Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kudinshi nasan kuma ba gidan uwar da zata samu ko da rabinsu a yanzu"

Kawu yace"zataci ubanta idan nazo gidan bazatai mishi wata karyar ba seda ni ta kiyayi haduwarmu"diff yakashe kiran,

Ummi ta kalli faseelat dake tsaye tana raba ido tace"kinji abinda yace ai"

Ta daga kai ta cunno baki tashige daki ta haye bed,

Kawu nagama wayar yayi shiru yana nazarin yadda zaiyi zaa sashi karyar dole ,

Ko minti 5 baai ba aka turo yaro sallama dashi matarshi tashigo tafada mai cikin zullumi yatashi yafita kofar gidan,

Yana fita alhaji dake tsaye still jikinshi nata rawa yayi sauri ya zukunna kasa yace"ina kwana kawu ?"

Kawu yace"lpy lau"yana kallon tashin hankalin dake tare dashi,

Bakinshi na rawa yace"kawu nazo ne inason amin alfarma dan girman Allah ni da faseelat mundade tare muna son junanmu mun shaku sosai kawu dan Allah abarmu tare kar a rabamu wlh muna tsananin son juna zamu shiga hali idan aka rabamu"

Kawu yana ta kallonshi koda bakin alhaji be fada ba yanayinshi ya gama nuna cewar yana tsananin son ta,

Kawu yace"kayi hakuri alhaji tun tuni naba yarinyar nan lokaci takawo miji bata kawo ba kullum kara girma take shine na zaba mata dan aminina yanzu angama komi daurin aure kadai muke jira sede kayi hakuri "

Alhaji nura zuciyarshi kamar ya cirota ya yarda yakeji ya dafe zuciyar jikinshi yakara daukar rawa sosai yanata kyarma yace"kawu ka temakamin yadda Allah ya temakeka kubarmin faseelat inasonta sosai..."

Kawu ya tsaidashi yace "kai ba yaro bane kasan girman alkawari don haka karkai ta rokona don bazan sauya magana ba Allah yabaka wadda tafi ta"

Alhaji nura ya mike dakyar yana hawaye ya juya yafara taku biyu yayi baya zai fadi kawu dake tsaye yana kallon ikon Allah yayi sauri ya tareshi ya rikeshi yace"bi a hankali alhaji kayi hakuri ka dau kaddara"ya sakeshi ganin yatashi

Alhaji ya cigaba da tafiya yana daga kafa daya kan daya kafafun sun masa nauyi har yaisa mota yabude yashiga cike da dauriya yake driving jijiyoyin kanshi na wani irin ciwo zuciyarshi na cigaba da bugu jikinshi na kara tsananta rawa duk da haka tunanin faseelat yake soyayyar da sukai a baya yanayin maganarta,shagwabarta,dariyarta,murmushinta da kalamanta masu dadi da shiga rai da tsayawa a zuci da take fada mai,

Ya rumtse idonshi dake jawur yabude yakara dallawa titi kallo yana cigaba da driving yana tariyo muryarta "I love u dear I really love u I can't do without u"zuciyarshi takara bugawa ya rumtse ido yanajin ciwo yabude saura kiriss ya kaiwa wata mota bugu yayi sauri ya kauce motar tafara kwace mai yarika driving kamar dan maye yana cigaba da tunanin firarrakinsu da suka shude" dear kai me kyau ne kullum kara kyau kake kafi duk mazan duniya" the more yake tariyo moments dinsu the more yake karajin ciwo still ya cigaba da driving to home,

Kawu na tsaye alhaji yaja mota yatafi beko koma gida ba ya nufi gidansu faseelat tana daki ta buga uban tagumi yashigo ummi tabishi da kallo ganin ranshi bace abinda be taba ba ya banka dakin faseelat yana huci,

Ta tsorata da ganinshi tai sauri ta matsa can Karshen gado tana raba ido,

Kamar ya jawota yayi ta jibga yace"ashe ke mutuniyar banza ce mayaudariya kin yaudari bawan Allah kina tunanin Allah zai kyaleki inshi yabarki toki sani Allah seya bi mishi hakkinshi sakarai marar tunani"

Ta dukar da kai tana hawaye tana kara jin tausayin alhaji nura,

Kawu yaja tsoki yace"shashasha komai ya sameshi kece sanadi"yajuya yafita ,

Ummi dake bakin kofa tace"kayi hakuri dan Allah wlh ni kaina naso ta aureshin don yana sonta sosai"

