Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sona sosai nasan duk time da yasan na fito ba karamar murna zeyiba na barine har nanda wata ukku"

Rabia tace"time din kau haryamanta dake gaskiya "

Faseelat tace"hmmm kince accident towa yayi accident inason sani "

Rabia tace aikuwa ina da wata kawa nurses bari na kira ta naji ko ankawo masu accident yau"

Tana kira kawar tafada mata ansamu wasu da marece ma tafadi sunan marwan da Matar,

Faseelat na jin marwan tai saurin tashi zaune tana kallonta zuciyarta na tuno mata marwan da yake bata girma ta tuno that ranar daya shigo hankalinta tashe tace"dan Allah ki shirya gobe kizo ki rakani na ganosa"

Rabia tace"yo ina ruwanki?"

Faseelat tace"kawai banji dadi ba yaron na girmamani "

Rabia tace "Allah yakaimu ni budemin wayarki ma in tura wani abu"

Faseelat ta bude mata key ta mika mata,

Rabia ta fara bin contact har zuwa number dear no din alhaji nura ta kwashe ta dan tura pics sannan ta mika mata ta tashi tace"se goben da karfe nawa?"

Faseelat tace"da karfe 10am ko "

Rabia tace "to sai goben" ta fita

Faseelat ta cigaba da tunani karde marwan baya cikin natsuwarsa saboda abinda ya faru?

Marwan ko se karfe 10 na dare ya bude ido duk jikinshi na ciwo yafara nishi yana rike da zuciyarshi,

Mommy da daddy sukayi kanshi mommy na hawaye tana "sannu marwan me kema ciwo?"

Marwan yanata hawaye da nishi yana girgizakai saboda azaba,

Daddy ya kira likita yazo ya masa pain killer injection sannan ya rage jin ciwon da yakeji,

Mommy ta rike hannunshi tana hawaye tanata masa sannu ,

Marwan na hawaye yace"mommy natuba mommy nadena komi amma baban Hafset yace karna kara zuwa gunta dan Allah daddy kuntemakamin inasonta sosai wlh inna rasata zuciyata bugawa zatai"

Mommy ta kalli daddy ,daddy ma ya kalleta yace"kayi hakuri marwan insha Allah zan nemo maka aurenta"

Yana ta hawaye yace"daddy tana sona sosai itama dan Allah kubashi hakuri wlh nadena komi"

Daddy ya shafi sumar kanshi cikin rarrashi yace"ka kwantar da hankalinka ba Wanda zai rabaka da ita kayi hakuri "

Marwan yayi shiru ya lumshe ido yana tunanin maganganun babanta zuciyarshi na ciwo ,

Mommy da kanta kamar ya rabe don ciwo ta hada tea daddy ya bashi ya samu yadanyi two sip ya meda shi ya kwanta idanunshi rufe yana tuno likitar zuciyarshi.
Wan safe tun 9:30am rabia tazo gidansu faseelat,

Faseelat ta shirya ta fito ta shiga dakin Ummi,

Ummi na mata wani kallo kanta duke tace"Ummi dan Allah zanje ganin friend dita tayi accident" bataso tace marwan dan kar tace zataje dubashi,

Ummi tace"Allah ya kiyaye hanya"fuskarta bawalwala,

Faseelat ta tashi ta fita tana jin ciwon fushi da Ummi keyi daita bazeyiwu tafada mata abinda ya faru ba har fahad ya saketa ,

Ta koma suka fito da rabia suka nufi asibity bayan sun sayi fruits suna zuwa suka samu kawarta tai masu kwatancen daki suka nufi dakin,

Dede shiga dakin Sega fahad shima zai shiga fuskarshi hade yayi mata kallo daya ya dauke ido ,

Faseelat tai karamin murmushi tace"ina kwana ya me jiki?"

Ko kallonta be yiba ya bude kofa ya shiga dakin ya tsaya bakin bed yana kallon marwan,

Rabia ta harareta tace"kikace bakisan komawa?"

