Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake, ga wani ™yallin angwanci da cikar kamala a tare da shi. ˜amshinsa kam gaba Waya ya gauraye da wanda ba nashi ba...........
'þ



Ehem-ehem >Ø#Ý>Ø#Ý=ØÞ<ØÃß<ØÃß<ØÃß




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ´ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =ØÞ=ØOÞ_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =Ø-Þ=ØOÞ_*

*_Typing=ØòÜ_*








*_=ØžÜAJIYA A DUHU....=ØžÜ_*




*_Bilyn Abdull ce >ØÝ<Øûß_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ™ai._

*_My TikTok account =ØGÜ_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=ØGÜ<Øûß_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=ØÞ=ØÞ<ØÃß<ØÃß_

*_BOOK 2_*
<ØÝþ–'1þã 2þã 0þã


______________



......... Oh jama'a, yaran nan jiyya kukeyi ko shargallenku? .
   Oum data le™o ta faWa tana kallonsu. Mu™uy AA ya haWiye murmushinsa yana nuna RK da Fawzan.  Oum kin san in dai waWan nan biyun na a waje to sai addu'a. Sun addabemu ki korasu waje dan ALLAH .
        Oum dake satar kallon Babban Yaya ganin yanda fuskarsa ke ta annuri ga murmushi ya™i barinta ta ce,  Ai za'a kai ga hakan Auta. Kunsa marasa lafiya gaba dan iya shege sai dariya kuke? .
      RK yace,  Aunty ai barci suke. Kuma dariyarmu nutsuwa ma zata basu su duka kedai jeki cigaba da hidimar bikinki Maman anguna .
    Kai Oum ta girgiza kawai da faWin,  ALLAH to ya shiryeku ta juya ta fita. Kusa da Babban Yaya RK ya koma ya tsaya. Da sauri Babban Yaya yace,  Kana cewa tak zan ajiye kawun gefe nima nayi ta auta yau. Tunda na fahimci kai da Fawzan kun zama ´an iska yanzu .
        Ai yanzu kam AA sai da ya dara. ALLAH sarki babban Yaya yana tsoron yan iskan biyu su tasashi gaba. RK da Fawzan kam dariya ba'a magana. RK ya ce,  Haba Son yada tsarguwa haka? Nifa tambaya kawai zanyi amma kana neman fassarani da wani abu kuma .
      Babban Yaya ya hararesa da faWin,  Bar tambayarka na yafe. Shiyyasa auta ya raina ku wlhy, manyan banza ne anan kawai. Kudai tuna ga Lilly nan kwance zata iya farkawa ta jiku. Ga kuma Mamy .
         Cike da mugunta RK yace,  Ai Mamy barci take bil ha™™i, Lilly kam tashinta ba yanzu ba.
     A hankali hawaye suka silalo ta gefen fuskar Mamy, kasancewar tacan take kwance ta juya musu baya ba gani suke ba. Tsinuwa take jerama RK a zuciyarta tari-tari. Dan yau tsanar da take ji tana masa tafi ta kullum shi da kowa ma dake a Darma Family. Wani irin sukar zuciyarta da ™onata dukkan hirar da sukeyi take mata. Zuwa yanzu ji take tazo gaSar da bazata iya ha™uri ba, dan in har tai hakan lallai Fateema na shirin cinta wasa ne. Kuma wannan cikin tayi alwashin ko zata tafi tsirara sai ta zubar dashi wlhy. Manaal bazata taSa haihuwarsa ba...

