Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata wasa da Sallah. Ta kira Daddy ta sanar masa Neehal fa bata dawo gida ba, kuma ta kira duk inda take tunanin zata iya zuwa amma an ce bata je ba. A gigice Daddy ya ce gashin nan zuwa gidan yanzu_yanzu. Sai da Mama ta ji ana kiran ishar sannan ta tuna bata yi Magriba ba, ta miƙe cikin sauri ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tayar da Sallah. A kowacce sujjada tana roƙon Allah ya dawo mata da Neehal gida, tana cikin Sallar ta ji anata kiran wayarta. Tana idarwa ta ɗauko wayar cikin addu'ar Allah yasa Neehal ce take kiran ta ko kuma wani da zai ce mata ya ga Neehal ko kuma ya tsince ta, ita a yanda take ji ma ko ce mata aka yi Neehal tana asibiti ta yi accident zata fi jin daɗi fiye da rashin sanin inda take da halin da take ciki. Amma tana dubawa sai ta ga Ameen ne yake kiran ta. Ta yi pick cikin sanyi jiki ta saka wayar a speaker, muryar Ameen ta karede ɗakin da yin sallama a wayar, Mama ta amsa masa cikin raunin murya. Ya ce. "Mum, I saw your missed call, time ɗin ina yin abu, hope dai ba wata matsalar ba ce na ji muryarki with so concern." Sai a lokacin Mama ta ji hawaye masu d'umi sun zubo daga cikin idanunta, muryarta da alamun kuka ta ce. "Ameen! Neehal has missed." A ruɗe Ameen ya ce. "What? Kamar ya?" Mama ta labarta masa abin da yake faruwa. With so concern ya ce mata gashin nan zuwa gidan. Mama ta ajiye wayar tare da rafka tagumi tana hawaye tare da tunane_tunane. Ganin tunanin ba zai kai ta ba ta kira Aunty A'isha da Aunty Sadiya ta sanar musu halin da ake ciki. Ƙarshen rud'ewa su Aunty sun ruɗe, su ma suka sanar da Mama gasu nan zuwa gidan. Ameen ne ya fara zuwa gidan a gigice, ya tarar Mama tana kuka sosai abun da ba zai iya tuna ranar da ya ta yi ba, kasancewar ta mace mai juriya da dauriya. Ya kama hannunta ya ce. "Please Mum stop crying, Insha Allahu za'a gan ta." Mama ta girgiza masa kai cikin kuka ta ce. "Ameen duba time ka gani har tara fa ta kusa, sai yaushe zata dawo? Ina tsoron yarinyar nan kar damuwa tay mata yawa ta yanke shawarar guduwa wani gurin." Ameen ya ce. "Miemerh will never do that I know, tarbiyyar da kikai mata baza ta taɓa yanke shawarar guduwa ba, may be Gombe ta tafi ko kuma Abuja, ko dai wani gurin daban." Mama ta kalle shi cikin sauri ta ce. "Abuja? Gombe? A daren nan zata ɗauki hanya ita kaɗai, amma kuwa idan haka ne yarinyar nan bata kyauta mun ba, ta san hankalina zai tashi sosai, kuma sannan ta kashe wayoyinta." Ameen ya ce. "No Mum, hasashe na ne kawai ba wai na tabbatar da hakan ba, a halin da ake ciki everything will happen." Mama ta sauke gwauron numfashi bata ce komai ba. Ameen ya ce. "Let me check har room, ko zan samu something like jotter da take rubuta Numbers a ciki, sai mu kira Freind's ɗinta da baki da Numbers ɗinsu, mu ji ko suna tare." Mama ta gyaɗa masa kai cikin gamsuwa da shawararsa. A dai-dai lokacin Daddy ya shigo ɗakin a gigice, hankalinsa a matuƙar tashe. Ameen ya gaishe shi amma ko iya amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Mama ƙarin bayanin abun da ya faru. Ameen ya fice dan zuwa bedroom ɗin Neehal, Mama tana ƙara yiwa Daddy bayani tana trying Numbers ɗin Neehal, but still wayar a kashe. Daddy ya shiga maimaita Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un sannan ya ce. "Ina wannan yarinyar ta tafi a dai-dai lokacin da bata cikin normal mood? Bata tunanin wani abun ya faru da ita? Ko dai accident ta yi?" Mama ta ce. "Na yi tunanin haka nima Gen. Amma da haka ne da tuni an kira mu an sanar mana, kusan 4 hours fa da yin wayar mu." Daddy ya jinjina kai with so concern ya ce. "Yanzu zan bayar da cikiyar ta a duk wata kafar sadarwa dake garin nan, sannan kuma zan baza yarana su bi asibiti_asibiti su duba mun ko an kai ta." Mama ta ce. "Allah yasa a dace." Ya ce. "Amin." Tare da zaro wayarsa a aljihu ya shiga kiran mutane.........














