Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubanta ta amsa mata sallamar, "Amarya ke ce a gari yau? inji maƙi baƙo." Haneefah ta ce "Ni ce nan, na zo mu yi wata magana ne, da zan bari sai gobe sai kuma kawai na ce bari in zo tunda babu abun da nake yi yanzun." Neehal ta ce"Gwara da kika zo ai, Ya Mommy?" Haneefah ta ce "Tana nan k'alau." Suka ɗan taɓa hira kafin Neehal ta ƙarasa gugar sannan ta koma bakin gado kusa da Haneefah ta ce "Wacce maganar zamu yi Besty?" Haneefah ta ce "Akan Sadik ne." Neehal ta ɓata fuska ta ce "Me ya faru?" Haneefah ta ce "Yanayin da kika koma yanzu shi ya tabbatar mun da kin san koma menene." Neehal ta ce "I don't know any thing." Haneefah ta ce "Any way dai, Jiya Sadik ya zo gida ya same ni and he told me duk yanda kuka yi, wanda kin fini sani ba sai na ƙara maimaita miki ba, amma Neehal na tambaye ki mana." Neehal ta ce "Ina jin ki." Haneefah ta ce "Me yasa kika yi ignoring ɗinsa? Ko kin manta Sadik ɗin ne?" Neehal ta ɗan tab'e baki ta ce "Saboda bana buƙatar sa a cikin rayuwata." Haneefah ta yi ɗan murmushi ta ce "Bakin ki dai ya furta haka, amma fuskarki da yanayinki sun tona asirin zuciyarki. Neehal kina son Sadik! Kuma kema kin sani." Neehal ta yi shiru saboda ba ta san me zata ce ba, sai ma k'walla data cika mata ido. Haneefah ta cigaba da magana "Ina lura dake a kwanakin nan walwalarki ta ragu sosai, kuma na san duk akan haka ne. Amma Sadik yana da wani aibu ne da ba za ki iya soyayya da shi ba? Ko kuma yana da wani halin ne mara kyau da kika fuskanta wanda mu ba mu sani ba?" Neehal ta girgiza kai cikin karaya ta ce "Ko ɗaya." Haneefah ta ce "To me yasa ba za ki yi accept ɗinsa a cikin rayuwarki ba? Wallahi Neehal baki ga yanda Sadik ya koma ba, gaba-ɗaya ba ya cikin nutsuwarsa, kuma duk saboda ke ne." Haneefah ta sassauta murya ta ce "Please Neehal dan Allah ki amincewa Sadik ku yi soyayya, ki tausaya masa ke ma kuma ki bawa zuciyarki abun da take so, kar ki cutar da ku dukanku." Neehal tana hawaye ta ce "I can't, ba zan iya ba Haneefah, na san ina son Sadik amma ba za mu yi soyayya ba, bana son na kuma yiwa iyayen kowa asarar ɗansu. Haneefah na rufe babin soyayya a rayuwata, ba zan ƙara soyayya da kowa ba!" Cike da tausayawa Haneefah ta ce "Kar ki yi haka Neehal, na sha faɗa miki ki daina faɗar irin wannan maganar, ke a karan kanki kina faɗar haka idan wani ya ji ya samu abun ɗorarwa fa?" Neehal ta ce "An yi na farko an yi na biyu, idan aka yi na uku Haneefah dole hankalin mutane zai dawo kan al'amarin, ko na faɗa ko ban faɗa ba, dole za a fara faɗar maganganu a kai na, ko so kike duk inda na yi a dinga nuna yi ana gata can, duk wanda zata aura sai ya mutu, sai....." Haneefah ta rufe mata baki ta ce "Insha Allahu haka ba zata faru ba, in Allah ya yarda za a yi auranku da Sadik lafiya babu abun da zai faru. Ke dai ki miƙawa Allah al'amuranki, sannan ki dage da addu'a. Su ya Ammar ma kwanansu ne ya ƙare a duniya, amma ba wai dan ke aka kashe su ba." Neehal