Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunyi breakfast sukai bankwana suka hau hanya,


Karfe 4 suka isa gidan aysha na murna tai cikin gida da gudu tana kiran ummanta,

Mommy tai murmushi tabi bayanta da kallo sannan ta nufi fada don kai gaisuwa,

Tana zuwa ta gaida sarki sannan tashiga cikin gidan,

Aysha na jikin Umma umma tacewa momy"sannu da zuwa"

Mommy na kallon aysha tana murmushi tace"yawwa ya muka sameku?"

Umma tace" lpy lau sannunku"

Taiwa mommy iso dakinta sannan suka fita,

Mommy tawuce toilet tai wanka tai salla tafito an cika dining da abinci ta danci sannan takoma falo ta zauna,

Tana zama aysha ta shigo harta sauya kaya atamfa kwadebuwa taji aikin wuta ,

Tanata murmushi tace"mommy daddy na son magana dake "

Mommy tai murmushi tace"aysha andawo gida anata murna OK mutafi"

Aysha tafita tabi bayanta,

Suna zuwa bakin dakin Umma ayshar ta nufi dakinta mommy kuwa tashiga ciki tasamu GU ta zauna tanata faraa

Sarki yace"hakika naji dadin ziyarar da kika kawomin gida na nagode sosai inafatan watarana zaki sake dawowa"

Mommy tace"nice da godiya bisa karamcinku a gareni nagode sosai Allah yakara girma,sedai ina rokon wata alfarma awurin sarki "

Sarki yace"hjy ki fadi komiye insha Allah inde befi karfi ba"

Mommy ta nisa tace"ina rokon kubawa yarona auren aysha na tafi daita tayi karatunta da take buri a rayuwarta"

Sarki da Umma da Amarya sukai murmushi sarki yace"hjy Amina nabaki aysha koda wane lokaci kuka shirya a shirye nake dana doramusu aure da yaronki"

Mommy na kan seat ta sauko kasa ta gurfana tana godiya kamar tai kuka saboda dadi,

"Nagode nagode sosai Allah yakara tsawon rai da lpy me dorewa nayi matukar farinciki nagode insha Allah zan rike amana Allah yasakamuku da alheri"


Sukace"ameen"

Mommy ta kara nisawa tace"ina neman alfarma abani ita mutafi tare taje tayi interview saboda tasamu damar shiga school a wanna shekarar after sunyi jarabawar zan medota"

Sarki yace"na riga nabaki ita kuna iya tafiya"

Mommy ta cigaba da godiya kamar zatai kuka anbata kyautar ya sunkutukum ta kalli su mommy tace"kumin godiya"

su Umma sukace"ai an zama daya"

Sundade awurin suna magana,

Aysha na komawa dakinta tai dialing number fahad ,

Fahad na wurin sabeer kiran number Niger ya shigo ya dauka yakara akunne yace"assalamu alaikum"cikin cool voice dinshi,

Aysha ta saki murmushi zuciyarta na kara narkewa,

Jin shiru ya cigaba da cewa "hello hello"

Tai tsit ta matse lips tanata faraa,

Jin ba reply ya kashe ,

Ta rumtse ido voice dinshi nata mata yawo ta matukar yi mata dadi,

Ta bude ido tana murmushi tace"ashe haka so yake?ya hanaka sukuni inba kasamu ganin masoyinka ba?"

Ta kalli sama tace"ya Allah kahadani da masoyina"

A ranar ma ba baccin kirki sunata shirin tafiya Nigeria gobe aka karawa mommy sha tara ta arziki ita batasamu tayi kira ba suma basu kira ba kowa na hidimarshi,

Da asuba aysha taje gaida Umma ,Umma ta amsa sannan ta kalleta tace"aysha zaku tafi Nigeria da mommy ki kara kama kanki kiyi mata biyayya macece me halin kirki kiyi hakuri da zabin mahaifinki ki kula da kanki da adduoi kinsan lalurarki karki yadda abubuwa su rika bata miki rai ki zama me ladabi ,biyayya,kawaici ,kunya,dan Allah "

Jikin aysha sanyaye tace"insha Allah Umma"

Umma tace"kiyi hakuri aysha ki kara hakuri hakuri shine rayuwa can ba nan bane karkice komi kkkso shi zaai"

Aysha tace"to Umma"

Umma tace"Allah yamiki albarka da nace zakije gidan sisters dinki ki musu bankwana but ba time kitashi kije ki gaida abbu kije ki shirya"

Aysha ta tashi ta nufi dakin abbu bayan taje tai knocking yace tashiga ,

Tashiga tanata sadda kai taje ta zauna gefenshi tace"ina kwana abbu"

yayi murmushi yace"aysha na kintashi lpy ?"

