Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iyayensa ba ya amince. Amma ya roa alfarmar a bari har sai babbar salla dake tunkaro mu. Zuwa lokacin itama ta ara jin saui sosai duk da dai Alhmdllh zuwa yanzu ma taji sauin. Shi kuma yana samun damar baje hajarsa yanda ya kamata a jikinta, sai dai taci kukanta a Soye da jera masa ALLAH ya isa babu damar yi a gabansa dan wani tsoronsa take ji bana wasa ba. A hakan ma sai yaga ta takura kanta da yawa ne yake Wan sassauta mata. Ko in yaga laulayin ya takura mata, dan wani lokacin takayi lafiya na kwanaki sai kuma jikin ya rikice..
Ga kewar yan uwanta dana mahaifiyarta, dan Alhmdllh a cima babu abinda ta rasa a gidan Sageer. Duk da kasancewarsa talaka yana iyakar oarin sa na bata abinda take ci a gidansu. Kuma duk abinda zai sakata a farin ciki yana iyakar oarin sa yay mata gwargwadon ikonsa....

_______&

angare na biyu kuwa su Baba Sardauna da Baba, Abbah, Uncle Mahmud, Hassan, Hussain, Najeeb da wasu aminansu Baba Sardauna uku a yau suka shiga garin Katsina domin ganawa da dangin mahaifan su Ameerah. Kwarjinin Darma a idanun al'umma da yawa daban ne. Ko sunan wannan family kaji alkairansu nasa kaji kimarsu da girmansu a zuciya. Duk irin alwashi da cika bakin da dangin mijin Hajiya Shuwa suka dingayi akan sai sun nuna mata su Win sune a bikin Ameerah sai gashi sunyi kurum. Dan kuwa wata gaban ai tafi gaban a taka...
Jikunnansu na rawa suka ma su Baba Sardauna tarba ta mutuntawa, ta girma, ta kuma martabawa. Dan kuwa cikin ikon ALLAH a cikin annen baban su Ameeran akwai mai aiki a arkashin asibitin Abbah. Wato KK HOSPITAL dake garin Kano. Babu wani ja'inja ko kai kawo sukace sun bama Babban Yaya Ameerah, kuma sun yarda a haWe biki dana Fawzan nan da kwanaki goma kenan.
Matuar jin daWi su Baba Sardauna sunyi da wannan karramawa. A take Uncle Najeeb ya ajiye sadaki daga aljihunsa. Uncle Hussain ya ajiye kuWin gaisuwa dana mungani muna so dama duk wani tarkacen tsarabe-tsarabe na aure. Akai huWWar arzii aka kuma rabu cikin mutunta juna da karramawa. Suma sukace suna nan tafe Kano nemawa Ameer auren Maimoon.
Shi halin girma duk mai shi to mai halin girman ne. Sai kawai Baba Sardauna yace in dai haka ne wace wahala kuma. Ai kawai ayi komai anan a gama sun hutar dasu a haWe ranar Waurin aure. Babbar magana. Dangin mahaifin su Ameerah fa mamaki ya sake kamasu da waWan nan bayin ALLAH. A take sukai kiran Hajiya Shuwa suka sanar mata. Ai sai ta sanya kukan farin ciki, babu wani jeka ka dawo tasa Ameer ya tura ma kawunansa kuWaWe. Suma dai a take anan akai hannun karSa kuma hannun bayarwa. Dan suma dai sun ajiye kuWin gaisuwar Ameer da sadaki da dukkan abinda ya kamata na aure. Kafin aka sake sabuwar addu'a suka musu rakkiya airport dan dama ta jirgi suka zo. Dan haka komai da komai cikin awanni biyar aka yishi aka kammala tamkar a cikin Kano akayi...

