Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a daf da ita cikin sanyin murya tare da marairaicewa ya ce "Please Aunty stop crying." Neehal ta d'ago kanta da sauri tare juyowa a tsorace dan ba ta ji shigowar sa ba, sai maganarsa kawai ta ji. Ta ɗan ja baya tare da kallonsa cikin mamakin ƙarfin hankalinsa na shigo mata har cikin daki. Ya marairaice fuska kamar ƙaramin yaro tare yi mata alamar rok'o da hannunsa. Ta tsaida kukan da take cikin jan numfashi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye, hannu ya zira a aljihun wandonsa ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya miƙa mata, ta karb'a ba tare da ta ce komai ba, ta shiga share hawayen fuskarta. Wani sassayan k'amshi ya daki hancinta wanda yasa ta sakin ajiyar zuciya ba tare da ta shirya ba tare da lumshe idanunta. "Princesss!" Ya faɗa murya ƙasa_ƙasa tare da jan sunan, buɗe idonta ta yi da sauri ta sauke su akan fuskarsa cikin nazartar wani abu. 'Princess?' ta maimaita sunan a ranta kamar mai son tuno wani abu, kusancin da suka samu a yanzu yasa ta samu damar ƙarewa fuskarsa kallo sosai, sai ta ga kamar ta san fuskar, amma ta rasa a ina ta santa, ko kuma dan yana kama da su Afrah ne shi yasa. Ta kawar da kanta da sauri ganin yanda yake sakar mata wani murmushi wanda yake ƙoƙarin zautar da zuciyarta. 'He is Handsome.' ta faɗa a ranta tare da miƙewa tsaye da sauri kamar wadda aka tsikara, shima miƙewar ya yi still idanunsa na kanta. Ba tare da ta kalle shi ba ta miƙa masa hancky ɗinsa tare da faɗin "Thank you." Ya karɓa tare da faɗin "You are welcome, and I want to talk to you." Da sauri ta kalle shi ta ce "Ni kuma." Ya gyaɗa mata kai, ta ce "Okay ina jinka." Ya ɗan ja numfashi sannan ya fara magan "Tun d'azu nake son na miki godiya akan tsintar yarana da kikai a titi kika ɗauke su ba tare da ƙyama ko tsoron wani abu ba, and....." "Kar ka damu ai yiwa kai ne." Ta katse shi da faɗin haka. Ya yi murmushi ya ce "Duk da haka ba kowa ne zai iya abun da kika kai ba, hakan ya nuna kina da kyakkyawar zuciya mai cike da tausayi da jin ƙai. Allah ya biya ki ya albarkaci rayuwarki, ya yaye miki duk wani abu da yake damunki a cikin rayuwarki, ya yi miki tukuci da gidan Aljanna." Cikin jin daɗin addu'arsa ta ce "Ameen ya Allah na gode sosai, Allah ya raya mana twins." Ya ce "Amin, and secondly I......" Turo ƙofar ɗakin da akai ya katse masa maganar da yake yi. Zahra ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Da mamaki ta ce "Yaya Doctor dama kana nan, muna ta nemanka zamu tafi, Ummi ta kira wayarka baka d'aga ba." Ya juya ya nufi ƙofa yan faɗin "Ina nan ina yiwa Aunty godiya." Zahra ta yi murmushi ta ce "Gaskiya ne." Neehal ta ƙirƙiro murmushi tana kallon Zahra bayan ya fice ta ce "Har kun fito?" Zahra ta ce "Ehh, sai tafiya." Neehal bata kuma cewa komai ba ta ɗauki wata leda dake cike da kayan wasan su Afrah suka fice daga ɗakin zuwa downstairs.







