Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bata lpy ina zataje a duk iya saninshi bawata asibity kan road din,

Don haka yayi following dinta ,

Ita kuwa batasan dashi ba driving kawai takeyi zuwa gidan alhaji,

Shi kuwa alhaji har ya farka Hjy Rukayya ta mishi brush sannan ta fita abida nata daure face ta kuma bashi breakfast da drugs yakoma ya kwanta yana kagare da ganin faseelat,

Faseelat nata driving harta iso bakin kofar gidan fahad beko iso ba ta bude motar tafito tashiga cikin gidan ,

Tana shiga fahad na isowa ya kalli babban gidan ya kalli motar ta he wonder me tazoyi a gidan alhaji nura memakon ya tafi se ya gangara yayi parking ya zauna zaman jiran fitowarta ,

A hankali take tafiya har zuwa bakin kofar main Palo nasu ta tsaya bakin kofar tai knocking sau biyu ,

Hjy Rukayya zaman ta kenan a falon tace"come in"

Faseelat ta bude kofar ta shiga da sallama bakinta,

Tana shigowa kamshi medadi yabaje falon ,

Hjy Rukayya nata kallonta ganin wayewarta da kuma yanayin jikinta me kyau,

Faseelat ta zauna a seat ta bakin kofar tana yar faraa ,

Hjy Rukayya tace"maraba da bakuwa"

Faseelat tai murmushi tace"nagode "

Hjy Rukayya tace"banganeki ba "

Faseelat ta sakeyin murmushi tace"sunana faseelat ni tsohuwar budurwar alhaji ce but a yanzu de saura kwana takwas bikina"

Hjy Rukayya tai murmushi dukda a ranta batajin dadi tace"maraba sannu ko bari nasa akawo miki drinks"

Faseelat tace"aa nazo na duba alhaji da jikine kibarshi nagode"

Hjy Rukayya ta kalli bene gabanta yafadi tuno hjy abida na ciki ta meda kallo gun faseelat tace"ina zuwa "

Ta tashi ta haye sama faseelat tabita da kallo inde har batayi tsarar Ummi ba to da kadan Ummi zata girmeta,

Hjy Rukayya ko dakin alhaji tashiga yana kwance idonshi lumshe,

Ta kalleshi tace"alhaji"a sannu ,

Ya bude ido ya dorasu kanta,

Tace"ga bakuwarka ta iso"

Hankalin Hjy abida tashe tace"wa?hjy shine har kika barta ?bari kigani"tatashi tai waje da gudu,

Alhaji nura yayi wuf ya tashi zaune jin kamar an sokeshi a zuciya yasa ya dafeta da hannu fuskarshi ya mutse ya kalli hjy Rukayya yace"follow her plss "

Hjy Rukayya daketa kallon kofa saboda yadda taga hjy abida tafita aguje tace"to ka zauna karka fito plss"

Ya daga kai yace"go"

Tafita dasauri ,

Hjy abida na fitowa falo tai tsaye zuciyarta na kara bugawa take kallon faseelat ,

Saboda yadda tafito a guje yasa faseelat ta tashi tsaye tanawa hjy abida wani kalar kallo,

Hjy abida ta fara kallon faseelat daga sama zuwa kasa inde fari ne ko kyau bata fita ba ,ta sauke akan breast dinta suna cike asaman riga ta karasa zuwa shafaffen cikin zuwa babban hips me fadi data tara kishi yakara tokare ta don tayi mata nisa ita da ke siririya sosai,dole alhaji ya rude kanta yaga kayan Hutu a tare daita,

Ganin irin kallon da take mata faseelat ma tabita da kallo shekeke sam ba class dinta bace tafita a koina,

Hjy abida taja tsoki ta yamutsa fuska kamar taga kashi, hannunta akan kugu tace"kece budurwan alhaji?"

In I don't care faseelat tace"yeah its me"

Hjy abida tace"banza marar kamun kai karuwa mebin maza har..."