Tace"lpy lau "

Yace"zaki tafi ki barmu are u happy?"

Ta daga kai kadan

Yace"Allah yamiki albarka tashi kije ki shirya"

Tatashi ta fita tanata murna ta nufi dakin mommy ta samu tana wanka tafito dasauri ta shiga daki tafada toilet,

Shaf_shaf tafito ta zauna tsara kwalliya ta saka doguwar riga red me hawa biyu kasa da milk tanata sheki tadora milk gyale tafito,

Dakin mommy takoma mommy na ganin ta tace"my daughter se Nigeria "

Aysha tai murmushi tace "mommy ina kwana?"

Mommy tace"lpy lau ya gajiya"

Aysha tai karamin murmushi tai shiru ,

Mommy tai murmushi itama,

Karfe 9suka fito aysha nata dan faraa sam bataso ta gayyato kuka kar aljanunta su tashi tanata faraa suka shiga mota aka tafidasu air port,

Suna zuwa9:30 jirginsu ya daga zuwa Nigeria,

Suna cikin jirgi bacci ya dauke aysha saboda an kwana biyu baaiba,

Mommy kuwa murna bata barta ba saboda doki takagara taga wace irin murna fahad zeyi in yaga aysha,

Karfe 3 da wani abu suka iso Nigeria mommy tafito rike da hannun aysha tanata murmushi suka dauki kayansu,

Sun fito mommy na niyyar kiran waya azo a daukesu sega wani ze wuce ta sanshi sosai yafito yazo wurinta yana murmushi ya gaidata yace"hjy daga unguwa kuke?"

Tace"wlh daga Niger "

Yace"kushigo na kaiku gidan kafin azo zaa kara bata miki lokaci"

Tace"to nagode"

Ta kalli aysha mutumin ya bude masu suka shiga tunda aka kama hanya bawanda yace wani abu aysha da mommy kowa yana magana da heart dinshi,

Har bakin gate yayi horn megadi yazo ya bude suka shiga da mota cikin gida ,

Yana parking suka firfito mommy taga motar fahad fa ke alamun yadawo kenan,

Ta kalli mutumin tace"to nagode sosai Dr"

Yace"bakomai Allah ya hutar da gajiya"ya fiddomusu akwatinansu yabar gidan,

Mommy ta kalli aysha tai murmushi tace"nanne gidan"

Aysha tai murmushi,

Mommy takama hannunta suka nufi ciki,

Tundaga bakin kofa taga anyiwa cikin gyara tanata faraa ,

Suna shiga tace"assalamu alaikummmm"tana dubar seats na dakin thinking that akwai kowa agun,wayam bakowa tafara bin kasan dakin da kallo tana kallon new seats din da sauyin part din,

Aysha ko suna shigowa hoton fahad da faseelat tafara cin karo shine yayi mata oyoyo zuciyarta tai mummunar faduwa tai saurin dauke ido daga kallonshi,

Mommy nata kalle_kalle ta kalli bangon ma duk an sauya wallpaper sannan idonta ya sauka akan pic din ,

Gabanta yayi mummunar faduwa ta kure pic din da kallo zuciyarta na harbawa fat!!!fatttt!!!

Abun ya matukar tsorata ta da bata mamaki fahad dinta da wata harta dafashi tadesan ba matarshi bace don me zata dafashi?ko kusa bata taba tunanin fahad ze yadda ya hada jiki da wata da ba muharramarsa ba se gashi yau tagani,

Tai tsaye kamar gunki ta kalli dayan hoton faseelat ta dan kwanto jikinshi tana murmushi ,

Haushi yakara mamayeta setaji tsanar faseelat din a ganinta yarinya me kamun kai da kunya bazata yiwa wani namiji daba muharraminta ba haka harta kwanto jikinshi,

Mommy ta kara kure fuskar faseelat da kallo se tai mata kama da wata tsohuwar yar bariki wadda tadade cikin shi,

Tambayoyi ne da yawa akanta to wacece?miye alakarta da beloved son dinta? Gyaran gidan me akayi?