________&

Lokacin da duk su Maanal ke dawowa aiki da wannan farin cikin suka iske Oum a ciki, su Mamy dai basu san anayi ba. Sai da su Oum da ayanta da RK da Matarsa dake gidan suka gama farin cikinsu da murna RK da Fawzan harda ma Babban Yaya liin kuWi dan neman tsokana. Abin ya bama Oum da Maanal dariya sosai, AA kam sai murmushi yake, shi kaWai yasan a irin kalar farin cikin da yake a ciki yau. Yayinda yake sake girmama al'amarin UBANGIJI. Wani gefe na zuciyarsa na addu'a da fatan ALLAH yasa Mamy kada ta Waga hankalinta akan wannan al'amari dan itace kawai damuwarsa ba wata Saheebar banza da wofi ba.
Sai bayan sallar isha'i a karo na farko tun bayan bikin AA da Maanal Abah yay kiranyen meeting a sashensa. Tsoro fal zuciyar Mamy kamar tace bazata je ba ita dai, sai dai bazata iya ba, dan koba komai tana matuar jin kishirwar rashin ganin Abah na tsawon kwanaki. ALLAH ya jarabceta da son bawan ALLAHr nan kwarai da gaske. Zata iya yin komai akan Abah. Jiki a sanyaye ta kimtsa ta amsa kiran ita da Saheeba. Nuratu nason zuwa Mamyn ta hanata. Sanda suke shigowa kowa ya gama hallara. Abah ne kawai da Oum basu fito ba suna bedroom Win Abahn.
Ganin harda RK da Nuwaira abin ya tsayama Mamy a rai. Amma dai batace komai ba ta zauna. Nuwaira bata taSa damuwa da zuwa gaida Mamy ba a gidan, dan tunda RK ya bata wasu labarai akan Mamy taji ta tsani matar sosai. Haka family Win Darma suke akwai kishin nasu. Akan Wan uwansu komai zasu iya maka suna son juna. Yanzu ma darajar su Babban Yaya dake a wajen taci Nuwaira ta gaisheta. RK ma dai ya gaisheta dan shi akwai iya taku, yanda Mamy ta iya fuska biyu shima baka isa sanin shike ullama Mamyn tsiyataku ta arashin asa ba. Suma su Maanal su Yaya Fawzan duk sun mata Barka da fitowa. Tadai danne duk tana amsawa fuska a sauae. A haka Abah da Oum suka sakko daga sama suna dariya. Daka gansu kasan baibaye suke da kwanciyar hankali da farin ciki, ga tarin aunar junansu da bata Soyuwa a cikin idanunsu kida a gaban ayansu ne. Abu mai nauyi ya tsayama Mamy a maoshi, haka dai ta danne sa da yar Hari Abah ya zauna Oum kuma ta zauna a kusa da ita tana gaisheta fuskarta da fara'a. Dannewa tai ta amsa, Saheeba ma da tunda ta shigo babu wanda ya kulata ta gaida Oum da Abah........
'





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai ==O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*

