Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace"dan Allah kayi hakuri an samin rana"

Yayi dariya yace"sa rana ai ba aure bane ni de kawai amincewarki nake nema inasonki sosai wlh kuma zakiji dadin zama dani"

Mansura ta kalleshi ta nufi cikin gida tanajin haushi ko yanayin kallon da yake mata be mata ba,

Yabi bayanta da kallo yana murmushi harta shige ya kalli gidan ya girgiza kai ya shiga mota yabar unguwar,

Yana kan titi yake waya da yaranshi akan akai kayan abinci gidansu mansura da dubu 100 cash ya masu kwatance shi ko ya tafi wurin harkokinshi,

Mansura na komawa mama na sauri tanajin dadi tace"wanene?"

Mansura ta yamutsa fuska tace"mama yanzunne fa muka hadu dashi a super market se wani kallo yakemin wai shine yabiyoni yana fadamin yana son aurena ni kuma nace.."

Mama na jin haushi tace"se kkce Yaya?"

Mansura tai kasa da murya tace"senace ansamin rana"

Mama tana harararta tace"gafara can marar wayo kinsamu ma yace yana son ki har kashewa kanki kasuwa zakiyi kice anmiki baiko yadda kowani yaji zaizo zaifada anbada ke sakarai marar wayo tafi ki bani wuri"

Mansura bata koma kan ruwan tea ba takoma daki ta kwanta zuciyarta na zafi kan me zata yarda dashi bayan ita din ba fara bace baka ce shi kuma duk yanayinshi ya nuna kyawun yake mawa,

Karfe 12 fahad yaje ya dauko aysha tunda tashiga motar ba Wanda yayi magana shi yana busy tunani itako tanata satar kallonshi harse da ya kusa isa gida sannan hankalin nashi yadan dawo ya kalleta yaga shi take kallo tai saurin yin kasa da kai,

Yayi murmushi yace"kanwata"

Tace"Yaya" a hankali,

Ya sakeyin murmushi yace"ya interview? "

Tace"very simple"

Yayi murmushi yace"yayi kyau"

Suna isa gida yayi parking ta bude ta fita,yana cikin motar yabi bayanta da kallo yana kara ganin yarintarta ya juya yakoma aiki,

Gidansu mansura mama na cike tamm tanajin haushi karfe daya saura Sega shi yara na shigowa da kayan abinci kwalaye katan_katan da buhunna,

Ranta yayi sanyi tanata washe baki har aka gama shigo dasu dan me wayon ciki ya damka mata bandir din 1k inji thermocool,

Mama ta amsa tanata murna tace"kuce angode angode sosai"

Tafara kilgen kayan buhu biyu na shinkafa jarkokin mai na ja da kwanti,2cartoon of indomie,pasta macaroni,pasta supergetti,cuos_cuos ga 100k dinta a hannu,

Tace"alhamdulillah mahakurci mawadaci mansura mansura fito kigani"

Mansura ta fito daga daki ganin uwayen kaya yasa ta bata fuska ta kalli mama da alamun tausayi fuskarta tace"mama yasa nifa fara ce kuma kingani ba ita bace"

Mama tace"shi ya fadamiki farinki yakeso?kiyi hankali wlh yanzu so kike kice de baki sonshi"

Tai saurin girgiza kai tace"aa wlh mama nima inason nai auren amma baa wannan halin ba sena koma ainihin color tawa sannan "

Mama tace"se akace miki gobe zaa dauramuku aure dashi ko?"

