Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tsorata ta yi baya. Da sauri ya buɗe murfin Motar ya fito, da mamaki ya ce "Princess." Neehal ta washe baki ta ce "Uncle ɗina ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, me yasa kwana biyu ba kya zuwa." Neehal ta ce "Uncle ne ya hana ni, ya mun faɗa sosai, He said in aka ƙara aike na na daɗe sai zane ni." cikin rashin jin daɗi Ahmad ya ce "Ayya I missed you alot dear." Neehal ta ce "Me too Uncle." Ahmad ya ce "Mu je gida in baki cake da sweet ɗinki." Da murnarta ta ce "Toh." Yanayin garin damuna ta fara shigowa dan shekaran jiya ma an yi ruwa, yau ma garin ya yi luf kamar hadari_hadari. Gashashshiyar kaza Ahmad ya bata da yoghurt, Neehal ta zauna ta ci ta k'oshi tay hamdala. Mantawa ta yi da wani tsoron Uncle Umar ta zauna ta shiga yi wa Ahmad hira, shi kuma yana ta aikin murmushi cikin jin daɗi da nishad'i, sai yanzu da ya ganta ma ya ƙara tabbatar da ya yi kewar ta sosai. Kiran sallar la'asar ne ya tashe su, Ahmad ya yi alwala suka fita tare ya rakata ta siyi kayan miyan sannan ya wuce masallaci ita kuma ta nufi gida. Zuwa lokacin hadari ya ƙara haɗuwa sosai har an fara Iska, sauri Neehal tay ta yi kar ruwa ya sauko tana waje, aiko ana idar da Sallah aka fara yayyafi, da gudu ta ƙarasa gidan dan har ta fara jik'ewa, kitchen ta nufa zata ajiye kayan miyan amma sai ta tarar da shi a kulle da mukulli, ga ruwan ya fara ƙarfi. Ƙofar falon ta dawo ta fara bugawa da ƙarfi tana faɗin, "Aunty! Aunty, na dawo ki buɗen ƙofa!" Amma Fauziyya tana ji ta ƙi buɗe ƙofar, gashi kaf tsakar gidan babu gurin fakewa, dan ko toilet babu duka suna cikin ɗaki, kitchen ne kawai kuma ta kulle. Gashi irin gidan nan ne da kana buɗe gate ɗinsa sai tsakar gida babu soro. Haka Neehal ta takure jikinta cikin ruwan dan bata da yanda zata yi, cikin ikon Allah kuma ruwan ya tsuge kamar da bakin kwarya, Neehal ta runtse ido tana jin saukar ruwan ajikinta. A hankali kuma ya fara ɗaukewa, sai da ya ɗauke dif sannan Aunty Fauziyya ta buɗe ƙofar falon ta fito, Neehal na tsugunne a bakin ƙofar sai rawar ɗari take saboda sanyi ta ci kuka ta gode Allah. Aunty Fauziyya ta ɗauke kayan miyanta tare da faɗin "Kar ki shigar mun ɗaki kina yarari, ki jik'a mun ɗaki." Neehal ta miƙe ta cire komai na jikinta ta shanya a igiya, pant kawai ta bari sannan ta shige falon da sauri. Aunty Fauziyya tay dariyar mugunta ta ce "Gobe ma kya ƙara tafiya gantali Shegiyar yarinya kawai." Ita kam tana shiga ɗaki ta yi toilet ta cire pant ɗin jikinta ta rarumi towel ta ɗaura a jikinta sannan ta tsugunna ta yi fitsarin daya matse ta. Tana fitowa ta hau kan katifa ta ja bargonsu Aiman ta lullub'a. Aiko kafin dare mura ta mata mugun kamu, ranar da tari ta kwana. Washegari duk masifar Aunty Fauziyya ba ta saka ta aiki ba, dan jikin nata ya yi zafi ba kaɗan ba, ta san ma ko ta saka ta ba iyawa zata yi ba shi yasa. Amma ta sha zagi da masifa, a cewarta cutar ma ta ƙarya ce da shegen rakin tsiya. Kwana huɗu ta yi a kwance, a ran na biyar ne ta fara samun sauƙi, shi ma sai da Uncle Umar ya ga ciwon ya ƙi ƙarewa sannan ya kaita chemist