Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ameen ne ya shigo ɗakin, yana sanye cikin uniform ɗinsu na sojoji wanda suka ƙara fito masa da kwarjininsa, suka kuma matuƙar yi masa kyau.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣1️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















..........Washegari da misalin ƙarfe goma na safe, Neehal tana cikin bacci ta ji muryar Hajiya tana tashin ta. Ta buɗe ido da ƙyar tana duban ta cikin muryar bacci ta ce "Bani da lafiyar ma ba zaki bar ni na huta ba?" Hajiya ta ce "To tafiya zan yi na tashe ki mu yi sallama ƴar nema." Ta tashi zaune tana hamma tare da yin salati. Ta dubi Hajiya ta ce "Kai Hajiya yanzu tafiya zaki yi kamar wadda ake kora? Ki ɗan ƙara mana kwana biyu mana." Hajiya ta ce "Ba zan zauna ba, yau a Gombe mahaifata zan kwana, in kuma na ƙara dawowa garin nan to sai dai in bikin na zo insha Allah." Neehal ta ce "Zaki yi shekaru kuwa baki zo ba, indai bikina ne." Hajiya ta riƙe baki ta ce "Ikon Allah, ka ga shashashar yarinya zatai wa kanta mugun baki, to in ba ki yi aure ba jiƙa ki su Faɗiman za su yi su shanye? ko kuma zama zaki yi kuna goga ƙafaɗa da ita a gidan?" Neehal ta sauko daga kan gado bata tare da tankawa Hajiya ba ta shige toilet. Hajiya ta ce "Kya shige banɗaki mana ja'irar kashi kawai, da kai kamar k'ullin magani." Ta ƙaraci mitarta sannan ta fice daga ɗakin. Bayan Neehal ta fito daga toilet ɗin ta saka kaya sannan ta hau gyaran dakin nata, tana cikin gyaran Mama da Daddy suka shigo. Daddy ya ce "Daughter da kanki kike gyaran ɗaki ke da ba ishashshiyar lafiya ce da take ba." Ta yi murmushi tare da ajiye filon dake hannunta ta ce "Ai na ji sauƙi Daddy na." Mama ta ce "Masha Allah, Allah ya k'aro sauƙi." Ta amsa da Amin, sannan ta gaishe su. Daddy ya ce "Jiya da daddare na zo ganin jikin naki na tarar kina ta bacci, ƙwaƙwa da dabidon da kika ce mun kina so yana cikin fridge na bawa Mamanki ta ajiye miki." Neehal ta ce "To Daddy na, na gode sosai." Ta kalli Mama ta ce "Allah yasa dai babu wanda ya ci mun." Mama ta ce "Tunda kowa irin ki ne ba, Ki sauka ƙasa ki yi break zamu je gidan Ameen yanzu mu dubo Hafsah." Neehal ta ce "Hajiya ta tafi ne?" Mama ta ce "Tana falo yanzu dai zata tafin." Bin su Mama ta yi suka sauka ƙasa tare, har parking space ta raka su, tay wa Hajiya sallama wadda direban Mama zai kai ta gidansu Aunty A'isha da Aunty Sadiya daga can zai wuce ya kai ta Gomben. Bayan ta koma cikin gidan ta haɗa tea ta sha ta ɗan ci Irish sannan ta sha maganinta. Suna zaune a falon ƙasa suna hira da su Dije suka ji ƙarar door beil, Zulai ta tashi ta je ta buɗe, a zaton Neehal Mama ce ta dawo amma sai ta ji muryar waɗanda bata taɓa tsammani ba wato Afrah da Amrah suna kwad'a kiran sunanta. Ta tashi tsaye da sauri tana kallon su cikin shock. Suka taho da gudu suka rungume ta. Ta tsugunna itama ta rungume su duka cikin tsananin farincikin ganin su. Ta d'ago su daga jikinta har lokacin fuskarta na ɗauke da mamaki ta ce "Sweethearts wa ya kawo ku?" Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ne, Aunty ina Mama?" Ta ce "Ta fita unguwa amma yanzu zata dawo." Afrah ta ce "Aunty ya jiki? Daddy ya ce baki da lafiya kar mu zo mu cika miki kunne da surutu." Ta shafi kuncin yarinyar ta ce "Da sauƙi Dialing ina Daddy'n." Amrah ta nuna mata bakin ƙofa inda yake a tsaye hannunsa hard'e a ƙirjinsa yana kallon su, ga trolley ɗin kayan su Afrah a gefen sa." Ta ƙura masa ido tunda suna ɗan nesa da juna baza su iya haɗa ido ba, yau sanye yake cikin manyan kaya wanda suka yi masa kyau sosai, tunda take bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba sai yau. Ya fara takowa a hankali zuwa inda suke, ganin haka yasa su Dije suka tashi suka nufi kitchen dan kawo masa drinks.






