Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaita istigfaree da tasbihi Allah zai gafartamaka zunubanka ka kuma tabbatar da kayi tuba dawwamamme ,iyayenka kuma ka rika kyautata musu kana bin umarnin duk abinda suka saka ka kiyaye ibadarka da duk abinda akasaka Allah zai shigar da kai aljanna,sannan yana da kyau ka koma makaranta kana daukar karatu domin inganta rayuwarka hakan zaisa karika kusanci da ubangiji kana kara sanin yadda zaka bautamishi zaka kuma nisanci abinda bayaso kuma shi ilimi haskene yana temakawa sosai wurin kyawun rayuwa da muaamala da mutane yadda musulunci yace,

anan akwai dalibai da suke daukar darussa duk bayan sallar Maghreb da asuba inafatan zaka rika zuwa kana daukar darussa da zasu temaki rayuwarka da ta ma iyalanka,

Daga karshe in kasamu hali kayi aure ,aure yana katange mutum daga kallon wasu matan yana kara natsuwa yana kuma da tarin lada sosai akwai wani hadisi ma dake cewa sallar mai aure tafi ta wanda baidashi da lada sabain"

Marwan na kuka yace"nagode sosai Malam insha Allah zan dawo daukar karatu zan kiyaye duk wani sabo kuma iyayena sun yadda zasumin aure insha Allah nan kusa zanyi don gudun komawa rayuwar baya nagode sosai "

Liman yace"bakomai Allah ya kara nuna mana gaskiya yabamu ikon binta"

Marwan yace"ameen "ya tashi ya fita,

Aysha tagama yin brown rice da taji veggies da banana milk shake tai setting dining ta shiga tai wanka tana fitowa tai salla still fahad nata bacci sam bazata iya tada shi ba ta sake kaya tasa riga da sket na atamfa cikinta ya mugun fitowa ta fesa turare ta koma bakin bed tana ta kallonshi ,

Fahad nata bacci be farka ba se ana kiran sallar laasar ya bude idanunshi yana ganin biji_biji ya saukesu kan aysha dake zaune tanata kallonshi a hankali yafara gani normal ya rumtse ido ya tashi zaune,

Cikin sanyin murya tace"sannu Yaya"

Ya karasa tashi zaune ya kalli agogo yaga 3:50pm ya kalleta batare da cewa komi ba ya sauka yayo alwala yadawo yasa jallabiya yayi salla sukayi laasar tare sannan ya tashi ya koma kan bed ya sake kwanciya,

Ta tashi ta linke carpet taje gefenshi ta zauna tace" Yaya katashi kaci abinci kasha magani"

Ya bude ido ya dora su kanta yace"kede kinci ko?"

Ta girgizakai ,

Yayi saurin tashi zaune yace"meyasa ?plss kirika cin abinci "

Tai shiru ya sauko ya kama hannunta suka fita dining ,

Ya zauna tayi serving dinsu plate guda ta zauna ta debo ta kai bakinshi ya kalleta yayi murmushi ya amsa sannan ya dauki spoon yafara bata suka cigaba da feeding juna,

A hankali idanunshi suka kai wurin seat din faseelat ya kurawa seat din kallo yana tuno abubuwa da dama,

Aysha tame da kallo gun seat din ranta badadi ta cigaba da bashi abinci batare da tai masa magana ba,

Bayan drip din mommy yakare daddy ya ciremata tai salla yayo masu order suka fito dining ,

Ganin ba marwan ta wuce dakinshi ta sameshi yana cikin tunani taje ta zauna gefenshi cikin rarrashi tace"dana kayi hakuri yanzu kataso muje nabaka abinci kaji danlele na"

Ya kalleta yayi karamin murmushi ya tashi ta kama hannun shi suka fita daddy na zaune yaga fitowarsu haka yayi murmushi harya manta last ranar ,

Suka zauna mommy ta zuba abinci ta rika bashi a baki yana ci kanshi sunkuye kunya na dawainiya dashi beci da yawa ba yace ya koshi don da ba ita tabashi ba bazaici kamarsa ba sannan itama taci nata,

Duk wunin ranar fahad yana tare da aysha suna jinyar juna gab Maghreb Sega sabeer gidan fahad ya masa iso har ciki,

Aysha ta gaidashi tawuce ciki,

Sabeer ya kalli fahad yace"lpy baka fita aiki ba anata kiran wayarka kashe"

Fahad yace"I'm not well amma gobe zan fita aiki in Allah yaso"

Sabeer yanata kallonshi yace"meya sameka?"

