Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga. Ya rufe su ya zagaya mazaunin driver ya tada motar suka fice a asibitin.
AA dai tuni ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, sai dai hannunsa na rie dana Maanal yai saki. Ita dai tana Wan kallon waje ne da mutane dake ta kai kawai duk da rana ta Wan Waga. Basu wani jima ba suka iso hotel Winsu, nan ma suna rike da hannun juna suka fito, Mr Li ya taimaka musu da kwasar an tarkacensu zuwa ciki.
An gyara Wakin nasu tsaf an canja bedsheet. Mr Li dama daga ofar Waki bai shigo ba ya juya, sai itace ta amshi kayan ta shigo da su ciki. A bakin gado AA ya zauna, ita kuma ta ajiye kayan data amso inda ya dace. Kafin ta kallesa murya a asa ta ce,  Ko zaka fara yin wanka ne? .
Idanunsa ya Wan zuba mata, ganin tai saurin janye idanunta a kansa sai yay ajiyar zuciya.  Uhmm kawai yace mata ya Wauke nasa shima. Itama bayin ta nufa batare data sake kallonsa ba. Bata wani jima ba ta fito, kallo Waya ta masa ta Wauke idanun ta dan ya cire jallabiyarsa daga shi sai boxer, muryarta har Wan sarewa take wajen sanar masa ta haWa. Shima sai baice komai ba ya mie ya nufi bayin. Itama kayan da zai saka ta fiddo masa, ta kuma fidda nata ta ajiye gefe. Fin mintuna ashirin sai gashi ya fito sanye da fara tas Win bathrobe. Baima gama zama ba ta Wauki nata kayan ta wuce bayin, bata fito ba sai da ta shirya tsaf. Tako yi yau cikin doguwar rigan, sai dai tana Wan jin takura saboda yanda rigar ta wani lafe mata a jiki ta kuma fitar da shef Winta yanda ya kamata, duk da bata matse mata jiki bane, kawai taushin rigar da yanda aka fitar da ita da ainahin shef na mutum ya kawo hakan. Haka dai babu yanda zatai ta fito, sai dai ta saki mayafinta ya rufe mata irji har ma zuwa cikinta. Bayan ne dai babu yanda ta iya. Fitowarta dai-dai ana knocking ofa, canta nufa, hakan ya bama AA damar ganin bayanta. Ai da saurinsa ya janye idanunsa a wajen maogwarinsa na wani irin kaiwa sama ya dawo asa a cikin wuyansa. Maanal dai data buWe ofa bataga kowa ba, sai Wan abun nan na kawo abinci kawai a ofar. an juyowa tai ta kalla AA daya duar da kai yana danna iPad...
 Abinci ne? .
Ta faWa a taaice. Batare daya Wago ya kalleta ba muryarsa a asa kamar tatan ya ce,  Ni nai order . Kanta kawai ta jinjina ta jawo Wan keken ciki ta maida ofar ta rufe. A gaban gadon ta tsaida shi dai-dai inda yake. Ganin zata kai asa ya kalleta, da ido yay mata nuni da gadon, tai Wan jimm sai kuma ta mie ta koma ta wajen afafunsa ta zauna.
 Ko dai zaka koma can kaci abincin ne? . Tai maganar tana nuna inda kujerun suke. Wajen ya kalla shima, sai kuma ya maido idanunsa a kanta. Batare daya janye ba ya ce,  Naki ne ai . Itama kallonsa tai da yau,  Kai da zaka sha magani ya dace kaci, ni bama najin yunwa nasha tea a asibiti ma .
Komai bai ce ba, sai ma ajiye iPad Win yay ya sauka a gadon, jan keken yay zuwa inda ta nuna, ya shiga fidda abincin yana jerawa a table Win wajen, sai da ya gama tsaf sannan, batare daya kalleta ba yace  oyaaa taso . Ganin yanda yay da fuska batai musu ba ta mie ta nufi inda yaken. Kusa da shi ya nuna mata, zama tayi tana satar kallon fuskarsa, batare da yay magana ba ya fara Wibar abincin yakai bakinta. Fuska ta Sata, shi kuma ya Wan harareta. Dole ta buWe baki ya fara bata, kusan lauma huWu taga shi baici ko Waya ba. Sai ta dauka wani spoon Win itama ta fara Wibowa cike da jin nauyi takai bakinsa. Baiyi musu ba kuwa ya amsa, sai suka cigaba da bama juna har ta fara cewa ta oshi. Bai matsa mata ba shima kuma bai cigaba da ci ba, taje ta Wakko ledar magungunansa ta dawo, duk yanda suka rubuta ya mata bayani dan da Chaines sukayi, Waya bayan Waya ta bashi yasha. Yana gamawa yace mata zai kwanta. A marairaice ta ce,  Yanzu babu yanda zamuji an gida su san mun sauka lafiya? .
