Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*_=؞άAJIYA A DUHU....=؞ά_*




*_Bilyn Abdull ce >Ψέ<Ψϋί_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ™ai._

*_My TikTok account =ΨGά_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=ΨGά<Ψϋί_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=Ψή=Ψή<ΨΓί<ΨΓί_

*_BOOK 2_*
<Ψέώ–'5ώγ 8ώγ


______________


.........Dariya yay Fawzan yay tare da shafa kansa ya taSe baki. AA ya wani Wan Wage masa gira. Harga ALLAH abun yazo ma Yaya Fawzan a bazata, dan haka yama kasa magana. Shi kansa AA yanda Yaya Fawzan Win yayi ya bashi dariya, amma sai ya dake dan yau shima sai ya Wan rama ko yayane daga tsiyar da Yaya Fawzan Win ke masa kullum.
           To Abah kallon ya isa haka mana .
     Ya Fawzan ya faWa yana hararar AA. Murmushi AA yay a karo na farko, cike da neman magana ya ce,  Yaushe aka fara? .
          Baki buWe Ya Fawzan ya ce,  Mi Win? .
    Gira AA ya Waga masa tare da faWin,  Ai ka gane. Yau dai ALLAH ya kama min kai .
      Dariya sosai Fawzan ya sanya, sai kawai ya rungume AA Win. Shima AA Win sai kawai ya hau dariya. Kusan minti biyu suna a haka kafin Ya Fawzan yaja hannun AA Win suka shiga mota. Ran AA fes da farin ciki ya ce,  Amma Yaya bata maka ™an™anta ba? .
        Murmushi Fawzan yayi idonsa akan ™anin nasa.  Ajwaad ai ita mace bata ™an™anta wa namiji. Kamar yanda mace bata yima namiji girma. Najma sa'ar Maanal ce fa. Kai ba gashi harka galla ma Lilly cizo ba tana mana amaye-amaye .
      Murmushi kawai AA Win yay shima ya girgiza kai. Shima Ya Fawzan Win sai yay dariya kawai, dan yasan Ajwaad da rashin son magana. Da ΄ar damuwa ya ce,  Ina sonta sosai, dan tanada tarbiyya. Zan iya cemaka ma kusan tarbiyyarmu iri Waya ce. Dan abubuwan Aunty Majdiya da yawa suna kamanceceniya dana Oum. A lokacin bikinku muka dai-dai ta, Ajwaad sam bana samun farin ciki irin na magidanci a gidansa. Bawai bamu samu haihuwar bane damuwata, nasan wannan lokaci ne, amma ita Mamy wannan take kallo kawai, shiyyasa ta sake zaSa min wata matar .
      Da sauri AA ya kallesa,  Wata matar? .
      Kai Fawzan ya jinjina masa yana murmushi.  Jiyan nan ta bani hotonta da number ta akan nayi magana da ita. Ajwaad bazan Soye maka ba, wasu abubuwa na Mamy a Wan tsakanin nan na saka zuciyata girgiza. Miyyasa take damuwa da sai itace zata zaSa mana matan aure? Miyasa Oum ita bata taSa kwatanta haka ba. Sannan abinda ke cimin zuciya matan ma duk bana ™warai ba. Kalla Babban Yaya, ALLAH nasan sam baya jin daWin zama da Saheeba, kawai dai bazaiyi magana bane. Kalla wannan yarinyar da ake neman manna maka Nuratu, wlhy ban ™ara jin tsanar yarinyar nan ba sai a wannan zaman. Kuna Chaina Win nan fa sai da naci ubanta wai ita zatama Oum rashin kunya....
     Wani irin kallon Sacin rai AA kema Yaya Fawzan, shifa da'a taSa Oum garama duk uwar ubanda za'ai ayi. Fawzan ya cigaba da faWin,  Wlhy kuwa, amma abinda ya bani mamaki da naje ina zaginta a sashen Mamy sai Mamy ta canja fuska, har tana faWin muma ni da babban yaya yanzun mun fara koyon halinka na ™in danginta. Nayi ™o™arin ta fahimta amma wlhy tama korini wai na bar mata sashe. Na jima abin nan na cimin zuciya. Ni yanzu babban tashin hankalina ban san yanda zan yi da wannan yarinyar data kawo ba, nama rasa ina tasan yarinyar wai daga gidan sarkin kano take, ko miye ala™arta da ΄an gidan oho .
        Gaba Waya ma AA ya kasa magana, dan bai taSa tunanin Mamy zata bar sauran ΄an uwansa su fara fahimtar wacece ita ba. Ya jima shiru, kafin ya kalla Yaya Fawzan da shima ya tafi tunani. Cikin lallashi ya furta,  Yaya badai kana son yarinyar nan ba? .
      Cikin sauke ajiyar zuciya Ya Fawzan ya ce,  Sosai Ajwaad, Wan zan iya cewa bayan Amaal Najma itace mace ta biyu da nake jin sonta har ™asan zuciyata.
         Tunda har kana sonta ka daina damuwa da batun Mamy, sannan kada kama yarinyar magana barni da su.....
       Uhm-uhm Ajwaad bana son kama nuna ma Mamy na maka wannan maganar, dan bayan ni Win bana son ta fahimci wani yasan wata matsala makamanciyar wannan game da ita, sannan ka sani Mamy duk da ta bama Oum mu na har abada hakkinta na uwa na nan a kammu bai kau ba, kuma dole ne mu saukesa in har muna son zama lafiya. In har auren yarinyar shine zai sakata a farin ciki zanyi sai na haWa da Najma Win .
     Murmushi mai ciwo AA yayi, sai kuma ya girgiza kansa.  Yaya in dai har ba kaine ke da ra'ayin tara matan haka ba baka da wani dalilin yin hakan saboda umarnin Mamy, eh ita uwace, komai zamu iya yi a gareta, amma addini bai yarda harda cutuwa ba. Koka faWa ko kai shiru kai hakan a gareka cutuwa ne. Ban sani ba ko ni kaWai ne keda wannan matsalar a cikinku, bazan iya zama da mace fiye da Waya ba dan ina da ™yan™yami, zan ma iya rantse maka bayan Manaal bazan iya haWa jikina da kowace mace ba, dan ita kaWai ce nake jin yin nutsuwar hakan batare da jin komai a raina na ™yan™yami ba. Amma mizaisa kace zaka haWa mata uku kaje wajen waccan kai amfani da ita ka koma wajen waccen like wani namamajo haba. Ai ko addini daya bamu damar yin hakan yace idan zamuyi adalci, sannan ga waWanda basa iya kauda kansu ga wasu mata. Ni kuma harga ALLAH ma nasan ko na sakan Waya bazan iyama wata adalcin haWata da Maanal ba. Dan haka Yaya be a man Please, ka rasa soyayyarka ta farko kayi ha™uri kayi juriya daga kai har Babban Yaya da ni na kasa a cikinku, sannan kunyima Mamy biyayyar amsar zaSinta, ya kama a wannan karon ka bama zuciyarka abinda take so kodan ka samu farin ciki, dan banga ta inda wannan wawuyar matar taka zata canja ba (Kayi hakuri na zageta a gabanka) .