Fahad yayi karamin murmushi yace "don't mind stress ne kawai "

Sabeer yace"to Allah yasawwake tafiya zanyi se na kuma leko Ku amma ya kamata ka kiramin Amarya mugaisa"

Fahad yayi murmushi me ciwo yace"tana gidansu ka sameta a can "

Hankalin sabeer tashe yace"ban..ganeba"ya kurawa fahad kallo,

Fahad yace"na saketa ai"

Sabeer yace"what meyasa faseelat ce fa"

Fahad ya kara yin murmushin yace"ita ta bukaci hakan "

Sabeer yana mai wani kallo yace"seka sakenta kuma"

Fahad yace"ya zanyi ne naso shawo kanta taki and ..."se kuma yayi shiru zuciyarshi na zafi tuno jiya,

Ran sabeer bace yace"u better take her back tun kafin kafara nadama"yana gama fada ya tashi ya fita,

Fahad yayi shiru yana nazarin maganarshi toshi nadamar mezeyi? Itace de zatayi nadamar wulakantashi inji zuciyarshi,

Anayin Maghreb marwan yashiga sahun masu amsar karatu wurin Malam,


Wanshekare tunda safe bayan mommy tagama shirinta zataje aiki ta wuce gidan fahad,

Shi da aysha sungama girka breakfast tare suna cikin shirin fita suna break sukaji knocking fahad yaje ya bude yaga mommy tsaye tanata murmushi,

Yayi murmushi yace"mommy shigo"

Ta shigo tana murmushi tace"nasa har kunfita"

Aysha dake dining tataso dasauri ta rungume mommy ,

Mommy ta riketa sosai tana faraa tace "daughter ya kk tashi?"

Aysha ta dago tace"ina kwana mommy?"

Mommy tace"lpy lau ya babies?"

Aysha tai karamin murmushi tai shiru,

Mommy ta meda kallo gun fahad tace"son ya jiki?"

Yace"naji sauki mommy"

Mommy tace"zuwa nai naduba jikinku kafin na wuce office and ina tare da albishir seka bani goro tukun"tanata dogon murmushi

Yayi yar dariya yace"nabaki aysha gabadaya"

Mommy da aysha sukai dariya ,mommy tace"ai dama aysha tawace ko aysha?"

Aysha ta daga kai sunata murmushi mommy tace"yan biyune acikin aysha so kusan ukku ana mata scanning duk biyune na biyun ya nuna mace da namiji na ukkun ya nuna maza "

Fahad ya fiddo ido zuciyarshi na harbawa tsabar murna yanajin mugun dadi yace"t...t..twins mommy? "

Mommy tace"identical insha Allah "

Yana murna ya kalli aysha kamar ya jawota ya rungume,

Aysha dake farinciki itama ta dan kalleshi ta na cikin farin ciki,

Mommy da taga sunata kallon masoya tace"ka kara kulamin daita sosai kuma karika kaita tana ganin doctor akai_akai"

Yace"nagode mommy"idanunshi kan aysha,

Mommy ta janye ayshar tace"daughter ki kara kula da kanki sosai na tafi I'm late"ta juya ta fita,

Tunkan ta fita fahad ya kankame aysha yana kai mata kisses ta koina ,

Mommy harta kai kofa ta juyo ganin yadda dannata ya rikice yasa ta juya ta fita ta na murmushi,

Fahad na rungume da aysha kamar ya tsaga jikinshi ya sata ciki ya dago fuskarta yana kallonta yace"princess twins for me?"

