Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasan yara bane. Dan duk abinda akace IBADA ne to lallai dole ne ka shirya da shiri na musamman. Dole ne ka yarda da dariya a cikinsa da kuma kuka a wasu lokutan, ita aljanna bata samuwa a kwance, kamar yanda kasan baka samun kuWi a cikin mafarkinka sai ka motsa ka nema. Idan har duniya da take ba komai ba bata samuwa a garemu cikin saui, taya zamu yi tunanin aljanna samunta zai kasance mana mai saui.Mata ALLAH mu farka mu ajiye wani ka-ce-na-ce na hallayar maza mu nema aljanna kawai sune a ruwa. Dan aljanna duniyace malam, komai fa akwai a ciki, wohoho Bilyn ku a aljanna ai ba'a magana zamu tsula tsiyarmu in sha ALLAHU. (ALLAH kasa mu Win an aljanna ne=-. ALLAH ka sani mun guji iskancin nan a duniya da gudun hakkin mutane duk da yanda suke da daWi ALLAH kai mana sakamako da aljanna domin rahamarka=-=O, mun tuba ka yafe mana kurakuranmu ka yafema iyayenmu ya rabbi ya arrahaman, ya arrahim, ya almalik, ya malikil mulki ziljalalu wal'iram=-=O).
Ba lectures ce kawai ta gudana a wajen ba, anci ansha tare da raba souvenirs masu yau da Waukar idanu. Abinda zai baka dariya da birgeka hoton AA da Maanal suna yara ne a jiki. Sai mutane da yawa basu ma fahimci ango da amaryar bane ba a jiki, ita kanta Manaal abin ya bata dariya da birgeta, har sai da walla ta cika mata idanu dan kuwa hoton dake jikin ita kanta bazata iya tuna sanda aka yisa ba, tana arama sosai, sai su Amaal ne keta oarin ma tunowa suma suna dariya. Bayan kammala walima amarya Maanal ta koma ciki, yayinda su Nene suke shirin wucewa. Amma Oum tace ina ai saifa gobe da safe in sha ALLAHU kowa zai tafi, dan haka suma dole hakan zasuyi, anjima da dare ma akwai event na ammata da yaran Darma Family suka haWama amarya. Rasama abin faWa Nene tayi, wai su mutanen nan basa tausayin kuWaWensu ne...
Dan shima dai acan ango wani Wan biki-biki matasan Darma Family suka shirya iya su maza, shiyasa ma abokansa suma dai duk sai gobe zasu tafi. Shi dai dauriya kawai yake dan harga ALLAH a takure yake. Hajiya Shuwa ta haWa masa bomb da turaren da take zazzagama Maanal a jiki, shiyasa ma yaketa kauce-kaucen haWuwarsu a yau gaba Waya. Sosai abokan nasa suka saka shi a gaba musamman abokan karatunsu na primary da Secondary da suka san wacece Maanal a wajensa, tunda mafi yawansu sun sha duka da rashin arziinsa akan taSa ta, ga rashin kunya itama ba raga musu tayi ba duk da sun girmeta. Haka suma dai wanda sukai karatu a tare na jami'a duk da bai taSa zama ya bama wani labarin a cikinsu ba kai tsaye, sun dai tsinta wasu a cikin abubuwan da suka shafetan a wajensa sai kuma jiya sukaji komai da ganin hotuna a wajen dinner. Duk iskanci da shaiyancin da suke masan bai yarda ya kula ko wannensu ba, to kuma dama dai sun san halinsa na rashin son yawan magana. Yakan Wan murmusa dai dan shi kam duk sun addabesa, badan Oum datace yau ya kwana anan ba dan su Nene sun kasa sakewa saboda jiya ya kwana a gidan da tuni ya fece gida abinsa.....

