Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta suna kuka suna kiran"mommy !!mommy!!! "

Nanny dinsu ta fito dasauri tace"subhanallahi "ta nufi kitchen debo ruwa,

Dedenan fahad ya shigo gidan da faraa ganin yaran suna girgizata suna kuka yasa shi sakin jikar hannunsa ya karasa wurinsu ya dauketa ya nufi bedroom daita zuciyarshi na zafi sosai,

Twins suka hade kai suna kuka duk time data fadi sosai suke shan kuka,

Fahad na ajiyeta ya fara mata tofi ta bude ido ta saukesu kansa,

Idanunshi jawur yana jin tausayinta ya rike hannunta gam yakasa cewa komi hawaye na zubomata tace" yaya se yaushe ne zansamu lpy?se yaushe zan zama kamar kowa?"

Zuciyarshi na zafi yace"lokaci na nan tafe aysha ki kara hakuri"

Tai shiru hawaye na zuba a fuskarta wayarta tafara ring harta tsinke takara daukar ring ya dauko wayar ganin Abbu yasa ya dauka ya kara a kunnenta,

Can bangaren Baban aysha yayi sallama ta amsa murya very cool tace"abbu kuna lpy?"

Yace"lpy lau ayshata kuna lpy ina twins ?"

Tace"lpy lau muke abbu"

Yace"aysha tonton baya lpy sosai yanata kiranki yanason ganinki"

Tafara kokarin tashi zaune fahad ya riketa,

Tace"abbu ya jikinshi dasauki?"

Yace"eh dasauki
kisamu kizo kiganshi yanata kiranki"

Tace"insha Allah zanzo abbu"

Yace"Allah ya baki lpy aysha se anjima yakashe wayar,

Ta kalli fahad tace" tonton ne baya lpy yanata kirana don Allah kabarni naje "

In cool yace"waye tonton?"

Tace"abokin abbu kuma wazirin shi"

Ya sauke ajiyar zuciya yace"kishirya weekend zamu tafi tare "

Tace"nagode yaya"ta lumshe ido,

Ya nata kallonta ya tashi ya fita yayi wanka ya fito cin abinci,

Nanny na rarrashin twins sukaje suka rikeshi ameer yace"daddy mommy ta warke?"

Yayi murmushi yace"ta warke"

Ameera tace"daddy rannan ma kace ta warke"

Yace"eh ta warke kuje kuganta tana bedroom"

Suka tafi dakin jikinsu sanyaye suka kwantar da kawuna gefen jikinta,

Aysha ta bude ido tana kallonsu,

Ameer yace"mommy nadena dukan ameera"

Tai murmushi ta dora hannu kanshi tana shafar sumarshi tace"Allah yamaku albarka"

ameera tace"nima nadena tsokanarshi"

Tai murmushi ta shafi fuskarta tace"kuje nanny tai maku shirin islamiya lokaci ya kusa"

Suka nufi kofa,

Ta tashi zaune tana kallonsu da murmushi tace"kunsan me ?ran Saturday zamu tafi Niger mugano su abbu"

Sukace"yeee yee zamuga abbu da dokuna"

Tace"to kuyi sauri kuje"

Suka fita da gudu suna murna tai murmushi tana kallon kofar ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta,

Ran Friday suka shirya ran Saturday suka tafi niger,

Tarba ta musamman akai musu bayan sun huta suka nufi asibityn da waziri ke kwance,

Suna zuwa tafara hawaye saboda halin da yake ciki tana gefen bed din tace "tonton sannu Allah ya tashi kafadunka"

Idanunshi rufe yanajin matukar ciwo yana sheshsheka yace"aysha ce?"

Tace"nice tonton Allah yabaka lpy "

Waziri ya bude ido dakyar idanun na kawo ruwa yace"ki yafemin diyata kafin na mutu da alhakinki"

Mutanen dake wurin shi suka kalli juna fahad na tsaye yana kallonsu ,

Aysha tace" na yafemaka tonton zaka samu lpy soon"

Danshi yace"baba meyasa kake neman yafiyarta?"

