Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

.
Batare da AA ya Wago daga abinda yake ba ya ce,  Besty fa? .
Sam AS bai gane kan zancen ba, dan haka ya ce,  Sir Besty kuma? .
Karan farko AA ya Wago ido ya kallesa, sai kuma ya dafe goshi ya Wan murza. Cike da basar da suSutar bakin nasa ya furta,  Maanal .
 Oh I'm sorry Sir, ai inaga tun five ta tashi .
Jimmm AA Win yayi, sai kuma ya jinjina kansa batare da ya sake cewa komai ba yay masa nuni yaje. AS na gama fita AA yaja numfashi ya fesar, sai dai a zahiri baice komai ba. Saima miewa da yay ya nufi bedroom yay alwala. Koda ya fito tattara dukkan abinda zai buata yay a cikin briefcase Winsa, dan dolensa yay aiki a gida kam daren yau. Yana fitowa AS ya amshi kayan hannun nasa ya haWa da nashi shima, a tare suka sauka asa. Sai da suka fara salla a massallaci su an tsiraru dan akwai irinsa an over time sannan suka nufi gida shi da drivern sa, AS ma tashi motar ya shiga ya nufi nasu gidan.....
Lokacin da AA ya isa gida tuni Maanal ta jima da hutawa. Dan har taya Oum girki tayi kasancewar rigimar Abah ta tilasta mata komawa kan duty. Bayan sun kammala ne suka nufi Waki yin salla. Ana idarwa tai zaman yin karatun Alkur'ani Oum kuma na lazimi har akai isha'i sannan suka fito. Sashen Abah Oum ta tafi, hakan yasa Maanal zama ta shiga duniyar tunanin nata na fama.
Gaba Waya kwanakin nan hankalinta ba'a jikinta yake ba. Dan al'amarin su Mamy yayi matuar jijjiga mata zuciya. Dauriya kawai take tana danne komai dan kar kowa ya fahimta musamman AA da Oum. Hatta a office yau dauriya kawai take da arfin hali. Dan tasan idan kowa bai fahimci halin da take ciki ba shi zai fahimta. Shiyyasa ma ta toshe duk wata hanyar kasantuwarsu a waje guda a gidan kafin yau, yayinda shi kuma ta fahimci yana fushi da ita akan hakan duk da dai yanda suka kasance yau a office kamar ya huce...
Bayan wucewar Oum zaman shurun ya isheta, gashi tana son yin waya da Didi Shahidah. Tasan kuma dole ta nemi inda zata kawaice idanun mutane kodan abinda zasu tattauna. Fitar Oum zuwa sashen Abahn ya bata damar Waukar novel Winta da glasses ta yafa aramin veil a kanta batare data Waura Wan kwalin atafar doguwar rigarta ba ta Wauka ruwa da popcorn dake ajiye a dining. Compound ta fito, sai da ta gama bin ko'ina dake wanyar da hasken security light da kallo sannan ta nufi hanyar inda AA ya taSa kaita kwanaki dake da swimming pool, dan tasan can Win ma sharr ne da hasken tamkar rana. Shigarta wajen ya sakata lumshe idanu saboda busowar wata ni'imtacciyar iska mai anshin furanni a cikin hancinta, murmushi tayi, zuciyarta na sake zumuWin arasawa gaban ruwan. Sai dai me tana Waga afa dole ta koma ta tsaya cak, sakamakon saukar muryar Mamy cikin kunneta. Magana take a kausashe, cike kuma da bada umarni. Kai kawai Maanal ta girgiza cike da takaici zata juya dan bama ta buatar jin baaen maganganun da Mamyn ke faWa akan Oum, amma mi sai taji Muryar AA a bazata yana faWin,  Amma Mamy yanzu baya ganin hakan zai zama wani abu daban idan nace yarinyar nan ta dakata da zuwa Company na. A yanzu fa Maanal matata ce, a ganina ta wuce dukkan wata alfarma kuma sai iko ma da take da shi akan komai na. Kema fa gashi faWa kike kullum akan Abah, dan na tabbata da ace baku haWa miji da Oum ba amintarku har abada bazata taSa rawa balle har kukai ga wannan matakin. Duk da dai daga Sangarenki ne aka samu rashin fahimtar, dan har zuciya wlhy Mamy kina a zuciyar Oum da girma da daraja. Ni dai Mamy bazan gaji da baki hauri da faWa miki gaskiya akan wannan al'amarin ba. Dan ALLAH ki ajiye makamanki akan Oum, bana son lokaci yakai urewar da wani a gidan nan zai ji wani abu akan hakan, musamman sauran an uwana da Abah. Sannan batun aurena da Maanal kiyi hauri, hakan wani hukuncine na UBANGIJI dake rubutacce a addararmu, kodan yanda abubuwa suka faru a baya, da yanda suke a yanzu yakamata mu fahimci al'amarin nan fa mai girma ne.....