Mansura tai shiru,

Mama tace"kede kksani idan ya kufcemiki sekita zama gidan"

Mansura ta juya ta koma daki tai zaune tabuga tagumi cikin ranta tai shawarar daya kara dawowa zata fadamai itafa baka ce ba fara ba,

Gabadaya angama hada lefen Khalil akwati set daya kayan gani nafada yau aka kaisu gidan madaurin auren jameela bayan an kaisunne abbanta yasan ankaisu ko kadan baiji dadi ba sede ba yadda zaai a meda don karsuyi tunanin wani abu dole yayi shiru ba don haka yaso ba,

Khalil yana kagare da ranar aurenshi shiri kawai sukeyi da friends nashi,

Da rana ya dawo cin abinci yana cikin ci hjy tace"Khalil ya kamata kaje kazabi gidan daya dace Ku zauna idan yana bukatar gyara a kara gyarashi kafin suzo Jere"

Tunda tafara magana ya tsaya da cin abincin a hankali yace"ai hjy na zagaya banga Wanda yayi min ba shiyasa ma na siyar da biyu na siye wani babba me kyau"

Hjy nata kallonshi tace"yanzu kai Khalil har seka seda gida batare da shawara dani ba?ka kyauta kenan?"

Yace"kiyi hakuri hjy mantawa ma nayi shiyasa ban fadamiki ba"

Ranta bace tace"toyayi kyau Allah yabada zaman lpy"ta tashi tabar falon nata,

Ya kalleta ya cigaba da cin abincin shi kurum,

Dandanan friends na fahad sukaji labarin zai auri mata biyu kowa kiranshi yake yana mishi shakiyanci shi ko murmushi ne kawai nashi ,

Faseelat ko duk jinta take marar lpy duk wani dokin da take taji tadena yinshi,

Bayan fahad ya koma gida yayi lunch ya wuce part dinshi ya watsa ruwa ya kwanta don ya huta amma bacci yayi kasa ko sama sautin kukan faseelat kawai ne ke yawo a brain dinshi,

Da marece ya sake wanka ya sauya dress ya nufi gidansu ,

Tafito fuskarta jawur ta kumbura muryarta harta shake ta bude motar shi ta shiga,

Yanata kallon fuskarta yace"Queen I'm sorry "

Ta kalleshi ta kakaro murmushi tace"sorry for what?"

Yace"for everything "

Ta sakeyin gajeren murmushi tace"bakayi komi ba kazomin ban kwana ne?"

Ya daga mata kai,

Tai karamin murmushi again tace"naji dadi"muryarta bata fita,

Ya lumshe ido ya bude yace"I'm really sorry ki kara hakuri "

Ta daga kai ,

Ya dauko ATM dinshi cos yana da different accounts a banks ya mika mata na FCMb kudin sunfi 50millions a ciki ,

Ta kalli ATM din ta amsa ta rike shi tana jujjuyawa,

Ya sauke ajiyar zuciya yace"kuyi duk hidimarku kafin na dawo"

Tai karamin murmushi tace"nagode "amma batada niyyar taba sisinshi,

Yace" 1436 is the pin ki kulamin da kanki "

Ta kalleshi ya mata yes da ido yace"banaso kina damun kanki promise me bazaki karayin kuka ba "

Ta matse lips tana dan murmushi ta juya kai,

Yace"plss mana "ya langwabe kai,

Ta girgiza kai tace " zaiyi wuya but I will try"

Yayi shiru suka dan kara fira jefi_jefi ya tafi,

Ta koma gida ta ajiye ATM din ta wuce toilet wanka ta fito ta dan shirya ta nufi gidan besty dinta ,


Fahad na komawa gida yasamu aysha zaune a falo bakowa se ita tana kallo,

Tanajin motsi ta tashi zata gudu tana tunanin marwan ne,

Ya riko hannunta tai saurin juyowa don harta haddace laushin hannunsa sukai four eyes ,

Ya sakarmata hannu ya daga mata gira yace"ina zakije ?"

Ta sunkuyar da kai tace"sannu da zuwa Yaya"

Yace"yawwa koma kiyi kallonki"

Ta koma ta zauna shima ya zauna kujerar dake gefen tata ya kurawa TV ido da take kallon Indian film love story khushi,

Bangaren alhaji yanata samun sauki ita kuwa hjy abida sama_sama take,

Wanshekare tunda asuba ya kira faseelat ,

Ta dauka da bacci idonta tace"ina kwana?"