  Ehem-ehem. Ashe watan samun matsalar AA da Mamy ya tsaya kuwa>Ø-Ý, dan wannan cikin duk wanda yay gigin taSashi to bara dai nai shiru, Wan soyayya ne fa, komu ai sai inda ™arfinmu ya ™are ko ya kukace mutane na?=ØÞ=ØÞ

_______&
     
      Anan Mamy na a birkice da batun ciki can ma Sangaren Nibras da Saheeba da su Nuratu da uwarsu cike zukatansu suke da ba™in ciki bayyananne kai kace sun haWa miji ne da Maanal Win su duka, dan kishinta suke ji na gaske a zukatansu bayan kishiyoyin nasu. Karan farko Nibras taji wani abu mai kama da tashin hankali a ™asan zuciyarta game da haihuwa. A sati huWu kacal cikin na biyar Maanal nada cikin masoyinta AA, itama Najma fa nanda wata sati biyar Win za'a iya cewa tana da cikin mijinta kuma. Hakama Ameerah zata iya samu. Ga Saheeba ance ciki ne da ita itama. To itafa?. Zuciyarta tai wani kalar motsawa. Ai babu shiri ta Wauka waya ta kira mamanta ta labarta mata komai. Itama dai Maman tata hankalinta ne ya tashi, dan sak irin tunanin Nibras Win ne yazo mata. A sanyaye Mom dinta ta ce,  Nibras kodai kinsha wani abun hana Waukar ciki ne a farkon aurenku? Shekara biyar ana shirin kulle ta shida ba wasa ba. Kin fa samu Saheeba da tsohon ciki a gidan nan, ta haihu kina nan, ta raina ta yaye ta sake samun wani ta haifa ta raina ta yaye, badan ma jinkiri data samu ba da yanzu maybe tayi wani wannan cikin da akace ta samu zai zama na huWu ne. Ga kuma wadda aka auro jiya-jiya itama harta samu. Suma wannan da suka shigo karki raba Wayan biyu nan da sabon wata su fara nasu amaye-amayen tunda Waukar cikin yanzu ba wuyane da shi ba. Shi ke nan kin zama ´ar kallo mu da dukiyar Darma sai hasashe daga nesa muna ji muna gani wasu naci. Lallai muna cikin babbar jarabawa, dan ba haukan kishi ya kamata na tayaki ba Nibras rashin samun cikin ki ya kamata ya dameni ma a wannan gaSar. Nibras kinsha wani abu ne? Ki gaya min dan ALLAH nasan ina zan kama ina zan samo mafita .
      Shiru Nibras tayi kalaman mahaifiyarta na mata luguden daka a zuciya da ™wa™walwa. Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa daga can.  Nibras! Magana nake dake fa kika min shiru! Ki faWa min kinsha wani abun hana Waukar ciki ne dan ubanki?!!! .
      Tsabar yanda tsawar ta ratsata sai da ta zabura jikinta na Wan rawa. Sai kuma hawaye sharrr suka shiga ziraro mata kamar an buWe fanfo. Tasan halin mahaifiyarsu sarai, da abinda zata iya, ta musu raino na gata musamman ma ita da take mace, amma idan tana son abu bakai mata ba ka banu, sarai zata iya Waukarta takai asibiti a bincikata. Dan haka gara ta faWa mata gaskiya kawai. Murya na rawa ta ce,  Wlhy Mom allura ce kawai nayi kuma lokacin ma da sukace zata daina aiki tuni yayi, kuma wlhy daga nan ban sake zuwa nayi ba, ban kuma sake shan komai ba shekara kusan huWu kenan .
       Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Amma ban taSa sanin ke wawuya ce ba mai dusa a cikin kai irin yau. Ashe ni wahalar banza ma nake. Nibras dama ke muguwar yarinya ce ban sani ba. Wlhy dana san abinda zakiyi kenan da ni na auri Aliyu Darma Win ma kawai bayan mutuwar ubanku, kuma wlhy babu abinda zai hana na haihu masa a shekarun nan nawa. Ai shike nan sai ki fara shirin dawowa gida mu cigaba da goga jigida dan amarya dai kam ta gama samun gida. Dama gata ´ar uwarsa, ke da kanki yanzu kike faWin irin murnar da sukeyi akan cikin facalarku, shiyyasa dama gaki nan ko kwarjini baki da shi a gidan, to kin kasa sama musu abinda suke so mara hankali wawuya kawai......
     ˜itt ta yanke kiran. Wani irin fashewa da kuka Nibras tayi dan kamar uwarta ta mata wata allura ne mai ™arfin gaske a yanzu.....