 Hakane ubana .
Mamy ta faWa cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa. Sai kuma ya Wan kalleta da idanunsa da suka kaWe sosai.  Kiyi hauri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar Wan uwansa.....
 Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na faWa maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...
 Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba .
 Okay haka kace? Toni zan tunkareta na amsa tunda ba uwata bace ba ai .
 Mamy Please....
Ko kallonsa batai ba ta wuce fuuu. Ja baya Maanal tai ta laSe a Wan lungun da akai adon wajen. Dan bata buatar Mamyn ta ganta. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata, matuar tausayin AA na ratsa mata Sargon jiki.Kenan shi Mamy ta bayyana masa ainhinta, tana kuma amfani da damartana tursasa masa yin abubuwa dan tasan yanda Oum keda muhimmanci a garesa. Murmushi ta saki mai matuar ciwo, sai kuma da sauri ta share hawayenta ta bar jikin bangon tamkar yanzu ne take shigowa saboda jin arar taku alamar shine zai fito. Bayyanarta ya sashi tsayawa cak, itama sai ta tsaya Win tana kallonsa, dan duk yanda taso basarwa ta kasa hakan. Tausayinsa ne ke neman fin arfin zuciyarta.
AA da ganin Maanal Win ya sashi jin shock wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi, addu'a yake ALLAH yasa yarinyar nan bataji tattaunawarsa da Mamy ba. Dan bazai taSa son hakan ta kasance ba sam. Cikin son basarwa ya shiga haWiye nannauyan abinda ke tsaye a maoshinsa ya daidaita fuskarsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali har zuwa gabanta. Kayan hannunta ya Wan zubama ido, kafin ya janye ya maida kan fuskarta. Cikin tausasa murya da ananceta ya furta,  Daga ina? .
 Sama .
Ta bashi amsa.
Murmushi yayi a karo na farko, tare da lumshe idanunsa ya sake buWewa a kanta.  Bakin nan dai bazai daina ma mutane baar magana ba ashe? .
Samun kanta tai da Wan sakar masa murmushin itama sai kuma ta kauda kanta gefe tana mai laSe bakin kaWan. Shima murmushin ya sake saki dan nata murmushin wani sanyi ya saukar masa a zuciya. A hankali kuwa ya saki ajiyar zuciyar tare da matsowa gab da ita. Matsawa tayi baya tana mai waro masa idanun kaWan, irin na (lafiya dai?) shima sai ya bita. Danganewa tayi da bango, hakan sai ya bashi damar dafe bangon da hannu Waya ya mata rumfa da jikinsa. Gaba Waya ta jita kamar a keji, ga wani irin watsal-watsal da zuciyarta ke mata, sassanyan amshin turarensa kuwa na saukar mata da kasalar jiki da gaSSai. Shima Win wani irin haurawa yaji jininsa nayi a saman kai, a hankali muryarsa cike da taushi da nauyi ya furta,  Bestie, please give me a hug mana .
Sosai zuciyarta ta harba, duk yanda taso daurewa ta kasa, idannunta ta Wago slowly ta sauke akansa, shima kallon nata yake, sai taga kamar idanunsa na yallin hawaye, duk da tasan wannan normal ne a garesa, dan in har ma yana cikin farin ciki sosai idanun na fari tas-tas zakaga tamkar kuma an bisu da mai ne. Amma na wannan yanayin babu abinda take hangowa a cikinsu sai tsagwaron damuwa da Sacin rai........
'