Kawu yace"ita tasani mutumin yashiga tashin hankali gabadaya illahirin jikinshi rawa yake yi harda kuka"

Ummi tace"Allah ya kyauta"

Yace"ameen"yana jimami ya tafi,

Ummi ta shiga dakin faseelat ta takure tanata goge hawaye akai_akai,

Ummi ta tabe baki tace"kinji de ai sai kita rokon Allah kar alhakinsa ya biki kuma ki fatan shi wanga din ya soki kamar hakan"itama tai tsoki tafita,

Faseelat ta kwanta tafara kuka marar sauti me cike da nadama,

Dakyar alhaji yakawo gida idanunshi nagani biji_biji yana shigowa ciki yayi parking ya kwantar da kai jikin sitiyari tari ya sarkeshi yafara ba kakkautawa yana cikin tarin yaji wani abu na dan biyowa a makoshinsa yasa hannu akan bakinsa sannan ya dago sega jini hakan yakara tada mai hankali yabude motar ya ziro kafa daya sannan ya fiddo dayar dakyar ya samu ya fito yana mikewa driver ya taho wurinsa domin yi masa barka da zuwa alhaji kuwa yanayin taku biyu yaji jikin kamar ba nashi ba yakasa yin komi yazo zai zube kasa driver yayi saurin isa ya tareshi yana fadin "subhanallahi alhaji!! alhaji sannu"

Me gadi ya taso ya kama mishi suka nufi cikin gida dashi jikinshi a sake baya cikin hayyacin shi,

Suna shiga main Palo da sallama Hjy Rukayya na zaune ta amsa ta meda hankali gun, abinda tagani yasa tai wuf ta tashi tsaye kamar kyaftawar ido ta isa wurinsu duk hankalinta a tashe bakinta na rawa tace"me...meya sameshi?"

Atare sukace "wlh bamu saniba yanzu yadawo a haka"

Hawaye shar_shar suke zuba a fuskarta tace"Ku hawo dashi sama ta kama musu suka haye bene dashi har bedroom dinsa suka kwantar dashi suka fita suna Allah ya bashi lpy,

Hjy Rukayya na kyarma ta dauko waya ta kira family doctor ta sheda mai alhaji baya lafiya sosai,

Doctor ya taho dasauri ,

Tana gama wayar takoma kan alhaji ta zauna bakin gadon tana kallon fuskarshi tana zubda hawaye ta tsorata sosai da taga jini gefen bakinshi,

Tana kuka tace"alhaji sannu Allah yabaka lpy "

Ta tashi ta nufi part din abida donta shaida mata ,

Abida suna ta wayar masoya da jamil dinta ya matsa akan yana missing jikinta yanata begging tace"alright naji gobe zan samu nafito da wuri zuwa marece zan dawo"

Jamil yayi ihun murna yace"I hug u sugar give u kiss of lifetime "

Tace"thank...."bata karasa ba Hajiya Rukayya tafado dakin tana kuka duk kwalamata kira da takeyi bataji ba saboda sunyi nisa cikin soyewa,

Hjy abida ta latse kiran hankalinta tashe take kallon Hjy Rukayya

Hjy na tsaye tace"taso_taso alhaji baya lpy harda aman jini"

Gaban hjy abida ya bada dumm hankali tashe ta baza da gudu zuwa dakin alhaji nura hjy Rukayya tabi bayanta,

Hjy abida na shiga taga yanayinshi itama tafara hawaye tana hawayen ta haye gadon tana kuka take cewa "meke damunka alhaji minene ya jefa ka a wannan halin?"Tana kuka sosai

Suna cikin haka bame rararshin wani alhaji nata numfashi sama_sama doctor yazo ya razana da yanayinshi ya shiga bashi temakon gaggawa,

Bayan minti 20 bacci ya kwashe alhaji ga drip hannunshi suna shiga,

Doctor ya ciro handkerchief ya goge zufa ya kalli su hjy Rukayya sunyi zugum_zugum suna ta hawaye hjy abida ko zuciyarta harbawa take tana jin tsoron kar asirinta ne ya tonu,

Doctor yace"akwai abinda ya dagawa alhaji hankali sosai har ya kamu da hypertension anyi saa sosai da yafadi da maybe yana iya samun paralyse alhaji na bukatar kulawa sosai a kiyaye duk abinda yakeso da wanda bayaso a kula da drugs dinshi da duk abinda zai bata masa rai domin idan akai kuskuren haka harya fadi zai iya kamuwa da paralyse"

Duk basu iya magana ba sede kai suka jinjina doctor yace"Allah yabashi lpy "yajuya ya fita,

Hjy abida ta hadiyi miyau me daci tana tunani meyasa alhaji yadawo kafin ya karasa two weeks din?meye dalilin hawan jininsa?