Ta saki murmushi,

Ya kaiwa bakinta kiss yace"I love u princess"

Tai masa kiss a cheek tace"mee too"

Ya dafe wurin yana sakin murmushi yace "we r late ko mu koma ciki?"

Tai masa wani kallo ta juya dining ta dauko jikkarta yayi murmushi ya tashi yana rike da kugunta yasata mota ya shiga suka nufi school dinsu,

Suna kan hanya yana driving yana kallonta ya nata murmushi yace "twins for me alhamdulillah alhamdulillah!!!"

Ta kalleshi tai murmushi tace"kuma duk kamarka"

Yace"noo plss"yana faraa yace"ni I choose mata kamarki kyawawa sosai"

Tai dariya tace"Yaya kafini kyau fa trust me "

Ya kalleta yayi murmushi yace"I trust u aysha"

Sunata sakin murmushi har cikin school ya ajiyeta tana mai waving ya tafi aiki cikin zallar farinciki,

Gidansu faseelat Ummi fushi takeyi daita kullum tana daki kwance tunani birjik ranta,

Wanshekare Ummi ta leko dakinta da safe tai saurin tashi zaune duk ta fada saboda tunani,

Ummi tace"ke baki zuwa makarantar ne?"

Faseelat ta daga kai,

Ummi tace"kitashi kiwuce school banga zaman da kike ba"

Faseelat na inda_inda tace"Ummi ai tunda nai aure ban kara zuwa ba"

Ummi tace"yayi kyau"ta fita a dakin,

Faseelat ta fara hawaye tai dialing no din rabia ,

Rabia ta dauka tai sallama,

Faseelat tace"yaushe zakizo gida kinsan fahad ya sakeni"

Rabia tace"saki!!!!?"gabanta na mugun faduwa tace"haba faseelat seda nabaki shawara kiyi hakuri kita lallabashi"

Faseelat ta katseta" dalla rufemin baki yar cika baki inkin gadama sekizo"ta latse kiran ta kira zainab suka gaisa tafada mata she's divorce,zainab ma bataji dadi ba taimata fatan alheri,


Another day marwan ya tafi gidan fahad bayan laasar shi kadai yasamu gidan jikinshi mace yanajin kunyarshi ya zauna yace"ina wuni Yaya ?"

Fahad yace"lpy lau"

Marwan ya fara hawaye "don Allah Yaya kayi hakuri ka yafemin kamanta abinda yafaru"

Fahad ya katseshi da cewa "stop it plsss meyafaru kuma?banason dawo da abinda ya wuce mun gama maganar nan tuni "

Marwan yayi shiru can zuwa yace"tnx"

Fahad yace"mekazoyi ne?"

In cool yace"I come to take my car"

Fahad yace"to ka tashi ka dauka katafi komai yawuce tunda kagane gaskiya ina maka murna da dawowa tunaninka"

Ya kara cewa tnx ya tashi ya fita fahad yabi bayanshi da kallo idanunshi na hangomai yadda yake kissing aysha yayi saurin kauda kai,

Marwan ya shiga motar ya fita yana driving a hankali yanata tunani ya hango wata budurwa tana tafiya a sannu ta saka hijab marar tsawo tana tafiya kanta kasa,

Bega fuskarta ba amma the way da take tafiya ya mishi ya nufeta yasha gabanta ya fito daga motar,

Budurwar tai tsaye tana kallonshi se sannan naga fuskarta ashe Hafset ce kawar sameera jaruma🤣,

Ya karaso wurinta yana kallon fuskarta kyakkyawa ta tafi da imaninshi sosai bayan kyawun tafiya harda na jiki ,

Tunkan yayi mgna tace"Malam amma baka lpy ko?"ganin yadda yasha gabanta,

Yayi murmushi yace"eh shiyasa nazo asibity "

Tace"ayya nan kusa ko ba asibity kuma ni ba likita bace "

Yace"likitace mana don ke kadai ce maganin ciwona"

Tai karamin murmushi tace"meke damunka?"