__________&

Kuce dani ina hajjaju Mamy ne? Tana can a sashenta abin duniya ya matuar isarta, dole kuma ta danne ta haWiye saboda wasu a cikin an Kano a sashenta suke zaune. Badan ALLAH ba dole ta taushe tafashen azabar bain cikin dake zafafa zuciyarta tanata yaen dole ga ciwo na cinta a tsaitsaye jiya ma sai dare akabi aka saka mata drip da allurar barci a ciki sannan ta samu ta rutsa, amma abinda ya faru a wajen dinner Win nan ya matuar tsaya mata a rai. Kowa Oum yake tayawa murna matsayin uwa, komai za'ai ta Sangaren uwa Oum Mc ke ambata. Babu mai kallonta, babu kai tunawa ita ta Wauka cikin Ajwaad wata har goma sai a cikin na sha Waya ta haifesa. Tsabar ma an maida wulaantaciya ita aka dinga nunawa matsayin step Mom Winsa wai. Ya rabba wannan abu ya Zafafa mata zuciya. Har sai da taji idonta na gani bishi-bishi alamar jini ya haura mata sama sosai. Shiyyasa suka baro hall Win kafin ma a tashi. Koda suka shigo gida saita sakar ma Babban yayarsu dake rie da ita kuka dan can suka baro maman Saheeba tace sai taga komai. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga irjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu Wan zane. Ga tsagwaron rainin hankali a ciki, yo inba rainin hankali ba taya zata shirya wannan abubuwa haka batare da ita Mamyn an nuna wani matsayinta ba matsayinta na mahaifiyar Ajwaad balle su danginta, sannan ga auren Fawzan da shima akai matuar raina musu wayo a gefe, wanda da yar suka taushi Mamy Win akan kar tace komai har a gama wannan taron kowa ya watse sannan su zauna da Abah. Dan basu so kowa ya tafi dasu a baki akan hakan.
Yau ranar walima yanda Mamy ta nema Waga hankalinta yasa suka taru a kanta harda dangin mahaifiyarsu da sukazo wajen biki suka dinga tausarta. Wasu suna gaya mata gaskiya da tuna mata itafa ta Wauka yaran ta bama kishiyar tata. Miyasa kuma zataji zafi dan yanzu an danganta yaran da ita. Wasu ko goyon bayanta suke da tayata kishi. Haka dai sukaita cece kunesu batare da su Oum sun ma sani ba. Koda lokacin walima yayi tace bazata fita ba yaleta kowa yayi. Tabbas Oum ta lura bataga Mamy ta fito ba, sai kuma hayaniyar mutane da mawafta masu shigowa da abokan arziinsu nan cikin abujar ya Wauke mata hankali. Ana gama walima kuma sallar magrib kawai akai aka shiga shirin faty na yaran family Win da suka shiryawa amarya. Anan cikin gidan shima akayi a garden, yanzu ma amarya Maanal tasha yau harta gaji cikin doguwar rigar atamfa data mata yau sosai. An gudanar da komai cikin aji da halin girma. Amarya Maanal tasha kyaututtuka daga annen ango dan mafi yawan yaran family Win mata su AA sun girmesu, sai dai kamar iyaye irinsu Majdiya, ko su Nuwaira matar su RK matsayin iyayen su AA Win suke ai. arfe goma an tashi kowa ya nema makwanci. Yau ma cike da murna Maanal ta kwanta an uwanta zagaye da ita.