aka bata magani, aiko suna tafe yana mitar ta ja masa asarar kuɗin da ya siya mata magani, maganin da ko 1K bai kashe ba, alhalin kuma dukiyarta da duk wata kadararta tana hannunsa. Bayan ta warware aka cigaba da aikenta, kullum sai sun haɗu da Ahmad amma ta daina shiga gidansu sai dai su haɗu a ƙofar gida, yasan lokacin da ake aikenta, dan haka time ɗin yana yi zai fito ƙofar gida ya zauna zaman jiranta, saboda ta bashi labarin dukan da ruwa ya mata har ya sata zazzaɓi akan ta daɗe ranar, shi kuma saboda tsananin tausayinta shi yasa ya daina tsayar da ita, dan kar a ƙara yi mata wata muguntar. Amma duk da haka bai daina bata abubuwan da yake bata abaya ba, idan ta je gurin mai kayan miyan akwai benci wanda dan customers aka tanade sa, anan take zama ta yi sauri ta cinye abun da ya batan sannan ta koma gida. Haka rayuwa tay ta tafiya da Neehal a gidan Uncle Umar cikin wahala da azaba kala_kala a gurin Aunty Fauziyya, gurin Ahmad kawai take jin daɗi, gashi ta yi magiyar a saka ta a makaranta an ƙi, har ta gaji ma ta dai na, sai ɗan lesson ɗin da Ahmad yake mata atsaitsaye.










Yau ma bayan Neehal ta gama shan ayyukanta tana zaune a kitchen tana juya miyar da Aunty Fauziyya take soyawa, ta shiga ɗaki ne shine ta ce Neehal ɗin ta cigaba da juya mata dan kar ta roqe. Wayar Aunty Fauziyya dake kitchen ɗin ce ta fara ringing, cikin ɗan daga murya Neehal ta ce "Aunty ana kiran ki a waya." Aunty Fauziyya bata amsa mata ba sai turo Aiman ta yi ya ɗauko mata wayar, kasancewar yau Friday ce suna gida. Aiman yaro ne mai k'iriniya baya abu cikin nutsuwa ko kaɗan, da gudu ya shigo kitchen ɗin ya ɗauki wayar, ya zo fita ya b'arar da taliyar da Aunty Fauziyya ta tace kafin ta bar kitchen ɗin, fiye da rabin taliyar ya zube a ƙasa. Neehal ta tashi da sauri tana faɗin "Ka ga ka yi ɓari ko?" Aiman bai saurare ta ba ya yi ɗaki da gudu yana kiran uwarsa, Aunty Fauziyya ta taso da sauri tana faɗin "Mene ne." Ya ce "Aunty Neehal ce ta b'arar miki da taliya." Ai bai ƙarasa ba Aunty Fauziyya ta fito a fusace ta shiga kitchen ɗin, Tafa hannuwa ta shiga yi tana faɗin "Eh lallai, tun da ba Ubanki ne ya nemo ba ba kuma Uwarki ce ta dafa ba ai dole ki b'arar." Neehal ta ce "Aunty ba fa ni na b'arar ba Aiman ne." Cikin tsawa Aunty Fauziyya ta ce "Rufe mun baki zaki ne bayani ne, shegiya mai baƙin hali, kwashe mun ita tass da hannunki, idan kin gama kuma ki zo ɗaki ki karb'i hukuncinki." Neehal ta sa hannu ta fara kwashe taliyar, ga taliyar sai tururi take saboda ba a daɗe da sauke ta ba, Aunty Fauziyya tana barin kitchen ɗin Neehal ta ɗauki serving spoon ta cigaba da kwashe wa da shi, saboda hannunta zafi. Sai da ta kwashe duka sannan ta debo ruwa ta d'auraye ta. Ɗakin ta nufa cikin tsoro ta ce "Aunty na gama." Aunty Fauziyya tay wani murmushi ta ce "To ƙaraso mana kika tsaya a bakin ƙofa." Cikin ɗari ɗari Neehal ta ƙarasa idanunta taf da ruwan hawaye. Aunty Fauziyya ta kamo hannunta, kuka ta saka ta ce "Aunty dan Allah ki yi haquri." Aunty Fauziyya ba ta kula ta ba, ta kamo hitar data jona a jikin socket ta ɗora a ƙafar Neehal. Wani irin zirrrrr Neehal