Itama hjy Rukayya tambayoyin da take tawa kanta kenan sukaita kallonshi sunajin tausayinshi,


Faseelat taci kukanta takoshi da azahar tana kwance sega kiran fahad ta tashi da zumbuleliyar hijabin a jikinta tafita tunda ta fito yake kallonta duk tayi wani iri kuma ta rame,

Ta bude motar tashiga ta kwantar da kai a seat ta rumtse ido yanata kallonta zuciyarshi badadi bayan minutes sannan yace" sannu Queen "

Ta daga kai kurum,

Yace"I have seen babu sauki ko mutafi asibity?"

Ta bude ido ta dan kalleshi ta girgiza kai,

Yace"oh my god!" ganin idanunta jawur sosai yace"I'm sorry bari mutafi asibity"

Tace"noo banaso naji sauki"

Yana ta kallonta ya girgiza kai yace"I insisted dole na kaiki asibity kina bukatar likita"

Tace"aa plss"fuskarta shagwabe,

Ya kalleta sosai batare da jiran komai ba ya dauki hanyar hospital,

Tai shiru tanata tunanin alhaji idonta lumshe fahad na driving butsu_butsu ya kalleta yace"sannu queen"

Ta daga kai har suka isa wata private hospital yafita dasauri ya bude mata tafito hannunta dafe da kanta saboda yunwa da damuwa harwani juwa takeji ya kulle mota suka nufi ciki a jere,

Ganin yadda take ta dan yin layi fahad ya karajin tausayinta sosai, ya rike mata hannu hannunsa cikin nata suka shiga ciki zuwa office din doctor,

Doctorn abokin fahad ne yana ganinsu yace"subhanallahi amaryarmu bata lpy zaunar daita "

Ya dan riketa ta zauna shima ya zauna ya sake rike hannunta yace"sannu"

Tai shiru doctor ya tashi yafara dubata fahad na zaune yana kallo,

Yana cikin dubata yacewa fahad"meke damunta ne haka?"

Fahad ya girgiza kai mean be sani ba ,

Doctor yakoma ya zauna ya kalleta yace"our bride meke damunki haka tension ne yayi causing fever da headache jikinki"

Tai shiru kawai,

Ya meda kallonshi gun fahad yace"ya kamata a kula daita and a rika bata abinci kar wani ciwon ya kamata"

Fahad ya jinjina kai,

Doctor ya kalleta yace"madam arage stress our friend beda problem ehen and he's gentle"yayi murmushi,

Fahad ya harareshi ,

Ya dauki waya ya kira sega nurse yabata paper few minutes tadawo da drugs ya amsa tafita shi kuma ya mikawa fahad yace"remember anashan magani ne only bayan anci abinci"

Fahad ya jinjina kai ya lumshe ido yabude yace"tnx u"in cool voice dinshi bare yanzu data kara sanyi saboda queen ba lpy,

Ya tashi sukai musabaha hannunta cikin nashi suka fita doctor yabisu da kallo yayi murmushi yace"lovers"

Sukaje bakin motor ya bude mata ta shiga ya rufe ya zagaya yashiga yafara driving,

Tunda yafara driving yake tunanin minene yake damunta ya kalleta still idanunta lumshe ya meda kallo a titi,

Sosai yakejin badadi kamar yadawo da ciwon jikinshi jin ance batacin abinci memakon yabi hanyar gida seya nufi wani babban restaurant har suka isa bata saniba seda taji tsayuwar motar sannan tabude ido memakon ta ganta a bakin gida seta ganta a bakin restaurant ta kalleshi a marairaice fuska tace"I'm not hungry ka kaini gida I want to rest"

Ya daga mata kai yace"idan kinci abinci kinsha magani zamu tafi ki huta"

Ta kalleshi kamar zatai kuka,

Ya hade hannuwanshi wuri guda yace"plsssss"shima a marairaice,

Se tai shiru yaji dadin hakan kuwa ya fita ya bude mata kofa tafito suka shiga restaurant din,

