Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai adalci data yankewa waɗanda ake ƙara hukunci dai_dai da abun da suka aikata, bisa ga shaidun da aka gabatar da kuma amsa laifunsu da sukai da bakinsu. Na gode ya mai girma mai shari'a." Sannan ya juya ya koma inda yake a zaune d'azu ya zauna. Alk'ali ya ja gwauron numfashi dan shi kan shi abun ya daki zuciyarsa ba kaɗan ba sannan ya d'ago daga rubuce-rubucen da yake ya ce. "Bisa tarin hujjoji da bayanai da wannan kotu mai adalci ta tattara ta yankewa Bilyaminu,Zakari da Hakim, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an ba su horo mai tsanani a gidan kaso. Sannan kuma kotu ta yabawa Hashim Isma'il na_kowa k'warai bisa yanda ya bayar da shaida ga abun da mahaifinsa ya aikata. Shi kuma Senator Na_kowa da wand'anda suka yi kisan tare da su Bilyaminu tunda sun riga mu gidan gaskiya hukuncinsu yana gurin mahaliccin su." Alk'ali ya buga guduma gum!gum! Har sau uku. Sannan mutane aka haɗa baki gurin faɗin "Koto! Su Bilyaminu kuwa ido ne ya raina fata ganin yanda gandirobobi (Ma'aikatan gidan yari) suka ƙaraso inda suke suka fara daurawa musu ankwa a hannuwansa, a gefe guda kuma ga turmutsitsin ƴan jarida kowa na son ɗaukar rahoto. Barrister Murtala kuwa sai gaisawa mutane suke zuwa suna yi da shi, shi kuma yana murmushin samun nasara.














Hajiya ce ta fara miƙewa a cikin su Mama tana faɗin. "Wannan la'anannen Senator ɗin Ubangiji ya ƙara masa azabar k'abari, mutane sai son zuciyar tsiya da rashin imani, wannan irin zalunci haka har ina?" Sai kuma ta kalli Neehal da har yanzu bata d'ago kanta ba ta ce "Wannan yarinya Allah ya bi miki haqqinki na marainiyar ƙarfi da ya ji da aka mayar da ke baki ji ba, baki gani ba." Aunty Sadiya ta taso daga inda take zaune ta dawo gurinsu tana murmushin takaici ta ce "Masha Allahu, an gano waɗanda suka kashe su Abban Neehal an hukunta su, saura kuma wanda yake kashe su Anwar shi ma." Kafin wani a cikin su ya yi magana Alhaji Ali da Daddy da sauran abokan Abba sun ƙaraso gurin, ƴan jarida na bin su yuu a baya dan son jin tofa albarkacin bakinsu a game da wannan al'amari a matsayin su na iyalan waɗanda aka kashe. Alhaji Ali ya dubi Aunty A'isha ya ce "A'isha! kin ji abun da bamu taɓa tsammani ni ba ko? Lallai ka ji tsoron duniya da mutanen cikinta, saboda ko mafarki na yi aka ce mun Na_kowa zai yiwa Gabasawa haka zan farka in yi tunanin ko addu'ar bacci ce ban yi ba, shaid'an ya kawo mun ziyara." Aunty A'isha ta girgiza kai ta ce "Yanda Abban Neehal yake yawan zancen mutumin nan da k'aunarsa da faɗar kirkinsa da mutuncinsa ashe shi zai yi sanadin barin sa duniya." Aunty Sadiya ta ce "Mutane sai addu'a kawai, amma wanda baka taɓa zaton zai iya cutar da kai ba, sai a wayi gari ya maka abun da ko mak'iyin ka na fili ba zai maka ba." Nan dai suka ci-gaba da tattauna al'amarin, su Uncle Umar ma sun ƙaraso ana jimanta abun da su, dan ya san Senator Na_kowa mutumin Abba ne sosai. Mama kuwa magana ma ta kasa yi, sai bin su da ido kawai take.








