Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alheri" tana rufe baki suka farajin order faseelat tai saurin fita,

Sega motar furniture's kofar gidansu ta tsaya ta kalli matashin dake tsaye kofar gidan tace"lpy ?"

Yace"eh alhaji nura yabamu address din gidan yace mukawo kaya"

Ta kalli babbar motar dake bayan ta ta kujeru a Leda while bed din a kwali purple da fari tana kara yaba halin alhajinta tace"kushigo dasu"takoma ciki,

Su kuwa suka fara jilar kayan suna shiga dasu ,

Tana komawa tafadawa Ummi ,Ummi taita sa masa albarka itako faseelat din duk jikinta mutuwa yayi yana sonta tsakani da Allah ita tana yaudararshi ta kirashi tai masa godiya suka tafi saloon dinsu acikin sabuwar motar ta da zata kai million 15,

Suna zuwa akafara gyareta na musamman na amarya but duk jikinta a mace

Fahad suna hidima yana tunani wata zuciyarshi na karyata shi tana nuna mai faseelat bazatai hakan ba idan kuma hakanne bazata yi yadda tayi ba idan mutum baiyi Abu ba akace yayi dole yaji ciwo bare zina kome tayi shiya jawo se yafara ganin laifinshi yafara tunanin yadda take masifar idonta jawur sosai yaji haushin kanshi wannan yasa bayan awoyi yayi dialing number dinta tana gani tayi tsoki taki dauka harta tsinke yanaji ta tsinke jikinshi yakara mutuwa yasan data aikata da bazata tsaya wani nuna bacin ranta ba hartaki daga kiranshi yafara tunanin yadda zai kara haduwa da ita yana tuno duk maganganunshi a kanta yanajin kunya,

Suna ta shirye_shirye har azahar sannan ya koma gida yana zuwa ya samu aysha falo tayi kyau sosai tana ganinshi tai murmushi tace "Yaya sannu da zuwa"

Ya kakaro murmushi yace "kanwata kina lpy?"

Ta daga kai,

Yayi shiru don duk hankalin nashi na kan faseelat yana zaune ya rike kanshi yana tunani,

Itako aysha dadi kawai takeji ganin lefenta da kuma jin yan gidansu na nan zuwa gobe,

Mommy ta shigo falon ta kalli fahad ranta badadi tazo ta tsaya kanshi tace"fahad lpy kake?"

Ya dago ya kalleta yace"mommy kaina ke ciwo sosai"

Tace"sannu katashi kaci abinci mu munyi kasha magani kaje ka huta dan Allah harda rashin hutu ma"

Yace"to mommy "

Ta kalli aysha tace mai"mu fita zamuyi katashi kasha kaji?"

Ya daga kai,

A hankali aysha tace"sannu Yaya"fuska bawalwala,

Ya daga kai ,

mommy ta mika mata hannu suka fita suka shiga mota suka nufi gidan wata friend dinta dazata rika koyamata karatu kafin tafara zuwa domin ko mommy ta biya kudi ko taci ko bata ci ba zata shiga school din,

Fahad na zaune Sam baijin dadi ya zaai ma wani Abu ya iya shiga bakinshi ya tashi yakoma part dinshi ya watsa ruwa yasha drugs ya kwanta yana cigaba da tunanin faseelat maganarta na rashin zuwa aiki ya fadomai yace"to fa"gashi aysha zatarika fita ita a ranshi yayi fatan Allah yasa de kar tadamu da hakan saboda ita aysha don baida choice ne,

Yanata tunani baccin gajiya ya daukeshi ,

Bangaren su Jamila Amarya takarayin fayau skin dinta yayi lufff yana shining saboda supplement da gyaran da tasha breast dinta sun kara girma suna cike ,

Ango kullum hada miyau yake ba arziki yake mafarki duk dare a kagare yake sosai,

Yau da marece sukayi kauyawa party Mimi ta gayyato friends dinta sunyi shegun kwalliya itama jameela tayi nata sukaita abubuwa a wurin su ko friend din Khalil ko a jikinsu sunata kallo ,Khalil sebin jameela yake da ido kamar ya kamota ya rungumeta ko yasata lungu,

Gab Maghreb su faseelat suka koma gida an mata saloon an mata kitso duk ya zubo a kan kafada kunshinta yayi mugun kyau sosai ,