Yasa ankawo pepper meat da yoghurt da ruwa only plate guda don shi he's not hungry,

Tayi tagumi ta tisa abincin gaba tanata kallonshi sam batajin dadi musamman yadda taga alhaji ya rude da maganganun kawu sun tada mata hankali,

Fahad nata kallonta yace"plsss eat sena medaki gida"

Idanunta cike da hawaye tace"I'm not hungry "

Ya rumtse ido ya bude ranshi na baci yunwa kanta ai ciwo ce,with out choice ya matsa da seat nashi ya dauki spoon ya debo naman yakai bakinta ,

Taki amsa sede ta kure spoon din da kallo,

Yace"plssss"in cool voice,

A hankali ta bude baki ta amsa ya cigaba da bata tadanci kadan yabata drugs da yoghurt tasha sannan ya kuma rike mata hannu suka fita suka shiga mota har bakin kofar gidansu,

Yanayin parking ya kalleta tanata jin bacci ya mika mata ledar drugs yace"plss do help me kirika shan maganinki akan time kuma I'm begging u plss kidena damuwa "he's thinking damuwa ce da kowace Amarya ke shiga idan ankusa bikinta,

Ta daga kai dakyar tayi karamin murmushi da yarage masa abinda yakeji aransa yace" I will come back later "

tabude motar ta fita tana tafiya a hankali tabude gidan ta shiga,

Yana ganin tashige ya sauke ajiyar zuciya ya nufi gida,

Tana shiga cikin gida ta wuce daki ta haye bed bacci takeji amma takasa ta dauki waya tafara kiran alhaji wayar nata ringing hjy Rukayya ta dauko takashe ta saboda karta dameshi,

Jin ankashe wayar yasa faseelat takara shiga tashin hankali wasu sabbin hawayen suka fara sintiri a kumcinta seda tasha kuka sannan bacci ya dauketa,

Fahad na komawa gida ya watsa ruwa duk seyaji baison cin komai saboda ciwon faseelat shiyasa yasha lemu ya dauki computer dinshi ya cigaba da aiki,


***************

A niger acikin kauyen shinkassane,

Aysha ce kwance akan cinyar mommy tana mata tsifa gashinta liya_liya me tsayi taushi sosai da salki,

Cikin dan lokacin nan duk yadda aysha ke jin nauyi seda ta dan saki jiki da mommy saboda yadda take nuna mata kauna da kulawa,

Mommy na mata kwanta tace"daughter insha Allah zuwa Sunday ko Saturday zamu koma gida inason mutafi da wuri donki samu kiyi jarabawa"

Dadi ya mamaye aysha tai murmushi tace"nagode mommy "

Mommy tace"and bayan jarabawa soon se a daura aurenku koba haka ba?"

Tai murmushi tanajin nauyi ta daga kai,

Mommy tace"yawwa daughter Allah ya gwadamin lokacin farin cikina baze misaltuba"

Suka cigaba da dan labari Wanda mommy ce keyi aysha na amsawa ,

Bayan tagama mata ayshar takoma kan seat ta dauki wayarta tabude pic din fahad tana kallo sosai sonshi yayi mata damkar da cireshi zeyi wuya,

Tana cikin kallon pic din mommy tazo ta bayanta taita kallonta kamar kar tai mgna se tayi dariya tace"kamar nasan wannan fuskar"

Aysha tai sauri ta boye wayar tana jin matsananciyar kunya ,

Mommy tai dariya tace"bazaki dena jin kunyata ba ko? Oya bani wayar na turamiki wasu aini dadin hakan nakeji aysha"

Aysha najin kunya ta mika mata wayar ta tura mata wasu sannan tabata tafara kallonsu tana akagare ta sanyashi a idanunta,


A gida kuwa abbu na zaune kira yashigo wayarshi,

Ya dauka yayi sallama one of his friend daya masa bincike yace"ranka yadade wani abu nagani daya dauremin kai yaron da kasa akaimaka bincike kanshi still shi din naga invitation na bikinshi next week"

Sarki yadan razana dajin wannan labari yace"ka tabbata shine?"

