Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ࡱ> .



 

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~Root Entry FWordDocument1,0TableXData
 P>'KSKS1,rr, 222222224$I*r222ss22s22 ^`^Normal d,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJTA`TDefault Paragraph FontOJPJQJ^Jfi`f Table Normal :V 4
l4a OJPJQJ^J(k`(No List 0V"\<TKPҰ4(Fb| 4:f,Dȉ@`*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_


BOOK 2
<'1


______________

*_Assalamualaikum. Barkanku da wannan lokaci, fatan ansha ruwa lafiya? Anyi salla lafiya?. UBANGIJI ya karSi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, yasa muna a cikin antattun bayi. Ina mana Barka da dawowa filin daga, ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda bazai cutar dani da ku ba. Ka tsarkake min alalamina domin rahamarka. Ka gafarta ma iyayenmu da malamamu damu baki Waya. Ka Wauramu a bisa tafarki madaidaici da bazamuyi dana sani ba. ALLAH ka hanamu cutar da junanmu koda da kalma mara daWi ce.=O_*

_Ayi mana afuwa da jinkirinmu yau da gobe sai ALLAH >p>pd'._

*an ungiyar Bati ku matso nan munada meeting =. Kun san dai AZUMI aka gama ko, goman arshen nan hummmm = karki yarda ki zama a cikin wanda na Waga hannu nace ya ALLAH gasu nan....*
_Bazan dai arasa ba amma gaskiya kada ki yarda sister dan in dai an amsa akwai cakwakiya gaskiya ====<_ 500 kacal ne =

_____________

........Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA Win zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani arfin jikinsa. Har cikin dare ba'a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita so tai ta kawo Maanal a daren sashen AA Win, amma ta fahimci take-taken Abah so yake ya kawo wani sharaWin hora AA Win, dan dama shine ya bata umarnin wucewa da Maanal sashenta sanda suka iso.
Bayan sun baro sashen AA bin bayan Abah tai nasa sashen ta masa magana, amma sai ya nuna mata shi barci yake ji ta barsa dan ALLAH. Haushi ne sosai ya kamata, dan haka fuuu ta baro sashen. Da kallo ya bita ganin yanda ta wuce, sai kuma ya shiga girgiza kansa a fili ya furta,  Fateema son yaranki yayi miki yawa, in dai fushi ne yama sakko dan sai na hora Ajwaad a gidan nan . Daga haka ya shige toilet yana murmushi...