Gudu na fitar hankali waɗanda suka ɗauke Neehal suka dinga shararawa akan titi, duk inda suka gilma sai an yi maganar su da irin gudun gangancin da suke yi kamar basa san rayukansu. Tafiya suka yi takai ta mintuna hamsin sannan suka tsaya a wata unguwa mai kama da jeji, saboda babu gidaje sosai kuma tsit take babu mutane. A gaban wani ƙaton gida wanda shi kaɗai ne a layin ba gida gabansa babu a bayansa suka tsaya, suka danna horn, ba jimawa wani buzu da ya sha rawani ya zo ya wangale musu gate ɗin gidan suka kutsa kai ciki. Girman compound ɗin gidan ya ninka na gidan Mama sau biyu saboda girman sa, sai da suka je har bakin ƙofar da zata sada su da ainihin cikin gidan sannan suka yi parking. Wanda yake cikin Motar Neehal ya ɗauki jakarta cikin sauri ya buɗe ya ciro wayoyinta duka ya kashe su, duk da kafin su tafi farautar Neehal sun katse network ɗin gidan, amma saboda tsaro kuma sun san ogansu zai yi magana anjima da Neehal ta waya, to za'a iya dawo da network ɗin akodayaushe shi yasa ya kashe wayoyin nata kamar yadda aka ba shi umarni. Ya buɗe Motar ya fita ya tarar already har ɗan'uwansa ya fita ya tafi buɗe musu kofofin gidan. Ya ciccibi Neehal ita da jakarta kamar wata yaririya ya nufi cikin gidan da ita. Corridor mai ɗan tsayi zaka tarar kana shiga ciki mai ɗauke da k'ofofi a jejjere, sai da suka kusa zuwa ƙarshen sa sannan suka buɗe wata ƙofa suka shiga da Neehal dake kwance tamkar gawa. Madaidaicin d'aki ne da ya ji komai na buƙatar rayuwa, akan k'aton gadon dake ɗakin suka shimfid'e ta. sannan wanda ya ɗauko ta ya kwashe wayoyinta suka fice daga ɗakin suka kulle ta.






Bata farka ba sai kusan goma na dare, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin dumm, ga warin wani abu a hancinta. So take ta tuno inda take da abun da ya faru da ita amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba-ɗaya ta cunkushe ta ƙi yin tunanin da take son tay mata, sai kayataccen ɗakin data gan ta a ciki wanda ya ji komai take bi da kallo, ta dai gane dare ne lokacin duk da wadataccen hasken dake ɗakin. A hankali cikin ikon Allah ƙwaƙwalwarta ta dawo dai-dai, ta fara tariyo mata last thing da ya faru da ita. Ta k'walla razananniyar ƙara tare miƙewa zaune a matuƙar hanzarce ƙirjinta na bugawa a million. Ta sauko daga kan gadon kamar zata kifa tana magana a fili cikin matuƙar rud'ewa da razana. "Ina ne nan? A ina nake? Wa ya kawo ni? Me na zo yi a nan? Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." Ta ƙarashe maganar tare da ɗora hannayenta duka a kanta. Ta fashe da kuka tare da faɗin. "Su waye ku da kuka kawo ni nan? Me nay muku? Me kuke so da ni? Nan kuma ƙaddarata ta kawo ni? Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan, Allah karka ba su ikon cutar da ni." Sai ta nufi gurin da take tabbacin nan ne ƙofar shigowa ta kama handle ɗin ƙofar tana murd'awa da ƙarfi tare da bubbuga ƙofar da ɗayan hannunta tana kuka tana faɗin su zo su mayar da ita gida. Ganin babu alamun akwai ma me jin ta balle ya taimake ta, ta zube a bakin ƙofar tana ƙara volume d'in kukanta. Tana jin zuciyarta kamar zata tarwatse saboda tension, tana jin dama Ubangiji ya zare ranta a yanzu ta huta da wannan masifar da bala'in da yake riskar ta daga wannan sai wannan. Nan kuma ina ne waɗannan mutanen suka kawo ta? Ta d'ago kanta a fili ta ce. "Why Neehal? Why? Me yasa na buɗe my car na yi magana da mutanen nan? Da na yi zama na a cikin Motar har Allah ya taimake ni ya kawo wanda zai iya taimako na, ko kuma Daddy ko one of our staff soldiers sun zo sun kori mutanen. Wanne ganganci ne ya kai ni zuge glass ɗina?" Zuciyarta ta bata amsa da faɗin. 