Kallonta ya Wan juyo yayi, sai kuma ya kai kwance.  Zamu kira su amma sai zuwa anjima dan su yanzu dare ne can suna gab da yin sahur .
 Lah anga wata ne? .
Ta faWa fuskanta na washe wa da murmushi. Kansa ya jinjina mata murmushin nata na tasirantuwa a garesa. A cikin maoshi ya ce,  Na gani yanzu a net...
 Masha ALLAH ..
Maanal ta faWa zuciyarta na wani irin sanyi. Wannan normal ne ga dukkan musulmi, muna jin wani irin farin ciki da nishaWi da annashuwa ta musamman a cikin jininmu a duk lokacin da watan Ramadan ya zagayo mana. Muna jin kamar mun shiga wata sabuwar duniya ne, muna jin nutsuwa da arfin zuciya mai cike da harsashi. Muna jin kamar a ranar muka fara riskar watan ne. (Ya rabbi kasa muyita ganin watan Ramadan cike da yalwar rayuwa mai tsaho da lafiyar jiki da tsarkin zukata. Ka gafarta mana kurakuranmu ka amshi ayyukanmu a bisa rahamarka da yardar ka, ka gafartama iyayenmu da al'ummar Musulmi baki Waya da suka rigamu kwanta dama=O=-)...........
'




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai ==O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'3 8


______________


........A yau Waukacin musulman Najeriya suka tashi da azumin watan Ramadan a wasu yankuna na ciki dama sauran asashen Afrika. Sai kuma wasu tsirarun asashe da basu da tazarar lokaci mai yawa da asan ta Nigeria. Yayinda sauran asashen duniya da lokacin Waukar bai kai ga arasa musu ba suketa shirye-shiryen hakan suma.

Anan Abuja ahalin Ambassador Aliyu Darma cike suke da farin cikin fara azumin da kuma kewar rashin jin AA da Maanal. Ga Mamy dai fargaba ce da damuwa cike fal a zuciyarta. A cikin aan nan uku tafi kasancewar a fargabar al'amarin Ajwaad fiye da kowa. Yaro ne mai biyayya, amma kuma yana da taurin kai, sannan yana biyayya ne a gareta a iya abinda ya tabbatar bai saSa shari'a ba. Ta wani gefe kuma tana tsoron kaidin mace, tare da masifaffiyar soyayyar da yakema yarinyar nan. Ta tabbatar zai iya mancewada wani gargaWinta can, shiyyasa tafi kowa matsuwa da agauta a jiran kiransa. Amma gashi har tsawon kwanaki biyu shiru kake ji, bayan duk inda Ajwaad yaje a tafiye-tafiyensa yana sauka baya rufa awanni biyar a asar bai kirasu a waya ko video call ba. Amma a wannan karon sai gashi ba haka bane saboda ya tafi da mace. Macen ma yarinyar data tsana fiye da komai a Wan tsakanin nan saboda arfin abinda take gani a idanun Wanta game da ita. Dan duk abinda kaga Ajwaad baya jin nauyin sakawa a gaba ya kalla a gaban kowa, baya shayin tattali da nuna kulawa a kansa, baya iya Soye feeling na farin ciki a kansa idan yana waje, baya iya rie miskilancin sa a kansa a gaban kowa. To lallai wannan abun ya kai ololuwar girma da daraja a garesa. Itafa yaron nan ya duba tsabar idonta ya sanar mata a yanzu Maanal nada power Win yin komai da dukiyarsa tunda matar sa ce, dan haka bazai iya cewa tabar kamfaninsa yin aiki ba. Tace ya faWa mata ma'anar *MAWAAD* yai, ita kuma a tsorace take da fassarawa bisa ga yanda zuciyarta ke hasaso mata. Shiyyasa take son ya faWa da bakinsa, dan in har ya kasance hakane lallai za'a jisu da Ajwaad fiye ma da gidan nan...