___________&

Zuciyar Babban Yaya cike da wasi-wasi ya nufi sashen Oum ganin har goma saura na dare yau ma Maanal bata koma sashenta ba, ga AA Win kuma ma jikin nasa ya dawo dan yanzu haka wani arin ruwa aka cire masa. Ganin bata a falo ya nufi bedroom Winta. Sai da yay sallama ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Yanayin yanda take a zaune da fiskarta dake cike da damuwa yasa gabansa faWuwa, duk da yasan akwai damuwar yanayin da Auta ke ciki dai.
 Oum baya jin daWi ne? .
Ya faWa cike da damuwa matua yana kaiwa kusa da ita zaune. Idanu ta zuba masa kawai, dan duk yanda taso yin murmushi ko sassauta damuwar tata hakan ya gagara sam. Sai ma walla kaWan da suka taru mata a idon. Ai sai babban Yaya ya sake rikicewa matua.
Hannunsa ta rio tana girgiza masa kai,  Kaga kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ba.
 Haba Oum yazan yarda da hakan, kalla fa yanda damuwa ta bayyana a fuskarki sosai. Dan ALLAH in ma dan ciwon Auta ne ki daina tada hankalinki komai zai wuce kamar ba'ayi ba in sha ALLAHU. Dan yanzu hakama barci yake yi na cire masa drip Win dan ya are. Jikinsa sam kuma babu zafi da ganin yanda yake barci ma kasan Alhamdullah babu wani damuwa ba kamar jiya da yinin yau ba. Yanzu haka ma nazo ne akan batun Maanal, nazata zata kwana a can ne yau ai tunda jikin da sauin itama? .
Sosai Sacin ran Oum ya ara bayyana akan fuskarta, ta ce,  Akan hakanne ai Abanku ya Sata min rai Fadeel, yace wai bazata koma can ba yanzu sai bayan salla ya koyama Ajwaad hankali. Wane hankali kuma ake buatar koyama yaron nan bayan wanda ya koya. Kama ajiye batun wahalar ciwo da yasha a shekarun baya, a kwanakin nan kawai kaga hanlin daya shiga fa da wanda yake a ciki yanzu. Kowa fa a rayuwa da irin yanayinsa da kuma addararsa, amma Abanku ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar Ajwaad nada zurfin ciki ne. Yanda Maanal keda muhimmanci a garesa bana tunanin dole sai ya buWe baki yace wani abu za'a yarda dashi. Shin so yake na rasa yarona ne saboda wannan tsaurin nasa? . Ta are maganar muryarta na rawa kamar zata saki kuka.
Cikin sake rikicewa sosai Babban Yaya ya shiga girgiza mata kai nasa idanun na kaWawa sosai shima.  Dan ALLAH Oum ki kwantar da hankalinki, ni bara naje na samesa yanzu. Ko kuma ki kira Baba ko Abba ki haWashi da su.....
 Saboda ban isa da gidana ba kenan ko mai uwa? . Atare babban Yaya da Oum suka juya da sauri suna kallonsa, arasa shigowa cikin Wakin Abah yayi, cikin nuna Sacin rai sosai ya cigaba da faWin,  Saboda biyan buatar taka uwar ni a kira nawa iyayen a haWani da su. Lallai Fadeel sannu, nace sannu kaji ko! .
 Kayi hauri Abah ni ba haka nake nufi ba, amma Oum fa......
 Malam tashi ka wuce sai da safe.
Abah ya sake katseshi cikin sake nuna Sacin rai. Kallon Oum Babban yaya yayi idanunsa na sake kaWewa, kanta ta jinjina masa alamar yaje Win. Dan haka ya mie kawai ya nufi ofa. Da kallo Abah ya bisa, sai kuma ya girgiza kai a zuciyarsa yana ayyana (su dai akan uwarsu kowa ma ya mutu har liman babu ruwansu). A fili kam dubansa ya maida kan Oum data Wauke kanta gefe tamkar ma bata san da shi ba a Wakin. Sai kuma ta yunura zata mie. Yasan mi zatayi, dan haka cike da bada umarni ya ce,  Koma ki zauna .
Komawar tayi ta zauna, kafin ta Wago idanunta da suka sake kaWewa a karo na farko ta kallesa, aiko ya sake yin kicin-kicin da fuska harda Wan willa mata hararar data sakata janye idanun nata a kansa sannan ya furta,  Oh ke yanzu saboda na yanke hukuncin daya dace akan Wanki shine kika Wauki fushi da ni kin kira babban Wanki kina sanar masa kuyi min taron dangi saboda ban isa nace ga yanda za'ai ba .
Idanu Oum ta Wan rumtse kaWan, sai kuma ta buWe a kansa. Baki ta buWe kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda wallar da suka cika mata idanu. auke nasa yay dan yasan yanzu sai ta karya masa zuciya, shi kuma a wannan karon ya Wauka aniyar tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, dolene ya hukunta Ajwaad kodan ya sake sanin muhimmancin Maanal. Bazai yiwu ya samu aurenta a Sagas ba su kuma bashi ita a Sagas. oarin barin Wakin yayi, sai Oum kawai ta saki hawayen da take riewa cikin muryar kuka ta ce,  So kuke sai kun kashe min shi hankalinku zai kwanta ko Gadanga, yanzu horon da aninka yay masa kawai bai wadatar a yafe masa ba .
Murmushi Abah daya tsaya cak tun fara maganarta ya saki a hankali, sai kuma ya maida fuskarsa ya haWe kafin ya juyo yana kallonta daga inda yake tsayen.  Rafeeq bai hora Wanki ba, takarar nema sukai yay muku adalci ya sadaukar saboda yayyawar zuciyarsa, da kuma nasan zai yi hakan sai na hana masa . Ya are maganar yana mai juyawa ya fice abinsa. Wani irin ululun abu ne ya sake tokare wuyan Oum, har zuciyarta na tunzurata akan takai Maanal sashen Ajwaad koma miza'ayi ayin mana.......