Babu kowa a falon duk sun fice. a parking space suka tarar da su tsaitsaye suna sallama. Su Afrah suna hango Neehal suka rugo gurinta suna faɗin "Aunty Daddy ya ce dake zamu tafi, zaki je gidanmu ko?" Neehal ta shafi kuncinsu tare da gyaɗa musu kai. Zahra ta karb'i ledar hannunta ta zira a Mota sannan ta dawo ta karb'i phone Numbern'ta. Cikin matuƙar dauriya Neehal ta ƙarasa bakin Motar da za su tafi a cikinta ta cewa Ummi. "Ku gaida gida, Allah ya tsare." Ummi ta ce "Ameen d'iyata, sai mun kuma dawowa ko kuma in kin zo ganin ƴaƴanki." Neehal ta murmusa bata kuma cewa komai ba, dan tana buɗe baki ta san kuka ne zai kufce mata. Ta buɗe murfin Motar ta zira su Afrah wanda suka mak'ale mata su sai da ita zasu tafi. Ganin bata shigo motar ba tana ƙoƙarin rufewa suka fasa kuka tare da ƙoƙarin fitowa. Ummi ta ce "Ah ah, me ya faru?" Afrah ta ce "Aunty, ni gurin Aunty zani." Cikin rarrashi Ummi ta ce "Ba ga Auntin nan ba ai tare zamu tafi da ita." Amrah ta ce "Ai bata shigo cikin Mota ba." Neehal da k'walla ta tarar mata a ido ta yi murmushi tare da shafa fuskar Afrah ta ce "Kayana zan ɗauko yanzu zan dawo sai mu tafi." Yarinyar ta ce "To zan biki." Ummi ta ce "A'a Afrah ku jira ta, ta dawo." Yaran suka saka kuka dan sun gane wayo ake musu, Neehal ta juya da sauri ta bar wajen hawaye na zuba daga idonta. Ahmad dake tsaye yana kallonsu ya bita da kallo, da sauri kuma ya bi bayanta ya sha gabanta. Ta tsaya ba tare data d'ago kanta ba. Fuskarsa cike da damuwa ganin tana kuka ya ce "I'm sorry na raba ki da yaranki ko?" Ta d'ago ta kalle shi cikin mamakinsa, shi da yaransa amma yana bata haquri. Ya yi mata murmushin nan nasa mai shegen kyau, tare da girgiza mata kai alamun ta daina kukan. Jin kukan su Afrah a kusa da ita yasa ta juya da sauri, ashe fitowa sukai daga cikin motar suka taho gurinta. Ta tsugunna ta rungume su a jikinta, sannan ta d'ago su ta musu pick a goshinsu tana murmushi. Afrah ta ce "Aunty ki zo mu tafi Please, mu dake zamu tafi." Kafin Neehal ta ce wani abu Ahmad dake tsaye yana kallonsu cikin burgewa ya kama hannun yaran ya ce "Aunty zata ɗauko kayanta ne, mu je Mota mu jira ta." Neehal ta miƙe tare da juyawa da sauri ta d'agawa Zahra hannu sannan ta nufi cikin gidan zuciyarta cike da kewar yaran, bayan tafiyarta ba jimawa su Ahmad suka fice daga gidan suna d'agawa su Mama hannu, sai da suka fice sannan su Mama suka koma cikin gidan.








Neehal ba ta yi kuka sosai ba kamar yadda Mama ta zata, tana komawa ɗakinta ta shiga toilet ta wanke fuskarta, sannan ta sakko ƙasa gurin Aunty A'isha suka sha hira, bayan Sallar Magriba Aunty A'isha ta tafi, tana tafiya ba jimawa Sadik ya zo. Shima ya yi tunanin zai zo ya same ta cikin damuwar rashin su Afrah, amma sai ya tarar da akasin haka, suka sha hirarsu kamar kodayaushe. Washegari da hantsi ta shirya ta je saloon aka mata wankin kai, daga nan ta wuce gidan Haneefah kamar yadda ta mata alƙawari. Sai Bayan Magriba ta dawo gida, a hakan ma dak'yar Haneefah ta barta ta taho suna ta shan hira. Bayan Sallar isha'i Zahrah ta kira ta a waya, bayan sun gaisa ta musu ya suka je gida ta haɗa ta da su Afrah. Sun daɗe suna wayar suna ta bata labarai, bayan ta sha complain ɗin rashin bin su da bata yi ba..... Ranar Monday ta fara zuwa siwes ɗinta na school, a gidan TV'nsu take yi, hakan yasa abun ya zo mata da sauk'i. Bayan tafiyar su Afrah kullum sai sun yi waya a wayar Zahra, dan yanzu duk abun Ahmad ya haqura ya bar su a gidan Ummi su cigaba da zama anan saboda abun da ya faru. Neehal ta rasa meyasa fuskar Ahmad ta ƙi bacewa daga idanunta, musamman murmushinsa da yay ta kashe ta da su a ranar, kullum sai ta yi imagine ɗinsa a cikin ranta, a gefe guda kuma tana son tuno inda ta san fuskarsa, dan tabbas ta taɓa ganinta a rayuwarta ko da a hoto ne kuwa.