A hankali Ameen yake takowa cikin takunsa mai ɗaukar hankali zuwa inda Neehal take, wadda bata ma san ya zo court ɗin ba tunda ba tare suka zo ba. Hannunsa yasa ya d'ago fuskarta bayan ya ƙarasa daf da ita, tun kafin ta kalli fuskarsa ta san shine saboda k'amshinsa da baya buya da ya ziyarci hancinta. A hankali ta d'ago ta dubi fuskarsa idanunta taf da ruwan hawaye, sai kuma ta miƙe da sauri ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Yasa hannunsa ɗaya ya zagaye bayanta yay mata kyakkyawar runguma ba tare da ya ce komai ba, sai lip ɗinsa da yake taunewa alamun abun ya taɓa masa zuciya sosai shi ma. Tsahon mintuna biyu tana jikinsa sannan ya d'ago ta a hankali ya rabata da jikinsa. Bai ce komai ba ya saka tafin hannunsa ya shiga share mata hawayen. Ta sauke ajiyar zuciya tare da yin ƙasa da kanta, ya kalli gefensa inda su Mama suke har yanzu gurin a cike yake da mutane. A hankali ya kama hannunta, bata musa ba ta bi shi suka fice daga cikin court ɗin. Da kansa ya buɗe mata Motarsa ta shiga ta zauna, sai aikin sassauke numfashi take. Ya zagaya ya shiga driver seat ya zauna shi ma. Yana ƙoƙarin kunna Motar wayarsa ta fara ringing, ya ɗauko ta daga aljihun gaban rigarsa, ganin Mama ke kiransa ya yi picked. Mama ta tambaye shi yana tare da Neehal ne. A takaice ya ce mata "Eh." Ya mayar da wayar aljihu tare da kallon Neehal wadda ta dunk'ule kanta a waje ɗaya saboda zazzaɓin jikinta dake son dawo mata sabo. Hannunsa ya kai ya taɓa goshinta ya ji da zafi, jikinta kuwa sai rawar ɗari yake. A hankali ya janyo ta ya kwantar da kanta a kan ƙafaɗarsa cikin tsananin tausayinta. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da lumshe idanunta, hannunta ɗaya ta saka ta zagaye bayansa da shi. Ya ɗan lumshe ido ya buɗe sannan ya kunna Motar ya yi reverse suka bar harabar court ɗin. A haka suka ƙarasa gida tana jikinsa har bacci ya fara ɗauke ta. Bayan ya yi parking ya d'aga kanta a hankali daga kan ƙafaɗarsa ya ɗan tsurawa beauty face ɗinta ido, gigirarta ya shafa da finger ɗinsa a hankali gami da ɗan bakinta da ya ɗan turo gaba saboda baccin da take. Hakan yasa ta buɗe idonta dake cike da bacci, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Yatsina fuska ta yi saboda kanta da ta ji yana sara mata, cikin muryar wanda ya ci kuka ya k'oshi ta ce "Yaya kaina ciwo." Ya shafi kuncinta ya ce "Sorry dear, mu je ciki ki sha magani." Ta gyaɗa masa kai tare da barin jikinsa cikin harfin hali, dan sosai take jikin nata babu daɗi. Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagayo ya buɗe mata itama ta fito. Hannunta ya kama suka nufi part ɗin Mama. Ya yi amfani da key ɗin hannunsa na part ɗin ya buɗe musu ƙofa suka shiga. Ta saki hannunsa da nufin ta kwanta anan falo kan kujera, fahimtar hakan yasa ya ƙara kama hannun nata ya ce "Mu je daki sai ki kwanta." Bata musa ba, amma bata ce komai ba. Har bedroom ɗinta ya raka ta ta kwanta akan gado. Yana ƙoƙarin fita ta ce "Yaya zan yi fitsari." Bai ce komai ba ya dawo ya taimaka mata ta tashi ya rakata har bakin toilet, ta shiga ta yi ta fito, ya ƙara kama hannunta zuwa bakin gado sannan ta hau ta