'Tsautsayi da rashin sani.' Tabbas tsautsayi ne wanda ba ya kaucewa ranar sa. Da kuma wata sabuwar ƙaddarar a cikin jerin ƙaddararorin rayuwarta. Jin ana buɗe ƙofar ɗakin ta waje ta tashi da gudu ta nufi kan gadon ta faɗa ta kudundune jikinta guri ɗaya tana cigaba da kukanta. Aka turo ƙofar ɗakin aka shigo aka mayar aka rufe, ɗaya daga cikin wanda suka kawo ta gidan ne, Neehal ta bi shi da kallo da jajajen idonta tsoro mai tsanani na ƙara lullub'e ta, ta ƙara makurewa a jikin gadon bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Abinci ne a hannunsa ya ajiye mata a kan bedside locker, yana duban ta da wani shegen murmushi ya ce. "Ki ci abinci ƴan'mata." A zafafe ta ce. "Ba zan ci ɗin ba, ku mayar da ni gida, me yasa zaku kawo ni nan, ku mayar da ni gurin Mamata, me nay muku? Me kuke so a wajena?" Ta fashe da kuka mai ban tausayi. Bai ce komai ba ya juya da niyyar fita, ta tashi ta biyo shi ta riƙe hannunsa ta fara ihu da ƙarajin ya mayar da ita gida ita dai. Ya hankad'a ta, ta faɗi a ƙasa, kafin ta yi yunƙurin tashi ya buɗe ƙofar ya fice. Ta ƙurawa ƙofar ido kamar idanun nata ne za su buɗe mata ƙofar. Ta tashi da ƙyar ta faɗa kan gado cikin rashin sanin mafita, "Mama." Ta furta a fili. Ta san tana can hankalinta a tashe, tana can cikin damuwar rashin dawowar ta gida. Ta tashi zaune da sauri ta janyo hand bag ɗinta dake tsakiyar gadon ta buɗe da niyyar ɗauko wayoyinta ta kira ta, amma sai ta ga babu ko ɗaya. Ta zazzage jakar hoping ko zata ga wayoyin sun mak'ale a wani gurin, amma kuɗi da earpiece da i.d card ɗinta na gurin aiki ne kawai suka fado. Ta yi cilli da jakar ƙasa ta kuma fashewa da wani sabon kukun, tana ambaton sunan Allah a ranta tare da neman taimakonsa. Tunawa ta yi bata yi Sallah ba hakan yasa ta d'ago kanta, idanunta suka sauka akan agogon bangon dake ɗakin wanda ya nuna sha ɗaya da rabi na dare. Ta miƙe ta sauko kamar zata fadi ta nufi ƙofar da take da tabbacin toilet ne, tana turawa ta ga ta buɗe, kuma kamar yadda ta zata toilet ɗin ne mai matuƙar kyau a tsabtace, ba ta shi take ba abun da ya shigo da ita kawai ta yi ta fito, ta gyara hijabin jikinta ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta rafka tagumi a gurin, tana tunanin ko kidnappers ne suka sace ta, ko kuma gidan masu yankan kai aka kawo ta. Tana nan zaune aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, bata ko motsa ba balle ta d'ago ta kalli mai shigowar, ta fawwalawa Allah komai, ta san duk abun da ya rubuta zai same ta babu makawa sai ya same ta, kuma shi kaɗai ne zai iya kare ta daga dukkan wani sharri da mutanen nan suke nufi da ita. Mutumin d'azu ne ya ƙara dawowa da waya a hannunsa, ya tsugunna a kusa da ita tare da miƙa mata wayar yana faɗin. "Oga zai yi magana da ke." Wata uwar harara ta zabga masa sannan ta ce. "Bazan yi maganar ba, ku mayar da ni gida na faɗa muku, ku kai ni gurin Mamata." Bai ce komai ba ya saka wayar a handsfree, wata murya mai kaushi ta karaɗe kunnen Neehal da dariya, daga baya kuma aka daina dariyar ya fara magana da faɗin. "Fateemah Zahra! Neehal! ƴar Mamanta. Ki kwantar da hankalinki zaki koma gurin Mama nan kusa, amma kafin nan zai mun amshi abun da muka kusa shekara goma muna dakon sa a gurinki, abun da *ƘUNGIYA* Mai daraja take da buƙatar sa shekara da shekaru, abun da bata taɓa shan wahala gurin mallakar wani abu kamar sa ba, yau gashi lokaci ya yi, dama an ce komai nisan dare gari zai waye. Yau ƙungiya tana cikin farincikin da bata taɓa kasancewa a cikin irin sa ba, yau zata kwana tana shan shagalin da murnar mallakar *BUDURCIN NEEHAL.