Ranar Asabar da yamma ta dawo daga gurin aiki ta tarar Hameedah da Mommy'nta sun zo gidan. A gajiye take amma duk da haka ta zauna a falon ƙasa inda ta tarar da su da fara'arta ta ce "Sannunku da zuwa." Hameedah ta mata wani shegen kallo ta ɗauke kanta. Haj. Saratu ba yabo ba fallasa ta ce "Yawwa." Neehal ta ce "Ina yini Mommy." Hajiya Saratu ta ce "Lafiya, ashe an yi bikin ƙawar nan taki mara kunya?" Neehal ta ce "Eh." Cikin rashin jin daɗin mara kunyar data kira Haneefah da shi. Hajiya Saratu ta tab'e baki ta ce "Ke kuma yaushe ne naki bikin?" Neehal ta ce "Mommy idan an saka bikina ai zaku ji." Hajiya Saratu cikin baƙin ciki ta ce "Au da akwai wanda kike kulawa yanzu kenan?" Neehal ta ce "Eh." Cikin takaici Haj.Saratu ta ce "Wanne me rabon ɗorawa iyayensa asararsa ne? Ko kuma munafuntarsa akai ba a gaya masa matsalar da kike da ita ba?" Neehal ta yi shiru dan ta gane inda maganar Haj Saratu ta dosa. Hameedah ta ce "Kema dai Mommy banda abinki ai kin san baza a faɗa masa ba tunda ana neman a shiga daga ciki kar a tsufe a gida." Haj. Saratu ta ce "Hakane fa daughter, shi dai Yaya Muhammad Allah ya haɗa shi da masifa, yana zaman zamansa za'a ɓata masa suna a idon duniya, daga ya fito a dinga nuna shi ana yarinya ce a gidansa ta zama annoba duk wanda zata aura sai ya mutu." Mama dake sakkowa daga sama karaf maganganun Mommy a kunnenta, ta yi wani murmushi ta ce. "Saratu kenan." Haj Saratu ta ce "To ƙarya na faɗa ne, ai gaskiya ce, wa ya sani ma ko dama can dangin nata sun san annoba ce ita shi yasa suka ƙi riƙe ta karta zame musu masifa." Har Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa, ta san dama haka Haj. Saratu take so ta tanka mata su yi ta yi, ita kuma bata da wannan lokacin. Ta dubi Neehal da take kuka sosai na kiranta annoba da Hajiya Saratu ta yi ta ce "Tashi ki wuce sama." Ta miƙe ta zari jakarta tana share hawaye ta yi sama, Mama ta bi bayan ta, ta bar Haj. Saratu tana cigaba da faɗar bak'ak'en maganganu marasa daɗi akan Neehal. A kan kujera ta tarar da Neehal ta kifa kanta tana kuka. Mama ta janyo ta jikinta ta shiga lallashinta tana faɗin "Ki yi shiru haka kukan ya isa, kar ki ɗauki maganganunta na banza ki saka a ranki har su zo suna damunki, na san halinki da saka abu a rai." Ta d'ago ta, ta shiga share mata hawayen fuskarta. Sosai maganganun Haj.Saratu suka daki zuciyar Neehal, musamman idan ta tuna kalmar annoba da Hajiya Saratu ta kirawo ta da ita, hakan yasa hawayenta suka ƙi tsayawa. Mama ta tashi ta shiga dakinta ta barta a falon. Haj. Saratu tana cikin mitar ta Ameen ya shigo falon, tana ganinsa ta yi shiru. Hameedah ta faɗaɗa fara'a cikin iyayi ta ce "Yaya Ameen sannu da zuwa." Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa tare da amsa mata ciki_ciki. Ba yabo ba fallasa ya gaishe da Haj. Saratu sannan ya haye upstairs abinsa. A falo ya tarar da Neehal durk'ushe inda Mama ta barta tana kuka, ya bita da kallo tare da faɗin "What happened to you?" Neehal ta d'ago kanta jin muryarsa amma ba ta ce komai ba, ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta a ɗan ruɗe ya ce "Tell me what happened?" Neehal ta share hawayenta ta ce "Mommy ce, ta kira ni da annoba." Sai ta kuma fashewa da kuka. Shiru ya yi cikin ɓacin rai, ya rasa uwar me Neehal ta tsarewa Haj. Saratu a rayuwa ta tsane ta. A hankali ya matso daf da ita ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam a ƙirjinsa ya shiga rarrashinta..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣2️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