*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'1 0 0


______________


.....Sai a lokacin Nibras ta shigo, duk tayi wani wujiga-wujiga itama ta rame. Itama dai ta gaida kowa sannan ta nema waje ta zauna. Aba ya fara da gyaran murya dan haka kowa ya sake nutsuwa ya bashi hankalinsa. Yay musu sallama da addu'a, kafin ya fara da faWin,
 Na tara ku anan ne domin dalilai guda biyu. Na farko nasiha a garemu baki Waya. Musamman akan zamantakewar gidan nan da nake ganin tana neman canja salo daga bigiren da muka ginosa na shekaru zuwa yanzu. Hakan baya min daWi. MuWin ahali Waya ne, da su da aka haifa a gidan, da ku da suka auro a wajena a yanzu duk matsayinku Waya ne, domin duk aa kuke a wajenmu. Ita rayuwar aure ibada ce, daga Sangaren mace har na namiji duk wanda ya samu raunin sauke hakkin Wan uwansa akan ganganci UBANGIJI bazai barshi ba. Sannan kuma masu haihuwa ne, wataran zaku aurar da naku aan ko mazan su auro muku. Dan haka ina nasiha a gareku da komai ma a ajiyeshi hakanan ya isa. Mu haWu mu zauna lafiya da junanmu kamar yanda muka saba. Karna sake jin ko ganin wani yazo daga waje ya tada min tarzoma a gida akan abinda bai shafesa ba. Idan ba hakaba kuma zan Wauki mataki.
A nutse suka shiga bashi hauri, tare da neman afuwa. Aba ya cigaba da faWin,  Abu na biyu hidimar biki dake tunkaro mu. Kowa dai yasan an Waurama Fawzan aure a cikin hidimar bikin nan na Ajwaad, bata tare bane saboda exam da take yi kuma Alhamdullah ta kammala. Dan haka zamu fara shirye-shiryen tarewarta nan da kwana goma. Sai dai ba ita kaWai bace, dan wani alkairin ya sake shigo mana. Shima Fadeel zai ara auren......
Wani irin kallon Abah Mamy da Saheeba sukai. Cikin rawar murya Saheeba ta ce,  Abah! Fadeel kuma? .
Wani banzan kallo Babban Yaya ya jefa mata na ki shiga hankalinki. Abah kuwa sai yay murmushi. A nutsensa ya ce,  Tabbas Fadeel Saheeba, domin ALLAH ya bamu dama mu maza muyi mace daga Waya har zuwa huWu. Sai dai ba hakan na nufin ku da muka fara ajiyewa zamu wulaanta ku ba, ko kuma mun ara ne dan mu wulaantaku. Sam ba haka bane ba, shi arin aure da son mace fiye da Waya a jininmu mu maza yake .
asa-asa Maanal ta kalla AA, sai akai sa'a shima kallonta yake. Ganin yanda idanunta suka cika da walla sai ya shiga girgiza mata kai, tare da yi mata alamar shi dai banda shi. Ba AA da Maanal kawai ba Nuwaira nacan ta tsare RK da ido itama fuska kicin-kicin. Shima dai lallashi yake da ido dan Abah na neman Sallo ruwa da wannan jawabi gaskiya. Duk abinda suke Abah na lure da su, dan hankalinsa nakan kowa. Sai abimma ya bashi dariya. Amma dai ya danne baiyi ba. Cigaba yay da faWin,  Amma hakan ba yana nufin kowane namiji nada wannan ra'ayin ba. Wani addara ce take sakawa ya ara, wani auren dole ma ake masa da tsiya-tsiya.... kallonsa Oum tai dan tasan da ita yake kuma yanzu, aiko shima kallon nata yake, ya saki wani guntun murmushi ya Wauke kansa. Mamy kam wani irin dukanta kalaman Abah Win sukayi, suka kuma shiga yimata kai-kawo a zuciyarta da tai nauyi sakamakon ambata zancen auren Fadeel. Oho Abah ya cigaba da maganarsa.  Wasu kuma sakacin matan dake gidan ne ke sakasu son su ara Win, wani kuma shi dama ra'ayinsa kenan. Kai wani jin daWin yautatawar da ake masa ma zata iya sakashi ya aro dan farin cikinsa ya aru. To koma dai miye sai mu zama masu tsarkake zukatanmu a komai na rayuwa. Ku dukanku shaida ne kun taso kunga iyayenku su biyu ne, kuma babu wanda zaice ga wata rana tazo suna sa'insa a tsakaninsu, ko cin mutuncin juna, ko wani abu makamancin hakan. Ina son kuyi koyi da su, domin mu haWu mu gudu tare mu tsira tare. Hakan zai sakamu a farin ciki baki Waya, dan gaskiya bana son halin banza. Nayi tunanin a saka musu gini suma, sai dai guri ya ure mana gaskiya, dan haka kuyi hauri zaku fara zama a tare waje guda zuwa bayan babbar salla za'a sanya aikin nasu suma tunda muna da filin yin hakan. Akwai auren Maimoon itama da Ameer, dan haka sai mu fara shirye-shiryen dukkan abinda ya dace. Ina sake gargaWin kowa da bana son kowane irin tashin hankali a gidan nan, mu mutunta kammu ayi taro lafiya a tashi kamar yanda aka saba. Idan ba haka ba, duk ta inda wani abu ya Sullo to lallai Zan hukunta ko wanene da hukunci mai tsauri. ALLAH yay muku albarka. Ya bamu zaman lafiya baki Waya. Kuje abinku. Amma Saheeba da Nibras su zauna zanyi magana da su. Kaima Rafeeq zauna ....

