Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kullum masoyan mu a shirye kuke da ganin labaranmu, nasan ba zaku bamu kunya ba, zaku iya biyan naku ta hanyar👇🏾_


*GUDA ƊAYA 300*
*GUDA BIYU 500*
*GUDA UKU 600*
*GUDA HUƊU 800*


ACCT NO: 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK


EVEDANCE OF PAYMENT
0814 210 5218


MASU TURA KATI KUMA SU TURA TA NAN👇🏾
0816 788 8934


GA MUTANAN NIGER KUMA SUYI MAGANA TA NAN👇🏾
+227 96 51 58 05


💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽Mun shirya tsaf domin sanya zuƙatan masoyan mu farin ciki, Muna fatan zaku fara bibiyar FITATTU HUƊU tun a ZAGON FARKO👏🏻😍.


Dan Allah share fisabilillahi Habibaties👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻.






FITATTU HUƊU ✍🏾




*Team fittattu huɗu*🥰
















............Misalin k'arfe hud'u da mintuna na yamma Neehal ce ke shiryawa a bedroom d'in Mama saboda d'akinta cike yake da bak'i 'yanmata, sauri take ta yi ta gama shirin nata saboda su Haneefah dake jiranta za su gurin kwalliya. Doguwar rigar abaya ta zira ta d'ora hijabi akai, turarukanta masu sanyin k'amshi ta feshe jikinta da shi, tana gama shiryawa wayarta dake kan mudubi ta fara vibrate, d'auka ta yi ta duba ta ga Ameen ne yake kiranta, a fili ta furta "Yaya kuma?" Kafin ta d'aga wayar ganin tana k'ok'arin tsinkewa ta kara a kunnenta bakinta d'auke da sallama. Ameen ya amsa mata ya k'ara da fad'in, "Ki kawo mun coffe part d'ina yanzu." Neehal ta ce "Ok gani nan." Kamar za ta yi kuka ta yi maganar, domin a haka ma tasan sai ta sha jarabar su Haneefah na jiranta da suke, gashi Yayan nata ya k'ara tsayar da ita, zata k'ara b'ata musu time. Fitowa ta yi daga d'akin ta shiga d'an k'aramin kitchen d'in dake saman wanda ba su fiya amfani da shi ba dan dafa masa coffee d'in.








Cikin mintuna qalilan ta gama had'a masa coffee ɗin, kafin ta gama ta window'n kitchen d'in ta hango Haneefah ta zo ta shiga d'akin Mama fuskar nan tata a cukule, ta san bayanta ta biyo. Bayan ta juye masa a k'aramin tea flaks ta d'auka ta nufi part d'in nasa tana ta sauri. Da sallama ta shiga falonsa bayan ta k'arasa, ba ya falon sai k'amshinsa kawai ke tashi a ciki, bedroom d'in sa ta nufa ta tsaya a bakin qofa ta fara knocking, mintuna biyu ya bud'e qofar tare da tsayawa yana kallonta. Neehal ba tare da ta kalle shi ba ta mik'a masa flaks d'in, cikin d'akin ya koma yana fad'in "Kika sake sa ya fad'i ya zube wani zaki sake had'awa." Neehal ta d'ago tana duban bayansa tare da turo bakinta gaba, shiga d'akin ta yi ta ajiye masa a kan bedside, ta juya zata fita ta tsinkayi muryarshi yana fad'in ta d'auko masa cup, ba tare data amsa masa ba ta je ta d'auko masa ta dire, zata kuma fita ya ce ta zuba masa coffe d'in a cikin cup, Neehal kamar ta zunduma ihu dan takaicin tsaida ta da Ameen yake gashi har 5 ta kusa, gashi Haneefah tana ta kiranta a waya, zuba masa ta yi ta mik'a masa, ya karb'a yana bin hannunta da ya sha jan lalle da kallo, lallen ya kama ya yi kyau gwanin sha'awa. "Ki jira ni a falo." Ya fad'a cikin had'e rai, Neehal ta marairaice ta ce "Yaya gurin kwalliya za mu tafi fa, su Haneefah na jiran...." Wani kallo ya watsa mata wanda yasa ba shiri ta had'iye sauran managarta ta juya ta nufi qofa ta fice daga d'akin. Tana fita kiran Haneefah na k'ara shigowa cikin wayarta, sai da ta zauna a kan kujera sannan ta d'aga wayar, cikin k'ufula Haneefah ta ce "Wai Neehal ina kika shiga ne tun d'azu inata neman ki amma ban ganki ba, kuma kin san jiran ki muke fa amma kika shanya mu, idan ba za ki taho ba mu za mu yi tafiyarmu." Neehal ta ce "Ki yi hak'uri Haneefah Yaya ne ya kira ni ina part d'in shi." Haneefah ta ce "Yaya kuma? Me kike masa toh?" Neehal ta ce "Coffe na had'o masa, yanzu kuma ya ce na jirashi a falo ban san me zai kuma sani ba." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka, Haneefah ta ce "Yanzu dai kinga 5 ta kusa, kuma muna da yawa wad'anda za'ayiwa make up d'innan, bana so mu yi late a gurin zuwa dinner nan." Neehal ta ce "Idan 5 d'in ta yi ku wuce kawai zan taho ni kad'ai ko'a Napep ne." Haneefah ta ce "Shikenan." Tare da katse wayar. Neehal tana zaune a falo Ameen ya shanya ta, har k'arfe biyar ta wuce, su Haneefah sunyi wucewarsu gurin kwalliyar, gashi dinner d'in k'arfe bakwai na dare ne, kuma bata son ta yi African time.