Ta ɗauke idonta daga kallonsa da sauri ta mayar ga su Afrah tana murmushi ta ce "Welcome dear, I missed you alot." Amrah ta ce "Missed you too Aunty." Ta ce "Ya school? Dafatan dai kuna karatu sosai?" Suka gyaɗa mata kai. Ta ce "That's is good, ina Ummi da Aunty Zahrah da Ammi?" Afrah ta ce "Suna gida mun bara su, Aunty Zahrah ta ce zata biyo mu Ummi ta hanata." Ta zauna sosai a kan carpet ɗin falon ta ɗaura su duka akan cinyarta suna yi mata hira, ko ƙara kallon inda Ahmad yake bata yi ba. Shi ma bai ce mata komai ba sai zama da ya yi yana kallonsu. Har su Dije suka dawo falon suka ajiye masu drinks da snacks. Ganin da gaske ba kula shi zatai ba ta yaranta kawai take sai ya cewa su Afrah su tashi daga jikinta ba su ga bata da lafiya ba. Yaran suka tashi da sauri suna faɗin "I'm sorry Aunty." Neehal ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kamo hannunsu da nufin su wuce sama, a hankali kanta na ƙasa ta ce "Ina kwana." Ya k'ank'ance ido yana dubanta ya ce "Lafiya, ya jikin naki?" Ta ce "Da sauƙi." Ya ce "Allah ya ƙara sauƙi." Tare da miƙewa ya ce wa su Afrah su ya kai su gidan Mamy, da yamma sai ya dawo da su. Neehal ta ce "Daga zuwanku, dan Allah ka bari idan Mama ta dawo sai mu je tare." Ya ce "Ke da baki da lafiya kuma zaki fita, idan kin ƙara warwarewa sai ku je, tunda za su kwana biyu a nan." Bata ce komai ba ta saki hannun yaran ba don taso ba. Ya kama hannunsu suka juya za su tafi, ta kalli abubuwan da su Dije suka ajiye masa ta ce "Uncle ko ruwa baka sha ba zaka tafi?" Ya yi mata ɗan murmushi ya ce "Idan na dawo zan sha." Ta ce "Shikenan sai kun dawo ɗin, Allah ya kiyaye." Ta d'agawa su Afrah hannu tana faɗin su gaishe mata da Mamy. Bayan fitar su ta zauna akan kujera zuciyarta cike da farincikin zuwan yaran. Ta miƙe dan kai trolley ɗinsu ɗakinta sai ta ga ƙaramar waya keypad akan kujerar da Ahmad ya zauna, da alama dai tasa ce ya manta ta. Wayarta ta ɗauko akan centre table da sauri ta kira shi dan ta sanar masa ya manta wayar tunda bai yi nisa ba ya dawo ya ɗauka. Ringing biyu ya d'aga, ta ce "Uncle ka manta ƙaramar wayarka a nan." Ya ce "Ohh, ki ajiye mun ita kawai Princess, idan na dawo anjima sai na karb'a." Ta ce "Tom Allah ya kai mu." Daga haka ta katse kiran. Ta ɗauki wayar ta ja trollin su Afrah ta yi upstairs. Tana shiga ɗakinta ta ji cikinta ya fara juya mata hakan yasa ta kwanta, ba jimawa da kwanciyar tata bacci ya ɗauke ta.










Sai wajen Azhar Mama ta dawo gidan, ita kaɗai ta dawo Daddy ya wuce gurin sabgoginsa. Kitchen ta faɗa ta ɗora girki, sannan ta barwa su Dije su ƙarasa dan ita Hospital zata tafi aiki, ta bar musu sallanun idan Neehal ta tashi su ce mata ta wuce office, a bakinsu take jin labarin zuwan su Afrah da mahaifinsu, ta ji daɗi itama sosai ta ce Insha Allahu zata dawo da wuri kafin su dawo daga gidan Mamy......
















