Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka kirani da sunana zaifimin dadi"

Yayi murmushi ya bude baki zaiyi mgna se kuma ya fasa,

Tace"nasan kana bukatar lokaci kayi tunani amma kasani dani da kai duk dayane bana kallon arzikin ka inasonka ne tsakani da Allah inafatan zaka amince"

Yayi murmushi yayi shiru,

Tai murmushi itama tace"kanata murmushi haydar amma kaki cewa komi ina sonka sosai ina fatan kasancewa matarka"

Ya sakeyin murmushi yace "hjy ai duk namijin daya ganki bazaiki sonki ba sede ina ganin kamar baki dace dani ba"

Tace"ai Aliyu nida kai na dace mun matukar da cewa da juna"

Yayi murmushi yace "to nagode zan tafi"

Tace"to ina jiran dawowarka ko samun sakonka zanyi farinciki sosai"

Baiyi mgna ba ya tashi tsaye ta mike tsaye itama sunata kallon kallo ya fita daga gidan ,

Tai murmushi ta koma gida tana tunanin kyawunshi fatanta kar yaki amincewa daita tana jawara wacce tayi aure har biyu ,

Aliyu ya tafi shago yana farinciki kuma yana tunani yanata tuno kyawunta da kudi da komi amma ta sameshi da zancen aure wane irin so take mishi haka?Yana bukatar lokacin tunani amma ba na amincewa da soyayyarta ba cos ya dade yanasonta lokaci de na karayin shawara da bincike akanta before ya amince daita,

Tunaninta ya hanashi sukuni ya koma very silent yanata tunani da marece abokinshi usman ya leko shagon ya sameshi suka gaisa suka zauna suna dan labari,

Usman yana kallonshi yace"yau azuminne ke gasaka haka?"

Aliyu yayi murmushi yace "soyayyace ke gasa ni "

Usman yayi dariya yace"haba?im so happy tuntuni kayi aure kaki ya kamata kamanta baya"

Aliyu yace"matsalar tana da kudi and ni kuma bandashi kana ganin ba matsala?"

Usman yace"tomiye ?arziki da dukiya duk na Allah ne kaima in yaso seya baka kuma abun akwai burgewa yadda ta amince da kai duk da tafi ka"

Aliyu yayi murmushi da zai iya daya fadamai ita ta fara furtamai Kalmar so,

Usman yace"wacece ita ?"

Aliyu yace"mu fita na nuna maka gidansu "suka fito waje suna labarin ya nuna masa gidansu Sega faseelat ta fito da mota zata fita ta fito ta rufe gate ta dauki hanya,

Usman ya jinjina kai yace" itace mijinta ya rasu watannin baya mijinta me kudi ne sosai gaskiya kundace da juna kuma inaga dama babbar macece dede kai saboda lalurarka na kwana ana duty dole se babbar mace"

Aliyu ya harareshi gabanshi na faduwa yace"shiyasa nake jin tsoron kar wani abu ya sameta"

Usman yace"haba ai duk tafi matanka girma da kwari idan akayi saa taku tazo daya shikenan se kaita dibar kayanka"ya karasa yana dariya,

Aliyu yayi tsoki yace"se anjima"ya juya shago,

Usman ya shiga motarshi ya nufi gida yanata sakin murmushi he's happy finally abokinshi zaiyi aure ,

Aliyu ya fara bincikar halin faseelat amma yakasa gano aibunta duk da haka yakasa kiranta ya kuma kasa dena tunaninta,

Bayan kwana biyu faseelat bata kira Aliyu ba har kwana biyun sannan ta kirashi tunda safe,

Ya dauka tai saurin cewa "ina kwana ?"

Yace"kintashi lpy?"

Tace"lpy lau "tai shiru tana murmushi,

Shima yayi shirun,

A hankali tace" Aliyu naji shiru bakace komi ba"

Yace"faseelat tuntuni na ke jin inasonki amma "

Tace"amma me? Aliyu kafadamin kana sona karmu yaudari zuciyoyinmu plsss bawani abu inde kana sona"

Yayi murmushi yace "inason kira amma nakasa kira "

Tai murmushi tace "shikenan nima zandena kira se idan ka kira"

Yayi murmushi yace "ina iya zuwa mugaisa?"

