Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunta,

Faseelat ta girgiza kai ta zare hannunta ,suka tafi suka fara rawa suna juyi a sannu cike da kwarewa,

Faseelat tameda ido wurinsu tana kallon rawar ,Ita sam rawa bata cikin rayuwarta da ace tanaso da setayi bawai don tarin jamaar dake wurin zasu hanata yiba,

Fahad da keta kallonta yanayi yana kallon waya yatsaya yana kallonta ganin taki zuwa wurin rawar ,a ranshi yanata kara yabamata yana kara kallon fuskarta innocent face ce bazakace zatai fada ba ga faraar da taketayi data kara mata kyau,

Hankalinta akan rawa yasha kallonta tana medo ido wurinshi shi kuma ya meda nashi wurin masu rawar sunata rawa bilhakki,

Faseelat ta kureshi da kallo, wani halittarshi kamar shi yayi kanshi tsabar kyau shima fahad irin hakane,

Yanmata suka gama casu aka gayyaci maza duk suka tashi bawanda ya gayyaci fahad cos sunsan baya ciki,

Maza suna cikin rawa wayar faseelat tafara vibrate tana dubawa taga yaya omer ta kalli time wai har 9:30 duka setake ganin kamar yanzu tashigo wurin,

Batare da tayiwa wasu magana ba tatashi ta nufi kofa dasauri ,

Fahad ya dago ze kalleta yaga wayam yafara dube_dube ya hangota zata fita dede wurin fitar yaga ta yadda wani abu,

Dasauri ya tashi yabita cos lokaci daya sonta ya masa dirar mikiya sosai a zuci ,

Itako harta fice tana zuwa bakin motor tabude mota taga wayam ba keys se waya hannunta tai tsoki tajuya tana tafiya tana kallon kasa,

Shiko fahad yana zuwa ya duka ya dauki keys din yanata kallonsu yana niyyar fita tana niyyar shigowa kowane hankalinshi na wuri daban sede sukaji sunyi karo,

Keys din dake hannunshi suka fadi,tai sauri tai baya sannan ta kalleshi shima yanata kallonta,

A time daya suka duka daukar keys din yariga ta dauka ,ta dago da murmushi ganin key dinta hannunshi murya kashe tace"I'm sorry plss"

Ya kalleta kawai yayi murmushi ya mika mata keys dinta,

Kamar karta amsa a slow ta mika hannu ta amsa tameda kallo wurinshi tace"tnx"

Ya lumshe ido kawai ya bude amsar yaji kenan,

Batare da jira ba tajuya ta nufi motor ,he don't know where to start wata zuciyar na cewa yabita ya fadamata feeling da yasamu lokaci daya akanta wata zuciyar na cewa yayi following dinta gida,

Hartaje bakin motor ta juyo ta kalleshi batare da murmushi ba yana tsaye yanata kallonta ta meda kallo a motor tasa key din jikin kofar ta juyashi,








Kwanan nan Baku samu kullum akwai abinda yake rikeni kuyi hakuri zan gyara
[11/22, 10:14 PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



2⃣2⃣


*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace idan dayanku ya gajiya bazeiya tara lada dubu ba toyayi subhanallahi sau 100 zaa rubuta masa lada dubu a kankare masa zunubi dubu*



*MY BRO ADAMU INDABO NABAKA THIS PAGE DON JINDADIN KA SON SO*




Ta juyashi taja murfin seda takara kallonshi still yana tsaye yana kallonta ta sakarmai murmushi daya matukar kama zuciyarsa tashiga motor zuciyarta nata lugude kamar zata fito saboda yadda taji tana masifar sonshi ,


Shikam yakasa zuwa ya mata magana seyaji ta masa kwarjini kuma betaba ba wannan shine karo na farko daya fara kallon mace dasunan so abun zeyi masa wuya,

Hankalinta duk yana wurinsa tana cigaba da kallonshi ta glass ta rufe kofar tasa key tafara tada motor sede data tashi seta mutu ,ta kwatanta kusan so ukku sannan tai jimm tana kallon sitiyarin,

Yana tsaye yana kallonta sosai yaji dadin kin tashin motar ya nufi motar yana tafiya a sannu ,yana zuwa yasa yatsu yadan kyankyasa mata glass so biyu kadai ,

Ta sauke glass din ta kalleshi tanata kara yabawa kyawunshi,

Yadan duko jikin motor muryarshi me sanyi yace"can I help u?"