A gidan su Sadik kuwa yau tun safe Kawunsu ya zo gidan shi da Hajiyarsu (Kakar su Sadik) wadda kawun ya biya ya taho da ita. Maamah ta tarb'e su cikin mutuntawa da girmamawa. Umma kuwa yau ita ce da girki tana ɗakin Abba tana zuba masa kissa da kisisina, zuwan su Hajiyan yasa suka fito tare da Abban. Bayan an gama gaggaisa sun taɓa abun da Maamah ta kawo musu Kawu ya gyara zama ya dubi Abba ya ce. "Surajo Rukayya ta kira ni ta sanar da ni wani zance mara daɗin ji da ma'ana." Abba ya kalli Umma ya ce "Wanne zance kenan Yaya?" Kawu ya ce "Zancen yarinyar da Abubakar yake neman Aurenta mana." Hajiya ta tari numfashin Abba da faɗin "Au Sadik ɗin har ya fara neman Aure ba mu da labari?" Abba ya ce "A'a, soyayya dai kawai suke, tunda shi batun Aure dole sai an fahimci juna kafin akai ga maganar yin sa." Hajiya ta ce "Gaskiya ne, To Allah ya taimaka. Amma me ya faru da ita yarinyar?" Kawu ya kwashe duk abun da Umma ta sanar masa ya faɗa musu. Hajiya ta zaro ido tana jinjina kai ta ce "Kai! Gaskiya kuwa matuƙar haka ne da matsala, to ya rabu da ita mana ya nemi wata, ga ƴan mata nan burjik da yawa a gari sai ya zab'a ya darje." Maamah ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin rashin jin daɗi, Umma kuwa murmushin farinciki ta saki a ɓoye." Abba ya ce "Ni fa Hajiya a gani na wannan duk ba matsala ba ce, yarinyar nan na yi binkice a kanta da iyayenta sosai mutanen kirki ne, mahaifinta ba b'oyayyen mutum ba ne, dan ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa, daga baya kuma ya daina siyasar kwata_kwata. Duk da dai ba shi ya haife ta ba, amma a matsayin mahaifi yake a gurinta tunda shi yake riqon ta." Maamah tay saurin d'ago kanta a karon farko ta ce "Au ba shi ɗin ne ya haife ta ba dagaske?" Abba ya ce "Ehh, amma itama yarinyar an tabbatar mun mahaifinta kafin ya rasu mutumin kirki ne, kuma ɗan asalin jihar nan ne a ƙaramar hukumar Gabasawa." Kawu ya ce "Wane ne marik'in nata?" Abba ya ce "General Alhaji Muhammad Tafida." Kawu ya jinjina kai ya ce "Tabbas na san sunan mutumin sananne ne, to amma mu yanzu ba nasabarta ce abun damuwar mu ba, damuwar mu batun kashe duk wanda ya ce zai aure ta da ake yi." Hajiya ta ce "Gaskiya fa, abun nan abun dubawa ne, dan watakila aljanu ne da ita suka aure ta." Umma ta ce "Nima abun da na gani kenan Hajiya, hankalina gaba-d'aya ya tashi har na kasa haquri na kira Yaya na sanar masa dan a yiwa tufkar hanci, tunda shi Abban nasu ya ƙi saurara ta." Abba ya ce "To, gaskiya ni dai duk a iya binciken da na yi ban ci karo da wannan labarin ba, kuma itama Rukayyan ban san a ina ta samo shi ba." Umma tay karaf ta ce "Ai ita marik'iyar yarinyar akwai ƙanwarta a nan unguwar, nan gaba kaɗan ne da mu babu nisa, to a gurin wata mak'ociyarta na ji wannan labarin, kuma babbar mace ce baza tay mun ƙarya ba." Abba ya ce "Ka ji fa, watak'ila ma ba gaskiya ba ne zuzutun abu ne irin naku na mata." Hajiya ta katse shi da faɗin, "Ba wani zuzutun mu na mata, maganar nan fa ya kamata a duba ta, kar mu zo mu yi abun da za'ai dana sani daga baya." Kawu ya ce "Ato, faɗa masa dai Hajiya." Abba ya ce "Shikenan, zan yi sabon bincike akan hakan Insha Allahu, idan ya tabbata haka ne sai ya haqura da ita ya nemi wata kawai." Daga haka suka rufe wannan chapter suka kama wata......