Yace"hope kintashi lpy?"

Tace"eh yanzu nake niyyar kiran ka"

Yace"noo na hutar dake"

Sukai shiru can murya very slow tace"zanyi missing dinka"

Yace"me too "

Tace"Allah ya kiyaye seka dawo"

Yace"amin zamuyi waya"

Tace "OK bye "

Yace"bye"ya kashe kiran,

Da shirin shi ya nufi part din mommy shima daddy harya shirya suna breakfast aysha tafito tana sanye da pitted gown sede bata wani matseta ba don bata da jiki,ya kalleta ya dauke ido tayi masa kyau sosai,

Tazo ta zauna ta gaidasu tana satar kallonshi,

Mommy da kanta ta zuba mata nata tafara ci a sannu,

Su mommy nagamawa sukabar wurin,

Aysha ta dan kalli fahad ta meda idonta akan plate tace"good morning"

Ya dago daga kallon plate ya kureta da kallo ,

Ta dan dago ido suka hada ido tai murmushi ta meda idon kasa,

Yayi murmushi koda bata fada ba yana hango irin son da take mai yace"ya kk?"

Tace"fine"

Yace"zamu tafi kasarku wane sako zakibawa su Umma?"

Tai dariya ta kalleshi tace"bakomai ina de missing dinsu"

Yace"really ?"ta jinjina kai,

Yace"to ko zamu tafi tare?"

Ta girgiza kai tace "inason zama da mommy"

Yayi dogon murmushi yace"kanwata kenan"daga cin abinci suka rika fira ,

Seda daddy ya fito sannan ya tashi suka fita har parking aysha tabishi tana tsaye har motarsu ta tashi yanata kallonta ,

Mommy ta kamo aysha suka koma ciki,su kuwa su fahad gidan yayan daddy da kanenshi sukaje suka daukesu suka wuce airport karfe 10 suka nufi Niger,

Bayan sun isa suka hau motocin da sukaje daukarsu suka karasa masarautar su aysha tarba ta musamman aka musu su daddy sun kara ganin girman mutanen sannan suka tafi wurin neman aurenta a mutunce akasa ranar daurin aure ran asabar da karfe 11am bayan sun biya kudade da kayayyaki masu tarin yawa,

Fahad na samun sarari ya kira faseelat ta dauka tanata jin kishi sukai waya sukai sallama batasan ita me kishi bace se yanzu da tasan zaai mata kishiya ,

Da marece likiss fahad zai wuce wani shago yaga sarka me kyau rumtse ido kawai yayi ya hangota yadda zatai kyau a wuyan faseelat ya tsaya ya saimata harze tafi seyaji wani iri ,sarkoki ne birjik a gun yanata kallo ya hango wata ya daukarwa aysha ita yabiya kudin ya tafi,

Sunso su dawo wanshekare don sungama komi amma ba jirgi da wuri se asuba hakan yasa se sunkai alhamis zasu isa Nigeria,

Ranar laraba aka sallamo alhaji daga asibity domin jikinshi dasauki sosai,

Yana bude wayarshi faseelat yafara kira ta dauka muryarta bawalwala tace "dear na kira so many times akashe inafatan kana lpy?saura kiriss na taho gidan"

Yayi murmushi yace"ban lpy ne amma naji sauki"

Tai shiru tanajin tausayinshi tace"sannu dear Allah yakara maka lpy "

Yace"amin gobe inanan zanzo "

Tace"ina duban hanyarka"

Yakashe kiran yana kashewa yayi waya yanason set daya na kayan daki with everything na 3millions kuma purple and white best color na faseelat suka gama magana akan zaa kawomai yabasu address ya kuma tura musu kudinsu,