      Murmushi Fawzan yayi, wata irin ™aunar ™anin nashi na ratsa shi. Tabbas sune yayunsa, amma Ajwaad ya fisu ™arfin zuciya da rashin tsoro, shi fa in dai addini bai hanashi abububa to babu mai tankwarashi yinsa. Ko iyayensu bazai ce bazayi ba kai tsaye, amma zai bi ta hanyoyi daban-daban ya gujema abin. Kalla aurensa da Nuratu, kusan shekara shida fa kenan ana abu Waya amma yaron nan yasan duk ™ulumboton da zai yi ya zame. A yanzu ma da yake tunanin ya mi™a wuya gashi yana tabbatar masa bazai taSa haWa Maanal da wata ba, shi ™yan™yamin ma matan yake, chai akwai bada™ala kenan a gidan nan, yanda dangin Mamy suka shiryama auren nan ashe AA zai taro musu match. Aiko duk ma mi za'ayi sai dai ayi suna bayan Wan ™aninsu....
       A hankali ya kai hannu ya dafa kafaWar AA dake danna waya yana wani Wan munafukin murmushi. Sai kuma ya Wan le™a yaga uwar mi yake kallo. Hotunan Maanal ne da alama kuma yanzu take turosu, yana le™owar AA ya kife wayar cike da shagwaSa ya ce,  Yaya ba ™yau fa le™en asiri .
     Dariya Fawzan yayi sosai, ya ce,  Ganin Lillyn ne le™en asiri kenan. Kai ni fa wlhy kallon Maanal nake kamar tare aka haifemu a gidan nan, dan ko sanda bama tare sai na dinga jin kamar an cire mana wani Sangare na gidan ne, data dawo sai naga mun cika cif, kai tsaye mu huWu nake kallo a matsayin ΄a΄a a gidan nan. Ban sani ba kodan a gabammu ta tashi ne oho .
     Murmushi AA yayi yana sauke ajiyar zuciya kawai. Yaya Fawzan ya cigaba da faWin,  Na gamsu da shawarar ka Auta, amma kai ya kake ganin zamu Sullowa al'amarin, ni bana son Mamy ta fito da al'amarin nan fili harma wani ya kalleta da wani abu daban, dan tunda har na fara wannan tunanin na miyasa take son zaSa mana mata ALLAH wasu ma zasuyi. Ko kai na tabbata zakaje kaita tunane-tunane ne yanzu
        Tausayin yaya Fawzan AA yaji a ransa, dan da yasan yanda yasan wacece Mamy da bai faWi haka ba. A fili kam sai ya ce,  Karka damu ka bar komai a hannuna .
       Ka faWa min me zakayi mana? .
 Zanyi magana da Aba, bayan sallar nan kawai ayi biki .
      Kai baiyi kusa ba Auta, yarinyar fa bata kammala makaranta ba .
 Ba wani kusa Yaya, makaranta kuwa ta gama a Wakinta. Ai aure bai hana karatu, haka karatu bai hana aure. Mu shaida ne akan hakan tunda Oum hatta Secondary a gidan aure tayi .
           Hakane na fahimta. ALLAH ya shige mana gaba .
     Amin ya rabbi. Yanzu yarinyar mika bata na gift Win salla .
         To baban soyayya, ka manta nace maka ko Oum bata sani ba .
     Tadai barku Yaya, Oum ai ba uwar banza bace idonta na'a kan dukkan notsinmu. Manta da wani kar kowa ya sani muje a saya mata gift .
    Yay maganar yana kallon agogon hannunsa. Murmushi kawai Fawzan yayi, a ransa yana jin daWin samun Ajwaad a matsayin ™ani. Key ya lalubo a jikinsa ya tada motar suka fice a gidan......