zata yi magana Haneefah ta katse ta da faɗin "Dan Allah Neehal kar ki ɗauko abun da baki da tabbas akai ki saka a ranki Please!" Neehal ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, sai kallon ƙanwartata kawai take tana hawayen tausayin kanta. Haneefah ta baibaye Neehal da kalamai masu kwantar da hankali gami da wa'azin da ya ratsa mata zuciyata. Ta nuna mata babu wani mahaluƙi da ya isa ya maka abun da Allah bai maka ba. Neehal ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi, kuma ta ji zata karb'i Sadik a matsayin masoyi a karo na uku a rayuwarta. Sai dai wani ɓangaren na zuciyarta cike yake fal da tsoro da fargabar rashin sanin abun da zai biyu baya a soyayyar tasu. Za su yi Aure da Sadik ɗin ne kamar yadda Haneefah ta faɗa ko kuma shima za'a kashe mata shi ne?..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:51] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*3️⃣7️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














...........Sai da Haneefah ta tabbatar da bayananta sun shiga Neehal kuma sun ratsa ta sosai sannan ta miƙe dan tafiya gida tana faɗin "Mu je in yiwa Mama Sallama na ga magriba ta taho." Neehal ta shagwaɓe fuska ta ce "Ki bari ki yi sallah mana." Haneefah ta ce "Tafiya zan yi, zan je in yi girkin dare." Neehal ta ce "Please dear!" Haneefah ta ce "Ikon Allah, to ki adana shagwab'arki idan yaya Sadik ya zo sai ki yi masa, amma bani zaki wa ba." Ta ƙarashe zancen da dariyar tsokana. Neehal ta ɓata fuska ta ce "Na ji ɗin zan masa." Suka fita daga ɗakin Haneefah tana ta tsokanarta. A ɗakin Mama suka tarar da twins suna cire uniform. Haneefah ta ce "Ashe kun dawo yanzu nake shirin tambayar su." Mama ta ce "Yanzu nan aka ɗauko su." Twins suka gaishe da Haneefah ta amsa, Afrah ta cewa Neehal "Aunty zamu biki." Neehal ta harare ta ta ce "Sarakan son yawo, to ba fita zan yi ba." Amrah ta kalli Haneefah ta ce "To Aunty ke zamu biki." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ku saka kaya sai mu tafi." Suka shiga tsallen murna, Mama ta ce "Babu inda za su Assignment za su yi." Lokaci ɗaya Suka ɓaɓɓata fuska kamar za su yi kuka. Neehal ta ce "Don't cry My babies, gobe zan kai ku unguwa." Sai suka saki ransu suka ci-gaba da sabgarsu. Haneefah ta dubi Mama ta ce "Mama zan wuce, sai da safe." Mama ta ce "Allah ya kai mu, ki gai da gida da Mominki, Insha Allah kafin tafiyarmu Saudiyya zan zo gidan naku." Neehal ta marairaice ta ce "Wai Mama baza ki tafi da ni ba?" Mama ta ce "In na tafi dake Neehal mu bar yaran nan a ina? Kuma ga makarantarki ma, ki bari Lokacin Hajji idan Allah ya kai mu sai ki je indai kun yi hutun school." Haneefah ta ce "ki ƙyale ta Mama, rigima ce kawai ke damunta, yaushe ne tafiyar taku?" Mama ta ce "Biyar ga azumi Insha Allah." Haneefah ta ce "Allah ya kai mu, sannan ta yiwa Mama Sallama suka fice ita da Neehal wadda zata ɗan taka mata. Bayan Sallar Magriba Neehal ta yiwa Sadik text kamar yadda suka yi da Haneefah zata masa.