Sannan yayi waya akan motar daya siya mata ko taiso akafadamai ta iso yau yace akawo mai ita gobe

Shi ko thermocool be kara zuwa gidansu mansura ba domin yasa amishi bincike kanta da iyayenta,

Babanta ko yayi mamakin kudin da kayan shiyasa suka ki taba kudin amma abincin tuni suka fara cinshi itako mansura takagara ya dawo tafadamai gaskiya bleaching takeyi,

Faseelat ko gyaran kanta take sosai while aysha kuma mommy ta tura ta gidan friend dinta domin tai mata gyara na musamman,


Gab asuba jirginsu fahad ya taso zuwa Nigeria,

A gidan alhaji nura ko jiya girkin hjy Rukayya ne abida na dakinta jiya ko kadan batai bacci ba amai da masassara kawai take,

Tunda bata gane meke damunta ba se jiyan da tafara amai tun asuban jamil ya kira don yasan batajin dadin jikinta wannan nema yasa benemi su hadu ba amma a kagare yake yakarajinshi a cikinta ,

Ya kira tana can tana amai harta tsinke,ba numfasawa yakara kira tadawo tana nishi ta dauka,

Jin nishinta hankalinshi yadan tashi yace"abida jikinne ?sannu _sannu"

Tana meda numfashi tace"jamil ban lpy sosai alamu duk sun nuna ciki ne a jikina"

Ya daga gira yana farin ciki yace"im happy sannu sugar Allah yabaki lpy ya raba lpy"

Tai tsit tana jinshi tace"jamil cikin jikina naka ne fa"

Yana murna yace" to miye ?keda kike da miji"

Ta yamutsa fuska tace"ni rabo na da alhaji tun last month wata daya da kwanaki ma"

Yace"to miye?"

Ta yamutsa fuska tace"Nide gaskiya zanje a zubar dashi
[12/13, 3:59 PM] SHALELE: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



3⃣3⃣



*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace Wanda ze shiga kasuwa se yace LA'ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LASHARIKALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU YUHYI WA YUMITU WAHUWA HAYYUN LA YUMITU BIYADIHIL KHAIR WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR ,zaa rubuta masa lada million a kankare masa zunubi million a daga darajarsa sau million kuma zaa gina masa gida acikin aljanna*



*HASSANA DAN LARABAWA my kawalli romon jaba🤣wannan shafin nakine kawalli ina matukar jinki cikin raina Allah yabar soyayya yakamata afara mana new book hakanan gaskiya*





Saboda wlh idan ina tuna ba cikin alhaji bane jikina kunyar kaina nakeji ina kuma tausayin abinda zan haifa "

Ran jamil bace yace"halan wani zaisan banashi bane in bake kk fada ba ?sannan kinfison alhajin a kaina kenan?to yayi kyau kije ki zubar karki manta labarin budurwata Zulaihat dana baki a wurin zubar da ciki ta rasu idan kuma zubarwar zakiyi se kije ki zubar"difff yakashe kiran ,

Hjy abida ta tsaya tana tunani yanzu nan seta haifi shege kode zubarwa zataje tayi?maganar jamil ta fado mata to idan ta mutu yanzu mezata tarar a lahira? Batasan time da hawaye suka zubomata ba tai saurin kiran jamil hartai ring ta tsinke be daukaba ta sake kira ya dauka yace"lpy?"

Abida na hawaye tace"bazan zubar din ba amma ni inajin tsoro kar alhaji ya gane"

Jamil yace"baze gane ba daya dawo kunyi sex?"