      _________&

       YAU TAKE SALLAH

    Ta kowane Sangare yau bakunan Waukacin musulmai a buWe yake da murmushin farin cikin zagayowar wannan babbar rana da akan risketa ne sau biyu rak a shekara. Farin ciki ne da baya Soyuwa a fuskokin yara da manya maza da mata. Tako ina anguwanni sun kacame da ™amshin girke-girke na musamman. Sai kuma shiri da kowa keyi na sallatar idi.
      Anan gidan Darma ma hakan take, dan tunda akai sallar asuba Oum bata bar kowa ya koma barci a yaran ba. Tuni masu wanka sun fara, masu taya aikin haWa abinci sun fara. Zuwa bakwai kowa ya gama shirinsa gwanin sha'awa kamar ka sacesu ka gudu. Baka jin komai sai ™amshin turarurruka masu ratsa zuciya. A irin wannan ranar tako wace shekara abincin da ake karyawa da shi kafin tafiya sallar idi ana samar da shi ne daga sashen Mamy, dan haka kowa na kammala shirinsa can yake tafiya. Dama masu aiki duk can suke tattaruwa a haWa abincin. Su kuma masu haWa abincin salla suna anan sashen Oum ne, idan an dawo anan ake yada zango.
Tuni Hajiya Oum tauraruwar Abah ta kaWa kan yammatanta zuwa sashen Mamy Win. Tayi ™yau harta gaji, kodan Oum Win ba haihuwa tayi akai-akai ba tana nan da ™yanta da ™yawun jiki kai kace ma itace amaryar gidan. Dan koda suka shigo harga ALLAH sai da Mamy taji zuciyarta ta motsa da salon gayun Oum Win, ba yaune farko ba, koda fita zasuyi tare har shakkar kwalliyar Oum take ji dan Oum akwai gayu. Cike da dakewa Mamy ta ™awata fuskarta da murmushin dole suka rungume juna ita da Oum Win tare da yin happy salla. Dai-dai nan Abah da Yaya Fawzan suka shigo, babu kunya ya rungume Oum yana raWa mata happy salla a kunne. Murmushi tayi ta amsa masa cike da jin nauyin yaran. Matsawa yay ya rungume Mamy data cika tai fam a zuciya itama. A bayyane yace mata happy salla, sai hakan ya sake ™untata ta taji a ranta wani abu ya faWama Oum ita bai faWa mata ba. Fawzan ma Oum ya Wan fara rungumewa yay mata Happy salla kafin Mamy, sai Nibras data shigo yanzu cikin kwalliya dan yin hakan kamar al'adar gidan ce a duk irin wannan ranar. Sam hankalin Nibras a son ganin AA yake kawai, dan haka a fisge tacema Fawzan Win happy salla kawai ta matsa ta rungume Oum sannan ta matsa ga Mamy, Abah kuma ta risina ta gaisheshi shima tamai happy salla. A lokacin da Fawzan ke rungume Nibras ido suka haWa da Najma. Ta wani Wauke kai gefe idanunta cike da kishi. Murmushin yayi, kafin ya nufi ta inda take cike da iya taku yay kamar zai Wauka abu a dining, cikin kunneta ya ce,  Sorry love a huce happy salla .
      Dai-dai nan Saheeba da Babban yaya da yara suma suka shigo........
'ώ