_To bazawarin Huznah dai kazo da bidia, runguma kuma? Gaskiya wannan salon cin amanar Abah ne kawai =_




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. =O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'1 5


______________

........Samun kanta tai da sakar masa sassanyan murmushi, tare da buWe hannayenta a hankali alamar bashi damar daya buata.
Idan yace zuciyarsa bata nema tarwatsewa ba a wannan gaSar yayi arya, amma wannan ba lokacin tunani ko nazari bane. Duk da ya mata tsaho sosai cike da jin illahirin jinin jikinsa na narkewa ya wani irin shigewa jikin nata ya rungumeta tsam har sai da ta Wan rumtse idannunta. Sosai tausayinsa ya shiga marmashe mata illahirin zuciya, dan kasancewar kanta kwance a irjinsa tana iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, ga hucin numfashinsa na sauka a kunnenta da zafi-zafi. Sun kai tsahon mintuna biyar a haka, ita harma ta fara jin afafunta sun mata nauyi. Sai taji shima kamar ya mata nauyin. Muryarta na wani irin komawa sanyi alau ta ce,  You're sleepy? .
Maimakon bata amsa sai ya girgiza mata kai kawai. Sai kuma ya mie tsaye sosai ya Wagota itama daga irjin nashi ta tsaya da afafunta. Fuskarta ya kafe da sassanyan kallo, ita sai ma ya bata kunya. A hankali ta risinar da idanunta ta koma kallon yatsun afarsa dake fes-fes cikin tattaunsan bain takalmin daya sanya. Hannu yasa ya Wago fuskar tata ta hanyar kamo haSarta cikin hannunsa. Maimakon ta kallesan kamar yanda yake buata sai ta lumshe idanun nata. Murmushi ya saki kaWan, cike da son tsokanarta ya Wan ranwafo ya dai-daita fuskar tasu numfashinsu na sauka a fuskokin juna. Cike da shauin yanayin nasu ya furta,  Besty! .
Kasa amsawa tayi, dan gaba Waya jinta take kamar ta nutse a cikin asa. Shima fahimtar bazata amsa Win ba sai ya sake sakin murmushi irin mai maalewa a gefen bakin nan. Cikin maida muryar tasa asa-asa sosai tamkar mai raWa ya ce,  An bani Hug saura kis....
Ai baima kai ga arasawa ba ta waro idanunta gaba Waya warrr a kansa. Sai dai kasancewarsu gab da juna ya sata maidawa kuma da sauri ta lumshe tare da janye jikinta baya tabar wajen da sauri. Dariya sosai ta bashi, amma sai baiyi ba ya saki Wan murmushi yana miewa tsaye da yau ya zuba duka hannayensa a cikin aljihun farin jeans Win wandonsa ya bita da kallo. Sai da ta zauna batare da ko waiwayensa tayi ba ta buWe novel Winta ta sanya eyeglasses a idonta sannan ya shiga takawa a hankali zuwa inda taken..