Wai!!! dadin dataji a zuciyarta baze misaltuba ashe in ka ganshi bakaga komi ba sekaji muryarshi me dadi da sanyaya zuciya da ruhi,

Ga kamshin dake fita daga jikinshi medadin gaske,

Tai karamin murmushi tace"tnx "ta dora hannu a murfin ya matsa tabude tafito ,

Batare da ya kalleta ba yashiga motor ya kunna tana tashi ta mutu ya sakeyi haka ,ya fito a motan yabude gaban motorn yaji kauri lalle awai inda matsala take ya kalli motor ya kalleta ya meda ya rufe ya kalleta yace" I think akwai matsala a motar bana tunanin zata tashi"

Faseelat ta dafe goshi ta latsa wayarta 10 saura minti 12 kacal ta bata fuska,

Yana kallonta a hankali yace"inba damuwa zan kaiki gida kibar motor din anan I promised bazata kwana ba zaa gyaramiki and gobe zan kawomiki ita da kaina"

Tai murmushin daukar hankali tace"nagode sosai"

A time din yayi murmushi da yakarawa fuskarshi kyau ya juya ya nuna wata mota da hannu yace"my car "ya medo ido wurinta sannan yajuya yafara tafiya sannu,

Tabi bayanshi tana tafiya a hankali farinciki fall ranta fatan ta de yace yanasonta amma batada wani big problem na miskilancinsa ai tana karanta novels tanajin yadda miskilan maza suke suna son mace zasuki nunawa bayan tana cikin zuciyarsu duk numfashi,tasani miskilaye murmushinsu da dariyarsu kididdigaggune amma they're jarumai in bed sun iya bawa mata hakkinsu ita kuma hakanne tafiso ,ita zata nunamai son zata nemawa kanta babban wuri a zuciyarshi da duk time da suke tare ze mance kanshi ,

Ita kadai take tunani har suka isa bakin hadaddar motar shi white color ya bude mata ya rike murfin ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya zagaya ya shiga ya tada yafara tuki a sannu kamar kullum,

Kamshin shi da nata da suka hadu suka bada kamshi daban medadi,tunda tashiga bata samu ta kalleshi ba kanta na kallon hannunta,

Shiko yanata kallonta ta mirror time to time,har suka dau hanya be tambayeta wace unguwa ba don yama manta shafff shide kawai yana driving to home hankalinshi ya dauku kanta,

Can zuwa ta dago taga tafiya kawai sukeyi ba hanyar gidansu ba,ta dan kalleshi ta dauke ido a hankali tace"zoo road "

Ya kalleta ya danyi murmushi karami yace"I'm sorry ban kula ba"

Tace"uhmm"

Yana cigaba da driving bayan yasha round yace"I'm fahad dawood"

Dadi a ranta ba magana muryarta very sweet tace"faseelat maaruf"

Bazato taji yace"I like the name"hankalinshi a titi,

Ta kalleshi tai murmushi tace"tnx"

Suka cigaba da tafiya duk sunyi shiru ita in mind tana ta rokon Allah yasa ya fadamata koda wata kalma me kama da so ,

Shi kuma yana tunanin kar tace she's in love ko she's married ko engage to some one,

Suka cigaba da tafiya har bakin kofar gidansu ,

Ranta badadi tace"wancan gidan"ta nuna da yatsa

Ya nufi bakin gate din gidan ya tsaya,

Ta kalleshi tace"nagode sosai se anjima"tadora hannu zata buda mota,

Taji muryarshi "ur number plsss saboda gobe na kiraki idan nakawomiki"

Tai murmushi ta amsa ta rubuta number ta mika mai tace"tnx once again"ta bude murfin tafita,

Yabita da kallo tana fita taga ya omer tsaye bakin gate ,gabanta yafadi karya fara mata masifa gaban fahad ta karasa wurinshi dasauri ,

Tana isa tace"yaya dan Allah kayi hakuri wlh mota ta ta lalace nasamu ne wancan ya kawoni"

Omer ya kalli motar fahad yana zaune be tafi ba ya daga mata kai,tawuce ta bude kofa ta shiga,

fahad na zaune na kallon su duk yaji maganarsu yaga omer ya nufo motar ,

Fahad yabude yafito tunkan ya karaso yana karasowa ya mikawa omer hannu suka gaisa ganin duk tsara suke,

Fahad yace"naga motar ta tasamu problem shine na kawota insha Allah gobe zan kawo motar "


Omer yace"nagode sosai"

Fahad yace"plsss is she ur sis?"