&&

      A Sangaren su Saheeba kam, ko le™owa duba Mamy basuyi ba kuma sunji sarai ance ta faWi, balle Maanal ta samu itama, suna can suna ™ulla hanyar salwantar da cikin Maanal Win kamar yanda Mamy tai alwashi. Maman Saheeba ta rantse ta ™ara rantsewa Saheeba ce kawai zata haihu a gidan sai Nuratu idan ta shigo itama. Amma har Najma da Ameerah da Nibras basu isa ba, dukiyar Aliyu Darma ta ´ayanta ce kawai a gidan. Har Mamy data haifi ´a´an zero zata tashi. Balle Oum datai wahalar banza.
     Saheeba dai da akema ™arin ruwa hawaye kawai take yi, hakama Nuratu kuka take rurus jikin Hajiya Turai data zo da likitar data duba Saheeba. Dan da wani mugun zazzaSi ta tashi tanata sambatu dole Nuratu ta kira Nana ta sanar mata. Shine Babban Yaya na fita suka shigo bayan hanyar bedroom Win Ameerah tasha harara. Hajiya Shuwa kanta yau tasha zagi gwargwadon iko bama Oum kaWai da Babban Yayan kansa ba.
     Suna gama ™ulle-™ullensu Hajiya Turai data fito tai kiran Sille ta labarta masa komai. Dariyar mugunta yayi da faWin,  Ai na daWe da gane shegiyar matar ™anin nan naki mayyar kuWi ce. Shashasha kafin ´a´an nata su gama haihuwa mazan nasu su mutu ni na gama tatikesu tas. Dan sai na ™arar da abinda kamila ta tara kaf ta koma amso na ´a´an nata tana tura min, ™arshe ta fara satar na mijinta shima dan ubana ma nada ha™™i a ciki ai.... sai kuma ya wani kwashe da dariya cike da mugunta. Hajiya Turai na tayashi. Dama Haule ta kira shi ta gaya masa komai na zancen ciki da faWuwar Mamy yanzu babu jimawa....

_______&

       Barci Babban Yaya ya bar Ameerah nayi, dan haka bata san wainar da ake toyawa ba sai kusan sha Waya ta farka. Wani irin zazzaSi take ji a jikinta, ga ciwo da ko'ina ke mata. Tunda taga babu Babban Yaya a Wakin tasan ya fita ne. Sai dai akwai wayarsa Waya ajiye bed side drawer. Cikin dauriya ta Wan kintsa Wakin ta shiga bayi tai wanka ta sake gasa jikinta yanda taga yayi mata Wazun. Sai kuma cikin ikon ALLAH taga maganin da Mommy ta dinga dafama Maanal tana sit bath. Tunanin itama tayi amfani da shi ne yazo mata. Dan haka koda ta fito a wankan sai ta zura dogon hijjab ta Wauka Wauri Waya ta fito cike da dauriya domin dafawa a kitchen. Gida cike da mutane ai bataso a shigo a ganta tana wannan tafiyar gwale-gwalen ba. Sannan ai ya kamata ta fita ta gaida su Oum amma take a haka ai da kunya. Dan duk wanda ya ganta ALLAH sai ya gane abinda ya faru. Ga idanu a kumbure tasha kuka. A bisa tsautsayi ta fito Win ne tana shiga kitchen taji wayar da Hajiya Turai keyi, kuma tas taji abinda ta maimaita ma wanda suke wayar da Nana ta faWa. Mamakin duniya ya zagaye zuciyar Ameerah. Gabanta ko sai faWuwa yake. Da sauri ta baro kitchen Win ta koma Wakinta zuciyarta na kai-kawo da fasa maganganun dalla-dalla. Tofa babbar magana, shin Maman kishiyar tata ba uwa Waya uba Waya suke da Mamy bane? Kamar dai haka ta sani tun tuni. To kenan akwai wata a tsakaninsu kokuma AJIYA A DUHU Maman Saheeban keyi batare da sanin Mamy ba. Wato su bazasu haihu ba sai ´a´anta kawai. Tur™ashi. Eh lallai tasan yau ta shigo family house aure kam. To lallai akwai tsallen baWake kenan. ALLAH sarki Maanal ashe ciki gareta, ta tayata murna sosai ita da Yaya AA, kuma sai inda ™arfinta ya ™are wajen kare cikin nan. Za kuma ta sanya ido akan su Saheeba ™warai d gaske..........
'þ
    