Cikin zafin ciwo yace"saboda nine sanadin ciwon dake damunta"

Yace"what?""yana kallon Baban nashi,

Iyayenshi mata suka zubamai ido ,

Fahad ya gyara tsayuwa zuciyarshi na harbawa,

Aysha tai tsaye tana kallon abokin baban nata data dauka kamar uba zuciyarta na harbawa sosai

Danshi yace"noo bari na kira likita "

Cikin muryar ciwo yace"ba seka kira likita ba ni tawa takare mutuwa zanyi "

Ranshi bace yace"to baba yaakai kazama sanadin ciwon ta?"

Yayi shiru sannan yace"inason sarautar garinnan na zauna nai nazari me martaba baida wani babban namiji daze gajeshi idan ya mutu nan kusa kenan nine zan amshi mulki idan kuma ya cigaba da rayuwa to akwai yiwuwar lokacin diyansa sun girma idan hakan ta faru bazan taba samun sarautar ba watarana naje wurin boka nafadamai kudirina boka yabani option yace ko akasheshi ko asamai cutar da zaisa ya sauka a mulki,na zabi asamai cutar yabani wani jan goro yace shine zaisa shi duk time da ranshi ya baci zai fadi hankalinshi zai gushe ko idan hankalinshi ya tashi daganan dole sarauta ta zame daga hannunshi,

Duk dakin yayi tsit fahad na cije da lip dinsa na kasa yanajin mugun zafi wannan ciwon ba aysha kadai ya shafa ba harshi yaci azabarsa,

Aysha na tsaye kamar statue tayiwa waziri kuri,

Waziri na nishi ya cigaba da cewa"nasan sarki nasan goro shine na karawasu akai na kaimishi kyautarsu,ina kaimishi yana wurin shakatawa ya bude ya Ciro jan Wanda yakeso yabawa Aysha ta cinyeshi nan take banji dadi ba don inason Aysha sosai na koma wurin boka domin ya karya asirin ya shedamin babu abinda zai karyashi aljanin dayayi asirin taurari sun kasoshi jiya,na dawo na zauna cikin zullumi na manta da batun mulki saboda halin dana sa diyata ciki ina daga cikin wadanda sukaita kawo malamai amma baa dace ba inaji ina gani take faduwa kowane lokaci batare da nai wani abu ba bayan shekaru na kamu da athmarnan duk time data tasomin ina shan wuya ina tunowa da ita irin wahalar da take sha dan Allah kuyafemin nayi nadama tuntuni bayadda zanyi "

Zuciyar Aysha na ciwo tai luuu zata zube kasa matan dake gun sukai saurin riketa sunata hawaye,

Fahad ya sungumeta ya dorata kan bed yana mata tofi yana hawayen tausayinta,

Dan waziri na jin zafi yace"wlh baba duk inda kayo asirinnan sekafada koya karya asirin komu jefeshi da ranshi mu kona kayan kafircin"

Waziri na hawaye yace "yana can cikin sahara nayi zarya na hakura amma nima ina cikin damuwa"

Danshi yace"baba baka kyautamana ba wlh mulkin duniya har abun so ne ?kwana nawace duniyar dukanta?"yayi tsoki ya tashi ya fita a hasale,

Wani bafade yabishi dasauri yana fita ya kira waya ya fadawa abbu jikinshi har rawa yake ya taho asibitin,

Fahad na tawa Aysha addua ta farka tana kuka zuciyarta na up and down suka kira likita dasauri tazo tafara dubata tasa mata drip da alluran bacci baccin ya dauketa,

Fahad ya kura mata ido yana kallon small cute fuskarta daga sanda yasanta zuwa yanzu yasan tasha wahala matuka ashe ciwo daban magani daban akeyi,

Ba jimawa abbu ya iso yayi wurinta hankalinshi tashe ganin tana bacci yasa ya koma wurin gadon da waziri ke kwance iyalanshi na zagaye dashi yanata nishi,