Yace"eh she's my sis ita kadai "

Fahad ya jinjina kai yace"I love her inason nasamu izinin zuwa wurinta mudedeta cos ban fadamata ba"

Omer yayi murmushi yace"all the best"

Fahad yayi murmushi yace"tnx"ya sake mika mai hannu suka kara gaisawa sannan ya juya yashiga motor yabar kofar gidan,

Omer yabi hadaddar motar da kallo ya jinjina mishi da har ya masa magana dukda shekarun sunzo daya ,ga kuma maza sunata zuwa wurinta bawani Neman izini hardasu alhaji nura dake babba magidanci,

Ya sauke numfashi memakon yashiga gidan seya shiga mota ya nufi gidanshi,

Faseelat kuwa nashiga gida ta wuce dakin Ummi ,Ummi na kwance tace"ke se yanzu dukda ya miki fada akan karki wuce karfe taran"

Ta zare gyalen jikinta tace"Ummi mota ta tasamu problem amma nasamu wani ze kulamin daita shine nasamu yakawoni gida ma"

Ummi tace"kin sameshi kofar gida hala?"

Faseelat tace"eh Amma nafada mai bece komi ba kila ma yawuce gida"

Ummi tace"kije ki shirin kwanciya bari naje na kulle kofar"

Faseelat ta juya ta tafi dakinta ,Ummi taje ta kullo gidan tadawo ta kwanta,

Faseelat nashiga daki tafara zame kayan jikinta tana tunanin fahad tana ta murmushi zuciyarta nabata he love her soon or later zai fadamata hakan,

Tana gama tube kaya ta dora Zane kan vest din jikinta ta haye gado ta kwanta rufda ciki tana cigaba da sakin murmushi,

Can zuwa taga haske akan wayarta ta daukota tabude Sega missed call din alhaji kusan 4 da message guda daya tashiga message din tabude "ina tsananin kewar muryarki a dare daya daban samu naji taba, dear nayi sabo dake da bazan iya jure rashin wani abu naki ba ,yau bazan iya bacci medadi ba nasan barawone kawai ze daukeni fatan zaki kwana cikin farinciki mijinki in Allah yaso"

Tai saurin cewa "ba amin ba insha Allah nita fahad ce fahad shi kadai"ta saki murmushi,

Se kuma ta tsaya tunani alhaji nura did so much for her sauyinta lokaci daya problem ne kuma bahaka tana wayayya yakamata tayi ba zata cigaba yadda suka saba in ankusa bikinsu tace dole akamata zatai biyayyane su rabu lpy salin alin ,

Tai dariyar rainin hankali tace"my dear kenan" ta kuma dannawa number dinshi kira,

Yana kwance dagasken yakasa bacci tunaninshi da zuciyarshi nata hangomai ga dear dinshi can tana fira da wani a wurin party Sega kiranta ya sauke wata nan nauyar ajiyar zuciya ya dauka,

Tai murmushi tace"inason kai bacci medadi dear that's y nakira domin hankalinka ya kwanta tundazu na dawo donma mota ta tasamu problem taki tashi seda nasamu wani ya ragemin hanya"

Alhaji yaji badadi duk dukiyarshi ace dear mota nabata problem yace"I'm not happy kuma insha Allah gobe zansa a kawomiki wata mota kidena using da wannan"


Tace"dear banaso plss"

Gabanshi ya fadi yace"why ?"

Da shagwaba tace"ni inason tawan "

Yace"karkidamu zansa akawomiki sabuwa desame color da takin"

Tace"nide aa "

Yayi murmushi yace"kima shirya gobe 10am motor naki zezo"

Taturo baki "dear plsss ni kashin kudin yayi yawa banaso plss"

Yayi karamar dariya yace"sleep well seda safe" yakashe kiran yanata murmushi,

Ta dauke wayar a kunne tana kallo setaji tausayinsa tasan yana sonta sosai tace"dama zan iya dana aureka kodan saboda soyayyarka gareni amma sede kayi hakuri nasamu
dream dina insha Allah burina yana gab da cika I'm sorry "