Faseelat tace"se naki masa ya mai jiki?"

Rabia tace"ni natsani daukar kai kina masa mgna ya wani shareki gani tsaye"

Faseelat tace"ke Nide mushiga mufito"ta tura kofar ta shiga rabia na bayanta suka shiga da sallama,

Mommy ta juyo tana kallon kofar ganin faseelat yasa ta kara daure fuska cos batason ta dawo gidan fahad dama can taga basu dace ba gani takeyi ma ta girmeshi,dukda haka tace"maraba da faseelat "

Faseelat ta karaso tana kallon marwan dake bacci da tausayi tace"mommy ya me jiki?"

Mommy tace"dasauki "

Faseelat tace"Allah yakara sauki yabashi lpy"

Mommy tace"ameen angode"

Rabia ma tai mata yame jiki,

Faseelat takara kallon fahad ya fiddo wayarsa yana latsawa fuskarshi daure,

Ta matse lips tace"mommy zamu koma Allah ya sawwake"

Mommy tace"amin nagode "

Suka nufi kofa,

Suna juyawa fahad dake latsar waya ya dan dago ido yana kallon bayanta shi kanshi besan dalilin kallon ba,

Mommy da suna juyawa ta kalleshi ganin idonsa na kansu yasa taji badadi cikin ranta tana fatan ba medota zaiyi ba ,

Su faseelat na fita rabia tace"naga ikon Allah shine ko mgna at least ya amsa gaisuwarki"

Faseelat tai karamin murmushi tace "naga Wanda ya fishi to miye nifa ba donshi nazo ba kawai naji inason zuwan"

Rabia ta kalleta tai shiru tausayi ma take bata ta rabu da me sonta sosai ta aureshi yanzu kuma ga abinda ya biyo baya sannan bata da tabbacin shi alhaji nuran ko yanasonta haryanzu,

saboda wasu mata na kuskure se suyi aure sunata dakon soyayyar wani se sun kashe auren sun fito su samu Wanda suka fito dominshi kuma yasamu wata ko yadena sonsu hakan na faruwa sosai as a friend tanaso ta temaka tanaso ta gane alhaji na son faseelat haryanzu ko kuwa yadena shiyasa ta kwashi number shi amfanin abotaka shine son gaskiya bawa juna kyakkyawar shawara temakon abokin in kanada hanya da kuma bashi kariya in kasamu damar yin hakan,

Da daddare kusan 8:30pm ahalin gidan alhaji nura sunyi dinner suna kallo wasu na wasa yayinda yake zaune yana kallon su ga boy zaune kan cinyarshi,

Kamar daga sama yaji wayarshi na ring ya dauka number ba suna kamar karya dauka ya dauka ya kara a kunne,

Rabia tace"ina wuni?"cikin siririyar murya,

Yace"lpy"in brief

Tace"amm nasan baka ganeni ba rabia ce kawar faseelat "

Jin ta ambaci faseelat yasa yakara dafe wayar a kunne he don't want to miss single word akan abinda ya shafeta,

Yace"ina saurarenki "

Tace"inason muyi mgna da kai amma inaso muhadu"

Alhaji nura yace"OK a ina?"

Tace"Inba damuwa kafadamin inda zan sameka"

Yace"I don't have time sosai kifadamin kawai ina zan sameki"

Rabia tace"aa in ba damuwa kazo kofar gidanmu gobe da karfe 5pm"

Yace"rabia I can't wait for that time yamin tsawo sosai zanzo da safe kamar karfe 10 ai is OK?"

Tai murmushi tace"to shikenan sekazo"

Yakashe kiran hjy abida da cikinta ya girma tana gefe tana masa wani kallo jin ya ambaci rabia ,

Yayi mata murmushi yabi wayar da kallo kamar ya jawo goben ta zama yau yanason sanin menene akan dear dinshi,

Rabia ko yana kashewa tai murmushi tace"zade mugani"

Wanshekare tun karfe 9:55 alhaji ke kofar gidan cikin motarshi tare da driver ,

Rabia ta fito tana dan karamin murmushi ya bude motar ya fito ,

Ta gaidashi kanta kasa ya amsa yanata kallonta yace"lpy de kike nemana?"