Ameen bai fito daga dakinshi ba sai da 6 ta wuce, zuwa lokacin Neehal harta fara hawaye, gashi Haneefah nata kiranta ita har angama mata make up d'inta, kuma kayan da zata saka yana gurin Haneefah ta tafi da shi a had'e da nata, da sai ta hak'ura da kwalliyar ta zira kayanta kawai ta tafi, get past d'inta ma dana Sadik duk yana hannun Haneefan." K'amshi turarensa da ta ji ya k'ara cika mata hanci shi yasa ta d'agowa da sauri ta kalle shi, shima ita d'in yake kallo hakan yasa suka had'a Ido, Neehal ta d'auke idanta da sauri tana yaba tsananin kyawun da ya yi a cikin zuciyarta, ya fito sak angonsa cikin dakakkiyar shadda mai tsadar gaske sky blue wadda aka maka aiki da Kalar Royal blue, tunda Neehal take ba zata iya tuno ranar da ta ganshi da hula ba a rayuwarta, domin shi mutum ne ma'abocin saka k'ananun kaya, idan ka ganshi da manyan kaya Juma'a ce ko kuma Sallah ko kuma idan za shi d'aurin aure, kuma suna masa kyau sosai idan ya saka, yau kam gashi harda babban riga (Malin_Malin) a kan kayan. Kiran shi ake tayi a waya amma ya k'i picking, Neehal kanta na k'asa ta ce "Yaya dan Allah ka barni in tafi, su Haneefah fa har an gama musu kwalliyar za su tafi ni kaɗai na rage." Ameen ya mata banza tamkar ba da shi take ba, tsadadden agogon hannunsa kawai ya kalla sannan ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon ya shiga latsa wayarsa hankali kwance. Sosai ran Neehal ya b'aci a kan abunda Ameen ya mata, haka kawai ya tsaidata kuma babu abunda zata masa, ita kuma bai barta ta je ta yi uxurin gabanta ba. Kiran Sadik ne ya shigo wayarta domin sun yi da shi zai d'auko su daga gurin kwalliyar ya kaisu gurin bikin, ba ta san me zata fad'a masa ba, shi yasa ta k'i d'aga wayar ta barta harta gaji ta katse.