Shiko yana kashe wayar yaji yadawo dede se sannan yayi tunanin abida duk yau bata kira ba ko hidima ta hanata kome ?kamar ya kira se yaga time10:45 seya fasa ya kwanta ya rumtse ido don yin bacci dama yanzu first lady a zuciyarsa faseelat se abida Hjy Rukayya last kuma ita kullum tana biye kamar jela,

Ba jimawa bacci ya daukeshi me cike da mafarkin faseelat,

Shiko fahad yana driving yana tunanin faseelat daya lumshe ido ita yake gani ga kamshinta da haryanzu bebar motar ba,

Yana tunanin yakira me gyara yafada masa yazo ya amshi key din motor dinta don gyarawa,

Yana karasawa gida ya samu me gyaran yabashi key sannan ya nufi part din daddy ,

Ya samu daddy nata aikinshi a system yashiga ya zauna seat takusa da daddy yace"sannu da aiki daddy"

Daddyn ya dan dago yace"yawwa son kadawo"

Yace"eh daddy marwan yadawo kuwa?"

Daddy yace"eh sunde kawoshi dazun yana daki kwance yana bacci"

Fahad ya girgiza kai yace"mommy fa kunyi waya?"

Yace"inaga bazaa sameta ba harseta dawo inaga inda take ba network"

Yace "Allah yamedota lpy"

daddy yace"ameen"

Fahad yace"seda safe"

Daddy yace"Allah yakaimu "

Fahad ya tashi ya nufi part din marwan ya leka yana kwance daidaya yanata numfashi ko takalmi basu ciremasa ba ya girgiza kai ya nufi part dinshi ,

Ya shiga toilet ya dan watsa ruwa da brush yafito yasa rigar bacci yahaye bed ya kunna system dinshi,


Sede yana aiki yana kallon fuskar faseelat se yadanyi jimm inya tuno da wani abu daya burgeshi gareta sannan ya cigaba, daga karshe yayi tsoki ya dauko waya yakure number dinta da yayi saving da dream girl da ido yanajin kamar yakira yaji sweet voice dinta sannan ya kwanta,

Ba yadda yayi ya kwanta ya lumshe ido ya cigaba da tariyo haduwarsun har bacci ya daukeshi cikeda dokin gari ya waye ya ganta,

Khalil yata kiran jameela har yagaji ya hakura kuma yakoma gidansu da marece still amsa daya ce "batanan" yanata tunanin to ina taje haka?

Itako jameela se Maghreb ta tashi jikinta a mace ta shiga toilet tai wanka ta sauya kaya ta dauko wayarta ta kunna kanta nata juyawa saboda baccin da tasha kuma hakan saboda over din datayi da drugs ne,

Tana kunna wayar messages na apologize suka fara shigowa from Mimi,

"Daughter I'm sorry but ki fahimci yadda nakeji inada kishi sosai yazan iya daurewa zamanki tareda wani muna sharing dinki ki duba mana"

"I'm sorry da yadda naimiki Amma plss ki lura da halinda zuciya ta zata shiga idan hakan tafaru"

"Shine haryanzu baki kunna waya ba?alright na yadda kiyi auren but promised me that bazaki yarda kiyi ciki ba"

Irinsu ne tasamu daga Mimi tana gama karantawa tai tsoki samm haushi mimi ke bata da take hadata da Khalil wai har take maganar haihuwa dashi hmmm,

Ta ajiye wayar ta fita tsakar gidansu,tunkan ta karasa fita taji muryarsu suna karatu,

Tana kara sawa tasamu ummanta nata yiwa kannenta karatu da sukeyi duk bayan Maghreb,

Ta samu wuri ta zauna tace"Umma sannu"

Umman ta kalleta ta cigaba da karatu suma yaran basu meda hankali kanta ba,

Tai tsit tana saurarensu gabadaya zaman gidan ya isheta kamar tafita takeji sede ba dama suna waje,

Anayin ishai yaran suka tafi masjid ita Umma tashige daki yin ta ta sallar ,

Jameela na ganin haka ta tashi takoma daki ta dora after ta zari takalmi da waya tai sauri tafita tatari mashin tahau se bakin gate din gidansu Mimi tana zuwa tafara kwankwasawa megadi na budewa yaga itace yabata hanya tawuce ciki,

Ba tsayawa ta wuce part din Mimi tana tura kofa taga Mimi tayi tagumi da duka hannu biyu idonta akan tv ,