_________&

Nasihar Abah ta saka kowa nutsuwa a zahiri. A bayan fage kam Mamy da Saheeba a birkice suke. Dan tunda ta koma sashenta bedroom ta shige ta kulle kanta. Bala'i ne fal a cikinta, sai dai shakkar sakamakon yinsa ya hanata fitarwa. Fin minti talatin ta gama yanke shawarar zuwa yau dai ga Abah, amma kafin haka zata fara da Fadeel ne.
Babban Yaya na tsaye a compound shi da AA da Fawzan suna magana kiran Mamy ya shigo masa. Koda yaga itace bai kawo komai a ransa ba ya Waga. Sai dai tunda ya ambaci sunanta AA da Fawzan suka maida hankalinsu kansa sosai. Koda ya sauke wayar daga kunnensa dan umarnin zuwa kawai ta bashi ta yanke baice ma annen nasa komai ba sai  Ina zuwa .
Da kallo duk suka bishi, sai kuma Fawzan ya kalla AA.  Da alama shima Babban Yaya Mamy bata son ara auren nan nashi .
Murmushin basarwa AA yayi, tare da faWin,  Kai ko Yaya taya zata so ama arta kishiya .
 Amma tana son aima ar wasu tunda tana son kai ka auri Nuratu. Ni nayi mamaki ma yau da bata kawo batun Nuratun ba .
 Maybe tayi shirun ne dan na Babban Yaya ya bata mamaki, tunda koda alama shi ba taSa nunawa yay zai ara ba. Lokaci guda abin ya taso .
 Hakane kuma .

&Babban Yaya yakai zaune yana kallon Mamy da mamakin ganin yanda ranta ke a matuar Sace. Cikin kasa iya shanyewa ya ce,  Mamy lafiya kuwa? .
Bata amsa masa ba, sai ma tambaya ta jeho masa a fusace.  Fadeel wace yarinya ce zaka aura?
Kai tsaye babu wani kwana-kwana ya ce,  Ameerah ce .
 Ameerah! Wacece hakan? .
an jimm yay na mamaki, sai kuma ya ce,  Wai Mamy lafiya kuwa? .
 Tambayarka nai wacce? .
Sai da ya furzar da iska sannan yace,  anwar Ameer nan makwaftanmu ar Momy Shuwa .
 To baka isa ba! Ba kuma zai yiwu ba! .
Murmushi ya saki a karo na farko. Cikin girgiza kai ya ce,  Mamy dan mi bazai yiwu ba? Saboda Saheeba kike tunani ko an uwanki. Mamy bazan Soye miki ba na gaji da halin Saheeba. Na miki iya biyya akan zama da yarinyar nan mara tarbiyya, nayi hauri nayi kawaici, sai dai anzo gaSar da komai zai iya faruwa. Dan zaSi biyu ne. Kodai ta zauna da wadda zan auro, ko kuma na saita mata hanya. Amma bazan iya haurin in ara aure ba. To mima ya rage iyaye har sun shiga hatta sadaki an bada. Mamy farin cikin Saheeba yafi nawa muhimmanci ne a wajenki? Nayi hauri na rasa Shahidah, ALLAH ne shaida kuma har gobe ina son yarinyar nan, na auri Saheeba, tsahon shekaru bana jin daWin zama da ita, ban taSa zuwa na miki orafi ba duk wani banzan halinta na shanye ma cikina. Yanzu kuma naga wadda zata bani salama da kwanciyar hankali saboda kar ran wata banza Saheeba ya Saci sai na haura Mamy. Oum ta bani goyon baya, Abah ya bani goyon baya, miyyasa ke bazaki bani ba? Dan tana Wiyar ar uwarki?. Gaskiya kimin afuwa babu abinda zai hanani auren nan sai dai idan na mutu ne kafin kwanakin .
Daga haka yay shiru ransa a matuar Sace. Ai mutuwar tsaye Mamy tai tana kallonsa. To ashe gwara-gwara Fawzan ma. Tana ganin AA yafi Fawzan, to ashe Fawzan ma mai biyayya ne. Dan gaba Waya ma Fadeel yau ya juye mata ne kamar Abah. Wlhy saima taji ta rasa abinda zatace masa. Sai wani irin tsuma da jikinta ke mata. Zuciyarta kam zafi take mata, gashi tai nauyi a cikin irjinta...
Dai-dai nan Saheeba ta shigo tana sharar hawaye. Ganin Babban Yaya zaune sai ta tsaya tana kallonsa kukan na sake kufce mata. asa takai durushe, tana ara fashewa da kuka ta ce,  Dan ALLAH na tuba Daddyn Naufal, dan ALLAH kada kamin kishiya, wlhy na rantse maka zan canja, duk abinda kake ganin inayi baka so zan daina shi. Dama bayin kaina bane Mamy da Mama ke sakani yinsu. Amma wlhy bazan sake biye musu ba....
Da wani irin sauri Mamy ta kalla Saheeba, har taune harshe take wajen faWin,  Saheeba! Wace banzar magana ce wannan. Nice ma zan sakaki ki masa halin rashin arzii? .
Babu ko War Saheeba ta ce,  Wlhy kece Mamy, ke da Mama kune ke tsara komai kuce nayi saboda na wato muku shi daga hannun O......
Ai wani irin tassss!!! Kake jin Mamy ta saukewa Saheeba mari. Zata ara magana ta sake Wauketa da wani marin na biyu. Sannan ta ce,  Wawuya kawai, kin haukace ne? Kodan mijinki zai aure sai hankalinki yabar jikinki har ki kasa tauna maganar dake fitowa daga bakinki. To idan kin manta bara na tuna miki nice na haifi Fadeel har kika aura shashasha .
Tsam Babban Yaya da mamaki ya kashe ya mie. RaSasu yay ya fice abinsa zuciyarsa na matuar jinjina al'amarin Mamyn da Saheeba. Mizai saka Mamyn harzua haka dan Saheeba tace sune suke sakata yin abu. Sannan a ina za'a watoshi kuma? To shi koma dai minene su suka sani, aure dai kam in sha ALLAHU babu fashi sai yayi. Ita kuma ya rage nata ta gyara ko ta cigaba da yin abinda tai niyya shima zai fara yin wanda yay niyya kuwa. Dan yanzu ya Wauki Wammarar saitata a layi. Abinda ya Wauka a baya ko kwatarsa bazai Wauka a yanzu ba daga garetan............
'

