Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a Wakin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a ofar bedroom Win sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga Wakin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na hauri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba. an nesa da shi ta zauna, sai kuma ta Wan zamo a kujerar kaWan cike da neman magana ta ce,  Yaya Aliy ina kwana (haka take kiransa lokacin uruciya). Hararta yay da faWin,  A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran Wanki zaki ce dani wani yayan gulma .
aramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce,  Kun tashi lafiya? .
 Alhamdullahi .
Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da faWin,  Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da sharaWin driver zai dinga kaita ba Wanki ba. Dan bana son wata alaa ta haWasu. Ki kuma gargaWesa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan ara yawan kwanakin suspension Win .
Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs Win yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips Winsa a hankali ya furta,  Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal . Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office Win....

Oum ma bayan tafiyar Abah Waki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje Wayan dama ya isheta sai taji gabanta ya faWi. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla an company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita Win matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?.....
 Ko baki son komawa ne Baby? .
Oum ya katse mata tunani. asa tai da kan nata tana aaro murmushi. Sai kuma asa-asa ta ce,  A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin an kamfani ne .
Dariya sosai Oum ta sanya da faWin,  Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki rie girmanki, ki ara wazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka .
Cikin jinjina kai Maanal ta ce,  Amin ...
Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen haWa musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal Win ta koyi yanayin fitar tashi tunda na Wan lokaci ne zasu koma fita a taren..

Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matuar yau da haska chocolate color skin Winta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan amshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da Wan lips-gloss kaWan. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye aramar handbag Winta saman table Win dining Win itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen amshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matuar yau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta Wan motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara oarin zuba abincin a ranta tana ununin (wayace ya sake airin kayanta)
 Auta har an fito? .
Oum ta faWa dai-dai isowar AA dining Win. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai Wan bata side hug. Sai kuma a asa-asa ya furta,  Barka da safiya my everything .
Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da,  Ka tashi lafiya ya arfin jikin? .
 Alhamdullahi Oumna, ai Wanki ya warke sarai in sha ALLAHU  .
 Masha ALLAH haka muke fata ai Auta .
A hankali Maanal data i sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumuWi da maradin hakan ta ce,  Ina kwana .
Batare daya kalleta ba shima ya ce,  Lafiya . Daga haka ya kalla Oum a Wan shagwaSe ya ce,  Oum yunwa zata cinye hanji na .
aramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal Win dai-dai ta Wago ta hararesa. Dan itace ke faWar haka idan tana jin yunwa. Gira Waya ya Wage mata irin (Ni Win kike harara?) sai ta sake murguWa masa baki sannan ta Wauke kanta. Ita dai Oum wurin tai oarin bar musu tana faWin,  Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne .
Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta Wauke idanun nata. Tsohon minti Waya kafin tace,  Me zaka ci? .
Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta Wago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya Wago lumsassun nasa ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips Winta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce,  Nace mi kake so? .
Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips Win nasa asa-asa ya furta,
 Ke! ...........
'


_Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba= =#, shine nace bara na tambayeku><<<<<<._




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. =O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'9