Tana shigowa ta iske gidannasu cike yanuwa yan nesa duk sunfara zuwa, tashiga dakin Ummi mana taga an sauya furniture's da na alhaji baki bude tace"Ummi yayi kyau sosai wlh "

Ummi tace"tunda ba kaimiki zaai ba gwarani naci biki dasu"

Faseelat tai yake tuno fahad ta wuce daki ta rage kaya tafito tai wanka takoma tai sallar Maghreb ta zauna tsara kayanta da zata tafi dasu a can gidan yayinda wata zuciyar ke fadamata kila kiran da fahad ya mata kirane na fada mata ya fasa aurenta dukda haka ta cigaba da shirye_shiryenta,

Bayan ishai bayan su fahad sunyi dinner shikam ya tsakurane mommy tabasu wuri,

Fahad ya Ciro karamin akwatin sarkar aysha ya mika mata,

Tanata murna ta amsa tace"nagode yaya "

Ya mata murmushi ya tashi ya fita dan baze iya wani janta labari ba,

Ya koma part dinshi ya kwanta ,

Abida na zuwa gidansu tasha maganinta ta danji dama zuwa 11 takoma gida ta kira jamil tafadamai taje tadawo yanata kasheta da kalamai harta saki tana dariya,

Yanzu bayan sunyi dinner alhaji nura ya koma part dinshi ,

Taje part dinta ta sanyo wata transparent rigar bacci tadora Zane sama ta dauki kwayoyin desire ta nufi part din alhaji,

Yanata latsar computer dinshi tashigo da sallama beko kalleta ba ya amsa tana kallonshi tace"alhaji kasha magani kuwa?"

Ya girgizakai ,

Tace"ya kamata kasha kuwa tunda wuri "ta nufi fridge ta dauki cup ta tsiyaya lemu ta jefa kwayoyin duka hudun ringis sannan ta kai masa,

Ya amsa ta balli maganin tabashi yasha ya kara shan lemun ya mika mata sauran ,

Tai murmushi taje ta ajiye tadawo ta zauna kan seat tana chart da jamil tafada mai tasa mishi ya nuna yanajin kishin alhajin,

Bayan awa harta fidda rai cewa zaiji desire alhaji yafara jinta ganin yana satar kallonta yasa ta yaye zanen jikinta ta ajiye jikinta yakara fitowa,

Jinshi wani iri de ya kashe computer ya kalli abida yace" anan zaki kwana?"

Tace "eh alhaji na" tana murmushi da kashe ido,

Yayi murmushi ya mika mata hannu yace"come to me"

Tatashi tana rangwada ta je ta haye cinyar alhaji yafara sunsunata yadan lagudeta sannan yafara sex daita,

Kokadan bata jin dadi se tunanin sex dinta da jamil kawai takeyi bayan 5minutes yayi release ya cigaba yayi na biyu badon joy stick din ta kwanta ba ya shiga toilet yayi wanka ya dawo ya kwanta yanata kwantar daita har bacci ya daukeshi,

Jin saukar numfashin shi yayi bacci abida tatashi ta dora zanenta ta koma part dinta ta kira jamil ta yaye zanen tanajin desire suka cigaba da sex vedio dinsu ,

Faseelat nata jiran kiran fahad shiru tai shirin baccinta ta kwanta tana tunanin meyasa tayimai haka karfa ya fasa don kuwa tana sonshi,

Fahad harya gama hidimarsa ya kwanta kusan 10pm yaji de baze iya bacci ba ya tashi yasaka doguwar riga ya dauki key ya fita,

Be zame ba se kofar gidansu faseelat ya mata text "ina kofar gida"

har bacci yafara daukarta tatashi ta saka hijab akan kayan baccin jikinta riga da wando ta dauki ATM dinshi ta fita,

Tana fita ta ganshi cikin motor yanata tunani ta nufi motar tabude ta shiga ta zauna tai shiru taki kallonshi,

Tana zama ya meda hankali kanta fuskar ba murmushin daya saba gani me sanyaya zuciya,

Ya lumshe ido ya bude yace"faseelat I'm sorry"

Ta dago ta kalleshi duk yayi wani iri ta meda idonta kasa tai shiru,

Yace"kiyi hakuri duk abinda na fada bahaka bane kishine kawai yasa na fadi hakan"

Ta dago ta kalleshi sai hawaye tana kallonshi tace"dama baka yadda dani ba ?har zakai wani mummunan tunani akaina?"