ta ji ajikinta na shock ta ji kamar an d'aga ta sama. Ai bata san sanda ta k'wala ihu mai ƙarfi ba tare da fizge jikinta ta fice daga Falon da mugun gudu, gaba-d'aya jikinta rawa yake kamar mazari, cikin fitar hayyaci ta fice daga gidan gaba-d'aya, gudu take da dukkan ƙarfinta gani take kamar Aunty Fauziyya ta biyo ta zata ƙara sa mata shock ajikinta. A ƙofar gidansu Ahmad sukai cikibus, ya dawo daga masallaci da Darduma a hannunsa. Neehal ta ƙarasa gare shi ta riƙe shi gam tare da sakin kuka, har lokacin jikinta rawa yake. A ruɗe Ahmad ya shiga kiran sunanta "Princess! Princess what happened to you?" Yana ƙoƙarin d'agota daga jikinsa, ita kuwa ƙara k'ank'ameshi ta yi. Fahimtar da ya yi a firgice take sai kawai ya sunkuce ta ya shiga cikin gidan da ita. A kan kujera ya kwantar da ita, cikin kulawa ya ƙara tambayar ta da faɗin "Princess mene ya faru? kika fito ko takalmi babu a ƙafarki." Cikin kuka ta ce "Un... Uncle shocking Aunty ta samun a jikina." A ruɗe ya ce "Subhanallah shocking kuma Princess?" Bai jira amsar ta ba ya miƙe da sauri ya nufi ƙaramin kitchen ɗin dake falon ya ɗauko gwangwanin pick milk ta ruwa ya fasa ya juye ta a glass cup, sannan ya fito ya dawo gurin da take a kwance tana ta sauke numfarfashi. Ɗago kanta ya yi ya kafa mata cup ɗin a baki. Ba musu ta shiga sha. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta lumshe idanunta ta koma ta kwanta, Ahmad nata jera mata sannu cikin tsananin tausayinta. Ranshi ba ƙaramin ɓaci ya yi ba yau game da Aunty Fauziyya, ya rasa matsayin da zai ajiye matar akan rashin imani, da Mamy zata ji maganar nan yanda take da zuciya ya san tsaf zata iya kaita a kulle. Ƙura mata ido ya yi da idanunsa da suka fara canza launi saboda ɓacin rai, yana jin wani abu na fizgar zuciyarsa game da Neehal ɗin. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta akai_akai alamun bacci ya ɗauke ta, gyara mata kwanciya ya yi yanda zata fi jin daɗin baccin. Babbar damuwar Ahmad a duniya ɗaya ce a halin yanzu, jibi Sunday zai koma gidansu Abuja, tun last week ya gama abun da ya kawo shi Kano, amma saboda Neehal ya kasa koma wa gida, gashi parent ɗinsa sun matsu ya dawo, kasancewar shi kaɗai ne ɗansu Namiji, dama su biyu ne a gurin iyayensu daga shi sai ƙanwarsa mace, ƙanwar tashi ma ƙarama ce bata fi 4_5 years ba, 20 years ya bata. Sai bayan la'asar Neehal ta farka, ya je masallaci ya dawo ya tatar ta tashi. Ya ƙarasa kusa da ita ya ce "Kin tashi." Ta ce "Ehh, Uncle ka kai ni gurin Mamy na yi wanka, jikina babu daɗi." Ya ce "Mamy bata nan, amma bari na kai ki ki yi anan." Ta ce "Toh." Toilet ɗin dake cikin bedroom ɗinsa ya kai ta, Brush ya bata sabo da MacLean ta wanke bakinta, sannan ya haɗa mata ruwa mai dumi ta yi wanka. Bayan ta shirya ya kawo mata abinci da drinks ta zauna ta ci. Tana gamawa ta ce "Uncle Thank you so much." Tattausan murmushinsa ya mata ya ce "Say Alhamdulillah." Itama murmushin ta masa ta ce "Alhamdulillah." Sannan ta tashi ta kwashe kayan ta kai kitchen, ta so tafiya gida amma ya zaunar da ita wai ta masa hira, ba musu ta zauna tana shan choculate tana masa hirar, shi