Tai dariya tace"a,a bazaka iya ba"

Yayi yar dariya cikin sanyin murya yace"zan shigo idan anjima "

Tace "to nagode sosai habibina Allah yabarmu tare yakara mana son juna"

Ya danyi shiru kamar bazaice amin ba yakasa hakurin barin amin da yayi tundazun a heart dinshi yace"ameen "

Tai murmushin jindadi tace"sai kazo"takashe kiran,

Aliyu ya dauke wayar a kunne yana jin matukar kaunarta yadda ta fito ta furtamai so shi namiji yakasa ya matukar karamata wuri a heart dinshi,

Memakon ya nufi gidansu seya koma gida ya sake wanka cikin dark blue shadda anyi mata black aiki dinkin ya masa kyau ya saka black and blue hula ya fito zai fita gidan yanata murmushi,

Mama na tsaye tsakar gida tana kallonshi ta tsaidashi tace"ina zakaje ne haka Aliyu naga harka fita aiki ka dawo? "

Yayi murmushi yace "amm daurin aure zamuje"

Ta kure fuskarshi da kallo ta dade bata ganshi cikin walwala haka ba,

Tai murmushi tace "to Allah yabada saa"

Yace"ameen "ya juya ya fita ya kama hanyar gidansu faseelat,

Yana zuwa ya kirata tabashi izinin shiga ya shiga yasamu seat ya zauna yana kagare ya sata a idonshi,

Faseelat ta fito tana tafiya sannu tana sanye da doguwar riga milk da kwalliyar golden jiki ta yafa mayafi milk ,

Tunda ta fito yaketa kallonta sam bazai iya dauke idonshi akanta ba,

Harta karaso tana sakin murmushi tace" sannu da zuwa "

Yace"barka da fitowa"

Ta zauna kan seat ta kalleshi yanata kallonta suka saki murmushi lokaci daya ta sunkuyar da kai.....
[2/12, 5:31 PM] Maman Mamy: 87



Ta dago ta kalleshi tana sakin kayataccen murmushi tace"naji dadin zuwan ka"

Yayi murmushi ya lumshe ido ya bude yace"nafi ki jindadi"

Tace"dagaske?"

Ya sanya lips din kasa acikin baki ya jinjina kai da murmushi fuskarshi,

Tai murmushi a hankali ya bace cikin sanyin murya tace"Aliyu dama kana sona bakafadamin ba? "

Yayi shiru,

Tace"yanzu idan da ban fadamaka inasonka ba bazaka fadamin ba?"

Ya karayin shiru still,

Ta cije lips tace"I'm not happy gaskiya haydar "

Yayi Karamin murmushi yace"I'm sorry"

Tai murmushi me hade da wani kallo sannan tace"matan ka nawa?"

Yayi murmushi lokaci daya kuma fuskarshi ta sauya tuno sakeena data bar duniya ta dalilin shi,

Ranshi na zafi yace"banda aure yanzu amma before nayi aure mun rabu da matata ta farko dayar kuma ta rasu"

Tana kallon fuskarshi da ta sauya, da tausayi tace "Allah ya jikanta ya mata rahma"

Yace"ameen"ya shiga duniyar tunanin rayuwarshi da sakeena ,

A hankali tace"nima nayi aure biyu mijina na karshe Allah ya masa rasuwa"

Ya kalleta yace"Allah ya jikanshi"

Tace"ameen "

Yace"thanks"

Sukai shiru kanta kasa a hankali tace"watarana zamu tarar dasu inda suke"

Yayi murmushi me sauti yace "ba yanzu ba amma"

Tai dariya tace"yes se bayan munyi aure mun samu zuria masu yimana addua"