Yace"ciwon so da kauna kuma nasan kina da maganinsa"

Tai murmushi tace"bandashi sede nai maka kwatancen inda zaka samu "

Yace "okay kimin"

Tai dariya ta girgizakai tazo zata wuce,

Yayi saurin shan gabanta yace"plss kishigo na ragemiki hanya "

Ta kalleshi tace"nibana amsar lift"

Yace"wannan motar takice fa halak malak ni ki dauka drivenki ne kawai"

Tai murmushi tace"to nagode "ya bude mata tashiga ,

Yanajin matukar farinciki yashiga yaja motar suna tafiya yace" ya sunan likitar?"

Tace"Hafset "in a light sound,

Ya lumshe ido ya bude yace" suna medadi"

Tace"nagode kaifa patient?"

Yanajin dadin tambayarshin yace"marwan "

Tace "suna medadi " kamar yadda yace mata ,

Yace"nagode likitan zuciyata"

Tace"au ashe ciwon zuciya ne nayi zaton Wanda ke kanka"

Ya taba bandage dake kanshi yayi murmushi shima besan a ina yasamu ba in cool yace"nayi accident three days back"

Tace"sannu Allah yabaka lpy "

Yace"ameen ina bukatar temakonki"

Tace"name fa?"

Yace"inason kibani number wayarki saboda na rika jin muryarki kona samu lpy"

Tai murmushi tace"nawa zakabiya?"

Yace"ko nawa"

Tace"to kawo"

Kamar wasa ya bude lokar mota ya fiddo bandir na 500 50k ya mika mata,

Ta kalleshi ta kalli kudin tai murmushi tace"bar kudinka inason inyi ceton rayuwa bani phone "ta mika mai hannu,

Yanawa hannunta Dan karami wani kallo ya dora wayar akai ta rubuta ta mika mai,

Ya amsa yace"nagode da temako ni kuma ga tukwici"

Tace"aa kabarshi nagode"

Yayi_yayi taki amsa yayi murmushi ,

Ya kaita har kofar gida yayi parking ya fito ya budemata ta fito zata jawo jikkarta ya karasa jawo mata yabata yana murmushi yace"se munyi waya"

Tai murmushi tashige gida,

Ya shiga motar ya tafi yanata farinciki,

Hafset na komawa gida tashige daki tai tagumi marwan ya hadu sosai amma kamar bai isa aure ba dukda yana da tsawo amma dakaganshi kasan yarone ita kuwa aure takeso tagaji da zaman gida,(wannan tunanin nata shine tunanin fin rabin yanmatan dake duniya )

Tana bude jikka ta dauki wayar ta Sega kudinnan ashe seda yayi dubarar sa mata su tafara tunanin yaushe yasaka bata ganiba but no idea ta jinjina kai Sega message ta shiga tabude sakon shi ne "my pretty girl my doctor as well its me ur patient marwan"

Tai murmushi ta ajiye wayar ko jimawa Sega kiranshi ta dauka da sallama ya fara janta fira sunata murmushin masoya,

Cikin kankanin lokaci soyayya ta kullu tsakaninsu amma yaki kawomata ziyara ,

Yau suna waya tace "my patient yaushe zakazo ne kode bakasona shiyasa baka son zuwa wurina?"

Yayi shiru sannan yace"doctor inajin tsorone"

Tace"tsoro kuma..? "

Yace"eh "cikin sanyin murya yace" Hafset bazan boyemiki komi ba dukda cewa inasonki sosai banason rasaki amma hakan bazaisa na boyemiki gaskiya ba "

Muryarshi na rawa yace"Hafset rayuwata nayita ne a baibai ba yadda addini ya koyarba na biyewa abokai da rudin shedan naita aikata mugayen zunubai nine shaye_shaye nine bin mata"

Zuciyar Hafset na bugawa tace"innalillahi mata fa kace marwan?"