___________&

Alamun shigowarsa ya sata dakatawa daga kai-kawon da takeyi, zama tai kamar ba ita ba ta nutsu a bakin gadonsa tare da Waukar littafin addu'oin sa dake a bed side drawer ta fara karantawa. Da farko Abah daya shigo ransa a Sace sam bai ganta ba. Sai da ta Wago ta kallesa cikin tausasa harshe matua ta furta,  Sannu da shigowa . Sannan ya kalleta. Ciki-ciki ya amsa mata, dan haka ta taso da ar sassarfa tana faWin,  Lafiya kuwa? Naga kamar ranka a Sace? . Tsaki yaja mai arfi, sai kuma ya wullar da wayarsa a saman gadon nasa shima yana kaiwa zaune hannunsa akan goshinsa yana murzawa.  Fateema ce ke neman Satan rai Kamila .
oyayyan murmushi Mamy ta saki, a zahiri kam cike da damuwa ta ce,  A haba kodai baka fahimta bane, amma nasan bazata Sata maka rai da son ranta ba yallanSai.
 Mtsoww!! Bazaki gane ba Kamila, ita dai sam bata gajiya da rikici akan aanta, dokar dana kafa jiya akan komawar Maanal sashen Ajwaad shine taketa faman fushi, yanzu naje mata sai da safe na samu ta tasa babban Wanta gaba tana faWa masa, shiko yana bada shawarar a haWani da iyayena.
Sosai Mamy takai zaune yanzu kam, hannunsa ta kamo cikin nata cike da kulawa.  Kayi hauri, zan sameta muyi nagana ta yanda zata fahimta. Dan tabbas Ajwaad ya cancanci a fara horashi kafin a bashi yarinyar nan kodan halaccin iyayenta da basu duba abinda ya faru a baya ba suka sake bashi batare da ko tada magana ba. Taurin kan yaron nan ne yayi yawa, ya kamata ya fahimci ba komai akema taurin kai ba a rayuwa....
 Abinda nake son ta fahimta kenan ai nima Kamila. Amma tamai ta nutsu ta saurareni, ni kuma so nake mu rabashi da halin kodan bambancin dake a tsakanin jiyansa da yau Winsa .
 Karka damu zata fahimta in sha ALLAHU. Ka bata lokaci ta huce yanzu sai mu haWu muyi magana. Idan ma ta kama Maanal Win ta dawo sashena da zama to, dan in ba hakaba bazai damu ba
an jim Abah yayi, sai kuma ya jinjina kansa cike da gamsuwa ya ce,  Kumafa kinzo da shawara Kamila, dan in har Maanal na a sashen Fateema ba'a rabu da bukar bane an haifi habu za'ai. Dan Wan nata dai can zai koma ya tare abinsa, kinga kuwa bazai damu ba.
 Tabbas hakan ce zata kasance . Cewar Mamy wani farin ciki na ratsa mata zuciya na nasara. Abah kuwa da bai san dawan garin ba ya sake furta,  To ai zanyi maganin abun, bari dai ya samu lafiya .
 ALLAH ya bada iko, ina goyon bayanka kuma Wari bisa Wari a wannan gaSar. Dan in aka biye ta Mamansu haka za'a mika masa ita kaga ya samu damar cigaba da mana abinda yaso tunda ta shagwaSa shi daga ita har an uwan nasa. Sun nuna masa komai ya nema sai ya samu komai girman sa .
Sosai kalaman Mamy ke shigar Abah, yana kuma jin gamsuwa da su da tasirinsu warai da gaske a zuciyarsa fiye da yanda take ma fatan ya fahimta Win.........
'


*(Mamy=. Mamy9&. Mamy=.
=ب. Matar nan ko>. Hummmm=%.)*

_Amin afuwa dan wlhy mura nake mai zafi, idan na samu saui za'afi ganin page Win da tsaho..._