kuma sai murmushi yake yana mata video a wayarsa. Sai gab da magriba suka fito daga gidan, a ƙofar gidan ya tsaya tare da hard'e hannayensa a ƙirji ya zuba mata ido. Neehal ta ce "Uncle bye." Tare da d'aga masa hannu, numfashi ya sauke cikin wata irin murya ya ce "Princess!" Ta ce "Na'am Uncle ɗina." Kusa da ita ya matso sosai ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce "I love You!" Neehal ta yi murmushi ta ce "Love You too Uncle." Lumshe idonsa ya yi cikin jin daɗi, a hankali kuma ya sunkuyo ya yi picking forehead ɗinta sannan ya sakar mata hannunta, har ta fara tafiya ya ƙara kiranta, ta dawo da sauri, tsugunna wa ya yi dai dai tsayinta yana kallon cikin idonta ya ce "Princess, promise me you will never forget me in your life." Neehal ta ce "I promised you Uncle." ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai. Fuskarta ya shafa ya ce "Thank you dear." Neehal ta masa bye_bye sannan ta juya ta fara tafiya, haka kawai ta ji jikinta ya mata wani irin sanyi. Shi kam Ahmad tsayawa ya yi yana kallonta yana jin jikinsa kamar babu laka ba tare da yasan dalili ba. Duk wannan abun da ya faru tsakanin Neehal da Ahmad Uncle Umar yana farkon layin akan machine ɗinsa yana kallonsu cikin tsananin ɓacin rai, yana shago Aunty Fauziyya ta kira shi akan ya zo gida babu lafiya, dan tun safe Neehal ta fita kuma har yanzu bata dawo gida ba, shine fa ba shiri ya baro shagon ya taho, yana shigowa layinsu Ahmad dai-dai lokacin su kuma su Neehal sun fito daga gidansu Ahmad, cikin shock ya tsaida machine ɗinsa ya tsaya yana kallonsu. Neehal ta juyo ta ga ko Ahmad ya shige gida idanunta suka sauka akan Uncle Umar wanda ya figo machine ɗinsa a fusace..........✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*3️⃣1️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














...........Ba ƙaramin kaɗuwa da firgita Neehal ta yi ba da ganin Uncle Umar, juya wa ta yi ta falfala a miliyan ta nufi gida. Ahmad dake tsaye yana kallonta ya cika da mamakin abun da yasa ta gudu da firgita lokaci ɗaya, bai gama mamakin ba ya ji tsayuwar babur a gabansa kamar yaƙi, kafin ya yi magana Uncle Umar ya sauko daga kan babur ɗin, yana ƙarasa wa kusa da shi bai yi wata_wata bae ya cakumi kwalar rigar Ahmad cikin zaro ido waje ya ce "Kai ne kake hure wa ƴata kunne dama, munufinki Allah yau Allah ya toni asirinka, kune irin mutanen nan masu ɓata ƴaƴan mutane wato, to ka sani wallahi sai na yi shari'a da kai, kotu ce zata raba mu." Kallon shi kawai Ahmad yake yi cikin rashin fahimta, k'wace jikinsa ya yi ya ce "Malam lafiya zaka zo ka ci kwalata kana faɗar maganganun da ban gane musu ba tare da jifana da munanan kalamai." Uncle Umar dake kallon gidansu Ahmad ganin gidan ƙato yasa ya yi baya dan ya san bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne. A harzuk'e yake faɗin "Zama ka gane ne, idan ka ga sammaci." Babur ɗinsa ya hau a fusace ya tayar da shi ya nufi gida. Ahmad ya tab'e baki sannan ya juya ya shige gida, a zuciyarsa yana Addu'ar Allah ya kare Neehal daga muguntar waɗannan azzaluman mutanen ya kuma hana su cutar da Ita.