* Tun da ya fara magana babu abun da Neehal ta fahimta sai kalmar virginity ɗinta, ta ji dai yana ambatar ƙungiya. Cikin rud'ewa ta ce. "What? Wacce ƙungiyar? Me kuke so a gurina?" Mutumin ya kuma ƙyalƙyalewa da dariya cikin ƙatuwar muryarsa sannan ya ce. "Zaki gane komai daga daren yau zuwa safiyar gobe, zan so ace ni ne zan ratsa kyakkyawar yarinya ƴar hutu wadda ƙungiya take girmamawa da tattalin budurcin ta, sai dai kash dole sai mamallakin budurcin ne zai amshi abun sa." Zuwa yanzu Neehal ta soma gane inda maganganun sa suka dosa, sun ɗauko ta nan ne domin yi mata fyade akan wata buƙatar su ta banza. Cikin ƙaraji da rashin tsaro ta ce. "Ƙarya kake munafukin Allah, Ubangiji ba zai taɓa baku nasarar cutar da ni ba, mushrikai kawai!" Mutumin ya ƙyalƙyale da wata muguwar dariya sannan ya ce. "Yaro man kaza, yaro baka san wuta ba sai ka taka. Dole a gobe ɗaya cikin ƴan ƙungiya ya mallaki budurcin ki, dole a gobe sarauniya ta sha sperm ɗinki da take ta ƙwadayin shi shekara da shekaru, ƙungiya bata taɓa neman abu ta rasa ba, ki hutawarki ƴan'mata." Daga haka wayar ta yi ɗil alamun an yanke. Neehal ta shiga jujjuya kanta dake barazanar fashewa, ta ɗora hannunta a ƙirjinta da yay mata wani irin nauyi tana ambaton sunan Allah cikin fitar hayyaci. Bata ma san time ɗin da baƙin mutumin nan ya fice daga ɗakin ba. Ta d'au tsawon lokacin da bata san yawansa ba a cikin wannan halin, a hankali cikin Ikon Allah ta fara dawowa cikin nutsuwarta. K'azaman maganganun mutumin da sukay waya na yi mata kuwwa a cikin kanta tamkar yanzu yake faɗa mata, ta shiga auna maganganun nasa a mizanin hankali, idan ta fahimta wannan kungiyar da yake magana akai ta matsafa ce masu asiri dan neman duniya, idan ta fahimta mitumin da suka yi magana ba shi zai amshi budurcin nata ba kamar yadda suke so, wani ne daban wanda ya alaƙanta shi da mamallakin budurcin nata. "To waye wannan?" Ta tambayi kanta a fili, bata da amsa ba kuma ta san inda zata samo ta ba, hakan yasa ta tafi point na gaba. Wanda ya ce kusan shekara goma suna d'akon virginity ɗinta, idan ta fahimta su ne suka kashe su Jameel kenan dan sun san idan ta yi aure zata rabu da abun da suke dakon shi a gurin ta? Me tay musu da zafi haka to suke bibiyar ta da wannan mummunar manufar? Su waye ƴan ƙungiyar da sarauniyar su? A ina suka san ta da har suke son cutar da ita? Tambayoyi barkatai ta shiga yiwa kanta, daga baya ta fara addu'ar kar Allah ya basu ikon cimma mummunan kudirin su a kanta. Sai kuma ta koma tunanin abun da Mama tay ta tambayar ta a cikin kwanakin nan, ko ta taɓa samun saɓani da wani shine yake ta bibiyarta rayuwarta dan ɗaukar fansa, amma kuma ta kasa tunowa tunda babu, bata jin ta taɓa samun babban saɓani da wani a rayuwarta. Ta kawar da wannan tunanin ta koma tunanin samarinta da ba su ji ba, ba su gani ba an kashe su saboda ita, ta tuno Jameel wanda da an yi auransu da tuni yanzu sun yi 6 years da aure yanzu, Anwar kuma 3 years da watanni, sai Sadik da sun kusa wata biyu. Idan har waɗan nan mutanen suka samu nasarar cimma burinsu a Kanta rayuwarta ta zo ƙarshe, bata ga amfanin sauran rayuwarta_ta ba, tunda an raba ta da abu mai kima da martaba da daraja a tare da ita. Ta girgiza kanta tare da addu'ar Allah ya ɗauki ranta kafin safiya, ko ta huta da wannan bala'in. A tak'aice yanda ta ga rana yau haka ta ga dare..........


