Abbu ya tsaya kallonshi yana hawaye cikin zafin zuciya yace"da kasameni kafadamin kanason mulki dana bakashi tuntuni kafi karfin komi awurina"

Waziri na tari yace"kuyi hakuri dan Allah sherin shedanne nai nadama tuntuni"

Abbu ya girgizakai ya meda kallonshi gun Aysha yana dubar dogon lokacin da ta dauka tana wahala yana sane bai fadaba se yanzu da yaga kamar zai mutu ,

Ya koma wurinta yayi tsaye yana kallonta ,har su Umma sukazo fahad ya koma gefe suka zauna suna kallonta suna hawaye suna jin tausayinta,

Dan waziri ko tuni yakama hanyar kauyen sahara don samun bokan tare da bafade yanata huci yana kagare sukai,

Suna isa suka fara tambayar bokan akai musu kwatance har bukkarshi,

Suna zuwa bakin bukkar shuaibu yafada ciki bokan na zaune yana tsahinshi ba tsoro ya cakumoshi yayo waje dashi ,

Boka ya zazzaro ido yafara kiraye_kirayen aljanu Shuaibu ya wanka mai marin daya fiddashi hankalinshi na wucin gadi sannan ya dawo ya shakareshi idanun boka sukai waje jijiyoyin idanunsa warwaje ,

Seda yabashi wahala ya sakeshi yana tari ya rike wuya ,

Shuaibu ya tsaya kallonshi sama da kasa harya tsufa amma yana ta tsiya cikin duniya yace"kai bakin tsinanne gabadaya asirin da kayi tundaga shigarka bokanci zuwa yanzu nakeson ka karya su yanzu inba haka ba zan kama ka na kaika wurin sarki a jefeka da ranka"

Boka nata tari baice komi ba ,

Ya daka mai tsawa yace"ba ka jina?"

Yana sheshsheka yace"wasu bazasu karyuba domin aljanun da sukayi sun riga sun mutu"

Shuaibu yace"haka kake bokancin shekaru da yawa bakasan makaryar aiki ba ? Ko saboda gudun bacin rana irin yau ?"

Yace"aiko yau dinnan zaka tafi lahira"ya jawoshi yafara daureshi zai kutsashi boot,

Boka na haki yana kallon kayan jikin bafade tabbas masarauta zasu kaishi kuma hukuncin kenan jifa,

Yafara begging "don Allah kuyi hakuri zan karya na tuba bazan sake wannan sanaar ba"

Shuaibu ya tsaya yana kallonshi yace"dan iska kasan Allah ne? Dama Sana'a kake ba kafirci ba ?laananne meyasa bakasa aljanun suyita kawomaka kudi ba sede ka rika cutar da jamaa kana amsa arnen banza "

Boka na firgice yace"kuyi hakuri sherin shedanne wlh amma kakata ladaniyace"

Shuaibu ya kwashe da dariya cos shima yana taba shaye_shaye kadan yace "ya zaka karya asirin da taurari suka kashe aljanin?"

Yana tari yace"akwai yadda zaai yallabai"

Shuaibu ya kalli bafade yace"taromin jamaar kauyennan yanzu"

Yace"angama yallabai"ya nufi cikin kauyen ,

Shuaibu nata fallamishi mari ba jimawa suka dawo da jamaa manya da yara Shuaibu yace"wannan shine yake kashe maku yanuwa yana haukatasu zai karya asirin da yayi yanzu idan bai karya ba zanyi rami yanzu mu jefeshi nan take"

Sukaita ihu dama sun rasa yadda zasuyi dashi suna tsoronshi,

Bafade ya kwaso kayan tsafi akayo out dasu kafff,

Ya zauna yafara abubuwa irinnasu na bokaye yanayi yana gyara wuyanshi dayakeji kamar ba nashi ba,

Can zuwa ya dauki wata kwarya ya bude yagama zube_zube cikinta sannan ya jefar daita kasa ta fashe garin dake ciki ya tashi sama yabi iska,