Hjy Rukayya dake saukowa daga bene ta katseta da karfi "abida kibari mana"

Hjy abida ta karasa zancen"har gida marar class anji haushi dai"

Faseelat ta kureta da ido tana kallonta sosai Kalmar karuwa ya sosa mata rai,saboda ta kiyaye ta rike mutuncinta har zuwa yanzu kuma baa taba furta mata hakan ba se yau ,

Hjy Rukayya ta karasa saukowa ta kalli hjy abida tace "amma baki kyauta ba hjy kuma banji dadi ba da girmanki kike abu kamar yarinya "

Hjy abida ta dage hanci ta kara rike kugu da hannu kanta sama,

Hjy Rukayya ta meda kallo kan faseelat tace"kishigo"

Jin abinda tace dasauri hjy abida tace"balai wlh ba inda zata bazata shigarmin dakin miji ba"

Hjy Rukayya ta na mata kallon mamaki sosai tace"abida don Allah kibari"

Idonta rumtse tace"wlh hjy bazata shigarmin bedroom din miji ba kawai ina gani karuwa ta shigarmin dakin miji bazeyiwu ba"

Faseelat taja karamin tsoki tafara tafiya zata hau sama ,

Hjy abida tasha gabanta tace"bazaki shiga ba karuwar banza marar aji kiyi gaggawar fitarmin a gida"

Ran faseelat bace ta daga hannu ta wanka ma hjy abida mari tasssss!!!!!

Hjy abida ta dafe kunci tana kallonta ,ba tsayawa ta daga hannu zata rama faseelat ta rike hannun gam ta meda shi kasa da karfi,

Sannan ta gyara gyalenta da ya rufe mata gemu cike da isa tace"karki kuskura kiyi gigin tabamin fuska domin har ubanki da yakawoki duniya seyayi nadama"

Hjy abida ta kureta da ido tana kallonta wai azo har gidanta a mareta ,

Hjy Rukayya kuwa tana tsaye tana kallon ikon Allah,

Faseelat ta Marmara ido ta kalli saman gidan ta yamutsa fuska tace"Allah ne yasoki shiyasa bazan shigo gidannan ba da wlh sekin barshi da kafarki "

Ta nunata da key din dake hannunta idonta waje muryarta kuwa bata wani dagata sosai ba tana bata warning tace"ni ba sa'ar ki bace na miki nisa kuma karuwanci mijinki ne ya koyamin tare dashi kadai na keyi "

Tai murmushi tace"kina maganar dakin mijinki ko? to zan shiga har ciki in zauna muyi iskancin da muka saba idan kin isa ki hana" tana gama fada ta nufi sama tana tafiya da yanga tana kara kada kugu,

Hjy abida da tai kasake tana kallonta tai wuff zata bita,

Hjy Rukayya tai saurin riko hannunta ,

Hjy abida tace "dan Allah mommy sakarni wlh sena mata illa sena nakasa ta ni zata mara?"

Hjy Rukayya tace"tun kafin tazo nabaki hakuri kinki yanzu wannan tashin hankalin naki seya tado ciwon alhaji kinajin abinda doctor yace idan yafadi zesamu paralyze idan hakan tafaru wa gari ya waya ?nima da kike gani inajin kishin abin amma ba yadda zanyi ne nide fatana ya samu lpy "

Hjy abida se hawaye shar_shar tace"wlh hjy bakya kishin shi da kinayi da bazakice nai hakuri ba"

Hjy Rukayya tace "Nide na fadamiki kiyi hakuri ki koma part dinki harta tafi in kuma bakiji ba seki zauna kijirata tafito ku cigaba karki bita can ,nikam nashiga ciki" ta saki hannunta tai gaba abinta ,

Hjy abida tabi bayanta da harara tace"don bake aka mara ba sena rama sannan ko zata bar gidannan"

Ta shafi inda faseelat ta mareta da hannu ta dago hannun ta duba domin ji takeyi kamar wurin ya fashe sosai marin ya shigeta itade bazata iya tuna sanda aka taba marinta ba ,

Tai kyarrrr! da baki tace "zakici ubanki ne"

Ta zauna kan kujera tana jijjiga jiki tana karkada kafa,

Itako faseelat tana hawan sama tafara cin Karo da part din hjy Rukayya hakanan taji ba na me gida bane tai gaba tun kafin takai bakin dakin da alhaji yake taji kanshin turarensa,

Ta kakaro murmushi a fuskarta ta isa bakin kofar tai knocking,

Muryarshi very cool yace"shigo"thinking that hjy Rukayya ce tare da faseelat ko kuma ita kadai abidar ta hana faseelat din shigowa,

Faseelat ta tura ta shiga fuskarta da karamin murmushi,

Yana ganin ta da murmushinta me sanyi yaji ciwonsa ya rage sede tuno batashi bace se kuma yaji badadi,