Tai murmushi tace"albishir ne nakeso nai maka"

Yace"inajinki"

Ta dago tana kallon idonshi tace"kusan one month kenan da mutuwar auren faseelat "

Zuciyarshi tai mummunar faduwa saboda dadi besan time da yace "what!!!!?" Idanunshi warwaje da kaganshi kasan yana cikin farinciki,

Tace"eh nasan bakasani ba shine naso in maka albishir nasan zakaji dadi sosai saboda nasan irin soyayyar da kakemata"

Alhaji nura yana murmushi ya shafi heart dinshi yanajin sanyi batare dayasan time da yayi hakan ba

Cikin tsantsar farinciki yana meda numfashi yace"rabia kintaba zuwa saudiyya?"

Rabia ta girgizakai,

Yace"to ki shirya insha Allah this year zakije saudiyya"

Rabia tai yar dariya tana kallonshi tace "nagode sosai amma ni kawai inason kasani ne tunda ita bazata fadaba"

Ya jinjina kai da gamsuwa yace"wannan tukwicin albishir da kika bani ne ban taba samun albishir kamarshi ba tunda nake a rayuwa"

Hannunshi dafe da heart yace"faseelat is my heart itace kowane bugun numfashi na"

Rabia tace"Allah de yakaimu musha biki"

Yayi murmushin jindadi yace "plsss kituromin AC no dinki plsss karki manta nagode sosai "

Tace"to nima nagode sosai Allah yabarka da faseelat "

Yace"ameen ameen" yana washewa ya buda mota ya shiga driver yaja,

Rabia memakon tai gida ta nufi gidan su faseelat tana ta farinciki,

Alhaji na cikin mota se sakin murmushi yake yana kallon titi love moments dinsa da faseelat yana dawo masa kalamanta murmushinta and every thing yakara fadada fuskarshi ya saki dogon numfashi yana hamdala ga Allah ,

Rabia nashiga gidansu faseelat ta leka ta gaida mommy tashiga dakin faseelat,

Faseelat na zaune tana kallo tana guga rabiar tashigo tana murmushi tace"dear guga kike"

Faseelat tai murmushi tace"dear dinshi ba"

Rabia ta zauna ta na murmushi tace"munyi waya da alhaji"

Faseelat tai mata banzan kallo tace"meya hadaki da no din alhajina?"

Rabia tai dariya tace"wai alhajinki yanzu ma yabar kofar gidan mu"

Faseelat ta ajiye gugar tana murmushi tace"barauniyar saurayi ko sata har cikin gida "

Rabia tai murmushi tace"nakasa hakuri ne harse nanda months na kirashi nabashi albishir kinsan me?hajjin bana da rabiatu ciki"

Faseelat ta fiddo ido ta na sakin murmushi tace"dan Allah?"

Rabia na faraa tace" wlh faseelat kina da masoyi alhaji na mugun sonki sosai da sosai fiyeda duk yadda zaki hango daga fadamai fa yace in shirya zuwa hajji kuma yace in tura mishi AC "

Faseelat ta lumshe ido tabude tanajin dadi tace "kintura de ko?"

Ta girgizakai tace"farinciki be barni ba na kwaso nazo fadamiki kinga yadda yake murmushi kai Allah ameen"

Faseelat tai dariya sannan ta runtse ido tace"nasan alhaji na sosai yanamin son da tunani bazai iya kayyadewa ba shiyasa nakeson karasa rayuwata dashi da dadi ko badadi inasonshi a hakan"

Rabia tace "bari kiga natura mai AC din" ta janyo waya ta tura,

Alhaji na office message yashigo ya duba yaga no din rabiar da yayi saving bazai taba mantawa daita ba saboda ta temaki rayuwarshi kafin nan da 2months ai wuyane amma gashi tasaka yaji saukin duk ciwukansa yanajinshi fresh bakomai cikin brain dinshi se soyayya,