Yace"eh amma natuba wlh nadena shiyasa nakeson yin aure don gudun komawa baya wlh Hafset wannan yafaru ne a baya yanzu na tuba inata gyara rayuwata don Allah karki gujeni ki temakamin kizama cikin masu seta rayuwata"

Hafset ta kashe wayar tana kuka tanajin ciwo dama yanayinshi yadanyi kama da wanda yake shaye_shaye amma bata yarda ba ashe ma harda bin mata ita kamila ya zata yarda ta aure shi,

Jin takashe hankalin marwan ya tashi yafara hawaye ya kuma kiranta taita ring baa dauka ba har kira biyar ya ajiye wayar ya rike kanshi yana kuka wannan na daga cikin illar shaye_shaye da bin mata kowata rayuwar banza koda ka tuba kadena mutane bazasu dena kallonka da abun ba ,

Bayan awoyi Hafset na hawaye tana ta tunani zuciyar ta ta bata shawarar aurenshi tunda ya tuba kuma idan tagujeshi maybe zafin abunma yamedashi ruwa gwara tayi jihadi ta temaki rayuwarsa,

Hannunta har rawa yake ta dauki waya ta kirashi,

Jin wakar Abdul d one kimanin numfashi da yayi set a contact ring dinta yayi saurin dauka jijiyoyin kanshi duk a waje,


Hafset na hawaye tace"inasonka sosai patient kuma zan aureka dukda haka kayarda dani kazo inganka ko zuciyata zatai sanyi"

Bakinshi na rawa yace"dagaske doctor?"

Tace"eh kazo zuciya da jikina kai kadai suke muradin gani"

Ya saki murmushi yana murna yace"I'm coming ganinan zuwa"yakashe wayar yana farin ciki yafada toilet,

Hafset ta share hawaye tana jindadi ta tashi ta nufi toilet itama ,

Marwan nata farinciki yayi shiri cikin kananun kaya sede ba irin swag dinnan ba yagaggu se shegiyar tsada 😂normal kananun kaya sede suma tsadaddune sun masifar yi masa kyau yabaza turare ya fito yana kamshi,


Daddy da mommy na zaune suka meda kallo wurinshi suna murmushi,

Daddy yace"marwan ina zuwa haka? "

Marwan yafara susar kai yana sunne kai yace"daddy na samu wacce nakeso fira zanje"

Da mommy da daddy sukai dariya mommy tace"kace na kusayin suruka "

Yayi shiru yana faraa,

Daddy yace"to a meda hankali"

Ya juya ya fita bayan fitarshi duk annurin fuskokinsu ya bace mommy tace"bazasu bashi ba fa "

Daddy yayi saurin rufe mata baki yace"kiyi shiru just pray for him in matarshi ce se subashi ai ya tuba"

Mommy tace"himmm!!!!"

Marwan yana driving yanajin sassanyar wakar west life my love,

Har yaisa yakashe mota ya kira no dinta,

Ta dauka tana gyara gyale tace "patient ka iso?"

Yace"imm my doctor "

Tai dariya tace"ganinan fitowa"

Ya bude motar yana kallon kofar gidan bayan minutes Sega ta ta fito tana sakarmai killer smile me narka zuciya tayi masifar kyau tana sanye da doguwar rigar wani hadadden paper lace,

Ya fito ya rufe motar ya karasa bakin kofar gidan inda take tsaye ,

Jin kamshin juna ya sasu lumshe idanu atare,

In cool tace"bakaji yadda naji dadin ganinka ba kaga yadda kayi kyau sosai "

Yayi murmushi yace"na rasa yadda zan kwatantamiki farincikin danake ciki"

Sukai dariya suna cikin haka baban Hafset ya dawo daga kasuwa yayi mamakin ganin marwan kofar gidanshi sonawa suna gifta shagonshi da mata cike da mota suna dariya so nawa yakejin mutane nace musu Allah ya shirya yau kuma seya ganshi kofar gidan shi,

Ya karaso kofar gidan ranshi bace yanayiwa marwan kaskantaccen kallo,

Marwan da Hafset sukai saurin durkusawa ,

Baban Hafset ya kalleta ranshi bace yace"tashi ki wuce ciki "a tsawace

Ta tashi dasauri tashige gidan tana hawaye,

Ya juyo gun marwan da jikinshi ke rawa yace" kai bakaine dangiyan danasaniba shine kazo gidana ka lalatamin yarinya?"