..........Lamo ta yi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da barin kukan da take. A hankali ya d'ago ta daga jikinsa yana dubanta da murmushi akan fuskarsa ya ce "Je ki wanke fuskarki ki zo ki raka ni unguwa." Ta gyaɗa masa kai tare da miƙewa ta shige ɗakinta. Ya bita da kallo cikin sauke numfashi. Miƙewa ya yi shima ya shiga ɗakin Mama. Bayan ya yi sallama ta amsa sun gaisa ya zauna a gefenta tare da faɗin "Mum ki taya ni murna, next month zan dawo Kano da aiki Insha Allah." Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin hakan sosai, ka ga an huta da fargabar barin Hafsah ita kaɗai a gida." Ya ce "Hakane, bari in je masallaci na ga lokacin Sallah ya gabato, idan na dawo zamu fita da ƴarki." Mama ta ce "Fita kuma? Zuwa ina?" Ya ce "Unguwa." Ta ce "Ita unguwar bata da suna?" Yana miƙewa ya ce "Sirri ne tsakanin Yaya da ƙanwarsa." Mama ta tab'e baki ta ce "Kamar gaske." Ya yi murmushi kawai tare da ficewa daga ɗakin. Itama Neehal data shiga toilet bayan ta wanke fuskarta ganin Magriba ta gabato sai ta ɗauro alwala ta fito. A gaban mudubi ta tsaya ta ɗan gyara fuskarta ta saka kwalli a idanunta saboda kukan da ta yi. Bata canza kaya ba, mayafi kawai ta ɗauko ta yafa ta ajiye hijabin da yake jikinta. Ɗakin Mama ta shiga dan sanar mata Ameen ya ce za su fita, zuciyarta cike da mamakinsa dan ta manta rabon da su je unguwa ko wani gurin tare da shi, dan tun da ko Mama ta ce ya kaita School ko gurin aiki sai ya haɗa ta driver, ya ce shi ba direbanta ba ne. Ta tarar Mama tana toilet tana alwala, ganin ƙofar toilet ɗin a buɗe ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce "Mama Yaya ya ce zamu fita yanzu." Mama ta ce "Ya faɗa mun, amma ai kya ci abinci kafin ku tafi." Ta ce "Bana jin yunwa." Mama ta ce "Shikenan ai, ki je ki yi sallah kafin ya dawo, shima ya je masallaci." Neehal ta ce "Toh." Ta dawo cikin ɗakin ta ɗauki darduma ta shimfid'a ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah. After some minutes Ameen ya shigo ɗakin, yana duban Neehal ya ce "Tashi mu je kar dare ya yi." Mama ta ce "Allah ya tsare, saura kuma kafin ku dawo ka samun ita kuka, dan na san hali." Ya yi ɗan murmushi bai ce komai ba. Neehal ta yiwa Mama Sallama suka fice a tare. Yanda ta bar Haj.saratu da Hameedah haka suka sauko suka same su, da alama ko tashi sun je sun yi sallah ba su yi ba. Ba suce musu ƙala ba suka fice, su kuma su Hameedan suka raka su dana mujiya. Bayan fitarsu Hameedah ta dubi Mahaifiyarta ta ce "Sabon salo b'arawo da sallama, ko ina kuma za su a daren nan?" Haj Saratu ta ce "Oho musu, amma ni fa na fuskanci take_taken Haj. Fatima so take ta aurawa Ameen shegiyar yarinyar can." Hameedah ta lailayo ashariya ta ce "Tab'dijan, da kuwa an yi ƙaramin yaƙi a family wallahi, ta hana shi aure na sannan kuma ta aura masa wata can bare." Haj Saratu ta ce "Hmmmm, ba dai tak'amarta ita ta haife shi ba, to ai ba ɗanta ba ne ita kaɗai, wallahi matuƙar ta ce zata aurawa Ameen yarinyar nan da taƙi auruwa sai na yi sanadin barinta gidan nan, mu zuba mu gani ni da ita." Cikin damuwa Hameedah ta ce "Mommy ni duk ba wannan ba ma, wai ya batun aure na da Ya Ameen ne? kin ce mun wannan zuwan da mukai akan maganar auren ne, kuma ban ga wata alama data nuna hakan ba, ni fa gaskiya na gaji da gafara sa ban ga k'aho ba." Ta ƙarashe maganar cikin botsarewa. Mommy ta ce "Me kike ci na baka na zuba ne? Ki bari ki ga me zan yi mana, akwai shirin da nake yi, da zarar ya kammala zaki sha mamaki, ke dai ki kwantar da hankalinki bana son kina damuwar nan." Hameedah ta sauke numfashi cikin damuwa, ita yanda Ameen yake nuna halin ko in kula da ita yafi komai d'aga mata hankali, gashi ita babu wani wanda yake zuwa gurinta a yanzu da sunan saurayi. K'awayenta duk sun yi aure, ita ga kuɗin ga aiki tana yi amma babu mashinshini duk da uwar maganin farin jinin da uwarta take dirka mata.