Yana murmushi ya turawa rabia 200k

Rabia na jin alert ta bude ganin 200k bawai 20k ba yasata ware ido ta na murna tace",wlh nazama hjy 200k a account dina"

Faseelat ta kara jin mugun farinciki tace"wlh rabia kin kara samun wuri a zuciya ta naji dadin hakan sosai baccin kar dadin ya miki yawa dana baki kyautata"

Rabia tai dariya tace"banaso kirike abunki"tai dialing no din alhaji ya dauka ,

Ta na murmushi tace"alhaji kacikani da alheri nagode nagode sosai Allah yakara yawan arziki da tsawon rai"

Yace"ameen ya faseelat dita tana lpy de ko?"

Rabia tace "lpyarta lau tana jiran lokaci"

Yace",to alhamdulillah nagode sosai ki kulamin daita"yakashe kiran,

Rabia na murna ta kalli faseelat tace" Allah yakaimu ran aure kinsan ranar dole mu juya sosai"

faseelat tace"sosai"tana murmushi

Rabia ta harareta tana murmushi tace"natafi "ta tashi ta fita,

Faseelat ta jingina da bango ta lumshe ido tana tuno kulawar alhaji akanta abun yana tsumata .
[1/24, 9:17 PM] SHALELE😍: 68


Bayan kwana biyu

Liman nata zuba ido yaga marwan masjid amma shiru babushi ba labarinshi bai zuwa salla bare daukar karatu,

Cikin ranshi yaji tsoron karde ya koma halinsa na bayane da kuwa beji dadi ba cikin ransa yasa da angama sallar laasar zaije gidansu domin dubashi,

Bayan anyi laasar liman na addua yaga daddy na salla da alamu besamu dukkan rakaoi ba,

Ya zauna jiranshi yaji lpy marwan shiru domin tare suke zuwa masjid wani time,

Daddy na sallame salla yayi addua ya tashi da niyyar fita,

Liman ya taso ya biyoshi yana niyyar shiga mota liman ya mai sallama,

Ya amsa yana kallonshi ,

Liman yace"marwan shiru kwana biyu baizo masallaci ba Allah yasa lpy"

Daddy yace"Allah sarki marwan yayi accident ne yana asibity amma yana samun sauki"

Liman yayi salati yafara addua "Allah yabashi lpy yasa kaffarane "

Daddy yace"ameen mungode sosai "

Liman yace"wane asibity yake kwance?"

Daddy yace "Malam aminu yanzu ma can zan nufa"

Liman yace"to ba matsala muje na duboshi"suka shiga mota suka nufi asibitin,

Bayan sun isa suka shiga dakin marwan na kwance kullum hannunshi dafe da zuciya yana cikin matsanancin damuwa,

Liman ya karaso ya zauna yace masa"marwan ya jiki?"

Marwan ya kalli liman idanunshi cike da hawaye yace"dasauki "

Liman yace "Allah yabaka lpy sannu Allah yasa kaffarar zunubaine"

Zuciyar marwan na zafi yace"dama kafadamin tunnan duniya Allah yake farawa mutum ukuba"

Liman yace"subhanallahi marwan aika tuba kuma Allah gafurur rahimune sede yakan iya jarabtarka yaga irin tubar da kayi ya kuma gwada imaninka"

Hawaye suka zubowa marwan yace"I totally change my life duk da na tuba mutane bazasu manta laifukan dana yi a baya ba"

Liman ya kalli daddy da keta kallon marwan ya meda kallo gun marwan din yace"idan wasu basu mance ba wasu zasu manta kuma dabiunka masu kyau su zasu shafe na bayan"

Marwan yace"inason na aureta amma babanta yace kada yakara ganina gunta bansan yadda zanyi da zuciya ta ba inasonta sosai "

Liman yace"wacece?"