Marwan yakasa cewa komi,

Baba yace"tashi kabarmin kofar gida koda wasa karka kara tako kafarka anan nan wurin masu mutuncine masu kiyaye dokokin Allah ba irinku ba mazinata"

Marwan ya dafe zuciyarshi tana bugawa kamar zata fito kanshi na juyi,ya tashi tsaye

Baba yace"karka sake zuwa wurin yata dana dade ina bawa tarbiyya kaje can wurin lalatattu irinka "ya shige gida yana huci tun shigarshi yake kwalawa Hafset matsoracin kira kuwa" Hafset!!!!Hafset!!!"

Marwan ya juya yana jin kamar ya zube ya shiga mota ya nufi gida yana driving zuciyarshi na zafi kanshi na juyi muryar Baban Hafset nata masa yawo akai"karka sake zuwa wurin yata dana dade inabawa tarbiyya kaje can wurin lalatattu irinka"

Hankalinshi baya jikinshi yana dafe da heart sede yafarajin order "biiiiiiiiiiii biiiiii !!!!!!" kafin yayi wani motsi motar takaiwa tashi banka duk motocin sukai gefe_gefe suna juyi.
[1/24, 12:36 PM] SHALELE😍: 67

Mutane sukayo kan motocin domin ceton rayuwarsu aka ciro marwan jini nafita ta hanci ta baki ga raunuka da yawa jikinshi aka nufi asibity dashi,

Dayar motar kuwa babbar macece ciki itama duk taji ciwuka aka nufi asibity daita,

Fahad na gida aysha kuma na school tunanin ranar yakasa fita ransa duk time daya kalli kofar shigowa yakansa shi tunowa baya ganin laifin marwan da aysha duk basa hayyacinsu faseelat yake ganin laifi but duk da haka in abun bai ranshi inya tunota yakanji shaawarta shi kansa ya sani karya bakinsa ya furta da yace baya kaunarta yanzu shi kanshi har mamaki yake yadda yake tunanin ta tabbas akwai wani son da komai zaa maka bazai bar zuciyarka ba amma kuma baya shaawar medota gidanshi yanzu batanan komai nata tafiya lpy lau a gidan aysha ciwonta kamar ya tafi domin baya tashi, kiran sabeer da ya shigo wayarsa ne ya katseshi ya dauka ya kara kunne ,

Hankalin sabeer tashe yace "yanzu naga wani accident kamar da motar marwan"

Fahad ya mike idanunshi na cika da hawaye yace "plsss tell me marwan dina ne ko kuwa?"

Sabeer yace"eh motar marwan "

Fahad yace"a inane dan Allah "jijiyoyin kanshi duk sun fito waje,

Sabeer ya fada mai adress jikinshi na rawa ya zari keys ya fita ya nufi gun ,

Yana zuwa yaga motar yana hawaye ya tambayi wani ya fadamishi antafi asibity dasu ba jira ya nufi babbar asibityn garin,

Itako Hafset tana shiga gida dakin mamarsu ta nufa ta boye bayanta,

Babansu ya shigo dakin yana huci yana nunata yace" ke dan ubanki wannan dan iskan zaki kawomin kofar gida?"

Ta kara boyewa jikin mamansu tana hawaye ,

Yace"daga yau kada nakara ganin ki dashi ke kome kama da halinshi kar in kara gani kofar gidana shashasha tashi kifita kiba mutane wuri"

Ta tashi dasauri ta fita ta koma dakinsu tana kuka me taba zuciya,

Mama tace"wai lpy meyafaru?"