Yayi murmushi yayi shiru yana tunanin problem nashi,

Suna haka ya omer ya shigo ya kallesu sau daya batare da magana ba ya wuce ciki,

Aliyu ya kalleshi ko kadan baiji dadin samunsu da yayi ba,

Faseelat sau daya ta kalli ya omer din itama yana wucewa Aliyu yace "zan koma shago"

Tace"tun yanzu?bamu gama gaisawa ba"

Yace"zan dawo wani lokaci"

Tai murmushi ,

Ya mike tsaye,

ta tashi tsaye itama tace"Allah ya kiyaye"

Yayi murmushi yace "ameen" ya juya ya nufi kofar fita,

Faseelat na tsaye tana bin bayanshi da kallo harya fita gidan ta saki murmushi ta nufi cikin gida,

Ya omer kuwa yana shiga yasamu Ummi ya zauna kusa daita ranshi badadi yace"Ummi waye da faseelat waje?"

Ummi tace"nade ga ta fita amma bansan ina taje ba"

In cool yace"ummi karde faseelat ta dawo da kawo samari kofar gida kamar can baya"

Ummi tace"da wuya tayi hakan"

Suna cikin magana ta shigo tana murmushi tace"yaya ina kwana?"

Bai amsa ba yace"zauna"yana mata wani kallo,

Ta zauna kan seat tana kallonshi ,

Yace"ke da waye nagan ku?"

Tai karamin murmushi tace "yaya sunan shi aliyu shagon shi na gaba kadan anan unguwar yake seda kifi aure nakeso nayi yaya" ta karashe murya sanyaye,

Ya omer ya tsaya kallonta jin ta ambaci me seda kifi se yaga kamar ba kanwarshi daya sani ba faseelat,

Ummi tace "da kin kyauta ko bai da wani amfani zama hakanan Allah ya tabbatar da alheri"

Faseelat ta kalli ya omer taga ita yake ta kallo ta sake sunkuyar da kai tana jiran me zai ce taji baice komiba,

Ta tashi ta wuce dakinta jikin ta sanyaye,

Tana tafiya ya kalli Ummi jikinshi sanyaye yace"zan fadawa kawu kuma zan fara bincike kanshi "

Ummi tace "ya kamata"

Aliyu ko shago ya koma yanata tunani ji yake idan be fadawa faseelat lalurarsa ba bai kyauta mata ba amma tayaya zai fara tunkararta da lalurar? Ya dade yana nazari zuciyarshi tabashi iyayenta zasuyi bincike kanshi before auren,
zuciyarshi tai mummunan faduwa ya cire hula ya ajiye kan table yayi tagumi da duka hannuwansa biyu ,

Da marece

Roshni ce kwance kan bed bata da lpy amma ba sosai dinnan ba takeyin ta ,

Tana kwancen idanunta lumshe jamil ya shigo dakin yana mata kallon tausayi ya hau gadon ya jawota jikinshi ya taba jikin yaji shi da zafi in cool yace"baby kitashi mutafi asibity"

Ta bude idanunta dake lumshe ta kalleshi can ciki tace"banason zuwa asibity ka samomin maganin fever kawai"

Yanajin tausayinta yace"sau nawa kikasha baiyi amfani ba?ki daure mutafi hospital "

Ta turo baki tace"ni ka kyaleni kawai in bazaka sauya maganin ba"

Yayi karamin murmushi ya dora hannuwa kan shafaffen cikinta yana shafawa yace"ko dai unborn ke wahalar min da ke?"

Ta tabe baki cos tasan bata da komi cikinta tuni take using implant kuma tayi mens dinta na wannan watan,

Yace"uhummm?"yana lalubar cikin,

Tace"bani da komi ni"

Yana mata wani kallo yace"rasheeda bakison haihuwa ne?"

Ta turo baki tace "ba yanzu ba"

Ya tsaya da abinda yake yace"sai yaushe? Roshni kinsan yadda nakeson yara kuwa? Ni banki ki haifo hudu time daya ba kiyi kokari plsss"

Tace"jamil ni zanbawa kaina haihuwar? Idan tazo ai yinta zanyi kuma miye na damuwa tunda ko yanzu ai kana da diyar ka"

Ranshi ya sosu yace"wai mi kike nufi ne rasheeda? Sometimes seki rika magana marar kan gado"

Tace"sarai ka fahimceni ko yarinyar hannun abida ba taka bace ? "

A tsawace yace"shut up wace maganar banza kike haka?"