==Hajiya Mamy yada haka kuma. Marin surukai fa baida yau gaskiya>#.




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai ==O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*

*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'1 0 1


______________


.....A wannan dare dai Mamy bata iya ta tunkari Abah ba, dan Babban Yaya da Saheeba sun fusata ta. Sai washe gari da safe suna shigowa daga massallaci tai dakonsa. Dan suna fita dama ta fito a nata sashen sai ga Oum ta fita daga sashen Abah Win dan dama ita haka take yi. Sai kawai tai wuff ta shige ita bayan ta gama zagin Oum da tsine mata a zuciya. Anan falon Aban tai sallar asuba. Ta cigaba da zaman tsammanin dawowarsa har suka shigo.
Koda Abah ya shigo ya ganta Wauke kansa yay tamkar bai gantan ba. Sai taji gaba Waya ta sake rikicewa. Amma haka ta daure tace masa ina kwana. Idan bangon Wakin ta tanka shima ya tanka. Jikinta na ar tsuma ta tari gabansa, muryarta na rawa tana kallonsa da idannunta da suka kaWe ta ce,  Dan ALLAH kayi hauri ka saurareni ko sau Waya ne. Wlhy-wlhy ba abinda kake tunani bane ranar zan gaya maka gaskiyar komai, Fadeel ne......
 Kinji nace miki ina buatar sanin miya faru ne? . Abah ya katseta babu alamar hayaniya a muryarsa.
 Kayi hauri dan girman ALLAH. Zan maka bayani koda bakace kana buatar ji ba ko hakan zai sa ka sassauta min. Wlhy a duniyar nan fushinka shine mafi ololuwar tashin hankalina fiye da komai kaima ka sani .
 Ni a suwa da fushina zai zama ololuwar tashin hankalinki Kamila. Idan ma shi Winne kwantar da hankalinki baki da matsala dani. Duk abinda kike tunanin dai-dai ne ofa a buWe take kiyi abinki. ya are maganar da raSata zai wuce. Da sauri ta rio hannunsa tana fashewa da kuka. Fisgewa yay oarin yi ta riesa da hannu biyu duka da iya arfinta kuma.
 Amma kin san zan iya marinki ko? .
 Gara ka marenin, wlhy gara ka mareni da wannan fushin dai da kake yi dani. Ka tausaya min dan ALLAH ka duba min, wlhy ji nake kamar zuciyata zata tarwatse. kuka mai arfi ya sareta. Shiru kawai Abah yay yana kallonta. Kamar wanda ya fahimceta sai kawai jitai ya zare hannunsa yay gaba. Sai da yaje zai shiga bedroom a kausashe ya ce,  Ki gayama an uwanki akan wannan bikin wlhy-wlhy duk wanda ya nema Waga hankalin iyalina nima sai na Waga nashi. Ba kuma lallai dole bane sai aana sun zauna da aansu. Hanawa su Wauki wani mataki akan yaran adalcina ne, amma a wannan gaSar duk wadda tace zata kawo musu shirme zan basu damarsu ta Waukar matakin da duk sukai niyya dan ina son farin cikinsu. Dan ko kece kika ce zaki Waga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu. Idan kunne yaji jiki ya tsira .
Yay shigewarsa. (Dan ko kece kika ce zaki Waga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu) Wannan kalma tai matuar dukan zuciyar Mamy da girgiza mata duniyarta. Ta kuma fahimci eh lallai da gasken gaske Abah yake yi. Itako ta shiga uku, shin mike faruwa ne? Anya kuwa? Anya ganin da Abah yay musu sun fito a sashen Ajwaad ne kawai matsalar kuwa? Kai da mamaki gaskiya, akwai lauje cikin naWi. Dole akwai wani abinda ke a asa. Batun Ajwaad da Maanal ya faWo mata a rai. To kodai binciken da take tunanin zasu iya yi suka yin ne?. To amma ta ina? Inma zasu bincika ai Doctor ne kwai, jiya jiyan nan kuma Hajiya Turai ke sanar mata a binciken da tai Dr Tofa ma baya Nigeria kusan shekara biyar kenan. To kodai munafukar matar can ce tai mata wani ullin?. Zuciyarta tafi tsayawa a hakan, sai dai hujjar ta mata rauni da yawa. Amma ko akan batun auren nan ta tabbata akwai saka hannun Fateema. Kenan dai Fateema ta cita wasa. Ajwaad ya auri ar awarta, Fawzan ar anwarta, ga Fadeel ma zai auri ar awarta. Shike nan yainta na shekaru ya tashi a banza. Tunda ga Saheeba nata auren na rawa, Nibras ma bata sakata a sahun mata ko wanda take amfana. Auren Nuratu na tangal-tangal. Tana a ruwa fa kenan har yana shirin zuwa mata wuya idan bata tashi tsaye ba. Ga wancan batun duk da tana oarin hidden Winsa yana nan daram a ranta, yana kuma cimata zuciya.....