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_


*_BOOK 2_*
<'2


______________

........A safiyar washe gari har kusan sha biyu Abah baiga idon Oum ba a gidan. Dan haka ya fahimci fushin nata fa na gaske ne. Shi dariya ma ta bashi, dan haka shima ya shareta. Har yamma dai bai ganta Win ba, ya dai daure har akai sallar magrib da isha'i sannan ya nufi sashenta. Ko'ina tsaff yake da amshi, sai masu aikinta daya samu a falon asa suna hira. Suka gaisheshi da girmamawa ya amsa musu da kulawa ya wuce.
Oum na zaune a doguwar kujera Maanal kwance ta Wora kanta a cinyarta su duka idanunsu a tv. Sallamar Abahn ta saka Maanal ta shi zaune, kanta a asa tai masa sannu da gaida shi. Shima fuska Wauke da murmushi ya amsa mata tare da tambayarta ciwon kanta. A tausashe ta ce,  Ya daina Abah Alhamdullah .
 Masha ALLAH ai haka ake so Wiyar Abanta ar albarka.
Murmushi Maanal tayi mai faWi, sai kuma ta mie tsam, dining area ta nufa ta Wakko ruwa a freight tazo ta ajiye gabansa, cike da dabara ta shige bedroom Win Oum. Shi ko Abah cike da mamaki sosai ya ke kallon Oum ganin tunda ya shigo falon bata ko Waga ido ta kallesa ba. Sai ma wani sake ciccin magani take. Ji yay kamar ya juya ya fita ya bar mata sashen. Har yay kamar zai juyan sai kuma ya dakata, ruwan da Maanal ta ajiye masa ya Wauka ya sha kafin ya dubeta da yau. A Wan kausashe yace,  Har yanzu fushin ne kenan? Dan na hana ki bama Wanki matarsa shine nima kika Siye min ganinki yini guda Fateema? Ni kenan ban isa sharWanta doka a fahimceni ba ashe dai?. Miyasa kike da son kanki da yawa akan aanki ne wai? .
Karo na farko ta Wago ta kallesa, idannunta cike da hawaye. Muryata na Wan rawa ta ce,  Miye abun son kai anan Abahn su?. Yaron nan kodan halin daya shiga ai ya cancanci a yafe masa a kuma fahimcesa. Eh naji shi mai kuskure ne, amma koda bai fito yace yana son Maanal ba halin daya shiga kawai amsa ce. Amma sai ace baza'a bashi matarsa ba har sai bayan salla. Haba Gadanga ka fahimta mana, baifa da lafiya, yana buatar mai kulawa da shi..... hawaye suka shiga ziraro mata batare data kai arshen zancen ba. Shi Abah sai abun ma ya fara bashi dariya. Yanzu dan kawai yace Maanal bazata tare ba sai bayan salla shine abin kuskure har ta zauna tana kuka. Oh ya rabba, Fateemansa sarkin daru kenan. Kansa kawai ya girgiza, batare da yace komai ba ya juya zai bar mata Wakin, dan dole ya turza sosai ta yanda ita da Wan nata zasu san ba wasa yake akan al'amarin ba. Da sauri ta ce,  Gadanga! . Tsayawa yay, tare da Wan waiwayowa ya kalleta. Sai kawai ta sake sakar masa kuka. Da sauri ya fice abinsa, dan in tana irin wannan darun nata yafi buatar yin nesa da ita, idan ba haka ba sai ta karya masa zuciya ta sakashi yin abinda bai niyyar ba.
Kai tsaye daga sashen Oum Win sashen AA ya nufa, dan son sake duba jikinsa, saboda yau ma a kwance ya yini ko salla bai fita ba sakamakon rashin warin jiki da yake fama da shi har yanzu. A sashen ya samu babban Yaya da Fawzan a tare da shi, sai dai shi barci ma yake AA Win, su kuma suna ar hirarsu. Cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da kulawa yana taSa goshin AA dake barci. Jikinsa babu zafi kamar jiya, dan da ganin ma yanda yake barcin zaka san Alhmdllh. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya Wago idonsa akan su Babban Yaya ya ce,  Alhamdullah yanzu kam babu zazzaSin ai. Ya kamata kuje ku kwanta ku huta kuma ni bara na zauna da shi yau .
Idanu Fawzan ya Wan waro waje da faWin,  Haba Abah da kanka. Ai sai Oum ta zane mu.
Dariya Abah yayi, hakama babban Yaya ya murmusa tare da faWin,  A'a Abah mun yafe maka kaje abinka. Dan gaskiyar Fawzan Oum zata iya zane mu ne .
Nan ma murmushi kawai Abah yayi, sai kuma ya zauna suka Wan tattauna akan jikin AA Win da tun shekaran jiya da suka iso daga Kano sai a hankali, dan duk dauriyarsa sai da ya sake kaiwa kwance. Gashi ya kuma kafe bazai je asibiti ba, sai nan doctor yazo yake duba shi. Bayan Abah ya musu sallama ya fito babban Yaya ya biyosa da sauri. Dakatawa yayi yana kallonsa harya araso.
 Lafiya dai ko Fadeel? .
Cike da ladabi babban Yaya ya ce,  Eh Abah, kawai dai akan batun tarewar Maanal Win ne dai, dan ALLAH kayi hauri a bashi matarsa, ALLAH bana jin daWin yanda nake ganin Oum a cikin damuwa. Abubuwan sun mata yawa, ga ciwon Ajwaad Win ga kuma wannan batun. Abah harfa rama naga tamun yau ALLAH  . Babban yaya ya are maganar kamar zai yi kuka.
Murmushi Abah yayi, sai kuma ya Wan furzar da iska tare da faWin,  Wato Fadeel ya kamata muma kammu adalci muyima yarinyar da iyayenta suma. Dan tabbas da nasan Rafeeq zai zagaye yay wannan aikin sai na hanashi, saboda nifa har yanzu ina akan bakana sai Ajwaad ya sauke kansa asa yazo da bakinsa ya nema na bashi Maanal bayan ya nema afuwarta, idan ma ta kama ya faWa mana dalilinsa na wannan dagewar .
Kai sosai Babban Yaya ya jinjina, ya ce,  Na fahimceka Abah, kuma nima ina bayanka. Sai dai hakan bazai hana na baka hauri ba na kuma nemawa Auta afuwa. Kasanshi da zurfin ciki, maybe akwai abinda bamu sani ba game da al'amarin, amma wlhy mu shaida ne Ajwaad na son Maanal matua. Kuma sai nake ga mata da miji sai ALLAH, kamar barinsu su kasance a taren zai sa su sasanta kansu kodan soyayyar da suke ma juna su duka
 Humm wace soyayya kuma Fadeel, yana sonta zai watsar da al'amarinta ya zauna jan jiki a sanda ya sake ganinta, to Miye na girman kan, aure abin wasa ne? Barshi dai a bata tare Win ba, zai fi jin zafin wannan bulalar fiye da wadda kake hangen. Ina son hakan ya zama izina a garesa ya canja wannan halin nashi kodan yanzu shi mai iyali ne nanda wani lokaci haihuwa za'a fara masa .
 Tabbas aure ba abin wasa bane Abah, mu kuma masu biyayya ne ga kowanne irin hukunci daga gareku. Amma idan mukai dubi da halin kawai daya shiga akan tsoron rasata abun muyi nazari ne. Ta wani Sangaren ina tsoron kar dangin mahaifinta ne fa sukai masa wani abun tun wancan lokaci tunda dama kakarsu ta nuna bata son aurenmu da su Shaheedeh. Abah kasan zata iya bin kowacce hanya domin cin nasara, sannan shi kansa asiri gaskiya ne fa .
Sosai Abah ke kallon babban Yaya. Zuciyarsa nata faman kai-kawo akan kalamansa. Sai dai kuma baice komai ba akan hakan illa nufar hanyar fita da faWin,  Zanyi nazari, amma ina akan bakana na bazata tare ba yanzu ku cigaba da jiyyarsa ALLAH ya tashi kafaWunsa . Daga haka ya fice abinsa. Da kallo kawai Babban Yaya ya bishi, shi kansa al'amarin Autan nasu na damunsa, da rikita shi, amma dai koma miye ai ta are tunda an Waura, komai mizai biyo baya mai saui ne insha ALLAHU......