Tace"gaskiya de na ke fada ni ba makauniya bace gatanan kamanninta duk naka kuma ai ba blood relation kuka hada ba"

A zafafe yace"to diyata ce seme?"

Tace"seka dena matsamin da zancen haihuwa tunda kana da diyar cikinka"

Yaja tsoki ya tureta ya sauka a gadon ya fita daga dakin,

Tai tsoki ta gyara kwanciya tana cewa"dan rainin wayo zakazo kana min surutan haihuwa_haihuwa to ban iyawa ni"

Sosai kalamanta suka mai zafi ya koma falo yayi zaune yana tunani yaakai tasan suhailat yar shi ce?idan ta kamanni ne kenan bayan ita akwai wadanda suka lura da hakan ?ya yamutsa fuska saboda yadda zuciyarsa ta kara zafi ya tashi ya fita a gidan ya koma gidan abida,

Yana zuwa yayi kwance kan seat ya rufe fuskarsa da hannu daya duk da ba bacci yake ba,

Ya dade Hjy abida ta fito daga bedroom ta ganshi kwance ta nufeshi ta zauna gefenshi ta dora hannu daya kan cinyarshi a hankali tace"daddyn suhailat meke damunka?"

Ya dan cire hannu ya kalleta yace "bakomai ban jindadi ne"

Ta dan dora hannu kan wuyanshi da zafi kadan tace"bari na kawo maka magani"

Yayi shiru ta tashi ta dauko PCM da ruwa ta dawo dashi tace"katashi kasha "

Ya mike zaune yana yamutsa fuska ta dan kamashi sannan tasa mishi maganin baki ta dora mai ruwan yasha sannan ta dauke robar,

Yace"thank u"a sannu,

Tace"Allah yabaka lpy "ta tashi ta wuce kitchen ,

Jamil kuwa ya cigaba da tunanin maganganun roshni fatanshi bawanda ya fahimci suhailat yarshi ce se yanzu ya fahimci kamanninshi data biyo matsalane,

Da dare

Faseelat na kwance kan bed yayin da Aliyu ma ke kan nashi gadon suna fira,

Fira sukeyi medadi irin ta masoya ,a hankali ya kira sunanta " Hjy "

Tai dariya tace"Allah idan kana cemin hjy bazan rika amsawa ba"

Yayi murmushi yace"na riga na saba da hakan"

Tace"yanzu sekayi kokari ka saba da wani sunan"

Ya sake yin murmushi yace"wane suna kikeso?"

Tace"kowane amma banda hjy "

Yace"ranki ya dade yayi?"yana boye dariyarshi,

Da shagwaba tace"ummmm!!! Ni banason shi"

Yayi dariya yace"to tell me wane kikeso?"

Tace"heartbeat"

Yayi murmushi yace "u're right kece zuciyar gabadaya"

Tace"happy"tana murna,

Yayi murmushi sukayi shiru,

A hankali tace "zakazo gobe?"

Yace"no banajin dadin zuwa haka kawai dazun banji dadin yadda yayanki yazo ya same mu ba"

Tai dariya tace "why?"

Yace"saboda basu San dani ba ,basu san wanene ni ba gashi ana kawoni har cikin gida"

Tai murmushi tai shiru,

Yace"ya kamata in fara turo iyayena ayi maganar aure sannan in cigaba da zuwa tunda mun fahimci juna"

Tai shiru batace komi ba saboda a kagare take tayi auren itama,

Ya cigaba da cewa"inaso kiyiwa su yaya magana subani lokaci in turo iyayena"

Tace"to shikenan zanfadamashi amma plss karinga zuwa kafin time din kaji haydar ?"