Yace"seda nai bincike sosai sannan nakira ance auren da nemenshi da sakashi baai week ba sannan yau na ganshi da yarinyar awani restaurant"

Jin haka yasa hankalin sarki yadan kwanta kenan mommy batasaniba and shi kuma mommy zai bawa aysha ba fahad ba ,

Yayi gajeren murmushi yace"shikenan zanyi shawara nagode sosai"

Sukayi sallama bashiri sarki ya shiga cikin gida yawuce dakin ummarsu aysha direct,

Tana kishingide yana shiga tatashi zaune tana karantar yanayinshi,

Ya zauna kusa daita ya sauke numfashi yace"labari yazomin fahad da zanbawa aysha zeyi aure next week"

Umma tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun!!! ya hakan zai faru bayan ga maganar da mukayi da mommyn shi?"

Ya kara sauke numfashi yace"yace min da neman auren da saka rana baayi week ba"

Fuskarta bawalwala tace"yanzu ya zaayi?"

Ya danyi shiru na minutes sannan yace"zan bashi aysha a second wife kuma zan bashi ne saboda mommynshi and shima yana da hali me kyau after shi bansaniba ko zata samu kamarshi but ya kika gani?"

Umma tace"gaskiya kuma ita mommynshi bazata ji dadi ba yadda takeson aysha sede muyi fatan Allah yasa hakan yafi zama alheri"

Yace"ameen"


***************

A Nigeria


Da marece fahad yakoma gidansu faseelat yayi ta kiran number dinta amma bata dauka ba saboda kanta kamar ze rabe biyu takeji yagaji da kira ya dan zauna yana ta kallon kofar kamar yashiga gidan se kuma ya hakura yanajin tausayinta yasan ciwon ne ya hanata dauka ya tafi,

Da Maghreb ma ya sake kira bata dauka ba hankalinshi yakara tashi dukda besan firar dare anayin ishai ya tafi gidan bayan ya siya mata drinks, ya dade tsaye sannan omer yazo ze shiga suka gaisa sannan fahad ya masa ya me jiki ya kalleshi yace dasauki sannan fahad yace"inata kiran wayar ta bata dauka ba nasan ciwon ne yayi tsanani hankalina duk ya tashi"

Omer yace"bari na shiga naganta"yajuya ya shiga ciki,

Yana zuwa ya samu Ummi na bata tea a baki haushi duk ya cikashi katuwa daita ana bata abinci kamar ciwon yayi waste sosai,

Ya kalli Ummi yace"fahad yazo yana kofar gida yazo ganin jikinta"

Ummi tace"to kace yashigo"

Ya juya yafita Ummi ta yafa gyale takoma ta zauna tana cigaba da bata tana sha,

Bayan minutes fahad yashigo shida omer suka shiga ya zukunna har kasa yagaida Ummi sannan yace"yame jiki?"

Ummi tace"dasauki"

Yace"Allah ya bata lpy"

Tace"amin angode"

Faseelat da idonta ke lumshe ta bude ta kalleshi ta kuma lumshesu taji dadin zuwan nashi sosai ita dama tariga tasan yana sonta over,

Fahad ya tashi ya ajiye ledar hannunsa ya kuma kallon faseelat yace"Allah yabata lpy" Ummi ta kuma cewa "ameen"ya juya yafita,

Yashiga motarshi yakoma gida yanata jin jikinshi shima kamar marar lpyar,

Ummi na gama bata takoma ta kwanta Ummin tafita,

A hankali ta dauki waya takara kiran alhaji switch off,

Tana kwance bacci ya fizgeta ta farka yakuma fizgarta ta farka haka de,

Shiko alhaji be farka ba se can tsakar dare yabude ido a hankali duk yaranshi manya da kananu sun zagayeshi sunata kallonshi ,

Su hjy Rukayya sukai saurin matsawa suna " alhaji sannu Allah yabaka lpy "

Ya lumshe ido yafara tunanin dear dinshi ,

Hjy Rukayya ta kalli yaran kallo daya duk suka tashi suka fita a dakin,

Ta kalli hjy abida tace"ki hado tea "

Hjy abida ta tashi ta tafi hado tea,

Hjy Rukayya ta na kallonshi da tausayi tace"sannu alhaji dan Allah kadena sa abu a ranka kasani samu da rashi duk na Allah ne kadena damuwa komai da kagani ka daukeshi kaddarar rayuwarka ba danni ba kodan yaranka duk muna cikin hali na rashin lpyarka kayi hakuri da komi plss"dukda batasan me ya rasa ba,

Shi kanshi yasan gaskiya take fadi ya jinjina kai ,

Ta tashi ta dauko bowl ta kamashi ta jingina shi a bed ta wanke mai baki Sega hjy abida da tea ya kalleta ya dauke ido ya lumshesu,