Ya cigaba da kwance_kwance da fashe _fashe harya gama ba wata _wata mutane suka sawa bukkar wuta ,

Su Shuaibu suka daureshi sukai fada dashi wasu mutanen gari sukabi don yin kallo,

A asibity Aysha na cigaba da bacci waziri nata neman yafiya akai masa ta baccin shima ,

Abbu ya koma fada bayan Maghreb Sega bokan sunkawoshi a wahalce haryayi fitsari a jiki,

Abbu da fadawa suka tsaya kallonshi tsoho sosai,

Cikin kunar zuciya abbu yace"shekara nawa kayi kana tsafi?"

Yace"30 "yadan rage saboda neman sauki,

Abbu ya jinjina kai jin shekarun yace" kasheka zansa ayi don irinku basu da amfani cikin alumma"

Boka ya kwanta kasa yana roko"dan Allah kumin gafara wlh na tuba nadena dan Allah kubarni da raina karku kasheni"

Can zuwa Abbu yace "ka tabbatar?"

Yace"na tuba nadena wlh "jikinshi na rawa

Abbu yace"zan sa asake ka don kasamu tuba amma bazan kyaleka ba zan baza mutane suna kulamin da duk inda kashiga da zaran kafara wani yunkuri zansa akamoka insa jamaa su jefeka"

Ya jinjina kai yana kagare a sakeshi zawone cike da cikin shi,

Zuciyar abbu na zafi komi zaiyi masa bazai kai wuyar da aysha ta sha ba Murya sanyaye yace"Ku sakeshi ya tafi"

Aka warwareshi ya tashi ya zunduma a guje yabar masarautar,

Abbu ya koma cikin gida kanshi na juyawa ya kwanta kan bed abun ya matukar dameshi waziri ne zai masa haka?amininshi na kusa dashi?

Su Ummi suna asibity wurin Aysha basu san halin da yake ciki ba,

Ya dauki waya dakyar ya kira Ummi tana jin muryarshi taja antinsu suka nufo gida suna zuwa suka kira likita yazo ya dubashi yabashi drugs ,

Fahad na zaune gun Aysha har bayan ishai shiru ya tashi yaje wurin likitar yace"inafatan matata lpyarta lau?"

Ta jinjina kai tace"nan da dan lokaci zata tashi Kaine mijinta?"

Yace"yeah"

Tai murmushi tace "congratulation she's pregnant"

Wani sanyin dadi ya ratsa zuciyar fahad ya saki kayataccen murmushi yace"tnx u very much"

Da murmushi fuskarta tace"u r welcome "

Ya juya ya koma gun Aysha ya rike hannunta yana sakin murmushi after long time takara samun ciki for second time,

Can tsakar dare Aysha ta bude idanunta a hankali ta saukesu kan fahad da yayarta data zo ta cije lips ta kalli gefenta ana taiwa tonton dinsu fita dukda AC din dake akwai,

Tafara yunkurin tashi zaune fahad ya riketa yace"ki kwanta u need to rest "

Tace"inason magana da tonton kabarni plss"

Fahad ya saketa ta tashi ta nufi gadon waziri ta zukunna ta kwantar da kai jiki tana kuka tace"tonton_tonton na yafemaka Allah yabaka lpy "

Ya dafa kanta yana nishi sama_sama,

Ta dago tana hawaye tace"zaka warke tonton"

Ya kulle idanu yana jin matsananciyar kunya,

Yayarta tazo ta janyeta tace"mutafi gida ku huta kundawo gobe"tana jin haushin kukan da ayshar keyi ga wanda yagama cutar da rayuwarta,

Daita da fahad da Aysha suka shiga motar dama baazo da twins ba tana tuki suka nufi gida suna zuwa Aysha ta rungume Umma tana kuka,

Umma na shafar kanta tace"kiyi hakuri Aysha"

Aka kaisu part din da suka sauka dakyar fahad yasamu tasha milk yasha sukai salloli suka kwanta bacci,