Tace"aa"

Yace"ok duk yadda zaai kiyi yau yayi sex dake kuma kiyi kokari karki bari kowa yagane kina da ciki se nanda two weeks kinga inkin haihu a 9 month ne ba two weeks kuma hakan baze kawo zargi ba"

Tai shiru sannan tace"ban lpy sosai da wuya hjy Rukayya bata ganeba shima yanzu da yaga ban lpyar zai matsa seya kira family doctor ya dubani "takare kamar zatai kuka,

Jamil yayi tsoki sannan yace" abida kiyi yadda nace sannan ki nemi fita unguwa kije kiga likita yabaki maganin daze temaka miki kinaji?sannan ita hjy Rukayya tasan last sex din ki da mijinki ne? Be smart mana kidena barnar hawayenki just do as i said inasonki abida inason duk wani abu daya fito daga gunki kiyi hakuri ki haifamin abinda ke cikinki ina sonshi plssss"

Murya sanyaye Tace"to"

Yayi murmushi yace"yawwa my sugar kitashi ki shirya kije kiga likitan kifada masa duk yadda kikeji kinjiko?"

Tace"eh"

Yace"thank u my sugar Allah yabaki lpy love u muah!!!" ya jefa mata kiss,

Tai karamin murmushi yace"bye"

Takashe kiran ta kara zama tana ta tunani sannan ta tashi ta koma toilet tai wanka ta fito ta shirya ta nufi dakin alhaji,

Shima yana shiri don tafiya wurin faseelat tashigo dakin,

Ya kalleta tana cikin shiri yace"abida ina zakije haka?"

Tai karamin murmushi tace"gida zanje bazan jima ba ko 3hrs bazanyi ba zan dawo "

Yace"OK sekin dawo amma meke damunki ne ?naga idonki kamar ya danyi ja sannan duk jikinki yayi sanyi ko haryanzu ciwon kan ne?"

Tai yake tace"naji sauki kuwa alhaji ni lpyta lau se na dawo"

Yace"kinyi breakfast ne?"

Tai murmushi tace"innaje can zanyi "

Yace"OK"

Ta juya ta sauka kasa ta samu hjy Rukayya na shirya dining tace"aa ina zakije tunda safe haka?"

Abida tace"gida ake nemana amma zuwa karfe 11 insha Allah zan dawo"

Hjy Rukayya tace"to Allah yasa lpy ki gaida su maman"

Hjy abida tace"zasuji"tafita tashiga mota sai asibity,

Da yake prvt ce tana zuwa ta siya kati tashiga ganin likita,

Ba bata lokaci tafadawa likita duk yadda takeji dukda haka aka tura ta awo,

Tai blood test dana fitsari ta zauna jira bayan sun fito likita ya kirata ya fada mata tana da ciki na sati biyu tai masa complain akan fever da headache da amai da takeyi ya rubuta mata magunguna sannan ta fito ta nufi gidansu kafin ta isa ta tsaya bakin wani babban pharmacy wani saurayi ne aciki ba kunya tace tanason desire pills ya kuwa siyar mata da wasu guda hudu akan 5k ta siye ta wuce gidansu don ta karasa lokacinta acan,

Alhaji nura bayan yagama breakfast ya fito yana fitowa aka kawo sabuwar motar faseelat,

Ya kira driver yace masa zai kirasa yaje ya daukesa sannan ya shiga mota ya nufi gidansu faseelat

Faseelat ta gama shiri kenan zasu tafi wurin saloon kiran alhaji ya shigo ,

Ta dauka da murmushi tace"my dear kazo?"

Yace"ina kofar gida my dear"

Tace"OK ganinan fitowa ta kalli bestyn ta tace"my alhaji bari naje"tatashi ta yafa gyale ta fita,

Tana fita alhaji nura ya kafeta da ido tana sanye cikin riga da sket atamfa orange da milk ta yafa milk gyale sosai tayi kyau sede tuni ya hango ramar datayi Wanda bakomai ne yasa ta rama ba se tunanin kishiyarta da yadda zasu zauna,

Tana ta murmushi ta bude motar ta shigo ta zuba mai ido duk ya rame,

Tace"sannu dear ya jikinka?"