Ta karaso ta zauna a seat da ke gefenshi tana mai wani kallo duk ya sauya sosai yabata tausayi fuskarta marairaice tace"sannu dear"

Ya matse lips ya jinjina kai,

Ta dukar dakai ta dago da hawaye tace"kayi hakuri plss ka yafemin inajin kamar na yaudareka rashin fada maka da nayi "

Ganin hawayen ta baya masa dadi yace"kidena banason ganin hawayenki haka Allah yaso kuma dama ni ba mijinki bane shiyasa hakan tafaru na dauki kaddara ki kwantar da hankalinki"

Ta kalleshi tana meda wasu hawayen tace"Nide ka yafemin plsss "

Yayi murmushi me ciwo yace"baki tabamin komi ba in ma kinyi na yafemiki my dear "

Tana share hawaye tace"nagode sosai dear zanyi missing dinka"

Yayi murmushi me ciwo yace"ina miki fatan alheri"

Ta daga kai tace" Allah yabaka lpy amma zakazo ko?"

Yace"its must"

Tai murmushi me sauti tace"nagode sosai dear bazan taba mantawa dakai ba"

Ya jinjina kai ,

Tace"zan koma domin nasha magani"

Yace"bari na taka miki"

Dasauri tace"aa plss kabari ka kara samun sauki"

Yace"no inasamun sauki kuma dear tazo wurina ban taka mata ba ai ban kyauta ba "

Tai yar dariya ta tashi tsaye ta fita ,

Da cije lips ya sauko a gadon ya dauki walking stick yafara takawa yana fita kofa tana tsaye suka jero suna dan labari suna murmusawa,

Hjy abida na zaune falo taji suna saukowa faseelat na magana"kasani ko na dawo anjima dubaka inaji dakai sosai fa"

Sukayi karamar dariya a tare yace"na hutar dake dear "

Hjy abida ta mike ta rike kugu zuciyarta na hawa jin patient ya fito rakiya hardasu fira ana dariya,

Suna saukowa ta sha gabansu ta ci kwalar faseelat,

Faseelat ta matse lips tanajin kamar ta hayeta taita jibga sedai idan ta taba Matar alhaji a gabanshi bata bashi girma ba bata mutuntashi ba dazun ma bayan idonshi ne,

Sabida haka setai tsaye kurum tana kallonta,

Hjy abida takara tattare rigar faseelat ta rike gamm tana huci tace"ke karamar karuwa ce wlh yanzunnan zan nuna miki yadda manyan yan bariki suke"

Ran alhaji bace fuskarshi hade yace"abida saketa"with command

Ta kalleshi ta wurga mai harara tace"bazan saketa ba se tayi nadamar shigowa cikin gida na wlh"

Faseelat jira takeyi taga ta dago hannu da niyyar marinta tarike hannun don bazatayi tsaye wata katuwa ta jibgeta a banza ba,

Alhaji yaja tsoki jin kalaman abida yace"ki saketa nace"a tsawace,

Ta zaro ido da mamaki tace"alhaji saboda karuwa kakemin tsawa?"

Maganar ta sokeshi ya daga hannu ya sharara mata mari ,

Ta saki faseelat ta dafe kunci idonta cike da hawaye take kallonshi tace "ka mareni?ka mareni saboda wannan karuwar to ka mari auren ka"

Ta haye sama da gudu tana kuka sosai tashiga daki tafara hada kayan sawarta,

Ta na tafiya alhaji yafara tari ya isa ya zauna kan seat dafe da heart dinshi,

Faseelat taje kusa dashi kamar zatai kuka tace"sannu sannu dear"

Ya daga mata hannu yana haki ya samu tarin ya lafa yace"kije gida zanzo in nakara samun sauki"

Kamar tai kuka tace"Allah yabaka lpy dear sannu se munyi waya"ta kalli benen sannan tafita a falon,

Tana fita ta saki murmushi ta cije lips tanajin dadi ta samu ya yafemata and yakara nuna yadda yakesonta ma fiyeda matarshi abun ya sata farinciki sosai,ta nufi hanyar fita tanata murmushi akai_akai tana tuno drama dinsu da abida,

Fahad tun yana zaune a moto har ya fito waje yayi tsaye yana ta kallon kofar gate din yanajin kamar ya shiga ciki,

Faseelat na fitowa idanunta suka sauka akan na fahad dake tsaye jingine da motor,

Tai ........