*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ΄ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =Ψή=ΨOή_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =Ψ-ή=ΨOή_*
*_Typing=Ψςά_*








*_=؞άAJIYA A DUHU....=؞ά_*




*_Bilyn Abdull ce >Ψέ<Ψϋί_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ™ai._

*_My TikTok account =ΨGά_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=ΨGά<Ψϋί_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=Ψή=Ψή<ΨΓί<ΨΓί_

*_BOOK 2_*
<Ψέώ–'5ώγ 9ώγ


______________


.......Suma dai haka sukaje suka rungume su Oum Babban yaya harda Abah ita kuma ta risina ta gaida Abah, Fawzan da Babban Yaya ma suka rungume juna. Kamar an saita dai-dai nan AA ya shigo shima. Da Abah, Babban Yaya, Fawzan, AA Win duk farrar shadda ce da akaima Winkin babbar riga na zamani, sai dai kowa da kalar nashi design Win. AA bai damu da saka manyan kaya ba, shiyyasa idan ya saka sai su masa wani masifar ™yau. A haka ma bai saka babbar rigar da hular ba duk suna a hannunsa. Sai wata ΄ar shopping bag mai shegen ™yau da tambarin MAWAAD a jiki a hannunsa. A kaikaice ya gama kalle falon amma bai hango zinariyarsa ba. Cikin dakewarsa ya ™arasa ya fara rungume Oum tare da mata Barka da salla. Ta shafa fuskarsa da murmushi ta amsa masa. Shima murmushin yayi ya buWe bag Win hannunsa ya fiddo wani Wan ™ya™y™yawan box fari tas ya buWe. HaWaWWen agogo ne new design daga MAWAAD ya ciro, hannunta ya kama ya cire agogon data saka ya saka mata wannan tare da zobensa shima mai ™yau, sai ya kama hannun ya sumbata. Hawaye ne suka cika idon Oum, ta sake rungumesa tana sanya masa albarka.
      Gaban Abah dake kusa da Oum shima yaje, ya rungumesa ya masa Barka da salla shima ya saka masa nasa agogon. Albarka sosai Abah yake saka masa harma da sauran ΄an uwansa. Sai Mamy data gama cika da kishi da ba™in ciki, a ganinta ita ya dace AA ya fara yima haka ba Oum ba. Sarai ya fahimci hakan a cikin idanunta amma sai ya basar ya mata murmushi itama yay hugging Winta yay mata barka d salla ya saka mata nata agogon. A ta™aice tace ALLAH yay masa albarka. Bai damu ba ya ™arasa ga babban Yaya, shima dai haka yay masa, sannan Yaya Fawzan. Dai-dai yana sakin Yaya Fawzan dake masa raWar sha™iyanci a kunne Maanal da Batool suka shigo. Dama ta tsaya yima Batool Win kwalliya ne saboda barci data koma da ™yar aka tadata tai wanka. Wani irin harbawa zuciyar Nuratu da itama take fitowa a lokacin cikin matsananciyar kwalliya da Nibras da AA sukai a lokaci guda. Dan harga ALLAH Maanal Win tayi shegen ™yau a Abayar data sanya fara tas da Wan kwalliyar ash kaWan like kalar aikin jikin shaddar AA, sai handbag Winta itama ash mai shegen ™yau designer, hakama takalman ™afarta, duka suna cikin kayan da AA ya bata jiya kuma shine yace ta sanya su yanzu. Bata fahimci ma'anar hakan ba sai yanzu ta gane ashe anko yake son suyi. Sai ma taji kunya ta kamata ALLAH. Amma sai ta basar ta dake. Suna ma haWa ido ya wani Wage mata gira sama sai ta kauda kanta tana guntun murmushi ciki-ciki.