Shigowa Nuratu tana cin indomie tana magana a waya ya katse ma Mamy tunaninta. Binta tai da kallo dai-dai tana mio mata wayar. Ganin yanda tai wani getse-tse a gabanta babu ladabi babu risinawa irin na yaro da babba sai abin ya sosa mata rai. Amma batace komai ba ta amsa, Mamansu Nuratun ce, suka gaisa ta tambayeta ya ibadar azumi da aka fara Mamy ta amsa mata. Cike da siyasa Maman Saheeba ta ce,  Yaya an tafiya an sauka lafiya kuwa? .
Sai da Mamy ta Wan nisa kafin ta ce,  To zamu iya cewa haka, dan muma bamu jisa ba dai har yanzu bai kira ba .
an jimm Maman Saheeba tai, sai kuma daga can tace,  Hummm ke ko Aunty ai ya tafi da mace sai abinda muka gani kam. Kefa da kanki kike sanar min yaron nan duk inda zaije baya rufa awanni zai kiraku yace ya sauka. Amma wannan karon kinji shiru ar iskar ta hana shi kenan, koda yake keko ai bata yar a asa ba tunda nn Asiya tasha kuma rainon Fatimah ce. To ALLAH dai ya jishemu alkairi kada a dawo ana an amaye-amaye, tunda ta samu dama yanzu daga ita sai shi ai bazata yarda su raba Waki ba, sannan duk yanda zata hillacesa ya bata abinda ta saba samu a titi ai yi zatai .
Wani irin tiririn zafi ne ya turnie zuciyar Mamy, muryarta har rawa take dan fushi wajen faWin,  Aiko dana tabbatar masa nice na Wauka cikinsa wata tara nai wahalliyar nauda kuma. Ni na rasa yanda zan yi da yaron nan Nana, nafi shan wahala a Waukar cikinsa fiye da kowa, ki duba yayin haihuwarsa kamar bazan rayu ba jini ya Salle min, inaga tunda cikin Ajwaad ya kai wata biyar a jikina na daina barcin kirki har sai da na haifesa. ALLAH kuma ya walla fin sonshi a rai fiye da sauran amma sam yaron nan baya dubawa.
 Ta ina zai duba kuwa Aunty, gashi nan yanda kika sha wahalar Waukar cikin nashi da haihuwa haka kike shan wahalarsa a yanzu, ai ke dai bar hatsabibin yaro kinji. Irinsu ai sune zakka a cikin aan da ake cewa. Dan basai yaro na rashin jin shaye-shaye ko makamancin hakan yake zama zakka ba a cikin aa. Amma koni taadarancin Ajwaad na ban tsoro, kuma ba komai ya kawo hakan ba sai shegiyar matar nan ta gefenki data ara busar masa da zuciya baya kallon kowa sai ita, baya jin maganar kowa sai ita. Ko tafiyar nan bana raba Wayan biyu itace ta shirya musu ita tunda Yaya ya hana ar gwal Winta ta tare, kinga in akai haka ai za'a samu abinda ake so. Shima Yayan da yake a arashin umarninta yake ya kasa duba gaskiya ya hana. Ai wlhy shi zaki takurawa ya dame su da waya da gargaWi, idan ma ta kama kwana huWu su dawo gida .
Sosai maganganun Maman Saheeba ke shigar Mamy, jin abinda tace akan Abah kuma sai ta nisa, muryarta cike da damuwa tace,  Nana maganar Abansu ma a barta, kin dai san halinsa ba'a cika masa gari kamar tuwon gero yake sai yay nauyi.Tsartar jaraba ce da shi, dan halinsa kaf sune a jikin Ajwaad, sauran an uwansa wasu abubuwa kawai suka Wakko. Amma wlhy Ajwaad bai bar komai na mahaifinsu ba. Da haka cire ma batun shi na sashi a azalzala musu zai harbo jirgina ne da wuri, duk abubuwan dake faruwa badan na kasance mai takatsantsan ba da tuni ba wannan maganar akeyi ba ai. Ki dai bari muyi wani tunanin daban, sannan yanzu dakonsa nake ya kira waya na samu number Win komai mai saui ne ai .