Duk tasha jinin jikinta tace"sannu alhaji Allah yabaka lpy "

Ya jinjina kai hakan da yayi yadan sa mata relief,

Bayan tagama bashi tea din tabashi drugs hakan yadan sa yasamu relief yakoma ya kwanta yanata tunani drugs din suka bugar dashi bacci ya daukeshi,

Yanayin bacci hjy Rukayya ta tashi tafita domin girkin hjy abida ne ,

Hjy abida tai zaune Sam bacci yaki zuwa mata se dana sanin abinda tayi takeyi a yanzu gabadaya tasa itace sanadiyyar rashin lpyarshi,

Can gab asuba ya farka yanata tunani yaga wayarshi akan bed ya mika hannu ya dauka ya ganta a kashe ya kunnata tagama booting ya shiga call log kiran faseelat ne asama and last kira anyi rejecting this means tayita kira suka kashe ,

Yana shirin kiranta sega kiranta yashigo unexpected ,

Abun yabashi mamaki besan time daya tashi zaune ba ya dauki wayar yakara a kunne hjy abida tai kasake tana kallon ikon Allah,

Faseelat da ko cikin daren seda taita kira akashe yanzu ma takira da niyyar idan tana a kashe zata masa text ,

Batasan tana son alhaji ba se yanzu ne tagane hakan tausayinshi da takeji yafi tausayi dole akwai dan son ko yane,

Jin an dauka murya na rawa tai saurin cewa"dear kayi hakuri dan Allah ka kuma yafemin"

Maganar cike da tausayi da rauni,

Idanunshi lumshe yace"bakimin komi ba dear ki dauki hakan kaddararmu kiyi hakuri kiwa iyayenki biyayya nasan sekin daure amma ki daure kamar yadda nakeyi amma ki sani inasonki sosai jiya I vomit blood saboda zafin rasaki"

Tai saurin tashi zaune jin yafadi jini tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!"ta rufe baki da tafin hannu,

Yace"yes dear ban lpy I'm seriously ill zanci gaba da rayuwa da cutar sonki"

Hjy abida ta cika tai fammm tanajin kishi da karfi tace "maganar banza"

Alhaji ya bude ido ya mata wani banzan kallo sannan yakuma lumshe shi,

Dukda faseelat tajita bata damuba tace"dear kana wane asibity I will come zanzo dubaka"fatanta tasamu ya yafemata su rabu babu hakkinshi,

Yaji dadi yana kara jinjina son da take mai yace"ina gida "in brief

Batare da tsoro ba tace"anjima da safe zanzo Allah yabaka lpy"

Yace"ameen my dear tnx u"

Tace"seda safe"ta kashe kiran,

Rabin ciwon ya dan tafi saboda wannan wayar data kira,

Hjy abida hannunta akan gemu tana jinjina rainin wayon yar iskar da alhaji yake kira dear tace"to wlh tallahi idan har tashigo gidannan sede ta fita babu wani part a jikinta"


Alhaji ya bude ido yana kallonta,

Ta rike kugu tana yamutsa fuska kishi fal ranta tace"dan ka me damu wawaye zaka gayyato karuwarka anan gidan to wlh idan har ta shigo cikin gidannan sede gawarta"

Ranshi a dan bace yake kallonta tace wa faseelat dinshi yar iska da karuwa ba karfi jikinshi yace"abida banason surutu kiyi ....shiru"

Tace"senayi surutun aikaine kajawo munafikin Allah ashe saboda karuwa kake ciwo duk kadaga mana hankali damu da yara duk bawanda yayi bacci to wlh idan har tazo sena kasheta"

Yayi shiru yana kallonta ,

Tace"ohoo !!!!!kasa ka akai auren karuwar kake nema baka samuba shine hardasu hypertension?" tabuga tafi tare da cewa"he_he ikon Allah baya karewa alhaji da soyayya to wlh baka isaba"

Yadda take ta daga murya hjy Rukayya da ta kwana salla tataso tafito tashigo dakin tana mamakinta yadda take daga muryawa patient,

Tazo ta sameta tsaye ta rike kugu tanata zuba,

Ta kalli alhaji yana zaune jikin bed yanata kallonta,

Hjy Rukayya tace"haba mommynsu minene kike daga murya kinsan baya lpy muyi fatan yasamu lpy ma kike ta daga murya koina anaji"