Ta na son sanin amsoshin tun wuri,

Dasauri ta kalli aysha da duk jikinta yayi sanyi tace"zauna aysha ina zuwa "

Tai waje dasauri,

Aysha takure kasan tiles da kallo batason kara kallon saman amma ina seda idanunta suka kara kaita gun ta saukesu akan pic din da faseelat ta kwanto jikinshi tabaya duk suna murmushi,

Zuciyarta takara bugawa sosai tanajin tsananin kishi,

Kafin ta dauke ido akan pic din tai luuu tai baya sheme a kan kujerar ,

Mommy kuwa dasauri tashiga part din fahad tun bakin kofa take kwala kiran "son!! son!!!"

Yana ta scrolling pics dinsu da sukayi dana faseelat da take turomishi yanajin sonta yaji muryar mommy kamar daga sama se ya dan dakata dan bai yadda ba,

Mommy ta karasa shigowa tana kiran son,

Yana ganinta ya mike yanajin tsananin farinciki ya tafi ya rungumeta ,

Mommy ma ta rungumeshi zuciyarta na cigaba da bugawa,

Yayi breaking hug din yana murna yana kallon face din mommy yace"mommy I have a very big surprise for u"

Tai shiru tana kallonshi tana so tai masa tambayoyi,

cike da dokin yafada mata yace"mommy I'm in love..."

Gaban mommy ya fadi aiko soyayya zaiyi bada kamar wannan ba ai ta masa girma donko idan bata fishi ba baze fita ba a ganinta,bare wannan kamar wata kilaki ta katseshi da cewa "love son?"

Yayi murmushi yace"yeah mom I tried my best ban samu number ki ba"

Mommy tace"wannan kalar tarbiyyar na baka ?zaka hada jiki da Matar da ba muharamarka ba?"

Ya lumshe ido yabude yace"I'm sorry mom but she's mine we're engaged saura 6days bikinmu this is d surprise da naso nabaki"

Mommy taji maganar kamar saukar guduma batasan time da tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun!!! "ba

Fahad ya kureta da ido shida zega murna seyaga akasinta.
[12/10, 7:18 PM] SHALELE: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



3⃣1⃣


*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace hakika naga wani mutum yana yawo acikin aljanna saboda wata itaciya dake kan hanya da ya sare saboda tana cutar da mutane*




*My real fans in paid for all group wannan debate haka🤪kunayi inajin dadi kuna bari ina sanya da typing*





Mommy fuskarta ya mutse tanajin balain haushi tai tsoki ta kalleshi ta kuma kauda kai tai tsoki takara kallonshi tama rasa me zata ce tace"wai meyasa baka da hankali ne fahad?"

Yayi still yanata kallonta,

Ta kuma kauda fuska a ya mutse tace "da auren ka zakamin surprise ?aure bananan bada sani naba " ta gumtse face tace "koda yake ba laifinka bane" tajuya dasauri ,

Fahad daya tsunduma tunani yayi saurin binta yana kiranta"mommy mommy!!! "

Tai banza tawuce part dinta tanata sauri tanaso taje ta kira daddy ya dawo ayita kanme zai yanke wannan shawarar batare da ya jira dawowarta ba,

Tana shiga tai still hango aysha sheme kan kujera,

Hankalinta tashe ta isa wurinta ta riko ta jikinta agigice take kiran sunanta"aysha!!aysha aysha kitashi"idanunta jawur ,

Fahad ya iso cikin dakin ganin wata yarinya kamar aljanna a jikin mommy gashinta duk yabaje dakaganta kasan bata cikin hayyacinta yasa shi rudewa cos mutum ne me tausayi,

Ya karasa wurinsu dasauri shima hankalinshi a tashe ya kalli fuskar ayshar mommy nata motsata shiru,

Cikin tashin hankali yace"mommy me..meya sameta who is she? "

Mommy tace"kawo ruwa a cup dasauri "

Yatashi dasauri yashiga kitchen ya debo ruwa ya dawo dasu ya mikawa mommy ,

Yana tsaye yana kallonsu mommy taita tofi da tagama sannan ta deba ta watsawa aysha a fuska takara deba ta watsa mata aysha ta yamutsa fuska ta rumtse ido ,