Yayi murmushi sosai yake jindadin haydar din da take kiranshi wani sanyi ke ratsashi duk time data fada,

Tuno matsalarshi again yasa ya tsaya da murmushin bazaiyiwu fadamata ba amma gwara tasani tun wuri kafin ya kara nisa a sonta yadda zaiji saukin rabuwa daita ba irin yadda ya rabu da sameera ba ,

Cikin sanyin murya yace"heartbeat ina da problem inafatan bazaki gujeni ba"

A hankali tace"problem?nan kusa bana tunani akwai abinda zai rabamu inasonka sosai "

Yace"nagode sosai nima nake sonki shiyasa bana son kyafta ido idan na ganki"

Tai murmushi cikin kunya tace "inason kallon nan sosai "

Yayi murmushi ya girgizakai yace"zaki ta samun shi"

Cikin sanyin murya tace"seda safe"

Yace"Allah yakaimu kiyi bacci lpy "

Ta kashe kiran tana murmushi tana jindadin fira dashi sosai ,ta cigaba da tunani se soyayyarsu da fahad ta fado mata a rai irin yadda yakeyi yana tuno mata shi ,duk farin cikinta ya gushe tana tuno sanyin jiki na fahad taushin zance kamshin jikinsa kyau da komai da irin yadda ya nuna mata soyayya,

Idanunta suka cika da hawaye tana tuno time da take matsa mai ya saketa yana zukunnawa gabanta begging for her forgiveness amma bataji saboda soyayyar alhaji now alhaji ya tafi mommy kuma ta hana su cika burinsu ,

Hawaye masu zafi suka zubomata tace"why mommy?why ?mena miki ?"

Ta cigaba da zubda hawaye har bacci ya dauketa,

Wanshekare tun asuba Aliyu ya shiga gaida mamanshi ,

Bayan sun gaisa kanshi kasa yace"mama akwai wata da muka fahimci juna inason in iyayenta sun bada izini su kawu su nemomin aurenta"

Mama na Jan casbi tace"naji dadi sosai Aliyu kullum addua ta Allah yabaka mace ta gari da zata mantar da kai matanka ta kuma iya da bukatunka naji dadi sosai wlh kuma insha Allah zan fadamishi kafin haka kaima seka sameshi kafadamai ya sunan diyar tawa?"

Ya sosa kunne yace "faseelat"

Mama tace"sunan medadi Allah ya tabbatar da alheri"

Yace ameen a zuci a fili yace"amma zawarace"

Mama tai murmushin manya tace"Aliyu inba jawara ba wace budurwa zata iya da kai? Dama kyanka babbar mace Allah de yabaka lpy "

Ya dan dago ya kalleta jin tace Allah yabashi lpy,

Ta cigaba da cewa "kullim azumi ai abun yazama lalura Allah yasa karshen abun kenan "

Yace"ameen"

Tace"kayi kokari kaje ka sameshi kafin ya fita"

Yace "to " ya tashi ya fita ya koma dakinshi yana shiri yana tunanin maganar mama wani irin tsoro ne cikin ranshi yana tsoron rasa faseelat maybe koina abinda zasu fada kanshi kenan tunda gashi mamanshi ma na fada,

Haka ya gama shirin gari na gama wayewa ya tafi wurin kawunshi sukayi maganar suna jiran abasu izini suje,

Faseelat ma bayan salla taje suka gaisa da Ummi cikin kunya tace"Ummi Aliyu ne keson abashi izini ya turo iyayen shi"

Ummi nata kallonta tace"kina de sonshi ko kuma kinji kingani? "

Faseelat ta daga kai tace"yana da kirki Ummi"

Ummi tace"ba kirkinshi nake tambaya ba kina sonshi na tambaya tunda kinji kingani shikenan banason a kuma memaita baya"

Faseelat tai shiru ,

Ummi tace"tashi kitafi"

Ta tashi ta tafi tana tunani saboda tace batason fahad ga auren alhaji haka sukaita tambayarta yanzu ma hakan setaji bata jindadi maybe da batayi hakan ba da bazasu cika mata tambayoyi haka ba,