Badan Maman Saheeba taso ba ta ce,  Hakane kuma Aunty. Mu barsa to ya kira a samu number Wib sai musan hanyar kamawar. Bara naje na Wan kwanta naji azumin farkon kamar zai Wan yi duka .
aramar dariya Mamy tayi, tare da faWin,  Ke dai raguwa ce dai . A tare yanzu sukai dariyar, Maman Saheeba tai mata sallama suka yanke wayar. Kallonta ta maida ga Nuratu, sai kuma ta Wauke kanta tana mai girgiza kai kawai. Tunda asuba data tasheta yin sahur tace ita bazatai azumi ba jini yazo mata......

&A Sangaren Oum kam kewar su Autanta ta isheta, amma kasancewar Najma na rage mata. Dan barcinsu ma su suka sha sai kusan sha Waya suka tashi. Sannan ne suka fito falo Najma ta saka musu *SUNNAH TV* sukai zaman kallon tafsir, dan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu fara fita nan cikin anguwar inda malam keyin na mata da safe, na maza da yamma. Sallar azhar ce ta tashe su, bayan sunyi suka Wan kwanta, kusan arfe uku Najma ta tashi ta fito saboda kiran wayarta da Fawzan yayi cewar ya dawo gida tun azhar, gashi a falon Oum tun Wazu baiji motsinsu ba. Koda ta fito ta gaisheshi zama tayi suna kallon tafsir, sai hira jefi-jefi da bata shafi komai ba. A haka Babban Yaya ya shigo shima, da'alama kuma ya Wan jima da dawo gida, dama lokacin azumi basa daWewa a wajen aiki. AA ne kawai idan bai gadama ba sai gab da shan ruwa zakaga ya shigo. Itama dai Oum fitowa tayi. Tana zama babu jimawa su Inte suna shigo dan tambayar miya kamata a rage na aiki, dan duk azumi gaba Waya nan sashen Oum kowa ke zuwa ai aiki, a kuma shirya komai a rumfar bunu dake can compound anan ake buWa baki ko a tsakiyar gida, ana kammalawa su fice sallar asham anan masallacin kusa da su, inda harda AA a masu jan sallar, dan kuwa babban Walibi ne na imam Win massalacin. AA akwai ilimin addini, kuma har yanzu akan nema yake bai zauna ba. Kawai dai idan ka gansa a harkar neman kuWi saika Wauka bokon kawai aka sani. Amma Alhamdullah anan wajen dukansu Oum batai wasa ba a kansu, kowa kansa cike yake da ilimin addini tunda hatta babban yaya har yanzu bai daina zama gaban malamai Waukar karatu ba shiyyasa suke a nushe (KU SAN BOKO BA ILIMIN ADDINI TAMKAR NAMAN KAZA NE A DAFE BA'A WANKE ARNI BA>q) ...

Bayan sallar la'asar badan Mamy taso ba ta tattaro su Saheeba zuwa sashen Oum. Dan cike take da jin zafin Oum Win. Oho ita baiwar ALLAH bama ta hankalta da yanayin Mamyn ba, kawai abinda ta kawo a ranta azumi ne dai na farko da kowa sai ya WanWana kafin a saba. Su duka sun kasance a kitchen harda masu aiki. Abah da Babban Yaya da Fawzan sai Naufal suna massallaci daga Asr basu dawo ba sukai zaman jin tafsir. Abinci mai rai da motsi suka shirya ana ar hira sama-sama. Wajen biyar na yamma sai ga tawagar an hutu daga Kano sun iso. Abah ne kawai yasan da zuwansu. Tuni fuskar Mamy ta sake tsukewa, yayinda ta Oum ta yalwatu da farin cikin ganin aan an uwanta. Domin kuwa samarin yara ne biyar, na Uncle Mahmud biyu, sai na Uncle Modibbo Waya da mace budurwa Waya, sai Waya na Uncle Hussain, Waya na Uncle Hassan. Sai sauran ammata uku, Autar su Nuwaira, sai biyu da suka kasance jikoki suma ta Sangaren Abbah mahaifin su Oum. Najma ma dai sosai take a farin ciki. Tuni aka buWe Wakunan asa na Sangaren Oum, samarin zasu zauna nan, su dukasu kusan sa'anni ne dan duk bazasu wuce 20, 21, 22, ba, su kuma ammatan wasu sun girmi wasu, akwai sa'annin Najma biyu, biyun kuma bazasu wuce 15 ba. A Wakin Najma su suka haWe, duk da Oum tace ya musu kaWan a sake buWe wani Wakin sukace a'a. Samarin kuwa biyu suka rabu. Dan sunce akwai Hashim daya rage shima yana zuwa daga Sokoto Wan Wan uwan Oum ne shima dai ta Sangaren Abbah. Shine wanda su AA suka taSa zuwa gidansa lokacin da zasu je Giro.