6:30 pm, Ameen ya mik'e ya dubi Neehal dake ta hawaye ya ce "Tashi mu je." Fuskarsa babu walwala ko kad'an ya yi maganar, Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan k'aya ta yi gaba, sai da ya kulle qofar part d'in sannan ya bi bayanta, har ta nufi part Mama ya tsayar da ita Neehal ta tsaya cike da mamakinsa gami da tsoro, domin ta kasa gane me yake nufi da ita, bayan zaman banzan daya sa tayi na fiye da awa ɗaya bai ishe shi ba sai ya k'ara tsayar da ita, to me yake nufi da ita ne? Gurin bikin ne baya son taje ko kuma me?" Dan ita zuwa yanzu ta hak'ura da kwalliyar kayanta kawai take so taje ta saka ta tafi tunda lokaci ya k'ure, gashi Sadik sai kiranta yake a waya ta k'i d'agawa, tafi son sai taje gurin kwalliyar sai ta kira shi ya je ya d'auke ta su wuce. Ameen ya nufi parking space bayan ya mata alamar ta biyo shi, harabar gidan Neehal ta kalla taga duk babu mutane an tafi gurin kwalliya wasuma sun fara tafiya gurin bikin. Bata da zab'i wanda ya wuce bin nasa, Motarsa ya shiga mazaunin driver, hakan yasa ita kuma ta shiga gurin mai zaman banza ta zauna zuciyarta na mata k'una, tana rufe murfin Motar ta fashe da kuka, Ameen ya dube ta da sauri ya ce "Me ne haka?" Neehal cikin kuka ta ce "Yaya wai me kake so na maka ne kake ta tsaida ni? alhalin kafi kowa sanin inda za ni, ga mutane suna ta jira na, kasan Mama ma Idan tasan ina gida har yanzu sai ta yi fad'a." Ameen ya tab'e bakinsa bai ce komai ba, yay wa Motar key suka fice daga gidan. Neehal ta cigaba da kukanta, a d'an fusace ya dube ta ya ce "Kar na k'ara jin kukan nan, yana cika mun kunne." Yanayin yanda yay maganar yasa Neehal ba shiri ta had'iye kukanta, Handkerchief d'insa ya zaro daga aljihu ya mik'a mata tare da fad'in "Share hawayenki, kuma kar na k'ara ganin ko d'igonsu." Ba musu Neehal ta karb'a ta share hawayen ta ci gaba da kukan zuci. Tafiyar mintuna k'alilin suka yi ya faka a gaban wani shago, wayarsa ya d'auka ya yi kira, mintuna uku wata matashiyar mata ta fito fuskarta d'auke da fara'a, Ameen ya zuge glass d'in Motar bayan ta qaraso suka gaisa tana tsokanarsa da ango ka sha k'amshi, nuna mata Neehal wadda idanunta ke lumshe ya yi ya ce "Gata nan, sai ki yi sauri please dan time ya qure." Matar ta yi murmushi ta ce "Kai dama wa ya fad'a maka sai i'yanzu ake zuwa make up? ai tun rana ake zuwa." Neehal wadda ta yi dif kamar bata Motar ta bud'e idanta da sauri jin an ambaci make up Tana kallon Matar, a hankali ta sauke numfashi ta ce "Ina yini." Matar ta amsa fuskarta d'auke da fara'a, ta k'ara da fad'in "Kai Masha Allah qanwar taka kuma kyakkyawa da ita, harma ta so ta fi ka kyau." Ameen ya yi murmushi kawai ya juyo da dubansa ga Neehal ya ce "Ki je ta miki, inanan ina jiran ki." Neehal ta ce "Amma Yaya kayana fa suna gurin Haneefah." Yana latsa wayarsa da ake ta kira ya ce "Zan kawo miki wasu." Neehal ta waro Ido ta ce "Yaya wasu kayan kuma? Anko ne fa wanda zan saka, kenan ni daban zan tashi?" A ɗan hasale ya ce"Kin san bana son musu ko?" Neehal ta turo Baki gaba cikin qoqarin maida hawayen da ya tarar mata a Ido ta bud'e Motar ta bi bayan Matar wadda ta koma cikin shagon nata tun sanda Ameen suka fara magana da Neehal. Ameen ya bita da kallo harta shige shagon sannan ya ja Motarsa ya tafi dan zuwa masallaci jin an fara kiran Sallah. Neehal ma sai da ta yi Sallah tukunna aka fara mata make up d'in, zuwa lokacin wayarta ta gaji da shan kiran Haneefah da Sadik harda ma da Mama. Matar da kanta ta yi wa Neehal kwalliya, sab'anin wasu a shagon da yaranta ne suke musu, gata da sauri cikin abun da bai wuce 40 minutes ba ta tsantsarawa Neehal kwalliya irin light d'innan amma ta yi masifar kyau, kowa dake shagon sai da ya furta "Wow, Masha Allah." Har wasu na tambayar ko Neehal amarya ce? Matar na ba su amsa da fad'in "K'anwar wani class mate d'inta ce da suka yi Secondary school, auransa ake shine ya kawo ta, ta yi mata kwalliya." Bayan kammalawa Neehal kwalliyar ta kira Ameen a kan ya kawo mata kayan Neehal, ya shaida mata ta fito bakin shagon ta karb'a. Neehal ta cika da mamaki ba kad'an ba ganin kayan da Ameen ya kawo mata ta saka, wata had'ad'd'iyar wedding gown ce sky blu, sai head Royal blue da takalmi da su sark'a harda pos wanda duk bata san da su ba, babu b'ata lokaci ta zira kayan me make up ta kafa mata had'ad'd'en d'aurin da ake yayi, nan fa Neehal ta qara fitowa bayan ta gama shiryawa tsaf, babu ta yanda za a yi ka ce ba amarya ba ce, matar ta ba ta turaruka masu sanyi da dad'in k'amshi ta feshe jikinta da shi. Neehal ta kasa d'auke idanunta saga kan mudubi saboda ganin kyawun da ta yi, sai tambayar kanta take a ranta tana fad'in "Ashe make up zai mata kyau sosai irin haka?" Matar ta mata pictures a wayarta sannan suka fito, dan itama matar zata je bikin, Ameen ya yi invited d'inta. Tunda suka fito Ameen ya kafe Neehal da Ido, ganin wani irin sihirtaccen kyau da ta yi, tana tafe tana faman rik'e Riga saboda jan k'asar da take ta baya, duk da kuwa takalmin k'afarta yana da tsini. Neehal ta bud'e front seat ta shiga, Matar kuwa ta shiga baya, zuciyar Neehal cike take fal da tarin tambayoyi ga Ameen, akan hanata zuwa gurin kwalliyar da ta yi niyya da ya yi, ya kawota wani wajen daban, sannan kuma ya bata wasu kayan daban wanda suka yi colour d'aya da nashi, Amma dole tabar tarin tambayoyinta a ranta saboda ba su kad'ai ba ne a Motar kuma ba taga fuskar hakan a gurin shi ba dan tana shigowa ya wani tsare gida.