Bayan ya omer yazo Ummi tafada mai yace"dama na fadawa kawu zan kara bincikawa sosai"

Tace"tom Allah yasa alheri"


Shiru har marece yayi Aliyu bai zoba faseelat ta kirashi tana kukan wasa,

Yana dauka yaji kukanta ya rikice ya mike tsaye yana in ina yace"lpy hjy meyasameki?"zuciyarshi na lugude,

Faseelat tace"ban lpy idan bakazo ba komai na iya faruwa"

Yace "sannu... sannu gani nan zuwa yanzu" hankali tashe ya kashe wayar ya fito a shagon dasauri ya nufi gidan ko minti biyar ba aiba yaisa yana zuwa ya kirata ta dauka ,

Yace"ina kofar gidan"

Tace"kashigo ciki"da shagwaba,

Hankalinshi duk ba kwance ba ya shigo ciki yayi tsaye zuciyarshi nata harbawa,

Se gata ta fito da zumbuleliyar hijab har kasa saboda kananun kaya dake jikinta tanata murmushi fuskarta tasha makeup yanata kallonta harta karaso,

Ya sauke ajiyar zuciya yace"idan kina haka watarana zuciyar tawa bugawa zatai"

Tayi murmushi tace "nima tawa zata buga idan bata ganka ba"

Ya gyara tsayuwa yace"to gani "

Ta bishi da kallo tun daga kasa yana cikin kananun kaya milk din jeans da orange din riga yayi kyau sosai ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "harna warke"

Yayi murmushi yace "to zan koma "

Ta dago ta marairaice tace"bamu gaisa ba"

Yayi murmushi yace "ina aiki kin dagamin hankali dole na taho kimun uzuri zan dawo anjima"

Tace"na maka Allah ya bada saa"

Yace"ameen sena dawo" ya juya ya tafi,

Da dare bayan ishai tana zaune kan carpet tagama salla tana zikiri text ya shigo wayar ta,

Ta dauki wayar ta duba taga message dinshi "ina kofar gida"

Ta cigaba da kallon wayar tana tuno alhaji baya gajiya wurin turamata sako hawaye suka zubomata inama zai dawo da bazata kula duk namiji ba seshi ya manyanta amma yanayin komi na yara yana bawa soyayya hakkinta sede wanda ya mutu baya dawowa ta share hawaye zuciyarta na bata shawara in taso zata iya sanya Aliyu ya rika mata abinda takeso in tafara tura mai sakonni shima zai rika kulawa yana turomata ,

Ta ajiye wayar ta fita har kofar gidan tana murmushi tace"sannu da zuwa"

Yace"ya jikin?"batare da ya amsa ba

Tace"ai tundazu na warke yanzu na karasa warwarewa"

Yayi murmushi ya mika mata ledar hannunshi,

Ta kalli ledar ta kalleshi,

Yayi murmushi yace "na kawowa patient dita"

Tai murmushi ta sake kallon ledar tana tuno wasu abubuwa tasa hannu ta amsa ta kalleshi tace"nagode sosai"

Yayi murmushi yace "se da safe"

Tana murmushi ta daga mai hannu,

Yayi murmushi ya hau mashin dinsa ya tafi,

Tana tsaye tabi mashin din da kallo bata manta time da motoci ke kai kawo kofar tsohon gidansu ba ta sakeyin murmushi ta koma cikin gida,

Tana shiga daki ta zauna ta bude ledar ganin kabab meat,burger da yoghurt da chocolate da sweet dasauransu ya daga mata hankali ba abinda ta tuno se alhajinta yana matukar kulawa da Wadannan tunda ya fahimci tana so zuciyarta na zafi ta rufe fuska da hannu biyu ta saki kuka ,

kuka take sosai na kewar mijinta tauraron zuciyarta tana cikin kuka taji karar shigowar sako a wayar ta, ta dakata da kukan time daya ta jawo wayar dasauri.