Tofa, sabon wasa kenan tsakanin su Saheeba da Ameerah >ØqÝ=ØÞ



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ´ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =ØÞ=ØOÞ_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =Ø-Þ=ØOÞ_*

*_Typing=ØòÜ_*








*_=ØžÜAJIYA A DUHU....=ØžÜ_*




*_Bilyn Abdull ce >ØÝ<Øûß_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ™ai._

*_My TikTok account =ØGÜ_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=ØGÜ<Øûß_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=ØÞ=ØÞ<ØÃß<ØÃß_

*_BOOK 2_*
<ØÝþ–'1þã 2þã 1þã


______________


.........Turo ™ofar da akai ya katse mata tunaninta. Ta Wago tana kallonsa. Shima dai kallonta yake cike da wani yanayi mai sanyi. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali zuwa inda take. Zama yay kusa da ita ya sanyata a jikinsa cike da kulawa ya ce,  Kin tashi? .
     Kanta ta jinjina masa kawai, dan bata jin ma yin magana sam. Zafin da yaji a jikinta ya sashi faWin,  Ya salam zazzaSi ne jikinki haka? Aiko bara na kira Uncle Rafeeq ya duba ki .
    Ganin duk yanda ya rikice ta ri™o hannunsa tana Wan girgiza masa kai. Cike da shagwaSa da disa-sashshiyar muryar ta ta ce,  Bafa sosai bane zan warke baga maganin daka bani ba Wazun zan ™ara sha Yaya .
       Bazai yiwu ba Ameerah .
Babban Yaya ya faWa yana Waukar wayarsa. Layin RK ya kira. Lokacin suna fitowa shi da Fawzan daga sashen Oum saboda dangin Mamy da sai yanzu ne zasu wuce. RK ya Waga, babu wasa a muryar babban Yaya yace ya tura masa likita zata suba Ameerah bata da lafiya. Jimm RK yayi, sai kuma ya danne dariyarsa da ™yar yace,  Okay bara na bincika wake asibiti a yanzu cikin matan, ALLAH ya bata lafiya .
Da Amin babban Yaya ya amsa.
   Yana katse wayar suka kalli juna shi da Yaya Fawzan.  Babban Wa fa yayi aika-aika da alama .
         A haba dai? .
Cewar Yaya Fawzan.
RK ya ce,  Gashi ya kira a nemi likita amarya babu lafiya, sai dakewa yake bai san na harbosa ba. Wai kai dan ™aniyarka ma mika zauna jira ne ana hayya-hayya kai kana nan gulma a cikin gida .
     Fawzan da dariyar Babban Yaya ke cinsa ya ce,  Oh mudai munga takanmu ALLAH ya bamu kawun banza. Haba shiyyasa naga Babban Yaya ya kasa zama hankalinsa duk yana can ashe yasan yabi dare kai jama'a girma yayi tangal-tangal
     Dariya shima RK Win yake yi, ya ce,  Kaima fa a ne wlhy Son. Amma ba komai zuwa zan na haWe kai da Ajwaad kaima mu maka tas gobe. Sai muga yaya naka girman zai yi tangal-tangal Win kaima .
       Karen hauka ya cizan kusan nayi, ai nasan Auta ma wannan shiru-shirun da yake jirace yake dani munafukin, shiyyasa Waukarta zan mubar gidan, gara muje honeymoon ma dawo muku da result .
     Kiran wayar da akai ta hana RK bashi amsa ya danne dariyarsa da ™yar ya daga kiran ya fara magana. Dai-dai nan kuma Najma ke fitowa daga sashensu ita da su Lailah zasu rakata gaida su Oum daga nan ta duba Maanal dan har an baza mata labari. Gaba Waya hankalinsa ya koma kanta. Tayi wani shegen ™yau daka ganta kaga amarya. Ya zubama lips Win daya gama morewa Wazun da safe idanu. HaWa ido da sukai da Najma ya sata du™ar da kai cike da kunyar abinda yay mata da safen itama, sai take jin kamar kowa idan ya kalleta zai gane ne. Kanta a ™asa ta ™araso inda suke ta gaida RK cike da girmamawa. Kamar ba shi ba ya wani dake yana amsawa da kulawa. Ta Wan kalli Fawzan ™asa-™asa tace  Sannu Yaya .
      Shima ™asa-™asan ya ce,  Yauwa sannu ™anwa .
     Kallonsa RK yayi baki buWe. Fawzan ya hararesa. Sai kuma ya maida kallonsa ga Najma,  Je ki dubasu wajen akwai zafin rana .
     Kanta ta jinjina a kunyace ta wuce. RK yace,  Eh lallai yau naga bariki, bafa Ajwaad bane kawai ™wallo a gidan nan kowa kwar-kwar Win kansa ne na lura .
       Ai karatunku muke bi kaida Yayunka su Abah. Idan bamu zama kwar-kwar Win ba zamu ™ara muku yawa ne. Ka jimin sa ido, kai mafa ko Waga ™afa babu mukaga Aunty Nuwaira na amaye-amaye ga ™aninmu nan na shiga wata na shida a ciki .
          Oh, nima iskancin zaka min to nayi nan . Dariya Fawzan ya sanya. Cikin Wan Waga murya yace,  Ai yau kaima sai kaji a jikinka bari dai Auta ya gama jiyyar ya fito .
     RK dake shigewa sashen Abah ya ce,  Idan kun ganni kenan . Ya ™arasa shigewa....