Da gudu Neehal ta shiga gida ta yi ɗaki dan neman gurin b'uya, domin ta san idan Uncle Umar ya kama ta yau mai k'watar ta a hannunsa sai Allah. Aunty Fauziyya jin motsinta ta fito daga ɗakinta, jijjiga kai ta hau yi ta ce "Sannunki, shegiya karuwar banza, ƴar ƙaramarki dake kin san bin maza, to yau zan yi maganinki dan Uwarki, gaban naki zan k'ona sannan in miki tsarki da jajjageggen attaruhu, sai in ga da abun da zaki yi iskancin gobe." Ta ƙarasa zancen tare da fizgo Neehal da ƙarfi. Neehal ta fasa kuka ta ce "Dan Allah Aunty ki yi haquri, wallahi ba zan ƙara ba." Wani wawan mari Aunty Fauziyya ta zabga wa Neehal. Neehal ta fasa ƙara ta ce "Wayyo Allah, Ummanah, Auntynah...." Wani marin Aunty Fauziyya ta ƙara kifa mata wanda yasa ta kifawa a ƙasa, Aunty Fauziyya ta ce "Uwarkin da Aunty'n su zo su cece mana shegiya mai kama da aljanu." Tsakar gida Aunty Fauziyya ta fita ta ɗauko wata igiya ta ɗaura a jikin windon kitchen sannan ta dawo falo inda Neehal take durk'ushe har lokacin ta janyo ta kamar wata tinkiya ta ɗaure k'afarta da igiyar, Neehal ta ƙara volume d'in kukanta tana ba ta haquri, amma Fauziyya bata saurare ta ba ta shiga kitchen ta ɗauko wayoyin wutar data haɗa dan zane Neehal. Dai_dai lokacin Uncle Umar ya shigo gidan a babur ɗinsa, kafe babur ɗin ya yi a fusace tare da sauko wa, bai bi takan sannu da zuwan da Aunty Fauziyya take masa ba ya k'wace wayar hannunta ya zabgawa Neehal a ƙafa yana faɗin "Dan Ubanki dama ashe bin maza kike har gida kuna iskanci, tarbiyyar dana baki kenan, yaushe ma aka haife ki da har zaki lalace haka ehe!." "Wayyo dan Allah Uncle ka yi haquri ba zan kuma ba, wayyo Allahna, Abbana......." Magiyar da Neehal take ta masa kenan cikin kuka, amma ya rufe idonsa ya dinga tafkar ta da waya. Aunty Fauziyya daɗi kamar ya kashe ta, duk wani makusancin Neehal a duniya sai da ta kira shi sunansa dan ya neman taimakonsa saboda azabar duka, tun tana kuka da da ƙarfin murya har muyar ta dashe. Wata mak'ociyarsu mai suna Binta wadda ta taɓa yi wa Neehal kitso ce ta shigo gidan a guje saboda ihun Neehal da take jiyo wa, ganin yanda Uncle Umar yake tafkar ta kamar an aiko sa yasa ba ta san lokacin data ƙarasa ta hankad'e shi gefe ba. Uncle Umar ya taso a fusace ya ce "Ki ƙyale ni in kashe ta data jawo mun abun kunya." Matar tana hawaye ta ce "Ba zan ƙyale ka ba, Kuma wallahi baza ka ƙara dukan yarinyar nan ba, sai dai ka haɗa ka dake mu tare." Ta fashe da kuka ta ce "Wannan wanne irin zalunci ne da rashin imani? Me yarinyar nan ta muku kuke azabtar da ita haka? Idan baza ku iya roqon ta ba kukai ta gurin waɗan da zasu iya mana, wallahi da wannan muguntar da kuke mata gara ta gwammace a gidan marayu ta tashi." Uncle Umar da sai huci yake kamar zaki ya yar da wayar hannunsa ya ja ƙwafa ya fice daga gidan. Aunty Fauziyya ta dubi Binta ta ce "Hmmm, Maman ikram dan baki san abun da yarinyar nan ta yi ba ne, da kin san abun da ta yi da kin bar Baban Iman ya cigaba da dukan ta." Binta ta ce "Ko me ta yi bata