      Abah ta fara risinawa ta gaida, ya amsa mata da kulawa, tai masa barka da salla ya sanya mata albarka. Sai ta matsa ta rungume Oum dake ta kallonta dan kwalliyar ta mata ™yau sosai. To dama kowa ai yasan Maanal da shegen son gayu da ™yale-™yale. Duk da Hararar da Mamy ke mata a kaikaice yitai kamar bata gani ba taje itama ta rungumeta. Kafin ta gaishe da Babban Yaya sai Yaya Fawzan. Ta haWa Saheeba da Nibras da duk ciwon hassada ya kamasu da ganin kaya masu mugun tsada da Maanal Win ta sanya a jikinta tun daga kan abayar har bag zuwa takalmi. Dan a yau kam sun sake tantance lallai AA yafi mazansu kuWi, saboda ita Saheeba tana saida kaya tasan nauyin kowane irin kaya. Musamman su abayas, lass's, atamfa, da shadda da yadi na maza. Ita ko Nibras uwarta ΄ar gayu ce kuma ΄ar ™arya da son ™yale-™yale dan haka irin wannan manyan kayan tun suna yara koda bala'i uwarsu kan haWa ta siyama kanta, ko koda kuWin cuwa-cuwa na mutane=Ψή=Ψή.
       Kan Maanal a ™asa ta juyo domin gaida AA kawai bawan ALLAH ya rungumeta. A kunne ya raWa mata,  Barka da salla and matsowar shiga daga ciki Mrs Ajwaad. You look great in white . Gaba Waya sai taji ta daburce. Balle ma da Yaya Fawzan ya wani ce.  Aouwwwww!! Kaga Masoyan asali .
       Sosai kunya ta sake dabaibaye Maanal. Ta janye jikinta tana Soye fuska da veil Winta da tai rolling yay mata ™yau kamar ka saceta ka gudu. Hannu AA ya kai zai ™wace wayar Yaya Fawzan dake musu video. Yay saurin sakawa a aljihu yana dariya. Ganin haka sauran yaran dake musu hoto da videos suma suka shiga Soye wayoyin suna gimtse dariya. Oum, Abah, Babban Yaya ma dai murmushi duk suke. Yayinda Mamy ke jin tamkar zuciyarta zata fito ta baki. Nuratu zata juya ta koma ciki Saheeba ta ri™o mata hannu ta hanata. Nibras kam sai da ta ya share hawaye...
      Zaman karyawa sukai, dama tea ne kawai sai Wan abinda ba'a rasa ba. Kasancewar ciki duk a cinkushe saboda azumi da aka sha babu wanda yaci na kirki duk suka tashi. Kowa ™ara gyarawa yay suka fito domin shiga motoci. Maanal na ™o™arin shiga motar babban Yaya AA ya wani ri™o hannunta, juyowa tai ta kallesa dan a zatonta cikin su Najma ne. ˜aramar harara ya sakar mata yaja hannunta kawai suka nufi tasa motar. Sai kawai Mamy catai itama Nuratu ta tafi can. Wani shegen murmushi Abah yayi, sai dai baice komai ba yay shigewarsa mota kusa da Oum dake waya bata san mike faruwa ba. Yayinda Babban Yaya da Fawzan sukabi Mamy da kallon mamaki. AA kam da sarai yaji Mamyn yi yay kamar baiji ba, sai ma buWema Maanal yay ta shiga hannunsa na ri™e da bag Winta ya zagaya nasa mazauni ya zauna, ita kuma babbar rigarsa da hula na saman cinyarta ya ajiye.
      Wani irin abu ya tsayama Najma na takaici, dan tunda Uncle R da Maanal suka tattauna akan Mamy a gabanta duk da basu fito fili sun ambaci sunanta ba itama ta sakama dukkan motsin mamy ido. Sai kawai itama ta fasa shiga motar Fawzan datai niyya ta koma ta AA suka shiga a kusan tare da Nuratu. Kallon juna sukai, Najma ta watsama Nuratu wani shegen harara ta Wauke kanta.
         AA kam baiyi kamar yasan bayan shi da Maanal akwai wasu a motar ba, yana gama zama bag Winta a saman cinyarsa ya juyo yana kallonta, sai kuma a hankali ya kai hannu ya kamo haSarta ya juyo da fuskarta inda yake dan da ta shagala ne da kallon design Win jikin babbar rigarsa da yay mata ™yau.
       Nan zaki kalla zuciyar Ajwaad. Dan rigar da mai rigar duk naki ne ke Waya. Aikin ya miki ™yau ne .