Yace"kiyi shiru kidena maganar plss"

Tai shiru ta juyar da kai tana share hawaye ,

Yace"I'm regretting fadamiki hakan kiyi hakuri but ni na yadda dake "

Ta kalleshi tace"ka yadda dani wlh ko hannuna bawanda ya taba rikewa"

Ranshi na zafi yace"nasani kiyi hakuri "

Tanata sharban hawaye ta share ta kalleshi tai murmushi tace"shikenan yawuce"

Yayi karamin murmushi yace"thank u"

Ta sake mai murmushi ta sunkuyar da kai,

Ya sauke ajiyar zuciya yace"nakasa samun natsuwa bare bacci har seda nazo gareki"

Tace"nagode"

Ta mika mai ATM dinshi,

Yace"no kibarshi kugama hidimarku"

Tace "aa ko tabashi ma banyi ba kudin da kabani sun isa "

Yace"aa kinde kara kudi zakice"

Tai murmushi tace"eh "

Yace"OK ya mika hannu tabashi se sannan ya lura da kunshinta yayi mata kyau sosai yana murmushi yace"kinyi kyau sosai "

Tai murmushi ,

Yace"gobe akwai dinner din karfe8"

Ta daga kai ,

yace"plss ki kara hakuri koda kinga wani abu cos dinner hada aysha"

Jin yace aysha tagane kishiyarta kenan ranta ya baci jin yadda ayshan yayi dadi a bakinshi ta daure tace"insha Allah my heart desire"

Yayi murmushi yace"kullum sena samu new suna"

Tace"kai dinne na musamman "

Yace"godiya nake"

Sukai shiru na minti biyar sannan yace"kije gida seda safe"

Tace"seda safe" har tabude zata fita yaga sarkarta yace"queen karnai mantuwa"

Ta juyo tana kallonshi ya dauko akwatin ya mika mata ta amsa tana murmushi tace"for me?"

Yayi murmushi yace"tsarabar Niger"

Jin Niger taji rabin jindadin kyautar ya tafi don ko sosai takejin tsanar yan Niger yanzu tai murmushi tace"nagode sosai Darling Allah yakara budi na alheri yabarmu tare"

Yayi murmushi yace"amin seda safe"suka rabu batare da ankara tado maganar mota ba

Tai masa murmushi ta fita ta shiga gida seda yaga ta shige sannan ya tada yakoma gida yanajin wasai duk damuwarshin tatafi yana komawa ya kwanta bacci,

Tun asuba motocin yan Niger suka dauki hanyar Nigeria kusan mota 3 saboda ba jirgi yayinda kuma yan daurin aure suke shirin bin jirgi saboda gobe daurin auren safe ne,

Daga cikin masu tafiya daurin auren harda daddy na faseelat kuma cikin yanuwanshi zasuyi wakilci,

Aysha cikin farin ciki take tana daki mutane kuwa nata kai kawo gidan mommy don hidimar yau data gobe,

Tunda safe faseelat ta kira fahad dinta tai masa good morning yau baze fita aiki ba saboda hidima sukeyi,

Bangaren gidan hjyar Khalil shima hidima ake tayi da gidan su jameela ,

Shi ko thermocool yau da misalin karfe 11am yakoma kofar gidansu mansura ,

Ta fito dolenta tai tsaye kanta kasa,

Thermocool nata faraa yace"hjy mansura karki damu da zuwana kauna ce tajawo hakan Nide ina rokon ki temaka kibani koda kankanin wuri ne a zuciyarki"

Ta dago ta kalleshi ya kureta da ido tai saurin meda kai kasa tace"alhaji ni ban dace da kaiba"

Yayi murmushi yace"aiko mansura nida ke mundace"

Tace"nifa ba fara bace bakace "

Ya kalleta yayi murmushi yace"to minene?"

Tace"kuma bleaching nakeyi"

Maganar tabashi dariya Yayi dariya yace"hjy mansura miyakawo maganar?"