ALLAH yaso su Oum da yawa sukai abincin, dan dama Abah nata jaddada musu ayi abinci sosai akwai masu ci. Da suka tambayi su wanene yace sudai su ara kawai. Ashe yaran ne a hanya. Gida kam dai Alhmdllh, sai hakan ya sake ragema Oum kewar su Maanal duk da dai sunan manne a zuciyarta a dukkan motsinta.
Da taimakon yaran aka shinfiWa manyan carpet da dama ana tanadarsu ne dan irin wannan lokacin ne kawai. A compound aka baza su, sannan aka shiga fitar da nau'o'in abinci da suka shirya abinka da mutane da yawa. Dandanan wajen yay yau daka kalla kasan a lallai Ramadan ya kama. Yaran sunata Wauka a waya abinka da an Wore-Woren social media. Da farko Nuratu nata Wauke-Wauken kai, sai dai fa tasha jinin jikinta dan ita kanta tasan yaran a goge suke da ilimi sannan gidan iyayensu akwai kuWi suma, dan sanin kanta ne ALLAH yayma zuri'ar Darma arzii tun na tushe daga iyaye. Hakama family Win su Oum ta Sangaren Abbah, K. Kura yana Waya daga cikin manyan likitoci a asar Najeriya ga shi kuma Wan kasuwa, mahaifinsa shima dai ya tara ya bar musu. Abinda ya sosa mata zuciya yanda yaran suka wani watsar da ita amma su kansu a haWe dan kamar su cinye Najma, haka ma sun janye Anum a cikinsu su adole ga an haWin kan dangi. Humm tasha jin Saheeba da Mamy suna faWin haWin kan Darma Family da masifar son juna da suke da shi, bata tabbatar ba sai a yau ganin an yaran nan yanda suke 5&6 matua. Gasu a nutse babu rawar kai sam a tare da su. A haka su Abah suka shigo bayan sallar magriba, lokacin kowa yaci dabino yasha ruwa sanata yin sallar magrib. Wani irin farin ciki a bayyane kowa ya gani a fuskar Aba, Babban Yaya, Fawzan. Dan tuni yaran sun wani zagayesu. Duk rashin fara'a da yawan magana ta Babban Yaya kamar zai cinye yaran a bayyane dan so. Kai wannan abu na kona ran Mamy, har mamakin irin haWin kan wannan family take yi.....
Abin sha'awa abin birgewa kowa ya nema wajen zama aka fara buWa baki, maza na nan Sangaren mata anan Sangaren abinci a tsakkiya. Kuma duka harda masu aikin gidan ne, harda wanda bama musulman ba duk an jawosu. Wannan itace ainahin Wabi'ar wannan gida, shiyyasa a cikin masu aikinsu mutum biyu sun taSa musulunta a bisa jin daWin wannan yanayin, dan haka suka kyautata rayuwarsu a yanzu haka suna zumunci da su sosai kuma suna zuwa gidan. Bayan an karya da gwargwadon abinda ya sauwaa marasa alwala suka tashi suka sabunta, masu ita suka kimtsa aka fice sallar asham anan masallacin dake kusa dasu dan jikin gidan su Hajiya Shuwa yake. Su kansu anan suka iske su Hajiya Shuwa suma sun fito. Massalacin upstairs ne. asa maza sama mata, kusan an street Win duk anan suke salla, musamman da azumi cika yake tab, wani ma sai a lokacin yake tuna wanene makwafcinsa.......