kwanta tare da jan bargo ta lullub'e jikinta da shi. Fita ya yi daga ɗakin, ba jima sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da drug da ruwa. Ya zauna a bakin gadon cikin kulawa ya ce "Tashi ki sha magani." Ta tashi zaune da ƙyar tana yamutsa fuska, ya bare mata maganin ya bata ta sha ta kora da ruwa. A hankali ya ce "Allah ya sauwaqe." Ta kalle shi idanunta cike da hawaye ta ce "Ameen, Thank you." Ta koma ta kwanta. Ya matso kusa da ita ya shafi gefen fuskarta cikin wata irin murya ya ce "Don't cry, bana son inga kina kuka, bana jin daɗi." Ta tsura masa ido kamar me mamakin abun da ya faɗa, shima kallon nata yake yi. Ta kama hannunsa a hankali ta ce "Insha Allah Yaya na daina kukan tunda baka so." Ya yi mata ɗan murmushi ya ce "Sleep well." Itama murmushin ta masa ta mayar da idanunta ta lumshe. Ya zare hannunsa a hankali daga cikin nata, ya gyara mata hijabin jikinta da ya ɗan shak'e mata wuya, sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin.........✍️










_*Long page, amma ban yi edit ba, a yi haquri da typing errors.*_








*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣0️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














..........Falo ya koma ya zauna, ya lumshe idonsa hannunsa ɗaya dafe da kansa. Sai aikin taune lip ɗinsa na ƙasa yake alamun something is hurting his heart cikin sauke numfashi kaɗan_kaɗan. Ya fi mintuna goma a zaune ba tare da ya motsa ba, jin an buɗe ƙofar falon yasa ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan. Mama ce ta shigo, cikin sanyin jiki ta ce "Ina Neehal ɗin." Ya d'ago ya dube tare da nuna mata ƙofar ɗakin Neehal ba tare da ya yi magana ba. Bata ce komai ba ta shige ɗakin. Bacci ta tarar Neehal ɗin tana yi wanda ga dukkan alamu bana daɗi ba ne. Ta yaye mata bargon data lullub'a ganin yanda take zufa ga jikinta ya yi zafi zau. Cire mata hijabin jikinta ta yi ta ɗan goge mata gumin fuskarta sannan ta juya ta koma falo. Ta dubi Ameen ta ce "Ka bata Magani ne?" Ya ce "Eh, na ɗauko mata a dakinki." Mama ta ce "Ashe ka je court? ban ma ga zuwanka ba." Ya ce "Ina ciki ma kuka zo." Mama ta jinjina kai ta ce "Ina Hafsat fa, me yasa baku zo tare ba?" Ya ce "Bata jin daɗi ne." Mama ta ce "Ayya, Allah ya bata lafiya." Kafin ya amsa Hajiya ta shigo falon tana faɗin "Ina Neehal ɗin ta shiga ne? ko ba gida Aminun ya kawo ta ba?" Mama ta ce "Tana ɗakinta, zazzaɓi mai zafi ne a jikinta, allura ma zan haɗa in mata yanzu." Hajiya ta ce "Subhallahi, dama jikin nata bai gama warware wa ba, gashi ta je ta jiyo wannan abun tashin hankalin ai dole zazzaɓi ya dawo baya." Mama ta ce "Allah ya bata lafiya kawai." Sannan ta nufi ɗakinta. Hajiya ta dubi Ameen ta ce "Au Aminu, ina matar taka ne? Ban ganta a kotu ba, ai yanzu an zama ɗaya ya kamata ace ta zo, duk abun da ya samu Neehal ai ya shafe ka, ko ma ince kamar kai ya sama, tunda ba ka da kamarta a duniyar nan. Koda yake ba zan yi mamakin ƙin zuwan nata ba dan ba wani son mutane take ba. Dan ranar da na je dubo ka..... "Allah ya kawo ki zaki cika mun kunne." Ameen ya katse ta da faɗin haka fuskar nan a haɗe." A zafafe