cancanci wannan cin zalin ba, kuma wallahi sai Allah ya saka mata, haqqin yarinyar ba zai taɓa barin ku ba." Aunty Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Bin maza fa take dan...." "Sai dai ki gani akan ƴaƴanki Insha Allahu wannan alkaba'in ba dai akan marainiyar Allah ba, kuma ko wanne hali yarinyar ta shiga laifinku ne, kun quntata wa rayuwarta da izaya da matsi haka kawai saboda ba ku kuka haife ta ba. Me tay muku? Me ta tsare muku a rayuwa? Wallahi ku bi a hankali da duniya, kuma ku ma kun haifa indai ƴaƴa ne, kuma baƙu san hannun wanda ƴaƴan nawku za su faɗa ba tunda rayukanmu ba a hannunmu suke ba, inda iyayen yarinyar nan suka je kuma zaku je ne, ina jiye muku ranar nadama da dana sani akan cutar da yarinyar nan da ku kai, ku kiyaye gamuwarku da Ubangiji Fauziyya daga ke har mijin naki." Aunty Fauziyya ta ɓata fuska ta ce "A'a, a'a Binta kar kuma ki yi wa ƴaƴana baki, ki faɗi duk abinda zaki faɗa amma kar ki kuma jawa ƴaƴana alkaba'i gaskiya ba zan ɗauka ba." Binta ta bita da kallon tausayin bin rud'in shaid'an da take wanda har take ganin hakan kamar ba komai ba ne. Ba ta kuma cewa komai ba, ta juya ta tallafo Neehal jikinta tare da kiran sunanta, amma ko motsawa ba ta yi ba, balle ta amsa. A gigice Binta ta shiga jijjiga ta tare da kiran sunanta cikin bugawar zuciya ganin babu alamar numfashi a tattare da ita. Dai_dai lokacin Uncle Usman ya yi sallama tare da shigo wa gidan...........✍️










_*Da babu gwara ba daɗi*_










*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*3️⃣2️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














..........Aunty Fauziyya ta amsa masa sallamar cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, Uncle Usman da idansa ya sauka akan Neehal wadda Binta keta jijjiga ta a jikinta. Da sauri ya zubar da manyan ledodin dake hannunsa a ƙasa yana tambayar "Lafiya me ya same ta?" Binta tana hawaye ta ce "Dukan tsiya ya mata, wanda har ya kai ta ga suma." Wani irin sarawa Uncle Usman ya ji kansa ya masa, yana ɗago Neehal daga jikin Binta ya ce "Duka kuma? Wa ya dake ta?" Binta ta ce "Babansu Aiman." Uncle Usman ya yi shiru kawai yana bin jikin Neehal da kallo, ganin yanda shatin duka ya fito b'aro_b'aro a jikin lallausar fatarta, wadda wahala ta sa yanzu ta fara canzawa. Lokaci ɗaya idanunsa suka kad'a tsantsar ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa. Cikin rawar jiki ya miƙe da Neehal a jikinsa amma sai ya ji sun koma ƙasa, da mamaki ya kalli k'afarta wadda a zatonsa wani abun ne ya riƙe ƙasan kayanta amma sai ya ga ashe ɗaure mata ƙafar akay. Cikin sauri Binta ta kwance mata igiyar tana Allah wadaran hali irin na Uncle Umar da Aunty Fauziyya. Wani kallo Uncle Usman ya yi wa Aunty Fauziyya sannan ya fice daga gidan cikin k'unar zuci. Aunty Fauziyya ta dubi Binta rai a haɗe ta ce "Kin ji daɗi kin haɗa ƴan'uwa uwa ɗaya uba ɗaya." Binta kamar zata tanka mata sai kuma ta fasa ta fice daga gidan. Aunty Fauziyya ta ja dogon tsaki ta shige ɗakinta.