'




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai ==O_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'3 9


______________

........A Sangaren an chaina kam a yau su kuma zasu Wauki nasu azumin.Dan kammala yin sahur Win Maanal da AA kenan. Yanda ta takura masa da batun kiran an Nigeria ganin da sauran lokacin kammala sahur ma balle ai batun sallar asubahi yay zaman kiransu video call dan yasan a yanzu darene an dawo sallar asham acan. Hakanne kuwa, dan shigowar su Oum Win kenan sun sake zama anan compound masu ara abinci na shiri masu hira nayi sao ya shigoma babban Yaya a waya. Murmushi yayi tare da miama Fawzan dake kusa da shi waya. Fawzan na gama karantawa ya wani kwashe da dariya. Duk kallonsa kowa yayi, baima jira kowa ya tambayesa ba ya mie yana faWin,  Oum ki shirya autanki zai kira video call yanzu .
Aiko tuni fuskar Oum ta washe da sabuwar fara'a, yayinda Mamy tai saurin duban Fawzan. Suko yaran suka shiga Woki zasu ga Yaya AA. Dan tunda suka iso suke tambayar yana ina. AA nada farin jiki ga yaran family Win, dan duk da bai sakar musu fuska indai suka ce suna buatar abu ko bashi suka tambaya ba in dai yaji zai yi musu abin yace wancan ya barsa. Sannan in dai sukai irin wannan zuwa hutun zakaga yana musu saye-saye na abubuwa daban-daban. Ranar salla ko zai sa a kaisu duk inda suke so koma shi ya kaisu. Nuratu kam jikinta har rawa yake, dan tunda Babban Yaya yaje ya Wakko laptop a sashensa ya dawo compound Win ji take kamar taje ta fisge system Win daga hannunsa ta hana kowa ganin AA sai ita kawai. Sai dai babu wannan damar. Ita kanta Mamy abinda take rayawa a tata zuciyar itama kenan.
Cike da girmamawa Babban Yaya yazo ya ajiye laptop Win a gaban Abah, Mamy da Oum na gefe-da-gefensa daman alamar sun gama shiryawa. Kasa hauri da yaran sukai duk sai sukazo suka zagayesu ta baya. Su dai su Saheeba basu motsa ba, amma hankalinsu na wajen, musamman Nibras da Nuratu ji suke kamar su fisge laptop Win.
Tar-tar AA ya bayyana a screen Win, hakama su Abah sun bayyana masa fes shima. Wani irin bugawa irjin Mamy yayi, dan haka kawai sai zuciyarta ta kissima mata ganin AA Win na wani waliyar mutumin daya sha angwanci. Abah da Oum kam murmushin da AA Win ya Wan sakin musu suka mayar masa. Cikin nutsuwar nan tasa da rashin hayaniya ya furta,  Assalamu alaikum. Abah, Oum, Mamy barkanku da shan ruwa .
A tare Abah da Oum suka amsa masa, sai kuma ya shiga gaishesu, dai-dai nan Maanal dake cin abinci a gefensa ta matso jin ya ambaci sunan su Abah Win. Dan ita da farko a tunaninta ma aiki zai yi. Ganin su Oum da tayi sai tai saurin komawa baya dan abin yazo mata a bazata. Dariya Abah da Oum suka sanya, shima AA dai murmushi yayi, kafin ya furta,  Tun jiya fa take rigima a kiraku a kiraku, ni kuma ban samu zama ba saboda Wan fita da mukayi shopping .
Sosai murmushin Abah ya sake faWaWa, cike da tsokana yace,  Haba Babyn Oum mune kuma ake Soye mawa, common zo na ganki .
Sosai kunya ta ara rufe Maanal, ta matso kusa da AA kanta a asa, shiko yai ya Wan gyara ta samu ta zauna yanda ba sai ta raSu da jikinsa ba. A haka ta gaishesu tare da yi musu barka da shan ruwa. Oum ta ce,  Naga takaina ni Fateema, Baby wannan boye-boyen fuskar na miye? .
Yanzu ko AA dariya yayi kaWan, hakan yasa Maanal mintsininsa ta yanda su Oum bazasu gani ba. Fuska ya Sata yana kallon Oum,  Oum kinga ta mintsine ni ba, na rama kuma Abanta yace na masa ba daidai ba .
Cikin dariya Oum ta ce,  Gaskiyarka Auta. Aba kama arka magana

Please Login or Register in order to submit comment