______________


.......Daburcewa taso yi, ta kuma rasa yanda zata fassara amsar ta shi. Cikin suSutar baki ta ce,  Ban gane ni ba! .
Wani Wan iskan gajiyayyen murmushi ya saki a iya lips Winsa. Kafin ya sake narke idanunsa dake sarafe da nata har yanzu.  Kince mezan ci? Me nake so? Nace KE! . Ya faWi (ke) Win da wani kalar sanyin murya yana Wan waro fararen oily idanunsa da yau cikin natan. Ai babu shiri ta janye nata zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Sai taji gaba Waya ma jikinta na neman fara rawa. Shi ko tsaf ya fahimci halin data shiga, dan haka ya saki murmushi cike da eta. A ransa kuwa rayawa yake (Ba Abanki yace bazai bani ba sai na horu. Kafin na gama horuwar kema sai kin horu yarinya) a fili kam harWe hannayensa yay a irji kawai ya zuba mata ido. Ita dai ta miskile tana haWa masa abincin a gabansa. Can asan ranta luguden daka kawai zuciyarta keyi, jitake kamar ta zura da gudu, amma bazata yarda ta zubar da kanta a garesa ba...
 Ehheem! Ehemm!! .
Gyaran muryar Fawzan ta maido AA daya zubama Maanal idanu a hayyacinsa. Janye idanun yay luuu ya maida kansa, Fawzan ya Wage gira yana murmushi. Shima sai AA Win ya Wage masa tasa girar irin (Miye?) Win nan. Dariya Fawzan ya sanya, tare da jan kujera kusa da AA ya zauna. Maanal data Wan rage Waure fuskar da tayi ta ce,  Good morning Yaya F .
 Morning anwar Yaya F, Baby Oum, Autar Abah, sannan kuma Bastyn Besty .
Duk yanda taso dannewa bai yiwu gareta ba sai da ta saki murmushi tana turama AA duk abinda ta zuba masa, sai dai bata yarda ta kallesa ba. Sai ma hankalinta data maida kan Fawzan ta ce,  Yaya miza'a zuba maka? .
 Ai duk abinda kika san yayi daWi zuba min kawai Lilly.
Murmushi Maanal Win tai tana jinjina kai. Sai da ta kammala zuba masa sannan ta koma cin nata. Suna gab da kammalawa Oum ta fito, duk da Maanal dama ba wani tana ci sosai bane ba. Oum na fitowa ma ta mie kamar wadda ke akan aya. Cike da tsokana Fawzan ya hau yima Oum kirari, kafin ya gaidata. Itako tana dariya abinta cike da farin ciki. Sai ga babban yaya da su Naufal dake cikin shirin makaranta. Saheeba biye da su. Suma Oum Win suka shiga gaidawa cike da girmamawa, yaran kuma sukaje suka rungumeta. Itama Nibras ta shigo cikin shirin aiki, da alama ta makara ne. Idonta akan AA ta gaida Oum cike da ladabi, hakama babban Yaya sannan ta juya tana gaida AA Win daya juya yana magana da Naufal. A taaice ya amsa mata batare daya juyo ba. Maanal dake karantar yanayin kowa musamman Saheeba da tunda suka shigo taga ta mata wani irin kallo ta Wauke kai a taaice ta ce,  Auntys barkanku da safiya .
Babu yanda suka iya daga Saheebar har Nibras Win dole suka amsa. Sai dai kowanne da kalar zafin da yake jin Maanal Win a ransa. Yayinda shigar tata ta saka zuciyarsu sosuwa. Duk da bawani kwalliya tayi ba, babu kuma wani yale-yale a tare da ita kamar nasu. Amma tayi matuar yin yau mai sanyi. Ga amshinta na fita a nutse babu wata hayaniya. Tunda kuma tai musu kallo Waya ta watsar da su a tasu fahimtar. Yanzu kuma ta jefesu da gaisuwar raini. Oho ita bama tasan sunayi ba. Tama maida hankalinta ga babban yaya suna magana...
Shigowar Abah ta saka kowa maida hankalinsa kansa. Sai Mamy dake biye da shi rie da briefcase Winsa. Sosai Abah dake kallon zuria'ar tasa farin cikin ya mamaye ransa. A ransa rayawa yake (Nanfa duk mallakina ne, zuri'ata ce. Idan kuma ALLAH yaba Fawzan haihuwa da Ajwaad shima Fadeel aka aro masa sai mu sake yawa). Mamy kam zuciyarta ce ta sosu da ganin wahalarta zagaye da kishiyarta. Tayi-tayi ta hana wannan zaman safen a sashen Oum tarasa yanda zatayi. Dan ita inma sun shiga gaisheta sama-sama ne, amma Oum kuwa anan ma suke breakfast wasu ranakun koda matansu sun girka sai su i cin nasu sai sun zo nan musamman Fawzan da matarsa ke malalaciya..... Tunaninta ne ya katse saboda gaisuwar da Maanal ke mata. Amsawa tai fiskarta da murmushi, sai kuma ta tsargu da yanayin shigar Maanal Win. Ta Wan saci kallon AA dake tsaye kusa da Maanal gab batare da suma sun farga da yanda suke ba. Dan ya mie ne zai amshi number a hannun Babban Yaya, kasancewar Maanal Win na tsaye a wajen suna magana da babban Yayan kuma sai tsaiwar tasu ta kasance gab-da-gab. Itama daba kallonsa take ba sam hankalinta bai kai da kasancewar kusancinsu ba duk da mayataccen amshinsa ya addabi hancinta. Hirama Naufal ke mata tanata murmushi. Itama dai Nibras hankalinta akan AA da kasancewar Maanal Win a kusa da shi yake. Zuciyarta na mata zafi da jin kishin hakan. Ganin Maanal bata tare a sashenta ba ita kaWai tasan a farin cikin da take ciki. Dan yanda take farin cikin har sai da Fawzan yay mamaki ma ya tambayeta. Amma sai tace da shi babu komai...