Ta girgiza kai tunkan ta shigo kamshinta yasa Mimi tagane tazo wurin ta tashi ta karasa wurin ta dasauri ta jawota ciki suka zauna tana kallonta tace"meyasa kika kashe wayarki don nace banason kiyi aure na nuna bacin raina? Duk kin tayarmin da hankali"

Ta kalleta da haushi tace"tunaninki shi yafi batamin rai kina maganar ciki zaman aure zanje ne ko kuwa zaman jindadi? Ya kamata kigane manufata zanyi auren ne kawai don Hutu na zan kasance ni kadai Wanda hakan dama ce agunmu ba takura bakomi, kuma kidena kishi da wancan gaulan da ko kallonshi banasonyi I love u kece nake gani naji dadi ke kadai ke cikin zuciyata"

Mimi ta rungumeta tana sauke numfashi tanajin sauki_sauki,

Jameela tace"just wait and watch wlh baze rika samu yadda yasoba u know bana shaawar namiji ko kyakkyawan namiji be taba burgeni ba bare har nayi shaawar this ugly kidena tadamin hankali momcy plss"taja plss din

Momcy ta kamo fuskarta taiwa kuncinta kiss fuskar na hannunta tana kallon idonta tace
[11/25, 10:57 AM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



2⃣3⃣


*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace ana bude kofofin aljanna ranar litinin da alhamis se ai gafara ga kowane bawa se wanda ke shirka da wadanda suke gaba se ace ku dakata ma wadancan har se sun shirya*




*Son ku a jinina yake sisters*
*Beelat (sarauniya)my heart beat*
*Matar soja feaner*
*My ruwan jiki golden girl*
*Kanwa Ummu farouk*
*My one and only Mhizzphydo*

*Ina mugun sonku proficient writers Allah yakara mana basira da daukaka*



Tace"promise?"

Jameela ta daga kai tace"promised "

Mimi tai karamin murmushi a hankali take matsawa da fuskarta idonta lumshe ta dora bakinta akan na jameela tafara kissing dinta,

Jameela ta lumshe ido tabude baki suka cigaba da kissing juna suna enjoying hakan,

Suna hakan nawani lokaci wayar jameela tafara ring ta katsesu Mimi ta zare baki tanata lashe lips tana meda numfashi ,itama jameelar na meda numfashi tana lashe lips ta kalli screen din wayar taga Khalil ne ke kira ta dan kalli Mimi ta dauki wayar,

Khalil da yake kagare jin an dauka ya sauke numfashi yace "beauty inafatan kina lpy duk yau wayarki a kashe duk hankalina ya tashi ko nayi laifi ne?"

Ta dan kalli Mimi taga fuskarta kumbure ta yamutsa fuska tace"lpy lau bansan ma wayar na akashe ba kana lpy"

Yaji sanyi jinta tambayi lpyarshi yace"gaskiya bana lpy saboda rashin jin lpyarki harfa gida naje so biyu bakinan"

Tace"ayya ina gidansu momcy yanzu haka "

Yace"yaushe zaki koma ne?"

Tace"yanzun nan zan koma"

Yace"to ganinan zuwa yanzu"

Tace"OK"takashe kiran yanajin dadi yashiga mota ya nufi gidansu Mimi,

Mimi kuwa fuskarta bawalwala zuciyarta na zafi,

Jameela ta kalleta ta langabe kai tace"plsss kidena damuwa kinji my sweety"

Mimi ta kakaro murmushi tace"yanzun tafiya zakiyi batare da munyi bankwana ba kinsan gobe school zantafi"

Jameela tai murmushi tace"karkidamu nan da time kadan zaki rika samuna koda wane lokaci ba takurar kowa"

Mimi tabata fuska ta turo baki tace"ni I'm not happy fa"

Jameela tai yar dariya tace"I sure u will nangaba kadan"

wayarta tafara ring seda takusa tsinkewa ta dauka ,

Khalil yace"ina kofar gidan"

Tace"alright "ta kashe kiran ta kalli Mimi tai mata killer smile tace" zansamu rakiyar?"