Kamar yadda Neehal bata iya runtsawa ba yau haka ma Su Mama ba su runtsa ba, dan Ameen ma sai ɗaya saura na dare ya bar gidan. Tashin hankalin da Mama take ciki ba zai misaltu ba, kwana ta yi tana kuka Daddy da Aunty Sadiya suna kanta suna bata baki, Aunty A'isha kuma tana gefe tana Sallah da roƙon Allah ya kare Neehal a duk inda take. Da yake su Auntie's ɗin a gidan suka kwana ganin halin da Mama take ciki. Jiya har ɗaya na dare suna buge_bugen wayar mutane suna tambaya ko Neehal ta je gurin su, duk wata Number da Neehal ta rubuta a cikin jotter data rubuta Numbers da Ameen ya yi nasarar gani a ɗakinta, ya kira amma babu wanda ya ce ta je gurinsa, kafin ƙarfe goma na daren kuwa cikiyar Neehal ta baza garin Kano kamar yadda Daddy ya bayar da sanarwa a kowacce kafar yaɗa labarai dake garin Kano. Sai da asuba sannan Mama suka kira mutanen Gombe da na Abuja ko Neehal ɗin ta je can, nan ma aka sanar musu bata je ba. Da sassafe Uncle Mahmud ya haɗo Hajiya da driver zuwa Kano wadda ta matuƙar gigice jin ɓatan Neehal, Yayan Dad ma asubanci ya yi ya taho hankali a tashe. Duk gidan ƴan'uwa da kawu Musa yake tunanin Neehal zata je ya kira an ce bata je ba, har Gabasawa sai da ya kira nan ma babu wani labari. Wajen ƙarfe shida Mama ta kira Wayar Uncle Usman ta ji ko Niger ɗin Neehal ta je, ko kuma tana hanyar zuwa idan ta ƙarasa ya kira su ya sanar musu amma sai ta ji wayar tasa bata shiga. Ta kira Haneefah ko Kogin Neehal ta je amma Ita ma ta ce bata zo ba. Idan ka ga Mama sai ka tausaya mata ko ka zubar mata da k'walla, saboda yanda duk ta fita hayyacinta lokaci ɗaya. Ƙarfe bakwai na safe Daddy ya bar gidan dan zuwa Hospital's da kansa duba Neehal, gani yake kamar yaran da ya saka aikin basa dubawa da kyau shi yasa tun jiya har yau ba'a gan ta ba..........














Neehal tana rakub'e a gurin da ta yi Sallar Asuba har gari ya waye, ta rafka tagumi tana jiran ganin ikon Allah, bata taɓa riskar ranar data tsinci kanta a cikin tsoro da fargaba irin na yau ba, ta sadaqar ta karaya yau sai yanda Allah ya yi da ita tunda ya nufa ta wayi garin yau da ranta, ita kaɗai a cikin wannan gida tare da waɗannan azzaluman mutanen ai sai yanda suka yi da ita, amma bata daina addu'ar neman ɗauki a gurin Ubangijin ta ba. Wajen ƙarfe takwas aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta runtse idanta cikin matsananciyar fad'uwar gaba da murd'awar ciki, a hankali ta ce. "Shikenan, sun zo ida mummunan baƙin nufinsu a kaina, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe." Jin an ajiye abu a gabanta yasa ta buɗe ido tare da d'ago kanta zuciyarta fal tsoro, wani farin saurayi ta gani tsaye yana kallon ta, gabanta kuma tire ne mai ɗauke da abinci, da alamun shi ya ajiye mata. Hawaye ya taru a cikin idonta ta fara kuka ta ce masa. "Fuskarka bata yi kala data masu cutarwa ba, ta yi kala data masu imani, dan Allah bawan Allah ka fitar da ni daga gidan nan kafin su gurɓata mun rayuwata, ni marainiya ce bani da kowa sai Allah, ka taimake ni dan Allah, na san baza ka so a wayi gari ka ga an ɓata rayuwar ƙanwarka ba, to ka ɗauke ni kamar haka ka fitar da ni daga gidan nan." Saurayin ya lumshe ido a hankali ya buɗe, kamar zai yi magana sai