A ɓangaren Sadik kuwa tun ranar da ya yiwa Neehal text bata masa reply ba kuma yana kiranta bata ɗauka, sai hankalinsa ya tashi. Gaba-d'aya ya ji duniyar ta masa zafi, ga wani sabon son ta dake ƙara mamaye masa zuciya da gangar jiki. Cikin kwanaki kaɗan ya rame saboda damuwar da ya saka a ransa. Hotunan Neehal su suka zama abincinsa, dan kodayaushe cikin tasa wayarsa a gaba yake yana kallon pics ɗinta. Duk wani program da take a gidan TV kuwa ba ya wuce shi. Mahaifiyarsa ta tambaye shi me yake damunsa haka duk ya fita daga hayyacinsa? Sai ya ce mata "Wani case yake ne mai wahala, ta taya shi da addu'a kawai." Ganin abun Neehal bana ƙare ba ne shine jiya ya shirya ya je gidansu Haneefah, ya faɗa mata duk abun da ke faruwa, Haneefah ta kwantar masa da hankali ta ce zata je ta samu Neehal ɗin, kuma ta san ta yanda zata ɓullo mata kar ya damu. To bayanin Haneefah ne ma ya ɗan kwantar masa da hankali. Yau kuma yana masallaci ya ji message ya shigo wayarsa, ya yi zaton ma kamfani ne amma da ya duba sai ya ga Neehal ce ta turo masa. Jikinsa har rawa yake yi wajen shiga ya karanta message ɗin zuciyarsa cike da fargaba. Wani sanyi ya ji ya ratsa zuciyarsa gami da farin ciki mara misaltuwa ganin abun da Neehal ta turo masa, a fili ya furta Alhamdulillah yana sakin murmushi shi kaɗai. Duk wannan murnar da Sadik yake ba fa wani abu Neehal ta ce masa ba a cikin text ɗin. Ta tambayi lafiyarsa ne kawai, a ƙarshe kuma ta nuna tana son ganinsa Yau idan babu damuwa. Amma shi a gurinsa hakan alamun nasara ne, dama tun d'azu zaman jiran kiran Haneefah yake domin ta sanar masa yadda suka yi da Neehal ɗin, sai kuma ya ga text ɗin Neehal ɗinma a lokacin da bai taɓa tsammani ba. Cikin sauri ya tashi ya nufi gida, jikinsa har rawa_rawa yake dan zumud'i. Shaf_shaf ya shirya cikin wani yadi milk colour ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin k'amshi ya fito ya ɗauki hanyar gidansu Neehal.








Itama Neehal ɗin ba'a barta a baya ba, wanka ta yi ta shirya cikin wata gown purple colour wanda ta zauna das ajikinta, ta kuma haska farar fatarta. Ta shafa powder a fuskarta gami da White lipsticks a lips ɗinta. Ta yi kyau sosai fuskarta sai annuri take, ita kanta ta san She Missed him over, zuciyarta cike take da d'okin ganin kyakkyawar fuskarsa ɗauke da murmushinsa da ba ya rabo da shi kodayaushe. Tana jin wayarta ta yi ƙara ta ji gabanta ya ɗan faɗi, kamar yadda ta yi zato tana dubawa ta ga shine, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga amma ba ta ce komai ba. Lumshe idonta ta yi tana sakin ajiyar zuciya a hankali jin muryar Sadik yana mata sallama, a sanyaye ta amsa masa masa. Yana jiran ta a waje kawai ya sanar mata sannan ya kashe wayar, kamar ya san kuwa da ya ce wani abun ba zata iya ce masa komai ba. Ta yafa mayafinta sannan ta fito falo, anan ta tarar da Mama ta tasa su Amrah a gaba suna Assignment. Kanta a ƙasa ta ce "Mama zan sauka ƙasa Yaya Sadik ya zo." Mama ta bita da kallo sannan ta ce "Okay ki gaishe shi." Su Afrah sarakan son yawo suka bi ta da kallon a tafi da su, Neehal tay murmushi ta shafi kuncinsu sannan ta fita. Inda suke zance da Anwar ta saka aka kai musu kujerun roba, tunda yau Sadik ɗin ya ƙi shigowa falo. Allah sarki rayuwa har ta tuna da sanda Anwar yake zuwa zance, ta hango zuwansa na ƙarshe gidan, sai ta ji zuciyarta ta mata rauni kamar zata yi kuka. Sai da ta mayar da k'wallar data tarar mata a ido sannan ta ƙarasa gurin cikin sanyin jiki. Tun da ta taho ya ƙura mata ido cikin shauƙin k'aunarta yana sakin ajiyar zuciya. Sai ya ga kamar ta ƙara kyau da iya tafiya a kwana biyun da bai ganta ba. Kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da yin Sallama cikin siririyar muryarta. Sadik ya amsa mata cikin kulawa da k'auna yana jifanta da wani irin kallo da murmushin nan nasa manne a kan fuskarta. Ta zauna cikin tsananin jin kunyarsa akan abun da ta yi masa, kuma dama can ita naturally ɗinta tana da jin kunyar wanda take so. A hankali ta ce "Ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau sarauniyar birnin zuciyar Sadik." Ta ɗan kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba, sai ta ga ya ɗan rame duk da manyan kaya ya saka. Tausayinsa ta ji ya cika mata zuciya. Ganin yanda ta takure ta hana kanta sakewa sai Sadik ya fara da zolayarta da ya saba, har ya samu ta ɗan fara sakin jiki amma duk da haka ta ƙi d'ago kanta ta kalle