Sai da suka shiga Mota sannan Neehal ta dubi Ameen ta ce "Yaya ina zamu?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Siyar dake zan yi." Jin haka yasa ta ja bakinta ta tsuke. Har suka ƙarasa wani had'ad'd'en Bakery dake cikin Nasarawa babu wanda ya ce uffan. Ya yi parking ɗin Motar ya fito itama ta biyo bayan shi suka shiga gurin. K'amshin abinci irin me tsinka yawun nan ne ya fara musu welcome. Gurin ya haɗu sosai kuma babu hayaniya ko kaɗan. Suka zauna a kujerun dake zagaye da table suna fuskantar juna. Ameen ya ɗauko wayarsa ya shiga latsawa, ita kuma ba ta fito da waya ba ta baro ta a gida, kallon gurin kawai take cike da burgewa. Wani ma'akaicin gurin ya kawo musu takarda mai ɗauke da duk wani abu da suke siyarwa a gurin tare da price ɗinsa. Ameen ya karɓa ya duba tare da selected ɗin abun da za'a kawo musu. Bayan mintuna biyar ma'aikacin ya dawo ɗauke da madaidaitan plates guda biyu a hannunsa, a gaban Neehal ya ajiye su duka kamar yadda Ameen ya ce masa. Neehal ta kalli snacks ɗin yawunta na tsinkewa saboda k'amshin daya bugi hancinta. Plate na farko meatpie ne a ciki da Spring rolls da samosa. Plate na biyu kuma Pizza and shawarma ne a ciki. Sai kuma Juice and bottle water a gefe, sai tissue. Ba tare da Ameen ya kalle ta ba yana cigaba da latsa wayarsa ya ce "ki yi sauri ki ci." Ta dube shi ta ce "Kai fa?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Ba ta kuma cewa komai ba, ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa. Cin abincin Neehal babu sauri, kafin ta gama fiye da mintuna ashirin sun wuce, kuma bai fi rabin abun da aka ajiye mata ta ci ba. Bayan ta gama, ya je ya biya kuɗin tare siyan wasu snacks ɗin, a leda biyu aka masa packaged, ya karbo suka baro gurin. Daga nan gurin shan Ice cream da siyar da su chocolate ya kai ta, suka shiga ya ce ta ɗibi abun da take so. Neehal masoyiyar choculate da wafer ta diba son ranta ya biya kuɗin suka fito suka nufo gida, lokacin har an yi isha'i. Suna hanya Hafsah ta kira shi, da ya duba ya ga ita ce sai ya ƙi d'agawa. Sun kusa zuwa gida ta ji Muryarsa ba tare da ya juyo ba ya ce "Ko mu ƙara zuwa wani gurin?" Neehal ta ce "A'a dare ya yi." Ya ɗan kalle ta ya ce "Ko dai wannan saurayin naki ne zai zo kike sauri ki koma gidan?" Ta ce "A'a wallahi, ka san idan muka daɗe Mama za ta yi faɗa." Ya ce "Hmmm." Kawai. A parking space ya ajiye ta bayan sun ƙarasa gida, ya bata ledodin ta ya ce ta gaishe da Mama shi ya wuce, ta yi masa godiya sannan ta nufi part ɗin Mama. Tana jin zuciyarta ta mata sanyi akan bata mata ran da Haj Saratu ta yi. Sosai ta ji daɗin fitar nan da sukai, ko dan ta daɗe bata fita irin guraren nan ba ne?