________&

        Su Ammie sun iso Kaduna lafiya. Sadda suke isowa gida sun sami ´an sanda na jiransu. Hajiya Yaya kuma ta farfaWo an sakata barci dan jininta daya haura ya sauka. Sai da suka fara zuwa suka dubata yaran sukai musu bayanin iya abinda suka sani suma ganin Wakin Hajiya Yayan kaca-kaca yasa babban Wan sandan faWin suma ya kamata su duba sashensu duka ko za'a samu wani abu. Dan maigadi ma dai an bugar da shi ne har yanzu barci yake. Likita kuma daya dubashi ya tabbatar musu tun kusan takwas na dare aka bugar da shi Win.
    Al'amarin ya sake bama Daddy da su Ammie mamaki. Badai suce komai ba kowa ya nufi sashensa dan dubawa. Hajiya Basariyya ce ta fara fitowa a haukace tana kuka da ihun ta shiga uku an yashe mata komai. Babu abinda aka bar mata kaddararta sai sutura. Sai ga Daddy ma ya fito a rikice. Yace ai shima komai an yashe, takardunsa da duk wani abu mai muhimmanci babu shi. Dama su Amrah sun faWa musu na sashensu duk an tattare suma. Fitowar Ammie tace ita gaskiya ba'a ma shiga ba dan komai yana a yanda yake yasa Hajiya Basariyya dake kuka riris sake fasa ihun tashin hankali. Yanda take kuka da ihu sai da abin ya bama kowa mamaki, can kuma sai gata ta zube a ™asa babu numfashi babu alamarsa. Babbar magana, babu shiri su Ammie sukai kanta, yara suka kawo ruwa aka zuba mata ta kawo numfashi, sai ta hau sambatu kamar wadda kan ya taSu. FaWi take shike nan an talauta su, ita babu Daddy babu, miyasa ita Ammie ba'a Wiba nata ba. ˜ilama itace ta saka aka kwashe musu.....
     Wata gigitacciyar tsawa Daddy ya daka mata. Cikin matu™ar faWa ya ce,  Halan kin haukace ne Basariyya? Matar tawa kike jifa da wannan mummunan aiki. To ki iya bakinki idan ba hakaba wlhy zakiyi kuka biyu shashasha kawai da bata da girma sai na jiki .
       Yanda yake faWan sai da kowa ya nutsu, sai Ammien ce ke lallashinsa ma da ido. Amma ya™i kulata itama dan harga ALLAH yaji matu™ar haushin kalaman Hajiya Basariyya. Ko ina ´an sanda saida suka shiga, suka ga komai daya faru sukai hotuna da aune-aune dan a bincika ko za'a samu hoton yatsu. Duk wannan bidiri da akeyi babu Nazeerah babu Yaya Yazeed. Suna sashensu kamar ma basa gidan. Hajiya Basariyya dake a birkice dan sai kika take ta ce,  Wlhy bazan yarda ba, a binciki matar Yazeed, mudai itace ba™uwa a gidan nan, yaranmu duk mun san halinsu .
