaye ta ce. "Abun ya yi yawa Neehal, daga wannan sai wannan, amma ba komai, komai na Allah ne kuma aure lokaci ne da shi idan lokacin yinki ya yi dole ki yi, babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana yiyuwar sa." Neehal ta ce. "Hmmm, Haneefah ni ƴar jarida ce cikakkiya, a kullum cikin jin labarin halin da duniya take ciki nake, haka kuma ina jin labarin ƙaddarar mutane da dama, kowa da irin tasa, wasu matsalar talauci, wasu ciwo, wasu matsalar gidan aure ga suna nan dai matsalolin da yawa barkatai. Amma ban taɓa jin irin nawa ba, Ni kam Haneefah na fitar da rai da Aure har abada, zan cigaba da rayuwata ni kaɗai, in dage da bautawa Ubangiji nah domin samun rabauta a k'iyama. Amma Haneefah na gaji da wannan tashin hankalin, ƴan'uwa da abokan arziki kowa babu kwanciyar hankali. Ki kalli Mama fa, matar da ba ita ta haife ni ba, amma na tabbata damuwata ta kusa saka mata wani ciwon, haka ma Daddy jibi yadda gaba-d'aya ya rame duk saboda ni, ga su Aunty su ma cikin damuwa suke saboda ni, ga ki kema da sauran mutane. A kwanakin nan sai na ji gaba-ɗaya na tsani kaina da rayuwata, amma da nai wani tunani d'azu sai na yi istigfari, na tuna Ubangiji ya bar ni cikin k'oshin lafiya, ga wasu can kwance a gadon asibiti cikin jinya, wanda da zasu ganni na san zasu ce ina ma sune ni yanda nake da lafiyar nan. Rayuwa cike take da k'alubale kala-kala, kuma kowa da irin tasa ƙaddarar, ni kam na karb'i tawa hannu bibbiyu, yanzu addu'a kawai nake Allah ya cire mun son Sadik da tunanin sa daga cikin raina, na san hakan zai rage mun damuwar da nake ciki." Haneefah ta ja gwauron numfashi ta zare hannunta daga cikin na Neehal ta ɗora su akan ƙafarta, cikin confidence ta ce. "Insha Allahu Neehal zaki yi aure da mijin kere sa'a nan ba da jimawa ba, duk wannan k'uncin da kike ciki zai wuce ya zamto tamkar firlm a gare ki." Neehal ta lumshe ido tana jin kamar abun da Haneefah ta faɗa ba zai taɓa tabbata a gare ta ba...........


















******************************








Sabuwar rayuwa Neehal ta buɗe a shafin rayuwarta, a ƙoƙarin ta na ganin ta manta da dukkan abubuwan da suka faru da ita a baya a rayuwarta. Ta yi ƙoƙari sosai wajen cire Sadik daga cikin zuciyarta tare da dagewa da addu'a. Ta koma shiru_shiru a rana bai fi ta furta kalmomin daza a iya irgawa ba. Kafin ka ga murmushi a fuskarta kam za'a daɗe. Alkur'ani da azkar su suka zamto abokan hirar ta, wani lokacin kuma takan taɓa karatun Hausa novels wanda Aunty Sadiya ta tuttura mata dan su ɗebe mata kewa. Tana kuwa jin daɗin karatun littafan sosai. Bata fita ko'ina, saboda a ganin ta tana fita za'a fara nuna ta ana gata nan ita ce duk wanda zata aura sai an kashe shi. Mama da Daddy sun yi sun yi ta koma gurin aikinta amma ta ƙi, da suka takura mata sai ta saka musu kuka, dole suka haqura suka ƙyale ta. Duk wani abu da Mama ta san zai sata farinciki shi take yi, haka zata fita da kanta ta jido mata su sweets wanda ada ita take hanata shan su, amma yanzu duk dan ta yi farinciki take siyo mata. Tun ranar da aka mayar wa da Sadik kayansa gidansu ya turo mata text ɗin ban haquri da nuna mata ba laifinsa ba ne ba su ƙara magana ba. Ahmad ya zo tun cikin week ɗin da ya samu labarin bayyanar Sadik, yay mata murna ya sanar mata bikinsa watan malaudi. Bata sanar masa an fasa bikinsu da Sadik ba dan ta san tsaf zai iya dawowa cikin rayuwarta a matsayin masoyi, ita kuma bata son hakan, ta riga ta cire babin soyayya a rayuwarta. Kuma baza ta so yabar yarinyar da zai aura saboda ita ba, dan ko ita akaywa haka baza ta ji daɗi ba. Ameen kuwa sai ya zo gidan ya tafi ma ba su haɗu ba saboda wunin ɗaki take, babban dalili ne yake fito da ita falo ko ya saukar da ita ƙasa.










Yau ta kama Monday, wanda ya yi dai-dai da wata ɗaya da fasa Auren su da Sadik. A jiya ne kuma ƙawarta Zee ta Bayero ta sanar mata result ɗinsu na last semester is on the corner. Hakan yasa ta shirya yau zata je gurin aikin su, saboda ta ciccike wasu takardu na promotion ɗin da za'ai mata, tunda yanzu zata bar aiki da k'walin Deplomer ne ta koma da na Degree, kafin result ɗin ya fito komai ya yi ready sai ta haɗa ta yi linking ɗinsu. Dama zaman gidan ya fara isar ta, kuma wannan aikin shine gatan ta a duniyar nan, baza ta so ta rasa shi ba.Ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa, ta yi kwalliya sama_sama a ƙoƙarin ta na ganin kar mutane su gane halin damuwar da take ciki. Sai dai a fuska ne kawai ta iya pretended amma damuwar na nan kwance a cikin zuciyarta. Ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, sai ta ga ta rame musamman ta wuya

Please Login or Register in order to submit comment