Hajiya ta zauna ta ce "An cika maka kunnen, na ce an cika maka kunnen, dan k'wal uba kawai, laifin matarka ne baka son a faɗa kuma sai na faɗa ɗin!" Hajiya ta cigaba da mitarta tana faɗar Abun da Hafsat ta mata na rashin kyautawa da ta je gidan. Idan kujerar da take kai a zaune ta tanka mata to Ameen ma ya tanka mata. Mama ce ma data fito ta ji tana mitar ta sanar mata Hafsan ce bata jin daɗi shi yasa bata zo ba. Kiran sallar Azhar da akai yasa ya miƙe dan tafiya masallaci. Hajiya ta ce "Idan ka dawo sai ka kai ni na dubo jikin Hafsan." Ko juyowa bai yi ya kalle ta ba ya fice abinsa." Ya bar Hajiya tana faɗin, "Dan Allah zani ba don halinta ba."








Har wajen la'asar su Aunty Sadiya suna gidan Mama suna cigaba da tattaunawa akan al'amarin. Yayinda a ɓangaren al'ummar gari ba'a wani yayata zancen ba, saboda ba'a lokacin akai kisan ba. Kafafen watsa labarai ma ba su yaɗa labarin sosai ba, saboda gargadi'n da akay wa kowacce kafar yaɗa labarai daga sama, musamman waɗanda suke zaune a ƙarƙashin gwamnati. Masu zaman kansu ne suka faɗi hukuncin da akaywa su Bilyaminu, amma suma an gargad'e su akan kar sunan Senator Na_kowa ya fito a cikin al'amarin. Alhaji Ali kuwa bayan ya koma gida ko ruwa kasa kurb'a ya yi balle akay ga cin abinci, saboda tsananin al'ajabi da ɗimauta shi da al'amarin ya yi.










Sai bayan la'asar ta farka daga baccin, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune, kanta ta dafe da hannunta saboda yanda ta ji yay mata dimm, amma babu ciwo kamar ɗazu. Jikin nata ma ta ji sauƙin sa babu zafi sosai kamar ɗazu, sai dai rashin k'warin jiki da kuma abun da baza a rasa ba. Ta ja ƙafa ta sakko daga kan gadon tana yamutsa fuska ta miƙe, taune lip ɗinta ta yi saboda yanda ta ji saman cinyarta ta hagu a ɗan daure, alamun Mama ta mata allura kenan da tana baccin. Toilet ta nufa cikin rashin k'warin jiki ta yi wanka da brush tare da dauro alwala ta fito. Tana fitowa Mama na shigowa ɗakin, dama ta shigo ta tashe ta ne ganin yamma ta yi sai kuma ta ga ta ma tashin. Mama tay sauri ta ƙarasa ta kamata ta kai ta kan gado ta zaunar. Mama ta ce "Sannu Daughter ya jikin?" Cikin muryar marasa lafiya ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, bari na shimfid'a miki darduma ki yi sallah sai ki ci abinci ki ƙara shan magani." Ta jinjina mata kai kawai. Mama ta ɗauko mata lotion ta shafa mata a hannu da ƙafafuwanta, sannan ta ɗauko mata wata gown mara nauyi ta bata ta saka a jikinta. Mama tana shimfid'a mata dardumar ta ce "Me zaki ci a dafa miki?" Ta yi shiru alamun nazari sannan ta ce "Babu komai, bakina babu daɗi." Cikin lallami Mama ta ce "Ai dole sai kin daure kin ci wani abun, cuta ba cin abinci ai bazai yiyu ba. Ga abubuwan da Ameen ya siyo miki can a dawnstairs, bari na ɗauki miki na san ba'a rasa abun da zaki iya ci ba." A hankali ta ce "Yayan ya tafi?" Mama ta ce "Eh, yakai Hajiya gidansa zata dubo Hafsah, itama bata jin daɗi." Ta ce "Su Aunty ma sun tafi?" Mama ta ce "Duk sun wuce tun d'azu." Bata kuma magana ba, dan wadda ta yi ma cikin dauriya ta yi ta, ta miƙe ta ɗauki hijabin da Mama ta ajiye mata ta saka ta tayar da