Muryar mommy tafara ji tana sannu"daughter sannu Allah yabaki lpy"tana gyara mata gashin kanta zuwa baya ,

Tausayin kanta ya kamata tafada son maso wani she love him she really do bazata iya rayuwa babushi ba,

Kamar daga sama taji muryar da tundaga jiya take mata yawo a zuciya murya me sanyi da sanyaya ruhi da sassan jiki,

Fahad yace"aysha sannu"in cool voice nashi,

Zuciyarta na harbawa ta bude ido a sannu ta saukesu kanshi,

Shima din ita yake kallo yanajin tausayinta,

Sosai taga ya mata kyau she knew ganinshi se yafi pic nashi he's real handsome without dress yana sanye da arm less riga da shorts,

Ta lumshe ido hawaye masu zafi suka gangara gefen idanunta,


Mommy na jin matsanancin tausayinta takara cewa"sannu aysha"

Aysha ta daga kai idanunta lumshe,

Mommy ta kalli fahad jikinta sanyaye tace "kaimin ita bedroom"

Ya kalli mommy ya matse lips ya rumtse ido ya bude ya duka ya dauko aysha daga jikin mommy in a bridal style ya nufi upstair da ita,

Aysha jinta jikinshi taji saukin ciwon da takeji a heart ta bude ido ta dorasu a kanshi,

Shima ita din yake ta kallo young girl with such beautiful figure,

Sukaita musayar kallo kowa yaki dauke idonshi akai ,yana ta tafiya dauke da ita going to upstair kamar yadda mommy ta bukata,

Mommy kuwa tabi bayansu da kallo hannunta akan gemu tayi tagumi gabadaya gwiwoyinta sunyi sanyi tana regretting nema mishi aysha ta sake daga kai ta kuma kallon pic din fahad da faseelat ta kure fahad da kallo sosai ta gano yadda yake mutuwar sonta don inba haka ba ba wani dalili da zesashi barin mace ta dafashi kuma its not by force gashinan duk Kansu suna murmushi,

Tai tsoki ta dukar da kanta kasa still da tagumi tana magana da kanta "why ?why meyasa na cusawa aysha son fahad ?yanzu ni ya zanyi?" take ta tambayar kanta,

Shi ko fahad har dakin mommy ya shiga da aysha yana shiga ta lumshe ido shi ko yakasa dauke ido akanta yaje ya kwantar daita a bed,

Yana kwantar da ita batare da bata lokaci ba ya juya yafita ya nufi wurin mommy,

Aysha ko seda taji ya fita sannan ta bude ido wani sonshi na kara kwaranya a heart dinta,

Tafara tunani shikenan yafara soyayya ?yafara son wata daban meyasa zaiyi mata haka? She don't know ma har bikin an kusa,tafashe da kuka,

Fahad yana saukowa yake kallon mommy da tashiga duniyar tunani he's regretting da seya bari ta dawo shi farin cikinta yake so but yanzu yaga batai murna ba ,

Har ya karasa mommy bata dago ba yana zuwa ya zukunna gaban mommy fuskarshi ba walwala yafara cewa"mommy I'm sorry ban taba tunanin hakan ze bata miki rai ba nayi ne saboda kiyi farin ciki I'm sorry "

Tunda ya fara mommy ta dago tana kallonshi ko da yaushe de bata dena yabawa danta this begging da yake ya rage mata zafi ,

She's smart tasan yadda zata tafiyar da abu with out bacin rai na kowa,

Ta dora hannu ta shafi kanshi ta gangara dashi a face dinshi ta dago face din sosai ya bude ido yana kallonta,

Tace "why son ?saurin me kake ?I have a better choice for u this girl aysha is very nice girl, cool just like u na cusa mata son ka na kuma nema maka aurenta iyayenta are good manyane but sun bani ita kyauta saboda ka aure ta" ta yamutsa fuska tace"but now ka riga kayiwa kanka zabi"

Yana ta kallonta he's not happy at all yanajin inama be taba ganin faseelat ba don for now baze iya rabuwa da ita ba, but his mommy is his happiness his life his world and every thing zabinta will always be the best for him,