Sai da ƙarfe biyu na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin da take, shima ƙarar wayar Ahmad da ake ta kira ne ya farkar da ita. Tashi zaune ta yi tana kallon agogon bangon dake ɗakin, mamaki ne ya cika ta ganin ta yi fiye da awa uku tana baccin. Ta sauke numfashi a ranta tana tunanin may be a cikin magungunan data ke sha akwai na bacci, dan wannan baccin nata daga jiya zuwa yau ya yi yawa. Ta sauko daga kan gadon domin yin Sallah, wayar Ahmad ce ta ƙara yin ringing alamun shigowar kira. Kamar ta share sai kuma ta ɗauki wayar ta duba mai kiran, *Jamila* sunan da ta gani kenan akan ɗan screen ɗin wayar. Ta mayar ta ajiye sannan ta nufi toilet dan yin alwala. Bayan ta fito ta ji still ana kuma kiran wayar, bata bi takan ta ba dan dama dalilin da yasa ta kira shi ya dawo ya ɗauka kenan kar ayi ta kiransa a wayar ba'a same shi ba. Har ta yi Sallarta cikin nutsuwa ta idar ba'a daina kiran wayar ba. Ta yi ɗan tsaki ta tashi ta je ta ɗauki wayar, 17 missed calls ta gani kuma duk mutum ɗaya ce wato Jamila. Ta tab'e baki ta ajiye ta sauka ƙasa. Ƙwaƙwa da dabinon da Daddy ya siyo mata ta ɗauko a cikin fridge ta zauna ta fara ci bayan ta ɗibarwa su Dije. Bayan ta gama ci ta ɗebo abinci kaɗan ta ci. Koda ta koma ɗakinta dan yin sallar la'asar sai tarar wayar tana ringing, still a fili ta ce "Kai wannan mai kiran akwai naci, tunda ta kikkira ta ga ba'a ɗauka ba ai sai ta haqura." Ta d'aga wayar a kufelen da ita kanta bata san ko ta mecece ba ta ce "Mai wayar ba ya kusa." Bata jira amsa ba ta katse wayar. 5 missed calls ta gani bayan na d'azu, kuma duk dai mutum ɗaya ce, sai kuma 4 unreaad message data gani. Har zata ajiye wayar sai kuma ta shiga message ɗin ta gani, ɗaya na kamfani ne sauran ukun kuma duk na Hajiya Jamila ne. Ta shiga na farko ta ga abun da ta turo, _*Please Dear pick my call.*_ ta fita ta shiga na biyu ta ga shi kuma haka ta rubutu, _*Dama kiran ka nay in ji lafiyar ka, dafatan kana lafiya Habibi?*_ bata karanta na ukun ba ta ajiye wayar saboda takaici. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci ba tare data san dalili ba. Ta nufi kan darduma ta tada ik'amar Sallah dan tana da alwalarta.








Ƙarfe biyar da ƴan mintuna Mama ta dawo, ɗakin Neehal ta leqa ta tarar da ita zaune a kan gado tana latsa waya. Ta d'ago ta dubi Maman ta ce "Sannu da zuwa." Mama ta ce "Yawwa ya jikin?" A hankali ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Ashe su Afrah sun zo, har yanzu ba su dawo ba ne?" Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta juya ta fice ganin kamar bata son magana, ita kuwa ranta ne a ɓace har lokacin, sai taune lip ɗinta take. Kafin Magriba Ahmad ya dawo da su Afrah, da gudu suka je suka rungume Mama dake zaune a falon ƙasa. Mama ta shafa kanwunansu tana murmushi ta ce "Welcome yarana." Ahmad ya zauna a kan carpet ya gaishe da Mama cikin girmamawa. Ta amsa masa tare da tambayarsa yanda ya baro Mamy da su Ummi. Su Amrah suka bar jikin Mama suka nufi upstairs dan sun san Auntin nasu tana can. Tana nan yanda Mama ta bar ta suka shigo ɗakin suna kiran sunanta. Ta d'ago ta kalle su bata ce komai ba, suka hawo kan gadon da murnar su, Afrah ta ce "Aunty mun dawo, Mamy ta ce mu gaishe ki." Ta yi ɗan murmushi ta ce "Sannun ku da dawowa, to ina amsawa." Amrah ta ce "Daddy yana ƙasa shi da Mama." Ta yi shiru bata ce komai ba, yaran suka cigaba da yi mata hira. Kiran Ahmad ne ya shigo wayarta, ta ɓata rai kamar yana gabanta ta ƙi d'agawa, haka kawai ta ji tana jin haushin shi ba tare da ta san dalili ba. Bayan kiran ya katse wani ya ƙara shigowa, still ƙin ɗagawa ta yi. After three minutes Mama ta turo ƙofar ɗakin ta ce mata ta je Ahmad yana jiran ta. Fuska a cukule ta ɗauki wayarsa dake kan bedside locker ta fice daga ɗakin, su Afrah suka mara mata baya........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣3️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