Sallah. Kafin ta idar Mama ta je ta ɗauko siyyayar da Ameen ya yo mata ta kawo mata. Ledoji ne guda biyu, ɗaya kayan fruits ne cike a cikinta, ɗayar kuma Popcorn ne da wafer da shawarma da yoghurt. Ta yi murmushi lokacin da Mama take fito da su daga cikin ledar, gaba-d'aya favourites things d'inta ya siyo mata, sai dai yanda take jin bakinta babu daɗi da ƙyar zata iya ci. Yoghurt d'in ta ce Mama ta bata, shima kaɗan ta sha ta ajiye. Sai ta ɗauki wafer ɗaya ta koma kan gado tana gutsira kaɗan kaɗan tana ci. Mama ta miƙo mata wayoyinta ta ce "Anata kiranki tun d'azu, Haneefah ma ta kira, amma na d'aga nata kiran." Ta karb'i wayoyin tare da faɗin "To bari na bi bayan missed calls ɗin." Mama ta juya ta fice daga ɗakin. Ta latsa wayar ta duba ta ga Sadik da Ahmad ne suka kira ta, sai wasu daga cikin abokan aikinta sai kuma Uncle Usman.










Ahmad ta fara kira saboda missed call ɗinsa ya fi yawa. Kamar jira yake ringing ɗaya ya yi rejected ya kira ta. Ta d'aga tare da yi masa sallama. Ya amsa tare da faɗin "Princess!" cikin sauke ajiyar zuciya da jan numfashi. Ta ce "Na'am Uncle, ina yini?" Ya ce "lafiya lau, jikin naki ne har yanzu?" Ya yi maganar cikin damuwa. Ta ce "Na ji sauƙi Uncle." Ya ce "Um,um Princess, sound ɗin muryarki ya tabbatar mun da baki da lafiya har yanzu, ko jikin ne ma nay ta kira baki pick ba." Ta ce "Ciwon kai ne, kuma na sha magani, time ɗin da ka kira ni kuma bacci nake." Ya ce "Oh God! Allah ya baki lafiya Princess sannu kin ji." Ta ce "Amin na gode Uncle, ina twins ɗina?" Ya ce "Suna nan k'alau, suna ta missing Auntinsu, da a cikin week ɗin nan zan kawo miki su, to kuma baki da lafiya, sai kin warke zan kawo su." Ta ce "Dan bani da lafiya baza ka kawo mun su ba." Ya ce "Eh mana, kar su zo su damar min ke." Cikin shagwab'a ta ce "Ni dai na warke, ka kawo mun su." Ya ce "Shikenan Princess zan kawo miki su, suna dawowa daga gidan Ammi, sun je can zasu kwanar mata biyu ne." Neehal ta yi murmushi cikin murna ta ce "Thank you." Ya ce "Uhm, ni fa na gane kin fi son yaranki da ni, da ni na ce zan zo baza ki yi wannan murnar ba." Ta yi murmushi mai sauti bata ce komai ba. Ya ce "Insha Allahu, inna samu chance gobe zan zo na ƙara duba jikinki." Ta ce "Uncle, Jiya fa ka zo, ka yi zamanka Please na ji sauƙi fa." Ya ce "In bakya son gani na ni ina son ganinki." Ta ce "I'm sorry ba haka nake nufi ba Uncle, na ga kana ta wahala...." Ya katse ta da faɗin "Babu wata wahala a zuwa ganin ki Princess, don't worry kin ji." Ta ce "Toh Shikenan Allah ya kawo ka lafiya." Ya ce "Ameen, sai ma in duba jikin naki da kaina in ga me yake damar mun ke haka." Ta ce "Kafin ma ka zo na warke Insha Allah." Ya ce "Allah ya amsa Princess." Daga haka suka yi sallama ya ce bari ya barta ta huta tunda bata jin daɗi. Bayan ya katse kiran ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, ta san dama by now yana gurin aiki. Uncle Usman ta kira, yay mata ya jiki da nuna jin daɗin sa akan hukuncin da kotu ta yanke akan su Bilyaminu, dan sun yi waya da Uncle Umar ya sanar masa da komai. Bayan sun gama wayar da shi ta bibbi bayan sauran missed calls ɗin da akay mata.