Ya lumshe ido ya bude yanajin ciwo yace"I'm very sorry mommy for all dis I don't know ne shiyasa, ni de inata kokarin faranta miki ne "

Tai karamin murmushi tana ta kallon shi ya cigaba da cewa "I love her inasonta zabinki will always be the best for me I love her and I will marry her " yayi shiru yana tunani ya zaai ya iya zama da mata biyu with out choice yace"I will marry both of them I want your happiness mommy idan...idan kuma u don't like faseelat I will leave her and marry aysher alone"

Mommy ta kalli pic din su again sam faseelat batai mata ba but bazata fito fili ta nuna hakan ba tunda shi yana sonta hakan baze masa dadi ba ,kuma saboda me zatace ya barta tunda bawani abu marar kyau ta ganta dashi ba da akwai wannan ko bayaso se ya rabu da ita but now tunda har daddy ya amince lalle bata da wani big problem shiyasa ya yarda da abin,

Amma tana mamakin miyaja raayinshi ga faseelat ga yara yanmata nan but dis ko da ze fita yrs da kadanne,

Kamar yadda yakeson farincikinta itama haka takeson nashi tai murmushi tace"no inason faseelat sosai tunda kana sonta I must love her too but aysha is not well tana da problem na iska kamar yadda kagani zaiyi wuya kafin ta samu sauki this means duk time da ranta ya baci ciwonta ze tashi I have seen tana da kishi sosai maybe this photo of yours ne ya tado mata da ciwo what kuma idan tana da rival? Kuma I dont think iyayenta zasu amince a yanzu kuma kaima yazakayi da mata har biyu?"

Ya dora hannunsa akan na mommy dake rike da fuskarshi yace"I can I love all of them kuma zan kula da aysha zan sota sosai mommy zan nema mata magani"

Mommy tai karamin murmushi tace"zan kira iyayenta nafada masu komi ake ciki idan sun amince ko after bikinku se ayi nakun daita ,idan kuma basu yarda ba I will take her back to dem"

Ya girgiza kai yace"this will not happen mommy insha Allah zasu yarda"

Tai murmushi tace"OK call ur daddy for me bari naje nabata abinci "

Ya daga kai mommy ta tashi ta shiga kitchen ta samu yayi simple supergetti jalop ,ta zuba tafita ta haye sama,

Yana zukunnen ya kira daddy sannan ya tashi ya hau seat ya ciro pic dinsu dana faseelat daya dora sama yayi tsaye yana kallon pic din musamman fuskar faseelat yana tuno faraarta da dariyarta ya dora hannu akan face din yana yawo dashi,yake tunanin how she will feel yaje mata da labarin su biyu zaya aura? bayajin abin zaizo dasauki,

Ya koma ya zauna yana rungume da pics din yana kare mata kallo,

Mommy kuwa dakinta tawuce ta samu aysha na kuka,hankalinta tashe taje ta jawota jikinta tana cewa"aysha lpy meya sameki?"

Aysha tai shiru tana ajiyar heart tace"bakomi mommy I'm just missing home"

Mommy ta matse lips cos tasan she's lying a hankali tace"I'm sorry aysha but insha Allah komi zai dawo normal kinji? I'm sorry kitashi kici abinci"

Aysha ta girgiza kai tace"I'm not hungry bazan iya ci ba"

Mommy tace"ki daure daughter kici kadan"

Aysha ta girgiza kai saboda ko ta sakashi a baki its hard ya samu wurin wucewa ,

Mommy tace"to shikenan ki tashi kiyi salla seki kwanta ki huta"

Aysha ta gyada kai,

Mommy ta medata ta kwantar daita ta tashi ta fita fuskarta badadi ,

Fahad na zaune yaga mommy tafito da tray din abincin fuskarta ba walwala kuma ba alamun anci abincin yabita da kallo harta shiga kitchen ba jimawa tafito ta koma sama batare da ta ko kalleshi ba,

Jikinshi sanyaye ya tashi ya ajiye pic daya cire ya shiga kitchen ya dauko tray din ya hau saman dashi,

Da sallama bakinshi ya shiga dakin aysha na kwance kuma bega mommy ciki ba,

Aysha na jin sallamarshi ta juyo idanunta jawur take kallon shi,

Yana tsaye yana kallonta ganin idanunta jawur yakara tabbatar da kuka tasha ,

Tayi mamakin ganinshi seta juya kanta kamar yadda take kwance,

Ya karasa bakin bed din ya ajiye tray din ya cigaba da kallon bayanta,

Ita kuwa zamanshi wurin yasa zuciyarta ta rika bugawa ta lumshe ido tana cigaba da saurarenshi tana shakar kamshinshi medadi,

For minute sannan da sanyin murya in calm ya kirata"aysha!!"