Murmushi mai faWi da yalwa Mamy ta saki, dan dukan tattaunawar Abah da su Babban Yaya a cikin kunnenta ta kasance. Tayi matuar yin farin cikin yanda shirinta yay tasiri akan Abah cikin saui haka, dan sam batayi zaton zai amshi batun da muhimmanci ba duba da sanda take tsara masa yin hakan yi yay kamar maganar tata bata tasirantu a gareshi ba. Shiyyasa taga ar gwal Win tashi har yanzu babu fara'a ashe an sake wargaza mata shiri ne. Wani murmushin ta sake saki haoranta na bayyana sosai, sai kuma ta gimtse fuska da gyara yanayinta ta arasa shigowa falon sosai tana sallama.
A tare Fawzan da Babban Yaya suka Wago suna kallonta tare da amsa sallamar. Cikin yanayin da take nuna musu na kawaici ta amsa gaisuwar da suke mata, tare da tambayarsu yaya mai jikin. Suma cikin girmamawar da suke bata suka tabbatar mata da saui, yanama yin barci ne. Kai kawai ta jinjina musu, batare data sake cewa komai ba ta nufi bedroom Win AA Win. Barcin kuwa yake har yanzu, fuskarsa tayi fayau. Guntun murmushi ta saki a hankali, dan tasan tabbas aunar da takemasa dabance a cikinsu, tun daga Waukar cikinsa har haihuwarsa duk da wahalar data sha shi Win na musamman ne a gare ta. A karo na biyu ta sake sakin murmushin, sai kuma ta kai zaune kusa da shi gab tare da kai hannun ta shafa yalwatacciyar sumar kansa dake a hargitse. Addu'ar samun lafiya tai masa mai Worewa tsahon mintuna kafin ta tashi ta fita....
A hankali AA da tun tsaiwar Mamyn a kansa ya farka ya buWe idanunsa ya bita da kallo, sai da ta maida ofar ta rufe ya sake maidasu ya lumshe luuuu. Ya jima kafin ya sake buWesu, sai dai sun masa nauyi sosai alamar barci bai gama sakinsa ba. So yake ya tashi zaune, sai dai kansa juya masa yake yi, dan haka dole ya sake maida idanun ya rufe barcin ya ara yin awan gaba da shi cike da mafarkin Mamy da haka kawai ganinta a kansa tsaye ya tsaya masa a rai duk da yasan ba wani abu mara yau tazo tayi a garesa ba, amma dai zuciyarsa ta rie abun matua..........
'