Ayi hakuri nasoyin long page to nayi bakuwa ne kunsan bana one read more kamar maman nur🤣
[12/8, 11:48 AM] SHALELE: ➰➰➰➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI RETURN*
➰➰➰➰➰➰➰➰




From the writer of the previous story

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*


*Wattpad@mumies122*



(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)



тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09



*dedicated to mansura Lady😘😘*


*Free page*



3⃣0⃣



*GARABASA👉🏼Manzon Allah (S.A.W)yace Wanda yace LAILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LASHARIKALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU YUHYI WA YUMITU WAHUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR tazame masa dede da ya yanta bayi goma kuma zaa rubuta masa lada dari akankare masa zunubi dari tazame masa kariya da tsari a wannan ranar kuma bawanda zaizo da aiki fiye da nasa se wanda yayi fiye da yadda yayi*



*dedicated to yan FIKIRAR MARUBUTA group musamman 80k gandujen dauda🤪,hassan bawan mata,my maryam Obam (anti mimi)😂,rabia sbs,my SHALELE (hasana dan larabawa),maman nur,mai daddawa,minert,Neeshar ,real ladingo,Faty Sardauna,Surrykhan, anty hauwa,binta abbale ,Mhizzphido, Aisha alto,Fatima Suleiman ,saadatu alkali,maajinkainuwa and other's ina gaisuwa Ku cigaba da gashi kuna bamu feelings❤*

*Akwai wacce bataji sunanta ba?🤣*


Tayi tsaye zuciyar ta seda ta buga but bata nuna ba a fili sema ta kara fadada fuskar ta tana kallon shi da murmushi ta nufi inda yake,

Shi ko se ya rika kare mata kallo daga sama zuwa kasa yana duba yanayin ta ,

Tana zuwa tayi murmushi me tsada tace"nayi mamakin ganin ka dear"

Yana ta kara kallon ta yace "me kike yi anan?"

Ta kalle shi tayi murmushi tace"gidan kawata ne nazo duba ta bata da lpy "

Fahad ya matse lips yace"faseelat bana son yawo keda baki da lpy kece har zaki zo ganin marar lpy"

Ta lankwashe kai tace"I'm sorry ni naji sauki ai kuma ban cika yawo ba"

Ya cigaba da kallon ta without saying something,

Ta matse lips fuskar ta ba walwala tace"kayi hakuri nadena fita seda izinin ka from now on"

Ya sauke ajiyar zuciya yace"ki koma gida"

Tayi murmushi tace"dama I want to talk to u"

Yace"miye?"

Tayi murmushi tace"yaushe ne za muje yin pre wedding pics?"

Yayi shiru shi sam baya sha'awar irin wannan abubuwan yama dauke su rashin kunya ne ya lumshe ido ya bude yace"baza muyi ba"

Tayi saurin kallon shi tace"why ?nide muje muyi gaskiya"da shagwaba,

Abun ya dan bashi dariya ya kauda fuska sannan ya kara kallon ta,

Tace"za muyi ko?ina son nima duniya taga kyakkyawan mijin da zan aura suga yadda muka yi matukar dacewa Whenever you are creating beauty around you, you are restoring your own soul."

Ya kalleta da karamin murmushi fuskar shi yace"any time u wish"

Tace"tnx u my handsome"

Yayi murmushi ,

Tace"yau zamuje"

Yace"done queen after na dawo aiki I will come se mu tafi ki shirya "

Tai murmushi tace"nagode sosai daka amince"

Ya jinjina kai yace"kitafi gida"

Ta daga mai hannu ta nufi mota ta shiga ta nufi gida,

Seda motar ta ta tashi sannan ya juya ya shiga tashi ya nufi office yana ta tunanin shagwabar ta ,

Faseelat kau tana driving tana sakin murmushi in ta tuno abida,

Abida na hada akwatinta ta zuge ta sabi gyale tayo waje tana cigaba da kuka,

Tana fitowa hjy Rukayya na fitowa ta kalle ta tace"aa ina zakije abida?"