Wurin biki ya cika ya tumbutsa da 'yan'uwa da abokan arziqi, anata cashewa amma har takwas na dare ta yi amarya da ango ba su qaraso ba. Haneefah kuwa tana gurin ne kawai amma hankalinta gabad'aya yana gurin Neehal, gashi sai kiranta take a waya ba ta d'auka, Sadik ma ya zo ya fi mintu talatin a harabar gurin, ganin Neehal ba ta zo ba kuma yana ta kiranta ta qi d'auka sai kawai ya tafi, kuma bai yi tunanin kiran Haneefah ya ji ko suna tare ba. Amarya Hafsat kuwa da tawagarta sun dad'e da qarasowa gurin, ango kawai take jira su shiga cikin gurin, ranta idan ya yi dubu ya b'aci saboda kiran Ameen da take ta yi amma ya k'i d'auka, gashi bata san me ya tsayar da shi ba ya qi qarasowa gurin har wannan lokacin, har ta gaji da d'adin bakin da abokanan Ameen suke mata na fad'in ya kusa qarasowa. Fadeelah dake zaune gefenta a bayan Motar da suka zo ta dube ta ta ce "Ki qara kiran Al'ameen ki ji wai yana ina ne har yanzu be ƙaraso ba?" Hafsat da ranta ya kai qololuwar b'aci ta ce "Sau dubu nawa zan kira shi yana qin d'aga mun waya Fadeelah? ni na gaji da kiran shi, Idan aka qara wasu mintinan bai zo ba zan koma gida ne kawai, haba wannan ai wulaqanci ne." Kafin Fadeelah ta kuma cewa wani abu wani abokin ango mai suna Salman ya leqo ta glass ɗin Motar yana faɗin "Ranki ya daɗe angon naki ya ƙaraso ki fito." Hafsat ta saki ajiyar zuciya tare da gyad'a masa kai. Neehal kuwa yana parking Motar ta yunƙura za ta buɗe murfin Motar ta fito amma sai ta ji ya riƙe hannunta, ta juyo tana kallon shi cikin tsananin mamaki sai ta ga ya ɗauke kansa, sai da matar da ta yiwa Neehal make up ta fita daga cikin Motar sannan shima ya fito bayan ya sakar wa Neehal hannun, bai bi takan abokansa da suke ƙoƙarin cinye shi d'anye ba na rashin zuwansa da wuri ba ya zagaya ya buɗe wa Neehal Motar, a hankali ta ziro k'afarta ta fito cikin tsananin mamakin Ameen da ya kusan kashe ta da shi na abubuwan da yake mata a yau kamar ba shi ba, dai_dai lokacin itama Hafsat an buɗe mata Mota ta fito, akan idonta Ameen ya buɗe wa Neehal Mota.............✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:39] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_