& Ya jima tsaye a inda ta barshi yana kallonta, kafin ya tako shima a inda taken. Kujerar dake facing Winta ya zauna, batare da yace mata komai ba ya zuba mata idanunsa kawai hannayensa duka harWe a irjinsa. Yanda ya zuba mata idanun nasa masu kaifi ya sakata daburcewa ta daina fahimtar abinda ma ta fara karantawa. Amma a zahiri bazaka taSa tunanin a rikicen take ba dan ta maze warai da gaske kamar bata san da shi a wajen ba. Dai-dai nan kiran Oum ya shigo wayarsa. Kasancewar ringing Winta na musamman ne ya saka shi dakatawa daga faWar abinda yay niyya ma Maanal. Wayar ya ciro daga aljihu yana gyara zamansa da yau. Sai dai idanun nasa har yanzu a kanta tamkar ya samu television Win kallo.
Cike da tsokana ya furta,  Assalamu alaikum uwargidan Abah har a ALJANNA .
Murmushi Oum tayi daga can. Cike da jin shauin aunar Autan nata tace,  ALLAH to ya tabbatar Autan Oum Winsa, sannan tare da ku Bestyn bestynsa.
Murmushi AA yayi mai faWi, sai kuma ya Wan saci kallon Maanal a miskilensa ya furta,  Shike nan dai Oumna kin rama 1-1 kawai.
Dariya sosai Oum tayi, sai kuma ta ce,  Dama zance kazo kaci abinci gamu nan zuwa tare da Abahn ku zaici abincin tare damu .
 I'm so happy, Oum! gamu nan . Daga haka ya yanke batare da Oum ta fahimci inda (gamu nan) Winsa ta dosa ba. Yana ajiye wayar ya zare book Win Maanal tare da Waukar kwalin popcorn Win nata da goran ruwan ya ce,  Oya let's go Oum na kira .
Komai bata kawo a ranta ba ta mie kawai. A jere suka fito duk da ba wata hira suke ba. Sai da sukazo fitowa ne cike da neman magana ya gwargwaWa mata magana a kunne. Da sauri tai gaba zata barsa saboda kunya, yayinda murmushi ya Wan awata fuskarta batare data shirya hakan ba. Shima murmushin yake yi dan haka kawai murmushin nata ya saka shi jin nishaWi. Ai cak Abah da Oum dake fitowa daga sashensa suka tsaya. Galala Abah ya saki baki yana binsu da kallo, yayinda Oum ta gimtse dariyar dake neman suSuce mata da yar. Suna tsaye kamar gumaka AA da Maanal suka shige sashen Oum batare da su sun ma farga da su ba. Gyaran murya Oum tayi kaWan, hakan ne yasa Abah maido da idanunsa kanta, harrarta yayi. Dayar ya iya gimtse dariyar tayi gaba tana faWin,  let's go tunda gasu can. bata jira cewarsa ba tai gaba tana murmushin data kasa riewa. Suna zuwa ofar sashen Oum Maanal ta zame tai hanyar baya ta kitchen ita adole bata son a gansu tare da AA. Bata san wanda take gudun su gansun ba sun riga sun gansu. Samun su Inte na haWa abincin da zasu kai dining sai kawai ta shiga tayasu.
AA kam daya shige shi kaWai dariya ma ta bashi. A ransa yace (Magulmaciya, kina so kina kaiwa kasuwa). Fawzan kawai ya samu a falon yana kallo. Zama yay kusa da shi. Fawzan ya dubesa da yau, sai kuma ya Wan matsa da fuskarsa yana shinshina shi. Harararsa AA Win yayi, ciki-ciki ya ce,  Miye? . Da yar Fawzan ya gimtse dariyar dake cinsa, cikin Waure fuska shima kamar yanda AA Win yayi ya ce,  Yada tsarguwa haka Malam, ka bari na gama tantancewa mana. Naji ne kana amshi kamar na turaren Lilly.
Irin Wan waro idon nan AA Win yayi, ya ce,  Kai yaya Fawzan ido ka koma samin? .
 Oh da mikake tunani? Kasan dai bazan bari aci amanar Abah ba. Kuma zanma anwata garkuwa .
Rasa ma abin cewa AA yay, sai kawai ya zubama Ya Fawzan Win asaitattun idanunsa. Sosai Fawzan ya kwashe da dariya, dan yasan ya gama kaishi maura kenan. Ai idan kaga Auta ya rasa abin faWa to yakai maura kenan...
A haka Oum da Abah suka shigo suka samesu. Gaishesu sukayi, suka amsa Oum na faWin,  A'a ina Baby na kuma? .
Fawzan ne ya bata amsa da,  Ai tunda na shigo ban gantaba Oum, maybe tana sama ko? .
Kai Oum ta jinjina tana jiran AA ya bada amsa, amma ya basar abinsa tamkarma baijisu ba. Sosai shima Abah ke satar kallon AA ta gefen ido ransa fal mamakin, dai-dai nan Maanal da su Inte suka fito a kitchen. Dariya taso kama Oum, amma ta danne da yar idonta akan Maanal ta ce,  Oh ashe kina kitchen Auta .
Kai Maanal Win ta jinjina tana murmushi da satar kallon AA daketa latsa waya kanshi kwance a kafaWar Fawzan hankalinsa kwance like baima san mike faruwa ba. Juyawa tai tana gaida Abah dayay Zuru yana kallonsu su duka. A ransa ko faWi yake (Aiko zakuci aniyarku ku duka) a zahiri kam amsawa yay cike da kulawa. Daga haka suka Wunguma dining cin abinci.....