Taki juyowa tana kwanciyarta sede ta bude ido tana mamakin kiranta,

In cool voice ya cigaba da cewa "aysha I'm sorry kitashi kici abinci"

Ta juyo da kai da jikakkun eye lashes dinta tana kallon shi,

Yana ta kallonta ganin idonta da hawaye yace"why are u crying aysha?"

Ta lumshe ido tabude tana kara tabbatar da maganar mommy da yabonshi da take,

Yana kallonta yana mata kallon yarinya very young yar 14yrs don baya tunanin takai 15 yan breast dake gareta yasa ma beyi tunanin bata al'ada ba da seyace ko mes bata fara ba,

Yace"OK kitashi kici abinci plsss"

Taji dadin damuwa daya nuna akanta ta yunkura zata tashi unexpected taji ya kamata ya rike mata kafadu ,

Ta kalli hannunshi sannan ta karasa tashi zaune ta jingina da bed,

Ya koma ya zauna shi yana mata kallon kanwarshi ya bude ido yafara zuba abinci a plate ,

Tana ta kallon shi ya zuba abincin ya zuba drink a cup ya dauki plate din a hannu ya kalleta ,

Tai saurin lumshe ido ya debo taliyar a spoon ya nufi bakinta,

Jin kamshin abinci na doso hancinta yasa ta bude ido ganin shi rike da spoon ya kara bata mamaki sosai taji dadin hakan ta kalli kyakkyawar fuskarshi,

Shima ita yake kallo yace"eat "atakaice

A hankali ta bude baki yasaka spoon din bakinta ta fara tauna abincin a sannu tanata kallon shi,

Ya debo abincin zai kai bakinta yace" kidena damun kanki kinji kanwata?"ya karasa samata shi a baki,


Ta daga kai tana cigaba da cin abincin,

Yafara debo abincin se yatsaya ya dago ya kalleta yace"kina sona?"

Tai saurin dora hannuwa a face dinta ,

Yayi karamin murmushi yace"ni inasonki sosai zaki aureni?"

Tai shiru fuskarta rufe tanata murmushi,

Yace"kunya ta kikeji?"

Nan ma ba reply ,

Ya koma ya cigaba da debo abincin ya debo ya daga ze kai bakinta yace"buda bakin to kici abincin"

Ta girgiza kai,

Yace"no se kinci"

Ta kuma girgiza kai ,

Yace"plss kici for me"

Ta cire hannunta ta kalleshi,

Ya sakar mata murmushi tai karamin murmushi itama,

Ya saka mata abincin ta cigaba da ci,

A hankali yace"u r beautiful "

Tai karamin murmushi tana kallon shi,he don't expected her reply se yaji muryarta medadi tace"not like u"

Ya fiddo ido yanajin dadi tafara sakewa da murmushi fuskarshi yace"ashe ina da kyau?"

Ta daga kai tana murmushi tace"sosai"

Yayi murmushi me kyau yace"nagode amma ban kaiki ba"

Yakara debo abincin zai kai bakinta mommy da tai salla tashigo dakin don duba aysha,

She is very surprise yadda ta gansu memakon ranta ya baci kamar yadda taji da faseelat ta dafashi se tai murmushi ta juya ta fita,

Dukkansu sun sunkuyar da kai tana fita ya cigaba da bata abincin yana dan jawo labari harta ci sosai ita kanta batasan time da taci me yawa ba,

Shi kuma yaji dadin saukin kanta,

Ya debo zai kai bakinta a hankali tace"nakoshi"

Yace"kin koshi ?"