Marwan yace"Hafset "yayi kwatancen mahaifinta,

Liman yayi shiru can zuwa yace" ka kara hakuri kuma ka dauki kaddara wani abun kanasonshi ba alheri bane se Allah ya hanaka shi wani kuma alheri ne amma ba rabonka bane kayi hakuri "

Marwan ya juyar da fuska ya cigaba da hawaye,

Liman ya kalli daddy yace"Allah yabashi lpy "

Daddy yace "ameen"

Liman ya juya ya fita bai nufi gida ba ya nufi unguwarsu Hafset da kwatance yagane gidan kasancewar marece ne yayi saa ya sameshi yayi sallama dashi,

Baban Hafset ya fito yanata kallonshi ganin bai ganeshi ba sukayi musabaha liman ya gabatar da kansa a matsayin limami ,

Baba yayi maraba da shi yana tambayar Allah yasa lpy,

Liman yace"akwai wani yaro dake daukar karatu wurina hakika yayi gurbatacciyar rayuwa a can baya amma yanzu yayi nadama ya tuba yanata kokarin gyara rayuwarshi,kwana biyu banganshi masallaci ba na tambayeshi ake shedamin yayi accident danaje dubashi yake fadamin ya samu wacce yakeso ya aura amma baka amince ba "

Baba yace"gaskiya ne"

Liman yace "nazo tunatarwane domin kai musulmine kasan kaddara yaron ya tuba yana nadamar baya be kamata kaki yadda dashi ba saboda Allah ma da yama laifi muna kyautata zaton ya yafemishi idan irinsu sun tuba duk da haka ana nuna masu kiyayya ana gudunsu yawanci bazasu ji shaawar tubar ba wasu kuma zasu koma halin baya dan Allah inarokon alfarma kayi hakuri kabashi diyarka tunda aurenta yakeso yayi kuma kasan kabawa yarka tarbiyya zata temaka mishi wurin gyara rayuwarshi zaka samu lada itama zata samu dade bai shiryuba da koni bazan bada shawarar bashi itaba saboda zai iya lalata tarbiyarta ko kuma ita tasamu nasarar gyarashi amma dukda haka akwai hatsari bawa yarka dan shaye_shaye ,tunda ya tuba Ku temaka kubashi don neman dawwamar natsuwarsa yaro ne sosai amma iyayensa sun hakura zasuyi masa auren don duk ya kara natsuwa"

Baba yayi shiru yanata sauraren liman jin ya dasa aya yace"nagode sosai insha Allah zanyi shawara "

Liman yace"karkabiyewa mutane so da dama in zaka biyewa mutane bazaka taba aikin alheri ba don Allah a daure a bashi tunda yana sonta sosai meyiwuwa ko sanadin korarshi yasa yayi accident ma "

Baba yace"bakomi wane asibitine?"

Liman yafadamishi yanajin dadi jin ya tambayi asibity yayi godiya ya tafi,

Baban Hafset ya koma gida yayi shiru yana tunanin maganar liman tana kan hanyar dede idan ana waresu dukda sun tuba zasu iya komawa ko su shiga wani hali mawuyaci kuma kaima bakasan kalar rayuwar da yaranka zasu yiba ,

Maman Hafset ta shigo ta sameshi yayi zugum ta zauna tace"lpy alhaji?"

Yace"yaronnan dana kora yayi accident limamin unguwarsu yazo yimin nasiha saboda yaron ya tuba"

Mama tace"to ya kagani ne? Wlh Hafset kullum jugum take wani time kuma har kuka nakesamun tanayi tace duk yakashe wayoyinshi ko bankwana basuyi ba"

Baba yace" hatsari yayi ni duk jikina yayi sanyi saboda jin ya tuba amma kuma inatsoron surutun jamaa ko kuma shi yakoma kamar baya"

Mama tace"karkabi ta jamaa kuma kayi fatan alheri seyafaru"

Baba yace"to kode abashi itan? Amma ni fa ban yarda da zancen nan ba sede in turo iyayensa kawai zaiyi ai mgna"

Mama tace"duk abinda kace yayi yana da kyau kuma ka kara bincikawa sannan "