     Kallonta Ammie da Daddy sukayi, sai kuma suka kalli hanyar sashen Yazeed Win. Salima ta ce,  ALLAH Ummi nima nayi wanan tunanin, kuma fa tun Wazun duk ihun kukan da muke ko le™e bata fito ba, dama shi Yaya sai ta bashi umarni zai yarda ya fito . Ta share hawayenta. Da yake yaran suma babu wadda suka tsana yanzu a duniya irin Nazeerah Win duk sai suka goyi bayan zancen Hajiya Basariyya. Šan sanda yace,  Waye Yazeed Win wacece Nazeerah? .
        Daddy ya gyara tsaiwarsa da faWin,  Yarona dai daka sani, ita kuma matarsa ce .
        A to ya kamata su fito, munata kai-kawo tun Wazun sunyi shiru, ni nama zata yaran nan ne kawai a gidan ai Alhaji. Kai kofur Hamza yi musu knocking .
      Wanda aka kira da kofur Hamza ya amsa da faWin,  Yea sir . Yana nufar sashen Yaya Yazeed.
     Knocking yayi har sau fin biyar sannan aka buWe a fusace. Nazeerah zata fara bala'i taci karo da kofur Hamza. Dama fuskar marasa mutunci ce da shi ai da gudu ta haWiye abinda tai niyyar faWa. Sai dai cikin ™arfin hali tace,  Lafiya .
       Lafiyar ce ta kawo haka, ku fito ke da mijinki ana nemanku .
    Šan jimmm tayi, sai kuma ta saki ™ofar tana faWin,  Yana ciki bari na kirashi .
           Basai kin koma ba kirashi daga nan inda kike .
    Rasa yanda zata yi tai, gashi sai mazurai yake mata. Dole ta Waga murya daga nan ta ™walama Yaya Yazeed kira. Sai ko gashi ya fito da saurinsa daga kitchen, da alama girki yake mata. Mamaki ya kusa halaka kofur Hamza, ganin har Wan du™awa Yazeed yay yace mata  Gani .
        Batayi magana ba ta fito, sai shima kofur Hamza Win yace masa ya fito. Amma Yazeed yay tsaye yana kallon Nazeerah. Dan in batace ya fito ba bazai fito ba. Kofur Hamza ya sake jinjina kai yana gaskata maganar yaran can, kai wannan koba ita ta aikata ba itace ta saka aka aikata dole. Tsawa yay mata, tai tsalle gefe tana tura baki gaba ga ciki tirtsi-tirtsi. Ta kalla Yaya Yazeed tana kumbura baki ta ce,  Malam ka fito fa akace . Ai a zabure ya fito kuwa. Sai Kofur Hamza ya sake mutuwa a tsaye a ransa yana ayyana (Kaga mata ´an wuta ™uru-™uru tun a duniya. Yo wannan ta mutu a haka ai tasan makoma itama). Haka dai ya tasasu a gaba har inda su Daddy suke. Babu wanda Yazeed ya gaida yana tsaye a gefen Nazeerah. Itama kuma bata gaida kowa ba. Daddy ya girgiza kansa zuciyarsa na masa zafi sosai. Ammie kam ™walla ne suka cika mata ido ranta fal tausayin Yazeed da Hajiya Yaya.........
'þ
    