*1️⃣8️⃣*












*JERIN LITATTAFAN ELEGANT ONLINE WRITERS MAI TAKEN ELEGANT 5STARS* ✨🔥


*IDAN ZUCIYA TAYI WAKE*- Meerah
*TUGGU BIYU*-diamond Aleesha
*ZUBAR HAWAYE*-Gimbiya Ayush
*MATA A YAU*-Aphserteen khairee
*NIHLA*-Mammy Kabeer


Akan farashi mai sauki
5_500
4_400
3_300
2_200
1_150


Zakuyi payment d'inku ta 0623151889 AISHA NURA MURTALA GT BANK sai evidence of payment ta wannan no 08148360851
Kati waya na MTN 09067211352


SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA 🤝🏻












...........A razane Hafsat take kallon Ameen cikin tsananin mamakinsa, wani irin baƙin ciki na mamaye zuciyarta. Tunanika da yawa ne suka ziyarci zuciyarta a wannan lokacin, "Kenan Ameen jiran yarinyar nan mai kama da aljanu ya tsaya shi yasa bai zo da wuri ba? Kan uba! Dress ma colour ɗaya suka yi?" Hafsat ta faɗi haka a fili cikin tsananin kaɗuwa da takaici. Fadeelah ta dafa ta cikin rarrashi ta ce "Calm down Hafsat, dan Allah kar ki nuna ɓacin ranki a dai_dai wannan lokacin, yau ranarku ce kar ki yi abinda zaki zo kina da na sani, nasan abun da ciwo amma ki ɗaure." Hafsat ta yiwa Fadeelah wani kallo tare da yin ƙwafa cikin takaici amma ba ta ce ba komai ba,wata irin tsanar Neehal na ƙara cika mata zuciya.