Baba ya zauna yana huci yace"wani dan iskan yaro na samesu tare kofar gida"

Mama tace"to Allah ya kyauta Hafset da bata cika kwashe_kwashen samari bama"

Baba yace"wlh idan na kara ganin ta dashi ubanta zanci sena mata jinajina"

Mama tace"insha Allah bazata sake ba"

Fahad na zuwa asibity ya nufi dakin accident da shigarshi aka fito da marwan kwance lifeless kayan jikinshi jina_jina,

Kafafunshi na rawa yana neman zubewa kasa ya jingina da bango ya rufe ido gam hawaye na zuba a fuskarshi,

Nurses suka kai marwan dakin jinya fahad na hawaye ya ciro waya ya kira mommy,

Mommy na zaune tana hutawa kiran ya shigo ta dauka da raha tace"daddyn twins "

Muryar fahad na rawa yace"mommy marwan yayi accident yanzu haka muna asibity"

Gaban mommy ya yanke yafadi tafara sallallami fahad yakashe wayar mommy ta kwantar da kai jikin kujera ta saki kuka me ciwo da tsananin tashin hankali tasha kuka sosai sannan ta tashi ta dauko mayafi ta nufi asibitin,

Tana zuwa ta samu fahad zaune bakin gadon marwan ta zauna tana kallonshi tana hawaye masu zafin gaske,

Fahad ya riko hannunta yana hawaye yace "mommy kidena kuka zai samu lpy"

Mommy tace"dolene nai kuka ku kadaine gareni idan na rasashi saura kai kadai ka rage"

Fahad na jin tausayinta yace"insha Allah zai samu lpy mommy "

Mommy tace"muna zaune yawuce yana faraa yace zashi fira ashe bazai dawo lpy ba"

Fahad yayi shiru yana kallonta,

Wayarshi ce tafara ring yana dubawa yaga aysha ya duba time 6:20 yasan tun dazu tanata jiranshi ,

Ya saki hannun mommy ya tashi ya fita,

Bayan fitarshi wayar mommy tafara ring ta dauka tana cigaba da hawaye,

Daddy yace"na dawo ban sameki ba kina ina?"

Muryar mommy dishe tace"ina asibity marwan yayi accident yaji ciwuka sosai baima ....baimasan inda kanshi yake ba"

Daddy yayi salati zuciyarshi na karyewa yace"ganinan zuwa ya nufi asibitin "

Fahad na isa school dinsu aysha ta bude motar tashiga tanata faraa sede tana kallon fuskar fahad taganta jawur dagani yasha kuka,

Jikinta yayi sanyi tana kallonshi tace"Yaya lpy?"

Bakinsa cije da lips yace"marwan yayi accident "

Gaban aysha yafadi saboda har mantawa take da wani abu yashiga tsakaninsu tanata renon cikinta karatu,kula da mijinta da gida she's full busy,

Hawaye masu zafi suka fara zubomata tasa hannu ta share wasu suka kara zubowa zuciyarta na karyewa ta kwantar da kai a kan mota tafara kuka ,

Fahad yayi saurin riko hannunta cikin sanyin murya yace"princess me kikeyi haka?kinsan baki lpy so plss kiyi shiru marwan yana samun sauki"

Ta dago kai ta kalleshi zuciyarta na ciwo tace"dagaske?"

Yace"eh ba wani ciwo bane zai samu sauki very soon"

Ta meda kallo akan glass din motar tasa hannu ta share hawaye,

Ya tada motar ya nufi gida zuciyarshi cunkushe,

Ganin sun nufi gida yasa ta kalleshi muryarta sanyaye tace"ina zamu?"

Bai kalleta ba yace"gida"

Ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tace"haba Yaya dan Allah ka kaini in ganshi "

Ya juyo da kai ya kalleta yace "kiyi hakuri aysha se gobe kinganshi "

Hawaye suka fara zubomata tace"dan Allah Yaya ka kaini in ganshi plsss ko hankalina zai kwanta "

Yace "kibari se gobe nace ko"

Tafara kuka tai luuu tai baya yayi saurin tarbeta da hannu daya yana kiran aysha !!!,

Ina tuni manyan sun bugar da ita ,

Hankalinshi tashe yayi saurin gangarawa yayi parking ya jawota jikinshi yafara mata tofi,

Ta bude idonta cike da hawaye tana kallonshi tace"dan Allah ka kaini "

Jikinshi na rawa yace"OK alright zan kaiki "