A nutse suke cin abincin, yayinda Oum da Abah ke Wan hira Fawzan kuma da Maanal. AA kam hankalinsa nakan waya komi yake oho masa. Abincin ma bawani ya maida hankali bane a cinsa. Wayar Oum ta zare daga hannun nasa, yako kalleta a shagwaSe. Harararsa tayi tare da nuna masa abinci tana faWin,  Ni tunda ka tashi ciwon nan kake neman maida abinci abokin gabarka Auta. Oya maza yanzu naga plate Win nan, in ba haka ba Wura zan maka .
Dariya Fawzan yayi, Maanal ma ta kasa rie nata murmushin saboda ganin yanda AA Win yay da fuska. A dai-dai nan Mamy ta shigo sashen da sallama. Gaisheta Fawzan yayi bayan duk sun amsa mata sallama, tare da faWin,  Naje sashen yaran nan sukace kina wanka .
Cikin danne takaici Mamy ta ce,  Eh sun faWa min . Ledar hannunta ta ajiye a gaban AA da tunda ta shigo ya maida hankalinsa ga cin abincinsa. Maanal kam sai satar kallon Mamyn take bayan ta gaisheta itama. Ajiye ledar ya saka AA Wagowa ya kalleta a karo na farko, hakama su Abah kallon ledar suke. Murmushi ta awata fuskarta da shi, tare da juyawa tana kallon Oum.  Bara na aiki Wanki gidan Aunty tunda dai yaji saui, na manta shaf har drivers Win gidan sun tafi gashi da sassafe zasu wuce lagos .
Fuskar Oum babu wani damuwa ta ce,  Eh ya kamata kam a kai mata su a daren nan. Auta sai ka maida hankali ka gama ko kar dare yayi, duk da dai kai ba tsoron fitar daren kake ba .
Kansa kawai ya jinjina batare da yayi magana ba. Dan shi yasan babu wani sao. Mamyn ce ta kafa masa sharaWin zuwa yaga Nuratu ya kuma bata kayan da zata bashi yace inji shi wai Ramadan basket. Zama Mamyn tayi suka cigaba da hira da Oum da Abah, sai kawai AA Win ya mie badan ya kammala cin abincin ba, dan zuciyarsa gaba Waya jinta yake a untace, amma miewar da zai yi suka haWa ido da Maanal sai wata dabara ta faWo masa. Guntun murmushin iya shege yayi, cike da shagwaSa ya dubi Abah.  Abah dan ALLAH ka bani aron arka ta rakani tsoro nake ji .
Atare gaba Wayansu suka Wago suna kallonsa, ya sake narke fuska kamar zai yi kuka.  ALLAH Abah da gaske nake . Ai kasa daurewa Fawzan da Oum sukai suka sanya dariya. Abah kansa da yar yake iya danne tasa dake neman kufcewa. Maanal kam baki da hanci tama saki tana kallonsa, yayinda Mamy ta cika tayi fam fa takaici har hakan ya kasa Soyuwa a fuskarta. Cikin dariya Oum ta ce,  Please Abansu a taimaka mana, ai bazasu daWe ba yanzu zasu dawo . Fawzan ma yace,  Abah ayi hauri ta rakashi kada yay mana kuka ko kura ta cinyeshi a hanya dan tsoro. Kasan Besty da Besty duk tsanani tare suke zuwa aika .
Kai Abah ya girgiza, tare da faWin,  ALLAH ya shiryeka Ajwaad. Jiba yanda ka wani Sata fuska like zakama mutane kuka. Shike nan kuje, amma ina nan ina jiran dawowarku, idan kuka daWe kwanakin zan ara .
 Thanks You sweet Abah .
AA ya faWa a hankali. Nan ma kan Aban ya girgiza kawai, yayinda Oum ke faWin,  Baby tashi ku tafi kinji .
Ji Maanal tayi kamar ta nutse dan kunya. Duk da kuwa a shekarun baya hakan ba komai bane a tsakaninsu. Dan ko tana gidansu aka aikesa zaije yace tazo ta rakashi kida cikin anguwa ne. Haka itama idan aka aiketa ko yana gida agaban su Abah Win zatazo tace masa (Besty zoka rakani aika) amma sai yau gashi tana jin hakan kamar sabon abu. Sarai AA na lure da mugun kallon da Mamy ke masa, amma ya fuske abinsa, sai ma nufar sama da yay ganin Maanal na niyyar warware aramin veil Win kanta alamar da shi zatama fita take nufi. Da kallo duk suka bisa, Fawzan kuwa na masa tsokanar daya saba da kirari. Babu jimawa ya dawo da mayafin da yafi na kan nata da ke kamar na yara dan na Abaya ne. Wanda ya mia mata Win ta kalla, sai kuma ta Wan tura baki gaba. Wancan ta cire ta amshi na hannun nata ta sanya, zata nufi saman itama ta maida Oum tace ta kawo kuje kawai kar dare yayi. Oum Win ta ba, shi kuma ya Wauka ledar Mamy da takaici ke neman bombing mata zuciya suka fice..........
'