Uncle Usman yana fita direct titi ya yi da Neehal saɓe a kadararsa cikin sauri_sauri gudu_gudu. Yana fita titin ya tsari a daidaita ya ce ya kai shi asibiti mafi kusa da sauri dan Allah, bayan ya shiga mai a daidaitan ya ja suka tafi. Cikin mintuna ƙalilan suka ƙarasa wani private Hospital, bayan ya sallami mai adaidaita ya shiga ciki rungume da Neehal a jikinsa. Cikin sauri wasu Nurses guda biyu suka karb'i Neehal suka nufi wani ɗaki da ita dan bata taimakon gaggawa. Uncle Uwar ya zauna a reception ɗin asibitin tare da dafe kansa da hannunsa ɗaya, a hankali yake fuzgar da zazzafan numfashi cikin tsantsar ɓacin rai. Tabbas kowa ya shaida Uncle Usman yana da haquri da sanyin hali gami da sauqin hali, amma fa bai iya ɓacin rai ba. Har aka kira Magriba likitocin dake duba Neehal ba su fito ba, hakan yasa ya miƙe ya nufi masallaci. Bayan ya dawo ɗaya daga cikin Nurses da suka karb'i Neehal ta ce masa "Yawwa malam ka shiga wancan office ɗin Doctor zai yi magana da kai." Uncle Usman ya ce "Toh." Tare da nufar office ɗin. Bayan ya shiga sun gaisa likitan ya dube shi ya ce "Kai waye ɗinta?" Uncle Usman ya ce "K'anin mahaifiyarta ne." Doctor ya ce "Ina mahaifiyarta ko mahaifinta?" Uncle Usman ya ce "Sun rasu." Doctor ya jinjina kai ya ce "Allah ya ji k'ansu da rahama." Uncle Usman ya ce "Ameen, amma ya jikin nata Doctor?" Doctor ya ce "Alhamdulillah, dan ta farfaɗo daga suman da ta yi sanadiyyar dukan da aka mata, kuma mun mata allurar rage zugi da zazzaɓin daya rufe ta lokaci ɗaya, ga wannan magunguna ne muka rubuta za a siyo yanzu kafin ta farka, sannan kuma zaka je ka biya kuɗin gado da sauran abubuwa." Ya ƙarashe zancen tare da miƙewa Uncle Usman wata takarda. Uncle Usman ya sauke numfashi ya karb'i takardar ya ce "Zan iya ganin ta yanzu Doctor?" Ya ce "Eh, idan ka fita daga nan room mai kallo ka nan zaka shiga." Uncle Usman ya ce "Toh Na gode sosai Doctor." Likita ya ce "Allah ya ƙara sauƙi, nan gaba kuma a kiyaye da dukan ƙananun yara irin haka dan wataran ba za su tashi ba." Ƙasa Uncle Usman ya yi da kansa ya ce "Insha Allahu." Tare da ficewa daga office ɗin. Tana kwance a kan gadon asibitin tana bacci an saka mata drip. Kallonta yake cike da tausayawa, sai ajiyar zuciya take saki a kai_kai alamun ta ci kuka ta k'oshi. Ko ina ka kalla a jikinta ya yi jajur saboda duka. Uncle Usman ya shafa kanta ya ce "Allah ya baki lafiya my baby." Sannan ya fice

Please Login or Register in order to submit comment