A masife abida tace"karya samu lpyar mommynsu alhaji neman aure yake aka kasa shi shine hardasu hypertension yanzunnan cikin daren nan karuwar ta kirashi wai yana ce mata dear"

Hjy Rukayya tace"aa abida"

Hjy abida tace"karya zanyi bari kigani" taje ta wafto wayar dake hannun alhaji ta latso dear ta nuna mata tace"kingani da idonki yar iskar wai fadamishi take zatazo dubashi har gida"

Hjy Rukayya da tun jiya tagani kuma ba yadda zatai tace"nagani yanzu de kiyi hakuri tunda an kasa shi tazo ta ganshin ta tafi bashi kenan ba"

Hjy abida tace"wa!!!! Billahillazi mommy idan har tazo gidannan senaci ubanta yama kirata ya fadamata kartazo tun wuri"

Hjy Rukayya ta girgizakai bata jindadin abinda abidar keyi karta karasa shi lahira ta anshi wayarshi ta aje kan bed taja hannun abidar suka fita waje,

Seda ta kaita kofar dakinta tace"kishiga kiyi salla kuma dan Allah ki temakamana alhaji ya samu lpy idan kinata wannan abun yazaai ya samu lpy kidena inbaso kike ki karasa mana shiba"ta juya tatafi tanajin haushinta,

Hjy abida tace"wlh sede kartazo gidannan inde tazo setaci ubanta sosai"zuciyarta nata pumping tanata balai tashiga dakinta tana zuwa wurin wayar ta sega different missed call na jamil tai tsoki ta shiga number ta sauya sunan to jameela,batare da ta kiraba tashige toilet ranta a matukar bace,

Hjy Rukayya dakin alhaji takoma ta samu yanata tari ta karasa gunshi dasauri tanata masa sannu har yadan lafa ta kwantar dashi ta zauna bakin bed din tabuga tagumi tana kallonshi idonshi rumtse,

Seda yara suka fara zuwa ganinshi bayan sunyi asuba sannan ta fita a dakin taje tasake alwala tayi tata sallar,

Ta dawo tasamu yaran sun haye bed sun zagayeshi wasu a jikinshi wasu a zaune ,seta juya taje ta hadomishi tea tadawo taturasu suyi shirin makaranta tanata masa sannu ta tadashi ta wanke mai baki tabashi yasha ta kwantar dashi ta rufeshi da duvet ,

Tana zaune take kallon fuskarshi a kullum idan wasu abubuwa suka faru seta rika ganin duk zamanta dashi bata fahimceshi ba saboda bata taba tunanin alhaji zeyiwa mace kuka bare hardasu aman jini lalle kowace ce tafisu matsayi,


Bacci ne ya daukeshi sannan taje ta sallami yara tashiga wanka,


Faseelat kau tana samu suka gaisa tai asuba ta kwanta bacci karfe 8 tatashi ta duba waya ba missed call din fahad tasan kila don karya tadata shiyasa be kira ba kuma kozai zo ganinta se tara kila ko yanzu takwas din gwara taje tadawo kafin yazo ,

Tatashi tai brush tai wanka tasaka doguwar riga black tai rolling da yellow din gyale ta dauki key dinta ta leka dakin Ummi,

Ummi na gyaran dakin ta tsaya tace"ke kuma ina zaki keda baki lpy ?"

Faseelat ta yamutsa fuska tace"Ummi a makaranta ake neman mu nama makara"

Ummi tace"toki sauri Allah yakiyaye"

Tace"ameen"tajuya tabude gate tashiga mota tabar gidan ta dauki hanyar gidan alhaji nura data dade da sani.



[12/6, 10:01 PM] SHALELE: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



2⃣9⃣


*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace na umarceku da yin gaskiya domin gaskiya tana kai mutum ga nagarta nagarta kuma tana kai mutum aljanna*




*My fans I'm sorry kunjini shiru nayi tafiya ne to bansan wurin ba network ba seda naje shiyasa ku kaita nema na baku samu ba I'm really sorry kuma nagode da kulawarku a kaina Allah yabar kauna ina sonku sosai*



*wannan pagyn na duk masoyana ne inde kinsan kina sona to kiyi murna domin pagyn naki ne🥰*



Fahad da yataho ganinta a dede round yaga motar ta ta nufi wani road abun yabashi mamaki sosai ita

Please Login or Register in order to submit comment