_Abah da kasan kura kaba ajiyar nama da baka bayar ba=>q_





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. =O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'1 6


______________


.......Wata Nurse da Sageer ya kira anan anguwarsu na tsaka da duba Huznah kiran Hajiya Basariyya ya shigo wayarta. Kasancewar yana a kusa da ita shi ya kai hannu ya Wauka dan ita ana mata arin ruwa ne. Shine ya fara yin sallama, dan haka Hajiya Basariyya tai Wib daga oarin maganar da tai niyyar yi. Da yar ta iya amsa masa gaisuwar da yake mata. Kafin ya ara cewa wani abu ta yanke kiran. Murmushi kawai yayi baice komai ba. A ransa kam dariyar eta yake da faWin (Mama ai sai kuma hauri, iyayya ta are tunda ruwa ya gauraya da jini). A zahiri kam murmushi yayi kawai....

Wani irin malolon bain ciki ne ya sake tokare zuciyar Hajiya Basariyya. Dan ita kam abin ya zame mata goma da goma. Tana yain ganin ta koma Wakinta kafin Hajiya Yaya ta koma, Daddy kuma ya saki Asiya a randa ta koma dan alwashine sai tayi maganin Asiya a wannan gaSar ga kuma batun Huznah da shima suketa faWi tashin ganin wannan auren ya rabe tazo ta auri AA sun fiddo waccan shegiyar agolan daga ciki mai wacen saurayi. Ita kuma sakaran tayi sakaci wannan matsiyacin ya kwace Wan mutuncin. Zaune takai a bakin gadon Wakin da take zaune a gidan yayanta, Wakin da saida akai uban rikici matansa suka bari ta zauna duk da kuwa Wakin bai ne. Kayayyakin data amso a Zaria tare da Maman Yaseerah take bi da kallo. HaWi ne sosai tayoma mutane guda biyar. Daddy, Asiya, Hajiya Yaya, sai mijin Huznah da AA. Kuma duk ana son ta aiwatar da su daga nan zuwa gobe, shiyyasa ma tai kiran Huznah dan taji yaya za'ai nata ya iso a goben itama ta aiwatar, ko Sageer na yawo da ubansa ko sai ya saketa da hannunsa. Dan sunan maganin KANWA UWAR GAMI. Amma shine tantirin ya Wauka mata waya.. Bumm!! Bumm!!! Bumm!!! Bugun ofar Wakin da take aka shiga yi da masifar arfi, a zabure ta mie tana yayimar kayan ta tura asan gado, kafin ta mirza idonta ta nufi ofa kamar mai barci. Dan bata raba Wayan biyu yayanta ne matansa sunkai ararta saboda yau ta zagesu tas wai suna saka mata nama biyu a abinci, duk naman dake gidan saboda an rainata ace biyu ne kawai kasonta...
Tana gama buWe ofar wani kakkauran mari ya ratsa mata kumatu. Da bala'in sauri da rawar

Please Login or Register in order to submit comment