Tace"saboda kasani niba fara bace"

Ya kalleta kallon koda tana bleaching tana da haskenta yace"aini ke nakeso mansura ba farinki ba "

Tai shiru yace"ki temaka"

Tace"senayi tunani"

Yace"a ganina nabaki isashshen time na tunani"

Tace"kabani lokaci yanzu ma"

Yace"to shikenan hjy mansura Allah yakaimu lokacin Nide bazan hakura ba zanta zuwa har Allah yasa nadace"

Aranta tace"cabbb ba rana"

Tace"se anjima "zata wuce

yace"zo hjy mansura"

Tadawo ta tsaya ,

Ya fiddo bandir din 1k yace"ki sayi kayan makeup "

Ta kalli kudin ta girgizakai tace "nagode"

Yace"Dan Allah ki amsa "

Ta girgizakai tace"nagode fa "ta shige gida,

Desame yaro zai wuce alhaji ya mika mai kudi yace ya kaimata ya shiga mota yayi tafiyarshi,

Yaron nashiga mama ta amshi kudin tanata murna tace" Allahu akbar mansura kinyi goshi wannan abun arziki haka"

Itako mansura tana can ta kunkume daki tana tunanin mafita don da duk alamu a sannu zai siye iyayennata ita kuma bata sonshi ,

Da rana yan Niger suka iso mommy murna aysha murna suka tarbesu aka kawo masu kayan makulashe suka gama ci suka tafi yiwa aysha jeren kayanta da aka siye anan Nigeria ,

Suna zuwa suka ga katon gidane me kyau sosai dama basu hau sama ba saboda sunsan ayshar bata lpy kasa ne yakamaceta amma wasu seda suka leka gulma suka samu royal chairs da bed na faseelat sukaita kallo ta glass suna kushe kayan,

A haka sukai jere wa aysha kaya masu kyau itama Royal ne hadaddu suka koma gidan mommy aka cigaba da hidima,

Fahad suna busy hidima dasu sabeer dasauran friends dinshi,

Yan daurin auren Niger tuni suntafi,

Shima Khalil da jameela suna busy domin yau suma suna da dinner Wanda bada son ran Umma zaaiyi ba ,


Har Maghreb sannan suka fara shirin dinner,

Me make up specialist faseelat ta kira tai mata 100k kwalliyar tanata sakin murmushi ta saka long gown dinta dark purple da white head yanata walkiya tasa white sarka da yan kunne da white purse and shoes sosai ta hadu kamar ba ita ba friends dinta ma duk they're wise sunci gayu sosai ankon blue net pitted gown da white head ,

Bangaren Amarya aysha ma tasha make up mommy ta biya me kwalliyar 150k taiwa amarya tayiwa su mommy da sis din aysha biyu,

Aysha nata danyin murmushi ta saka white gown da white head da dan net bayanshi ta dauki green and red flower sak tafito kamar turawa in zasuyi aure akaita daukarta pic,

Bakwai da wani abu suka fita ango fahad yasaka yadi black da babbar riga tasha golden aiki hula baka akasa aysha motarshi yanata kallonta ya danyi murmushi tayi wani mugun kyau kamar aljana,

Wasu sunyi Hall din dinner su kuwa gidansu faseelat suka nufa already wasu motocin friends na ango sun riga isowa , friend's suka kawo faseelat bakin motar tana shigowa suka hada ido da aysha ta gumtse face itama ayshar ta gumtse tata ta kauda kai,

Shi ko yanata kallonta sosai tayi masa kyau kamar ya kama hannun ta,

Ta shigo aka kulle kofar sun saka shi tsakiya ,

Motar tai tsitt su kadai se driver gaba yana driving,

Da aysha da faseelat kowa ya shaka kishi a zuciya musamman faseelat da bata taba ganin aysha ba se yau tsoki kawai takeyi wai ashema yar yarinya ce sosai zatai sharing miji daita mtswww,

Itama aysha na magana da heart dinta ta na cewa "ji barta katuwa daita amma ahaka yakesonta mtswww"

Shi ko yana tsakiya ya rasa me zaice ,

Abokinshi dake driving dariya se cinshi takeyi ya kunna waka ya cigaba da tafiya

Suna isa kowace friends dinta da yanuwa suka taho su ukku suna gaba su kuma a baya suka shiga hall din dake makil da jamaa daga ciki harda mommy da friends dinta se daukarsu pics akeyi sukaje suka zauna yana tsakiya,

Duk cikinsu faseelat ce me faraar itama duk ganin aysha ya bata mata rai amma dukda haka ta na dan murmusawa abinta,