Abida na kuka tai mata banza ta nufi downstairs ,

Hjy Rukayya ta bita da kallo tana mamakin ina za taje haka,

Alhaji na falo zuciyar shi ta cunkushe gaba daya duniyar tai masa kunci ya rika jin amai beyi kokarin tashi ba don baze iya ba ya tarba hannu ya amayo abinda ya keji ya tsaya masa a zuciya sega jini gulama_gulama shi kan shi hankalin shi ya tashi ya rike hannun yana kallon jinin dake ciki ,

Can se ga abida na sauko wa tana kuka tana janye da trolley din ta,

Hakan ya kara tada mai hankali wani aman ya kara yo waje har jinin na diga kasa ga wani a bakin shi,

Duk da haka ita yake ta kallo cos shi yana son matan shi sosai kuma be iyajin zai rabu da ko daya sedai faseelat ta daban ce,

Tana karasa fitowa zata gifta shi ta watsa mai harara tai hanyar waje,

Cakk ta tsaya ganin kamar jini kode idanun ta basu gane mata dede ba?tai saurin juya wa ta kalle shi still jinin de ne,

Ta saki trolley da gudu ta isa wurin shi tana kara volume na kukan ta ta rike hannun shi me jini,

Jikin ta na rawa ta kalle shi ta kuma kallon hannun a dimauce ta fara kwalawa hjy Rukayya kira ,

Hjy Rukayya ta sauko da sauri tun kan ta karaso taga halin da alhaji nura ke ciki ta karaso da gudu jikin ta na rawa tana kuka,

A tare suna kuka suke cewa" alhaji sannu sannu alhaji"

Shi ko hannun shi kawai yake kallo me jinin ,

Hjy Rukayya tai saurin kama shi abida ma ta kama suka fita da shi suka nufi asibity da shi suna isa aka amshe shi aka shiga dashi emergency aka fara bashi temakon gaggawa,

Faseelat ko tana isa gida Ummi ta ganta ta wartsake tana ta kallon ta tai shiru hakanan taji ba school faseelat taje ba,

Bayan minutes aka fito da alhaji yana sheme sun mai alluran bacci aka kai shi rest room aka kwantar ,su hjy abida suna bakin kofa suna ta sharar hawaye abida na regretting abin da tayi,

Ita kuwa jameela ana gyaran ta Mimi na kwashe wa don tun da ta dawo taki komawa school din saboda ko batai attend ba lpy lau ko test ko wata exam in batayi ba lpy lau domin tana tare da big girls da suke harka da lecturers , suka yi ta enjoying life suna kara son junan su ita jameela taso ta jira bayan wedding su cigaba sede ta kasa hakura da jikin Mimi domin ta riga ta saba da shi,

Soyayya su jameela ke ta zuba wa da Khalil Wanda ita a baki kawai ne ko sau daya bata taba jin son shi ba, shi kuwa son ta yake sosai tsakanin shi da Allah kamar zai yi hauka,

Da karfe 12 Khalil yazo kofar gidan su jameela ta fito tana baza kamshi tana mai kallon karya garkuwar jiki,

Yana murmushi yace"barka da fitowa"

Tai murmushi me sauti tace"yawwa ango na"

Yaji dadi sosai yace"insha Allah"

Tai murmushi ta mai wani kallo ,

Yace"dama naxo ne naga yadda kk tashi ko akwai abin da kk so?"

Tace "immm! Ina son zuwa gidan su momcy"

Yace"beauty wai baki gajiya ne kullum momcy momcy anya zaku iya rabuwa kuwa?"

Ta harare shi ta turo lips tace"Baza mu rabu ba har abada after my biki zata rika zuwa nima inna samu lokaci zan rika leka ta"

Yace"to yayi muje ko?"

Ta daga kai suka nufi gidan yana ajiye ta yace"karfe nawa zan dawo ?"

Tace"yau zan jima kasan mun fara tsara yadda za muyi events namu ina son mu gama sai na fada maka yadda muka yi"

Yace"OK se na dawo da Maghreb yayi?"

Ta daga kai,

Yace"ki gaida ta"

Tace"tom nagode seka dawo"ta bude murfin ta fita ta shiga gidan,

Ta samu Mimi na yiwa granny tausa ta mike kafar ta tana mata,

Mimi tace"oyoyo sis "

Jameela tai dariya tace"tnx momcy"

Ta kalli granny tace"tsohuwa ina yini?"