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ´ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =ØÞ=ØOÞ_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =Ø-Þ=ØOÞ_*

*_Typing=ØòÜ_*








*_=ØžÜAJIYA A DUHU....=ØžÜ_*




*_Bilyn Abdull ce >ØÝ<Øûß_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ™ai._

*_My TikTok account =ØGÜ_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=ØGÜ<Øûß_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=ØÞ=ØÞ<ØÃß<ØÃß_

*_BOOK 2_*
<ØÝþ–'1þã 2þã 2þã


______________



........Tambayoyi ´an sandan suka fara musu. Sai dai Yazeed baya amsawa sai Nazeerah. Sai da kofur Hamza yace,  Idan bata bashi umarni ba bazai taSa magana ba fa sir.
     Mamaki ya kama ogansu, ya kalla Daddy. Sai kawai Daddy ya Wauke kansa. Ya fahimta, dan haka baiyi magana ba yay shiru. Cigaba yay dama Nazeerah tambayoyi, tana bashi amsa kai tsaye cike da rashin kunya. Bai dai kula ta ba ya gama tattara bayanan. Yacema Daddy zasuje anjima idan Hajiya Yaya ta tashi zasu dawo. Su kwantar da hankalinsu koma wanene in sha ALLAHU za'a kamashi, dan duk yanda akai yana da ala™a da su yasan sirrinsu ne natu™a.
        Addu'a su Daddy sukayi da godiya. ³an sandan suka wuce suka barsu jigun-jigun, sai shashshekar kukan Hajiya Basariyya. Babu abinda take hangowa sai gwalwagwalnta dana yaranta da takardun filayenta. Da farko Nazeerah bata Wauki abun wani serious ba. Sai da Baban su Hajiya Yaya da Yayanta da Baban su Najma suka iso gidan sannan ta fahimci al'amarin fa babbane. Sashen ta ta koma tai kiran Mamanta Sabuwa tana labarta mata abinda gidan nasu ke ciki. Itama Sabuwar hankalinta ne ya tashi. Yo an tattare dukiyar gida gaba Waya su kuma minene ribar wahalarsu. Yau sunga Suturewa. A rikice ta katse wayar ta kira mijinta tana sanar masa. Munafukin sai ya nuna ya fita rikicewa ma. A birkice yace masa ta sameshi a gidan Chalawan shi yayi gaba ma. Haka kuwa ta yayibi hijjab ta fice dan harga ALLAH a rikice take jinta. Yo duk fa wannan wahalar tasu da kasa zama waje Waya da bin malamai da bokaye akan dukiyar ne dai fa. Idan babu ita ai babu magana. Suda suke jira kawai Nazeerah ta sauka lafiya suga mi aka samu. Dan tsoron ma kar ace masu mace ce ya hanata Waukar Nazeerah suje a duba musu. Sai kuma suji wanan Wanyen aikin da rana tsaka haka ai basuga ta zama ba kam gaskiya.....

________&

        A hankali Maanal ke buWe idanunta. Tuni ruwan da aka saka

Please Login or Register in order to submit comment