Neehal kuwa tana gama fitowa daga Motar ta dubi Ameen ta ce "Thank you." Ameen dake kallonta kamar zai cinye ta ya ce "Jira ni anan, kar ki je ko'ina." Bai jira amsarta ba ya nufi gurin Hafsat ya barta da baki a sake. Fadeelah ta sakar masa murmushi bayan ya ƙarasa inda suke tana faɗin, "Haba Ango ya zaka mana haka, gaskiya mun yi fushi." Ameen yana duban Hafsat wadda ta haɗe rai tare da ɗauke kai ya ce "Afuwan." Fadeelah ta yi murmushi kawai tare da matsawa ta koma gurin sauran ƙawayensu. Ameen ya kama hannun Hafsat ya ce "Ba magana." Hafsat ta d'ago ta kalle shi ba ta ce komai ba sai ƙura masa ido da ta yi ganin irin kyawun da ya mata, a hankali ta ce "Ka yi kyau sosai." Ya kashe mata ido tare da faɗin "Ke ma haka amaryata." Hafsat ta saki murmushi cikin tsananin farin ciki, gaba-d'aya ɓacin ranta ta neme shi ta rasa kasancewar Ameen a kusa da ita, dan sosai take farin ciki da Allah ya cika mata burinta na mallakar Ameen a matsayin miji. Neehal dake kallonsu ta tab'e baki tare da maida dubanta a kan wayarta, lalubo Numbern Sadik ta yi ta danna dialing. A lokacin ne kuma mutane suka fara zuwa inda Ameen da Hafsat suke suna ɗaukar su a hoto, Neehal dai bata motsa daga inda take ba takaicin Ameen ya kusa kashe ta na tsayar da ita da ya yi, gashi ta kira layin Sadik har sau biyu bai ɗauka ba, kiran Haneefah ta yi ringing uku ta d'aga, hayaniyar gurin yasa Neehal bata jinta sosai hakan yasa ta katse wayar. Haneefah ta fito daga cikin hall ɗin zuwa harabar gurin sannan ta kira Neehal, Neehal ta d'aga da sauri ta kara wayar a kunnenta. Haneefah ta ce "Wai ina kika tsaya ne Neehal? Tun d'azu nake ta baza ido ko zan ga kin shigo amma shiru, kuma na kikkira ki baki ɗauka ba." Neehal ta sauke numfashi ta ce "I'm sorry sai yanzu na ƙaraso ne." "Kina ina?" Haneefah ta tambaye ta cikin zak'uwa, Neehal ta ce "Ina harabar gurin tare da Yaya." Haneefah ta ɗan kalli gabanta inda take hango mutane ta ce "Gurin da nake hango mutane?" Neehal ta ce "Eh." Haneefah ta ƙaraso gurin tana duba Neehal, Neehal ta hango ta ta je kusa da ita tare da dafata tana faɗin "Ga ni nan fa." Haneefah ta juyo amma ta gaza cewa komai sai bin Neehal da ido kawai take ganin kayan dake jikinta da kuma irin kyawun da ta yi. Neehal ta ce "Ya dai, wannan kallon fa?" Haneefah ta ce "Na mamaki ne sai kuma kyawun da kika yi kamar ke ce amaryar, amma yana ga kin saka wasu kayan ba irin namu ba." Neehal ta shagwab'e fuska ta ce "Rigimar Yaya mana." Ta kwashe duk yadda suka yi da shi ta faɗa wa Haneefah a tak'aice. Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kuma wallahi kin yi kyau sosai, make up ɗin naki ma ya fi namu kyau." Neehal ta ce "Kuma takun ta yi kyau, ina su Ameera fa?" Haneefah ta ce "Suna ciki suna cashewa, nikam tunda na zo ko rawar ban yi ba, hankalina yana kan ki, musamman da kayan ki suke wurina, har fa Mama sai da na kira na faɗa mata, shima Yayan na kira shi bai ɗauka ba." Neehal ta ce "Shi yasa na ga missed call ɗin Mama." Haneefah ta ja hannun Neehal tana faɗin "Zo mu shiga ciki, kafin su amarya su shigo." Neehal ta kalli inda su Ameen suke ta ga anyi arranged ƙawayen Amarya da Abokanan Ango, domin shiga wurin. Ameen duk abun da ake hankalinsa na gun Neehal da ya tsaida ta, domin so yake su shiga gurin tare, amma