ya tuna ba'a ba su umarnin hakan ba, kuma akwai CCTV camera a ɗakin, sai ya juya cikin wani irin yanayi ya fice daga ɗakin. Neehal ta fashe kuka tare da saka ƙafa ta yi ball da abincin gabanta. Cikin kukan take faɗin. "Yaya where are you? Ka zo ka fitar da ni daga gidan nan kar su cutar da ni, kar su yi abun da zai sa zuciyar Mama ta buga, Daddy......." Haka ta dinga kiran sunan duk wani makusancinta tare da neman taimakon su, abun tausayi ta zama kamar wata zararriya. Ƙarfe goma saura wasu maza majiya ƙarfi guda biyu suka shigo ɗakin, Neehal ta tashi da gudu ta haye kan gado ta koma can ƙarshen gadon ta takure jikinta dake karkarwa kamar ana kad'a mata mazari. Gifd'a_gifd'an mutanen nan guda biyu suka bi ta gadon suka kamo ta tana ihun su sake ta har su kai ta inda za'a *keta mata haddi* amma kamar da dutse take magana abun da aka saka su kawai sukay. Fitar da ita suka yi daga ɗakin, wata ƙofa dake ƙarshen corridor ɗin gidan suka buɗe suka shiga, steps ɗin bene ne ya bayyana suka fara hawa da ita. K'ofofi uku ne a upstairs ɗin da suka hau, ta farko suka buɗe suka tura ta tana tirjewa sannan suka ja ƙofar suka fice. Ta d'ago kanta ta kalli mutumin dake tsaye a gaban gado yana saka face maks ta bogi a fuskarsa, sai dai kafin ya gama zirawa ta ga ainihin fuskar tasa, kuma ta gane shi. Ta miƙe cikin matuƙar dimaucewa daga fad'uwar da ta yi lokacin da mutanen nan suka yarda da ita. Dai-dai lokacin mutumin ya gama saka fake face maks ɗin, suka haɗa ido da shi ta cikin face maks ɗin da ya saka. Ko a cikin magagin bacci take ta ga mutumin nan sai ta gane shi, ko makancewa ta yi ta shafa fuskarsa sai ta gane shi, tsayuwarsa da siffar jikinsa kaɗai idan ta gani sai ta gane shi ko da ya juya mata baya ne, ko a cikin duhu ne, balle yanzu da yake tsaye a gabanta cikin haske suna pacing ɗin juna, ba fuskar bogi ba ko jikinsa duka ya ɓoye a cikin kayan ƙarfe sai ta gane shi, balle kuma ta riga ta ga fuskarsa ba tare da ya sani ba, ga kuma k'amshinsa da ba baƙo ba ne a gurin ta da ya mamaye ɗakin. Amma ita duk ba wannan ne damuwarta ba, damuwarta me ya kawo shi gidan? Me yake yi a cikin gidan da ake ƙoƙarin keta mata haddi? Me yasa k'artan mazan can suka kawo ta inda yake? Ko shine wanda mutumin da suka yi waya jiya ya ce zai aiwatar da mummunan ƙudirinsu a kanta? Ta d'aga hannunta dake karkarwa kamar an jona masa shock da ƙyar kamar yadda zuciyarta take fat fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta nuna shi, cikin rawar murya numfashinta na fita da ƙyar kamar ana zarar ranta ta ce. "Ya..........✍️




(😭🙄 *Neehal wa kika gani ne!?* )


















*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣6️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














...........Sai kusan ƙarfe goma na dare Daddy ya dawo gidan, Yana cikin cire kaya Mama ta shigo ɗakinsa. Ta zauna akan stoll tana duban shi ta ce. "Daddy yau ina ka je ka daɗe haka? Gashi ina ta kiran wayarka bata shiga?" Daddy ya ce. "Au har kin manta inda na ce miki zan je da safe kenan?" Mama ta ce. "Sorry na sha'afa, sannu da zuwa da fatan kun dawo lafiya kuma an dace da abun da aka je nema?" Daddy ya ce. "An dace

Please Login or Register in order to submit comment