Gaba Wayansu abin sha'awa a tare suka fito wajen da gwarazan motocin mazajen gidan suke duk a wanke. Dan tun jiya Bola ya wanke su fes kasancewar aikinsa kenan. Yara aka fara sakawa a motar su ta makaranta, sannan Baban yaya ya shiga tasa. Abah ya shiga shima tasa driver a gaba yace Maanal ta shigo kusa da shi. Murmushi AA yay a kaikaice kawai ya shiga shima inda nasa drivern ya buWe masa. Shima Fawzan ya shige tasa hakama Nibras da taji wani kalar daWi ganin Maanal tare da Abah zata tafi ba AA ba. Cike da mamaki Mamy take kallon motar Abah, dan bata san da komawar Maanal office ba. Sai da duk motocin suka gama ficewa maigadi ya maida gate ya rufe sannan Mamy ta kalla Oum dake murmushi.
 Wai nikam arki badai aiki aka koma ba? .
ar dariya Oum tayi, ta ce,  Ai na manta muyi maganar jiya. Da yar muka samu mijinki ya yarda, shine aka kafa mana dokar bazata bi Auta ba nace munji .
Dariyar yae Mamy tayi, a asan ranta tana faWin (munafuka abinda kika ullo kenan jiya dama. Ba komai zan yi maganinku) a fili kam sai cewa tai,  Ai ina bayansa yay maganinku keda Wan naki .
 Oh na manta ar adawa ce kefa. Nayi nan . Cewar Oum tana barin wajen. Dariya Mamy tayi kawai, sai da Oum tai nisa da wajen ta gimtse fuska da rakata da harara. Sai kuma suka kalla juna ita da Saheeba dake cike fam da takaici itama. Dan ita sai yau da taga Maanal da yau fiye da ko yaushe taji zuciyarta ta sake girgizuwa. Maanal ba fara bace ba, amma irin Black beauty Win nan ce da ALLAH yayma wani kalar sassanyan yawun fuska dana jiki dana fata. Ga idanu masha ALLAH. Ba namiji ba ko mata da yawa sun sha yaba yawun halittar Maanal, a hakanma tana da oarin sututurta jikinta ne. Dan bata shigar banza, ko Winki bazaka taSa ganinta da matsatstse ba sam. Gata ar walisa dan tasan sirrin kula da jiki matua. Rashin yawan fara'arta a yanzu kansa irinsu Saheebar shakkarta, dan sai suga kamar ta cika girman kai ne, ita kuma sam a gareta ba haka bane. Maganar ce kawai yanzu bata cika son yi ba ne.....