Washe gari kam da wuri Nene tasa suka gyara ko'ina na sashen Maanal. Dai-dai nan mota ta iso daga Kaduna ta kayan gara daga Daddy sai kuma kayan rabo da zasuyi na buWar kai. Dan zuwa arfe Waya na rana an gama shirya Manaal cikin wani arnen lafaya da yay mata yau. Ana idar da sallar azhar sama-sama sukaci abincin da aka kawo musu na lunch, sannan sukai zaman sake yima amarya Maanal daketa hawaye nasiha. Bayan sun kammala sashen Oum suka nufa da Maanal dan acan za'ai buWar kai. Dole suma dangin Mamy nan suka zo aka haWu gaba Waya. Anyi buWar kai, tare da damama su Oum kayan rabo na al'ada daya bada mamaki, dan su Shahidah sunyi matuar oarin nuna bajintarsu suma. Saboda tunda akace za'aima Maanal biki kafin tarewa suma suka shiga yin wannan tanadi su da Ammie babu wanda yaji ko ya gani sai Nene. Sai yau da ake fiddo kayan arzii aan su Hajiya Yaya da na Hajiya Basariyya sukai tsuru-tsuru jikinsu na arasa yin sanyi. Dan da gasken gaske an goge musu kaf haddarsu a wannan biki. Hatta su dangin Mamyn abin ya basu mamaki, dan su dai Mamy ta gama sanar musu Maanal ar matsiyata ce. Sai gashi a wajen baye hatta su Naufal dake matsayin aa sai da aka basu rabo. Haka kaf manyan family na Darma kowa da nashi har su RK dake ananun uncle's kuma ta Sangaren mace ma. Ga kayan gara mota guda, kaf kuma a sashen Oum aka ajiyesu ba'a ajiyewa Maanal komai a cikinsu ba dan sun Wan saka mata wasu abubuwan a store da su Shahidah sukai dabarar saya suma ta Sangaren kayan abincin.
Bayan gama rabo aka zagaya da Maanal gaban iyaye. Anan fa suma Darma Family suka sake zuba tasu bajintar. Dan sun sakama amarya kuWin al'ada sosai, saboda ba kunya Oum ta bada babban basket na kaba tace sotake ta gansa cike da kuWi iyayen ango da annensa da auntys. Cikin dai raha akai wasa akai dariya. Tuni dangin Mamy suka tsure, dan da alama dai zasu sha kunya a wajen. Saboda su wai a gadarance suka taho da kuWi mai dubu Wari mai hamsin Maman Saheeba ma Wari biyu wai za'a nunama Oum ita ba komai bace koda basa son amarya sai sun bada mamaki sai suka ga yara anana na ajiye 1m da 500k kamar kuWin banza. (To banda abin talaka ana faWa da mai kuWi ko gasa ne akan kuWi==>q). Tuni su Mamman Saheeba suka fara Soye an dubu Wari biyu dana hamsin Win su, daga baya dai Saheeba data fahimci kunya fa dangin nasu zasu sha tace su haWe kuWin waje guda su bata. Haka sukayi, ita kuma ta fita ta undumo 1m a cikin kuWin sana'arta ta haWa ta ajiye matsayin na dangin Mamy gaba Waya. Tsabar muguntar Hajiya Majdiya sai tace to matan yayyan ango Saheeba da Nibras kenan dole suma su sanya, hatta kuma Najma bata Wagama afa ba.
Wannan abu ya girgiza Saheeba. Nibras da duk ta fige ta rame a kwanakin bikin nan uwarta tazo ta ajiye 1m dan itama bata son harkar zubda girma>#. Ganin haka fa Saheeba aka sake zuwa aka Wakko 1m aka ajiye itama. Aunty Rufaidah na ganin haka tazo ta ajiye 3m matsayin na Najma tace ta fanshi Wiyarta itama. Zokaga ihu da ihu na shaiyancin yaran family Win darma. (NIKO NACE SHEGIYA NERA, ALLAH KA BAMU NERA MAI ALBARKA==O). Wanna abu ya tsayama Saheeba da uwar Nibras a ahon zuciya, dan ita Nibras ma hankalinta ba awajen yake ba. Uwarta kuwa tayata kishi take da an uwanta akan Najma. Dan ko bikin nan sun halarci shi ne kawai dan kar ace gashi-gashi. Amma Maman Nibras ta gama shirya bala'in da zasuyi da Mamy jira take kawai biki ya watse taji dalilin yima arta kishiya batare da an sanar dasu ba..........
'



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai ==O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https:/  /whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'6 9


______________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Shin kuna Neman in da zamu samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?kayan yara masu kyau unique na yan gayu ? To shiga link din grp na Imzeedventure>p>p>p Kisha mamaki= idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi tanayi>s>s