sa. Cikin sanyin murya ta ce "Dan Allah Yaya Sadik ka yi haquri da abunda na maka, nima ba son raina ba ne, sai dan wani dalilin daban." Sadik ya yi murmushi mai sauti ya ce "Kar ki damu Neehal, tun farko dama na fahimce ki kuma na san haka zata faru, dan haka wannan ba komai ba ne, ki manta kawai. Alfarmar da kika mun ma har na samu ganin kyakkyawar fuskarki a yau ya tabbatar mun da ina wani matsayi a gare ki, ko da kuwa matsayin mai goge miki takalmin ƙafarki kika bani zan yi farin ciki da hakan." Neehal ta d'ago da sauri ta kalle sa, ya kashe mata ido ɗaya wanda yasa ta ji tsigar jikinta ta ɗan tashi hakan yasa ta yi saurin mayar da kanta ƙasa. Ya cigaba da magana da faɗin "Kina mamaki dan na ce miki ko da matsayin mai goge miki takalmi nake a gurinki zan yi farin ciki sosai da hakan? Neehal a yanda nake jin sonki a cikin zuciyata ko da bawanki kika mayar da ni zan yi farin ciki da hakan sosai, ni indai zan kasance dake a kodayaushe ina ganin kyakkyawar fuskarki to zan yi farin ciki gami da alfaharin haka." Neehal ta ce "Haba Yaya Sadik ka daina faɗar haka, matsayin da kake da shi a gurina kafi ƙarfin na mulke ka sai dai kai ka mulke ni." Cikin jin daɗin kalamanta ya ce "Are you Sure! Neehal matsayina har ya kai haka agurinki?" Ta yi murmushi tare da rufe fuskarta da hannunta. Kafin Sadik ya tafi yau sai da suka gama fuskantar junansu yanda ya kamata, har tahirinsa ya bata a tak'aice. Har sai da Mama ta kira ta a waya sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya ce ta gaishe da Mama, tun da a suruki ya zo gidan yau ya ƙi shiga ciki.










Soyayya sosai Neehal da Sadik suke, Haneefah kuwa ta samu abun tsokanarta, matar Barrister ma ta koma ce mata. Mama ma tana lura da ita a kwanakin nan Sadik ya bar Friend or brother ya koma Habibi. Ta kuwa ji daɗin hakan sosai, sai ta ƙara dagewa da k'aimi gurin yi musu addu'a akan Allah yasa Sadik shine mijin Neehal. Sadik ya iya tafiyar da mace yanda ya kamata, ga tarin kyautatawa da daɗaɗan kalamai wanda suke ƙara dulmiyar da Neehal a kogin k'aunarsa. Ranar Asabar ta kasance ranar farin ciki ga kowane musulmin duniya, saboda tashi da azumin watan Ramadana mai girma da ɗaukaka da akai. Ranar da aka ɗauki azumi na Shida su Mama suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki ita da Aunty Sadiya dan yin Umrah. Gidan Aunty A'isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, wannan karon har da su Dije suka tafi. Mama ta yi addu'a sosai a gaban ka'aba akan Allah ya kawo ƙarshen ƙaddarar Neehal gami da tona asirin duk masu hannu a kisan su Anwar............












*THREE MONTHS LATER*










Neehal ce ta fito cikin shirinta na tafiya school, a kitchen ta tarar da Mama tana yin lunch, ta cewa Maman. "Mama zan tafi school." Mama ta ce "Har kin gama karatun?" Da yake Neehal ɗin sun fara exam ɗin second semester level three. Ta ce "Eh, na ga 2 ta wuce, kuma ƙarfe 3 zamu shiga exam ɗin. Mama ta ce "Allah ya kiyaye ya ba da sa'a, ki biya fa ki dubo Yayanki kar ki manta." Neehal ta ce "Zan je Insha Allah, zan kira Haneefah ma idan tana free sai mu je tare, idan ma tana School ɗin sai mu wuce ta can kawai." Mama ta ce "Shikenan ki masa sannu." Neehal ta ce "Zai ji." sannan ta juya ta tafi. Kamar kodayaushe tsawon watanni ukun nan da suka wuce kullum Neehal ta fita sai Motar nan ta bita a baya, idan zata school,aiki,shopping da unguwa duk tana biye da ita a baya. Ita har mamakin ma yanda mai Motar yake sanin time ɗin fitarta dana dawowarta take sai ka ce aljani. Kuma har yau bata taɓa faɗa wa kowa ana bin ta ba, Ubangijinta kawai take faɗawa, dan babu mai bata kariya sama da tasa. Bata son kuma ta d'agawa Mama hankali shi yasa bata faɗa mata ba, duk da a zahirin gaskiya a tsorace take da bin ta da ake yi ɗin. Watarana ta kai su Afrah shopping a hanyarsu ta dawowa motar tana bin ta sai ta ce a ranta bari ta gwada wani abu. Parking ta yi a gefen titi ta kulle su Afrah a cikin motar sannan ta shiga wani shago da ake sayar da zobuna da agogo, ta ɗauki zobe ɗaya ta siya duk da bata fito da niyyar hakan ba. Bayan ta fito daga shagon ta kalli titi ta bayanta ko zata ga motar nan amma bata ganta ba. Amma abun mamaki bayan ta shiga tata motar bata fi 3 minutes da fara tafiya ba ta hango motar tana bin ta a baya. Hakan ya tabbatar mata da abun da take tunaninta akan wani ne yake bibiyarta, kuma koma waye Allah ya fi shi.