Aka bude taro da addua akafara abinda ya tara mutanen,

Abinci da lemuka nata kai kawo,

Aka kira kawar aysha tazo tabada tarihinta zainab da tazo da sabeer ita tabada na faseelat sannan aka kira amaren su cashe dukkansu sukai tsaye kowa yafito yana musu liki a wurin likin abun yazama gasa tsakanin freinds da yanuwan aysha mommy ko duk aysha taiwa liki se daidaya taiwa fahad da faseelat har kidan yatsaya suka koma suka zauna aka kira uwar ango da friends dinta,

Su mommy ansha head milk color da orange din lace me shegen tsada suka fito suka dan rausaya tanata farinciki ,

Aka kira friends na ango da Amarya sannan aka kira amaren yanka cake,

Sukazo suka tsaya bakin cake mc na fadin yadda zaai fahad yadora hannu faseelat ta dora aysha ta dora kannata suka yanka akadau tafi da wakar love me sanyi tanata playing,

Fahad ya Ciro yakai bakin Faseelat ta bude ta dan diba tana murmushi,

Ran aysha adan bace mommy ma tanajin haushin fara ba faseelat ya deba yakai bakin aysha ta bude ta dan iba sannan faseelat tabashi aysha ma tabashi anata tafi suka koma suka zauna akafara shigo da masu rawa sunayi ana kallo haka de har 10 sannan aka gama mommy takama hannun aysha ta fita daita,

Faseelat ta kalli momyn ta dauke ido tanajin haushin ta sosai,

mota daya suka shiga da fahad zasu koma gida,

Suna cikin tafiya taji yace"queen tnx u"kasa_kasa,

Ta kalleshi tai murmushi tai shiru,

Ya mata murmushi shima har suka isa suna isa friends dinta suka budemata suka nufi cikin gida,

Fahad yabita da kallo abokinshi na driving yana dariya yace"Allah seka dage Wadannan matan daka Tara "

Fahad ya mishi banza,

Abokinshi hafeez na driving yace"seka kula da kanka sosai in kanaso se mubaka sirrin"

Fahad yayi murmushi yace"bana bukata"

Wurin friends dinshi yakoma sukaita labari anata dariya se 12 saura wasu friend dinshi suka tafi su kwana part dinshi wasu kuma suka kama hotel,

Yan daurin auren Niger tuni suka isa aka tarbesu hannu biyu ,

Da darennan faseelat aysha fahad bawanda yayi bacci su duk kishi ya hanasu kowace tana tunanin kwalliyar yaruwarta dagani de duk kishin tsiya ne dasu,

Shi ko tunanin nauyin daze rataya kanshine ya hanashi bacci yana ta rokon Allah yabashi ikon adalci tsakani,

Tunda safe aketa shiri tunkan takwas aysha hartayi wanka tayi dress na material milk da black ba ita ba har yan bikin duk sunci gayu,

Su mommy ma anata hidima ai can ai nan

Gidansu faseelat ma hidima kawai sukeyi anata kai kawo ,

Karfe 11am dot aka daura auren fahad dawood da aysha Yusuf akan sadaki 2millions daurin auren da ya samu halartar manyan mutane attajirai,sarakuna,harma da gomnoni da ministoci,

Ana dorawa wasu friends nashi suka fara kira suna ango _ango ba bata lokaci kuma suka hawo hanyar Nigeria,


Aysha najin an daura dadi ya mamayeta shikenan de tazama Matar fahad har farin cikinta yaki boyuwa,

Karfe 2 aka daura auren Khalil da jameela akan sadaki dubu100 shima daurin auren ya samu halartar dumbin mutane,


Tun 2 su fahad suke ko far gidan kawu da aka kawata da rumfuna da shimfidu yana cike da mutane yanata dan murmusawa yasha farar shadda da babbar riga,

Karfe 2:30 aka daura auren shi da faseelat akan sadaki million daya

Jin an daura yakara fadada fuskarshi akaita masa murna ana pic akai de reception sannan kowa ya tafi,

Faseelat na jin an daura taita murna itama ,

Jameela ma ita da Khalil murna ba magana,

Tana gidan yan uwan mamansu a can suke setting Mimi ta bata wasu kwayoyi duk ta hadiye suka cigaba da shirin evening party da zasuyi,

Gidansu faseelat da marece Malama HASANA dan LARABAWA 😅aka kira tazo tai waazi me shiga rai da sanyaya gabobi,