___________

..........To su dai su Shahidah sunyi godiya sannan aka kai Maanal sashen Mamy, Mamy na bedroom, su Shahidah suka zauna a falo. Kasancewar tare suke da Aunty Suhaima, da Aunty Zainab, sai Aunty Kursiyya matan Uncle Hassan da Hussaini da Uncle Mahmoud kenan suka shiga har cikin suka mata magana kasancewarsu matan annen miji. Dole Mamy ta danne ta fito sanye da hijjab, dan kwance take ciwon kai ya addaba mata. Ganinsu warr a falon suka cika mata ido, dole ta aro murmushin yae ta yafama fuskarta. A gabanta aka zaunar da Maanal dake lulluSe. Da yar ta iya daurewa tace ALLAH ya sanya albarka kawai. Wai ai tasan duk wanda ya isa ya mata nasiha ita basai tace komai ba.
Shahidah da a yanzu Maanal ta gama nuna mata wani abu kaWan daga Mamyn sai tai murmushi kawai, tare da fassara zancen nata da yau a zuciya. Ita kanta Nene yau dai kam tasha jinin jikinta akan Mamyn, amma batace komai ba suka fito da Maaanal. Sashenta suka maidata, aka ara mata nasiha sukai sallar la'asar suka firfito dan tafiya. Kuka sosai Maanal keyi abin tausayi, dan ma Amaal na nan tare da ita sai Aunty Sakina. Sai zuwa magrib su zasu koma gidan Shahidah su sake kwana gobe su wuce kd.
Sashen Oum suka koma yimata sallama. Sosai Oum tai mamaki ganin wannan tafiya tasu ta yamma haka. Ta shiga lallashinsu akan su bari sai gobe da safe Nene tace ina ai in sha ALLAHU yau a Kaduna zasu kwana, abin ai sai ya koma rashin kangado kuma. Anyi komai an gama ai suma sai a barsu su huta haka nan abi yara da addu'ar zama lafiya.. Badan Oum taso ba ta haura, nan fa aka shiga shirya musu kayan biki da aka tanada domin su, dan hatta Ammie sai da Oum ta haWa mata nata. Sashen Maanal Win suka sake dawowa tare da ita, acewarta ya kamata suyi sallama da AA dan ta kaisu sunyi da Abah yanata musu godiya, a can kuma suka sami Mamy itama. Kiran wayar AA datai a kashe kuma Fawzan ya tabbatar mata yana gidan sanda suke buWar kai ya shigo ya sata biyosu.
Rungume Maanal dake zaune a bakin gado ta takure waje guda tana sharar hawaye har yanzu tayi, cike da tausasawa ta shiga lallashinta. Kafin ta bata umarnin hawa sama ta kira musu AA Win. Mayafin lafayarta ta gyara da yau, tayi yau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan amshinta daban ne, ga unshinta raWam yanata Waukar ido daga bain har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autan ta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai Worewa kuma.Tare da Oum suka baro bedroom Win nata suka haura sama. Zuciyar Maanal bata arasa fashewa ba sai da ta hawo upstairs Win, ya subahannallah komai yaji, ga wani mayataccen amshi mai ratsa zuciya. Zama Oum tayi a Waya daga kujerun, Maanal Win zata zauna itama ta katseta tana nuna mata kofar bedroom Win AA. Jikinta cike da sanyi ta nufa ofar, tana gab da isa sai gashi an buWe. Cak ta tsaya tana kallonsa. Kamar yanda shima yake kallonta irin na mamakin nan dan ko motsinsu bai jiba. Yama fito ne zai fita dan dama wanka ya shigo yayi rabonsa da wanka tunna safe manyan kayan jikinsa sun takurasa shiyyasa yazo yay wankan ya canja da ananu. Juyawa kawai Maanal tai tabar wajen, shima sai bai ce komai ba ya biyota saboda hango Oum zane a falon.