Wanshekare aka farka da mutuwar waziri basu samu suntaho rannan ba se ran Monday suka biyo flight suka dawo Nigeria,

Suna dawowa fahad ya nufi gidan mommy yafara bata labarin abinda ya faru,

Mommy ta rike gemu tana mamaki tace"oh!! mutum ba abun yadda bane duk abinnan asirine ke wahalar da daughter Ashe kasan time dana amso mata wasu maganin Islamic abun ya lafa to inaga asirin bai karye duka bane shiyasa ya dawo su kuwa malamannan duk karyane suna cewa datai aure zata warke"

Fahad yace"mommy dama irin malamannan bai kamata ana gayyatosu ba ko saurarensu saboda da yawa harsashe sukeyi ko kuma amfani da aljanu"

Mommy tace"Allah ya kyauta daughter de ta wahala sosai danasan asirinne da tuni zan rika mata wankan ganyen magarya insha Allah da bazai wani jima ba"

Fahad ya lumshe ido in cool yace"haka Allah yaso"

Sega wata yarinya ta fito daga sama tataho wurin mommy ta zauna yana kallonta yace"wannan fa?"

Mommy tai murmushi ta jawota jikinta tace"kanwarka ce tazomin weekend taki komawa"

Yayi murmushi yana kallon ta.
[2/28, 5:47 PM] Maman Su: 95







Da dare sosai Aliyu na kan faseelat yana aiki ba ji ba gani sosai HQ din faseelat ke ciwo da marar ta musamman marar data kejin ciwon yau na daban tanata nishi har hudu da wani abu sannan ya sauka yana ta meda numfashi idanunta rumtse tana cije da lips dinta yana kallonta yana lasar lips dadinta har zautashi yake ya tashi ya shiga toilet,

Faseelat ta gyara kwanciya ciwon marar ta na kara tsananta jin ciwon na karuwa yasa ta tashi zaune ta rike ciki tafara hawaye tana cije lips dinta,

Aliyu nata wanka hankalinshi kwance besan halin da take ciki ba,

Ta cigaba da hawaye tana dafe da marar ta dake mugun ciwo tana nishi ,

Aliyu na fitowa wankan ya ganta zaune tana ta hawaye hannunta biyu dafe da ciki,

Hankalinshi ya tashi zuciyarshi ta harba dasauri ya karasa saman bed din ya riketa bakinshi na rawa yace"heartbeat minene?"

Tana hawaye muryarta dishe tace"hero marata kamar zata balle "ta cigaba da rike cikin

Jikinshi ya dau rawa lokaci daya yana tuno time da yasa sameera miscarriage yayi saurin jawota jikinshi yana duban kasanta sede ba jini kokadan kuma tana cigaba da hawayen ciwo,

Ya kalleta cikin tashin hankali ya dade beyi irin wannan jimawar ba yau ma besan meyasa ba cikin jin tausayinta lips dinsa na shaking yace"sannu_sannu bari mutafi asibity"

Marar faseelat tai wani irin juyi tai kara ta rike Aliyu gam tana kuka da hawaye kamar famfo,

Aliyu ya rikice besan time daya fara hawaye ba jikinshi na rawa yace"faseelat dan Allah karki bari ya zube ki temakamin"

Ta kalleshi tana cikin ciwo ta cije lips tana cigaba da kuka,

Ya tashi dasauri ya jawo jallabiya ya zira ya daukomata riga da zane jikinshi na rawa yasamata ya kinkimeta zuwa mota,

Yana fita ya bude motar ya sata ciki ya zagaya ya tada ya nufi prvt Hosp daita,

Faseelat ta kwantar da kai jikin seat tana hawaye tana kara dafe mara,

Aliyu na driving dasauri duk hankalinshi na kanta yana kallonta yanaji kamar ya dagata sama ya dubata ko ta fara bleeding bakinshi na rawa yace"ki...ki kara hakuri honey munkusa"