Granny ta harare ta tace"kin kusa tsufan kema kwana nawa ne"

Sukai dariya baki daya ta yaye gyale ta zauna sukaita matsawa granny kafar suna yiwa juna signal har bacci ya dauke ta,

Suna ganin hakan sukai murmushi tare suka sargafe hannuwa akafadun juna suka nufi part din Mimi,

Tun kan su kai Mimi nawa jameela wani kallo ta tsotsi lips tace"ya na ganki haka yau?"

Jameela ta yamutsa fuska tace"wani abu Umma tabani yau da safe tunda ta bani na ke jina wani iri daban"

Mimi tai murmushin jin dadi tace"kwanakinnan fa Allah special taste kikeyi inajin kamar in kwana kan ki"

Jameela tace"ai naso mu bari har after biki amma bazan iya ba nima sede yanzu ya kenan in ban matse din ba?"

Mimi tai dariya tace"aiba sekin matse ba zo kiji"

Ta dora baki kan kunnen jameela tai mata rada,

Jameela ta fiddo ido tace"Allah ?"

Mimi na dariya tace"wlh kuma ki bari ki gani"

Jameela ta rungume ta sosai tana murna tana cewa "I love u momcy u r d best"

Momcy tace"wash!!!"tanajin feeling taja jameela ciki,

Suka tube suka fara aikin daya fi musu dadi akan kome da basa gajiya ,


Alhaji na asibity se 2pm ya farka da sunan abida bakin shi abida ta matso kusa da shi tasa hannu cikin nashi tace"sannu alhaji Allah yabaka lpy"

Muryarshi na rawa yace"plsss abida don't leave me"

Ta daga kai tana hawaye tace"kayi hakuri nayi kuskure "

Ya lumshe ido jin ta hakuran,

Tace"sannu"

Hjy Rukayya ta matso tace"sannu alhaji"

Ya bude ido ya kalleta ya dan daga kai,

Ta kalli hjy abida tace"zan koma gida yanzu zan dawo "

Hjy abida ta daga kai,ita kuma ta juya ta fita ta nufi gida don yanzu yaran sun dawo,

Tana zuwa ta samu yaran sunyi zungum suna ganin ta suka fara tambayar ta daddy ta fada masu suyi masa addua'a yana asibity,

Sukai kasake duk se suka bata tausayi sunyi kamar wasu marayu ta sake wanka ta daukar musu abinci da kayan bukata ta koma asibitin,

Bayan laasar fahad ya dawo aiki wanka kawai yayi ya nufi gidan su faseelat bayan ya isa tafito da doguwar riga black jikinta da stone green da mayafin rigar ,

Tana ta murmushi ya kalleta yace"kinyi kyau"cikin makoshi,

Tai murmushi tace "kamar kai"sukai karamar dariya suka tafi wurin daukar pic din,

Suna zuwa aka fara musu ko kadan faseelat bata wani nuna kunya ba tana ta farin ciki akai musu tana sanye da rigar shi kuma da golden colour shadda, ta dafa kafadar shi ya kalli kafadar yanajin wani iri sannan ya kalli me hoton ya dauke su,

Ta saka milk and green material lace shi kuma yasa green yadi yasha black aiki ta dan kwantar da jiki jikin shi aka dauke su,

Suka sauyo da maroon yadi dukan su tana zaune ta kalle shi suna dariya aka dauka ,

Me pic din yace suna iya tsayawa ya basu suna zaune suna fira jefi_jefi har aka kawo musu fahad ya nuna masa na doguwar riga dana milk lace yace ai masa enlarge dinsu me pic yace yadawo anjima ya amsa,

Sannan suka fito yana ta kallon ta itako tana ta murmushi suka shiga mota suka nufi gida ,

Yana tuki yana dan kallon ta can zuwa yace"yau kina cikin farin ciki"

Ta kalle shi tace"biki na ya kusa mana shine nake doki"

Yayi saurin kallon ta da murmushi fuskar shi,

Ta rufe fuska da hannu biyu ,

Yace"wane events za muyi"

Tace"dinner"

Yace"OK yaushe Friends nawa zasu zo wurin friends din ki?"

Tace"se Monday yanzu fa se jiya muka fiddo anko"

Yace"anko"yayi shiru sannan yace"alright zan biya ankon yan matan sun kai nawa?"

Tai murmushi sosai tana murna tace"basu da yawa naji dadi sosai nagode Allah yabar mu tare"

Yace"amin kina ganin 100k zata ishe su?"