Gidansu mommy kuwa wani walima ta hadawa friends dinta akaci akasha DJ ya kunna suka cigaba da casu a can Niger ma dangin aysha casu kawai sukeyi irinnasu,

Bayan angama waazi abokan faseelat suka fara nasu waazin wata tace "kinga wlh karki saki kibata fuska kokadan ki daure mata karda ta samu ko fuskar yi miki magana kuma wlh waccen yar tsigudidin da kkgani seta fiki iya kissa yan Niger? hmmm!!! sekin tashi tsaye kinyi dagaske sannan zaki kai labari ki dage da kula da jikinki abinci medadi tsafta biyayya ma mahaifanshi da yan uwanshi"

Rabia tai saurin katseta "ke yi shiru wannan uwar tashi har wata biyayya zaai mata bakiga yadda take ta nan_nan da amaryar ba?"

Faseelat tai dariya"ihinn!! fada mata de besty aini wlh sede na kalleta kawai amma bawata biyayya niko shiga harkarta ma bazan ba tunda kiyayyarta a fili take ita kuma waccan shegiyar aljanar zanyi maganinta sena ta gayyara rayuwarta yadda fitowa ma falon gidan se ya gagareta"

Suka kwashe da dariya suka tafa tace"Allah ko ke kinga yadda take jefamin wani kallo kamar nai kama da gyatumar ta tacan "

Suka kara kashewa,

Wata tace"faseelat yau se gidan miji yau zaa angwance to Nide ga gudummuwata ready made asha ashiga aiki kisha yanzu kafin time kin jike shakaffff ya shiga ya gigice"

Faseelat na murna tace"yawwa yar gari bani kiga ni koda ba kome ai ana shakaff din an hakura fa anyi dauriya aida bahaka ba"ta kafa kai a wani karamin galan,

Tana sha wata friend dinta na can baya tace"himm immm aure ba yanzu ba se munkara shakatawa"

Duk suka kalleta sukai dariya suka ce "Allah yashiryaki"

Tana taunar cingum tace"amin aure yanzu ina dalili"

Faseelat tashiga wanka ta fito tai salla aka tsaya tsara mata wata make up din,

Aysha ta sake wanka tasa material lace riga da sket sun mata dede red color da white cikinshi akai mata make up yan uwanta suka fara mata nasiha "aysha zaman aure duk hakuri ne kiyi hakuri da rayuwar da zakiyi yanzu ki rike mommy sosai duk wani matsalanki kifada mata insha Allah zatai miki maganinta ki kula da mijinki sosai ki kula da gyara jikinki da tsafta ki kuma kauda kai daga kishiyarki kinga de ta girmeki ba tsararki bace karki yadda kurikayin kishin fada aa kirikayin abun cikin kissa da wayau yadda wani time shi kanshi koda anyi gabanshi baze gane ba,karki sake kibiye mata aysha don tafi karfinki ki rike ibada da adduoi kisani addua itace makaminki duk dubararki ba ita bace duk bukatarki kafin kifadawa kowa ki fadawa Allah shine zai biya miki ,ki dena yadda kina ganin abinda zai bata miki rai kinsan baki lpy ki kula da addua kuma idan kina neman shawara in bazaki iya fadawa mommy ba ki kira cikinmu kinemi shawarar duk abinda ya shigemiki duhu"

Aysha ta daga kai idanunta cike da hawaye suka yafa mata white veil suka kaiwa mommy ita,

Mommy ta dora da nata akan tabi mijinta tai masa duk abinda zaisashi farinciki inde be sabawa sharia ba,

Sannan aka dauketa aka kaita gidan fahad acan sukai ishai,


Bayan ishain aka dauki faseelat bayan tasha nata nasihohin aka kaita,

Bangaren jameela ma tasha nasiha da fada wurin Umma dole ta rika kuka sosai ,dukda umma bata jin dadinta amma da da uwa seda tai kukan rabuwa daita aka dauketa aka kaiwa Khalil ita cikin tangamemen gidanta,


Bayan an kai su faseelat karfe tara kowa ya watse,

Su fahad na zaune cikin harabar gidansu sabeer da abokanshi sukace"ango muje muraka ka kashige ko"

Yace" na hutar daku ni kadai zan shige "wayarshi datai kara yasashi tashi yakoma gefe ganin faseelat ce ,

Tagaji da jira tace" kana ina?"don duk jinta take somehow

Yace"ganinan zuwa heartbeat "