       Wani kasalallen murmushi Maanal ta sakar masa mai taSa zuciya, cike da shau™i ta kai hannu ta ja masa hanci kaWan,  Duk ™yan aikin kaine zaka sakashi yay ™yau dan kai ke saka ™yawu yayi ™yau zuciyar maanal. I like you in manyan kaya .
      Ya arrahaman, ji AA yay kamar zai wani shiWe, bai ma san ya matso da fuskarta gab da tashi ba ya manna lips Winsa kan nata ya Wan sumbata kaWan. Sosai kunya ta kamata sanin basu kaWai ne a motar ba, shiko idanunsa har sun Wan sirka. Maanal ta Wan maida fuskarta gefe kawai tana Wan murmushi. Dai-dai nan babban Yaya yayima AA Win horn dan shine a bayansa. Ajiyar zuciya ya sauke a kasalance yay ma motar key, Nuratu da zuciyarta ke neman tarwatsewa ta kama murfin zata buWe dan ta yanke gara ta fita a motar kawai taji ya saka luck. Dole ta koma ta zauna dan tsoronsa take ji bazata iya cewa zata fita ba kai tsaye.
       AA kam da shi yama manta da zamanta a motar a hankali yake mirza steering motar kamar baya so, dan gaba Waya Maanal ta gama kashe masa gaSSan jiki. Hannansa yakai a hankali ya kamo nata, sai ta juyo ta kallesa, shima kallon nata yay suka sakarma juna murmushi mai sanyi. Sai kowa ya janye, shi ya maida ga hanya ita kuma tana kallon waje har lokacin da murmushi a fuskarta dan ita kaWai tasan mi take hangowa a cikin idanun ΄an maza. Najma kam cike da munafunci take musu video, dan wannan gulmar bazata gani ita kaWai ba sai ta gumtsawa su Maimoo.. Sai kuma uban murmushin sha™iyanci take zubawa da son ™ular da Nurry. Tako ci nasara, dan zuciyar Nurry har wani tururi take yi. Wata irin nadamar shiga motar take ji, ga zuciyarta fal bala'i amma babu damar nunawa tana tsoron shan mari a hannun AA Maanal ta samu na nata gori...
      A haka suka iso massalaci. Nuratu ta fara ficewa AA na kammala parking, Najma ta bita tana ΄ar dariyar ™ularwa. Maanal na yun™urin fita AA ya ri™ota. Juyowa tai tana kallonsa. Ya marairaice mata fuska kuwa da faWin,  Idan kin fita wazai ™arasa shiryani, bayan kin san ban saka bane saboda kema ki samu kada .
      Murmushi kawai Maanal tayi da Wan girgiza kai, batare da tace komai ba ta Wauka babbar rigar dake jikinta ta shiga warwarewa yana kallonta ™uri kamar ya haWiyeta yake ji. Amma dai ya daure dan yana son tsira da alwalarsa. Nuni ta masa da idanu ya du™o, babu musu ya ran™wafo sosai yanda zata ji daWin saka masa ta saka, cike da kulawa batare data yarda sun haWa ido ba ta gyagygyara masa duk da yana a zaune ne harda naWo duka gefen biyu ta ajiye masa a kafaWa duk da bawai babbar rigan nada faWi bane. Dan anyita ne ΄ar cif-cif babbar rigar zamani dai da faWin nata duka baya wuce gwiwar hannu. Hula ta Wauka ta shiga mata kari dan ta iya, tun suna yara tana masa karin hula, shiko sai kallonta yake, nan ma kan ya du™o mata ta sanya masa, cike da kunya tasa yatsanta tana gyara masa Wan gashin daya fito gefe-da-gefe kaWan.
      Batare data yarda ta kallesa ba ta ce,  An gama .
    Wani ™aramin box ya mi™a mata, cikin raWa muryarsa na sake komawa ™asan ma™oshi yace,  Saura agogo da turare .
    Batace komai ba ta amsa box Win ta buWe, irin na su Yaya Fawzan ne shima, hannunsa daya mi™o mata ta amsa a cikin nasa kunya na sake rufeta, tadai daure ta saka masa sannan ta Wauka turaren dake ajiye a tsakkiyarsu ta shiga fesa masa. Sai da ta ajiye turaren ta Wago ta wani kallesa, sai

Please Login or Register in order to submit comment