Ta jinjina kai ta hadiyi miyan wahala yanata mata sannu har suka isa bai bari tayi tafiya ba ya dauketa har ciki nurses suka amsheta suka shiga daita ciki suka fara dubata,

Kokadan ba jini amma daf cikin dake jikinta na 3wks yake da zubewa sukai mata allurai suka bata magunguna nan da nan ciwon jikinta ya lafa ta dora hannuwa kan cikin tana meda numfashi a sannu,

Likitan data dubata ta kirashi office ya zauna yana kallonta hankalinshi tashe yana jiran ta fadamai faseelat tayi miscarriage,

Doctorn tace"ur wife is 3wks pregnant yana da kyau ka daga mata kafa har zuwa lokacin da cikinta zaiyi kwari yanzu shes safe mun bata drugs bayan paying bills zaka iya daukarta ku tafi gida amma ka kula sosai"

Wani sanyin dadi ya mamaye Aliyu yana faraa yace"thank u doctor nagode"

Tai murmushi tace "ade kula" ta mika mai paper,

Ya tashi yaje yayi paying sannan ya shiga dakin da faseelat ke kwance tana kwance har bacci ya dauketa hannunta biyu kan cikinta,

Yana sakin murmushi ya karasa ciki ya janye hannuwanta ya dora nashi akai yafara shafar cikin yana cikin farinciki marar misaltuwa,ta bude ido tana kallonshi suka hade ido ya sakarmata murmushi,

Ta mayar masa ta sauke numfashi,

A hankali Aliyu yace"tnx u"

Ta harareshi ta turo baki,

Yayi dariya ya kamata ta tashi zaune yana murmushi yace"zaki iya tafiya? "

Tai murmushi ta fara kokarin sauka kasa,

Yace"bi a hankali heartbeat akwai ajiyata"

Tai murmushi tana ganin bazai fita farinciki da cikin ba ta mike tsaye yasa mata takalma ya kamata suka fita har bakin mota ya bude mata ta shiga ya zagaya ya shiga ya tada suka nufi gida,

Wata irin kula suke da cikin kowanensu na fatan fitowarshi lpy,

Dole Aliyu ya hakura saboda a yanzu yafi son haihuwa fiye da sex din burinshi yaga jininshi a duniya,

cikin yazo da wani irin laulayi bata cin komi se abu me sanyi drinks fura yogurt kunun aya kunun zaki sobo kunun tsamiya dasauransu duk tabi ta rame tai fayau gashi bata son ko kamshin turare kamshin man shafawarta kanshi bataso, yana 3months tafara samun sauyi tana samun sauki time dinne ta fara cin abinci suma irin na masu ciki kuma time din cikin yazo da son sex duk yadda takeso sede Aliyu ya danyi kadan saboda karyayi asaran babynshi ,

Yau da safe Aliyu ya shirya zai fita shago tana falo kwance idanunta lumshe ya fito ta bude ido tana kallonshi tanajin desire ,

Yazo ya zauna gefenta yana mata kallon kauna yace"heartbeat ya jikin ki?"

Tai karamin murmushi tai shiru,

Yace"kinki cin komi wai me kkso?"

Tace"tuwon dawa miyar kuka da yajin jego"

Yana dariya yace "kutt yajin ma se na jego?"

Ta harareshi lips dinta gaba ,

Yayi murmushi yace "sorry ko ina yake sena nemo shi aiba zama my princess zataci tuwo"

Ya fiddo waya ya kira mama ta dauka ya gaidata yace"am mama nace jiya tuwon dawa kukai ?"

Tace"eh "dukda bashi akaiba da niyyar zata girka,

Yace" yawwa mama akwai tashshin jego?"