Yace"naji sauki dear"

Ta matse lips tace"kayi hakuri "

Yayi murmushi me ciwo yace"bakomi"

Suka danyi shiru kowa nata magana da ranshi cikin ranta haushin kanta takeji da tabiyewa son zuciya bata auri alhaji ba yana mata son gaskiya so me tsananin gaske,

Shi yakatseta yana murmushi yace"my dear ga motar ki na kawomiki"

Tace"dear wannan motar tawa ce?"

Ya daga mata kai yace"tun ina Cotonou na siyeta da sunanki jiya ta iso Nigeria shiyasa na kawo miki ita"

Faseelat ta zaro ido ta bude ido sosai tana kallon haduwar cikin motar kuma tunda ta fito taga yadda motar ke sheki ,

Tana murna tace"nagode dear nagode bansan irin yadda zan misalta maka ba naji dadi sosai I love u so much "

Ya kafeta da ido yana kallonta yayi murmushi jin tace I love u sosai yaji dadi shide yanason farin cikinta yanaso ya ganta cikin walwala ya dauki wayarshi yayi mata transfer na 5million's ,tana ta murna taji alert na shigowa ,

Tana dubawa taga million 5 from him tai saurin dagowa ta kalleshi yanata murmushi yace"my gift "

Ta cigaba da kallon shi tana tunani anya tayiwa kanta adalci da bazata auri alhaji ba ?a duniyar nan waye zai sota fiye da yadda yakeyi batasan time da hawaye suka gangaromata ba na haushin kanta da biyewa son rai ,

Ganin hawaye idonta alhaji yace"dear plss don't kada ki batamin hawayenki "

Hawayen na kara zubowa ta dukar da kai ta matse lips saboda kukan da yakeson kufcemata tana ta ajiyar zuciya,

Alhaji nura ya bata fuska yace"banaso plss kokinaso hankalina ya tashi ne kiyi hakuri "

Tasa hannu ta goge hawayen ta dago ta kalleshi tace"dear dukda bazaka aureni ba har yanzu kana sona? Har yanzu zaka iyamin kyauta?"

Ya girgizakai baijin dadin hawayenta yace"dear ke nakeso koda bazan aureki ba sonki na nan kuma haryanzu zan iya mallaka miki komi dake gareni ina sonki sosai dear"

Tace" nima inasonka" tana sake zubda hawaye,

A duk ganinshi da tunaninshi auren dole zaai mata shidinne zabinta besan time da hawaye suka zubomai ba na tausayin kansu da kuma na tunanin maybe daga yau shi daita har abada,

Ganin yana hawaye yasa ta kara dukar da kai tana cigaba da zubar da nata,


Karfe 10 jirginsu fahad ya sauka Nigeria ba tsayawa suka nufi gida,

Suna shiga falo sukaga akwatuna set 6 jere ringis a tsakar falon duk suka tsaya suna kallo,

Mommy ta sauko tana farin ciki tace"oyoyo oyoyo sannunku da zuwa"

Daddy yaje zai zauna yace"Wadannan fa?"

Mommy tai murmushi tace"kawata naima waya ta hadominsu from dubai"

Fahad ya zauna a seat yana cigaba da kallon kayan akwatina masu tsada ,

Daddy yace"sunyi kyau sosai kuwa"

Mommy tace"ai aysha ta cancanci fiye dasu"ta kalli fahad tai murmushi,

Daddy yace"gaskiya iyayenta masu mutunci da karamci ne sun karramamu sun karbemu hannu bibiyu"

Mommy tace"ai Allah de ya saka masu da alheri Nide banda kamarsu sunmin komi a rayuwa"

Daddy ya cigaba da bata labarin abinda ya faru a can,

Fahad ko hankalinshi na wurin faseelat sosai yakeson ganin ta,

Suna labari mommy tace"son munyi waya gobe zaazo yiwa aysha Jere awane gida zata zauna?"