...........Cikin sauri ta zare jikinta daga na Ahmad, shima bai yi musu ba ya sake ta tare da faɗin "Ki yi a hankali Princess." Ganin yanda ta zare jikin nata cikin gaggawa ta koma ta kwanta a kan gadon, wani irin fad'uwa gabanta yake kamar zata yi fitsarin sa gami da matsanancin tsoron da ya cika mata zuciya saboda ganin Ameen, ta runtse idanta tare da jan bargo ta lullub'e jikinta. Cikin matuƙar shock Ameen yake kallon su, tun daga turo ƙofar da ya yi ya kasa ko da d'aga ƙafarsa ne, shi mutum ne da ba kasafai ake gane halin da zuciyarsa take cike ba, amma a yanzu kallo ɗaya zakai masa ka san ran Maza ya kai matuƙar ɓaci. Afrah ta waro Ido ta ce "Uncle are you a soldier? Dama Aunty Zahran mu zata gan ka, she like soldiers over." Amrah ta ce "Uncle show me your gun, I want to see it." Ahmad ya ɗauke idonsa daga kan Neehal ya dube su ya ce "Ba ku gaishe shi ba sai surutu ko?" Yaran suka rufe baki a tare suna murmushi. Ameen bai bi ta kan zancen yaran ba ya tako zuwa inda Neehal take, Idanunsa akan Ahmad yana masa wani kallo ta gefen ido. Ahmad ya miƙe tsaye, Allah ya taimaka Neehal bata ɓata shi ba kamar yadda ta yi zato. Hannu ya miƙawa Ameen yana murmushi ya ce "Barka da zuwa Babban Yaya." Ba tare da Ameen ya kalle shi ba ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha amma bai ce komai ba. Ahmad ya lura da yanayin da Ameen ɗin yake ciki, sai ya danganta hakan da halin sojoji ne kodayaushe fuska a cukule, ko kuma wani ne ya ɓata masa rai, amma ko kaɗan rashin maganar bai dame shi ba. Neehal wadda tun sanda Ahmad ya yiwa Ameen magana ta buɗe idonta ta kalle shi hawaye na zuba daga cikin idanunta, ganin ya zauna a kusa da kanta ta runtse ido da sauri cikin saddaqarwar zata ji duka a jikinta saboda ganin yanayinsa, ta san Ameen ta san waye shi, ta kuma san ɓacin ransa babu kyau. Saboda tsabar fargaba da tsoron da zuciyarta ke ciki da wani irin gudu ta ji jinin yana fita daga jikinta, ga gefen mararta da ya k'ulle. Zuba mata ido kawai ya yi bai ce komai ba, wanda hakan yasa ta kuma runtse idonta da sauri tare da jan bargo ta rufe har fuskarta. Ahmad daga tsayen da yake ya ce "Princess bari na je na kawo miki magani ki sha, Allah ya baki lafiya." Bai jira amsar ta ba ya nufi ƙofa, Ameen ya bi shi da kallo har ya fice, yaransa suka mara masa baya cikin gudu wai sai sun bi shi. Ya dauke idonsa daga bakin ƙofar yana ɗan furzar da numfashi, akan syringe ɗin allura dake ƙasan gadon idanunsa suka sauka, ya ɗauke kansa ya mayar kan Neehal wadda ƙirjinta ban da bugawa babu abun da yake. Ya ɗan lumshe idonsa ya buɗe sannan ya janye bargon daga kanta tare da ɗora hannunsa ɗaya akan goshinta. Ta buɗe ido cikin tsoro wanda hakan yay dai-dai da zubar wasu sabbin hawayen, cikin muryar marasa lafiya ta ce "Yaya!" Cikin muryar da bata taɓa zaton zai mata magana ba nan kusa ba ma yanzu ba ta ji ya ce "Na'am." A matuƙar sanyaye. Ta kama ɗayan hannunsa tare da fashewa da kuka ta ce "I'm sorry." Ya taune lip