Bata tarar da su Hameedah a falo ba, da alama sun shige ɗaki, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya mata ba. Ɗakin Mama ta nufa ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. "Mama na dawo." Ta faɗa tana zama a gefen gado. Mama ta ce "Sannunki da zuwa, ina Ameen ɗin?" Ta ce "Ya wuce gida." Mama ta ce "Ina kuka je ne?" Neehal ta ce "Wani Bakery ya kai ni, sai kuma muka biya muka siyi Ice cream." Mama ta ce "Shine dan wulaqanci ba zai je da Matarsa ba sai dai ya zo ya ɗauke ki." Neehal ta yi dariya ta ce "Kai Mama, itafa ta zama cuss yanzu tunda matar Aure ce, da ƴan mata ake fita, kuma itama ya siya mata nata, kema ga naki ya ce na kawo miki." Mama ta ce "Ko ma da jarirai ake fita daga yau ya dinga fita da matarsa." Mama ta ƙarasa zancen tana duba ledar da Neehal ta ajiye. Neehal ta miƙe ta ce "Bari na je na yi sallah." Mama ta ce "Alright." Tana shiga bedroom ɗinta ta dauko wayarta, kamar yadda ta zata missed call ɗin Sadik ta gani har biyu. Tana ƙoƙarin bin bayan kiran nasa wani kiran ya shigo amma da new Number. Ta d'aga ba tare da ta ce komai ba. Muryar Amrah ta ji ta ce "Hello Aunty." Neehal tana murmushi ta ce "Sweetheart, ke ce? ya kike?" Amrah ta ce "Lafiya k'alau Aunty, yaushe zaki zo?" Neehal ta ce "Soon Insha Allah, ina Afrah?" Ta ce "Tana toilet tana pupu." Neehal ta ce "Ina Ummi da Aunty Zahra?" Amrah ta ce "Suna gida, mu kuma muna gidan Daddy." Neehal ta ce "Anan zaku kwana?" Ta ce "A'a, idan Afrah ta fito daga toilet Daddy zai mayar da mu gidan Ummi." Neehal ta ce "To ƴar gidan Daddy ina Daddy'n?" Amrah ta ce "Gashi nan, yana jinki." Ta ce "To ki gaishe shi." Muryarsa ta ji a maimakon ta Amrah, cikin marairaicewa ya ce "Uhm, ke baza ki gaishe ni da kanki ba kenan?" shiru ta yi, jin muryarsa a bazata yasa ta ji wani abu a cikin zuciyarta, har da lumshe idanunta ba tare data sani ba, tare da tunanin a ina kuma ya samu Numbern'ta? 'A gurin Zahra.' zuciyarta ta bata amsa. A kasalance gami da shagwab'arta ta ce "Ina yini." Ya kwaikwayi muryarta ya ce "Lafiya k'alau Aunty, ya Mama." Ta turo baki gaba kamar yana kallonta ta ce "Tana nan k'alau." Ya ce "My regard to her." Daga haka ya miƙawa Amrah wayar jin Afrah tana kwad'a masa kira daga toilet. Suka ci-gaba da hira da Amrah tana bata labarin school ɗin da aka mayar da su, har Afrah ta fito daga ta karb'i wayar tay ta mata surutun ta itama, ganin dare yana yi Ahmad ya ce su mata sallama zai mayar da su. Bayan sun gama wayar ta bi wayar da kallo kamar zata ga yaran a cikin wayar. Sosai take jin kewarsu a cikin ranta, musamman in ta zo bacci sai ta ji gadon ya mata faɗi ita kaɗai, ta saba da, da twins manne a jikinta. Tashi ta yi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da dauro alwala ta fito ta yi Sallar isha'i. Bayan ta idar ta kira layin Sadik amma bai ɗauka ba, hakan yasa ta kunna data ta shiga yanar gizo. Jimawa kaɗan Sadik ya kira ta, ta d'aga da sauri dan yau gaba- ɗaya ba su yi waya ba, ta yi kewarsa ba kaɗan ba.......










Washegari Sunday tana gida through out saboda ita kaɗai ce ranar hutunta a week, tunda ta fara siwes Monday to Saturday take zuwa gurin aiki. Tunda ta tashi da safe bata huta ba tana ta aikin gida. Mama sun fita gidan wata Freind ɗinta ita da su Dije tun wajen 11, daga nan kuma za su wuce kasuwa su siyo kayan girki. Suma su Hameedah tun safe suka wuce Abuja, saboda gobe Monday Hameedan zata je gurin aiki. Bayan Sallar la'asar tana kitchen tana girki ta ji ƙarar door beil. Ta fito tana kwab'e fuska saboda gajiyar da ta yi, a tunaninta su Mama ne suka dawo, amma tana buɗe ƙofar sai ta ga wanda bata taɓa tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba. Cikin matuƙar mamaki ta tsaya tana kallonsa. Ya sakar mata murmushinsa wanda ya kasa bacewa idanunta tun ranar da ya tafi har kawo yau. Ta yi ƙasa da kanta tare da faɗin "Sannu da zuwa." Ta ƙarashe zancen tana matsawa

Please Login or Register in order to submit comment