Baba yace"eh shiyasa nakeso Ku shirya muje asibitin ganoshi daganan kuma zanyiwa iyayenta maganar suma su kara bincikawa "

Mama tace"Allah yakaimu anjiman"

Bayan ishai Hafset na kwance tanata trying no din marwan kashe domin da sukayi accident wani yayi tashi ,

Sega mama ta kalleta tana murmushi tace"kitashi babanku zai kaimu asibity mugano marar lpy"

Tace"to "ta tashi ta saka hijab suka fita suka tsaya suka sai drinks sannan suka shiga asibitin,

Da kwatance suka gane dakin suka kwankwasa suka shiga ciki da Hafset da mama da babanta da kannenta su biyu,

Mommy da daddy da aysha suna dakin suka meda hankali Kansu,

Su baba suka karaso sukayi musu ya me jiki,

Itako Hafset tunda taga marwanne dadi ya kasheta tanata boye murmushi,

Marwan idanunshi kulle jin anata gaishe_gaishe yasa ya bude ido,

Wa zai gani Hafset da iyayenta ya yi wuf ya tashi zaune yana murmushi yace"doctor"

Kowa yayita kallonshi,

Hafset ta kara matsawa tace"patient ya jiki?"

Yayi murmushi be amsaba ya kalli mommy yana faraa yace"mommy ga Hafset Wadannan kuma iyayenta ne"

Mommy ta cigaba da sakin fuska tace"sannunku maraba"

Daddy suka kara gaisawa da babanta,

Da marwan da Hafset sunata sakarwa juna murmushi yace"my doctor "

Ta sunkuyar da kai tana jin kunya,

Fahad da aysha da keta kallonsu wai doctor da patient sukai dariya,

Sun danyi mintoci sannan suka fita su mommy duk suka tashi yi musu rakiya fahad ma yabi bayansu aysha na tsaye kowa ya fita banda Hafset,

Ta na sauri tace"ina wayarka?"murya kasa_kasa,

Shima yayi kasa_kasa da murya yace"I don't know"

Tai murmushi ta bude voice tace"Allah kasiye waya nagaji da missing dinka"ta juya dasauri ta fita,

Yayi dariya ya kalli aysha yace"anty tayi ko?"

Aysha tai karamin murmushi tace"sosai"

Yayi murmushi ya lumshe ido can zuwa Sega su mommy sun dawo daga yi musu rakiyar ,

Marwan nata murmushi yace"daddy ya kamata a sallameni naji sauki"

Daddy ya kalli mommy sukai dariya yace"kabari ka kara warwarewa ciwukan jikinka basu gama warkewa ba"

Yace"daddy zasu warke ko muna gida "yayita matsawa ,

Fahad sede yayi ta kallonshi ganin lokaci daya ya wartsake ,

Wan safe dole aka sallamesu suka koma gida,

Yayin da iyayen Hafset maza suka dada bincike sosai bayan marwan ya warke su daddy sukaje nema mishi auren Hafset aka bashi akasa rana nan da one month ,

Shiru faseelat tayi 2month amma fahad yaki ko leko kofar gidan,

Omer ne zaune shi da Ummi sunyi shiru ,

Ummi tace"kaga shiru yaki zuwa yaki aikowa"

Omer yace"shima yadena sonta din abinda yasa ban koma ba saboda nasan idan har yana sonta zaizo yanzu ma zamu cigaba da jira in baizo ba tagama idda shikenan tunda dama ta tura ankwaso mata kayan sawarta"

Ummi tace"banji dadi ba wlh banji dadin mutuwar auren nan ba"

Omer yace"Allah yasa hakane mafi alheri hakuri zamuyi"

Bangaren jameela kuwa da cikin ake cigaba da jindadi ba sauyin komi duk da bata zuwa koina saboda fitowarshi,

Khalil ko ya koma very silent tarbiyyar yaranshi kawai yake tunani,

Mansura ko ta na cigaba da rayuwarta sam ta dena damuwa da rashin aure tunda tasamu aka biya thermocool kudinshi shikenan hankalinta ya kwanta mama ko tasa mata ido,