I'm sorry my fans that are in paid for all group hausawa suna cewa zo mu zauna zo mu saba cikin media banda group kamarku saboda akwai real fans dina da tun a hamdalat muke tare u know aski idan yazo gaban goshi yafi zafi se hakuri😉 I'm gentle and friendly bayan haka ma akwai ban dariya sede ni mutum ce ina da zuciya akwai responsibilities na mutane akaina amma duk yadda ake ciki senayi kokari na maku typing don kuji dadi ya kamata arika Sara ana duban bakin gatari,ina baku hakuri kuma dan Allah ku min bikon kawata ikra😹 charting din duk ya dena dadi da bata🥴 ,

thanks u all
[2/14, 3:11 PM] Maman Mamy: 88




Tana dubawa taga sakon Aliyune ta bude message din dake dauke da dan karamin rubutu sakon shine "nagode kwarai da yadda kike sona kike damuwa dani inasonki sosai"

Hawaye masu zafi suka zubomata batasan dalili ba ta bude kabab din ta dauko ta faraci tana sakin ajiyar zuciya, bai samu shiga sosai ba saboda yadda zuciyarta ke cunkushe da tunanin alhaji ta tashi ta shiga toilet tayo alwala ta dawo ta kabbara salla tanayi tana mai addua a sujud bayan ta dade tana salla bacci ya dauketa,

Tunda safe ta turamai text "barka da safiya masoyina ina fatan zaka wuni a cikin farinciki tare da tunani na "

Aliyu na kwance yaga sakon ya bude yayita kallonshi yana sakin murmushi,

Wanshekare da safe shima ya tura mata sakon daganan suka fara turawa juna sakonni ba rana ba dare,

Bayan 1 week ya omer da kawu sun gama binciko waye Aliyu yaya addininsa da mutunci da dangantaka halin rikon iyali da komi,kuma bawata matsala problem din shine kowa yana fada hariji ne matarshi daya ma seda tayi yoyon fitsari ta mutu dayar kuma tayi miscarriage iyayenta suka raba auren ya omer naso yawa Ummi maganar amma bazai iyaba kawu kuma bai dauki wannan matsala ba yadda ya gama gano matan nashi duk yara ne and idan baa ba irinsu aure saboda suna da bukata ya zasuyi da rayuwarsu?

Aliyu ya karawa faseelat magana akan turo iyayenshi,ya omer na zuwa tafadamai yace su turo ta koma daki tana farinciki ta kirashi ta fadamai yace zasu turo faseelat nata murna ta fadawa yaya yasamu kawunsu bayan two days iyayen Aliyu sukaje nema masa aurenta da kudin neman aure dubu arbain akasa ranar daurin auren nan da sati biyu kacal iyayen Aliyu nata godiya suka tafi,

Kawun Aliyu gidansu yawuce ya samu mama da maganar mama na murna tai ta godiya saboda kokarinshi akansu ,

Aliyu na jin labarin ya kira faseelat ta dauka tana kwance yace"yau is a special day ranar murna ce"

Faseelat tai murmushi azumi takeyi sosai yake bata wahala tace"saboda me?"

Yana farinciki yace"anyi fixing date din bikinmu nan da two weeks"

Faseelat tai wuff ta tashi zaune tana murna tace"alhamdulillah naji dadi sosai haydar"

Aliyu yayi murmushi yace"ina kara godiya for choosing me"

Tai murmushi tace "nima nagode"

Yace"sena zo anjima "

Tace"sai kazo bye"takashe kiran ta koma ta kwanta ta lumshe ido fatanta ta ganta dakin mijinta suna zaman lpy da nunawa juna kauna shine burinta kuma tana ganin yana daf da cika,

Tuno gyaran jikinta yasa ta tashi zaune dole ta gyara kanta don yajita daban da Matansa no din maman mujaheed me kayan mata yar sokoto da tai saving tuni ta latso awayarta bazata manta yadda kayan maman mujaheed suka karbeta ba cos kayanta akwai sauki da biyan bukata tai dialing no din,

Maman mujaheed ta dauka da muryarta ta sokkotawa tace"assalamu alaikum"

Faseelat tace "waalaikumussalam maman mujaheed ya gida? ya kasuwa?"