Bata zauna ba, sai tai kamar ana kiranta a waya ta gudu ta barsu dan ta basu damarsu. Murmushi kawai Oum tayi danta fahimci wayo Maanal tayi ya gudu babu wani kiranta da akayi. Bedroom Winta ta wuce inda su Nene suke. Bata wani jima ba Oum ta shigo da sallama itama. Ta sanarma Nene ga AA zai shigo suyi sallama. Gyagygyarawa suka shiga yi kafin ya shigo bakinsa da sallama. Duk suka amsa banda Maanal datake kallon hotunansu a wayar Aunty Sakina. Cike da girmamawa ya rissina ya gaida Nene, hakama Aunty Sakina duk da ba girmarsa tayi ba, amma tunda akace matsayin anwa take a wajen Ammie yake girmamata. Shahidah ta ce,  Oh mu baza'a gaishemu ba Ajwaad .
Hararrata yay ya Wauke kai. Su Nene suka sanya dariya. Oum da itama ke dariya tace,  Gaskiya fa Shahidah ta faWa Auta, dan yanzu babu batun ar gaddamar cewa bata girmeka ba matsayin yaya take dai .
 Ni banzanyi Auntys da su ba Oum, Aunty Sakina ta isheni . Yay maganar asa-asa yana hararar Amaal itama. Dariya kowa keyi, Amal ta ce,  Ni dai na haura ma Yaya Ajwaad basai kace min Aunty ba, dan nasan bama cewar zakai ba. Kuma nima bazan so kace ba dan kai Yayana ne .
Oum ta ce,  Amaal yada saurin sallamawa haka .
 Oum gara na sallama wlhy, dan kozan mutu na dawo Yaya Ajwaad bazai ce min Aunty ba kema kin sani .
Nan ma sosai suke dariya. Shi ko ya fuske abinsa. Sai ma satar kallon Maanal yake ta asan ido. Itako tayi kamar bata san ma da shigowar tashi ba, rabin fiskarta ma gyalen ya Wan rufe. Godiya sosai AA yayma Nene, tare da alawarin zuwa gaisheta nan kusa in sha ALLAHU ita da su Ammie. Sosai Nene taji daWin hakan ta kuma sake yaba AA Win dan tarbiyyar sa ta birgeta sosai. Leda dake a hannunsa ya miama Oum, yace ta basu, bai jira cewar kowa ba ya mie bayan Oum ta amsa ledan ta miama Nene tana murmushi. Amasar ledar Nene tayi tana faWin,  Tofa mi muka samu kai Wan nan.....
Ta kasa arasa maganar sakamakon tozali da tai da kuWaWe an dubu bugun Abuja sabbi fil. Da wani irin sauri ta kalla Oum, sai kuma ta girgiza kai tana mia mata ledar.  Bazamu amsa ba Wiyata. Ai abun ma sai ya zama rashin hankali .
Roonta Oum ta shiga yi itama, amma Nene ta dage akan bazasufa amsa ba. Sai ma ta mie tana ficewa tunda su Amaal da Aunty Sakina anan za'a barsu su arasa gyara mata gidan sai zuwa anjima kafin anguna su shigo dan ba'a barta ita kaWai ba. Shahidah dai zata bisu saboda sai sun koma ta gidanta. Suma su Maanal Win fitowa sukai yi musu rakkiya, tuni AA ya haWa motocin da zasu kaisu can gidan Shahidah su Wauka sauran kayansu sai su kaisu train station. HaWa ido yay da Maanal dake sharar hawaye Aunty Sakina rie da hannunta. Su su Aneesa nata tsokanarta wai sai sun dawo Abuja suna bata kulasu ba. Suna ma haWa ido da AA Win ta risinar da idannunta asa. Haka suka shishshiga mota Oum ta dana ledar a hannun Shahidah, zatai magana ta harareta da mata alamar tai shiru. Dole tai shirun kuwa suka wuce. Ciki su Amaal suka koma da Maanal dake kuka sosai, AA ya girgiza kai kawai ya shiga mota ya fice a gidan dan zaije wajen abokansa dake shirye-shirye tafiya suma. Wasu dama tun safe duk sun wuce sai wanda suka rage da zasubi flight Win yamma....