________&

Anan Sangaren Oum kam shirye-shiryen biki suke hankali kwance. AA ya riga yay order Win kayan lefen Fawzan tuni, yanzu kuma gana babban Yaya. Duk da zai iya yin hakan shima saboda kawai yaje ya Wan huta da tashi amaryar sai suka tsiri tafiya Dubai wai haWo lefe shi da RK da Maanal da Nuwaira. Sarai Oum ta fahimcesu, dan haka batace komai ba face binsu da addu'a. Shima Abah koda suka faWa masa addu'ar yayi. Dan daga shi har Oum Win an ba ruwa na ne.
Haka kuwa suka shirya suka tafi, suka bar su Oum kuma anan Nigeria suna shirin fara gyara amare ita da Hajiya Shuwa. Sai dai ita Najma ma can wajen Ammie zata zauna nata gyaran. (Kun san dai itama Ammie tsohuwar mai gyaran jiki ce) Dan haka Hajiya Shuwa data haWa duk abinda ake buata aka aikama Ammien, itama kuma daga can Ammien ta aiko musu da tata basirar da za'ama Ameerah da Maimoon da itama ta dawo nan Abujan amma a sashen Oum zata zauna dan ba'ayi abin kunya suruka Hajiya Shuwa tayi gyara ba..
Babban Yaya da Yaya Fawzan kuma sai suka maida hankali a gyaran sassan nasu. Amaren zasu zauna a downstairs kafin a gama musu nasu ginin. Amma duk da haka sai da aka gyara duka sashen biyu. Hakan yasa Nibras komawa sashen Oum da zama. Saheeba dama har yanzu tana a sashen Mamy. Duk da dai sunata zuba rikici ita da Mamyn, dan kota sakata abu yanzu batayi. Mamanta da itama ta tadama Mamy hankali tace Saheeba ta taho gida amma Saheeban tace babu inda zataje, dan Babban Yaya ya rantse mata indai ta fita a gidan ta fita kenan na har abada.
Hajiya Turai ce da yar ta sasanta Mamy da Maman Saheeban. Ta kuma nuna musu illar bari kan nasu ya rabu. Acewarta a yanzu ne ma ya kamata kansu ya haWu suyi yai na gaske dan abaya wasan yara sukayi. Fargarwar tata ta shigesu,

Please Login or Register in order to submit comment