Maman mujaheed tace"lahiya lau kwana biyu"

Faseelat tai murmushi tace "ai mijina ya rasu amma kwanan nan zanyi wani aure shine nakeso ki gyarani sosai gyaran mayarda zawara budurwa inaso ya jini daban"

Maman mujaheed tai murmushi tace "Allah sarki Allah yajikanshi kuma karki samu damuwa"

Faseelat tace"yaushe zaki turomun kayan nawa ne zan biya?"

Maman mujaheed tace"20k saboda andade tare "

Faseelat tai murmushi tace "to nagode sosai kisake turomun AC no dinki plsss"

Maman mujaheed tace "to nima nagode sosai sena turo" takashe kiran,

Bayan maman mujaheed ta tura mata no din ta tura mata kudin maman mujaheed kuwa tana ganin kudin tafara hadamata kayan da zasu dace da ita,

Wanshekare ta turomata faseelat ta fara shan nasha tana matsi dana matsi don idan sunhadu tauraruwarta takara haskawa,

Ba jimawa mutane sukaji labarin auren Aliyu da faseelat wasu nason fadin matsalar Aliyu babu hali daga cikin neighbours na Aliyu wata mata tace itakam bazatai shiru ba ta shirya tazo gidansu faseelat Ummi ta tarbeta tana faraa ta kawomata ruwa ,

Matar babbar macece ta sha ruwan sannan tai murmushi tace "nasan baki sanni ba"

Ummi tace"eh gaskiya ban dauki fuska ba"

Matar ta sakeyin murmushi tace "unguwar mu daya da Aliyu Wanda yarki zata aura"

Ummi tace"Allah sarki"

Matar tace"ni macece yaruwarki be kamata inga zaku hada yarku da abun cutarwa inyi shiru ba dukda de bamusan juna ba"

Ummi tana ta kallonta tace"lpy ko?"

Matar tace"gaskiya Aliyu harijine abinda ke rabashi da matansa kenan don daya ma ta dalilin yoyon fitsari ta rasu shiyasa ya dau lokacin nan ba aure saboda tsoronshi Matan ma suke "

Ummi tace"ikon Allah "

Matar tace "dan Allah Ku tausayawa yarku tun kafin abunnan cikin matanshi akwai wacce kullum kwana take ihu har da miscarriage tayi"

Ummi tace "to nagode sosai insha Allah zan duba maganarki"

Matar tace " Allah ya kyauta yazaba mafi alheri se anjima"

Ummi tace "se anjima" tana zaune kan seat duk jikinta ya mutu,

Ba dadewa da fitar Matar faseelat ta shigo cikin gidan daga zabo kayan dakin da takeso harta biya kudin,

Ganin Ummi sukuku yasa taje ta zauna kusa daita cikin sanyin murya tace"Ummi lpy?"

Ummi tai shiru har ya omer ya shigo gidan ya shigo dakin yayi tsaye bakin kofa sukuwa basu lura dashi ba ,

Faseelat tace"Ummi dan Allah minene naga kamar baki lpy"

Ummi ta kalleta tanason diyarta sosai batason wani abu ya sameta bare mutuwa yanzu ,

Cikin sanyin jiki tace"anya faseelat bazaki hakura a fasa auren nan ba? banason wani abu ya sameki"

Gaban Faseelat ya fadi tace"dan Allah minene Ummi?wani abu akace Aliyu yayi?"

Ummi tace "to mutumin da bai lpy ai kinga akwai matsala auren shi"

Cikin zallar tashin hankali faseelat tace"meya sameshi Ummi?"

Ya omer yayi karamin murmushi don yasan ina maganar ta dosa,

Ummi tace "wata mata tazo ta fadamin harijine matanshi suna miscarriage harda me yoyon fitsari da mutuwa"

Faseelat na kallon Ummi ta juyar da kai tana gumtse dariya wai harijine matanshi na miscarriage ita ai tafi son harijin ma tana da buri akan sex mijin novel

Please Login or Register in order to submit comment