Bayan Sallar Magriba Haneefah suka zo gidan ita da Mijinta Faruq, ta ƙara kyau abinta kana ganinta ka ga amarya. Mama ta tarbe ta cikin mamakin ganin ta tana faɗin "Yau Amarya ce a gidan namu?" Haneefah tana murmushi ta ce "Ni ce Mama, dama ina so in zo muku sallama jibi zamu wuce Kogi, ga kuma rashin lafiyar Besty, shine na ce mu zo yanzu kawai na duba jikin nata." Mama ta ce "Har tafiyar ta zo? Sai yaushe kuma zaku dawo?" Haneefah ta ce "Sai week ɗin da za'ai resuming School." Mama ta ce "To Allah ya kiyaye hanya, ki hau sama tana ɗakinta." Ta amsa sannan ta wuce upstairs. Tana kwance rigingine tana latsa waya Haneefah ta shigo ɗakin da sallama. Ta d'ago kanta da sauri ido waje ta ce "Amarya!" Haneefah ta ce "Na'am Ango." Neehal ta tashi zaune tana murmushi ta ce "Welcome dear." Haneefah ta zauna a bakin gado kusa da ita ta ce "Yawwa ya jikin naki? Gaskiya kina jin jiki Besty duk kin rame." Neehal ta ce "Da sauqi, ai na yi kyan gani ma yanzu." Haneefah ta ce "Sannu, Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne." Ta ce "Amin ƙawata, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce "Yana cikin Mota, tare muka zo." Neehal ta ce "Shine kuma kika bar shi a waje, ki ce ya shigo mana." Ta ɗauko wayarta a jaka ta kira shi ta ce ya shigo ciki. Neehal ta ce "Ko ke fa, ya amarci?" Haneefah ta ce "Mu sauka ƙasa ki tambayi Ya Faruq zai baki amsa." Neehal ta yi murmushi. Sun ɗan taɓa hira Haneefah ta sanar mata tafiyarsu Kogi, Neehal ta musu fatan sauka lafiya. Sannan suka sauka ƙasa inda suka tarar da Ya Faruq da Mama suna hira. Haneefah ta ɗauki juice ɗin dake gaban Ya Faruq tana duban Mama cikin zolayarta ta ce "Mama shi ne ni ba'a kawo mun ba sai shi?" Mama ta ce "Ɗana kawai na sani, ke ai gidan ba baƙon ki ba ne." Haneefah ta ce "Allah sarki ni Mama ta daina yina yanzu." Faruq ya yi murmushi tare da yiwa Haneefah gwalo a fakaice. Sannan ya dubi Neehal suka gaisa yay wa Neehal ya jiki yana tsokanarta gawa ta ƙi rami. Ana kiran sallar isha'i suka tafi saboda daga nan gidan iyayen Faruq za su biya. Bayan fitarsu Mama ta zubowa Neehal abinci ta tilasta mata ta ci, tunda ta ji sauƙi har tana iya surutu abincin ma zata iya ci. Tana tutturo baki ta fara cin abincin kamar bata so, kaɗan_kaɗan take tsakurar sa tana kaiwa baki kamar mai irgawa, gashi Mama ta ce sai ta cinye wanda ta zubo mata duka. Tana zaune ita kaɗai a falo fiye da mintuna ashirin akan abincin da ba wani yawa ne da shi ba, Ameen da Hajiya suka shigo Falon. Hajiya ta ce "Ke kaɗai ina Faɗiman? ta bar ki ke kaɗai kuma ke da ba lafiya ba" Ciki_ciki ta ce "Tana sama." Hajiya ta