Ƙarfe huɗu ta fito daga exam ɗin kuma Alhamdulillahi ta mata sauƙi, masallaci ta nufa ta yi sallah sannan ta kira Haneefah dan su je su dubo Ameen dake fama da zazzaɓi. Haneefah ta sanar mata bata gida sun fita kasuwa da ƙanwar Mommy, kasancewar bikinta ya gabato saura sati uku, dan ma exam ɗin da suka fara ne da tuni an yi bikin. Yanzu sai bayan Babbar Sallah da sati biyu za'ayi. Sallama Neehal ta yiwa k'awayenta ta tafi. Sai wajen biyar ta ƙarasa gidan. Babu kowa a falon ƙasa hakan yasa ta nufi sama, a nan ta tarar da k'awayen Hafsat su uku zaune a falo. Ta musu sallama ta shiga, suka amsa suna bin ta da kallo. Ta zauna a kujera sannan ta gaishe su. Cikin fara'a Fadeelah ta ce "Laa Neehal ke ce, ai ban gane ki ba da farko sai yanzu." Neehal ta yi murmushi ta ce "Aunty Hafsan tana ciki ne?" Fadeelah ta ce "Eh wanka take, ki shiga Yayan naki yana cikin ɗakinsa." Neehal ta ce "Toh." Tare da miƙewa ta shiga ɗakin. Ɗaya daga cikin k'awayen Hafsat ta ce "Wannan yarinyar kamar mai aiki a ASTV ko?" Fadeelah ta ce "Ita ce, ƙanwar Ameen ce fa." Wadda tai maganar ta ce "Allah sarki, Ni kam tana burgeni, yarinyar a nutse take bata da rawar kai." Fadeelah ta ce "Ga ta da kirki wallahi so friendly babu ruwanta."










Neehal ta tura ƙofar ɗakin Ameen a hankali bakinta ɗauke da Sallama, k'amshinsa ne ya fara mata Welcome. Yana kwance akan gado jikinsa sanye da jallabiya brown colour idanunsa a lumshe. Neehal ta ƙarasa ta zauna akan bedside locker tana kallonsa cikin tausayawa, ya ƙara haske kuma ya ɗan faɗa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa ta ji jikin nasa da zafi, a tunaninta bacci yake. Ta zare hannunta a hankali daga jikinsa ta ce "Allah ya baka lafiya Yayana." A hankali ya buɗe lumshashshun idonsa ya sauke su a kanta. Ta ce "Yaya! Sannu, ya jikin?" Bai amsa mata sai tashi zaune da ya yi yana taune lips ɗinsa. Cikin murya mara sa lafiya ya ce "Yaushe kika zo?" Neehal ta ce "Yanzu na zo, ya jikin naka?" Ya ce "Da sauƙi, ina Mum?" Ta ce "Tana gida daga school na biyo ta nan." Ya jinjina kansa tare da lumshe idonsa, daga gani babu tambaya ka san yana jin jiki. Neehal ta ji duk hankalinta ya tashi dan baza ta iya tuna sanda ya kwanta ciwo irin haka ba, hannun damansa ta kalla ta ga abun ƙarin ruwa alamun ya sha drips. Kamar zata yi kuka ta ce "Yaya me yake damunka? Mama ta ce mun zazzaɓi kake, kuma na ga kamar ba iya zazzaɓin ba ne kawai." Kafin Ameen ya bata amsa wayarta dake cikin jakarta ta fara vibrate, ta zuge jakar ta ɗauko wayar tare da d'agawa ganin Sadik ne. "Hello Yaya Sadik." Jin haka yasa Ameen ya juyo da sauri ya kalle ta, ta ce "Eh na dawo, ina gidan Yaya na je duba shi." Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce "Tom sai ka zo." Tare da kashe wayar. Ameen ya mayar da idansa ya lumshe a hankali ya ce mata "Bani ruwa." Da sauri ta ɗauko ruwan dake gaban gadon ta buɗe sannan ta tashi ta miƙa masa tare da faɗin "Sannu Yaya Allah ya sauwaqe." Ya d'aga mata kai tare da karɓar ruwan ya sha. Ganin yanda ta damu sai ya kamo hannunta a cikin nasa yana kallon fuskarta ya ce "Menene?" Ta yi ƙasa da idonta ba ta ce komai ba, ya d'ago hab'arta da ɗayan hannunsa ya ce "Don't cry." Dan ya san halinta, ai ko kamar zugata ya yi sai ta fara hawaye, ita haka Allah ya halicce ta idan ta ga mutum ba shi da lafiya duk sai ta ji ta damu sosai, musamman ma Yayan nata da take jin kamar ta mayar da ciwon nasa jikinta. Ya ɗan tauna lips ɗinsa murya ƙasa_ƙasa ya ce "Kukan na mene?" Ta ce "Yaya baka da lafiya, na ga duk ka rame." Ya ce "Ai na ji sauƙi, kuma soon zan warke Insha Allah." Ta gyaɗa masa kanta. Ya yi ɗan murmushi sannan ya shiga goge mata hawayen fuskarta da tattausan tafin hannunsa ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da hannunta har lokacin. Dai_dai time ɗin Hafsah ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:52] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*3️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












..........Turus ta tsaya a bakin ƙofar cikin shock, wani abu mai tsananin ɗaci ya tsaya mata a mak'oshi, dama a fusace ta taho saboda Fadeelah ta sanar mata Neehal ta zo tana cikin ɗakin, sai da ta mata masifar me yasa zata bar wata ta shigar mata ɗakin miji sannan ta taho ɗakin. Neehal ta yi ƙoƙarin zame hannunta daga cikin na Ameen jin ƙarar buɗe ƙofar ɗakin, kuma ko tantama ba ta yi Hafsat ce, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma ƙara matse hannunta yake a cikin nasa duk da shim ya ji shigowar Hafsan. Sai da ya goge mata hawayen fuskarta tass sannan ya saki hannunta yana murmushi ya ce "Mommy's girl, rigimammiya kawai." Neehal ta koma kan bedside locker ta zauna ta turo ɗan bakinta gaba. Duk yanda Hafsah taso daurewa kasawa ta yi, sosai fuskarta ta nuna ɓacin ranta. Ta janyo ƙafarta data ji ta mata wani iri tana bankawa Neehal harara ta ƙaraso cikin ɗakin, ji take kamar ta janyo ta ta shak'e ta dan tsananin ƙiyayyarta da take ji a ranta. Neehal ta dube ta da murmushi akan fuskarta ta ce "Ina yini Aunty Hafsah." Kamar an mata dole ta amsa da faɗin "Lafiya." Neehal ta ce "Ya mai jiki?" A ranta ta ce ''Gashi nan a gabanki ai, kin ga jikin nasa munafuka' Amma a fili sai ta ce "Da sauqi." Daga haka Neehal ta ja bakinta ta tsuke sai ma ƙoƙarin tashi da ta yi dan ta ba su guri. Hafsah ta ɗan saki fuska ta zauna a kan gadon ta kai hannunta jikin Ameen wanda idanunsa ke lumshe ta ce "Baby ya jikin naka?" Ameen ya buɗe idanunsa ya kalli Neehal ba tare da ya amsa mata ba, ya ce "Ki bata abinci, daga school take." Neehal ta miƙe ta ce "No Yaya am full." Wani kallo ya wurga mata wanda yasa ta yin ƙasa da kanta. Hafsah ta had'iye wani malolon baƙin cikin da ya tsaya mata a mak'oshi, 'wato ba ma zai amsa mata magana ba, sai ma bata umarnin da bawa wata banzar yarinya abinci. Amma da yake makira ce sai ta dake kamar ba ta ji komai ba. Cikin kissarta ta

Please Login or Register in order to submit comment