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_


*_BOOK 2_*
<'3


______________


........Mamy kam a inda tabar su Fawzan anan ta samesu, sai dai yanzu Nibras ta aru.
an tsurama Nibras Win datai mata wani iri idanu tayi, sai kuma cikin tausasawa ta furta,  Nibras baki da lafiya ne? .
Kallon Nibras Win Fawzan da Babban Yaya suma duk sukayi saboda jin furicin Mamyn. Cikin damuwa Fawzan ya ce,  Mamy gara kam ki tambayeta ke, dan tun jiya nima nake fama da ita amma sai tace ba komai gajiyar biki ce wai.
Cikin jinjina kai Mamyn tace,  Itama gajiyar bikin akwaita Win ai, dama sai a hankali zata saki kowa duk da ga wani na tunkarowa kuma dai. Kinga kije ki samu ki gasa jikinki da ruwa mai zafi sosai sai kisha pracitemol ki kwanta abinki kiji. ALLAH ya ara saui .
Ji Nibras tai kamar ta zageta, amma sai ta daure ta jinjina mata kai kawai da faWin,  To Mamy . Daga haka ta juya ta fita zuciyarta na mata zafi da una matua. Tazo ne dan taga fuskar AA ko zataji sassaucin abinda ke cizon zuciyarta, amma Mamyn ta wani korota. Ba komai zata dawo ne, dan in har yau Fawzan anan zai kwana ALLAH sai dai su kwana tare a sashen AA Win. Koba komai ta rage raWaWin kishin dake dafa mata zuciya. Sau in ma har yanzu ko sau Waya bataga Maanal a sashen nashi ba..

Fitar Nibras ya saka Mamy ma yunurin tafiya, amma sai Babban Yaya ya dakatar da ita cikin ladabi. Tsayawa tai tana kallonsu su duka. Fawzan ya ce,  Mamy dan ALLAH magana zamuyi ne .
Wani irin sanyi mai silalar da kuzari ne ya shiga bin jijiyiyin jininta

Please Login or Register in order to submit comment