ce "To ya jikin naki?" Ta ce "Da sauqi." Hajiya ta ce "Ke gashi kin warware, ita kuwa waccan da na je dubowa tunda na je tana nad'e akan gado, sai masu aiki ne ke ta kai kawo." Neehal ta saci kallon Ameen wanda ya zauna akan kujera yana kallon Hajiya. Ta mayar da duban ta ga Hajiyan ta ce "To ai bata da lafiya ne." Hajiya ta ce "Duk da rashin lafiyar, amma kuma da rakin tsiya ma, sai langwab'ewa take kamar lagwani." Neehal ta ce "Dan ciwon ba'a jikin yake ba dole ki ce haka." Hajiya ta wuce sama bata tanka ba. Ameen ya tashi ya koma hannun kujerar da Neehal take kai ba tabo ba fallasa ya ce "How was your body?" Kanta a ƙasa ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Na ga kin ji sauqi har da magana haka." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsat?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, ka yi mata sannu." Idansa akan abincin da take ta juyawa da spoon ya ce "Zata ji." Suka yi shiru dukan su, ita bata cigaba da jin abincin ba, shi kuma ya zuba mata ido. A hankali ta ji ya ce "Ki ajiye abincin mana idan kin k'oshi." Ta ɓata fuska cikin shagwab'a ta ce "Mama ta ce dole sai na cinye, kuma da ƙyar nake ci bakina babu daɗi." Sai kuma ta kalli fuskarsa iya gaskiyarta ta ce "Yaya ka cinye sauran Please kafin ta sauko." Ya ce "Uhm, jagwalgwalon naki zan ci?" Ta kalli abincin dan ita bata ga wani jagwalgwalawa da ta yi ba, ta turo baki ta ce "Taimakona fa zaka yi Please." Ya yi wani ɗan murmushi ya ce "Sai dai in zaki bani a baki." Ta kalle shi da sauri ta ga fuskarsa babu alamun wasa ya sha mur, kamar bashi ya gama maganar yanzu ba." Ta yi shiru ta rasa me zata ce, shi kuma ya tab'e baki irin zaɓi ya rage natan nan." Jin taku ta d'aga kai ta kalli steps, ganin Mama ce ke saukowa sai ta ɗibi abincin ta kai baki tana yamutsa fuska kamar mai cin kashi. Mama ta dube ta bayan ta ƙaraso cikin falon ta ce "Tashi ki kai kitchen ki rufe, cin ɗan wannan abincin fiye da 30 minutes kamar mai cin gandar da bata gama dahuwa ba." Ta miƙe da sauri ta nufi kitchen ɗin. Ameen ya raka ta da ido. Mama ta ce masa "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya ƙara sauƙi, da safe Insha Allahu zamu zo ni da Dad mu duba jikin nata." Ya ce "Allah ya kai mu." Daga haka ya miƙe yay mata sallama ya tafi. Bayan Neehal ta yi Sallah suka yi waya da Sadik, sannan ta kwanta. Kafin ta kai ga yin baccin Mama ta shigo ta yi mata allura wanda da ƙyar ta bari aka yi dan bata son allura ko kaɗan, gwara ta sha magani duk da shi ma ba wani son shi take ba, amma duk da gwara shi sau dubu akan allurar.

Please Login or Register in order to submit comment