Abida ma tana cigaba da holewa da jameel dinta dazaran tasamu ta fito yayi sex daita yaji dadi kuma tabiyashi kudin service da ya mata,

Yayin da alhaji nura ke lissafe yana jiran wata ukku subada baya,

Bikin su marwan ya taho su sameera yahya 😂sune kirjin biki sune best friend sunyi ankon material lace white da red shine zasu saka awurin dinner,

Su mommy anata hidimar biki saura sati daya aka kai lefen Hafset akwati goma sha biyu masu shegen kyau kuma daddy yabawa marwan sabon gida dazai tare da amaryarshi ga sabuwar mota dall da fahad yabashi don yaji dadin hidimar biki yakara zama dangata gabadaya kome yi masa akayi,

Ranar daurin aure daruruwan mutane suka sheda auren marwan yasha babbar Riga ya nata washewa su aysha ko ana cikin gida anata fama da nauyi Yan gidansu harda abbu duk sun halarci daurin auren,

Da karfe shidda suka nufi hall inda zaa gabatar da dinner yara da manya su fahad da friends dinshi sun hallara aka fara gabatarda event din inda sabeer tunda yayi tozali da sameera yaji in ba ita ba se rijiya Sam bai tunanin jawara bace ya koma kusa daita yanajanta da surutu ,

Bayan anci ansha an cashe aka dauki Amarya aka kaita dakinta,

Kowa ya tafi se Amarya ita kadai tana jiran angonta marwan a tsorace take da daren saboda tuno sameera,

bayan wani lokaci marwan ya shigo ya nata baza kamshi bakinshi kuwa baya rufuwa yana shigowa sassanyan kamshinta ya bugi hancinsa yanajin kamar ya afka mata ya daure ya isa wurinta Hafset ta bude mayafi ta sakarmai murmushi,

Ya saki murmushi yace"doctor kitashi kiyo alwala muyi salla mu godewa ubangiji daya hadamu a inuwa daya ,

Tai murmushi ta tashi sukayi salla sukaci suka sha suna ta dan labari yadda biki ya kasance ,

Ta rigashi tashi tayo brush ta dawo ta fiddo kayan bacci yanata kallonta ta kalleshi yayi saurin tashi ya nufi toilet,

Ta zuge zip din riga dasauri ta cire tana balle bra taji hannunshi bayan ta ,

Tai saurin rike bra din marwan ya kai baki setin kunnenta cikin rada yace"let me help u"

Ta dafe wurin yana murmushi ya zare hannunta ya balle bra din hannunshi da Lamar ruwa,

Tai saurin rike ta don karta fadi ya juyo daita a hanzarce wannan yasa bra din faduwa tai kasa

Hafset ta zaro ido shi kuwa ya kure breast dinta da kallo yanajin muguwar shaawa,

Tai sauri zata rufesu da hannuwa ya rike hannuwan da nashi yayi mata wani kallo ya sunkuya ya kama breast dinta yana tsotsa cikin yanayin fitar da hankali,

Hafset ta lumshe ido ta cije lips tanajin matsanancin dadi yadda yake abun cikin kwarewa,

Yanata shan breast din yana zukowa seda ya tabbatar duk jikinta ya mutu sannan ya karasa cire mata kayan ya jata kan bed ya cigaba da rikitata cikin salon bariki sede da banbanci cos yau yanayin abinda Allah ya halattamishi da malaiku suna rubuta masa zunubi yau kuwa dumbin lada ce zai samu,

Hakan yasa ya dage sosai ya rikita Hafset da wani salon da ni ban sani ba bare na rubutamuku salo me rikita tunani da sada ka da wata duniya daban da wacce mutane ke ciki,

Time daya fara sex daita ne tagane cewar namiji baya karami don kuwa duk kankantar marwan seda yasata zubar da hawaye ,