Tai murmushi tace"seka dawo"

Yakashe kiran yana murmushi,

Suko abokansa yana tashi hafeez ya kalli sabeer ya fiddo power man yace"inason nabashi gudumuwa yasha ina tsoron ya gwalesheni kasan mutuminnaka "

Sabeer yace"kuran baze sha ba "ya kalli cup din kunun aya da fahad ya zuba yanasha ya tashi,

Yacewa hafeez" zubamishi anan"

Hafeez ya balli 2 ya jefa ya girgiza ya ajiye,

Fahad na dawowa ko zaunawa beba ya duka ya dauki cup din ya karasa shanyewa don yunwa yakeji ko abincin kirki beci ba ya ajiye cup din ya kallesu sunata kallonshi suna dariya yace"kude kukasani seda safe"

Suka ce"seda safe "suna dariyar shakiyanci,

Fahad na fita ya nufi gidan mommy har bedroom ,

Yana kasa tana zaune saman bed cikin Jan hankali da nasiha tace" dana kullim ina cikin yabonka kullum ina godewa Allah daya bani kai ina alfahari da kai dan Allah karkabani kunya kayi iya kokarinka karike amanar da Allah yabaka matanka suna da hakki akanka ka kula da hakkokinsu kayi musu adalci kada ka fifita wata akan wata domin kasamu rabauta nasani ba daya suke ba amma kadaure ka kokarta"

Kanshi duke yana jinta duk jinshi yake yana samun erection ya rasa meyasa,

Tace"son nabaka amanar aysha ka kulamin daita sosai ka guji bacin ranta karika yawan dubata saboda lalurarta kuma insha Allah tunda yanzu anyi biki hankali ya kwanta zan fara neman magani"

Yace"insha Allah mommy nagode sosai "

Tai murmushi tace"Allah yabaku zaman lpy da zuria dayyiba "

Yace"ameen"

Yayi zaune ,

Tace"tashi kaje dare nayi "

Ya tashi a kunya ce yanajin kunyar kanshi saboda erect dayayi hannunshi kan joystick dinshi yabar gidan,


Dukda yadda yakeji seda ya tsaya ya siye kaji da drinks wa amaren shi sannan ya nufi gidan nashi yanata dorawa desire dayakeji alamar tambaya,

Yana isa





*Ta faru ta kare aurenku an daura fahad dawood dashi da faseelat soyayya kuyi zaman ku lpy kuba maradda kunya🎶*


*Hadin da Allah yayi mutum be isa ya ware ba aysha ga dan mommy nan yau kun hadu akan kauna🎵*
[12/14, 4:51 PM] SHALELE: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



3⃣5⃣



*Specifically for u exceptional twins Hassan and Husain 80k*




*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A W)yace Wanda yace A'UZU BIKALIMATILLAHI TAMMAT MIN SHARRI MA KALAK da safe da yamma ba abin cutarwa da zai samesa ,wanda kuma yafada sau ukku zaa wakilta malaiku dubu sabain suna masa salati idan ya mutu kuma ya mutu shahidi*




Yana isa yayi horn megadi ya bude masa ya shiga da motar cikin gidan,

Yanayin parking ba bata lokaci ya fito ya dauki ledoji ya rufe motar ya nufi cikin gidan,

Ya bude yashiga tsit main falon se kamshi dake tashi ya ajiye ledojin hannunshi kan center table ya nufi sama dakin faseelat,

Yana ta dokin ganinta ya tura kofar ya shiga ya sauke ido akanta tana kwance,

Yayi tsaye yana bin jikinta da kallo tayi mugun kyau kayan sunyi fitting dinta kamar yaje ya afka mata,

Kamshin shi da taji yasa ta tashi zaune ta kalleshi ta sakarmai murmushi tace"sannu da zuwa"

Yayi murmushi ya karasa wurinta yanata mata mayen kallo yace"yawwa Queen ya gajiya?"

Ta yamutsa face a shagwabe tace "wlh nagaji sosai shiyasa na kwanta har bacci yafara daukata fa"

Yayi karamin murmushi yanata daurewa yace"sorry yanzu kitashi mu sauka kasa inaso na gabatar daku ga juna"

Tai murmushi tace "to dear"

Ya tashi ta mika mai hannu ya kamata ta sauko a gadon hannunshi zagaye a kugunta

Please Login or Register in order to submit comment