Mama tai karamin murmushi tace"eh akwai kowane iri"

Yayi dariya yace "ganinan zanzo na dauka kar asa mata manshanu amma batace dashi ba"

Mama tace"se kazo "ta kashe kiran ta tashi ta dora tuwon tunda ta gama gano faseelat tana da ciki take murna shiyasa take aika mata da kayan kwalamar masu cikin time to time,

Faseelat ta harareshi tace" se kafadamata na wa ne? sai kace kai keso"

Yayi murmushi yace "tasan komi ai rannan bayan kinje naje taita zuba adduoi"

Faseelat tai murmushi tana tuno abubuwan da ake kawomata but bata kawo komi ba cos dama can tana dan aiko mata da abubuwa,

Aliyu ya mike tsaye sannan yace"ni me zaki dafamin?"

Tai dariya ta kwantar da kai jikin kujera tace"ni mana kullum a dafe nake amma cin ya gagara"

Yayi dariya yace "na lura babyna yana son abun nan sosai ko gajiya bayayi"

Tace"kuma se gudunshi kake ba"

Ya duka ya dora hannu kan cikin yace"my blood kayi hakuri inason lpyarka banason wani abu ya sameka I'm sorry"

Ya kalli faseelat sukai dariya tare ya kama lips dinta yadan tsotsa sannan ya zare nashi yace"sena dawo"

Idanunta lumshe tace"Allah ya dawomin da kai lpy"

Ya fita ya nufi wurin aikinsa cikin farinciki,

Faseelat ta rungume cikin tana jin kaikayi a jikinta tace"kaji abinda abba yace ko? ka bari ka kara kwari tukun abbanka jarumi ne sosai"ta saki murmushi tana tuno baya,

Bayan 6 months,

Da rana su aysha na zaune suna launch taji fitsari ta tashi dakyar ta sauka ta shiga toilet din falonsu,

Tana zukunnawa faya ta fashe azabar ciwo ta taso mata ta fara kwalawa fahad kira "yaya... yaya"

Fahad ya debo abinci zai kai baki ya saki spoon din ya shiga toilet din da gudu ganin halin da take ciki yayi saurin komawa ya kira doctor dake dubata ,

Ya koma kanta ya riketa tana ta nishi,

Ameer da ameera sukai zaune suna kuka har likitan tazo ta shiga ciki ganinta toilet yasa ta medata bedroom sannan ta fara temakamata fahad na gefe yana rike da hannunta ya kasa ko da motsi me karfi a gun yana ta adduoi a zuci,

Cikin kankanin lokaci aysha ta haifi kyakkyawar budurwa wacce ta kerata kyau da komi yarinyar gwanin shaawa ,

Likitan ta kimtsasu da diyar fahad ya rungume diyar ya nata kallo kamar ya medata ciki saboda so,

Likitan tai masu bankwana ta fita,

Tana fita taga su twins nata kuka nanny dinsu na rarrashi tana farinciki tace"kukanme kuke?ku shiga ciki mommynku ta haifi baby girl"

Suka kwasa a guje zuwa dakin suna murna suna shiga sukai wurin fahad suna kallon babyn yana murna yace"kunga new babyn mu"

Ameer na ganin babyn ya matsa gun aysha ya saki kuka,

Aysha na kwance tana gajiye ta rikoshi tace"miye ameer baka murna?"

Yana kuka yace "seki haifo mace kiwa ameera yar'uwa ni ni kadai"

Sukai dariya tare ta rungumoshi jikinta tace"sha kuruminka next time baby boy zan Haifa nai maka aboki"

Yayi murmushi yana turo lips,

Ameera kam se washewa take gata ga kanwarta,

Suna cikin haka mommy ta shigo gidan tana murna ta amshi diyar tanata sa albarka ta fara shirin wankansu,

Da dare Aliyu na rungume da faseelat suna bacci faseelat ta farka ta fara shafarshi yanzu ita tafi neman abun da kanta ga ciki ga sabo,

Aliyu ya bude ido ya kalleta in cool yace"kiyi bacci heartbeat ki huta "yanajin tausayinta

Tace"banajin baccin hero kai kadai nake bukata"

Ya kalli girman cikinta yace"tausayinki nakeji heartbeat kiyi hakuri har ki haihu"