Ya tadata zaune ta jingina da motar idanunta lumshe ya tada yafara driving yana yi yana kallonta itako tausayin mommy ne sosai a ranta tasan uwartata tana cikin tashin hankali,

Suna isa ta fito ya fito dasauri ya kamata suka nufi sashen masu hatsarin dede fitowar rabia ta gano wani danuwansu yayi accident na mashin ta bisu da kallo suko ko ganinta basuyi ba,

Ta wuce tanata kallonsu tatafi su kuma suka wuce ciki,

Suna shiga gaban aysha ya fadi ganin marwan kwance duk ya kumbura jini na shiga jikinshi ga mommy da daddy zaune sun zuba mai idanu,

Aysha ta tafi dasauri ta rungume mommy tana kuka sosai me ban tausayi,

Fahad ya jingina da kofa yana kallonsu yana hawaye,

Mommy ta janyota gaba tana hawaye tana share mata nata tana cewa"kiyi shiru daughter zai samu lpy "

Ta cigaba da kuka tana jikin mommy kafin ta lafa tai shiru in cool mommy ta kira fahad ya karaso jikinshi mace,

tace"ka tafi da daughter gida ta huta ka tabbatar kabata abinci"

Ya jinjina kai ya kamata suka fita suna zuwa gida tai kwance falo kan kujera ya tafi dining ya dauko abincin daya girka ya dawo wurinta ya zuba abincin ya zuba drink ya tadata ya medata kan cinyarshi yafara bata abincin tana ci tana hawaye cikin rarrashi yace"aysha kiyi hakuri plss kina kara dagamin hankali kiduba kiga yadda cikin ki ke motsi kiyi shiru hakanan"

Tana hawaye tace"zaiji sauki ko?"

Yace"eh idan Allah yaso kidena kuka ki masa addua"

Tai shiru tanata ajiyar heart ta cigaba da cin abincin seda ya tabbatar takoshi sannan ya kamata suka nufi toilet domin yi mata wanka,

Rabia ko direct gidansu faseelat ta nufa faseelat na daki kunkume sam bata jindadin gidannasu su Ummi basa sakarmata fuska haryanzu bata ganin laifinta don ta rabu da fahad saboda aganinta wannan shine dede kuma ta ceto rayuka daga halaka fahad baya iya adalci kokadan tasan yana sonta amma yafifita abunda mommy keso fiyeda muradinshi baze iya masu adalciba komin yadda yaso dole kuma itace zaai ta cuta aysha ko ta riga tagama karantar halinta na zafin kishi ta tabbatar koda ciwonta na gaskiya ne amma akwai kishi yadda yake tashi da zaran tana tare da fahad ga wani iyayi datakeyi ita yar gata,

Idan zasu cigaba da zama haka to wace kalar rayuwa zasuyi?ita tariga tasan bazatai hakuri ana fifita aysha ba sannan shi fahad baze yi adalciba wannan matsalace babba garesa sannan mommy komin yadda zatai mata biyayya bazata taba hadata da aysha ba da iyayenta suka damka mata kyauta kuma amana,

Taki fitowa tafadi wani abu dangane da gidan tayi shiru duk kowa na mata kallon me idda itako tasan tana zaunene kawai ,ta kanji son kiran alhajinta sede taki kiran nasa saboda kowa na mata kallon me idda beda kyau ta kirashi tun yanzu harse bayan jini ukku,

Tana cikin tunani rabia ta shigo ta kalleta tace"daga ina?"

Rabia tace"daga asibity nake se kuma naga mijinki da matarshi sun nufi ward din masu hatsari hankalinsu tashe"

Faseelat tai mata wani kallo tace"tsohon mijina de ko"

Rabia tace "to tsohon mijinki kikasani koki koma"

Faseelat ta tabe baki tana dan girgizakai tace"alhaji ne zabina shi nakeso ba fahad ba"

Rabia tace"to yasani ne?ke keta abunki shi ai yasan kinyi aure yama manta dake nasan yanzu"

Faseelat tace"bazai manta dani ba alhaji

Please Login or Register in order to submit comment