ɗinsa sannan ya ce "For what?" Ta yi shiru sai kukan ta cigaba da yi tana ƙara k'ank'ame hannunsa cikin nata. Ya shafa kuncinta da ya jik'e da hawaye ya ce "Stop crying Miemerh, kin ga baki da lafiya, kuma You promised to me kin daina." Cikin matuƙar mamakin yanda yake mata magana cikin sanyin murya mai cike da tsantsar kulawa ta tashi zaune tana yamutsa fuska tare da goge hawayen fuskarta da bayan hannunta. Ta kwantar da kanta akan ƙafaɗarsa, tana sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da ƙara lafewa a jikinsa. A hankali ya ce "Ya jikin naki?" Ta ce "Ya yi sauqi, Uncle ya mun allura." Ya ce "Na gani ai." A zaton ta gatse yay mata sai ta ce "Dagaske fa Yaya." Bai kuma magana sai hannunsa da ya ɗora akan cikinta ya ɗan danna cikin. Ta ce "Aushh! da zafi fa Yaya." Ya ce "Ba haka Mama take miki ba?" Ta matso k'walla ta ce "Ai itama yana mun zafi idan tay mun." Ta cire hannunsa daga kan cikin tare da ƙoƙarin saukowa daga kan gadon, jikinta lullub'e da bargo. Ya riƙe ta tare da faɗin "Where are you going?" Ta ce "Toilet." Ya sake ta, ta sauko tana ƙara rufe jikinta da bargon, locker mudubi ta nufa tana jan ƙafa da ƙyar ta janyo ta ɗauki abu a leda, ba tare da juyo ba ta shige toilet. Ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo da idonsa kan gadon, abun da ya gani a zanin gadon dai-dai inda ta tashi ya ƙurawa ido. A hankali ya tashi ya cire zanin gadon gaba-ɗaya ya ajiye a ƙasa. Ta yi kusan 30 minutes a toilet ɗin sannan ta fito, har lokacin yana zaune a ɗakin idanunsa a lumshe. Tana yamutsa fuska ta ƙaraso, ganin zanin gadon a ƙasa ta ji wata irin kunya ta lullub'e ta domin ta gane ɓaci ya yi, bata kalli inda yake ba ta faɗa kan gadon ba tare data saka wani zanin gadon ba, kwanciya ta yi tare da juya masa baya. Sai a lokacin ya buɗe idonsa ya kalli bayanta. "Miemerh!" Ya kira sunanta, ta ce "Na'am." Ya ce "Juyo." Ba musu ta juyo, amma bata iya kallon fuskarsa ba. Cikin muryar da idan yay mata magana da ita take bala'in tsorata ta ji yana cewa. "Ina gurin aiki aka kira ni baki da lafiya kuma Mama bata nan, hankalina a tashe na baro abubuwan da nake na taho dan taimakon ki, amma ina zuwa na tarar dake a jikin wani." Ya ɗan taune lip ɗinsa sannan ya miƙe ya zuba hannayensa duka a aljihu ya ce "I will punish you, kin san ba ay mun laifi in ƙyale." Ta saka kuka zata yi magana ya ce "Shiiii." Sannan ya ɗan sunkuyo da kansa kusa da fuskarta a hankali ya ce. "Just Sleep." Ta had'iye kukan nata tare da lumshe ido. Ya shafi gashin gigirarta ya ce "I will go, idan ya dawo ma still ki kuma ɗane jikinsa." A firgice ta ce "Wallahi Yaya allura yay mun, kuma su Aunty Dije suna nan yay mun ka tambaye su ka ji, dan Allah Yaya ka yi haquri kar ka faɗawa Mama." Bai ce komai sai iska da ya shiga hura mata a fuska daga cikin bakinsa. Ta ja hanci tare da turo baki gaba tana cigaba da tsiyayar da hawaye, a hankali ta ji wani irin bacci na fizgarta, 80% na ciwon cikin d'azu ya tafi, yanzu kaɗan_kaɗan yake mata. Jin saukar numfashinta alamun ta tafi duniyar bacci, ya gyara mata kwanciyar kanta akan pillow sannan ya juya fice daga ɗakin. A falo ya tarar da su Dije, ya sanar musu ta yi bacci su kula da ita. Suka amsa masa cikin girmamawa tare da fatan Allah ya tsare hanya. Da Ahmad ya dawo ko saman bai kuma hawa ba, ya bawa su Dije magungunan da ya siyo mata bayan sun sanar masa ta yi bacci. Ya kuma ba su sallahun idan

Please Login or Register in order to submit comment