__________&

ZARIA

 Mom please ki barni naje. ALLAH acan nake son yin azumi nidai .
Harara Hajiya Majdiya ta wurga mata.  Ni kinji nace karkije ne Najma? Ni nace ki kira Mah-mah ki sanar mata, tunda ita tace kije mata azumi kika kuma amsa. Sai yanzu ne zakice kin fasa Abuja zakije. Kina gani kuma tunda muka dawo Rufaidah kullum cikin kira take akan yaushe zaki koma. Ita kanta Mah-mah Win jiya muna waya sai da tace yaushe zaki taho.
Sosai hawaye suka cika idanun Najma. Haushin kanta ya kamata. Miyasa ma ta amsa ma kakar tata zataje can ne. Wayar da sukai Wazun da Yaya Fawzan ta sake dawo mata. Yanda yake roonta akan tazo Abuja tai azumi inba haka ba kullum zai kasance a hanyar Zaria ne. Kuma tasan sunyi alawarin Soye komai har sai nan da bayan salla Babba ta kammala exam Winta... Kamar wadda tunanin nata ya zaburar da ita tai saurin kallon Mom Winta.
 Mom na yarda zan kira Mah-mah Win, har ma da Aunty Rufaidah Win .
 Sai ki haWa da Babanki ma. Tunda shima kin san Kano kika gaya masa, kuma ya tsani magana biyu.
 Mom dan ALLAH ki taimaka min ke ki sanar masa .
 Wa? Ni? A'a kema kin san ganganne wlhy. Babu abinda ya shafeni. Kinga tashi ki arasa min aiki malama kafin yarana su dawo school da yunwa .
Sosai Najma ta zunSura baki tana miewa. Kitchen ta nufa dan Waura girki. Tana girkin tana neman mafita. Dan bata san yanda zata tunkari babansu ba kasancewarsa mutum mai zafi. Dama da gyar ta samu ya barta zuwa Kanon dan shi kam bai son yaransa suyi nesa da shi ko yaya. Harta kammala tana faman ullawa da kwancenwa. Sai da ta fara zuwa ta sanar da Mom ta gama sannan ta nufi Wakinsu. Miss call har biyu ta samu daga Ya Fawzan. Ta Wan waro idannunta waje. Kiransa ta shiga yi, sai dai harta tsinke bai Waga ba. Tana oarin yin na biyu kiransa ya shigo mata. Cike da shaui tai masa sallama. Daga can yay Wan murmushi da faWin,  Uhm-uhm wannan anwa tawa dai bata jin magana .
Sosai ta sake kwantar da murya,  Yaya dan ALLAH kayi hauri, ina kitchen ne Mom ta sani girki .
 Ba damuwa na haura ai Mom ce .
 Yauwa Yayana. Dama fa yanzu zan kiraka. ALLAH akwai matsala...... tsaf ta zayyane masa yanda sukai da mamanta. Murmushi yayi kawai,  Kinga karki damu, ni zan kira Grandma Win da kaina. Sannan ki shirya zanzo Zarian na Waukeki in sha ALLAHU  .
Cikin waro idanu kamar yana gabanta ta ce,  Baba fa? .
 Shima ki barni da shi .
 Yauwa yaya Fawzan shiyyasa nake sonka .
 Da gaske? .
Ya faWa da wani irin shaui. Ai da sauri ta yanke kiran fahimtar katoSarar da tayi. Ita kuma kawai irin tayi maganar normal ne bada wata manufa ba. Duk kiran da yay mata in sake Wauka tayi kuwa. Shi kuma daga can yayta murmushi. Tabbas kasancewarsa da Najma na bashi farin ciki, duk da kulawar da yake samu a gareta iya ta kalaman baki ce ta Wara masa Nibras. Shi kaWai yasan irin haurin da yake akan rayuwa da Nibras. Amma yana addu'ar Najma ta zama sanadin sharuwar hawayensa......

Itama dai Najma cike take da wani irin shaui, dan har tsakkiyar rai jin son Fawzan take yi. Kafin yanzu soyayya take masa na an uwantaka kawai, amma lokaci Waya da bayyana mata manufarsa sai taji al'amarin ya zarce hakan. Yaya Fawzan shine irin mijin da take ma kanta fata. Wato mutum mai sauin kai. Gashi yayyawa ga nutsuwa da dattako. Sai dai kuma wani gefe na zuciyarta na jin shakkar matarsa. Duk da a zahiri Nibras Win ba wata masifaffiya bace, sai dai irin matan nan ne marasa sakewa da mutane.... Shigowar kira a wayarta ne ya katse mata tunani, a zatonta Ya Fawzan Win ne ya sake kira, amma sai taga Uncle Rafeeq. Idanu ta waro sosai, tare da Wagawa da sauri.
 Lah Uncle R kai ne? .
 A'a bani bane .
Rafeeq ya bata amsa cikin gatse. Da sauri tace,  I'm sorry Uncle mamaki nayi ne. Ina yini? Ya Aunty Nuwaira .
 Lafiya Lau muke. Miya samu wayar Aunty inata kira a kashe? .
 Nah-nah ce ya shiga da ita bayi Wazun da safe ta tsunbula a ruwa, shine aka sakata cikin shinkafa .
 Tofa ALLAH ya kiyaye to, jeki kai mata taki .
 Okay Uncle. Amma dan ALLAH kafin na kai mata na roeka wani abu .
 Banda kuWi nayi brock .
 Kai Uncle nifa ba kuWi nake nufi ba .
 To ina jinki .
 Uncle kaga so nake naje Abuja nai azumi, sai aka samu matsala nariga na faWama Baba Kano zanzo tun kwanaki, yanzu idan nace masa na canja bazai yarda ba, zai ma iya cewa duka a fasa...... .......
'