A hankali yace"mommy inason na ajiyesu gida daya already anyiwa faseelat jere asama se aiwa aysha a downstairs "

Mommy tace"baka ganin akwai matsala meze hana kowa ya zauna gidansa daban? Itafa aysha nada matsalar aljanu kasani kuma duk idan ranta ya baci suna tasowa hakanan ma suna tashi wani lokaci"

Daddy yayi saurin cewa"tunda ma bata lpy yakamata ace tana tare da wani cikin gida saboda lalurarta"

Mommy tace"ai se a Samar mata yan aiki ni nafiso kowa da gidansa"

Daddy yace"tunda shi zabinshi ya hadesu ki barshi a hakan"

Fahad yace"mommy faseelat batada matsala itama zasu zauna lpy"

Tace"to"badon taso ba

Fahad ya tashi zai fita,

Mommy ta kalleshi tace"ina zuwa son? Katsaya kayi breakfast "

Yayi murmushi yace"mommy yanzu zan dawo"

Tace"OK kai sauri plss kazo kaci abinci "

Yace"to"da dan murmushi fuskarshi ya fita,

Ba sake wanka bakomi ya shiga mota ya nufi gidansu faseelat,

Yana zuwa yaga mota fake a gaban gidan yayi parking bayanta ya ciro waya ya kira faseelat har tashiga se ya hangota cikin motar alhaji ,

Yayi saurin katse kiran yanata kallonsu,

Su kuwa basu san dashi ba sunata rarrashin juna ,

Faseelat nata godiya ,

Ya kalleta badon yaso ba yace"zan tafi"

Tace"se yaushe ?"

Ya matse lips yace"maybe for ever "

Tai saurin girgizakai tace"plss kadawo muyi bankwana inason nakara ganinka plsss"

Yayi murmushi yace"to dear "amma ba dan zai kara dawowa dinba ,

Ta kara goge fuska tace" nagode sosai "

Ya kalleta yayi shiru,

Ya kira driver dinshi suna zaune fahad na bayansu duk jijiyoyin kanshi sun tashi driver yazo ,

Alhaji ya fita ya shiga suka wuce office,

Itako takoma seat din driver ta zare key din motan ta fito ta kulle ta duba baya mana se ganin motar fahad tayi,

Gabanta yayi mummunan faduwa fuskarta bawalwala taje tashiga motar ko kamshin amare da fahad yaji tanayi ya kara bata masa rai ya zuba mata ido,

Ta sunkuyar da kai ta na wasa da key din hannunta,

Cikin bacin rai yace"waye wannan?me kkyi a motar shi for all most 1hr ?"

Tai shiru batace komi ba,

Yace"wannan bashine naganki kinfito daga gidanshi ba ?kkce kawarki kikaje gani meyakawoshi anan?sannan wannan motar daya bari ta wacece? "

Ta dago tana kallonshi tanajin mugun haushinshi se wani fada yake tace"tsohon saurayina ne"a takaice takuma meda kai kasa saboda kallon da yake mata,

Yaji maganar kamar sukar mashi ya karkata kunne yace"faseelat kina da hankali kuwa ? Yau saura kwana biyu bikinki kina kula samari?"

Tai shiru kanta still kasa,

Ranshi na kara baci yace"wannan motar fa?"zuciyarshi na raya masa abubuwa,

Batare data dagoba tace"kyauta yabani"

Da zafin rai fahad yace"bullshit saboda me zai baki mota kyauta?a kanme zai dauki wannan motar yabaki ?"

Faseelat ta dago ranta bace tace"dakata plss me kake nufi ?kana nufin lalata mukayi yabani motar ko me?"

Ran fahad bace yace"eh that's what I mean mikomin wayarki kuma sekin mayar masa da motarsa"ya mika mata hannu ,

Ta kureshi da ido tanajin haushi yama zaai tabashi wayar ta yaga messages na love da sukeyi da alhaji,

Fuskarta hade tace"fahad ni kakewa kallon mazinaciya?"