suna zuwa inda ya barta ya neme ta ya rasa. A cikin halla kowa ya zazzauna filin rawa ma babu kowa, sai Mc dake ta karaɗin isowar ango da Amarya. Neehal kuwa gurin cousins ɗinta suka nufa, tana zuwa kowa ya fara yaba kyawun da ta yi, hotuna suka shiga ɗauka kowa yana so ya yi da ita. A nutse ƙawayen Amarya suka fara shigowa suna ɗan rausayawa abun gwanin sha'awa, nan fa mutane suka mik'ewa suna video a wayoyinsu, ga masu Camara ma nata fama ko ta ina, shigowar Ango da Amarya aka sauya sauti zuwa wak'ar masoya, a hankali suke tafiya har suka ƙarasa mazauninsu. Nan fa wurin ya fara cika da jama'a kowa yana so ya ɗauke su a hoto, da ƙyar Mc ya samu mutane suka ragu. Amarya da ango sun yi kyau sosai, abu ɗaya ne ya musu cikas rashin dacewar kalar kayansu, dan ita Hafsat gown ɗin jikinta purple colour ce. Hafsat har ta gaji da ciwon bakin da ƙawayenta suke mata akan me yasa ba su saka kaya kala ɗaya ba ita da Ameen? Itama ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan, kuma ta tambayi Ameen ɗin tun kafin yau amma bai faɗa mata kalar kayan da zai saka ba. Neehal tana zaune dan su ba su tashi ba saboda cikowar mutane, ji ta yi kamar wayarta tana vibrate tana dubawa ta ga Ameen ne ke kiranta. Da mamaki ta ce "Yaya kuma, yana high table amma yana kira na, to me zan masa?" Haneefah dake gefen ta ta kama hannunta ta ce "Taso mu je, sai a mana hotuna ma da su." Neehal ba dan ta so ba ta mike tana faman riƙe riga suka je. Ta zauna a gefen Ameen Haneefah kuma ta zauna a gefen Hafsat aka ɗauke su a hoto, Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya na ga ka kira ni." Ameen ya harare ta ya ce "Me na ce miki?" Neehal ta ɗan turo baki gaba ta ce "To ai na ga shigowa za ku yi shiyasa kawai na taho." Duk maganganun da suke masu ɗaukar hoto nata musu ba tare da sun sani ba, domin sai suka zama tamkar suke Ango da Amaryar. Neehal ta tashi ta zagaya bayan kujerar da suke ta ɗan sunkuya tsakanin Hafsat da Ameen ta ce "Aunty ina yini." Hafsat ta saci kallon Ameen ta ga ita yake kallo hakan yasa ta ɗan saki fuska ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta ce "Ya taro." ta ce "Alhamdulillah." Kusa da ita Neehal ta je ta zauna ta ɗan rungumo ta aka musu hoto, Hafsat kuwa ji ta yi tamkar Neehal wuta ta sa mata a jikinta da ta taɓa ta.






An cigaba da gudanar da shagalin biki yanda ya kamata, Amarya da Ango sun fito tsakiyar fili anata zuba musu lik'i. Neehal ma ta yi liƙi da kuɗin da Ameen yasa wani abokinsa ya bata bandir ɗin 200. Neehal tana gurin bikin ne amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin Sadik, sai kiran shi take amma ba ya picking. Mama ma ta zo gurin ita da tawagarta ta yi kyau sosai cikin wani haddadden less kalar orange and black, Maman Hafsat ma ta zo. Neehal da taje yiwa Mama lik'i Maman tai ta kallonta cike da mamakin kayan da ta gani a jikinta, amma bata mata magana ba, kuma ko shakka ba ta yi tasan duk shirin Ameen ne wannan.






Ƙarfe 9:30pm Neehal ta ja Haneefah gefe cikin damuwa ta ce "Besty Ina ta kiran Ya Sadik ba ya picking, Allah ya sa lafiya." Haneefah ta ce "Nima tun d'azu nake son na ce miki banga Ya Sadik ba, amma bari na kira shi na ji." Neehal ta ce "Ya kikkira ni fa, time ɗin

Please Login or Register in order to submit comment