Ta turo baki tana shagwaba ta hade bakinsu wuri daya ta riga tasan aliyunnata,

Suka cigaba da romancing juna cikinta ya girma ba style na kwanciya ta duka yafara sex daita yana mugun jindadinta itama tana enjoying lokaci daya tafara jin ciwo me radadi tafara kokarin kwanciya shi kuma time din yake jindadin abun ya rike kugunta gam ya cigaba tanata nishi da yar kara tana "hero bari ...bari dan Allah"

Kokadan baya jinta harseda yayi release yana yin release ya janye yana meda numfashi faseelat ta jirkita ta sauka a gadon tana nishi ta zukunna ta rike kugu tana nishi tana kuka da zufa,

Aliyu yayo kanta dasauri yana rikice yace"minene ? Haihuwarce?"

Ta jinjina kai tana kara damke kugunta tana hawaye,

Kamar zai kuka yace"seda nace ki hakura kika ki Sam bakya tausayin kanki"

Faseelat tai kara tace"cikina!!!"

Ya tashi dasauri ya sa mata sutura ya kwashi kayan haihuwarta suka fita suna zuwa aka amsheta suka shiga labour room daita tanata nishi nurses na kokarinsu ,

Aliyu yanata kai kawo ya kasa zama wuri daya zufa nata ketomai tsabar tashin hankali ,

Ta nata labour se ana kiran asuba ta haihu ta sambado kyakkyawar budurwarta itama me kama da ita sakkk,

Bayan an kimtsata suka fito sannan Aliyu ya samu damar shiga ciki babynta na gefenta tana kallonta tana murmushi ya shigo ya zauna gefe yana matukar farinciki ya zubawa babyn idanu yana jin kamar yayita zunduma ihu don dadi,

Faseelat ta kalleshi tana murmushi ,

Ya saki murmushi me kyau ya dauki babyn ya rungume yanata kallonta ya kalli faseelat yace"she's ur photocopy "

Tai murmushin jindadi,

Yana kara shigar da babyn jikinshi yace"nagode sosai faseelat da kikashigo cikin rayuwata gashi harkin haifamin baby nima yanzu ina da jinina a duniya nagode sosai Allah ya miki albarka ya barmu tare har'abada"

Ta lumshe ido tana jindadi tace"ameen my hero"

Wata nurse ta shigo dakin dubasu yana murmushi yace "hope komi lpy lau?"

Tai murmushi tace"lpy lau munajira ta kara hutawa a sallemeku"

Yace"alhamdulillah Allah abun godiya ina kara godiya gareka"

Nurse din ta juya ta fita,

Faseelat ta lumshe ido tana tuno haihuwarta ta farko tai karamin murmushi tana tuno danta nura da tsohon mijinta nura,

Aliyu na murna ya kira mama ya fadamata ya kira ya omer ya fadamai haihuwar ba jimawa suka karaso asibityn suka fara amsar babyn kowa na matukar farinciki da rana aka sallamesu suka koma gida mutane suka fara zuwa ma faseelat barka friends dinta kullum suna hanya zainab da take kusa tun da wuri take zuwa se dare ta tafi,

Ranar daren suna Aliyu ya shigo dakin faseelat tasha kunshi da kitso se walkiya take yanata binta da kallon love ya dauki diyarshi duk sanda ya kalleta ba karamin farinciki yake tsintar kanshi ciki ba ,

Faseelat na kallonshi da murmushi tace"gobe suna amma bansan sunan da kasa mata ba"

Yayi murmushi yace "wane suna kike so?"

Tana murmushi tace"kowane kasa yayimin "

Ya sakeyin murmushi yace "ina tsananin sonki heartbeat tun kafin ki haihu ina da kudurin idan na samu mace zansa mata suna faseelat ba wani suna da nakeji yanzu yana sanyayamin zuciyata irin sunanki ina tsananin kaunarki sosai matata"

Ta lumshe ido tana jin tsananin farinciki ta tashi zaune ta kwantar da kai jikin

Please Login or Register in order to submit comment