_Mu haWe a Maawad da wanda suka shirya<<<<=2_





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. =O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'=


______________


........ To ke wace gulmar ta saki canjawar, bayan naji Mah-mah da Aunty Rufaidah na maganar zuwan naki ma .
Baki taWan tura gaba, sai kuma cike da shagwaSa ta ce,  Ni Abuja nake so yanzu Uncle please, idan akai salla su kuma basai nazo musu ba. Kaga nayi ma Ya Fa... Uhm uhm Aunty Maanal alawari itama . Tai saurin waskewa jin katoSarar da ta nema yi. Jimm Rafeeq yayi yana nazarin sunan data so fara ambata. Sai kuma tunaninsa ya Wan koma baya akan ganinsu daya dinga yi a bikin nan tare da Fawzan. Tabbas ya zargi akwai wani abu kam, sai dai rashin hujja ya sashi sakin zancen tun a lokaci.....
 Uncle Please mana...
Ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya Wan sauke. Tare da faWin,  Ba ruwana, kije ke ki samesa ba babbanki bane .
Sosai ta sanya masa kukan shagwaSa. Dan haka yace yaji zai yi tunani ta kaima mamanta wayar....
Badan taso ba ta fita kai wayar, tana addu'a a ranta ALLAH ya Waurata akansa, dan tasan yanama Baban nata magana zai amince......

_________&

Kusan a tare motar Abah data AA suka iso MAWAAD COMPANY. Maanal dake murmushin hirar da Abah ke mata tabi ko'ina da kallo. Komai yana a yanda ta sanshi. Sai da Abah ya ara mata nasiha na karta sakarma AA fuska da Addu'a sosai sannan ya barta ta fito. Hango AA tsaye jikin motarsa yana waya yasata tsayawa har sai da motar su Abah ta fita. Numfashi ta sauke a hankali, wata irin auna ta Wa da mahaifi na sake mamaye zuciyarta akan dattijon arzii Abah. Tabbas alkairin Abah a gareta mai yawa ne, da baki bazai iya musaltashi ba ma. Jinsa take a ranta shi da Oum matua gaya a matsayin mutane masu muhimmancin gaske. Wani murmushi mai sanyi ya Wan suSuce mata hawaye na taruwa mata a cikin ido tunawa da nasihar Oum ita kuma. Ita fa dariya Abah da Oum Win ke bata ma a kwana biyun nan, Abah na nuna mata ta hora AA, Oum na lallashinta ta yafe masa komai ya wuce su koma kamar da can baya da suke.....
Tunaninta ne ya katse jin an rio hannunta da wani tattausan abu da ta tabbatar hannu ne shima. Sai kuma amshin turarensa yay mata irin shigar zuruff Win nan ya wuce har tsakkiyar brain Winta yabar maainsa a maoshinta. Cikin Wan motsawar zuciya ta waiwayo, sai ko idanunta a cikin nasa daya wani tsatstsareta da su. wacewa numfashinta ya nema yi, ta fisgoshi da arfi tana mai saurin juyawa ta kalla harabar Companyn. Sosai ma'aikatansu ke shigowa ciki, wasu a abin hawa wasu a afa. Da yawansu idanunsu a kansu suke, duk da dai sai wani sinne kawuna suke wanda ta tabbatar na munafuncine kawai. oarin sake juyawa garesa ta sakeyi, dai-dai ya kawo Wayan hannunsa zai zare handbag Winta a Wayan hannunta. Hucin numfashinsa ya wani irin sauka mata a fuska. Gaba Waya sai tai mutuwar tsaye kawai, harya gama zare handbag Win ya koma tsaye sosai hannunsa a

Please Login or Register in order to submit comment