Mimi ta harareta ta tsinkulo cikinta ,jameela tafara dariya mimin ma nayi ta kama hannunta suka fito har bakin gate sannan tasaki hannun jameela ,

jameela tai mata bye da hannu tabude kofar tafita mimin tabi bayanta da kallo tadanyi tsaye sannan tajuya cikin gida,

Jameela na fita taga Khalil zaune a motor ta nufi motor din,

Tana zuwa yafito yabude mata yanata faraa tashiga ya rufe yakoma yashiga yakama hanya,

Motar shiru khalil ya kalleta yameda kallon a titi yace"hankalina ya tashi sosai yau ko abinci nakasa ci"

Maganar tabata dariya waiko abinci yakasa ci tadanyi dariya kadan tace"ka kasa cin abinci because of me?"

Yace"inasonki sosai har rashin lpy senayi kodayake yau dinma nida marar lpy duk daya"

Tai murmushi tace"I'm sorry to"

Yace"thanks" yanajin dadin hakan,

Suna zuwa bakin wani super market yatsaya ta kalleshi da alamar tambaya ,

yana kallonta yace"zamu shiga mu danyi shopping semu karasa gida ko?"

Tai murmushi kawai ,

Ya bude motar yafita ya bude mata ta fito suka jera suka nufi ciki ya dauki shopping cart suka nufi wurin cosmetic suna zuwa ta dauko lotion da take shafawa tasaka yanata sakin murmushi shi ko ta dauko turare da take using tasaka shikenan bata sake daukar komi ba,

Sunata yawo ganin bata kara daukar komi ba yafara daukar different perfumes yana sawa,

Ta kalleshi tace"ba kowane turare nake using ba kabarsu hakanan "

Ya kalli kayan yan kadan yace"shopping mukazo? Kinki daukar kome"

Tace"ihmmmm"

Yayita kwasar kayan makeup yana sakamata suka koma kan sweet ya kwasa sannan suka nufi wurin biya,

Aka fiddo kayan aka dora a bot mutumen ya kalleshi yace"60k"

Abun ya bawa Khalil mamaki 60k ga kayan bamasu yawa ba besan lotion nata ba kadai 20k Mimi ke siya masu turarenta me tsada ne 25k cifff ,

Beda 60k a hannu yabada ATM nashi aka cire akasa masu a shopping bag suka fita suka nufi gida suna zuwa ta kalleshi tana mai wani murmushin dauke numfashi tace"zaka zo gobe?"

Yace"dole na "yana murmushi,

Tace" nagode seda safe"

Tabude mota tafito yafito ya mika mata bag din ta amsa takara cewa "thanks" tajuya tashiga gida,

Tana shiga tasamu Umma tsaye ta jingina da bango ta nata tunani tazo ta wuceta tace"sannu Umma"

Umma tace"jameela zonan"

Ta dawo ta tsaya,

Umma ta cigaba da cewa "jameela baki tsoron bacin raina yanzun cikin darennan kika kama hanya kika fita"

Jameela tace"ayya ummanmu Khalil ne yazo shine nafita muka gaisa seya kaini mukayo shopping kiyi hakuri plss banason ranki na baci saboda ni"tana kaiwa karshe takama hanya zata tafi hartayi tako biyu seta dawo tace"amm Umma nasamu Wanda nakeso ku auramin"

Umma tai shiru tanata kallonta,

Tace"inasonshi sosai Umma kuma wlh auren nakeso kumin da wuri"

Umma ta cigaba da kallonta,

Ta kalli ummar tace"kifadawa Abba" tajuya ta shige dakinta,

Hawaye masu zafi suka zubowa Umma tasa hannu ta kwashesu tace"Allah ya shirya" ta shiga dakinta ,

Bayan mintina abba yadawo yana gama cin abinci Umma tace"jameela tabani sako tace afadamaka tanason Khalil kuma aure takeso"

Abba ya girgiza kai Sam beyi mamaki ba muryarshi sanyaye yace"Allah ya shirya gobe zanje da kaina na samu manu in sun shirya su turo koma basu da gidan da zasu zauna ni zanbashi gida"

Umma tace"kana ganin hakan yayi"

Yace"toya zaayi tunda auren takeso gwara ai mata kar abin yazo yafi haka har tafara bin maza"

Umma tace"to Allah yasa alheri"

Yace"amin"


Bangaren su jameel basuyi bacci ba anata kashe arna ,


Wanshekare


Tunda asuba fahad ya tashi da tunanin faseelat yagama shirin shi yakira me gyaranshi ba jimawa yakawo motar faseelat an gyarata tsaf,

Karfe 8:30 ya nufi gidansu seda yaje sannan ya dauki waya ya latso number dinta dream girl ya kira,