Tace"eh basu da yawa majority duk sunyi aure"

Yace"OK ki bani account number dinki"

Ya mika mata waya ta sa mai suna isa ta bude ta fita bayan sunyi bankwana da shigar ta gida 100k din suka shigo tana murna ta gwadawa Ummi ta kuma bugawa besty din ta a yanzu rabia akan za suje su sayo ankon a dinkawa kowa,

Fahad ya juya ya koma gida yana ta tunanin faseelat besan meyasa ba dandanan seya dafa kafadar shi dede inda ta dafa shi abun yaki goguwa a kan shi,

Yana zuwa gida ya samu marwan yayi dukun_dukun da fuska yana kan mota a parking lot,

Fahad yayi murmushi yafito ya isa wurinshi yace "yaakayi bro?"

Marwan yace"bakomai"ranshi hade,

Fahad yace"tell me mana miye?"

Marwan yace"I don't have any money duk kudina sun kare"

Fahad yace"shine kakewa kumburin?" Yasa hannu aljihu ya fiddo yan 1k sun kai 50 dunkule ya mikawa marwan yace "to gasu"


Marwan ya amsa ya kalli kudin ya kuma kallon fahad batare da godiya ba yace"yaya dan Allah kasa baki amin aure wlh inason nayi aure"

Fahad ya dafa kafadarshi yace"OK zanyi but se mommy tadawo"

Marwan ya bata fuska shifa so yake shima ya angwance,

Fahad yace"nashiga ciki yawuce abinshi"

Part din mommy yafara shiga duk an sauya mai wallpapers an sake furniture's dakin yayi kyau se kuma ya fita ya shiga part dinshi,


Se Maghreb Khalil yaje ya dauko jameela ya meda ita gida,




***********

A Niger bayan Maghreb su mommy suna ta shirin tafiya don gobe tun da safe zasu dau hanyar garinsu aysha,

Aysha nata murna badon komi ba sedan zataga muradinta fahad,

Mommy ta kwashi kaya an musu sha tara ta arziki suna gama park mommy tafita fitsari,

Aysha da take kagare taji muryar fahad wurin network kawai take bukata tai sauri ta dauki number dinshi tai saving a wayarta da heartbeat,


Bayan ishai a nigeria


Gidansu Aliyu jarumi yana zaune da cup a hannu samira tafito da kayan bacci tayi kyau har kiba tayi hakan ya kara mata kyau sosai,

Aliyu yayi saurin dauke ido a kanta ,

Tai murmushi ta zauna Dan nesa dashi tana kallonshi tace"yau ma kanwar kk sha?"

Yayi karamin murmushi yace"yana iya"

Tai murmushi tace"zakayi kadan dinne?"

Yace"eh amma inkin shirya"

Tafashe da dariya tace"to ban shirya ba"

Yayi dariya yace"samira niko"

Ta daga kai ,

Ya tashi zai kamota ta gudu bedroom tana dariya ,

Yana ganin ta shige ya dawo ya kwanta ya kalli silin yana tunani abun ba na kare bane ana batun two weeks ba harka amma bata bukata gashi yace seta nema anya zai cigaba da hakuri kuwa?

Da ishai fahad ya amso enlarge din sun masa kyau sosai hakan yasa ya amshi biyun yakuma sa akara mai biyu,

Biyun gida ya tafi dasu ya kafasu a main Palo sukai gwanin kyau yatsaya yana kallonsu yana murmushi,

Daddy yafito daga sama idonshi ya sauka akan pics din yana murmushi yace"good"


Fahad yace"thanks daddy"

Daddy na rufe baki marwan na fadowa wurin yanata tangadi yana raba hannaye yake cewa "ai min aure kawai inji dadina"

Suka bishi da ido harya shige part dinshi,

Fahad beko kara kallon daddy ba yace"good night daddy"yajuya ya fita,

Daddy nata kallon kofar part din marwan yakoma nashi bedroom din,


Fahad na komawa faseelat yakira sukai good night sannan ya zauna aiki,

Itako suna gamawa setaji tana kewar alhaji ta latso number dinshi taji yanata ring baa dauka ba kira biyu sannan takashe wayar tana tunanin ko yayi bacci ,


A Niger mommy da aysha bawanda yayi dogon bacci aysha na murnar tafiya Nigeria taga fahad dinta eye to eye ita kuma mommy na murna zata kaiwa danta best gifted ever,


Da safe bayan

Please Login or Register in order to submit comment