Ta daga kai tace"I'm ok"

Yace"to zanje nayi salla zan dawo kibani labarin ya niger take kema kitashi kiyi sallan before na dawo"

Ta daga masa kai,

Ya tashi ya dauki tray din yafita,

Tabi bayanshi da kallo tana murmushi,

Yana fita ta lumshe ido tana tambayar kanta kode wancan pic din ba budurwarsa bace?wata zuciyar na karyatawa saboda yanayin nasu na masoya ne ,ta tabe baki ta tashi ta shiga toilet,

Mommy tunda ta fita cin abinci taga pic din daya cire akan kujera tai murmushi ta girgiza kai ta debo abinci takoma dining tana ci,

Tana cikin ci yafito ya kai plates kitchen ya fito ya dauki pic ya juya yaga mommy a dining,

Da hannu tai masa alamar yazo,

Ya ajiye pic ya karasa wurinta ta jawoshi jikinta tai masa kiss tace"nagode son"

Yayi murmushi ta sakeshi tace"kaje kayi salla"

Yace"OK"ya tafi ya dauki pic ya fita,

Mommy tagama cin abinci kenan zata tashi daddy ya shigo ganinta yabashi mamaki yana ta murmushi yace"welcome my love "ya nufi wurin ta ze rungume ta ta hade fuska ta juya mai baya,

Yana isa ya riko kafadunta yace"I'm sorry nasani nayi laifi but kimin uzuri nata nema bansame kiba"

Ta juyo tana mai wani kallo tace"ni ba wannan ne gabana ba ya zaai ka yarda da maganar fahad kabashi goyon baya har ace zeyi aure bana nan wannan wane kalar surprise ne?"

Yayi shiru yana ta kallonta sannan yace"a iya sani na kinaso yayi aure naga yarinyar da iyayenta a OK shiyasa na yarda kuma naga yanasonta shima that's y"

Tace"toni I'm not happy ko kadan yanzu zakusani jin kunya naje na samo masa yarinya harna taho daita ga kuma abinda na taras kunyi bansan yadda zan ba"

Yace"wait kina nufin kin samo mai mata a can?"

Tace"eh"fuskarta bawalwala ta cigaba da cewa "d sad news is mahaifinta shine yabani masauki shine ya kula dani suna son yarsu suka bani duk da matsayinsu yanzu na rasa ta inda zan fara fadamasu"

Daddy ya dafe goshi yace"innalillahi wainna ilaihi rajiun"ya zauna akan dining seat,

Mommy ma takoma ta zauna tana kallonshi,

Ya cire hula ya ajiye yanata tunani yace"ina son yasan kindawo?"

Tace"eh kuma na nuna mishi banji dadin abinda yayi ba"

Daddy yace"duk matsalar network ce bakomai ba da akwai communicating da hakan bai faru ba"

Mommy ta girgiza kai tanajin takaici tace"nayi mamaki daka yarda da wannan yarinyar aita mishi girma kamata yayi yasamu yarinya ya aura zefi "

Yace"banga girmanta ba tunda suna son junansu inafatan de baki fadamai hakan ba?"

Tace"eh kuma na fadamai nai masa zabi ya nunamin zai auresu gabadaya yanzu dama inajiran kadawo muyi maganar sannan in kira iyayenta "

Daddy yace"to Allah yasa hakan shi yafi zama alheri daze yiwu se ayi auren time daya dan karnan kusa kuma a kara tara jamaa"

Mommy tai kasake tace"hakan baze samuba"

Daddy yace"tunda ya amince abu ne da sauki yanzu kikira babanta"

Mommy tace"to wayar na ciki bari naje"

Tatashi ta hau sama yabi bayanta ,tana shiga ta dauki waya tai dialing number abbun aysha,

Daddy ya shigo ya zauna kusa da ita,tana ta ring sannan ya dauka yayi sallama,

Mommy ta amsa a mutunce tana dan in_ina tace"abbu mun isa lpy lau har mun huta "

Yace"alhamdulillah"

Tace"sede akwai matsala bayan baninan ansawa fahad biki ban sani ba, wlh bansan hakan zai taba faruwa ba"

Abbu yayi karamin murmushi yace"karkidamu kanki hjy nadade da sanin zaiyi aure duk da hakan nabashi aysha"

Dadi ya mamaye mommy tana ta murmushi me sauti tace"nagode nagode Allah yakara girma da nisan kwana yabar zumunci ,gashi saura 6days bikin da lokaci be kureba da anyi rana daya"

Batare da shawara da ummar aysha ba sarki yace"nariga nabaki ita ko da wane lokaci kukeso

Please Login or Register in order to submit comment