Faseelat na kwance tana bacci kasancewar weekend ne tai sauri tatashi ta dauki wayar don tuni take jiran kiranshi,

Ganin shine yasa ta dafe heart ta sauke numfashi ta dauka da sweet voice tace"assalamu alaikum"

Yaji sanyi a ranshi yace"waalaki salam"

Sukai shiru tace"ina kwana"

Yace"lpy lau ina kofar gidanku"

Dadi ya kasheta tace"alright ganinan fitowa"takashe kiran tanata murna tatashi dasauri tashiga toilet tai brush ta wanke fuska tadawo tasaka gown tadora Dubai abaya akai ta fesa perfumes tasa flat shoes tafita,

Tana bude gate ya kureta da kallo seyaga ba makeup din tafi mishi kyau kuma dis dressing yafi mishi na jiyan kyau,

Yanata kallonta harta iso bakin motar tai tsaye ,

Yadanyi murmushi ganin taki shigowa ya bude motar yafito,

Ta kalleshi tadanyi murmushi ta sunkuyar da kai kasa tace"sannu da zuwa"

Yayi gajeren murmushi yace"na cika alkawari ga motanki na kawo"

Batare da ta dago ba tace"nagode sosai"

Sukai shiru yanata kallonta yarasa ta ina zefara dakyar yayi kokari yace "bantaba soyayya ba I don't know what love is seda naganki kallo daya na miki naji kin kwantamin a zuciyata I love you faseelat and I want to marry you"

Kanta sunkuye ta lumshe ido wannan moment din shine best in her life da dream man dinta ya furta mata love zuciyarta har narkewa takeyi,

A hankali tace"I feel desame when I seeing u nima inasonka but I don't think we will get married"

Yayi saurin cewa"why?"cikin sanyin murya

Muryarta very low tace"my uncle suna da Wanda sukeso suhada ni dashi I don't love him suma sun sani they're planing to get me married to him nafada masu banason shi sunbani only 3weeks na fiddo miji sumin aure and idan bankawo miji ba zasu aura mun wancan and now only two weeks left for me"

Ya lumshe ido ya bude ya medasu kanta yace"I love you and I will marry you in two weeks time"

Tai saurin dagowa ta kalleshi yanata kallonta ya daga gira yace"yeah I'm ready ko one week ne bare I have 2weeks ,faseelat tunda nake bantaba furtawa wata soba saike u r my first love and you will be the last zan aureki a 2weeks and I'm happy to heard this my mom tanata so nayi aure yanzu tatafi Niger I wanted to surprise her data dawo ayi bikinmu amma yanzu zata dawo ta samu nayi aure kuma nasan she will be in so much happy"

Faseelat tai dogon murmushi tanata kallonshi shima yanata kallonta,

Yace"I love you "

Tai murmushi me kyau ta sunkuyar da kai,

Sukayi shiru yanata kallonta ya sauke ajiyar zuciya yace"I will go kibani number bro dinki I want to talk to him"

Tace"OK"

Ya ciro wayarshi a aljihu ya mika mata ta amsa tasaka masa tabashi,

Yayi saving ya kalleta yace"sai munyi waya"

Tai murmushi tace"bye"

yajuya ya fara tafiya tai still tanata kallonshi,

Ba jira taga ya tari me mashin yahau beko waiwayo ba suka tafi,


Ta sauke ajiyar zuciya tanata murna ta ciro key na motan ta rufe tai cikin gida dasauri tana murna,

Ummi na tsakar gida tace "lpy kike?"

Faseelat tai murmushi tace"Ummi I'm in love"

Ummi tace"tooo Allah yasa alheri "

Faseelat tace"ameen"tai cikin daki dasauri ta haye gado tana murna itade zuwa dinner tai mata rana gashi tasamo miji irin Wanda takeso,

Ta dauki wayarta ta latso number dinshi tanata kallonta special number har a gunta tai saving da *My handsome* tai kwance tanata sakin murmushi,


Shi ko fahad yana zuwa gida part din mommy yawuce yasamu daddy na breakfast ya zauna yayi shiru,

Daddy ya kalleshi yace"my son lpy?"ganin da magana bakinshi,

A hankali da yar kunya yace"daddy nasamu wacce nakeso"

Daddy na murna yace"I'm

Please Login or Register in order to submit comment