Yaja tsoki yace" I said give me ur phone "a tsawace,

Cikin ranta mamaki take yadda yake bata order tanabi yanzu kuma har ya rika zarginta a hasale tace" bazan bada ba saboda kaga inasonka shiyasa kake wulakantani kace bakason aiki na amince don kawai kaji dadi haryau banfadawa kowa nabar aiki ba don kar a rabamu kadawo kace mu biyu zaka aura na hakura da hakan yanzu kuma kallon yariska ma kakemin to bazan bada wayar tawa ba kuma wlh sena hau motar can sede in mutuwa nayi idan kaga dama kafasa auren nawa seme bafa kai kadai gareni ba na zabeka ne kawai saboda ina sonka"

Tunda tafara yake mata kallon mamaki jikinshi yayi lakwas zuciyarshi na ciwo yace"faseelat ni..ni kike fadawa magana?"

A fadace ido rufe tace"amfada din kanme zakarika kindayamin dokoki se kace kaina farau aure to wlh sena hau motar kuma koda ka aureni daita zaakaini" tana gama fada ta tura murfin motar da karfi ta fita dasauri ta shige gida ,

Fahad yabi bayanta da kallo yana cigaba da mamaki ashe ta iya masifa ya dafe kanshi ya rumtse ido kanshi kamar zai rabe,

Idonshi nata hangomai ita da alhaji a motor da ranar da taje gidanshi ta dade
[12/14, 8:08 AM] SHALELE: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



3⃣4⃣



*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace Wanda ya karanta karshen suratul hashri (lau an zalna hazal kur'an...zuwa karshen surar)da rana ko dare seya mutu a wannan ranar ko daren aljanna ta wajaba gareshi*




*pagyn besty ta sis Ikra Rukayyat🥰*




Gabadaya ya rasa me ke masa dadi ya kalli dan karamin akwati na sarka daya siya mata ranshi yakara baci ya tada mota yabar kofar gidan ya nufi gidan sabeer domin suje su cigaba da shirye_shiryen dinner da zasuyi gobe,

Faseelat nashiga gida tawuce daki bestyn ta tana kwance a bed tace"kindade harnagaji na kwanta "

Faseelat tai tsoki tace"ai da seki fita Ku gaisa" takara tsoki tace"waikinsan me?alhaji yakawomin mota sega fahad wai a dole sena mayar masa da motarsa kiji wani shirme?kinga motar kuwa?"

Rabia tace"ke dan Allah kawata to se kika ce masa me?"

Faseelat tace"na fada mai bazan mayar ba kuma ko gidansa da ita zaakaini waima fa zargina yake wai hakanan alhaji baze bani mota ba"

Rabia tai dariya tace "wlh kinmin dede haka kawai tunkan ya aureki se wani juyaki yake nifa wlh nafison ma alhaji ba wannan gungumin ba da ko faraa bayayi"

Faseelat ta harareta tana dan murmushi,

Rabia ta cigaba da cewa" Allah ko alhaji shine ya dace dake ba fahad ba daya fara sonki jiyannan ba"

Faseelat tace"hmm kinsan tsarin ubangiji haka Allah yaso "

Rabia tace"yanzu ya tafi knan?"

Faseelat tace"matsalarshi Nide nabaro masa motar na shigowa ta gida albishirinki da sabuwar motar zamu tafi saloon"

Suka kashe faseelat tace"ina zuwa"ta fita dasauri tashiga dakin Ummi,

Tana samunta tace"Ummi alhaji ya bani motor ya kuma bani kyautar 5million's"

Ummi tace"bawan Allah duk gudunsa da kkyi ai faseelat kinyi missing masoyi na gaskiya"

Faseelat tai shiru tana kara jin haushin kanta tace "Ummi haka Allah ya tsaro"

Ummi tace "kuma Allah ya saka mai da

Please Login or Register in order to submit comment