_________&

Mamy dai ciwon kai ya hanata sukuni, gashi tasha magani babu wani canji, dole Hajiya Turai ta ara turo musu Nurse Win nan ta dubata. Cikin damuwa ta ce,  Hajiya akwai matsala fa gaskiya, in dai bazaki rage wannan damuwar ba bp Winki fa bazai taSa ya sauka ba. Gashi zuwa yanzu hatta bugun zuciyarki ya canja. Jininki kuwa ba'a magana wlhy, shiyyasa ma kike ganin dishi-dishi ciwon kan kuma yai sauka. Dole zan sake miki allurar barci mai arfi sosai dan ki samu barci, amma ki sani allurarnan barci kawai zata sanya ki, kwanciyar hankalinki shine maganin matsalar  .
Ita dai Mamy komai tama kasa cewa, dan abun duniya ne ya taru yama zuciyarta rubdugu. Haka Nurse ta mata allurar barci. Tun tana kallonsu da saurarensu har barci yay awon gaba da ita.....

Oum bata san wainar ba ake toyawa ba, tana a tsakkiyar an uwanta dan duk dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce su kuma. Itama Oum Win bata kawo komai a ranta ba tunda taga Mamyn na zagaye da nata an uwan ne. Duk da dai duk yau bazatace tama ga giccin Mamy ba, koda yake ko Abah ba bi take takansa ba tanata hidimarta.

& Bayan sallar isha'i su RK da ire-irensa dake sa'oin su AA a family Win na Darma suka iso gidan domin masa rakkiya. A dai-dai lokacin ne su Amaal ke fitowa cikin shirin tafiya ita da aunty Sakina. Sun sake gyara ko'ina na sashen sun baza uban amshin da har a compound ana jinsa masha ALLAH. Sai da suka shirya Maanal Win itama da taimakon Hajiya Shuwa. An mata wanka da turare iya wanka fiye da yanda ake mata shi tun fara gyaran jikin nan. Kafin Hajiya Shuwa ta naWeta a cikin sabuwar wata lafayar ar ubansu mai shegen yau kalar peach da Wan fari-fari, sai uban stones saketa waliya a jiki, an mata kwalliya ar dai-dai a fuska aka sake mata turaren turare. Sai Wauri daya zauna mata akai sannan aka rufeta da lafaya Win. Suka saka mata ac dai-dai misali aka zaunar da ita a tsakkiyar kadon Wakin nan asa Win, Hajiya Shuwa tace su barta anan idan AA Win yazo da kansa sai ya mata jagora Upstairs Win idan ar rakiyar tasa sun tafi. Suna jin shigowar motocin su AA suka fito dan dama su suke jira. Suka ma Maanal wayon cewa bara suje wajen Oum kafin su AA Win su gama. Dan tun Wazun take roonsu su kwana anan, ganin zata botsare musu da kuka sukace sunji zasu kwana. Shine suka mata wannan wayon suka gudu. Dan ko sashen su Oum Win basu koma ba ganin can su AA suka shiga....

&Su AA sun shiga falon Oum a dai-dai lokacin da dukkan mayan matan family Win ke zaune zaman jiran su, dan dama a'ida kenan ga duk wani angon family Win a lokacin masa rakkiya Wakin amarya. Kuma abinda zai birgeka isu-isu sukema juna rakkiya ba abokai ba. Su duka su a asan carpet suka zauna dan duk iyayene. Yayinda AA yaje gaban Oum ya zauna, cike da sanyi ya Waura kansa a saman gwiwoyinta ya wani lumshe idanu. Abin mamaki sai ga hawaye. Murmushi sosai Oum tai saboda jin saukar hawayen nasa a saman afarta, cike da kulawa da tsantsar so irin na uwa ga Wa ta duo ta lea fuskar tasa. Kukan kuwa yake yi da gaske, itama sai taji hawaye sun cika mata ido. Ta dai daure tasa bakin mayafinta ta share masa su. Kafin a hankali cike da kulawa ta ce,  Haba Auta na yau ai ba ranar kuka bace, ranar farin ciki ce mun mallaki Maanal na har abada in sha ALLAHU. Dan haka bana son ganin hawayen nan kaji Babyna, addu'a zamuyi mu godema UBANGIJI daya nuna mana wannan rana bayan jarabawoyin da muka tsallake Abaya. Harma mu haWa da sadaka domin nuna farin cikin mu ga ALLAH okay .
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya buWe idonsa yana kallonta, tare da kamo hannunta ya sumbata...........
'





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai ==O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'7 0


______________


........Cike da tsokana RK ya ce,  Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa .
Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya Wauka fillo ya jefa masa. Cafewa RK Win yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta

Please Login or Register in order to submit comment