Bayan yasamu gamsuwa ya rungumeta yana meda numfashi,

Hafset na kuka tace"ni ka kyaleni "

Ya kara rungumeta yace"haba my doctor"yana kara shigar daita jikinshi,

Tace"karka sake ce min doctor saboda ni ce patient din"

Marwan yayi dariya jin zancenta yana dariya se kuma yayi shiru ya saki kuka me sauti da hawaye masu zafin gaske,

Hafset tai saurin jirkitowa tana kallonshi idanunta cike da hawaye ta riko face dinshi in cool tace" patient idan maganar danayi ce ta saka kuka kayi hakuri idan kuma u r not satisfied kayi banason ganin hawayenka"

Yana kuka da hawaye yace"na farin cikine Hafset da kyautarki da Allah yabani domin ban kamaceki ba"

Ta rufemai baki tana girgizakai tace"kadena tuno baya ,baya ta tafi bazata dawo ba kayi shiru plss"

Yayi shiru yana share hawaye ya jawota yace"to kidan kara bani"

Tai murmushi tace"tom"

Yayi murmushi yace"nasa guduwa zaki ashe jaruma ce"ya kai mata kiss yace"nagode sosai Hafset da sona duk yadda nake da kuma amincewa dani"

Tace"karkamin godiya ni likitan ka ce hakkina ne na soka na kuma kula da kai da lpyarka"

Yayi dariya yace"thank u muje na gasaki karkiyi tsami"

Maganar tabata dariya shima yana ta dariya ta tashi ta shige toilet ta kulle domin gyara jikinta,

Anyi auren marwan 31dede da wata ukku da sakin faseelat

wanshekare faseelat na baccin safe kusan 7am taji ring din wayar ta Sam ta manta ta kashe da bazaa ma sameta ba saboda ba kamar da bane da take zuwa school,

Ta jawo ta dauki wayar tana dubawa taga dear ta duba date taga daya ga wata tana murmushi da matukar jindadi ta dauka ta kara kunne,

Alhaji na farinciki yace"dear"

Tana farinciki itama tace"dear"

Ya lumshe ido yanajin dadi na tsargamai har cikin tafin kafa yace"inafatan komi yadedeta inafatan lpy lau?"

Tai murmushi don tagane inda maganarshi ta dosa tace"lpy lau my dear"

Ya nata farinciki yace"zan iya zuwa ?"

Tace"u r always welcome dear"

Ya saki murmushi me sauti yace"tnx u dear nagode ina nan zuwa anjima kadan I'm very eager naganki"

Tace"me too "

Yace"senazo "

Tace"bye"tana Jan bye din ta fitar da wani sassanyar numfashi ta kashe ,

Alhaji nura ya rungume wayar yanajin matukar farinciki ya tashi ya nufi toilet domin yin wanka na musamman a matsayinshi na bazawari,

Faseelat ma tasanshi sosai yana iya zuwa tun yanzu ta tashi dasauri ta nufi toilet tai wanka da brush ta dawo ta zauna ta tsara sassanyar kwalliya tanata kamshi ta saka riga da sket atamfa Côte diviore tasa milk gyale tasa brown shoes tayi kyau sosai ,

Takoma ta zauna tana zama kiranshi yashigo ta dauka tana murmushi,

Dasauri yace"ina kofar gida"

Tace"tom "ta tashi ta fito ,

Tana fitowa Ummi dake waje tana aiyukanta ta kalleta tace"ke ina zakije tun da safe ba kince kindena zuwa school ba?"

Faseelat kanta sunkuye tace"eh dama alhaji ne yazo"

Ummi tace"dama saboda shi kika fito ko?to Yayi sekice ya fito don ba komawa zakiyi kamar da ba"

Faseelat ta kalli Ummi ta wuce,

Tana wucewa Ummi tace"shashasha kinsan kina sonshi kika ki aurenshi "

Faseelat naji ta fita ,

Tana fita tai tozali da dalleliyar motar alhaji nura ta nufeta ta bude ta shiga kamar kullum

Please Login or Register in order to submit comment